indomie sharp sharp yau ko ganinta baiyi ba ko daya shiga daukan kayansa tana toilet,bayan yafita already tayi wanka tashirya ta fito tun dazo take son tafita ta dauko tsintsiya amma bata son ta fita su hadu wani irin girma da kunyarsa take ji gani take babu wani sauran abu kuma daya rage yanzu yariga da ya gama da ita, guntun hawaye tashare kafin ta mike ahankali ta bude kofan dakin tana kallon cikin parlor ya share koi na babu kuma shimfidar shi hakan na nuni daya fita komawa tayi bedroom din ta fiddo warmer jiya takai kitchen tana shiga taga nan ma ya share tass sai warmer nan ajiye tabude taga indomie ce ciki.
Ta dinga bin indomie da kallo kafin ta rufe warmer,Sai da ta gyara bedroom din tass yau hadda toilet ta wanke ,tana aiki yau duk jikinta babu dadi kaman wace batada lafiya,ahankali ta fito daga bedroom din tana tafiya kamar mai counting steps dinta kitchen din tashiga ta ajiye mopper da tsintsiyan kafin ta bude warmer ta dauki plate ta zuba kadan ta fita parlor,bata ci dayawa ba ta ajiye ,kitchen ta mayar da plate din tayi zaune nan parlor, knocking kofan akayi kamar bazata bude ba sai kuma ta tashi,tace waye? Shiru taji ba a amsa ba kuma ba’a sake knocking din ba hannu tasa tabude kofan ahankali, kallonta yake ko kiftawa babu ita dai kanta na kasa kafin kuma ta juya tashige bedroom,bedroom din yashiga zaune take kan katifa ta zuba ma waje daya ido yayi kasa da murya yace hala baki iya gaisuwa ba? Kaman bazata amsa ba sai kuma ta tuno da abunda yafaru jiya,ahankali bata kallonsa ta juyan da kai gefe kafin tace “ina kwana” bai amsa ba sai bin dakin da kallo da yakama yi,itadai kanta na kasa bata dago ta kallesa ba, can yamike tsaye yace yau bazaki yi sharan ba?ta ware ido ta kallesa tace nan din fa dana gyara ,duk dayaga yarda dakin yayi kyau amma kawai so yake ya tsokaneta, yace nan din ne kika gyara? Ta bata fuska tace nafa gyaraaaaaaaa yanda taja kalaman kamar yar baby yasa shi kallonta, yace tau said ai ki sake gyarawa nan dai babu alaman anyi shara gaskia dai,batace masa komai ba tayi shiru ta kawar da kanta “can ya mike har yakai kofa ya juyu yace,dakin yayi kyau “sai kuma yafita ta dinga bin kofan da kallo kafin tayi murmushi can kasa tace sai kace shima iyawan yayi, yana fito ya wuce wajan dayake yin cefane vegetables yasiyo masu sai nama, dr hafsa ya hango yakarasa in datake,sai sannan ta gansa tayi murmushi tace “ina kwana “yallabai? Malik yace Alhamdulilah ya aiki? Tace Alhamdulilah,kafin yace inna fa? Dr hafsa tayi kasa da murya tace bata da lafiya fa,malik yace subhanallah dr hafsa ta gyara tsayuwanta tace fever take nayi magana k ozan mata allura ta rufe ni da masifa yanzu haka tana can kwance malik yace dasauki ba? Tace ehhh gaskia dasauki kasan dai halin ciwon inna malik yayi murmushi yashafa kansa yace in sha Allah zamu zo shigo idan anjima ki gaishe ta dr hafsa tace in sha Allah. Tana parlor zaune yafito da knife sai karamin rubber da cabbage sai carrot a ciki gawani plate rike a hannunsa,kallon shi tayi sai kuma ta dauke ido bai kalle ta ba ya zauna yafara yanka vegetables din kamar wani hadaddan chef,tunda yafara yanka vegetables din take kallon yarda yake duk abunda takeyi yana lura da ita sai daya kankare carrot din tass kafin yace, “yanka “kamar daga sama taji maganar sa batace komai ba ta sa hannu ta karba yarda yakeyi haka ta dinga bi tana yankawa ahankali, kallonta yake har ya shagala bakaramin kyau tayi masa ba,yarda take hade gira tana yanka carrot din murmushi yayi kadan kafin yayi kasa da murya yace “kin gaji ne? Ta girgiza kai tace ah’ah zanyi, malik yace tau muje kitchen sai mu karasa girkin?ta gyada