aure poor man abba ka fada mata ni babu wani auren da zanyi if mah Auran zanyi I will make sure na aure wanda yafi kowa kudin in whole world ko abbanah gyada kai Alhaji habib yayi tamkar yana gaban yace exactly baby ki barni dasu zan koya masu hankali kuma kin natsu ki kwantar da halinki very soon zaki koma school your holiday is over mah self kinji baby ita kuwa rufaida kibar ni da ita dasauri tace wait abba ynx kasan da kace zaka kore anty rufaida oum mah fushi zatayi tace saida su tafi tare kaga lets fine another solution
Abangaran malik kuwa tashi yayi da safe ya fara gudanar duk aiyukan da zama dawaniniyyar shi a gidan har gari ya karasa wayewa jama,a suka fara kai kawo domin gudanar da kasuwancin su Abby ne zaune kan clean mat din radio a gefenshi yanaji morning news su aisha da ummi na ta faman hada break fast wanka yafito dakinshi ya nufa ya kintsa kanshi yayi matukar kyau ya taje sajenshi tareda kafa hular p-cap ta zauna dass a kanshi kusa da abby ya zauna domin yana son magana dashi tare suka cigaba sauraron news din har aka kammala sannan abby yayi gyaran murya yace Malik ina son a kullum ka kasance mutun mai hakuri da juriya da jajircewa akan komai malik duniyar nan ba Komai kake nema kasamu bah kasance mai hakuri a duk idan ka samo kanka kada ka taba cutar da wani wai dan yana karkashin ka cikin gamsuwa da maganar abby malik ya ce in sha Allah abby nagode Allah yasaka da alkhairi yakara girma murmushi yayi sosai wanda sai da naga kamar shi da Alhaji habib har yaso yafi da malik
Ahankali take takawa tamkar wace bata son taka tiles din dakin har ta karasa gaban bedside dinta ta dauke wayar ta yau ne karo na farko a rayuwarta da zata kira salma da kanta ba ita ta kira taba
Ba tare da ita salman ce takirata bah dialing number salman tayi amma har tanuna call ended ba a dauka bah tsaki tayi tareda jefan da wayan
Karo na baadadi oum tasake saukar da ajiyar zuciya tareda fesar da numfashi yanda gabanta ke buguwa har kana iya hangowa tacikin riganta Rufaidah ce tsaye akanta tana tofa mata adduo’in samun sassauci wajan mahalice mikewa tsaye Rufaidah tayi ban tagama yi wa oum dukkan azikarin datasani wanda zai sa zuciyan ta sanyi kallonta oum tayi tareda kiran sunanta nagaskiya ,Rufaidah ma kallon oum tayi tabbass tasan anzo gabar da yakamata kaddara da kuma gyaruwar alamurra su pah taka rawa a rayuwar aydah hakika anzo lokaci da rayuwar sauyi dakuma gyara ta pa wanzuwa a duniyar aydah mafita daya ce kuma hanya daya tal wanda zaya sa ququwar sauyi da tarbiyya mafi inganci su fara taka tasu rawar a fili dakuma zahiri na rayuwar aydah dukkanin hanaye biyu na oum Rufaidah ta rike cikin natsuwa soyayya irin ta yan uwan asali Rufaidah tafara wa oum magana, Uktieee anzo wajan lokacin yayi amma kafin wanzuwar komai sai kin jure sai kin daure da duk irin matakin da zamu dauka domin shine mafita ta har abada a rayuwar aseeyarh kallon Rufaidah oum keyi cikin tsantsar son jin wannan mafita wanda tasan duk dunia bayan Allah Rufaidah ce kawai zaran dazaya daure mata duk wani matsalanta idanunta dasu kayi laushi ta zubawa Rufaidah tace uktie bana shaka ko kuma fargaba akan duk abunda zaya faru indai abunda muke so zai faru indai abunda muke nema zai samu! Murmushi Rufaidah tayi tace uktieee komai zaya faru yanzu zai zamo sanadin abu guda biyu tunuwa da hakan da oum tayi yasa taji kashi tamanin na damuwanta yarage amma uktieee wani hanzari bah gudu bah abban aydah fa murmushi itama oum tayi tareda cewa wannan mai sauki ne uktieee tashi tsaye Rufaidah tayi tace yau zamu fara duk wani plan namu sosai oum takara samun kwarin gwiwa da kuma karsashin aikata duk abunda ta tsara wanda abu ne wanda zata jifi tsuntsu biyu da dutse guda
