bayan ta dayar takasa hakuri tace maman baffa wai bakuji wani irin kamshin dake fita daga jikin wannan sabuwar zuwan ba?wace aka kira maman baffa tace wani iri ma naji wallahi tana shigowa ai gaban sit dina take, dayar tace niba kamshin ba dan Allah kuji diamond rings a hannunta, maman noor ai ke kinsan diamond ko gasu nan dai kananna kwara biyu a yatsanta nafarko dana can karshe kafin babban yatsa ko? Maman noor data gama bawa yarta nono ta gyara zama tace sosai ma wllh diamond rings ne ko da mukayi zaman malaysia babu yarda banyi da dad noor yasiyan man ko daya bane yace bazai siya ba waye shi, maman baffa ta zara ido tace hadda fa English gold a dayan hannunta gashi can a yatsa na biyu, maman noor ta tabe baki tace wallahi kuma mai shegen tsadar ne saboda yan kanannan can sun fiye tsada, dayar tace ji ma yarda skin dinta kewani milk milk gawani shegen glowing datake,maman baffa tace Allah daya gari banban naso ace babu nikkab a fuskan naga fuskan maman noor tace uhm ni fa duk wannan bai daman ba kamar yarda tazo batayi manah magana ba tayi wani shiru,maman baffa ta rike baki kafin tace kiji maman noor dawani zance saninmu tayi ne kuma wannan duk ma abunda tayi ai takai tayi wallahi maman noor tace tau saura kuma ku da shigen shishigi wata taje tayi mata magana,maman ta mike tsaye tace haram haramun wallahi kau sai nayi mata magana yoo ko da wannan turaran banayi mata magana ba kin kau san yarda baban baffa ke son kamshi kuwa? Maman noor tace haka kuka iya aie da kunga mutun tsab sai ku shige masa ai ni wallahi har yanzu baayi wacce zan shigemawa ba,maman baffa tasaki baki tana kallon Maman noor tace aaa fa maman noor da dai anan ajin dai babu kamarki amma yanzu an kawo wace idan tana wuri baki isa ki nuna kin san komai ba,maman noor tayi mata wani dan iskan kallo kafin tace tau tsaya kafin kije nagaya maki wani abu maman baffa,ko da turaran tabaki kamshinsa kawai zakiyi bazakiyi kamshi irin nata ba saboda ita natural body scent dinta yahade da turare maman baffa tadawo ta zauna tace kai haba da Allah? Maman noor tace wallahi kuwa maman baffa tace tau ke taya kika sani ma? Maman noor tace Maman baffa kenan kamar dai kinta miye sana’ata mudai gyara idan na diya mace babu wanda bamu sani ba wallahi,maman baffa tayi shiru sai can kuma tace gaskia dai ita wannan Allah ya yabata, duk abunda suke cewa tana jinsu ko juyawa batayi ba balle ta kallesu,ta cigaba da abunda takeyi,12:00pm daidai ake tashin su tun 11:40 yazo ya zauna cikin office din headmaster suna fira sama sama kamar irin sun san junan duk kusan headmaster ke yinta,shidai malik na sauraron sa,yana jin an tashe su yayi ma headmaster sallama yafito bakin kofa duk kansu da nikkab wani ya sauke nashi wani kuma ya dage sa sai fitowa sukeyi wasu da goyo wasu ciki wasu kuma da yara rike a hannun sai baza ido yake yaga ta inda zata fito,Gently take tafiya kamar wacce bata son taka kasan har tafito bakin kofan school din duk inda ta bi sai maman baffa da maman noor sun sa kafar su suma,so suke suyi mata magana;tana dago kai suka daga ido har yanzu fuskanta da nikkab murmushi yayi kadan kafin yayi mata waving hannu hango sa tayi hakan yasa ta tafiya ahankali ta iske shi kafin tadaga nikkab din tace “ka cire mun “ya girgiza kai yace mutafi gida sai nacire maki din tayi kaman zata fashe dakuka tace noo zafi fa “ahankali ya sa hannu ya kwance nikkab din ya rike a hannu, maman noor da maman baffa da tun dazu suke kallonsu, ganin abunda yafaru yasa su hada ido, kafin maman baffa tace yah rabbil alameen maman noor ashe larabawa ne?maman noor tace maman baffa ko dai yayanta neb a mijinta ba kiji kama fa suke dan dau kawai kalar skin dinsu ya bambanta, maman baffa tace