masa kai kafin tayi wani cute smile tace erh nima zaka koyamun? Malik daya sakankace yana kallonta kamar wani yaro ya gyada kai yace mu tafi ,kitchen suka shiga ya mika mata cubes yace bare wannan kin iya? Tayi kasa da murya kafin tace to ka bude daya sai nagani,kallonta yayi bai ce komai ba ya matso kusa da ita ta matsa kadan tadan bada space a tsakaninsu cube din star daya ya dauka yace look up,ta dago kanta yafara bare maggin kwara daya ya bari kafin yace karbi ki bare sai nagani, fine fingers dinta tasa ta dauki cube daya tafara barewa, yarda take juya hannunta tana barewan yake bi da kallo sosai kananun diamond rings dinta sunyi ma hannun kyau sosai, tana bare daya ta dago tayi wani hadaddan smile tace,”nayi” malik ma yayi murmushi yace Good job mamana jin sunan daya kirata yasata bin shi da kallo dauke idonsa yayi kafin yacigaba da frying kayan miyan tacigaba da bare maggin har tagama kafin murya can ciki tace “nagama”kallon maggin yayi ya kalleta kafin yayi saluting dinta tayi murmushi kadan har cikin ranta take jin dadin yarda taga tabare maggin sosai take son ta iya girki kusan duk abunda ya dauko zai zuba sai yafada mata ko ya nuna mata duk babu wani dogowan magana amma ahaka take koyon duk abunda ya nuna mata din cikin few minutes suk agama girkin dake ta faman kamshi kallonta yayi itama shi ta kalla sai kuma ta saukar da kanta kasa hannunsa ya zuba a aljihu kafin murya can kasa yace zamuje mu duba inna ,batace komai ba shima bai sake magana cikin warmer da dr hafsa ta ba ta wainan flour jiya yazuba abincin kafin ya juye sauran cikin warmer su jin ana kiran sallarh yasa shi cewa idan nadawo masallaci sai mu tafi,fita yayi a kitchen sharp sharp kasancewan Friday ce yayi wanka wani white shadda yasaka duk da ta kwana biyu amma bakaramin kyau tayi masa ba agogon daya siya black yasaka sai azurfan shi black itama wani ubansu black shade ya kafa a ido yah arrahamar rahimin ya rabbil alameen Malik yafi kyawu kyau yayi wani irin kwantacan musulmin kyau, sai lokacin tafito bayan tagama wanke abunda suka bata wajan girkin bata ko kalli inda yake tsaye ba a parlor yana linke prayer mat zai yafa a shoulder tawuce cikin bedroom din, wanka tashiga ta dauro alwalla kafin ta fito sai datafara yin sallarh kafin ta dauki vaseline tafara shafawa,har zata cire hijab din jikinta sai kuma ta tuno da abunda yafaru jiya yasata barin ta , yau hadda powder tashafa wanda tunda yasiyo ya ajiye ko taba ta batayi ba tayi using kajal da kuma masccara sai lips stick kadan tasa brush ta gyara giran ta, bude wardrobe tayi tafito da black lace foam bra sai wani black pant wanda suka siyo waccan ranan a shagon matannan, kafin tajawo fitted gown din da ummi tabata wanda kullun kayanta na a wanke goge har baya gajiya ma da mata wanki duk da kayan bawani yawa ned asu ba,saidai har yau taki barinsa ko da kallon bra dintayi yayi kar aje ga maganar wankewa ma,shiyasa jiyan nan taji kamar dakin ya tsage ta shige, ko’ina na jikinta sai da tabi sa da perfume as usual, kallabin atamphar ta daura all back irin nasa hijab ,gashin gaban kanta ya kwanta luff kamar na babies, bude kofan dakin tayi tafito tana fitowa ta samesa zaune kan carpet yana cin nasa abinci batace masa komai ba ta dauke kai tayi hanyar kitchen dole sai tabi ta gabansa kafin tashiga kitchen din kafa yasa mata kawai sai ji kayi yaraff, ta fado a cikinsa wani dan banza kara tasaki duk da bawani muguwan faduwa tayi ba ,da karfi tafadar da kirjinta akan laps dinsa saboda yanayin faduwan datayi,murmushi mugunta yayi jin yarda tayi karan, dasauri tafara kokarin mikewa ta kasa tadinga kallonsa kwalla cike a idonta kafin