Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
scent dinta yadinga bada wani super special din scent mai tafiya da imani har aka kira isha’I domin ba karamin bata lokaci tayi wajan shafa perfume din ba, salla ta kabbara,a masallacin ya zauna har akayi isha’I kafin yagama azkar dinsa, yadawo gidan lokacin daya dawo itama taga sallarh ta cire hijab inners ta gama sakawa tana kokarin parking hair dinta yakaraso yasa hannu yakarba yayi mata,kanta akasa tace thanks yace ki shirya kifito zamuje wani wuri haka nan taji dadin fitan nasu ta dago kai har zatace ina zasu sai kuma tayi shiru wardrobe din yabude yafiddo wani white plain yard an masa dinkin kaftani cotton yard ne mai azaban kyau duk da bawani tsada bane dashi amma yayi kyau perfume dinsa ya dauka sai comb ya fita parlor yashirya,itama wardrobe din ta bude kafin ta fiddo straight gown din da dr hafsa takai mata dinki tasaka tasake shafa perfume hijab tasaka har kasa kafin ta dauki lip balm ta sha,don zafin da lips dinta ke mata a tunanin ta ma taji rauni, kusan 10mins ta bata kafin ta fito,kamshinta ya riga ta karasowa,tunda ta fito yakasa dauke ido kanta “shi har rasa ma godiyan da zaiyi ma Allah yake kan wannan kyautar dayayi masa ahankali yake tasbihi, kafin yace Tabarakallah,kamshinta is very amazing a jikinta taji yana kallonta har ta karaso kafin ahankali tana wasa da rings din hannunta tace nashirya “yayi murmushi yace you are not looking bad you fine “sai sannan tadago kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta kafin tayi wani cute smile dayakara mata kyau kafin calmly tace you too Abba’s copy yayi murmushi yace let’s go gaba yayi tabi sa baya,har suka fita part din kafin yasa key ya rufe yasaka key din a pocket din gaban rigansa kasancewan gidan koi na akwai haske don akwai nepa hannunta yakama suna tafiya har suka fita kofan gidan suka kau yi saa suna fitowa sai ga keke,malik yafada masa sunan eatery da zai kai su suka shiga,ya zauna very close da ita saboda baya son yayi missing kamshin ko na one second duk da ko ba a kusa ya zauna ba zaiji saboda yanda kamshin ke da bala’In shiga rai babu mai magana cikin su sunyi shiru,duk kunya take ji ganin take kaman duk inda suka gifta sai an kallesu saboda yanda duk ya shishige mata,har bakin wani hadaddan eatery mai napep din ya sauke su duk da ba babba bane amma yayi kyau sosai eatery din mai napep din malik yabiya kudinsa kafin ya kama hannunta suka shiga eatery din,ai hankalin kowa kansu ya dawo mutanan wurin kaman sun ga t.v daga shi har ita babu mai son kallo duk sai taji ta takura ai kam tasake shigewa jikinsa tana rike hannunsa kaman wani zai kwace mata shi shikam fuskan nan babu yabo babu fallasa suka cigaba da tafiya har yanzu kuma duk idanun kowa kan su. Ganin yarda ake kallonsu non stop,gashi ya lura hakan yana affecting dinta sai sake shigewa jikinsa take,sake rike hannunta yayi Sosai “ har suka karasa can karshan eatery din “yaja mata kujera ta zauna kafin yajuya wajan waiter din “cike da respect ya gaishe da malik “amsawa yayi yana tambayar sa akwai wani wurin bayan nan?waiter yace masa akwai vip “ malik yace tau muje can din “hannunta yakama waiter yakai su har karamin parlor wanda yafi cikin eatery din kyau “wajan yayi kyau sosai ba na wasa ba, couples ne su biyu kawai mata da miji sai dan baby boy dinsu daga can karshe suke zaune “ kujera ce kawai a hade kwara biyu sai table a gabanta “ waiter yace yallabai mi za’a kawo malik yakalli aydarh ‘ kafin murya can kasa yace mi zaki ci?tayi shiru kafin tace grilling meat sai ice cream “yakalli waiter yace akwai grilling meat? Da ice cream? Waiter ya gyada kai yace asa onion da chill ne? Aydarh ta gyada kai ‘’malik yace je kazo da plate biyu sai scoop din ice