tana tuntube da ghanan hajajju dake bakin kofar daki ,tana fitowa tayi ido hudu da aydarh murmushi tayi tareda karasawa gaban aydarh ta kamo hannunta tace Aseeyarh mi yahanaki karasowa ciki kallonta aydarh tayi tace babu komai ji take kamar zata fasa kara ji take kamar ta kwasa da gudu .hajajju dai na tsaye ta makale jikin bango tana kallon ikon Allah can taga baaba zata shiga tareda aydarh cikin daki dasauri tace yaaya mike damunki daga gani mata zaki shiga daki da ita minene haka baki tsayawa ma a tambaye a ji daga wace kasar aka aiko ta zata ki kama hannunta ku shiga ciki kallonta baaba tayi tace bana son shirme Aseeyarh ce fa,kankance ido tayi tace wacece kuma Asiya?ko dai itace adar? Baaba ta gyada mata kai tace ehh itace baki gane ta ba washe baki hajajju tayi tace billahi ban gane ta ba kiji yarinya kamar ana kara zana ta Allah mai halitta sai kuma ta fashe da kuka tace tau abunda zanyi saidai Allah ya yafe man amma dole tasani da kuma matan dasuka sak ani gaba sai kuma tayi shiru tace tau bismillah ada mu shiga daga ciki ita dai aydarh kallonta kawai take ,karasa shiga dakin su kai malik na zaune yana kallon t.v dasauri hajajju tarika su shigowa kamar an jifo ta ,ta zauna kusa da malik ta daure fuska kamar bai ta ba daidai sanda ta shigo daidai lokacin gabanshi yawani irin fadi har saida yadan dafa kirji yana mai karanto addua zaunar da ita baaba tayi a kujera kallo daya malik yayi mata ya dauke ido karamin tsaki yayi a ranshi domin tacika parlor da kamshi a tsarin shi baya son macen da take ado da kamshi da fizgar hankalin namiji yasan yanada kyau sisters dinshi na dakyau amma wannan nata yayi yawa tsaki yakara saki yana mai kwabar kanshi da gulmanta dayayi azuciyan shi,ko kallon inda yake batayi ba domin bata masan da wanzuwar shi a dakin ba,duk a takure take she is eager su bata abunda ta zo karba ta wuce bata gaishe da kowa cikin su ba domin gaisuwa ba halinta bane still bata cire shade dinta da yakasance black kanta na kasa tana juya black stone English gold din hannunta baaba tace Aseeyarh bara a kawo abinci ko?girgiza kai tayi alamar aa batareda tayi magana ba hajajju da ta hade rai ta mike tsaye tace yaya bismillah inada magana tayi hanyar fita baaba ta mara mata baya suka shiga dayan dakin hajajju tace yaya baa bori da sanyin jiki kwara ayi komai kafin yamma koh?
Ummi shine yah malik yatafi bai jirani bah?auta ce mai maganar tana wani bata fuska cikin shagwaba tana turo baki halime tace tau hala mu ba mutane bane da bamuyu complain ba da yatafi yabarmu? Aysha tace rabo da ita maybe she is only human being here autarh dai batace masu komai ba tayi shiru taji haushi da yatafi wajan hajajjun yabarta,mikewa ummi tayi tace sai kuyi hakuri ai kwa je gobe idan Allah yakaimu kafin ta koma kusan dai hajajju ba ta ban kwana,dariya aysha tayi tace hajajju ikon Allah ni da abby zai yarda da wallahi bin ta zanyi ina son zuwa kano da sauri halime tace idan abby ya yarda yah malik fa? Kuma fa dariya autarh tayi tace ahtau dole dai mutun ya zauna adamawa har aysha ta mike zata kwade ta ummi tace ba fa na son shirme ku tashi ku kama aikin gabanku da alamar hadari a garin nan ,yauwa ummi daman so nake mu juya tsarin dakinmu cewar halime,Maryam ta kwabe fuska tace ku kullun da aikin da za ku dinga jawo manah babu wanda ya tan ka ta cikin ,Abbyn malik ga ruwan can na kai bayi idan sanyi baiyi ba sai nasake sirka shi mikewa yayi yakamo hannunta yace Allah yayi maki albarka yabiya ki da gidan aljanna murmushi ummi tayi tace Ameen yah rabbi miji nagari .