aaa gaskia kila dai auran zumunci ne gaskia saboda ai kinga class dinmu ba akawo yan mata,maman noor tace ai gaskia naga kyau yau wai Allah.Malik yace mutafi daga wurin aiki nake ,keke suka samu har gida tare suka shiga kasancewan rana ce babu kowa tsakan gida, suna shiga tawuce bedroom sai datayi wanka tashirya kafin tadawo ta linke uniform dinta ta ajiye,tayi tunani yafita shiyasa ta fito ta shiga kitchen din,tsaye tagansa yana zuba pasta cikin ruwan daya tafasa yanzu, kallonta yayi yace aiki ke akwai Sosai yau zaki iya yin stew da kanki ne?gyada masa kai tayi, yafita yace sai na dawo.
Tsaf tagama girkin kafin ta zuba a warmer already tayi sallan azahar, kitchen din tasake gyarawa kafin ta dawo parlor ta zuba abinci kadan tacit asha ruwa,kafin takoma bedroom ta dauko jikkanta ta bude littafin daaka koya musu yau tadinga bi da kallo tana maimaita karatun daki-daki du kinda ke bata gane bas ai tasaka pen tayi underlining ta niyyar idan yadawo sai ya ta nuna masa ya gyara mata,knocking taji ana yi ta warware veil din ta yafa kafin ta tafi wajan kofan tace waye? Dr hafsa tace nice,aydarh ta bude kofan tayi murmushi tace welcome auntie,dr hafsa ta mayar mata da murmushi tace thanks dear kafin aydarh tabata hanya tashigo anan parlor suka zauna,aydarh tace ina wuni?ya jikin inna?dr hafsa tace lafiya lau aydarh inna taji sauki ta fita ma,aydarh tayi murmushi tace masha Allah kafin tashiga ta zuba mata abinci data dafa sai ruwa kan plate ta kawo mata,dr hafsa ta girgiza kai tace aydarh kullun nazo ko gajiya bakiyi abinci dai abinci dai dana shigo amma ke idan kika zo nabaki kice kin koshe “aydarh tayi murmushi kafin tace “Allah auntie nakoshin ne “dr hafsa ta girgiza kai tace ai dayake ina lura dake baki son cin abinci sam aydarh tayi shiru tana murmushi bata ce komai ba,dr hafsa ta kalli aydarh bayan tagama kallon books din dake nan ajiye kan carpet kafin tace islamiya kika shiga ne aydarh ta gyada kafin tace erh,dr hafsa tace masha Allah Allah yataimaka,yau kika fara zuwa ne?aydarh tace erh yaune first day dina,dr hafsa tace Allah yabada sa’a aydarh tace “Ameen “babu wanda yasake magana cikin su, dr hafsa ta cigaba cin abinci ta kafin can tace yauwa aydarh so nake ki tambayi yallabai gobe zamuje wajan suna na lura babu inda kike fita sai tare da shi kawai aydarh tayi kafin tace “gobe akwai islamiya kuma “dr hafsa eyyerh karfe nawa kuke tashi ne?aydarh tace twelve ne closing time dinmu,dr hafsat ace ahh Alhamdulilah kinga ai sai wajan four zamu tafi kinga time din ai kun taso har ma kingama girki time din kin huta aydarh tace Allah yakaimu dr hafsat ace Ameen kafin su cigaba da fira sama sama duk labarin friends dinta take bata wani abun dariya wani kuma abun tausayi can dr hafsa tace kinga har naso na manta yau dasafe nafita clinic aka kawo wata zata haihu ,inalilahi waina illahil rajiun aydarh mata na wahala wajan haihu yaron kansa fa yakoma a chest din matar nan gashi yanzu doka ne an hana juyawa saboda ana samun matsala gashi jini ya balle wa matar nan sai bleeding take wallahi abun tausai abun yafi karfin clinic saidai nahada su dawani Doctor a genral da taimakon sa fa muka shiga aiki da ita emergency munyi aiki successfully am the saddest part of the event yaron komawa yayi daga karshe abun ba dadi,aydarh datayi shiru tana sauraron dr hafsa har tayi shiru duk da bawani Sosai ta fahimce abunda labarin ya kunsa ba amma sai data nuna jimamin ta sosai bakaramin tausayi matar taba ta ba da babyn dayarasu,tace babyn ya rasu auntie?dr hafsa ta gyada kai tace ya rasu aydarh ya rasu gyada ta sauke ajiyan zuciya tace Allah yayi masa rahama yaba maman lapia,dr hafsa tace Amin,kafin ta mike tace bara kiga na wuce gida