cream daya,sai da waiter yatafi kafin aydarh tawara ido ta kallesa kafin tace baza ka sha ice cream din bane? Ya girgiza kai yace bana shan ice cream “Aydarh tace eyyerh yayi shiru hankalinsa na kan couples din dasuka iske wajan he wished shima rana irin haka zai zo masa a rayuwarsa duk da bai fidda rai ba amma he is eager shima yaga lokaci irin haka ganin abunda yake kallo yasata itama kallon direction din wurin babyn dake ta wasa hannun mamansa,fari mai kyau dan lukuti ‘yasata yin cute smile kafin ta kwantar da kanta bisa kafadan shi, jinta a shouldered dinsa turn him up shima ‘ahankali tace na karbo babyn? Malik yadago ta suna facing juna yace kinsan su ne?aydarh ta girgiza kai tace no I just like the baby ina son babies sosai,yayi smile har dimples dinsa suka loma, yace sai ki haifa kema tawara ido tana rufe baki tace ni din? Ya gyada mata kai ta girgiza kai cike da yarinta tace ance akwai wahala ni bana so na haihu yace waya gaya maki tace kawai nasani ni ai,yace tashi ki karbo sa tau “ki gaishe su first kinji? Ta gyada kai tajuya tanufe su ya dinga kallonta yakasa daina murmushin dayake yi, ahankali take tafiya kaman bata son taka carpet din wurin har takarasa kanta akasa tayi musu sallama,matan dake zaune bazata wuce saan Doctor hafsa ba jin wani irin kamshin dadi yasata daga kai tana kallon aydarh da murmushi ta amsa mata “ Muryan aydarh very calm and sweet tace good evening matan tace evening dear “kafin aydarh ahankali ta gaishe da mijin shima ya amsa mata da fara’a kafin yadauke kansa yana cigaba da danna wayarsa “Aydarh tace auntie zan dauke sa, matan tayi murmushi tace tau gashi Allah yasa ya yarda quiya ne dashi Aydarh tasa ahankali ta daukesa aikam hadda wangale baki yayi yana zillo,matan tayi murmushi tace abban farhan kagansa fa ya yarda,mijin yayi murmushi yace ah abunsa ai ganin dama ne, matan ta kalli aydarh tace anyi saa ya yarda Aydarh tana murmushi tana kallon boy din, duk da bawani iya daukan ta iya sosai ba tace zamuje dashi can tanuna direction din dasuke zaune ita da malik da hankalinsa ke kan waiter suna magana, matan tace tau shknn sis ba matsala amma dan Allah daga wani kasan kuke?aydarh tayi shiru kafin tace a adamawa muke matan tace Tabarakallah,amma kafin mu rabu sai kin gayamun sunan wannan perfume din nan naki,aydarh ta gyada kai kafin ta juya matan dai ta kasa dauke ido daga kan aydarh tayi masifan burgeta tana son dan gayu sai yau ta hadu da gayun dakansa hijab fa ne jiknta amma ji wani bala’In kyau datayi, kusa da malik takarasa ta zauna hannunta rike da babyn, malik yayi murmushi yana kama hannun yaron kafin ya karbesa ya daga sama “ yana masa wasa aydarh dai sai murmushi take malik yajuyu da yaron kafin yakalli aydarh yace miye sunan sa? Tace naji maman takira babansa da abban farhan so maybe he is farhan,malik ya gyada kai yace ki mayar dash isai muci abincin Aydarh ta shagwabe fuska tace nooo malik na kallonta bai ce komai ba ya gyara zaman yaron a jikinsa kafin yayi mata cutting meat din wanda yaji onion da pepper sai red chili this is her fave tayi missing grilling meat sosai,kasancewan yaron bai da riga wasan shi ya cigaba dayi a kan laps din malik yana jawo hijab din aydarh ‘ abincin suke ci babu mai magana cikinsu sai baby farhan kawai dake nasa yaran “jefi jefi malik ke kallonta ganin how passionate take cin naman, bawani dayawa taci ba tajawo scoop din tafara shan ice cream din ai kaman farhan na jiran tafara shan ice cream din ya fashe da kuka,yana mika mata hannu alaman ta daukesa murmushi tayi kafin ta shagwabe fuska tasa hannu ta daukesa tana ce masa sorry, malik yakasa dauke ido kanta ganin yarda take lallashin farhan din bakaramin kyau tayi ba da babyn farhan yayi lamo kanta jin yayi