da lakwari da aka aike da shi magarƙama a wancan zaman da kotu ta yi.
Babban abin da ya bawa Nabila mamaki, bai wuce ganin barrister Naja'atu Bunkure a cikin kotun ba, duk da ta ji gabanta ya faɗi, amma ta dake ta adana mamakinta a zuciyarta.
Ta fito ta gabatar da kanta, aka fito da lakwari, Nabila ta nemi Walid ya fito.
Walid ya fito ya tsaya, ta dubi Walid ta ce "Ko zaka iya bayyana wa kotu sunanka?"
"Sunana Muhsin Hassan, wanda ake kira da Walid".
Ta nuna masa lakwari, ta ce "Ka san wannan?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh na san shi"
"Ka san laifin da ake tuhumarsa da shi?"
"Eh na sani, laifin ki san kai ne na matar Al'amin da ɗan cikinta"
"Ka tabattar?"
"Eh na tabattar"
"Za ka iya shaidawa kotu abin da ya faru?"
Walid ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ranar da za a kasheta, ni na aro babur ɗin adaidaita sahu, kamar yadda Al'amin ya buƙata, da ni da shi da abokinmu liti, mu ka je asibiti. Likita ya dubata ya ce ta wuce lokacin haihuwar ta, dan haka za ayi inducing ɗin ta, amma idan bai yi ba tiyata za ayi mata.
Ta ce tana son cin ƙosai, muka yi ta yawo bamu samu ba, na yi alƙawarin zan nemo ƙosai da sassafe na kai mata, daga nan mu ka ajiye su a gida, mu kuma muka wuce.
Da sassafen da na je, na tarar da layin a cike da jami'an tsaro, wai an yi kisan kai"
"Ka ga gawar jauhar da ciki?"
"Eh, a kan idonmu aka fito da ita an rufeta a cikin ledar gawa, ta na zubar da jini".
"Waye ya kira jami'an tsaro ya sanar da su abin da ya faru?"
Walid ya ce "Ban sani ba gaskiya"
Nabila ta yi godiya, Bunkure ta taso ta gabatar da kanta a matsayin lauyar lakwari, sannan ta yi suka ga shaidar Walid, cewa shaida ce mai rauni, tun da bai tabattar da ganin lokacin da lakwari ya kashe jauhar ba.
"Ya mai girma mai shari'a, ina son kotu ta bani dama, zan yi wa Al'amin wasu tambayoyi"
Viper ya fito ya tsaya, ya na tuna abin da ta yi masa a wancan lokacin.
"Malam Al'amin, a haka ba ka yi kama da malamai ba, balle ace wa'azi ka yi wa su lakwari ba su ka ji haushi, suka kashe maka mata ba.
Me zai haɗa mutum kamar ka da mutane irin su lakwari har su shiga gidanka, su kashe maka mata? Ko ka na ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ne kai ma?" Tayi maganar tana tsare shi da idanunta.
Ayshercool
08081012143
93
Har Nabila ta zaburo za ta yi magana, Baba ya ce "Amma kamar ƙoƙarin tabattar da mutuwar jauhar ake yi, wannan tambayar abin da ya shafe mu ne personal issue ne"
Nabila ta yi carf ta cafe, da sukar abin da Bunkure ta aikata.
Da haka dai aka saurari wasu daga cikin shaidun na ranar, aka sake ɗaga shari'ar.
Viper ya din ga jin jikinsa wani iri, sai da ya fito ya tsaya su na gaisawa da Baban su jauhar.
Bayan Nabila ta fito daga cikin kotun, ta samu wuri tana amsa waya, babu tsammanni Nabila ta ji an janyota baya, an riƙe damtsenta.
Ta waiwaya ta ga Naja'atu Bunkure, ta yi wa Nabila wani munafukin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari barrister Nabila, lallai na yadda da kirarin da ƙawarki take yi miki, na a lady of her words, the voice of voiceless. Kin yi alwashin kai ni ƙasa, ki na ta faɗi tashin ganin kin ga bayana. To kafin ki ga nawa bayan ni zan ga naki, sai na tabattar miki da wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi.