daga general din nake ruwa kawai na watsa na fito so nake nadan samu hutu clinic zan kwana,aydarh tace sorry “dr hafsa tace tau sai anjima ki gaishe da yallaban idan yadawo,aydarh ta gyada kafin ta raka dr hafsa din har kofan part din,ta dawo ta kwashe plates din ta wanke ta ajiye kafin tadawo ta dauki books dinta ta wuce daki. Wanka yayi kafin ya zuba abinci yaci yana ci yana murmushi bakaramin mamaki take basa ba how sharp her brain is yana sa shi jin tana sake shiga ransa, yarda tayi abinci da yarda ta gyara kitchen din sai ya dinga tuna masa dream din wani abu mai kyau daya tabayi a baya yasha yin mafarkin wanda wani lokacin har murmushi yakeyi shi kadai idan yana tunanin mafarkin har yanzu kuma bawai yadaina ba time to time yana yi girgiza kai yayi kafin ya cigaba da cin abinci har yakarasa kafin ya mayar kitchen, parlor yafito kafin yahada iron ya goge sabon dinki dayayi kala biyu wanda daya kala daya ne shi da ango dr ibrahim wanda zasu saka a ranan daurin aure wani hadaddan ash gezner ne mai azaban kyau da tsada wanda Allh musa ne yasiya musu shida dr ibrahim din dayan kuma plain yard ne yasiya white aka masa dinkin kafta duk na bikin ne wanda ranan Tuesday zasu tafi su dawo sat bayan angama daurin aure, Sai da ya gama gogan kafin ya dauki kayan yashiga bedroom din ya ajiye kayan a wardrobe ta na nan zaune kan katifa Still hannunta rike da littafin ta tana sake dubawa malik bai ce mata komai ba kamar yarda ita batace masa ba ya ajiye kayan yafita yawuce masallaci bai dawo gidan ba har sai da akayi isha’I ,yana shigo parlor wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga dr ibrahim daga wa yayi kafin yayi kasa da murya yace “bad ai basu gama din ba?dr ibrahim ya fizgan da iska yace ina fa basu gama ba waye daman haka hidiman aure yake malik?malik yayi murmushi yace sai kayi hakuri ai ance idan aski yazo gaban goshi yafi zafi,just keep patience remaining just few days komai yawuce in sha Allah yeah,dr ibrahim yace in sha Allah amma wai daman haka kaji kaima?malik yashafa kai kafin yasa key din hannunsa ya dan sosa girar sa yace haka ma kowa yaji ibrahim amma kasan ko da hidiman sa, dr ibrahim yace hakane amma gaskia yau bazan iya fita kallon wasa ba,malik yace likewise ni gaji yau mun sha aiki oga ma yace idan muka dawo nasarawa Akwai maganan dazamuyi dashi dr ibrahim yace tau Allah yasa muji alkhairi abokina malik yace Ameen, ahankali ta bude kofan bedroom din tafito hannunta rike da books din islamiyanta ,yadinga binta da kallo kafin ya zauna itama ta nemi wuri ta zauna can nesa dashi babu wanda yace komai batayi magana ba shima baice komai ba can tayi kasa da murya kafin tace “ga shi nan din inda bangane bane “malik ya karbi book din yakalli inda bata gane ba, yace tau karanta naji book din takarba tana karantawa ya dinga binta da kallo yayi mamakin jin lokaci daya har ta iya rike karatun, inda bata gane din bane yasake maimaita mata lokaci kadan ta rike ta karanta masa tsab,har sai datagama kafin yace masha Allah, tashi tayi har takai wurin kofan bedroom din kafin ta juyu kuma ahankali ta koma ta zauna ta saukan da kanta kasa tace “ dazu ne auntie tazo tace mun wai nashirya zamu je wurin suna gobe kuma wai na tambayi ka “malik yayi shiru yana ta kallonta kafin can yace wacece kuma auntie? Aydarh tayi shiru kafin ahankali tace dr hafsa,malik yace itace tace ki tambayi ni cike da yarinta aydarh ta gyada masa kai yace su idan zaku sunan kin san sune ko miye?ta girgiza kai kafin yace idan ta zo kice nace aaa bazaki je ba,aydarh tayi shiru kafin ta daga kai tana kallonsa tace itace fa tace zamuje “malik yace nikuma nace bazaki je am I cleared? Aydarh batace masa komai ta koma bedroom dinta ta zauna