shiru yasa ta dago kanta suka hada ido da malik wani cute smile yasakan mata kafin ya dauke kai ya cigaba da cin naman sa ,ice cream din ta sake jawo wa nan fa farhan yasake tsala ihu “malik yakallesa kafin yakalli aydarh yace shi fa ice cream dinki yake so,aydarh tawara ido tace ice cream fa ai he is too young sir ko na basa?tafara kokarin basa malik ya rike mata hannu dasauri,ya girgiza kai kafin yakai bakinsa daidai kunnata yace ai shi baya iya shan ice cream saidai ki basa nono,dasauri tadago tana kawar da kanta shi ko kunyan maganan, baya ji ganin abunda tayi dinne dariya tazo masa amma ya danne bai yi ba,taki dago idonta ta cigaba da lallashin farhan a haka Wallahi duk yabata kunya ita, maman farhan tayi musu sallama ita da mijinta malik ya amsa yana ba baban farhan hannu sukayi musabaha,maman farhan tayi murmushi tace tau aunt din farhan mun gama zamu wuce “Aydarh tayi murmushi kafin tace laah kaman kar ku tafi , maman farhan tayi murmushi tace karki damu har gida zan kawo maki shi ya miki wuni, aydarh tace “dan Allah auntie?maman farhan ta gyada mata kai “ malik yace da munji dadi kam baban farhan yayi murmushi yace in sha Allah yallabai mungode sosai Allah yasaka da alkhairi,malik yace babu komai “Aydarh da kaman karta mika ma mamanshi shi, ta mika mata tana mashi waving hannu shi hannun yadaga yana so yayi mata amma ba wayon haka, murmushi duk sukayi ganin abunda yayi din,maman farhan tace muyi exchanging digits auntyn farhan sai ki gayamun sunan perfume din aydarh ta kalli malik tana wasa da yatsun hannunta da maman farhan takasa dauke ido daga kallon rings dinta,malik yace bara naba mai gidan nawa kwana biyu babu waya hannunta “baban farhan yawashe baki yace ba damuwa yallabai mungode sosai,exchanging number sukayi shi da malik, kafin sukayi sallama har suka fita aydarh nayi ma farhan bye bye, malik yayi murmushi yace there are nice aydarh tayi murmushi tace shima fa bye bye yake son yi mun “ malik yashafa kansa yace yes “ ice cream dinta ta cigaba da sha, malik ma karasa cin abincin yayi yasa tissue yana goge hannunsa da bakinsa kafin ya kalleta yace ayi miki take away ne na ice cream din?ta girgiza kai tace ah’ah fa ya isa,kasan a gida oum ma bata bari nasha “yace tofa why? Aydarh ta tabe baki tana langwabar da kai tace wai asthma sai sannan malik ya tuno dasauri yajanye scoop din yace ni kaina na shafa’a shiyasa nabari kika sha,kaman zatayi kuka tace pleaseeeeee sir only for today fa “malik ya girgiza kai yace no ya isa haka you will not take it anymore,ai kaman jira take sai hawaye sharr a kuncinta malik ya dinga kallonta ko kiftawa babu shi mamakin saurin kukanta yake, miye na kuka kuma yanzu,bai ce komai ba yajawo ta jikinsa ya dinga Patting bayanta without saying a word,jin kukan nata duk shagwaba ne ‘ yasa shi cewa shiii idan kuma bakiyi shiru ba you will feed me here kukan nan nasani, loosing har sai da gabanta ya yanke yafadi farko tayi tunanin abincin sai daga baya, ta fahimce abunda yake nufi lamo tayi kaman irin ruwa ya ci ta, murmushi yayi kafin gently yadago ta yace tashi let’s go it’s already late, hannunsu rike da juna suka karaso cikin main eatery din, sai dayayi payment kafin yasake mata take away din perfect cake da sponge sai red velvet yabiya yamika mata ta rike Leda kaman dazu ma haka yanzu few mutanan dake zaune wurin suka dinga kallonsu,this time kasancewan basu da yawa basu wani damu ba har suka fito bakin eatery ko ‘ina akwai nepa hasken glob tarr ya haskata,keke suka samu malik yafada masa inda zasu suka shiga, har kofan gida ya ajiye su malik yabiya kudin suka shiga,rike hannunta yayi har suka isa cikin gidan Ramlah na nan zaune bakin ventilations dinsu ganin su rike da hannun juna yasa ta dinga kallonsu