sha gabansa wani kalan wawan kallo yayi mata yahada fuskar sa yawani hada giran sama da kasa billahi yarda yayi din kamar zata suma, gathering courage tayi tawani lankwasar da murya tace karar matarka na kawo maka aydarh najin haka tawani hada rai tayi wucewanta tana tafiya kamar batasan taka kasa, batasan raini ita kunyar kanta ma zataji ace ta tsaya tana magana da wannan trash din,malik ya ja da baya ya gyara tsayuwar sa bai ce komai bay ana sauraron ta tace kofan part din ku ta sakar mun a fuska daga naje duba ko kana nan malik bai ce komai ba yayi wucewar sa yabar ta nan tsaye kamar status.
Toilet tashiga tayi alwalla kafin tafito ta chanza kaya ta hau prayer mat ta kabbara sallarh shigowa yayi dakin ganin tana sallarh yasa shi zaunawa kan katifa har sai da ta gama sallan ,yace miyasa kika buga mata kofa a fuska aydarh tawani hada rai ta juyo tana face dinsa sai kuma ta juya kai tace to ita miya hanata ka tambaye ta abunda tamun,shi wallahi dariya ma ta basa yarda tayi din yayi kasa da murya yace ai nasan ita ke da gaskia shiyasa kuma ni naso ma ace ta rama,aydarh ta mike tsaye tace to ai sai ka turo ta tarama din, bata tsaya jin abunda zai fada ba tayi fitan ta parlor ta bar masa bedroom din.
Kitchen ya shiga ya zuba mata pasta daya dafa a plate yazo parlor ya ajiye mata gabanta without saying a word ya shige toilet din nan parlor yafara wankin kayansa jiya yayi mata nata wankin,bin bayansa tayi da kallo ta kafin ta mayarda idonta kan plate din ahankali take cin abinci cikin nutsuwa har tagama kitchen ta kai plate din ta ajiye ta dinka bin kitchen din da kallo ko dauke ido babu maganar dr hafsa ce ke dawo mata fresh a brain tama rasa kalar tunanin da zatayi,juyawa tayi tafita bedroom din ta koma ta zauna ta zubawa waje daya ido,yanzu haka na nufin ita zata cigaba dayin duk wani aikin dayake yi?sai kuma ta girgiza kai a ranta tace ai Allah bai kamaki da laifi tunda shi keyi bake kika saka shi ba dawannan tunanin ta zame ta kwanta amma sam zuciyanta bai yarda da wannan conclusion din,ahaka har bacci yayi gaba da ita da tunanin a ranta.Tun safe yake jin yanayin jikinsa babu dadi yasan kuma cewa maybe ciwonsa ne zai taso sam sai yabar hakan a ransa ya cigaba da addua domin bai san yarda zaiyi ba idan ciwon nashi yataso a yanzu,ko daya dawo sallan isha’I da kyar ya kwanta kan shimfidar sa dayayi anan parlor wani irin yanko masa zufa keyi lips dinsa har hadewa sukeyi yarda ciwon ke masa a yau sai yaji kamar ransa zai fita he is seriously in pain his condition is much critical babu abunda yake iya furtawa sai inalilahi waina illahil rajiun zuwa wani lokaci he is trying much to breath in and out numfashin sa ya toshe waje daya salatin ma yakasa bakin shi yahade waje daya.So take yashigo ta tambaye sa inda littafin azkar dinsa da take karantawa yake shine kawai abunda takeyi yanzu zuwa yanzu har tafara fahimtan wasu abubuwa daga ciki tafara gyara kura kuranta na sallarh shiru shiru taji sa bai shigo ba yasata bin kofan bedroom din kallo kamar zata hango sa ta kofan tashi tayi ta yafa mayafin abayanta tana tafiya ahankali har tafita parlor ganinsa tayi a kwance yayi facing wall tasan ba bacci yakeyi ba maybe da gangan ya dauke littafin daman dan yasan zata zo nema shine yake wani pretending as if he is sleepy,batace komai ta zaune can karshan parlor tayi raurau da ido kafin murya can kasa tace ni kabani,shiru bai tanka ta ba bakaramin haushi abun yabata ba,bata gaji ba tace ai nidai babu ruwan ka dani tunda bana taba ma abu wallahi,still malik bai tanka ta basai wani irin numfashi da yasaki kamar wanda aka zarewa numfashi gabanta ya yanke yafadi ta mike tsaya batasan abunda yasa yayi numfashin amma numfashin dayayi