mulki a gida “malik dai yayi shiru yana sauraron inna,mikewa tsaye tayi tashiga daki,can sai gata ta fito hannunta rike da kula da kuma jug “tayi kasa da murya tace bara nashiga na kai mata abinci saboda idan bani na kai mata ba saidai fa yunwa ta kashe ta wallahi bazata fito ta dauka ba,malik dai nata kallon drama inna, inna ta kalli dr hafsa tace nasan daman dawuri zaki taso shiyasa nace bara nayi kokarin gama girkin da wuri ita dai dr hafsa bata kalli inna ba ta cigaba da linke lab coat dinta, inna tayi kasa da murya ta kalli kofa tace wai zararra ce ni ko mi ina magana kinyi shiru kin maidani kamar wata yar iska dai, dr hafsa tace wai ba naga bak’o gareki ba? Ki fita ki same sa manah abinci ne dai kin kawo kuma nagode, sai nafara yin wanka kafin,inna ta tsuke bakin ta tace tau Allah yabaki hakuri bara na fita kafin ki zage ni kuma”,tana fitowa tace yawa daman ai na gaya maka nice daidai da ita, malik yace ayi hakuri dai ni bara na koma naga magrib ta kusa, inna ta washe baki tace tau ba laifi ka gaishe da mai dakin naka nima nasamu lokaci sai nashigo na dubata, har kofar gidan inna ta rako sa labari kau kamar kar yatafi inna takasa shiru. 6:00pm daidai yashigo gidan ,Ramlah na zaune a ventilation dinsu ita da mahaifiyar ta sai dayar matar part din fadila da yaranta biyu maza da mata, su biyar ne wurin amma kamar mutun dari fada suke sosai kan Ramlah ta bige yaron fadila musa aiken sa tayi bai je ba tayi magana yace bazaije aiken karuwa ba,ta dakesa uwarsa tace bazata yarda ba ai gaskia ya fada, shine suke faman wannan masifar, ko kallon su bai yi ba yayi wucewar shi part dinsa, dawani irin mayyan kallo Ramlah ta bisa ta mance ma shaf da abunda sukeyi, har sai daya shige building din part dinsa ta daina hango shi domin an zagaye ma kowa ventilation dinsa, fadila tayi gyaran murya tace haka fa aka yi, Ramlah ta maka mata wata wani shegen harara tace tau uban miye yayi ruwanki da ni?maman Ramlah tace duk ba wannan ba kuyi shiru, tayi kasa da murya tace ma fadila “ shin fadila kinga abunda nake gani kam? Fadila data saki baki tana kallon maman Ramlah tace nagani tun jiya abun ke ci na hakuri nayi kawai banyi magana ba wallahi, maman Ramlah tace tau wai balarabe ne ko mi wannan din? Fadila tace wallahi tun jiya dana ganshi nake tambayar kai na tau baki nan shiyasa na ja bakina nayi shiru (kamar basu bane ke fada yanzu) Ramlah ta tabe baki tace ba fa balarabe bane kawai dai haka yake, maman Ramlah tace ki bari baban musa yadawo kila ma ji magana daga wurin shi,fadila tace in sha Allahu saidai idan basu hadu dashi ba amma nasan sai ya tambaye shi wayeshi,kin fa san halin sabo, Ramlah tace ku kwantar da hankalin ku zan binciko maku komai ni fa ai naga miji wurin nan, fadila ta tabe baki tace ko makaho yasan wutsiyar ragumi tayi nesa da wuyan zakara “ maman Ramlah tace aa fadila mi kike nufi?fadila tace babu komai bara na tafi kafin sabo ya shigo,
Sai daya fara shiga kitchen ya daura ruwan zafi kafin ya fito knocking yayi saboda ya taba kofar yaji ta a rufe, sai dayayi almost 8mins atsaye yana knocking kafin a bude kofar ahankali ta bude masa kofar ta juya ciki, bin ta yayi da kallo ganin abunda tayi masa a rayuwa baya son raini ya tsani rashin kunya,bai ce mata komai ba itama hakan ko kallon sa batayi ba kanta na kasa tana wasa da Expensive diamond ring din hannunta,plates din daya kawo mata abinci yabi da kallo ba laifi taci sosai saidai ga yajin nan gefe