Zan kunna miki wutar da sai ta ƙonaki har lahira, abu mai daɗi da ya sauƙaƙa mini komai shi ne, samun labarin ke yar uwar matar Viper ce, ki na kare mijin yar uwakki, da kuma neman hakkin jininta da ya riga ya tafi a banza a wofi, zan illataki da wutar zahiri da ta baɗini ta zuci, sai na tona asirin miyagun ayyukan Viper sun koma kansa, na kassara Rayuwarki yadda zai zame muku baƙin ciki goma da ashirin, kamar yadda ku ka tarwatsa nutsuwarmu da ni da uban gidana Indabo"
Nabila ta saka hannu, ta buge hannun Bunkure daga damtsenta, sannan ta hankaɗata iya ƙarfinta ta nunata da yatsanta ta ce "Jinin 'yar uwata ya fi ƙarfin ya tafi a banza, ƙarya ki ke yi, kuma wutar da ki ke shirin kunnawa, reshe ne zai juye da mujiya, dan kuwa ke zai koma ya ƙona, daga ni har Al'amin ƙarafa ne a cikin wuta da babu abin da wutar da ki ka kunna ta isa ta yi mana. Jinin yar uwata bai tafi a banza ba, duk wanda ya saka hannu wurin zubar da jininta, sai jinin jauhar ya zame masa mummunar gubar da sai ta kai shi lahira".
Nabila ta daki ƙirjinta ta ce "Gani gaki Naja, ki tsammaci abin da zatonki da hangenki bai taɓa tsammani ba" tayi maganar ta na nuna Naja'atu.
Sumayya ce ta hango abin da yake faruwa, Viper ya na can ya na magana da Baba cikin girmamawa, ya na tsugunne Baba ya riƙe hannunsa, ya na ta yi masa nasiha da bashi ƙwarin gwiwa, Alhaji mu'azzam har mamaki abin ya bashi, dama haka Viper ya iya ladabi.
Karaf idanun Viper su ka sauka a kan na Abbu, da bai san ma Abbun ya zo kotun ba, gabansa ya yi mummunar faɗuwa, Baba ne ya kalli in da Viper yake kallo, shi kansa bai lura da mahaifin Vipern ba sai yanzu.
Cikin hanzari ya nufe shi, shi ma ya nufo shi cikin sauri, Viper kuwa kawar da kansa ya yi daga kallon Abbu, zuciyarsa na ci gaba da harbawa da sauri.
Suka gaisa Abbu ya ce "Malam Bashir kwana da yawa, kawai sai samun labari mu ka yi kun tashi, babu ko sallama"
Baba ya ce "Wallahi kuwa, ai na yi laifi ayi mini afuwa, ashe ka zo zaman shari'ar Al'amin, kuma kawai sai ka ga Nabila ita ce lauyarsa"
Abbu ya ce "Abin ya bani mamaki sosai ya ɗaure mini kai, duk wannan abun ashe Jauhar ta na da 'yar uwa, ban taɓa sani ba, ta hanyar yar jaridar nan ƙawarta sumayya muke magana, ta kaini wurinta, wallahi na razana sosai, Allah na zata marigayiyya ce"
Baba yayi murmushi ya ce "Allah kenan, mai jujjuya lamarinsa yadda ya so"
Viper ya bar wurin da zai ci gaba da ganin Abbu, saboda yadda zuciyarsa ke neman tsinkewa, sai azalzalarsa zuciyarsa take yi ya ƙarasa wurin da Abbu yake.
Can ya hango Sumayya ta danƙo hannun Nabila, sai surutai take yi, fuskarta ta koma ja, da alama ranta ne ya ɓaci.
Nufar su yayi da sauri, ya na tambayar su ko lafiya.
Sumayya ta ce "Faɗa su ka yi da Naja'atu Bunkure"
Cikin mamaki ya ce "Faɗa kuma?"