tacigaba da juya maganan kamar hadda miyasa ma ta tambaye shi ai da bata tambaye shi ba amma ai ita auntie tace na tambaye sa to yanzu idan tazo yazata ce mata,wata zuciya tace ki gaya masa yarda yace din. Kamar yarda sukayi jiya yau din ma haka har sukaje islamiyan kafin yace a maida hankali, tana shiga aka fara karatu kaman jiya yarda lokacin break ajin kamar kasuwa yau dai su maman baffa sun samu dama aydarh na zaune tana duba littafinta maman noor tayi mata sallama ahankali ta amsa masu sai da suka hada ido jin yarda aydarh ke magana hausan ma kaman foreign take mai mugun dadi Maman baffa ta washe baki tace ina kwana ya gida ya yara,aydarh tace Alhamdulilah maman noor tace anya dai yara saidai ki tambayi mai gida amma da ganinta amarya ce, maman baffa tace haka fa,zaman sukayi kafin maman baffa tace amma anan anguwarku kuke ne?aydarh tace ah’ah maman noor tace Allah sarki ya sunanki ?aydarh tace ASEYARH maman baffa tace masha Allah auntie asiya nidai sunana farida yara na biyar amma anfi kirana da maman baffa a nan anguwar nake,aydarh tace Allah sarki still bata dauke nikkab din taba,maman noor tace sunana hadiza yarana biyu a malaysia muke nida mijina kafin mu dawo nan kano maman noor ake cemun,Aydarh tace Allah sarki labari suka dinga janta dashi duk bata amsa su,sai kadan kadan wasu daga cikin yan ajin suka taho inda su aydarh suke cike da girmamawa, cike da isa na yarda suke bata girma kanta na girma tace masu lafiya wata tace anty hadiza dan Allah wai turare muke so waccan ya kare nawa dayar ma tace haka maman noor tace tau badamuwa amma gaskia sai zuwa jibi saboda inda abun yi yau da gobe,suka ce tau Allah yakaimu lapia nan fa maman noor ta tsinke tacigaba basu labarin malaysia wanda babu ranar dabazata zaunar dasu tabasu labarin nan ba, bakaramin ganin girmanta sukeyi ba ganin duk tafisu wayewa daga ita sai maman baffa ,dayawan labarin karyane aydarh najinta yawwanci abunda tafada duk karyane kan labarin malaysia,ita kau duk dan ta birge aydarh takeyi duk dan itama tadawo wajanta, ringing bell akayi lokacin komawa break yayi kowa ya koma wajan zaman sa aka cigaba da karatu,yau ma kamar jiya tun kafin twelve yazo daukanta, suna fitowa already ya tsayar da keke suka shiga suka wuce gida, ko gidan bai shiga ba mai keken ya wuce dashi wajan aiki.
Dr hafsa tace babu komai karki damu tunda bai bari ba shikenan wani lokaci idan yabari sai mu fita din aydarh tayi shiru bata ce komai ba amma sai taji duk bata ji dadi ba,dr hafsat ace karki damu fa aydarh babu komai kinji sai nadawo in sha Allah aydarh tace Allah ya tsare,dr hafsat ace Amin thank you aydarh kafin tawuce, tafita kofan ta rufe ta shiga kitchen jallof din pasta tayi masu already yayi cefane hadda cat fish tsab ta yi girkin kafin tayi slicing fruits a plate tashiga tayi wanka ta karasa gyara kitchen din,kadan kadan take jin ciwon maran datake tun dazu na kara karuwa,daurewa take amma ina ta kasa bedroom ta koma ta kwanta a dadafe, yana shigowa toilet yafara shiga yayi wanka jallabiyan sa daya wanke yazagaya ya dauko yasaka kafin yashiga kitchen yadinga bin abincin da kallo,yarinya nan komai nata nadaban ne abinci yayi dadin da shi kansa ya manta when last daya ci abinci mai dadi irin wannan ummi yatuno, dasu aysha sai yaji hawaye ya taru a idonsa dasauri yasa hannu ya goge he surely missed them words cannot express how he missed them, bayan yagama cin abinci yasha fruits din sosai yadawo parlor ya kwanta tun daya dawo bai ganta ba shiyasa yatashi ahankali ya mike yashiga bedroom din ya tarar da ita kasan carpet zufa yarda take juye juye kawai ya tabattar masa da she is sick hankalinsa tashe yakarasa kusa ita dasauri ya dago ta ya daura ta a jikinsa yace ASSEIYARH kimun magana what’s wrong with you tell me mike damunki dakyar ta iya nuna masa maranta dake masifafan ciwo kamar zata rasu gently yasa hannu.