guda da alama bata son yaji dan bata ma taba shi ba saidai star din kawai eggs din kuma daya kawai tace ga sauran two din nan danwaken ma gashi nan ledan maganin ta ya dauka yanzu ma tasha daga yau ya kare daman na 3days ne kawai, kallonta yake ko kiftawa babu so yake ta dago idonta yayi mata concrete warning kan rashin sallama amma tak’I baya jin kuma sai iya yi mata magana tayi shiru ta kyale sa saboda ko saar maryam auta bata wuce ba bazaiyi tolerating shits ba, bai ce komai ba ya kwashe plate din ya fita dasu da harara ta bi bayansa a ranta tayi karamin tsaki , kwanciya tayi ta rufe idonta daman can bata saba zama cikin mutane ba ,shiyasa bata jin kadaici ‘Ko a gida sai ta wuni bata fito ba,a can school Cyprus daman idan ba lectures zatayi attending ba bata fita daga campus dinta, her life is always private bata da friends bata jin magana ya hada ta ko sau uku ne dawani a school din tun zuwan ta duk da yanda school din yake akwai yara masu yawa yaran masu hali ne,amma bata gani akwai wanda zata iya zama dashi balle har a kai da wani abu wai friendship.sai da ruwan yatafasa kafin ya dauko bucket ya juye mata, this time ma bata amsa sallaman shi ba, bai ce komai basai da ya kai ruwan toilet yafito ya zuba mata ido mistakenly ta bude idonta suka hada ido dashi wani irin fadi gabanta yayi tayi maza ta saukar da kanta kasa, ya kafe ta da waennan idon nashi , cikin tsare gida da muryan nan tasa babu alamun wasa yace “baki iya amsa sallama ba hala ? Sai taji wani iri da tambayar tasa abun yazo mata wani kala,shiru tayi batace komai ba, yace “daga yau kar nasake sallama naji kinyi shiru “ bai jira amsarta ba yayi ficewar sa daga dakin, sai time din ta dago kanta idonta cike da kwalla , umarni yake bata kenan? Ita yake ba umarni ? Saboda yaga bata da kowa sai shi babu inda zata je sai wajan shi? Who is he? Mi yake daukar kanshi? Mi ma yake nufi da ita ne wai? Tayi ma kanta tambaya kusan goma amma bata da amsar ko daya,hawayen ta tasa bayan hannu ta share tass tayi ma kanta alkawarin baza ta sake takura kanta ba ko daura ma kanta damuwa,kuma shima bai isa ya daura mata damuwa ba ko ya juya ta,idan girman kai yake ji dashi ta fisa idan izzgili yake ji dashi ta fisa, hararar datayi ma kofan dakin sai ka rantse da Allah malik ne tsaye a gabanta, toilet ta shiga nan taga bucket din ruwan zafin da ya ajiye mata, kallon bucket din take ko kiftawa babu ita yakawo ma wa kenan? Tunda taga shi baya using da wannan toilet din,tsaki ta saki kafin ta fito cikin dakin ta cire kayanta ta dauki towel ta daura, Sai da tayi wanka tsarki dan tagama period kafin tayi wanka ta fito, kamar dazu yanzu ma Vaseline da tashafa da perfume din abayar ta mayar ta koma ta kwanta. Daga masallaci daya fito garin dinke yake da hadari tunanin abunda zai yi masu na dinner yake mai awaran daya gani a gefen gidan su kawai ya yanke shawaran siyan masu,sallama yayi yarinya ta amsa wurin a share yake tass da alama awaran na da tsafta na 500h yasiyan musu ya wuce. Kofar dakin ya tura this Time bata saka key ba sallama yayi yaji shiru bata amsa ba,karasa shiga dakin yayi ya ganta tana salla,murmushi yayi iya lips dinsa yafice daga dakin a plate ya saka mata awaran kafin ya zuba tasa a warmer , sallama yayi ta amsa sa can kasan makoshi kamar wace throat din ta ke ciwo mamakin halin yarinyar yake,ta idar da sallan still kuma tana zaune kan prayer mat din “ bata tashi ba ajiye plate din yayi ya fita.