"Eh"
Ya ce "Meya haɗa su?"
"Wallahi ban sani ba, ƙarar da aka yi bayan taku na tsaya saurara, na yi picking wani abu a cikin rahotannin da zan yi yau, kawai da na fito na gansu su na cacar baki"
A nutse ya kalli Nabila da take ta huci ya ce "Meya haɗa ki da ita?" Shiru Nabila ta yi ta kasa magana.
"Ina tambayar ki menene?" Still ta kuma yin shiru, sai sauke ajiyar zuciya take yi.
Ya ce "To wuce mu tafi"
Ya sakota a gaba su ka fito harabar kotun, a wannan karon har da Alhaji mu'zzam kankarofi suke tare da su Abba, Abban ya gabatar wa da Alhaji mu'zzam Abbu mahaifin Viper.
Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan su Viper, da su ka taho fuskar Nabila sam babu annuri.
Rige-rigen tambaya su ka fara yi, ko lafiya Nabila take cika ta na batsewa.
"Ya aka yi ne, meyafaru?" Baba ya tambayeta cikin kulawa.
Kawai ta durƙusa ta fashe da kuka.
Viper ya ce "Wai ke wace irin yarinya ce, wannan ai halin yarinta ne, barrister ce fa ke, a harabar kotu ki zauna ki na kuka saboda wauta da abin kunya?"
Alhaji mu'azzam ma ya ce "Nabila menene, kar ki ɗaga mana hankali mana"
Abbu ma cewa ya yi "Idan yanayin yadda shari'ar ya gudana ne bai yi miki ba, ki yi haƙuri mu je a ci gaba da addu'a da neman ɗaukin Ubangiji"
Abbu na fara magana, Viper ya yi ɗif, ya juya ya bar wurin.
Abin da Viper ya yi ya ƙara wa Nabila takaici, cikin mamaki Baba ya ce "Ya haka kuma?"
Abbu ya girgiza kai ya ce "Rabu da shi kawai, komai yayi mini na cancanci hakan"
Still wani mamakin ya sake cika Alhaji mu'azzam, ya na mamakin wane irin mutum ne Viper haka, baban na sa ma.
A dai-dai lokacin liti da Walid su ka ƙara so gaban Abbu, su na zuwa suma durƙusawa su yi a gaban Abbun, cikin matuƙar girmamawa su na gaishe shi tare da Baba.
Abbu ya dafa kafaɗunsu ya na amsawa.
"Ya ƙoƙari ya fama da Al'amin"
Walid ya yi murmushi ya ce "Babu fama Abbu"
"Ina ta godiya Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, dan Allah a ci gaba da bashi haƙuri, ace ya yafe wa Abbansa"
Liti ya ce "In sha Allah"
Walid ya kalli Nabila da take kuka ya ce wa Sumayya "Me ya sameta?"
"Shagwaɓa mana" Sumayya ta bashi amsa ta na kallon Nabila.
"Mai zamani ne ya yi mata wani abun kenan?"
"A'a faɗa su ka yi da Naja'atu Bunkure, ban san me ta yi mata ba dai"
Liti ya ce "Ai matar nan shegiya ce, wani abun ta ƙudurce a ranta za ta aikata, mussaman yanayin tambayoyin da take yi a kotun nan"
Abbu ya ce "Ki kwantar da hankalinki, kar ki damu kin ji jauhar, in sha Allah za ayi nasara"
Baba ya ce "Nabila dai".
Abbu ya ce "Ni jauhar nake gani, duk ɗaya ne a wurina"
Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Nabila akwai ƙoƙari da jajircewa, sai faɗa da tsiwa, unlike jauhar, so calm ba ta da hayaniya"
Abbu ya ce "Dan Allah dai ko da tsayayye wannan ma mu na riƙo, a taimake mu a bamu, ta maye mana gurbin jauhar da muka rasa".