Kamar wanda ke struggling da breath ensa ahankali ta matsa kusa dashi tana kallon shi,juyuwa yayi jikinsa ya jiqe sharkaf da zufa ganin yanda yake zufa yasata binsa da kallo ahankali ta daga idonsa da kyar yayi mata alama da hannu nata zo,yarda gabanta ke faduwa kamar zai fito waje yasata bin bango har ta karasa kusa dashi ahankali yake fadin ruwa ruwa bataji da kyau bah akan yasa cewa baka da lapia ne hankalinta a tashe gyada mata kai yayi ahankali kuma yasake buda baki yace ruwa dasauri tashiga kitchen ta dawo hannunta rike da pure water yakasa daga hannunsa balle yakarbi ruwan yasha ganin hakan yasa ta fasawa ta kai ruwan daidai satin bakin sa daga nan kwance tabasa ruwan yama kasa sha sai zubewa yakeyi ta gefen bakinsa, yarda jikinsa yake kyarma bakaramin daga mata hankali yakeyi ba tarasa abunda zatace masa,ahankali tace sannu,hannu yasa ya rike nata hannun tanajin yarda jikinsa yayi mugun zafi he is running temperature ahankali tace sannu mike maka ciwo?kanka ne?you are running temperature mike damunka yarda take maganan muryanta very slow and innocently kamar zatayi kuka ,daurewa kawai yake amma ji yake kamar zaa zare mashi rai cikin shi nawani irin masifar ciwo har yanajin yarda jinin shi ke gudu a veins dinsa ,aydarh dai tarasa yarda zatayi banda bin sa da ido babu abunda take bata son taga wani na ciwo tana da mugun tausai wayar dake flashing light wanda a silent take ta kalla kiransa ake da kamar kar ta dauka sai kuma ta kai hannu ta dauki wayar kallo daya tayiwa sunan mai kiran tagane ko waye sallama akayi cikin sanyin murya ta amsa daga can dr ibrahim yace ahh madam ina wuni,ina wuni tace masa kafin yace baya kusa ne?aydarh ta kalle shi ganin yarda yake kyarma na yanzu yafi na dazu can kasa da murya kamar zata fashe da kuka tace bai da lapia dr ibrahim yayi salati yace subhanallah tun yaushe miyasa me sa?Tace nima bansani ba yanzu ne kawai nasame sa ahaka dr ibrahim yace karki damu ganin zuwa yanzu,15mins sai ga kiran dr ibrahim yasake shigowa tana nan zaune ta zuba masa ido ko daukewa babu hankalinta idan yayi dubu yatashi bata kowa batasan kowa anan ba sai shi,a duniyar ma baki daya yanzu bata da kowa sai shi,daukan kiran tayi yafada mata yana bakin kofan part dinsu dasauri ta koma bedroom tasaka hijab dinta kafin ta bude masa kofan,tun daga bakin kofa ya hango malik din ya hango yarda yake kyarma ga zufa yanayi dasauri yashigo ya durkusa kusa dashi yarda jikin yayi zafi yana zufa ga kyarma ba karamin dagawa dr ibrahim hankali yayi ba dasauri yasaki gudun fan din parlor,yakalli aydarh yace tun yaushe yake haka madam kuma miyasa baki kirani tun dazu ba sai dakika bari abun yayi worst har haka ita dai aydarh batace komai kanta nakasa ko dagowa batayi ba hawayen idonta take gogewa gently ganin bata ma kanshi lokaci yake ga condition din malik fita yayi yatafi pharmarcy yasiyo pain reliever injection yafara yiwa malik din kafin yasamu nutsuwa gano abunda yasami malik din sosai yake kokarin kan malik din amma abun kamar yana so yafi karfin sa duk yahada zufa,juyawa yayi yana kallon aydarh dake tsaye kamar zata shige jikin wall din parlor da ka kalli fuskanta kasan hankalinta ba a kwance yake ba yace madam ko mutafi asibiti ne naga kamar his condition is getting worst aydarh dai takasa cewa komai sai bin malik da kallo take,ahankali yake bude idonsa kafin yadaga hannunsa ya taba dr ibrahim dr yayi sauri ya matsar da kunnan sa daidai satin bakin malik din murya can kasa malik yake gayawa dr ibrahim alluran da zaya siyo yayi masa,dr ibrahim likitane yasan kalar alluran yasan amfaninta kallon malik din ya dinga yi kafin ya mike yafita pharmacy ya koma yasiyo alluran ya hadu dana bacci yayi masa,cikin good 10 