Gently yayi placing hannunshi kan maran wani irin ajiyan zuciya ta sauke,kafin tawani irin rike shi sosai kaman zata shiga jikin shi tsabar azaban datake ji, malik din ma yarasa abunda zaiyi bakaramin daga masa hankali tayi bad uk abunda take sam batasani ba, zufa keta keto ma duk iya kokarin sa na yagane abunda ke damunta yakasa addua kawai ya keta faman tofa mata kafin tayi wani irin yankuri sai data wanke masu jiki kaf da amai zuwa yanzu hankalin malik yakarasa tashi amai take kwara wa kamar zata fito da kayan cikinta, duk ya kara rungumeta a jiki du kaman datake a jikinshi takeyi ,sai da tayi kusan 10mins tana abu daya kafin ya lafa wani irin kuka take naban tausai da kaganta kasan she is in pain duk tabata musu jiki yasa shi tashi ahankali dauke da ita hannu kamar yar baby sam bayajin nauyinta idan ya dauketa kamar paper toilet yashiga da ita kafin ya zaunar da ita nan kan kujeran dake a toilet din bazata iya yin komai ba dan she is in serious pain, hannunsa yakai gaban zip din bubu gown din jikinta wace duk tabata da amai, kafin gently yaja zip din kasa yabude white soft boobs dinta dake cikin black lace foam bra suka bayana, dawani irin speed malik ya dauke idonshi yah rabbil alameen ya furta ahankali yasa hannu yakama shoulder dinta jikinta very warm and soft, yafara cire rigan gently kamar mai tsoron cire mata din har sai daya zo wajan wrist kafin yasa tsaya ganin yarda take wani rufe ido kaman zata suma yasa shi karasa cire mata gown din yasaka gown din a bucket kafin yadawo cikin dakin ya dauki flask din ruwan zafi ya koma karamin towel din datake tsane gashin yadauka ya goge mata jikin tass kafin ya cire nashi rigan shima yasaka a bucket yarda yashiga da ita rike ahaka yadawo da ita daga ita sai bra da undie still inner cap din kanta na akan wasu kayan ya chanza kafin yadawo ya bude duvet din daya rufe ta,ganin yarda take shaking,kafin ahankali dakyar ta iya bude bakinta tace “abdominal pain “jin haka yasa shi tuna farkon haduwar su da kalan drugs din daya siya mata dasauri yamike ya fita,pharmacy din nan bayan gidansu yashiga yasiya allura da magani sai sanitary babba kwara daya,yarda yabata haka yadawo ya iske ta alluran yahada idonta na a rufe kafin gently yayi bismillah yayi mata dan ya mutsa fuska tayi kafin tasake maida idonta ta rufe gyara mata kwanciyan ta yayi yacigaba da tofa mata addua kusan 5mins kafin yaji numfashin ta na sauka ahankali alaman bacci ya dauke ta sauke ajiyan zuciya yayi kafin yatashi ya shiga toilet din ya wanke rigan ta dana shi ,kafin ya wanke toilet din fess,yafito ya dinga bin ta dakallo yarda ta cure jikinta waje daya,fita yayi parlor kafin yashiga kitchen ya daura ruwan zafi a tukunya yafita oat yasiyo sai madara da sugar,lokacin daya shigo ruwan sun tafasa ya juyu su a flask kafin yafito yakoma dakin Still bacci take daman yasan zatayi baccin carpet din yagoge da detergent kafin yakoma kitchen din yasake daura wasu ruwan masu yawa a tukunya sai dasuka tafasa kafin ya juye a flask yadawo parlor ya zauna. Ahankali take bude idonta sunyi mata nauyi ,ya dinga bin ta da kallo ko kiftawa babu ahankali tafara kokarin mikewa zaune kafin tabi jikinta da kallo babu riga jikinta sai bra da undie wani irin fadi gabanta yayi,yana lura da ita so take ta tashi yasa shi mikewa tsaye yafita daga dakin, har sai da ya rufe kofan kafin tasamu ta tashi walking slowly ta dauki flask din wanka tayi kafin ta wanke pant dinta da undie dasukayi stain kadan ta daura towel wani pant din ta dauka da pad tashiga toilet din sai data