TWO WEEKS LATER
Zuwa yanzu malik ba karamin sabo yayi da inna ba sosai suka saba kullun ne da yamma sai yashiga gidan indai kau baije baya tare da dr ibrahim suka fita wanda yanzu ya zamar masa kamar wani dan uwa tsakanin sa da aydarh har yanzu babu mai ma dan uwansa magana, kullun ne sai yadafa ma ruwan wanka ya kai mata abinci kau babu fashi kullun sai ya girki duk wani gyaran gida shi yakeyi,ya fuskanci abubuwa dayawa game da ita,wani lokacin idan tayi wani abun dariya take ba sa akwai ranar da inna ta matsa mashi sai sunje ta ga mai dakin sa, suka tafi tare shiga yayi daki yasame ta tsaye inda take tsayuwa kullun tana kallon mutanan gidan,bai san mi zai ce mata ba kawai yasa shi cewa ga innata nan zaku gaisa batayi magana ba dan batasan wace inna ba. Kayan ta kala biyu ne daga gown din atampha sai abayar ta wllh ta gaji da saka su bra daya take using idan tayi wanka ta wanke sai ta zauna haka har sai ta bushe sannan ta mayarda,abayar ce jikinta ta daura kallabin akai fita parlor tayi wanda bata cika zama a nan din bas ai idan baya nan ko kuma an dauke nepa tazo ta tukure kanta waje daya shidai yana ganin abunda takeyi baya tankata ya fahimce yarda take tsoron duhu hakan yasa shi siyan mata torchlight indai babu nepa ta dinga haske haske kenan, Ahankali take tafiya har ta iso cikin parlor kasancewar yamma ce akwai nepa hasken globs din parlor sun haske fuskarta tarr kullun kara kyau take sometimes malik har mamakin ta yake yakan tambayi kansa wai mata haka suke ko kuwa? Wani lokacin dr ibrahim neke yawon kawo masa zancan mata da zamantakewar aure har wani zakewa yakeyi shima yakusa shigo daga ciki yaji abunda suke ji, shidai malik saidai yayi murmushi kawai har mamakin dr ibrahim yakeyi shi baya kunyar ko wace magana “. Murmushi kadan a fuskar ta,ta zauna kan carpet din parlor tana gaishe da inna dake ta faman zara ido kamar wacce aka tsikara haka inna ta mike tsaye tana kallon malik da aydarh tasake bude idonta sosai kafin ta koma ta zauna tace Allah mai halitta sai kuma ta kalli malik tayi kasa da murya tace audu ashe kafini gaskia danace boyun matarka kake ashe dole ka boyeta, masha Allahu sai kuma ta washe baki tace tsali yo Allah na tuba audu ku wannan kamar dai ku aka hada ma wa, sai kuma taja bakinta tayi shiru tace ah babu ruwana balle ace nayi sabo amma wannan dai wannan dai sai kuma tayi shiru,shidai malik sai kallon inna yake aydarh ma tarasa abunda zata ce mata, inna tace ya sunan ta kace?ahankali malik yace ASSIEYERH yarda yafadi sunan kamar da larabci yasa inna kasa fahimta yarda yafada , zata sake magana akayi knocking kofan part din nasu malik yace waye muryar dr hafsa suka ji tana fadan ita ce, bude mata malik yayi inna tadafe kirji tana kallonta tace yanzu kuma haka kika zama ni hajara nabani, tayi kasa da murya tana kallon aydarh tace kiji bala’I daga taji labarin nazo nan har ta biyo ni, dr hafsa dake gaisawa da malik ko ta kan inna bata bi ba, ta kalli aydarh tace patient daga rana ban sake ganinki ba kuma saidai yallabai murmushi aydarh tayi tace ina wuni dr hafsa ta amsa tana tambayar ta ya jiki, labari sukeyi duk da inna ce mai labarin ita dai aydarh murmushi ne nata,malik kau da har yasaba fira da inna biye mata yayi suna fira, ana labari da dr hafsa tayi magana sai inna ta kwale ta sai wajan six suka yi sallama zasu tafi har waje suka rako su dr hafsa da ta daga waya tayi gaba sai inna a bayanta aydarh a bayan inna malik ke can bayan su, har suka fito building din parts dinsu inna batayi shiru ba, ganin tana neman fita yasa shi jawo………