minutes malik yafara sauke ajiyan zuciya numfashin sa yafara daidaituwa sweating din dayake yana bushewa kyarman dayake yana rage da alama alluran baccin na fizgar sa, dr ibrahim ya kalli aydarh yace Alhamdulilah madam he is getting better ,ina ga zan tafi yanzu tunda nayi masa alluran bacci ko zai farka sai cikin dare ko da asuba kuma in sha Allah daya farka shikenan ma,ko ki kamasa ku shiga bedroom kar ya kwana anan dan akwai sanyi sosai aydarh ta gyada sallama sukayi da dr ibrahim kafin taje tasakawa kofan key ta dawo ta kusa 5mins tana kallonsa ko dauke ido babu,yarda yake bacci a matukar wahala zaka san yayi matukan jigatuwa, mikewa tayi ahankali ta bude kofan bedroom din first kafin tadawo ta dinga binsa da kallo to ita ta ina ma zata fara kama sa ina ita ina shi ma? Kuma yace akai sa bedroom saboda sanyi yanzu yazatayi? Dr hafsa ce tafado mata a rai tayi saurin kunna wayarsa takalli time kusan pass ten yanzu girgiza kai tayi aranta tace yazaayi ta taba sa ita da ba matarsa ba ma ai haramune wata zuciya tace mata ke ce matar ke yakamata ki kamasa,da wannan tunanin yasa ta kara gyara zaman hijabin jikinta hankali tasa hannu ta bubbuga pillow dayake kwance akai,baccin nasa bawai yayi nisa ba duk wani motsin datakeyi yana ji amma bazai iya ce mata komai ba hannunta ta mika masa,kallonta yakeyi sosai ita kuma ta saukar da kanta kasa wani irin rahama ke bin duk wani parts na jikinsa har cikin soul dinsa yake jin sallama da nutsuwa sosai yarike hannun nata as if his life’s defenses on her hand kallonta yake cike da tausai da tunanin daban daban sai yanzu ta dago ido takalli kwayar idonsa tayi saurin dauke kai domin wani irin fuzgagen kyau da tagani kwance a sick face dinsa, tunda aka daura auranta dash isai yau yake kallon kaddarar da abunda aure ke nufi ba karamin tausayin kansa yaji ba da ita baki daya a yanzu fa su basu da kowa basuda komai bayan su biyun shikenan yau da ta Allah takasance akansa bai san irin halin da zata shiga ba,yasaba da wannan ciwon amma bai taba jigatuwa irin na yau,tagaji da durkusan datayi ga tafin hannunta da nashi dasuka hade waje daya very soft and clean, hankali muryanta can kasa tace yace nan da sanyi kaje bedroom bai ce mata komai bas ai bin da yake da kallo kafin ahankali ya mayarda da idonsa yarufe yafara motsa bakinsa ahankali kafin yace sai ki dauke ni ki kaina can din,sai sannan ta bude ido tana kallonsa sosai baki bude kafin tace baka da lapian ma amma sai ka dinga gaya magana “to ni ai bazan iya daukan ka ba wallahi wait did you ever look your self through the mirror?ya girgiza mata kai bakaramin relief yake samu a maganar nan dasukeyi ba tayi kasa da murya kamar mai tsoron abunda zatace tace to wallahi you are very tall and fat takarasa tana kawar da kanta gefe tareda turo baki duk da halin dayake ciki bai hanashi yin murmushi ba dan ba karamin dariya tabashi ba zatayi iya yin kwana biyu batayi magana Amma duk ranar datayi magana sai ta bashi dariya she is very sturbborn and arrogant ga mugun tsoro da raini kuma Allah yaga abunda yagani yayi miskila bai ce mata komai sai kokarin mikewa tsaye dayayi cike da karfin hali yake komai dan he is brave enough duk yarda alluran baccin ke fizgar sa haka ya daure yamike ganin ya mike yasata mikewa itama tana kallonsa hannu yasake mika mata itama ta miko nata hannu da taimakon ta duk da bawani karfin kirki gareta ba har suka isa bedroom din side din datake kwanciya anan yayi ma kansa masauki,wallahi scent din wurin ba karamin dadi yake masa ba hankalinsa nawani masifan kwanciya (ni fa no words can express waye aydarh gareku)komawa tayi can waje wardrobe ta zauna bata jin bacci sam sai ta tura kanta tsakanin laps tun yana kallonta har