shirya kafin ta fito wardrobe tabude ta dauki rigan atampha ta tasaka, ta koma ta zauna kan katifan looking so pale and weak,ga tunanin yarda yacire mata riga daya kasa barin ranta tunda ta farka taganta a haka,bude kofan dakin akayi yashigo tayi saurin sukunyan da kanta kasa, kwalla har ya cika mata ido,fita yayi yakoma kitchen ya hada mata oat,yadawo dakin ahankali yazauna kasan carpet kusa da kafanta kafin yace “take “gently tayi raising head dinta takasa hada ido dashi tasa hannu ta karbi cup din oat din dayake mika mata, hannu ta dinga rike cup din kanta a kasa shima zama yayi nan kan carpet bai sake ce mata komai ba,kusan 3mins yaga bata da niyyar sha kafin yakalleta yace “take it sai ki sha magani “kamar mai jiran umarnin sa haka ta mutsa spoon din dake cikin cup din kafin tasa spoon din ta debo oat din tafara sha ahankali sam bakin ta babu dadi amma ahaka ta daure tasha kusan cup daya ,bai tashi ba har sai datagama shan din kafin yawuce kitchen ya dauko mata ruwa yadawo drugs dinta yabude ya balla mata duk 2din kafin yace take this ta dinga bin maganin da kallo kamar yaune na farko data fara ganin magani,hannu ta miko gently ta karba kafin ta karbi ruwan sai data rufe ido da karfi kafin ta hadiye maganin, kafin ya kalleta yace how are you feeling now?tayi kasa da kai ahankali tace “better “yamike yace sorry yasa kai yafice daga dakin.
Wajan nine yasake shigowa dakin yanzu ba bacci take ba ta farka,kallo daya tayi masa ta dauke kai shikuma kallon yake ko kiftawa babu ciwon datayi na wunin yasata fadawa sai wani milk glow da skin dinta tasake yi calaban kanta ya tsufa still da kyaun sa, sallama yayi ta amsa kafin yace yah jikin? “Tace dasauki “kitchen yashiga ya dauko mata abinci a plate sai apple daya siyo mata yanzu yayi slicing ya daura a plate yadawo ya ajiye mata kafin ya juya ya koma parlor kadan tace Abinci sai apple din data sha,ba laifi tasha dayawa har yanzu jikinta bai dawo nata ba , kwashe plates din tayi tafita zata kai su kitchen bai parlor sai kofan dake bude iska nata daga curtains din parlor kitchen din tashiga ta ajiye plates din kafin sama sama ta dinga jin maganar malik din duk da ba da karfi yake maganan ba amma yanayin voice dinsa irin na boss din nan ke shiga har brain din mutun, tayi shiru har zata koma bedroom sai ta dinga jin maganan wata can kasa kasa,kamar wace magnet ke ja ko kuma wani yace tafito haka ta sa kai ta lika kadan,Ramlah tagani tsaye sai malik dake tsaye ya zuba hannunsa a pocket din jeans dinsa fuskan nan babu yabo babu fallasa ,yarda take wani fari da ido yasa aydarh dauke kai daga duban datayi mata,bata yi magana ba dan shi bai ma lura da ta fito ba,Ramlah kau sarai ta ganta shiyasa tawani kara gyara tsayuwa tana turo kirji kaman allon sha,slippers dinsa dake nan bakin kofan black ta saka akafanta sunyi mata yawa sai sukayi ma kafan wani extraordinarie kyau ahankali tasa kafan ta sauka daga kan step daya dake nan wajan kofan kafin ka sauko ventilation dinsu wani wawan kallo tabi Ramlah dashi kamar taga abun kyama,hannu tasa ta kamo damtsan malik din,kamar daga sama yaji soft tafin hannunta dake warm gashi soft kamar pure cotton tunda ga kafan shi har brain dinsa yaji wani irin abu ya tsarga sa wallahi bakaramin kokari yayi ba wajan controlling kansa,Ramlah kau kamar zata mutu batasan miyasa take bala’In shakkar aydarh ba, malik ya juyu yana kallonta kamar yarda take kallonsa ido cikin ido yarda ta hade rai fuskanta babu alamun wasa bakaramin tafiya da imaninsa tayi ba duk yanda kafin idonsa yayi tasiri a kanta amma ta daure ,Still ta kama hannusa gam ta rike ko shoulder dinsa bata kai ba Wallahi kallonsu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 83