Rufaidarh tace amma dai uktiee duk da halin da ake ciki yakamata ko saloon ne kije sharp sharp ayi maki sabo fa da Allah mutunan ya saba duk tafiyan da zaiyi yadawo zai tarar dake kal kamar amarya wannan karon kuma yazaayi kibari yadawo ya tarar dake babu lalle babu gyaran kai oum batace komai sai warware salkaqiyar sumar kanta baka sosai har gadon baya tashafa tace yanzu uktiee gashin nan fa babu abunda yayi and kuma na fiso yazo ya tarar dani ahakan domin tun kafin wanzuwar komai yasan akwai matsala ,hakane fa uktiee wannan ma wani tsarin ne saboda shi kanshi zaiyi mamakin ranshi gyaran naki,can kuma tayi murmushi tace uktiee n isai naga ramar nan dakikayi kamar ba wannan damuwan bane kawai anya uktiee tafada tana sake rike dariyar zaro ido oum tayi tace anya mi? Babu komai rufaidarh tace sannan tace ko dai aydarh zaa wa kanni ko kanwa ban sani bah hararar wasa oum ta ballawa rufaidarh tace saidai ke idan kin amince da doctor Ahmad sai kiyi mata amma nikam badani ba dariya rufaidarh tayi tace uhm ni kwana biyu ma ya hakuri ko waya bama yi oum tace ai laifinki shi pa gani yake kamar takura maki yakeyi shiru rufaidarh tayi domin bata shirya kare kanta wajan oum ba kan korafin ta kan doctor Ahmad din,oum tace uktiee nagani nake lokaci bai gudu kamar komai bazai faru a ya uba gyara zama rufaidarh tayi ta kamo hannun oum tace ki kwantar da hankalinki uktiee in sha Allah Komai zai tafi daidai karar ringtone din wayanta ke tashi tana dubawa taga abba ne da number shi ta Nigeria that means sunyi landing kyarma jikinta yakama kirjinta na lukude yana dugan tara tara cikin sanyin da jikinta yayi ta amsa wayar tamkar mai jin bacci ko wace take fama da kasala kuma agajiye sallama tayi daga can ya amsa tareda sanar da ita yana airport basai tazo ba tabar driver yataho kawai ya daukeshi da tau ta amsa tare mikewa tsaye duk wani nutsuwa ta, ta tanema ta rasa sai kai kawo take har rufaidarh ta fadawa drive sakon ta dawo oum ta tsaye zaunar da ita rufaidarh tayi tace uktiee ki nutsu ki kwantar da hankalinki nasan abba aydarh bai daukar komai dasauki amma in sha Allah abunda mu ka saka ma ranmu shima shine hukuncin shi Allah yasa uktiee Allah ya amince Ameen rufaidarh tace sannan tawuce kitchen domin karasa girkin da suke ita oum da kansu domin abba bayace girkin kowa idan ba na oum ba inhar yana kasar. Zama hajajju tayi tace am audul tashi zakayi ka dauke ni da ada mu tafi can gidan naku ai Ibrahin nan koh? Kallonta malik keyi ko kiftawa babu yace wacece haka? Sake daure fuska hajajju tayi wai ita ala dole taci serious tace zaka tashi ko sai na zab zabga ma mari,aydarh sam bata fahimtar su zufa ke tsatsafu mata a goshi da hanci zuwa yanzu har tayi ja ba karamin dauriya take ba amma marar kamar zata fito tsananin azabar da take mata duk baaba kulu na lura da yanayin ta cikin sanyin murya tace Aseeyarh ta shi ki bisu ki bashi key din motar naki ku tafi can gidan su sai ki karbi sakon ki wuce gida tau kawai aydarh tace tareda mikewa tabar key din kan kujera domin bazata iya mika mashi ba da hannunta bacin bazata iya driving da kanta ba kuma rufaidarh tace mata da ta karbo maganin shikenan ba amma da babu abunda zai sa tabar su ,su shiga motan ta ba ganin key din da tabari kan kujera yasa baaba dauka tamikawa malik bai ce komai ba yakarba yayi gaba shima.Bayan fitar malik da aydarh hajajju tayi kasa da murya tace yaya muna fita kema ki rufe wannan kurkukun ki tafi can gidan habibun zuwa yanzu ya sauka ku jirani acan kar ku damu zanyi komai kan tsari in sha Allah baaba tace tareda zama tana jiran tashin motar su sannan itama ta shirya tafita, back sit ta bude ta shiga tana hade rai ganin yanda yake wani shan kamshi yana wani isa trash shine abunda tace can kasa yanda babu wanda ma zai ji ta hajajju tafito da wata katuwar jikka da uban mayafi ta bude front sit ta hakimce sai daurewa take babu wanda ta tan kamawa cikin su shidai malik bai ce mata Komai ba duk da ya lura da daurewar da hajajjun keyi cikin kwarewa nutsuwa kamala yake driving yanda motar tayi fitting dinshi kana iya rantsewa kace tasa ce har suka isa anguwarsu babu wanda yayi magana cikin su ukun bin anguwar da kallo aydarh tayi kusan iri day ace da anguwarsu baabarh sai dai wannan gidan yafi gidan baabarh girma da kadan ko Parking bai gama ba hajajju tasako ta bude baya tace ma aydarh tasako ahankali aydarh tasako yau kam angama da rayuwarta zuciyarta har dace take ganin irin anguyoyin da oum tasaka ta zuwa a yau din gani take tamkar rashin aldalci ne mahaifiyarta tayi mata,hajajju ta katse mata tunani lokacin dake cewa malik tau dan cifil sifense kazama ba’a sani ba komai kawani tokare jikin kofa kamar wani rubabbe ba zaka kwankwasa a abude manah ba shidai kallonta yake he was speechless ganin lokaci daya hajajju ta juye tana ta masifa kamar ba ita tagama wasa da dariya ba dazo,knocking yayi halime ta bude.