ko dauke ido babu,kaman zata fashe da kuka ganin sunyi kaman basu san dawani hallitta zaune wajan ba, aydarh ta ganta shiyasa tasake shigewa jikinsa,shikam duk ya rude “ jikinsa yayi wani iri tun daga brain dinsa har toes wani vibrating yake masa shiyasa ko Ramlah bai lura da ita ba, idan ana sallarh ba’a magana,suna isa ventilations dinsu,malik yasa key yabude kofan part dinsu da sallama suka shiga “ yasa hannu ya kunna fitilan parlor yakama wrist dinsa,kafin yace na gaji yanda yayi din yasata yin murmushi tace sorry nima nagaji, yace eyyerh kije kitchen ki ajiye ai bazaiyi melting ba right? Ta gyada masa kai tace whipped cream din ne zaiyi melting amma zan sha a haka yace tau shknn kitchen ta shiga ta ajiye lokacin da ta dawo parlor har yashiga bedroom,sallama tayi tashiga taga bai cikin bedroom din karan ruwa taji alaman yana toilet kenan “kofan toilet din ta kalla for few seconds kafin ta dauke ido hijab din ta cire ta linke kafin ta bude wardrobe har zata ciro bubu gown din ta ta tuna yarda ya dire ta ranan “rufe idonta tayi don har bata son tuna yanayin sa a lokacin ta tabattar da ba don dr hafsa tazo ba har lahira yana iya kasheta, dayan gown din wani cotton material white anyi mashi touches da pink,sai hula pink sharp sharp ta cire rigan jikinta da niyyan tayi sauri tasaka kafin ya fito bayin,amma ina tana kokarin saka rigan already ta cire waccan daga ita sai bra da undies ai gashi yafito da karamin towel a hannu yana goge sumanshi alaman wanka yayi kara tafasa tana saurin saka rigan shidai mutuwan tsaye yayi yana kallonta kawai “kafin ya lumshe ido yana cigaba da yamutsa suman kanshi billahi Ko kallonta yayi sometimes sai yayi loosing shiyasa yanzu kullun cikin wanka yake kaman duck, tana gama sakawa ta juya masa baya gabanta na sake faduwa ita dai tashiga uku yariga da yagama da ita yanzu inda yayi saura bai gani a jikinta ba bai da yawa gashi ko kunya kallonta bai yi ahaka ita ko da singlet da boxers bata iya kallonsa,hawaye ya taru a idonta tana turo baki bai ce mata komai yazo yabude wardrobe ya fiddo jallabiya yakasa kafin yakoma toilet din ya shanya towel din yafito, shimfidansa yayi ya kwanta yana juya mat abaya itama can karshan katifan ta koma ta kwanta tayi lamo tana rufe har kanta da duvet sai kusan bayan 10mins kafin yamike ya tafi kitchen maganin daya siyo jiya yasake sha yadawo yakashe wutan ya kwanta. Tunda gari yawaye haka kawai yaji sa duk wani kala bazai ce fargaban haduwa da dr usama bane aaaaa kawai tunanin makomar rayuwarsa yake idan ya cigaba da zama ahaka zai halaka kanshi ya lura ita yarinyar har yanzu da sauranta dole ya ajiye nashi miskilancin domin shi ke cutawa ba ita ba sonta na neman kasara shi, duk wani aikin gida atare suka yi sa yau,ruwan tea kawai suka dafa taci basai sunyi breakfast bas ai su hada da cake din “tun safe ta lura da yanayin sa duk bayan seconds sai ta kama sa yayi shiru yana satan kallonta,yanzun ma nan suke kan carpet ‘ suna breakfast duk tana lura dashi yanda yake shan shayin kaman an ma sa dole yayi shiru looking so disturb,ahankali ta matsa kusa dashi tace sir “nakara ma ka sugar a shayin ne? Sai sannan ya dago ya girgiza mata kai kawai,takasa dauke ido kanshi ita fa seeing him like this didn’t suit her mind, tayi shiru kafin can tace are you sick? Ya girgiza mata kai kafin ahankali yaja long pointed nose dinta yace am okay dear just eat badan ta gamsu ba kawai dai ta gyada masa kai, domin bata son takura sa, wayan shi yayi ringing yana dubawa yaga dr ibrahim ne picking call din yayi suka gaisa kafin dr ibrahim yace dr faisal yakira ka?malik yace aaaaa bai kira ba, dr ibrahim yace kila wani abun ne ya dauke masa hankali malik yace ba mamaki, wani abu?dr ibrahim yace no yace muje