shi da kansa yasa hannu ya dago ta,ta zauna tasa hannu ta rufe idonta tabare masa baki zatayi kuka yasa karamin yatsa kan mini bakin nata kafin yace this should the first and last dazaki ganin zaune baki gaishe ni ba idan lokacin gaisuwan ne am I cleared yakarasa maganar da alaman tambaya? Tana jin sa Still kuma batayi shiru ba tacigaba da kukan ta wanda yafi kama dana shagwaba,yawani hade rai yace secondly wannan perfume din naki yayi yawa ki daina cikasa hakanan,sai yanzu ta saki hannunta daga kan fuskan ta kafin tace “perfume? Ya gyada mata kai yace kin ji ni aie batasake cewa komai ba kafin ta mike tsaye ta nufi ahanyar kitchen abinci ta zuba kadan kafin ta dauki ruwa ta fita still yana zaune parlor ko style din dayayi nazama bai chanza ba, ita dai tayi wucewan ta bedroom.
Yana gani Ramlah yasace kallon aydarh kanta na kasa har yariga da yasaba ma tafiya da ita ahaka kullun kanta na kasa idan suna tafiya,Ramlah nagani malik dayake zuciyan kare gareta tawani gyara yafin mahayafin abayar ta tawani katon kwan chewing gum din datake chewing ta karasa fita zauran gidan tana jiran isowarsu, shidai malik ko kallon ta bayi ba balle ma ya ga abunda tayi aydarh kau da daman ko zata mutu ba ta ita takeyi ba, hannunshi rike da warmer inna dasuka zuba mata abinci suna zuwa zauran Kamar daga sama sukaji muryar Ramlah tace yallabai kawo a rike maka kulan cike da duniyan ci tayi magana malik ya girgiza kafin ya juya ya kalli aydarh yarda tawani hada rai ta tsuke fuska tana kallon Ramlah yace aaa kibarshi nagode aydarh dAi natsaye tana kallon su.
Tana kallonsu kafin ahankali ta bi ta gefen Ramlah tafice a gidan,kofar gida ta tsaya tana hade fuska kamar wacce rana ke bugu “ tawani bata rai, malik yazo zai wuce ta gabantaa kamar bashi take ma magana yanzu ba,shidai yayi shiru baice mata komai tun dayake a duniya bai taba ganin raini irin haka ba,baisan kalan tsaurin ido kalan na Ramlah shi da ko namiji dan uwansa ke shakkar sa balle ita wannan abun yayi tunanin warning din daya yayi mata jiya ya isa, amma ina kamar ma bayi mata ba,yarda yau tafi shishige ma sa fiye ma da,daa ahankali yake fitowa daga cikin gidan,Still aydarh na nan tsaye, kallonta yakeyi ko kiftawa babu yarda tawani hada rai da ta gansa matsawa yayi kusa da ita kafin yace sorry I keep you waiting ,kinsan halin yarinyan nan bata so taga ina wahala baki ga tace na bata daukan warmer din ba?aydarh ta juyo sai da tafara zubawa kofan gidan harara kafin ta kalli malik ido ido cikin ido,cike da masifa tace “why baka bata warmer? Ai da ka bata,malik ya dinga bin ta da kallo ganin irin masifan datakeyi cike da yarinta shagwaba da tsiwa irin sturbborn girls din nan,malik yashafa kai kafin yayi kasa da murya yace,”yanzu dakike ta masifa sai kin ja an kallemu ace kina wa mijinki fada?tawani hade kafin tace “to bana ci ta daina kallona ba kuma bata daina din ba malik ya juya yaga babu komai kofan gidan kafin yasa hannu yaja long nose dinta yace ai dole ta kalleki tasan kishiyarta sosai aydarh ta bige masa hannu kafin tace Allah ya kiyayaye waye kishiyanta? Wannan shashashar kake hadawa dani wai kishiyar ta ko ma wacece ni dinta that’s not my business kawai nidai ta daina kallo if not hmm ,Malik yayi murmushi yace if not what? Ai da kin karasa malama, aydarh batace komai ba ta juya tayi gaba ya bi bayanta yace sturbborn bea, har sunyi nisa Ramlah ta sake biyo su baya da sassarfa ta isko malik wanda shine baya yana binta ita tana gaba, Malik dayake bin Ramlah da kallo fuskar nan babu yabo babu fallasa,Ramlah tayi wani tsayuwa irin na yaran nan masu rawan kai kafin tace naga fa gidan inna zakaje nima kuma