Halime ta bude ganin hajajju tsaye kamar wata yar wrestling sai faman hura hanci take yasa ta washe baki tace yau tsofaffin kano ne a yola kenan?wata muguwar harara hajajju ta watsawa halime tace yau dai anbani muna ganin jafa’I kala kala bacin maganar da dan uwanki ya kwaso sai kin tsaya a kaina kina kallona kamar wata rubabba, shidai malik kallon hajajju yake sam ya gaza fahimtar abunda hajajju ke nufi to waye dan uwan nasu shi ko wa?to mi yayi? Kama hannun aydarh hajajju tayi suka shiga gidan aydarh sai bin ta take da kallo suna shiga hajajju tasaki aydarh,Ta fadi kasa kamar mai aljannu ta dinga kwarara ihu kamar wata tababba da sauri ummi da abby suka fito daga cikin daki suna kallon sarautar Allah ummi dai takasa cewa hajajju komai sai kallon aydarh take da mamaki domin har abada bazata taba mance fuskar da kamanin oum ba ko tayi rantsuwa babu batun kaffara wannan jinin habib da zarah ce to amma miya kawo ta gidan wannan wacce kala sabuwar kaddarar ce takasa ba kanta amsar ko wace tambaya a ciki yasa ta mara wa abby baya suka doshi inda hajajju ke ta zabga ihu tana kuka, mun shiga uku mun lalace wannan wace kalar rayuwa ce ibrahin kana zaman zamanka an yayo ma jafa’I an yayo ma bala’I ,abby was shock har kusan 5 mins abby da ummi na kallonta babu wanda yayi kokarin hanata domin sun kasa fahimtar komai sun shiga matukar rudani ganin aydarh da hajajju a gidan ga kuma malik tsaye ya zuba hannu a aljihu yana kallon ikon Allah,halime maryam da aysha suma duk sun tsore babu wanda yasan abunda ke faruwa sai kallon aydarh suke lokaci daya suka ji tayi mugun shiga ransu.shiru hajajju tayi ta goge idonta tass ta kalli abby tace ai batsaye za kuyi kamar matattu ba shiryawa zakuyi mu tafi aje asan yarda za muji da wannan bala’in ummi tayi karfin halin cewa hajajju mike faru ne? Shiru hajajju tayi sannan tayi mitsi mitsi da ido tace idan mukaje can kwa ji komai ,abby yayi ma ummi alamar datayi shiru sannan ya juya ya shiga daki binshi ummi tayi domin kaf ji take hankalinta da tunaninta baza su iya daukar duk abunda ke faruwa ba ,ajiyar zuciya abby yayi cikin sanyi murya yace Aseiyarh kisaka hijab dinki mu bi hajajju domin ni kaina a cikin rudani nake.Tafiya suke cikin mota babu wanda ke magana cikin su biyar din sai hajajju dake ta rusa kuka babu sararawa wallahi daza’a bude zuciya aydarh ji take kamar zata mutu wannan wasan kwaikwayon yayi mata yawa a kai daga karban magani sai wahalan da rayuwarta ake what’s all this? Hajajju tayi shiru tace tau ada yazaki barmu munata walagigi kan hanya bazaki gaya manah anguwar ba ?aydarh da bata fahimce tambayar da hajajju tayi mata ba tunda suka shigo motar da abby da ummi ta saukar da kanta kasa takasa hada ido dasu gabanta cigaba da faduwa yake sosai batasan dalili ba ga ciwon maran nata kamar kara karuwa yake tunda tafarawa malik kwatancan gidansu gaban abby ya yanke yafadi gidan habib? Shine tambayar dayayi wa hajajju shiru hajajju tayi kamar bata ji shi ba ummi dai kamar bata cikin motar tsabar yanda hankalinta yakasa kwanciya da tafiyar tarasa yanayi da zata saka Lamarin jujuya maganar hajajju take , tsaki malik yayi cikin ranshi yace wai wannan wace kalar yarinya ce komai nata kamar ba mutun ba who is she yasake jan dogon tsaki kasa da murya hajajju tayi tace Allah na tuba wannan abu dami yayi kama ibrahin ni bakina ma yayi nauyi wajan fadin wannan masifar sai