Kallonta yake ko kiftawa babu itama ido cikin ido take kallansa ,kasa yayi da murya cikin tsare gida yace duk ranar da kika kara kokarin fita a haka babu hijab sai na karya ki,yasake ta yafice “anan tsaye yabar ta mamaki ya cikata har kofan gida ya raka inna sannan yadawo, bata parlor yasan cikin daki ta koma, hakan yasa shi yin zaman shi a parlor kwana biyun nan kudin hannunshi sun kusa karewa,shiyasa yake so idan anjima suyi shawara da dr ibrahim kan abunda zaiyi.Dakin yashigo ko kallansa batayi ba yana tsaye kanta “ta turo baki “tace nan da ka tsaya mun akai fa? Malik mamaki ne ya cikasa, sai yaji kamar bai ji da kyau ba, yace dani kike duk yarda gabanta ke faduwa na masifan tsoron shi da yanzu ta yarda tanayi bai hanata ,mikewa tsaye ba tace erh, bai ce mata komai ba ya fice daga daki “ . Kallonshi yakeyi har sai da yayi shiru yace tau shknn na fahimta Allah yakaimu lapia, dr ibrahim yace Ameen “shiru ya biyo baya dr ibrahim yamike tsaye yace bara na fita na jira ka kar time ya wuce,malik ya kalli watch din hannunsa yace har na kusa mantawa ma fa ashe yau ana wasa “ dr ibrahim yace sure kayi sauri mu tafi, fita dr ibrahim yayi kofan gida,shi kuma malik ya juya yashiga kitchen indomie daya dafa masu ya zuba mata a plate sauran tasa kuma ya zuba a warmer, salla take sai da yatsaya kallonta yake ko dauke ido babu,ganin yarda take salla ajiyar zuciya ya sauke tareda girgiza kai kwata kwata ba a daidai take sallan ba hakan na nufi bata iya ba ko mi? Har tagama kafin ajiye plate din hannunsa yace ki kashe globs kuma din kafin ki kwanta bazan dawo da wuri ba, batace komai ba shima daman baiyi tunanin zata ce din ba,yayi ficewar sa, kusan five minutes tana kallon plate din indomie hawaye yazo mata a ido tashare ashe zata iya saba wa ahaka ashe zata iya rayuwa dasu ashe zata iya cin cimar su?zuwan inna yau sai ya wanke mata kashi ashirin cikin dari na damuwan ta ashe suma suna rayuwa cikin farin ciki, kullun sai ta tsaya bakin window bedroom dinta tana hangen yarda yan cikin gidan ke shiga da fice zuwa yanzu ma tasan fuskokin su,sau dayawa zataji suna fada wanda kullun ma cikin haniya suke, share hawayen ta tayi ta jawo plate din tafara cin abincin kaman bata so, halinta ne rashin cin abinci shiyasa bata ci dayawa ba ta mayar kitchen ta rufe kamar yarda taga yanayi, shimfidar shi da ya fito ta bi da kallo tana karamin tsaki ta shige daki haka kawai taji bazata yi abunda yace din bas ai taga yarda zaiyi, a ranta tace shi kullun Kamar wani force ya dinga daure fuska yana magana Kamar baya so, trash tafada kasa kasa, ta je ta kwanta kasa bacci tayi domin ba ta iya bacci cikin haske ka’ida ne shi ke kashe mata glob,yau kuma daya sata kashewar bazata kashe ba so take ya dawo taga abunda zaiyi tunda shi komai na masifa ne bala’i’a kawai ta fada kasan ranta. Bayan yagama duk wani aiki da shi keyi na gidan ya kai mata ruwan wanka tayi, sai da yabari ta shirya kafin ya shiga dakin ya jingina da kofa yayi folding hannunshi a kirji straightly yake kallonta da waennan idon nashi , kanta na kasa bata dago ta kalle sa ba tana dai jiran abunda zai ce, babu wasa a muryar shi yace I asked