zanje please ka bani na rike maka, aydarh tawani juya batace komai ko kallan su batayi ba kafin tace give me,kamar wanda aka ja da magnet haka ya mika mata wannan warmer kafin fuskan nan ba wasa ta kallesa murya cike da ba da umarni da isa tace masa let her to go back, wallahi malik kamar wani mai jiran umarnin ta shima ya juya kafin yace ma Ramlah “go back “yabi bayan aydarh suka cigaba da tafiya Ramlah kau ta na nan tsaye ji take da tanada bindiga yau sai ta harbe aydarh har suka shige gidan inna tana nan tsaye kamar an dasa ta.sai da suka gaisa da dr hafsa kafin su shiga dakin inna, sallama sukayi inna dake nan cikin wani katon bargo ta amsa masu Kamar irin wace ta shekara dari tana ciwo nan kwance, Malik yace asha kam sannun inna jikin new ai har yakai haka yafada yana kallon dr hafsa da ta shigo yanzu ko zama bata kai dayi ba, dr hafsa ta sauke ajiyar zuciya kafin ta gyada ma malik kai alaman aaaa ya fahimta bata son yin magana ne saboda tasan halin yan kayan ta, malik ya sake matsawa kusa da inna kafin murya can kasa yace sannu inna,tayi shiru yace yanzu mike maki ciwo nan ma tayi shiru daga aydarh har dr hafsa su dai suna nan zaune sun zubawa sarautan Allah ido ba kamar dr hafsa da taga innan cikin bargo mata da yanzu ta gama Kare mata tanadi har ta fita shine wai yanzu dan taji su malik din sun shigo dubiya ta kwanta,juyin duniya malik yayi inna tayi magana amma tayi shiru bata ce komai,can ya sake dan kasa da murya kafin yace tau inna tashi mutafi asibiti kwara ai allura asa karin ruwa tunda naga jikin yayi kasa kwarai bara mutashi yafada yana kokarin mikewa aikam inna ta riga malik tashi ta na ajiye bargon gefe,kafin tayi mitsi mitsi da ido tace ni fa bana son kiran masifa daga mutun ya kwanta sai a fara kiran wasu bambaman tijara wai karin ruwa wa zaa karawa ruwa banda neman jafa’I aaa tau lahiya ta lau naji sauki Alhamdulilah,aydarh ta dinga murmushi bakaramin dariya inna tabata ba, malik ma sai dayayi murmushi kafin ya koma inda yake zaune ya zauna, dr hafsa dai batace komai ta fice daga dakin,malik yace tau sannu ai yanzu jikin da sauki koh?inna tace ah dasauki Alhamdulilah ai naji sauki sosai kafin yace tau yanzu ga abinci nan sai ki tashi k ici inna tace tau shknn zuba man abinci daman idan ba kai ba wa zai bani shidai malik bai ce komai ba ya dauki wani clean plate daya gani da spoon nan gefe ya bude warmer ya zuba mata abincin daidai daidai yace tau gashi sai ki daure ki ci,inna ta karbi plate din sai da ta cinye tass kafin ta kalli malik tayi kasa da murya tace tau ita mai dakin naka taci abinci ko baza taci bane? Malik ya girgiza kai yace ehhh taci,inna tace tau madallah ita fa waccan matar fa? Malik yace bara tadawo ai nasan zata zuba, inna ta dinga zuba labari kamar ba ita bace ba marar lafiyan malik na biye mata ita dai aydarh bata cewa komai sai sauraron su take can ta mike,malik yabita da kallo inna bata ma lura ba,bai ce mata komai ba har tafice ta shiga dakin dr hafsa kafin ya dauke kanshi daga kallonta ya maida hankalin shi wajan inna da take ta zuba kamar kanyan da ba dadi, dr hafsa tace naji dadi ma dayake yallabai ne daidai ita baki ga ta mike ba, aydarh tayi murmushi , kafin tace aie yanzu har taci abinci ma dr hafsa tace kai haba,ah anci sa’a ko dayake ma aie inna bata wasa da cikinta, aydarh tace uhm dr hafsa tace kinga fa wata friend dina ce ta haihu kar jibi suna ban samu naje barka ba,aydarh tace oh Allah sarki, dr hafsa tace bari zanyi naje sunan ma baki daya, aydarh tace gaskia dai,kwara ki bari din kije baki daya, dr hafsa tace yallabai da zai barki da sai mu tafi tare ma Aydarh tayi kasa da kai batace