Dumm gaban Alhaji mu'azzam ya buga, Baba kuwa ya ce wa Abbu "Ai a yanzu dai wannan ba ni da iko da ita, akwai ƙura a kanta".
Nabila ta ce "Baba ni na tafi"
"To kya tafi ki na kuka Nabila, ko in tafi da ke can gida?" Ta girgiza kai alamar a'a ba zata bi shi ba.
Ya ce "Hafsa kullum cikin zancenki take Nabila, yanzu ina zaki tafi?"
"Gida wurin Abbana"
Ya ce "Dama ai Abbanki ne, ban ce nawa ba ne ba"
Alhaji mu'azzam ya ce "Ko mu tafi na ajiyeku a hanya?"
Liti ya ce "A'a ga mota can da security ɗin da suke kula da ita ai, zamu rakata"
Alhaji mu'azzam ya yi murmushi, ƙiri-ƙiri Viper suke taya wa kishi, sun manta da saka hannunsa aka ba wa Nabilan security.
Baba ya ce "To Allah ya kiyaye hanya, ina nan tafe wurin Abban naki, ki gaida mutanen gidanku"
Sumayya ta ja hannunta su ka yi gaba, Abbu ya kalli Baba ya ce "Ni ranar da na fara zuwa office ɗin ta, na zata Jauhar ce, ta yi mini wani bayani da ban gama fahimta ba, yaya aka yi Jauhar take da yar uwa bamu taɓa sani ba?"
A lokacin Abba ya warware masa komai, har yadda aka yi auren Jauhar da Al'amin, da yadda ya mayar wa da Alhaji mu'zzam kuɗin aurensa, da tsamar da suke yi yanzu da Major a kan Nabila, ya na son ya karɓi 'yar sa, ko yaya ya zauna da ita kafin ta yi aure, amma ya san major ba zai taɓa bari ba, ita kanta ba zata yadda ba dan ya ga tsanar iyalinsa muraran a idon Nabila.
Abbu ya ce "Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya yi gaskiya da ya ce bai bar wata fitina a bayansa mafi cutar da maza ba, dai daga mataye.
Sai yanzu na ƙara yadda da mata su ne ƙashin samar da duk irin al'ummar da suke so, na gari ko kuma akasin haka.
Wallahi Alhaji Bashir, ina cikin matsananciyar nadamar wofantar da rayuwar Al'amin, a ganina haka ne mafita, matar nan ta din ga zigani ina hawa kai, 'ya'yana na cikina su ka rayu kamar bayi, duk rufin asiri da nake da shi amma rayuwar Al'amin ta ƙare a haka. Ina baƙin ciki haɗuwata da shi ta ƙarshe da ya dawo daga prison, ya na tambayata ya aka yi da matarsa, ban saurare shi ba balle na yi masa uzurin ba zai iya kashe jauhar ba. Na ji kunya da kai a matsayin ka na mahaifinta ba ka aminta zai kasheta ba. Na tafka kura-kurai duk a dalilin rashin dace da mace ta gari".
Sai su ka ɓuge da hira, da jajantawa juna, sosai su ka yi wa Alhaji mu'azzam a kan gudunmuwar da ya ba wa rayuwar Nabila da Viper.
Har gidan Abba su ka kai Nabila, sannan su ka watse, sumayya ma ta tafi wurin aikinta.
Azahar ce lokacin, kuma dama ba salla za ta yi ba, ta na period, ta tafi falon Abba.
Ya na tare da Mama, Nabila ta yi sallama, Abba ya amsa, mama ta haɗe rai.
Ta dire jakarta, ta ware veil ɗin kanta, ta haye kan doguwar kujera ta kwanta.
Mama ta yinƙura za ta yi magana, amma Major ya kalleta, hakan ya tilasta mata haɗiye maganar da ta yi niyyar yi.
Nabila ta ci gaba da kuka, amma Abba bai kulata ba, ta ce "Abba wai ba zaka kula ni ba?" Ya yi mata shiru.