after isha’I lokacin ne dr usama yace muje din “malik yace tau Allah yakaimu dr ibrahim yace Ameen kafin yace mu hadu bakin clinic zai fi kusa right?malik yace ohk kafin sukayi sallama yakashe wayan “Aydarh na juya teaspoon din hannunta cikin kofin shayin takallesa tace ko nasake hada ma wanda babu madara? Yace eh hada mun mikewa tayi ta nufi kitchen after five minutes sai gata tafito da wani kofin rike ahannu a gabansa ta ajiye kafin tasa sugar ta mika masa karba yayi idonshi kanta yace thanks cuddle bug ‘tayi murmushi kadan tace anytime sir “mayar mata yayi kafin ya cigaba da sipping shayin kadan kadan itama p cake din ta cigaba da ci,hankalin ta nakanshi haka nan taji bata son ganinshi a wannan mood din. Ta dinga bin kofin shayin da kallo ganin ya ajiye ko rabin shayin bai yi ba,kallonsa tayi fuskanta cike da damuwa “tayi kasa da muryanta tace you are not okay sir just tell me what’s wrong please,malik yayi murmushin karfin hali ya girgiza kai kafin yace am okay dear ,tayi shiru tana dai kallonsa amma bata tasake cewa komai ba shima bai sake magana ba yayi shiru ya lumshe idonsa tunani fal aransa, can ta mike ganin kaman shayin ya ishe sa don ya ma barsa har ya huce, kwashe kayan tayi ta wuce kitchen ta kai sai ta wanke kafin ta sake goge kitchen din ta fito ‘ ta sake kallonsa for few seconds, kafin ta dauke kai ta shiga bedroom din kan katifa ta zauna jikinta a sanyaye haka kawai tasamu kanta da rashin jin dadin yanayin dayake,ahankali tazame ta kwanta tana rufe idonta zuciyanta na mata ba dadi, kawai seeing him in suchs situation duk sai taji itama jikinta babu dadi,duk bayan few seconds sai taji kaman ta tashi taje ta duba sa sai kuma ta zauna kasa hakura tayi kawai ta mike, walking very slow tabude kofan tana kallonsa zaune yake yahada kansa da gwiwa,ta dinga kallonsa ko dauke ido babu,gently ta dinga tafiya kaman mai counting steps dinta har ta karasa kusa dashi ta zauna kafin tamika hannunta ta dago kansa, ya zuba mata idonsa yana kallonta kaman wanda ke ciwo, tace sir wai mike damunka hannu yasa ya jawota jikinsa ya kwantar da kanshi a shoulder dinta,ahankali yake sauke ajiyan zuciya yana fesar da numfashin mai zafi a wuyanta lumshe ido tayi tana sauraron bugun zuciyanshi kusan 30minutes suna ahaka babu mai magana cikinsu kafin gently ya zare ta daga cikinsa kaman wani ciwo yakara ma kanshi mikewa yayi yawuce toilet ta dinga kallonsa ko kiftawa babu yanda yake tafiya kaman wanda yayi ciwo, har sai da yashige toilet din kafin ya janye idonta,mikewa tayi kawai ta shige bedroom. Tace tau ai bansan baka son chili dayawa a noodles ba,yayi shiru kafin yace ai ba yawa yayi ba kawai dai ina jin zafi kadan kadan a chest dina,tace ko dai ulcer ne sir? Malik ya girgiza kai yace ai bana jin sign din ulcer kawai dai yanayi ne tayi shiru tana kallonsa kafin tace to na Chanza maka wani abincin ko shayi? Ya girgiza kai yace zan ci ahaka ai kin sha aiki kuma just rest now tace “to”shiru yayi yana cigaba da cin indomie dinsa, kafin can yadago kai su hada ido tayi saurin dauke kanta,murmushi yayi kadan yana girgiza kansa this is not the first time a yau da ya kamata tana kallonsa sai kuma idan suka hada ido tayi saurin janyewa tana pretending as if ba kallonsa tayi ba,kanta kasa ta cigaba da fidgeting fingers dinta,ita bata masan ya akayi ba those this kawa isai ta shagala tana kallonsa yana dauke mata kewan abbanta sosai saboda kama suke ba nawasa ba da abba,karasa cin indomie yayi yasha ruwa,kafin ya mike da plate din zai kai kitchen dasauri ta mike tana karban plate din tace sit sir I will do it murmushi yamata ahankali yace thanks cuddle bug, batace komai ba ta karasa kitchen takai plate din kiran salla la’asar yasa shi mikewa yashiga toilet sai