Ranar baki daya wunin malik yayi a kwance sanadiyyyar alamu dayafara ji na tasuwar ciwon shi bbu sunayan Allah dari ba daya yake ta faman ambata domin bai ga ranar dawannan ciwo nashi zaizo karshe bah duk wani kokarin da abby ke son yi sam malik bai bari saboda yasan cutarwa ce dakuma cuta ga duk Wani d’a da abby ya haifa saboda a ganin malik din wani karin nauyi ne dakuma dawaniya ga abby din Allah shaidane irin wahalar da cutuwar dayake a duk sanda ciwon ya taso abby ne da ummi kawai ka kwatanta halin dayake shiga wanda bayan Allah su kawai suka san da ciwonshi sai shi da yabar wa kanshi sani bai da abokin daya zamar mashi na jiki kuma aganin shi wannan ba kamar irin normal ciwo bane daya kamata kowa yasani tunanin ne fal aranshi har bacci yayi nasarar kwashe shi .Abby ne zaune kan prayer mat sallarh nafila ya idar wanda shafa adduar shi kenan tun dazu yake lura da ummi ganin kamar akwai magana bakin kasancewar ta ba kasa fai tafiye magana ba har sai idan maganar tazama mai ma ‘ana dakuma amfanin cikin natsuwa da haiba dakuma kamala irin ta dattijan kwarai cike da so yace mata tagari uwa tagari kuma sirika tagari in Allah ya yarda tamkar mashi ya soka mata azuciya kamar wani fami yayi mata a tsohon ciwon dake ranta tamkar soso mata idan yake mata kyakya yayi har ga Allah wani irin abunda ya dirar mata arai wanda take kwana take tashi da dawainiyyar shi arai hawaye suka fara zarya bisa kuncin ummi wanda ba karamin dagawa abby hankali yayi bah
Kallonta abby yakeyi babu kiftawa shiru yayi tamkar mai nazari kaf kalaman shi baiga idan yayi kuskuran zance ba wanda zai saka zuciya da kuma ran ummi bace ba kallo yake mata irin na mamaki da alajabi kallonta yake har sai da tagaji da kanta tayi shiru gyaran murya yayi tareda da fara magana ahankali tamkar wanda yake kan gabar ban hakuri a laifin daya aikata banyi tunani ko zaton a duk cikin kalamai na akwai wanda zai bata ranki ba ummin malik share hawayenta ummi tayi cikin karaya da tarin rauni tace abbyn malik duniya gudu take kwananki karewa suke abubuwan kullun tsayawa suke babu sauyi har sai yaushi har sai wane lokaci komai zai zamu daidai har sai wani lokaci komai zai dawo bisa mizani rayuwa tazamo manah kamar busar sarewa duk yanda iska ya kada haka sautin fitar busar zaiyi damu tunda tafara maganar yake juya kalaman nata kamar mai bita ko kuma hadda su akai, cikin karfin zuciya da tarin kwarin gwiwa yace ina ji a jikina lokaci yayi ban san ta ina ba ko ta wace hanya bah amma adduar damuke tana gab da karbo wa mu bar wa Allah komai kallonshi kawai ummi keyi bstareda ta amsa ba ko fahimtar kalaman da yake amfani dasu wajan maganar bah hankalinta sam baya tareda dashi.Tashin yayi cike da karfin hali da kuma dauriya sakamakon kira mafi daraja a duniya dayaji kaf massallanta anguwar tasu ta dauka ahankali yake tafiya har yakarasa bakin kofar dakin shi daidai ummi na fitowa daga dakin domin duba jikin nashi kasancewar tasan idan ciwon yafara lafawa bacci ke daukar mai nauyi da nisa hada ido sukayi taga lokaci guda yafada irin fadawar da ciwon ke saka shi yi cike da tausai take jera mashi kalmar sannu da adduan samun sauki kallonta yayi ya amsa mata yana nufar hanyar bayi saida yayi wanka tass sannan ya daura alwalla zuwa yanzu Alhamdulilah jikin nashi da sauki shiryawa yayi cikin cream jallabi mai matukar kyau wanda tafito da ainahin kyauwunshi na hausa fulani karfafan kirar jikin dayahade da tsawon shi wanda ke kara fito da asalin kwarjini da haibar shi takawa yake ahankali da kuma nutsuwa har ya shiga cikin massallaci ko bayan angama sallarh zaunawa yayi ya cigaba da azkar yana jiran lokacin magrib wanda tun farko dabi’ar malik din ce ahaka.