komai dr hafsa tace naga kamar baya so kina fita ma ba? Aydarh ta girgiza kai tace ah’ah fa,dr hafsa tace kin fadi gaskia dai,yawwa har zan manta ina mutuniyar mu?aydarh tayi shiru alaman bata gane abunda dr hafsa ke fadi ba,dr hafsa tace Ramlah manah,nan shiru tayi kafin tace waye haka? Dr hafsa tayi dariya domin har tafara sabawa da halin aydarh itama ita dai komai nata unique ne,dr hafsa ta dinga dariya tace kinga kishiyarki nake nufi, sai sannan aydarh ta daga kai tace, ni miye hadani na da wannan, dr hafsa tace ga hadin ki da ita nan kina kokarin sa ido ki bar ta da mijinki kinga aydarh nib a zugaki nake ba amma a matsayina na babba mai hankali bazan so taba barin ki bar shi wannan abun nashige ma rayuwar sa ba,ina ma ace wata macan kirki ce wannan ai yanada daman da zai yi aure ya aure duk wace yake so,aydarh dai ta kasa dauke kanta daga kallon dr hafsa maganar ke shiga har brain dinta batace komai ba dr hafsa tacigaba dacewa yanzu haka fa akwai wani na nan sosai yake sona amma matarsa kamar haukace ma ce gaskia haka na lura,saboda irin cin mutunci da take mun nidai ban iya masifa ba kuma bana son raini wallahi aydarh shiyasa har yanzu nake ta adduar zabin Allah ku dai ku godewa Allah,aydarh kinyi sa’ar miji saidai fatan kuma yara nagari, aydarh kanta nakasa.malik ya tsaya daga bakin kofa yayi sallama dr hafsa ta amsa masa,kafin yace ta fito mu wuce gida yamma yayi , dr hafsa ta kalli aydarh tace mai gida ya ce ki tashi ku tafi, aydarh ta mike ahankali tace sai anjima auntie “har kofan gida dr hafsa ta rako su.
Ta dinga kallonsa kafin tayi shiru can kuma ta dago kai tace to a ina ne zakuje bikin? Malik bai yi tunanin zata amsa sa ba dayana fada mata shiyasa yayi mamaki, yace mata can nasarawa,tace lafiya? Yace yeah a can ne matar take “aydarh tayi shiru tarasa ma mi zata ce masa, kafin yace yau saura kwana biyu mutafi islamiyan ku ai naga maki na sat sun ne kawai right? Ta gyada masa kai alamar erh, babu wanda yasake magana cikinsu yayi shiru bai ce komai ba, Ahankali ya mike ya bude wardrobe dinta, ya fiddo uniform din kafin ya fito parlor iron ya hada yagoge mata uniform din tass kafin ya kwashe su ya koma bedroom din saida ya mayarda su cikin wardrobe kafin ya jira tafito daga toilet da alama wanka tayi domin fuskan ta da alaman lema sai gashin gaban kanta da ya kwanta luff, kasancewan hijab dinta tayi baya, ya dinga bin fuskan ta da kallo ita dai bata kallonsa kanta nakasa, juyawa yayi har ya kai kofa idan kin gama ki same ni a cikin, kafin yafita ya rufe mata kofa sharp sharp ta shirya bakaramin dadi take ji ba,yarda take koyon abubuwa yanzu abaya tasaka tayi shafa perfume sai inner cap black da tasaka tafita , a kitchen tasame sa kafin su ya daura white macaroni da zaiyi stew dan tagani,cikin nutsuwa da aji suke komai duk da babu wani dogowan magana da ke shiga tsakanin su amma tsaf take koyon komai zuwa yanzu zatayi iya yin stew tadafa farin pasta da kuma macoroni wainan flour dakuma jallof.cikin fe minutes su ka gama kafin ya fita saboda lokacin isha’I ya kusa ita tagyara kitchen din ta kuma wanke duk wani plate dasuka bata, sharp sharp tashiga tayi alwalla tafito tayi sallarh shima sai sannan ya shigo sai datagama sallan tafito a parlor tasame sa zaune kan carpet ga warmer sai plate biyu spoons biyu da serving spoon kan plates din yana gani tafito ya bude macaroni ya zuba mata daidai yarda take ci a plate kafin yasa stew din kadan yasaka mata spoon din a gefe, ya tura mata gabanta kafin shima ya zuba ya sai ta kalli abincin nasa ta gefen ido kafin ta cigaba da cin nata ahankali,shima abinci yake ci babu wanda ke ma wani magana, bata