kuma tasake fashewa da kuka,duk yanda aydarh ke faman riqe ciki tana zufa duk da sanyin a.c na kadawa ummi na lura da yanayinta kallo daya tayi mata tagane tabbas itace to amma mike faruwa ?mike shirin faruwa ? Wannan wane irin rikitaccan al’amari ne mai wuyar fassarawa yah rabbi kasa duk abunda zai faru yazama alkhairi tafada tana lumshe ido , sannu shine kalmar da ummi tacewa aydarh duk da bata gaishe su bata ko daga ido takalle su ba amma wani irin yanayi ummi taji game da ita lokaci daya yarinya ta kwanta mata rai,gyada kai aydarh tayi batareda ta amsa ummi ba still kanta na kasa bata dago ba abby da hankalinshi sam bai jikinshi sam bai ga abunda yafaru ba kuma bai ma kalli aydarh ba balle yasan wacece tunda bama sanin nata yayi ba.
Welcome sir tafada cikin sanyi da kuma raunin murya hugging dinta yayi sosai dukkansu ajiyar zuciya suka dinga saukewa zuciyoyinsu na musayyar bugawa kamshin jikinsu dana fatarsu na aikawa kowa sako cikin su ahankali ya zare ta daga cikin jikinshi yazaunar da ita kan sofa dake bedroom din nashi wanda yanayi bedroom din kamar show room shima kan sofa ya zauna tareda jawo ta ya kwantar da kanta akan shoulder dinsa yana shafa sumar kanta ta cikin Jersey veil din da tayane kanta dashi ,Zarahhhhhh yanda yaja sunanta sai da gabanta yafadi bata amsa ba sai ma kara riqe hannunshi datayi sake maimaita sunanta yayi yace zuciyata na bani akwai abunda ke faruwa wanda kike boye mun cikin sauri ta dago kanta ta zuba mashi ido kallonta yayi yace yes zarah akwai abunda ke faruwa kuma kin barni a cikin duhu girgiza kai tayi cikin sauri tana kokarin tsayar da hawayanta tace babu komai abban baby idan ma akwai ni kaina bansan ta yarda zan fara ma bayani ba kallonta yake ko kiftawa babu yace zarahhhhhhhh da dan karfi saukar da kanta kasa tayi batareda tayi magana ba zuciyarta bugawa take da sauri numfashin ta tsananta fita yake yah rabbi kaine mai kowa yah rabbi kaine mai komai yah rahaman ka gyara al’amarin nan shidai abba kallonta kawai yake ba haka yasaba ganinta ba duk sanda yayi tafiya yadawo ba yasaba riskar ta cikin walwala da annushuwar ganin shi wannan karon kuma tamkar ma bata da lapia tamkar wacce ke cikin matsananciyar damuwa da takura duk ta rame tayi haske asalin kyauwun fuskarta yasake fito tarr kamar lokacin da take shekarun kuruciyarta to mike faruwa? Mike shirin faruwa?shi kanshi yanajin wani yanayi na daban inalilahi waina illahil rajiun shine kalmar dayake maimaitawa a zuciyarshi yarasa gane kan oum sam duk yanda yaso ya lallashi ta amma abun yace tura kuka kawai take mai tsananin ban tausai zuwa yanzu hankalin shi yagama tashi yarasa ta idan zai fara mikewa yayi tsaye tareda kwantar da ita flat kan sofa yayi hanyar kofa da sallama yashiga parlor part din oum wanda yasan anan ne zai tarar da rufaidarh ko daya shigo bai ganta ba ya tambaye oum tana ina bata bashi amsa ba as well ya tambayeta ina aydarh nan ma tayi shiru sai aikin kuka take mashi duk da tasan duk dunia babu abunda ke daga masa hankali irin ganin hawayanta shi kanshi bai san iya adadin son dakewa zarah ba amma he knows that words will never enough to express his feelings on her,Mikewa tsaye rufaidarh tayi tare da fadadda fara ‘ar fuskarta tace ah masha Allah yallabai sannu dazuwa ya hanya anzo lapia? Duk tambayar da take mashi bai amsa kallon baabah dake sallarh kawai yakeyi zuwa yanzu kuma bai masan yanayin