wani baccin ciwo yayi gaba dashi.Anan inda take tazame ta kwanta bacci barawo yayi gaba da ita,kiran sallan asuban da akayi yayi daidai dawani irin azababan ciwo daya Sake saukar masa wani irin nishi yafara yi wanda yasa ta farkawa daman bata da nauyin bacci sam,jin nishi dayakeyi yasa ta saurin kunna globe din dakin haske tarr tasauke idonta a fuskar sa idonshi yayi wani kala kamar rushin wuta gabanta yawani fadi tama kasa matsawa kusa dashi domin batasan abunda zatayi ba yanzu ma kamar jiya kiran wayan dr ibrahim ne ya shigowa wayan shi daman yabari sai asuban saboda ya daidaici lokacin da zai farka din dasauri tayi accepting call din bata jira jin abunda dr ibrahim ke fadi ba muryanta cike da rauni tace bai fa da lapia har yanzu he is breathing hardly inalilahi waina illahil rajiun shine kawai abunda da dr ibrahim ke fada yace wait kwantan da hankalinki ki bara nakira dr hafsa yanzu tazo ku same ni a clinic kafin yakashe wayan,cikin few minutes taji ana buga kofan part din tajin haka tasan dr hafsa din ce dasauri ta fita ta bude mata hankalinta a tashe kwalla cike a idonta dr hafsa ta kama hannunta tace kiyi hakuri aydarh in sha Allah babu abunda zai same sa kinsan yanzu asuba ne babu masu keke shiyasa na kira yaron neighbor mu shima keke garesa ki shiga sai ku fito mu wuce, komawa dakin kawai aydarh tayi wardrobe ta bude ta fito kudin nan dake cikin bag din ta rike a hannu bazata iya kamasa ba kuma ai bazata ce ma dr hafsa ta kama mata shi ba ahaka tasamu da yarda yake daurewa ta kamo shi dr hafsa ta rufe part din ta cire key din,titi babu kowa hakan yasa basu hadu dawani traffic ba sosai suka isa clinic din dr ibrahim yanajin tsayawar keke yasan su ne yayi saurin fita zuwa yanzu bakaramin galabaita malik din yayi ba da taimakon mai gadi da dr ibrahim suka shigo da malik din cikin clinic dr ibrahim da dr hafsa ke tsaye akanshi dayawa basu da manya alluran da zai bukata tunda zuwa yanzu su biyu duk sun san abunda ke damun shi,fita dr hafsa tayi tabar dr ibrahim a dakin aydarh ta ganinta ta taso daga inda take zaune kafin dr hafsa tayi magana aydarh tasa bayan hannunta ta goge kwallan idonta kafin ta mika mata kaf kudin dake hannunta 20k babu yanda dr hafsa ta iya haka ta karbi kudin domin suna bukatansu wajan siyo sauran alluran, fita tayi tafido wayanta daga aljihun wando baccin tayi dialing wata number ana daga tace gatanan zuwa mai keken daya kawo su shi yakaita babban pharmarcy din duk wani medications daza su bukata tasiya ta koma dr ibrahim ya dinga binta da kallo ganin data da alluran da maganin basu da lokacin tsayawa tambayoyi kawai ya amsa yacigaba dayi wa malik din duk abunda yadace .
Dr ibrahim dai baice komai ba har sai datayi shiru ,ajiye abunda ke hannunsa yace ni kaina abun yabani mamaki kuma naga miye zai kawo masa wannan ciwon bayan yanada aure?dr hafsa taware hannu tana tabe baki tace ni kaina shi nake tunani dr,dr ibrahim yasauke ajiyan zuciya yace anyway inaga personal life dinsu ne saboda haka there’s no any need muyi involving kanmu a ciki dr hafsa ta sauke ajiyar zuciya tace “gaskia” ta mike tsaye tace bara naje office dina aydarh na can nasan nagaji nima I need to rest dr ibrahim yace tau ba damuwa zuwa anjima idan yafarka sai kice tashiga ta duba sa bacci yake yanzu tace tau.dr hafsa dake kallon aydarh ko kiftawa babu with seriousness a fuskanta tace aydarh am older than you nayi mamakin dakika bari har mijikin na shiga irin wannan condition din, kinsan mi yafi bata mun rai?yarda.