Tashi mama tayi ta bar masa ɗakin, ganin magana take yi da shi mai muhimmanci Nabila ta zo ta kwanta tana kukan rashin mutunci.
Doguwar ajiyar zuciya da ta sauke, ya sanya ya kalleta, bacci ta yi, hakan ya tabattar masa akwai gajiya a tare da Nabilan.
Ya gyara mata hannunta, ya na kallon fuskarta, wadda take sak ta chubaɗo.
Kawai ya din ga hango ina ma duka ya ɗauke su ya riƙe, da Nabila da Jauhar, ɗaya lauya ɗaya likita, da sai ya fi alfahari da hakan, amma haryanzu bai ga alfanun tsaya wa Viper da Nabila ta yi ba, duk da kasancewarsa ɗan daba, kuma da ya ɗan bibiyi abin da ya faru, babu wani history mai kyau a kan Viper, ban da dillancin ƙwaya da sara suka, sai kuma tserewa daga prsion bayan an kama shi da laifin kisan kai, kuma wai daga baya an hana kama shi.
****
Mahaifiyar Abdul ta kasa nutsuwa gabaki ɗaya, ta na ta ƙoƙarin yadda za a bayar da belin Abdul a sake shi, amma abu ya ci tura, duk da irin tayin kuɗaɗen da ta sanya aka din ga yi wa masu ruwa da tsaki a kan shari'ar ɗan nata, amma kuɗi su ka ƙi tasiri, alamu su ka nuna da gaske so ake a hukunta Abdul.
Ba ita ba, hatta abokan Indabo, sun yi iya yin su amma aka nuna musu ba za yiwu ba.
Sau ɗaya ta je ta ga Abdul, hankalinta ya yi mummunan tashi, gashi dai a wuri na musamman yake, ba wai haɗa shi aka yi da sauran fursunoni ba, amma gaba ɗaya ya fita daga hayyacinsa.
Ya ƙara ramewa, gashi mutum ne mai kufan gashi, saboda haka tuni gashi ya cika masa fuska. Duk da ana kula da shan maganinsa ya na samun abinci, amma ba irin wanda yake so ba.
***
Da la'asar Nabila ta tashi, ta yi wanka, ta ɗauki abin da za ta ɗauka za ta fita.
Baba Magajiya ta tare ta ta ce "Arfa, duk yadda major yake kaffa-kaffa da ku, mussaman ke yake saka miki ido da kula da ke, amma ya zuba miki ido, ki na shige da ficenki, mutanen gidan nan har da maƙwabta su na ta surutu a kan hakan, yakamata fa ki kula ki yi wa kanki faɗa".
"Baba magajiya, Abba ya san ko nan da bangon duniya zan fita, Abba ya na da yaƙinin ba zan lalace ba, ba zan yi abin da zan cutar da kaina, ko na janyo masa abin kunya ba. Kar ki manta har ƙasar ƙetare na fita na yi karatu ban lalace ba, in sha Allah ba zan baku kunya ba"
"Abin kunya na nawa kuma, banda wanda ki ke aikatawa yanzu? Kwana a in da ki ka ga dama, yawo da ƙaratan 'yan daba me ya rage kuma?"
Nabila ta kalli mama cikin nutsuwa ta ce "Hajiya mama yaushe ki ka fara damuwa da ba na kwana a gida ne? Tun yaushe ki ke yi mini fatan abin kunya? Ni ban aikata abin kunya ba, ba kuma na fatan na aikata, Nasir shi ne mai abin kunya a ƙugunsa, da ya canza mota ya gama gini, yake wadaƙa da kuɗi wanda ya wuce samunsa ba ki tuhume shi ba, Abba ya yi yinƙurin tuhumarsa ki ka hana ki ka kare shi.
Ki daina shiga harkata tun kafin na nuna wa duniya waye ɗan naki"
Baba magajiya na takaicin yadda mama ta daɗe da zubar da mutuncinta da tun Nabila na jin nauyinta ta na girmamata, har an kai ƙadamin da ta daina ɗaga mata ƙafa.