Kasancewar fita suke so suyi cikin sirri hakan yasa oum da kanta driving motar hankali take juyawa fararan yatsun hannunta da suka sha ado da jan lalle dan asalin kasar sudan duk bayan seconds take sauke ajiyar zuciya duk abunda take rufaida tana kallonta wanda itama kusan hakane addua kawai takeyi Allah yasa matakin dazasu dauka ya zamu silla da kuma sanadin daidaituwar komai har suka karasa anguwar dake dauke da gidaje waenda ke nuni da tsarin anguwar ta masu karamin karfi ce sauka sukayi daidai kofar wani madaidaicin gida hankali suke takawa kowa da abunda yake rayawa a ranshi
Tafiya take tamkar wace wani ke counting steps foot dinta tafiya take cikin nutsuwa aji kamala da kuma tsabar kwarewa a gayu har takai gaban wardrobes dinta wacce ke dauke da tsarin kaya tamkar ana shirin bude boutique wata grey abaya ta fiddo batada hanyani sam amma kuma tayi musulmin kyau komawa tayi bangaran underwears dinta ta fiddo wata black lace form bra tare pants dinta tsaba ta shirya kanta Yah rabbil alameen!
Yah rabbil alameen!A koda yaushe tamkar ana kara fiddo da ainahin kyauwunta ne tamkar ana sake kera hallitar tane kyauwun jiki dana fuska hade fata tamkar rabawa akayi ta zaba gayun da jikin nata ya hadu dashi ke sa duk wani bawan marmarin kallonta ko da sau dayane wanda hakan ba karamin cutar da ita bane sam bata son mutane bata so hayani bata son duk wani abunda ya shafi mutane towards her Mirrow ta maida kallonta tashi tayi tareda sauke ajiyar zuciya fuskarta ta dan bata kadan tareda turo karamin bakinta hannu ta mika tareda daukar uniques perfumes dinta wanda tsabar kudi aka sa aka siya ANGHAM ALHUM,Dhahab Arabiyat sune asalin turaran da take amfani dashi wanda tun daga kan shower gel dinta face cream body cream shampoos soaps toothpaste hand cream dinta duk na company Dhahab dinne shiyasa ni’ima da asalin kamshinta wanda ya cukude da natural skin scent dinta yake bada wani ni’imtacan kamshi mai saukar da nutsuwa game da kantar da hankali tunuwa tayi batayi sallan la’asar bah dasauri tamike tana turo baki saboda tasan yanzu oum zata shigo tafara mata fada baki da sallarh da alwalla basu wuce 3mins har tayi tagama yunwa takeji hakan yasata daura bakin salkakin gashinta da scarf din abayar wasu soft flat shoes ta zira kafar ciki tafito zuwa dining area ko da tasauko babu kowa t.v ce kawai ke nata aikin sai na’urar da sanyi dake aiki hankalin sanyi wajan ya hade da kamshin rosemary air freshener hakan yataimaka matuka wajan fitar da siring kamshin a parlor din bude warms din tayi taga white spaghetti da kayan lanbu anyi slices dinsu in very attractive shape dan bata fuska tayi tabude dayan warmer din itama dai vegetables stew ce taji kayan ciki fresh watermelon juice ne cikin jug din wanda hakan yana daya daga cikin aladar oum baa taba shan wani drinks apart from fresh juice kadan ta zuba tafara ci ahankali tamkar wacce ke ci dan dole ba dan yunwar cikinta bah takai 30mins tanacin abinci da bai fi yaro dan shekara 3 ba zai ci shi kusan rabin hankalinta yakoma kan tunanin abunda ke jawo mata faduwar gaba duk kwanan bah so take Abba tafada masa haka kawai take jin kamar wani abu na damunta to miye wannan tasamu kanta dayiwa kanta wannan tambayar sam bata san oum bata cikin gidan duk tunanin tana dakinta ko part din auntie rufaideerh karar danna door bell din