Dr hafsa tace aydarh baki san fushin da mala’ikun rahama zasuyi dake ba kan kusamu sabani da mijinki kin kaurace masa,aydarh are you normal?am highly disappointed on you! wallahi aydarh kina aikinmi zaki bar mijinki kinsan halinsa kinsan yanayin rashin lapian sa amma fushin zuciya yasaki barin sa cikin wannan halin,aydarh dai kanta nakasa sam tarasa abunda dr hafsa ke nufi can ta dago kanta ta goge hawayen dake zuba a kuncinta ta dinga kallon dr hafsa din ta dai yi shiru batace komai ba ahankali dr hafsa tamike ta zagayo inda aydarh ke zaune taja kujera kusa da ita ta zauna,murya can kasa takama hannun aydarh tace nabaki shawara?still aydarh na kallon dr hafsa,dr hafsa tace don’t be silly aydarh you are wise enough take me as your biological sister your eldest sister just feel free let’s talk mike damunki kika bari har kika aikata abunda yafaru? Aydarh ta sauke kanta kasa kafin tasa bayan hannu ta goge hawayen ta tass” tace Allah babu nidai babu abunda nayi masa wallahi, dr hafsa ta saukar da ajiyan zuciya ta mike tsaye tace anyway aydarh zan jiraki duk lokacin dakika ga yadace you are always welcome ,I will be waiting, Aydarh dai tayi shiru batace komai ba,can ta mike takalli Doctor hafsa tace zanyi sallarh,dr hafsa tace tau shknn ki shiga toilet sai kiyi alwalla akwai prayer mat a bag dina,sai datayi sallarh kafin ta mike,tace auntie zan iya duba sa?tafada tana wasa da gefen hijab dinta kamar mai jin kunyar abunda tafada din,Dr hafsa tayi murmushi ta girgiza kai tace kya ji dashi kibari sai anjima yanzu yana bacci muje gida kiyi wanka kisamu kiyi girkin dazaki kawo masa ki dauko masa kayan da zai sake, Aydarh ta girgiza kai tace ahah zan tsaya anan din babu yarda batayi ba dr hafsa tabar ta amma tace dole sai sunje tayi wanka tayi girki kafin tadawo ba dan taso ba haka tabi dr hafsa din suka wuce cikin gidan tawuce da key din a hannunta ko da tashiga tsakar gidan babu kowa part dinsu ta wuce ta bude tashiga, bedroom din ta wuce tacire hijab din ta linke,few minutes ta dauka tafito a toilet din daure da toilet sai karamin da ta daura akai, Vaseline ta shafa kafin ta dauko sabon bubu gown din dasuka siyo tasaka,plain light purple inner cap din ta tura calaban kanta dake nan ya maida ta kamar kan yaran hadaddun larabawa ba karamin kyau rigan yayi mata ta kwanta a jikinta luff color din rigan yabi skin dinta Side din wardrobe dinsa ta bude ta dinga bin kayan dake nan a wanke tass da kallo faran jallabiya ta daukar masa sai short da singlet dinsa perfumes din dasuka siyo jiya ta dauka tasaka masa a ledan ta yafa mayafin gown din ta fito hannunta rike da ledan,sai sannan gabanta yafadi tunuwa datayi dr hafsa fa tace tayi masa girki ita mi zata dafa masa? Bata taba tunanin rana irin haka zata zo a rayuwarta ba ranar dazatayi regretting duk wani actions dinta na baya bata tsaya ta koyi girki ba duk kokarin oum akan ta koya din kwalla ne a idonta ta gaji da kukan nan she just wants to face the reality now tashirya karban rayuwan da suke a yanzu wata zuciya tace hadda karban shi a matsayin miji? Noo shine ta furta a fili this is the last thing dazanyi a rayuwa na karbansa a matsayin miji bana son sa, knocking kofan da akayi yamaido ta daga dogon tunanin data tafi, ahankali ta ajiye ledan hannunta tanufi kofan ta bude dr hafsa ce tsaye rike da basket a hannu, sanye take da doguwan rigan atampha sai labcot din ta tayafa white jersey veil, murmushi tayi tabi aydarh da kallo kafin ahankali tace Allahumma bareek tabarakallah mrs ABDOOLMALIK you fine die matan malik aydarh tayi murmushi tace thanks dr hafsa tace Allah yasa dai baki daura girkin ba ina shiga gida fa na tuna akwai stew a frigide din inna white spaghetti kawai na dafa,aydarh tayi murmushi kadan tace aa yanzu ne zan daura sai naji knocking dr Hafsa tace tau Alhamdulilah tunda baki daura ba,sai ki dauko masa kayan mutafi na hada abinci dake nasa baki karya bai dan mukaje