you to off the globs yesterday and you refused to do sures why, wani banzan kallo tayi mashi sai kuma tayi saurin janye idonta ta juya masa kai, tace I can’t “ wallahi banda umarnin ummi ba yarda yake da zuciyar nan baya son raini da rashin kunya da yau kam sai ya balla yarinyar nan,shiru yayi yana cigaba da kallonta still bata juyo ba tana yarda take,takawa yake ahankali kan carpet har ya kusa zuwa inda take,dawani irin mugun speed ta mike ta manne a can karshan wall din dakin tace wallahi’bada kai nake ba don’t beat yarda jikinta ke shaking yagane ba karamin tsorata tayi ba amma rashin kunya bata hanata murguda masa baki ba, sai dayazo towards her sun kure ma juna sosai numfashin ta na barazanar fita ta rufe idonta gam yana iya hango yarda gaban ke over racing kirjinta na dagawa sama da kasa,wannan bakaramin daman kare mata kallo yabashi ba kallonta yakeyi ko kiftawa babu yah rabbi,dasauri ya dauke idonshi,yace this should be the last time da zanna saki abu bakiyi ba I will surely deal with you and your mate ko kuma na kai ki can wurin wanda yayi maki cikin aka like mun sharri sai ki cigaba da mashi ranshi kunyar bani ba idiot, wallahi har cikin ranta taji zafin kalmar dandanan idonta ya kada yayi ja bude ido tayi fuskanta har yayi ja kuka na kwace mata cikin wannan shagwababiyar innocent voice din nata da dan karfi take maganar tace ni babu wanda yayi mun ciki ban san kan abunda suke magana ba kuma duk wanda yasake ce mun wannan abun ban yafe masa ba kafin ta fashe da wani irin kuka tana silalewa kasa kan tiles ta hade kanta da gwiwa tana kuka mai shegen karfi numfashin ta har sama sama yake,daga yarda tayi maganar kawai yasa kan malik sarawa he cannot lie or deny anything yaga tsabar gaskiya a idonta inalilahi waina illahil rajiun wannan wane kalar alamari ne, kusan 10minutes bai tashi ba ita kuma batayi shiru ba har sannan kukan take,hankalinsa baya jikin shi tunani ne kala kala aransa, can yaji tana wani kalar numfashi kamar tana kokowa ma da numfashin, dasauri yasa hannu ya dago kanta fuskar tayi ja sosai idonta yayi bala’In reddish sun fito waje ,ahankali take fadin inhelar baya jin ta da kyau amma ko baa fadi masa bay asan asthma ce da wani irin sauri yakira dr ibrahim yace masa yana asibiti eh kawai yatsaya dr ibrahim din yace ya kashe wayar bai tsaya jin sauran maganar da dr ibrahim din ke fadi ba ya kashe wayar, hijab yasaka mata, kafin ya kamata ko tsayuwa da kyau bata iyawa dakin ya jawo, yarda ya rike ta kamar baby ba guntuwa bace amma tsawon su ma bai hadu ya kere ta sosai, kofan parts din nasu ya rufe yataho da ita rike a jikinshi “kaf yan gidan na zaune a a tsakar gidan kowa na harkan gabanshi suna fitowa ido ya koma kansu kamar zasu cinye su da kallo, Ramlah kau kamar zatayi hauka,yana fita yasamu keke suka shiga. Cikin few minutes dr ibrahim da taimakon dr hafsa sukayi kokarin daidai ta numfashin nata allura akayi mata saboda ta huta, Dr ibrahim yace malik yarinyar nan na shan wahala asthma nata chronic ne, malik yasauke ajiyar zuciya yace Ya jikin nata? Dr ibrahim yace she is getting better dr hafsa ma tayi mata allura, zuwa anjima zaku iya tafiya idan ta farka, malik yakalli dr ibrahim yace idan badamuwa dr hafsa zata iya mata p test? Dr ibrahim yayi murmushi yace awwww tun farko Malam kayi magana amma ka wani tsaya kwana kwana,bara ta farka tau.