cinye ba ta mike ahankali yana kallonta ta shiga kitchen ta ajiye plate din ta rufe kafin ta dauki ruwa ta sha kafin ta dauki plate ta saka mashi pure water biyu a kai tafito takawo masa kallonta yayi har ta ajiye kafin yace thank you,duk sai taji taji kunya ita bai taba yi mata abu tace masa thank you ba shikam yau ruwa kawai tabasa yace thank you,bata tsaya ba tayi wuce bedroom din ta zauna,littafin dasuka siyo a islamiyan ta dauka tana dubawa kafin ta tashi ta dauki books din ta zuba cikin hadaddan back bag din da yasiyo mata na zuwa islamiyan, abu biyu ne ya hade mata murna da kuma fargaba,is she eager gari yawaye ta ganta a islamiyan a haka ta kwanta.tass suk agama aikin gidan as usual ta gyara bedroom ta wanke toilet dinta shikuma ya gyara parlor da kitchen ya wanke toilet din nan parlor,sai daya tabbatar da tagama gyaran bedroom din sannan yashiga tana tsaye ta tasaka camesole din uniform din da aka dinka mata sosai rigan ya karbi jikinta kasancewan bata da hannu yasa har kana iya ganin hannu light blue din bra dinta exactly irin uniform din, wanda yabi jikinta ya kwanta luff gashin kanta take kokarin cusawa cikin light blue din inner cap din dayasiyo mata ta dinga sakawa da uniform dakin ya dauki kamshin jikin ta juyuwa tayi ta gansa tsaye jikin kofa , dasauri ta karasa saka hulan ,kafin ya kalleta yayi smile yace yan islamiya an shirya tayi kasa da kai ta gyada mashi kai tace erh yace Alright kafin muyi later kizo sai muyi girki tace alright, ahankali ta biyo bayan sa har kitchen din indomie sukayi sharp sharp sukayi vegetable indomie kafin sukayi frying egg kusan komai ita tayi yau sai dai ya nuna mata,yana kallon yarda takeyin komai ga zufa kadan a goshinta wani irin hadaddan kyau tayi masa a yau din he likes everything in her,her sturbborness ,shiru shiru dinta tsiwa yau din hakan nan sai yaji kansa a matsayin mijin aure shima yarda tagama indomie tayi serving dinsa kadan ta zuba taci kafin ta koma daki abayan tasa ta dauki back bag dinta ta koya kafin tasake fesa perfume kadan nikkab din ta dauka ta dinga bi da kallo bata san yarda zata daura sa ba,Ahankali tafito tajawo dakin rike da nikkab din a hannu kallonta yake ko kiftawa babu kafin yace Tabarakallah, a ranshi takalli sa kafin ta wara ido tana mika masa nikkab din tace gashi ya kalleta yace ni zan saka hala? Tabata fuska tace ahah ban iya sakawa bane aie bai ce komai ba ya bude nikkab din yazo daidai ita duk da ba guntuwa bace amma yayi mata tsawo dayawa ahankali yake daura mata nikkab din har ya gama,Sosai nikkab din yayi mata idonta dayasha kajal yafito tarr , gaba yayi tadinga bins abaya har sai dasuka fita part din kafin yasaka key yarufe, suna fita suka samu keke ya mika su har makarantar, Sai ya tabbatar an ta shiga aji kafin ya wuce wajan aiki. Sit tasamu daga nan gaba babu kowa anan ta zauna kasancewan duk matan aure ne waenda basu samu isa shan illimin addini ba saboda haka aka bude ajin tunda ga farko aka fara karatun lokacin al’quran ne kowa yafito da quranin sa aka fara krt, Sosai aydarh ke fahimta saboda tasa ma ranta karatun ba karamin maida hankali tayi ba .lokacin break ne babu malami sauran students din kowa yacigaba da harkan gaban sa masu surutu nayi masu cin abinci haka masu ba yara abinci ma haka kasancewan dayawan su duk goyo suke ,bata cire nikkab dinta ba kanta nakasa tana duba karatun da mai tajwid yayi masu yanzu sai bin book din take da kallo zata iya maimaita larabcin amma bazata iya fassara hausan ba,a zuciya tace idan naje gida sai na nuna masa yakoya mun, wasu gang din mata ne zaune a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 83