can sai ki ci ba?aydarh ta gyada mata kafin ta dauko ledan suka fito tana rufe kofan ne dr hafsa,tace yawwa aydarh har zan manta yanzu naga Ramlah a kofan gida tau kinsan inna bata nan,shine nake fada mata yallabai na asibiti idan innan tadawo sai tashiga tafada mata idan yaso sai ta iske mu can kinsan halin inna,idan baa gaya mata ba rashin mutunci sai wanda ta manta,aydarh da tagama rufe kofan ta kalli dr hafsa tace waye kuma Ramlarh?dr hafsa tace yarinya dake part din can aydarh tagane wacce take nufi tsaf amma bata nuna mata ba ta juya kawai suka wuce, a kofan gidan suka samu keke suka wuce clinic din,a keken dr hafsa takalli aydarh tace wannan perfume din naki yanada masifan dadi kuma kinsan mi yahadu da natural body scent dinki shiyasa yake fitan dawannan kamshin aydarh tayi murmushi tace “ Erh” dr hafsa tace ahakan bakiyi lacking komai shine kike nima ki jazawa kanki ko aydarh tafada da alaman tambaya aydarh dai tayi shiru batace komai ba,bakin clinic din mai keken yayi parking dr hafsa ta biyasa suka shiga ciki.Rabiah ce zaune a dakin a kujeran dake kusa da gadon da malik din yake kwance idonsa arufe yake amma ba bacci yake ba,sai wani kallonsa take kamar tasamu t.v dr Ibrahim ne yakira iya yace ta ba rabiah takawo masa ruwan zafi a flask shine tace zata shiga ta duba malik yace mata tau zata iya shiga bara yaje yayi attending wasu patients dasuka zo yanzu, kallo daya aydarh tayi mata ta dauke kai ta ajiye kayan dasuka zo dashi a gefen drawer drugs din dake dakin,dr hafsa ma ta ajiye kayan dake hannunta tace sannu rabiah sai sannan rabiah ta dago tace mata yawwa mun kwana lafiya?dr hafsa tace Alhamdulilah,aydarh ko,ko iskan daya kwaso rabiah bata kalla ba balle har tasa ran zata amsa ta,dr hafsa ta kalli rabiah fuska babu wasa tace rabiah ina ga ki tafi tunda ga mai dakinsa tazo rabiah takalli dr hafsa kafin ta maida kallonta ga aydarh,kallo daya tayi mata gabanta yayi wani irin faduwa wani irin kyau tagani kwance a fuskan aydarh rigan jikinta kamar dan ita akayi ta,batace komai ta mike ta fita daga dakin dr hafsa tabi bayanta da harara, sai da tafita kafin tace aydarh bara naje sai ki tashi sa yayi wanka yace abinci drip din naga ancire masa saura allura daya maybe anjima,ku koma gida,Aydarh tace to, bayan fitan dr hafsa zama tayi a kujeran da tashi wanda tafi kusa da malik din cikin few seconds takare ma fuskansa kallo kafin ta dauke ido karaf yabude idonsa fess a kanta kallonta ko kiftawa babu, ta kalle sa kafin ta saukan da kanta kasa tace how are you feeling? Murya can kasa irin na wanda yayi ciwo yace “fine”batasake magana ba shima bai sake magana basai can yace zanyi wanka, bata tanka sa ba ,ta shiga toilet din dakin very tidy koi na fess kafin tadawo ta dauki flask din ruwan zafin da tagani a gidan tahada masa kamar yanda yakeyi mata,tadawo ta tsaya atsaye tayi folding hannunta a kirji yarda yake kallonta kamar irin yau dinnan yafara ganinta can ta gaji da tsayuwa tace “ko ba yanzu zakayi wankan ba? This is the first datayi masa magana with full respect mamaki yafara yi anya kau itace? Bai ce komai ba yatashi ahankali dan yanzu sosai yake jin saukin jikin nasa sai dan abunda baa rasa ba, hannu yasa ya dauki ledan dayagani nan kan drawer din komawa tayi ta zauna kan kujera ta zubawa waje daya ido ta ina zata farawa dr hafsa bayani to?mi zatace mata tana son koyo? Idonta tasauke kan basket din abincin dasuka zo dashi yunwa takeji amma bata jin cin komai haka yasata yin lamo ta rufe idonta tanaji bacci kadan kadan yana fizgan ta,sai dayayi spending kusan 20mins kafin yafito shirye cikin jallabiyan sai kamshin perfume din data kawo masa yakeyi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 83