Kallon paper dake hannunshi yake ko kiftawa babu mamaki ne sosai a ranshi duk da dr ibrahim yayi masa bayani amma bawai ya yarda bane sai da ya gani da kansa, dr ibrahim yace sai fa kawai hakuri this time bakayi nasara ba,atari gaba,malik yayi murmushi yace tau wani yace maka na kagara ne,dr ibrahim yayi kasa da murya yace tau miye nasawa ayi mata awo,malik yamike tsaye yace sai anjima zan fito sai na tarar dakai gida muje wajan tare dr ibrahim yace tau ba damuwa sai munyi magana tace ma dr hafsa da inhelar take amfani an bata,malik yace tau shknn nawane bill din dr ibrahim yace nabiya ai,malik ya kalleshi bai ce komai ba ya wuce.Haka kawai yaji bai kyauta mata ba shine silan faruwan komai har tayi kukan da asthman ta taso ko da yashiga dakin zaune take hijab din ta rike a hannu fuskanta tayi wani kala, she is fine,she fine,she is damn cute,and cool in body structure ,sannu yace mata batace mashi komai ba,kafin yace saka hijab din mu tafi yayi gaba bai jira amsarta ba.Ramlah ta kalli mamansu da fadila dake tsaye tace wallahi mama nake gaya muku fa ba larabawa bane, maman Ramlah tace wai ya’yan waye a kasar Ramlah ta tabe baki tace da yaran wasu ne sunzo su kama haya a wannan compound din ina kuma kullun kuna nan baku ga wani alamar ansa furnitures ba fadila tace hakane amma ranar dana ga sun rako inna wallahi abayar jikinta dana ganshi a wayar maman boy data zo kitso wajena yakusa dubu dari biyu maman Ramlah tazaro ido tace ke fadila!fadila tace sai kiyi kuma ai ita Ramlah tasani,Ramlah tace mama idan ma bata fi ba,maman Ramlah tace ni ba wannan ba kyan jiki da haduwar yarinya ke kamar haddadun yaran masu kudin larabawa fa, fadila tace ni haushi na mijin ko gaisuwa da kyar yake amsawa ita bata ma fitowa balle mu ga fuskar mata magana,Ramlah ta mike tsaye tana wani kashe dauri tace ai wallahi ko ma miye sai munyi soyayya dashi,fadila tac eke Ramlah baki da tsoro wai?ina laifin ki tsaya akan auwal din,Ramlah tace minene kuma auwal ana maganar mutane wannan yar iska siyamar daman danayi maganin ta naga tana wani dauke manah kai a gidan nan siyasa ma na nuna ina sonsa duk da hakan kuma har yanzu babu ruwanta damu bata shiga harkar mu shiyasa na rabu da ita,nidai na fita maman Ramlah ta washe baki tace a dawo lafiya diyar albarka ita dai fadila na kallon ikon Allah tafa san inda zata je shine hadda wani addua take mata. Sai daya shimfida mata zanin gadon daya wanke kafin ta kwanta sai bacci,parlor yadawo yana cigaba da tunanin abunda ya faru yau , without making any sound yashiga bedroom din yabude wardrobe ya fiddo turmin atamphar da ummi taba ta kudi yagani a kasan atamphar kallon kudin yake ko kiftawa babu tunuwa yayi da 20k sadakin ta yasa shi yin murmushi ya girgiza kai yasan ummi ce tasaka mata kudin tunda kudin ta ne ai sadakin ta ne,Bakan leda ya saka atamphar kafin ya rage fankar dakin yasa duvet yarufe ta she is sleeping so tight kamar yar baby kallonta yayi few seconds kafin ya juya da ledar atamphar a hannu ya fita, “Gidan yashiga tana zaune gidan nan kal kamar a zuba abinci ka ci kan cement din da aka shafe tsakan gidan dashi,tana ganinshi ta washe baki tace yanzu fa nake labarin ka araina nace yau shiru ko kana ina zama yayi kan tabarman da take yace asibiti mukaje bata jin dadi ina wuni inna?tace asha kam Allah yasawwake,malik yace Ameen kafin yace dr hafsa fa?inna tayi mitsi mitsi da ido tace wacece kuma haka? Malik yace hafsa nake nufi tace ohh wannan matar zaka ce,nidai tun safe datasa wannan farar rigar ta fice har yanzu bata dawo ba,malik yace eh asibiti muka baro ta ai nayi tunanin ta dawo inna tace aaaa wallahi bata dawo ba,tayi kasa da murya tace audu ko dai yaron ciki ne ke gana mata wannan azabar?malik yace aaa inna asthma gare ta, inna tace Allah ya kyauta ciwon lumfashi baiyi ba sam, malik yace yawwa inna ga wannan atamphar idan hafsa ta dawo a bata sai ta kawai mai mata dinki ,a dinkawa ASSEIYARH inna tace tau shknn daga haka suka cigaba da fira da malik kafin yayi mata sallama ya wuce. A kofar gidansu suka hadu da dr ibrahim dake tsaye yana waya da murjanatu matar da zai aura wata mai zuwa bayan ya kashe ya kalli malik yace ya mai jikin?malik yace dasauki bacci ma take mutafi kawai basai na shiga gidan ba akasa suka cigaba da tafiya har wani babban gida,dialing number mai gidan dr ibrahim yayi yace masu su shigo “ parlor daidai cikin mutunci suka gaisa dashi, Allh musa yace ma malik nasan Ibrahim yayi ma bayanin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 83