da zai kamanta abunda ke faruwa ba zama yayi cikin daya daga cikin cushion din parlor yana amsawa rufaidarh gaisuwar da tayi mashi yana tambayar su yasuke lapia lau alhamdulilah daga nan babu wanda sake magana cikin,zama yayi har baaba ta karasa sallarh murmushi tayi domin rabon data ganshi kila anyi 15yrs sam habib wani kalar mutun ne wanda shine tushe kuma shine silar faruwar komai a ahalin baki daya babu yabo babu fallasa suka gaisa duk da ba karamin nauyi da kunyar baabar ya keji ba shi kanshi yasan duk abunda ke faruwa amma sam bai damu ba shirune yabiyo bayan gaisawar dasukayi da abban kowa da yake sakawa a ranshi. Nikam adda aysha wai wacece wannan wadda suke tareda hajajju da yah malik? Naga duk a tare mu ka gansu koh tau amma adda mike faruwa ne hajajju na ta kuka kuma naga ummi da abby sun bisu tareda yah malik , ajiyar zuciya aysha tasauke tace dan Allah ku rabo dani kawai kuyi adduar Allah yasa komai lafiya Ameen suka amsa can maryam tace nikam daman na kara ganin ta ta burgeni Sosai ta iya gayu wallahi kallonta halime tayi tace nima haka wallahi aysha dai murmushi kawai take so take ta tuna idan tasan fuskar amma takasa. Wata irin zabura hajajju tayi gani gidan dasuka kazo da sauri ta kalli malik sannan ta juya ta kalli aydarh tace inalilahi waina illahil rajiun yau naga abunda ya isheni bai ishe Allahnah nan kuma ina ne jama’a ? Babu wanda ya tanka mata cikin su aydarh har wani ajiyar zuciya ta sauke ganin sun dawo gida kamar kan kaya take a cikinsu duk da babu wani datti ko alamar wahala a tattare dasu amma sam ta kasa nutsuwa cikin su cilla motar yayi cikin gidan yana mai tambayar kanshi tau miya faru miyasa zasu zo gidansu? Babu mai bashi amsar tambayar shi har ya paka motar cikin jerin motocin dake jere a parking space din aydarh da kamar jira take dasauri ta fita daga cikin motar kamar jira take tafita marar ta tawani irin murda har sai da ta saki siririyar kara dasauri ummi tace subhanallah tare da rike ta,wani irin murmushi hajajju tayi tace tau riketa mu karasa still malik bai fito daga motar ba yana ta kallon ikon Allah shi kam yau mamaki kala kala yake Sha, tsawa hajajju ta daka masa tace kai da baza ka fito ba hala wani abu yasami kafar ta ka ? Shidai bai ce mata komai ba yasa kafa yafito daga motar ya mara masu baya yana bin tsarin gidan da kallo tsaki yaja ganin yar ummi ke ta lallaba yarinyar kamar kwai itakuma sai wani narkewa take kamar wacce ke ciwon mutuwa. Wani irin harbawa zuciya abba tayi iya gigita ya gigita cikin wani irin yanayi yake binsu da kallo musamman malik dayake iya ganin zallar tsananin kamarsu dashi Abby yakasa saka kafarshi ma cikin parlor wani irin iska ke kada duk illahirin jikin shi wani sanyi ke ratsa zuciyarshi da ruhin shi,hajajju takaraso tane mi kujera ta zauna kusa da baaba da oum rufaidarh ma karasawa tayi ta taho da ummi dake rike da aydarh ganin yarda ta tsaya tsaye kamar babu numfashi a jikinta tsabar yanayin da ta shiga still bata saki aydarh ba ahaka suka zauna itama aydarh bata nemi hakan ba domin wata nutsuwa ke bin jikinta har cikin veins dinta wani sanyi ke ratsawa duk abunan abba bai lura da aydarh dake jikin ummi ba oum kau tun shigowar su tazuba masu ido tana jin wani rahama ta ko ‘ina to mi hajajju tayi haka dayasa komai ya cika tamkar gaske? Hannu abba ya daga yana nuna abby cikin rawar murya da tsoro yake furta ya..y…yarh