dayayi wanka kafin ya dauro alwalla yawuce masallaci, itama dakin tashiga tanada alwalla sallarh ta kabbara. Farin shadda dasuka dinka a auran dr ibrahim yasaka “ kayan cikin kawai yasaka bai daura babban rigan ba,ita dai sai satan kallonsa take ya bude kwalban perfume dinsa ya fesa,Allahumma bareek billahi malik ko yaron qatar president sai haka he looks more than handsome,yayi wani irin kyau kaman balarabin qatar, black shade yasaka yah rabbil alameen, yafi kyawu kyau “Aydarh dai takasa hakuri,muryanta very calm tace sir ina zakaje?da har zai jata sai kuma ya tuna wani abu sai yafasa,yajuyu yakalleta kafin yayi cute smile yace zamuje wani waje da Doctor,aydarh tayi shiru kafin ta gyada kai ta cigaba da wasa da yatsun hannunta, har yakai kofa zai bude kafin ya juyu yace say a prayer for your handsome husby “Aydarh tayi saurin janye kanta kafin tace Allah yadawo da kai lapia “yace Ameen yace tau kuma baki ce nayi kyau ba ,murmushi tayi ahankali tace Tabarakallah masha Allah Allahumma bareek yayi murmushi yace Ameen yah rabbi sai nadawo take care waving hannunta tayi masa kafin tace you too.kaman yanda suka tsara haka malik ya tarar da dr ibrahim bakin clinic yana jiransa,Doctor ibrahim dai yakasa rufe baki yana kallon malik ‘yace ni wannan kyau haka karka firgita mata kano fa,wannan kyau haka kaman dai zamuje gasan kyau ko hula ya bazaka saka ba kenan nan gaba zaka dinga parking gashin nan naga yau suman yafi kama da nalaraba ko indiyawa ma zance,malik yashafa kansa yace it’s already late muje kawai baka rabo da abun dariya, keke suka samu har nasarawa G.R.A aka kai su bakin wani mad mansion aka ajiye su,malik dai yakasa dauke kansa daga gidan,bawai kauyanci yake ba aaaa kawai dai gidan yayi masa kama da gidansu Aydarh dr Ibrahim ya kallesa kafin yace kodai kiransa zamuyi da kyar securities din gate dinnan su barmu mu shiga,malik yayi shiru kafin yace no kawai muje maybe yana tare da iyalinsa fa,dr ibrahim yayi murmushi yace ai baida iyali shi malik dai yayi shiru amma yana mamakin magana dr ibrahim din,hanya hadaddan gate din suka bi,yayi knocking securitie yabude yana kallonsu already dr usama ya sanar masa da zuwansu, murmushi yayi yabasu wuri suka shigo gaisawa sukayi kafin yace su jira sa nan yaje ya sanar masa,bayan security yatafi dr ibrahim yakasa shiru,yace yallabai kaji gida kaman baa mutuwa kuma fa daga sh isai securities dinnan suke rayuwa ko maids babu idan baya Nigeria su kawai ke zama a gidan nan fa,malik yace Allah sarki “kafin yayi shiru shima dr ibrahim shiru yayi can sai ga securitie yadawo kafin yawashe baki yace bismillah ku iso,daga bakin gate din zuwa main entrance din gida Akwai tafiya ba laifi tunda gidan kusan anguwa guda ce, malik da ya lumshe idonsa tasbihi yakeyi har suka isa cikin wani babban parlor dake nan kaman show room wani mahaukacin royal cushions ne a parlor babu hayaniyan kayan decoration sosai sai babban t.vplasma dake aiki koi na kal kaman a turai babu dirty ko kadan sai kamshin wani freshener mai sirin kamshi ke tashi a parlor ga a.c dake nasa aikin securitie yace musu bismillah ku zauna yanzu yashiga cikin in the next five minutes zaku gansa ya fito shi yace ku shigo dr ibrahim yace tau badamuwa mungode, securitie yasa takalman shiga kitchen din tsaban zaman turai yasa ko ‘ina zaka shiga a gidan da shoes din wajan kitchen din yashiga kafin yabude fridge din ya fiddo da fresh apple green manya masu kyau yayi sliced dinsu kan wani clean bowl sai daukan ido yake kaman irin sabo dinnan dagani kasan tsaban kudi aka zuba wajan siyan sa, flask din coffe ya bude ya zuba musu a mug biyu kafin yadawo parlor yakawo musu “ bottle water yakawo musu kafin yayi musu sallama yace sai sun fito bara

Chapter 32 of 83