Bayan ta fita wayar Viper ta kira, liti ya ɗaga.
Ta ce "Ina mai wayar?"
"Bacci yake" ya amsa mata kai tsaye.
Ta ce "Bacci da yammacin nan, shikenan"
Rabon Nabila da gidan har ta manta, liti ta tarar da ɗan mama a tsakar gidan su na hira, amma rabin hirar ɗan mama zagi kawai yake sha a wurin liti.
Amsa sallamar su ka yi, Nabila ta ce "Ɗan mama ka yi free kenan?"
"Eh belina aka bayar ai, dama za mu tattauna da ke, nima zan iya bayar da shaida"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ina Oga?"
Ya na cikin ɗaki, ya na ta aikin danna waya.
Nabila ta yi murmushi ta shiga ta tarar da shi, ya tashi daga baccin, ya na zaune ya na ta danna tab. Gefensa duk abin sauran sigari da ya sha.
Ta zuba masa ido, ya cigaba da abin da yake yi, sai da ya kammala sannan ya kalle ta ya ce "Daga ina ki ke?"
Ta kwaɓe baki ta ce "Gida"
"Wai meyasa ba kya ji ne? Ke duk wani abu da za ki aikata, ace ba ki kyauta ba, kin san shi kuma za ki aikata. Kin sani sarai you are not safe, an kai ki in da zaki zauna, an baki wanda za su din ga fita da ke, saboda tsaronki, amma sai yawonki ki ke yi yadda ki ka ga dama, tarar aradu da ka fa ki ke yi?" Tayi shiru kamar gaske ta na saurarsa.
"Meya haɗa ki da Naja'atu Bunkure, har ku ka yi faɗa ɗazu a court, kar ki je da gayya take yi miki abin da za ki yi reacting, ta samu kafar cutar da ke"
Nabila ta ja numfashi ta ce "Ni matar nan za ta kalli tsabar idona, ta ce mini wai jinin 'yar uwata ya tafi a banza? Ban san ya aka yi ta samu labarin cewa jauhar sisterna ce ba. Da fari na fara karaya, jin yadda take zaƙulo tambayoyi a kotu, duk da na yi tsammanin hakan, amma abin da ta gaya mini, tamkar ta yi mini allura ne, jinin jauhar sai ya zame musu bala'i ya zame musu guba mai mummunan hatsari"
Ya ajiye tab ɗin ya ce "Haka ta ce Jinin matata ya zuba a banza?" Ta jinjina masa kai.
Ya numfasa ya ce "Haryanzu su na wasa da ni, daga ita har ubangidanta, daga nesa suke hangena a cikin wutar, zatonsu hannayensu za su iya jure zafin da na ɗauka su ɗaukko ni, na san abin yi"
Nabila ta gyaɗa kai ta ce "Ko ni sai na ba wa matar nan mamaki, shashasha kawai"
Yayi shiru yana juya maganar, da jin zafin abin da Nabila ta ce Bunkure ta faɗa, kamar ita aka gaya wa.
Kamar wadda aka mintsina ta ce "Yauwwa kai kuma" ya juyo ya kalleta tamkar uwar da take shirin yi wa ɗanta faɗa.
"Viper ka bani haushi, zan iya cewa abin da ka yi ya kusa fin abin da Bunkure ta yi mini" tsuke fuska ya yi ya na kallonta.
"Ai ko za ka cinye ni ɗanya sai na faɗi abin da ya kawo ni. Abbu da kansa ya je Office ya same ni, ba aike ba a kanka, ni na ce ma ya zo kotu ya din ga ganin yadda shari'ar take gudana, ya damu ya damu saboda kai, amma a gaban mutane, a gaban kowa da kowa ka yi tafiyarka ka bar shi, me ka aikata kenan? Nuna wa duniya cewar mahaifinka bai isa da kai ba ko kuwa? Kai ka ce har da bijire masan da ka yi Allah yake jarabtarka, so ka ke wani bala'in ya same mu ne a sanadin wulaƙanta iyaye?.