da akayi shi yaja hankalinta ta mayarda da dubanta kan kofar maids din da aka tanada domin aikin tuni ta tambaye waye tareda bude kofar bayan amsa mata da salma tayi ,masha Allah salma itama bai laifi komai nata daidai bazata wuce shekarun aydar bah koma tawuce sai dai da 1or2 years sanye take cikin dinki fitted gown din atamphar yayi matukar amsar jikinta kasancewar ta mai dan murjajan jiki saidai ko kama kafar aydarh batayi bah wajan kyau da ma surar jiki baki daya ta sallama takarasa dining din iyakar lips kawai aydarh ta amsa sallamar ganin yanda tayi ne yasa salmar tuna ita fa mai laifi ce takirata bata dauka,sannin halin aydarh yasa salma yin murmushi tareda fara ba aydarh dalilin dayasa bata shigo da wuri bah tunda tafara magana aydarh ke kallonta ko kiftawa babu saninin bazata amsa bah yasa salma chanza labarin,aydarh miya faru naga kamar ba yarda nasake ganinki ba wani abu yafaru ne ita dai aydarh batace komai tacigaba da kallon salmar harararta salma keyi tace wait kinga bana son rashin kirki ina maki magana kin mun shiru can tamike tace mata sannu da mamaki salman ke kallonta wannan hali nata bata san ranar chanza ce shi dakinta takoma ta zauna kan sofa daurin datayi ma kanta ne take warwarewa zuba mata ido salma tayi tace aydarh oum pah mutsa bakinta tayi tace she is in room mikewa salman tayi tafita domin gaishe da oum sosai suka saba da oum wacce take ma kallon mahaifiya itama oum na mata kallon diya da sallama ta bude kofar dakin amma shiru babu kowa girgiza kanta tayi tana jinjina irin halin aydarh bata ma san oum bata gidan ba ma girgiza kayi takoma dakin aydarh cikin wannan muryarta ta mai nuna zallar shagwaba da kuma aji tace nakiraki baki daga ba kuma baki tambayeni dalilin kiran salma tayi kasa da murya tace naga dana shigo har fara baki hakuri nayi amma tsabar rainin hankali kika zuba man ido sorry tafada agajarce salma tace to miya faru kika kirani bana kusa ban daga bah nayi kokari nazo gidan kuma kika zuba ido kina kallona kamar wata yar iska tashi tayi tareda daukar wayarta tace babu komai kuma sakin baki salma tayi tana kallonta kamar taga abun mamaki tace hala kanki babu dadi yanzu kuma shiru aydarh tayi har salma tagama masifar tayi shiru tace kingama wani katon bakin ciki ya tsayawa salma a rai ta watsa mata harara bag dinta tadauka tare nufar hanyar kofa cikin masifa take cewa in sha Allah ankusa yi manah maganinki miskilar banza miskilar wofi murmushi tayi kadan ita dai duk nan bataga abun masifa amma dayake salmar ita komai na fada ne da masifa shine har taji haushi wayarta ta dauka tashiga playing games amma kaf hankalinta na kan faduwar da gaban takeyi runtse idonta tayi tanajin wani yanayi tamkar bada ta lapia tun tashinta yau duk tunanin ta cramps zatayi rau rau tayi da ido gabanta na faduwa domin ba karamin wahala take bah idan tana cramps har allura ake mata sometimes har dayan ciwon nata yake tasowa watau asthma hakanan taji tana so daga curtains din window dinta Allahumma bareek yanayin jikin su aydarh shi ake kira da package shape gyara zip din gaban abayar nata tayi boobs dinta dake cure waje guda suka fitar wani shape mai kyau da daukar hankali fatar wajan tasamu Hutu da tsabata game da kulawa ciza lips dinta take tana takawa ahankali zuwa yanzu ta fahimce ciwon marar ne take komawa tayi ta kwanta kan gado.