ya…y..yarh kaine ko idona ne daman yayah kana adamawa har yanzu? Malik dake kallon su tamkar idonshi zasu fado yarasa gane kan komai hankalinshi da tunaninshi baki daya sun gaza fahimtar komai anan tsaye yake ko zama yakasa haka shima abby a tsaye yake yana jinjina girman da kuma ikon Allah wacce kaddara ke son tadawo baya wacce gaskia ke son bayanna kanta ashe suna da rabon sake ganin juna a duniyar nan Duk da yasha mafarkin hakan kuma kullun cikin ba ummi kwarin gwiwar faruwar hakan yake amma sam baiyi tunani yanzu ba baiyi tunanin kwana ku saba,Mikewa tsaye hajajju tayi tare da gyaran murya tace duk ku tsaya kowa sai wani gwale gwalan ido yakeyi ku da ko abunda yakawo mu nan din baayi ba har kun fara wani yan sane sane ku zauna kuji abunda yatara mu nan kafin ku cigaba da wannan ya tunane tunane ahtau ku tsaya kuji jafa’in da yaran ku suka kwaso zama sukayi kowa na mamakin maganganunta cikin abby da abba da ummi baki dayansu ta daure masu kai wasu yaran nasu?oum dai kanta na kasa itama rufaidarh haka while baaba hajajju take kallo tareda yi mata alamar datayi shiru ita zatayi magana dasauri hajajju tafashe da kuka tace aaa yayah wllh aaa dole nayi magana ki daina hanani dole nayi magana kowa ita yake kallo cikin su,kafin takira sunan abba tace habibu kaga wannan sai sannan abba yakalli direction din ummi da aydarh da hajajju ke nuna mashi, nagani hajajju kiyi magana manah kin sani a duhu mitsi mitsi da ido hajajju tayi tareda gyara zama tace tau tunda ga farko har karshe zan zayyana duk abunda yafaru domin niba’a munafurci dani ba oum kadai ba hatta rufaidarh da baaba saidai da hankalinsu ya tashi sun san halin hajajju tsaf zata iya watsa duk wani shiri nasu ta fadi gaskia amma kau da sunyi dana sanin involving dinta a case din sake fashewa da kuka tayi cikin muryar dattako abby dasai yanzu yayi magana tunda suka shiga yace hajiya kamata yayi kuyi magana ba ku dinga kuka ba duk kun bar mu a cikin duhu wani abu ya farune mutuwa akayi ko mai? Yoo Allah na tuba ibrahin ba kwara mutuwa ba da zagin da yaran nan suke shirin jawo manah.
Jawo manah ba still dakin babu wanda yayi magana kowa kallon hajajju yake banda rufaidarh oum da baaba da gaban su ke ta lugude hantar cikinsu na kadawa jiran jin abunda hajajju za tace, suke. tana matsar kwalla Takai 5mins ahaka sai tayi kasa da murya tace tau Alhamdulilah haka naso kuma haka na bukata mu hadu baki daya pameli domin mu yanke hukunci tare na’am shine abunda abby yace tare da gyara zama yana kallon hajajju gyaran murya tayi “tace tau saidai fa kuyi hakuri ita zuciya bata da kashi yara ne ka haife su baka haifi halinsu zamani ne yazo da haka habibu mai mace kuma kullun mai mace shi ake cuta kai zaka lallaba ka rufawa kanka da rayuwar ka asiri ka zubda makaman yakinka ka bada hadin kai abba dai bace komai duk a birkice yake sauraran bayanan hajajju, “sai kuma ta kalli abby tayi kasa da murya tace kai kuma sai ka goye bayan gaskia kayi adalci “zuwa yanzu jikin abby yagama yin sanyi yace in sha Allah hajajju zan zamo mai adalci a duk hukunci da zaa yanke,wayar ta fiddo daga cikin katuwar jikkarta keypad ce anyi mata mugun daure da rubber bands bugu daya tayi aka daga sannan tace bismillah ku shigo,within 2mins sai ga salma da doctor ashraff sun shigo gaishe da kowa na parlor sukayi sannan doctor ashraff yafara
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 83