Kasancewar garin da alamar hadari yasa ummi fitowa tashiga dakin su aysher zaune suke halime ce ke gyarawa maryam (autarh) kallabar da aysha tayi mata take complain din yayi zafi har aysha ta saba da complain dinsu na zafin hannu da suke cewa tana dashi tun tana biye musu suyi chapter har takoma idan sunyi saidai tayi shiru tana kallonsu gyaran murya ummi tace tau fadan da bai karewar ne kuka dasa koh?takarasa maganar alamar tana tambaya dasauri maryam tace wallahi ummi adda zafin hannunta kullun karuwa yakeyi halimai ta turo baki tace ummi adda pah da gangan takeyi saboda ace ta daina yi kitso daman ai bataso aysha tace ummi ni duk banda lokacin wannan abun nasu abinci zaa daura ne? Eh ummi ta amsa mata tare da bata umarnin abunda zaa daura din ko da ta fito saida tafara shiga dakin malik ta mashi ya jiki tareda tambayar shi ko akwai abunda yake da bukata maida duban shi yayi gareta cikin wannan muryar tashi kamar mai magana dan dole yace mata tea tasan daga wannan babu saura abunda zai ce mata kasa tayi da murya tace wai yayah itama auntie tamu haka kake magana da ita?mugun kallo ya watsa mata da gudu ta fito daga dakin saboda tasan sauran ma ko bayan fitar aysha maganar tace tadawo mashi akai kalmar ‘ auntie’ tana nufin budurwa murmushi yayi yana shafa salkakiyar suman kanshi bakaa sol shi kam bai ga ranar bah ma kan murhun gawaye ta daura mashi ruwan zafin 5mins tagama ta hada mashi ta mika mashi daki idonshi na rufe amma ba bacci yake bah ta ajiye ta fita domin cigaba da aikin girkinsu, oum ta maida dubanta ga rufaidarh ganin cikin plan dinsu wani yazo dasauki domin kau harda gudun zuwa wajan hajajju garesu domin itace zata nuna masu kofar cikan burinsu madaidaicin gidan dake shafe da cement ko ina tsab a gyare gida tsofi ne babu wani hayaniya sam mama Rabi wace matsayin kaka take ga abba ita daya ta rage musu shi da dan uwan nashi kaf dunia amma rashin son zumunci irin na abba dakuma ware kanshi dayayi tun farko daga lamarin familyn shi tun bayan rasuwar mahaifinsu mahaifiyarsu ta jima da rasu tun suna yara
Wanene dan uwan abba?
Wane irin plan oum da rufaidarh garesu wanda suke ganin zasu jifi tsuntsu biyu da Dutsi daya?
Miya kawo su wajan kanwar kakarsu abba wacce ke matsayin kakarsu?
Salma tace ankusa maganin aydarh wani irin magani?
Mi yajawo kamar da malik keyi da abba?
Tun suna yara cikin tattare kwarin gwiwa da karfin zuciya oum ta fara ma baaba kulu magana tunda ta fara magana hajajju ke kallon oum da baaba kulu da rufaidarh baki daya kallonsu take kamar wasu zararru tana mitsi mitsi da ido tana jiran taji iyakar idan oum zata tsaya cikin sanyi murya game da raunin zuciya da sarewa oum ke magana tunda tafara baaba kulu ke kallonta cikin tausaya da tsabar kauna baaba har yaushe zamu bar cigaban wannan gaba da kiyayya dake tsakanin yan uwa biyu har yaushe zan cigaba da jure ganin ASEEYARH a wannan yanayin baaba fashewa tayi da kuka mai taba rai rufaidarh tacigaba da magana baaba maganar damuka zo ita itace mafita maganar da muka zo ita tace makama itace wukar dazata yanke duk wata damuwa da kowanin muke ciki! cikin gamsuwa da fatan cikar buri baaba tace rufaidarh kuyi saurin fadin abunda ke tafe daku kuyi saurin yin man bayani cikin gagawa kuyi saurin bani haske in sha Allah nayi alkawarin goyan bayan ku,bayanin duk plan dinsu sukayi ma baaba shiru yabiyo bayan rufaidarh takai ayar maganar ta ajiyar zuciya baaba tasauke domin ta yarda ta amince ta gamsu da duk bayanin da rufaidarh tayi mata zata fara magana kenan hajajju ta mike tamkar wacce kunama ta harba salati tagama tamkar wacce aka aiko ma sakon mumunan accident tace hala oum dai kun chanza addini daman ance waennan rubabbun larabawan sudan din ba hankali gareku ba Jama’a kuji wata maganar dauri tayi kasa da murya tace amma dai gaskia kulu baku da imani keda waennan masu zubin abzinawan nijer din haka kawai ku bankawa bayin Allah sharri saboda baku kaunar Allah wai wani saboda a gyara zumunci ita kuma adar ta gyara halinta tau sam babu ni a wannan bakin zunubi wannan sharrin ko a fim sai haka fashewa da kuka tayi tamkar wata tababba cikin daka tsawa da daga murya baaba kulu tace ke wai hajajju mahaukaciyar ina ce ina nan naga basu sa dake ba cikin wannan lamarin kuma saboda sun ga cikin mu guda dake yasa basu ce ke bamu wuri bah,haba dan Allah ki dinga abu kamar wata zararra ina amfanin wannan abunda kikayi haka tau ba ruwanki idan bazaki goye bayan wannan baiwar Allan ba a wannan sadaukarwa da tsoron Allah nata ba ba’a zage ta ba share hawaye hajajju tayi tareda fesar da majina ta mike tsaye tace tau gaskia kun zama abun tsoro tun zuwana yola nake ganin jafa’i kala kala babu irin mugun abun dake ban gani ba shiru sukayi babu wanda batayi mamaki bah domin a tunaninsu itace mutun ta farko dazata amince ta nuna yardar akan lamari amma har cikin rai rufaidarh tasan hajajju daga baya zata chanza magana ta amince domin idan da sabo kowa yasaba da wannan halin nata sosai baaba kulu ke jinjinawa oum wata irin kauna da soyyayarta na sake karuwa har cikin ranta addua tayi musu sosai da fatan alkhairi dakuma fatan cikar burinsu batare da wata matsala bah hajajju kau daki tashiga tayi zaman dirshan ta cigaba da hada kayanta a ghanan ta yau ban kwana yola gaskia duk idan dare yayi man yau a kano zan kwana ah ni binta ina zan iya zama cikin masu zuciyar kafurai da mugun abu ina zaman zamana wannan tsohuwar ta taso ni wai nazo batada lapia bancin kaddara da mi zai ma kawoni wannan gida nata kamar zuciyar talaka gida ko farin glop babu sai ja kamar dai bamm,Har hajajju tagama hada kayanta su oum na zaune suna cigaba da tautaunawa da baaba kulu fitowa hajajju tayi da katon ghanan ta tashare hawaye ta nemi kujera ta zauna ta mike kafa tayi kasa da murya kamar ba ita tagama kuka yanzu ba tace a gaskia rufida’u ban taba sanin kunada hankali ba irin yau idan bahaka har miya hadaki dasu dazakiyi musu irin wannan halaccin tau ko ni nadake ciki guda da kakarsu habibun bazan iya wannan abunda kikayi bah gaskia kinyi kokari Allah yayi muku albarka ahankali kuma tace amma shi mai zubin yan fim din indiyan ya amince itakuma diyar wurin naki hwa?murmushi oum tayi daman tasan daga karshe hajajju zata sako tace in sha Allah hajajju komai zai zo manah cikin sauki tunda gaki murmushi hajajju tayi tace aikam nasan ta kan tsiya daman tun sauka ta jiya na kira shi audul din nace mashi gani a yola yace zai zo tau nasan wannan bahillatanar uwar tashi zata hana shi zuwa shikuma rubabben ibrahim din daman bana san ran zaizo idan nake saura yaran dama ba fita suke amma ki bari ya shigo sai nasa kulu ta kiraki kituro man ita adar shima habibun ki tada mashi hankali ki nuna wani jafa’i ke shirin faruwa a najeriyar yayi gaggawar dawowa yauwa tunda tafara magana baaba kulu yake murmushi domin tasan halin yar uwarta tsaf saidai ta shirya yarda komai zai tafi daidai daman tasan sai ta amince da zancan daman kowa yasan halinta shiyasa tayi mata wannan gorin.
Karar kiran wayar yasake shigowa a wayar tashi a karo na ba adadi yasan mai kiran kuma ko daya daga bai san abunda zai fada ba bai shirya daukar darun mai kiran ba shiyasa bai daga ba so yake kawai ya cika alkawari yaje dasafe Idan Allah ya kaimu ummi na lura dashi saboda tasan da maganar sai tayi murmushi tace miyasa ba zaka daga ba? Shafa sumar kanshi yace so nake kawai naje zuwa dasafe in sha Allah,Allah yakaimu tace babu wanda yasake magana acikinsu har kowa yagama cin nasa abinci bayan sun kammala halime ta kwashe plates din tayi kitchen dasu shirin tafiya makarantar dare sukayi amma sai malik din yace su bari saboda har yanzu garin akwai alamun hadari ya yayi musu kari a gida godia sukayi mashi aysha har cikin ranta taji dadi saboda sam bata cika son zuwa makarantar bah saboda malamin su dayafiye takura mata da sunan soyayya har ummi takawo ma zancan tashare ta tareda fadin Allah yakyauta kawai babu abunda tace wajan takwas daidai abby yashigo gidan hannunshi dauke da bakar leda wanda fura ce a ciki da fresh nono mai kyau irin na fulanin adamawa gaishe sa sukayi tareda masa sannun da dawowa tambayar su yayi abunda yahana su zuwa karatun dare maryam tagaya masa bace komai sai shiga daki dayayi gidan a tsabtace yake sai tashin kamshin tsintsiyar tsinke yake abinci shi ummi tashigo mashi dashi tareda wajan dazata dama mashi furar
Zarah bansan abunda yasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 83