A cikin Alƙur'ani mai tsarki sau nawa Allah ya maimaita yi wa iyaye biyayya? Ka daina kallon ya yi maka laifi, kai sai Allah ya hukuntaka da ƙaurace masa da ka ke yi. Nan fa ni ka zaunar da ni ka na yi mini nasiha, kai meyasa ba za ka yi aiki da nasihar ba"
"Ke shut up! Kullukum ra'in, wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi, sau nawa Abbu yayi wannan tunanin a game da ni? Ya wofantar da mu ni da ɗan uwana, an kashe shi ya ce ni ne sila, a duniya ina cikin 'ya'ya masu tsananin ƙawazucin iyayensu.
Kin san sau nawa daga gidana kan sallar asuba nake tafiya unguwarmu, dan ayi sallar asuba a idar ya wuce na ganshi na ji ƙamshin turaren sa, saboda ƙamshin ya na tuna mini lokutan da su ka gabata mu ka rayu cikin farin ciki da son juna.
Babu nasiha tsakanina da shi, babu rarrashi sai zagi hantara da kuma kora, alhalin ina kallon ya na ta haƙilon alkinta rayuwar yaran matarsa? Ni kuma ina yawo babu sana'ar kirki da zan kula ma da matar da ya aura mini, ki na tunanin ko na fi kowane ɗa lalacewa a duniya, idan mahaifiyata na da rai watsar da ni za ta yi?. Kin san sau adadin zuwan da nake yi in da yake ya na korata, kamar wani kare, kin san cin mutuncin da ya yi mini a lokacin da na baro prsion na je in da yake, ya kore ni ya ci mutuncina wai ba ya ƙaunar ganina na kashe jauhar, me ya rage nake nema a wurin Abbu ne tun da ya furta ba ya ƙaunar ganina? Har cikin zuciyata ina son mahaifina amma ba zan ɓoye miki ba, gaba ɗaya ya sire mini, uwata da ta mutu ma Allah ya raya ni, ɗan uwana mai tausayina da aka kashe shi, shi ma Allah ya raya ni. Dan haka zan iya rayuwata ko babu Abbu. Da ya tallafi rayuwata da wataƙila duk wannan azabar ban sha ta ba a rayuwa. Ki gaya masa ya rayu da waɗanda yake so, halarta wurin shari'ata ma na yafe ya zauna ya huta, Allah zai wanke ni"
Nabila ta yi masa ƙuri da ido, har ya yi gama, idanunsa su ka yi jawur kamar an zuba masa gauta, dama ga sigari ya sha.
Ta ja ajiyar zuciya ta ce "Ni da kai ta wata fuskar tamkar jirgi ɗaya ne ya kwaso mu, amma sai dai akwai in da ƙaddarorinmu su ka sha bamban.
Vi" ta kira shi a sanyaye.
Ya kawar da kansa gefe, ya na ta sauke ajiyar zuciya.
"Ka kalle ni mana magana za mu yi"ya ƙi waiwayo wa.
Ta zagaya saitin in da ya kawar da kansa, hawaye ya cika masa ido.
"Vi dan Allah kar ka yi kuka, ka yi haƙuri, amma kasancewar ka abu mafi soyuwa a wurin 'yar uwata ina fatan har a lahira ka kasance da rahamar Allah, ban yi maka wannan maganar dan na ɓata maka rai ba, lokuta da dama sai Allah ya jarrabi bawansa kafin ya yi masa wani tagomashi na alkhairi. Dan Allah ka yi haƙuri, amma ba zan haƙura da rarrashin ka ba, a kan ka daidaita da Abbu. Iyayenmu duk da sun dace da mataye na gari, da ba su aikata wani abun ba"
Ya haɗiye wani abu mai ɗaci ya ce "Tashi mu je na mayar da ke barrack, na san kan ki koma duhu yayi, kuma idan na sake ganin kin zo nan sai na ɓallaki na gaya miki"
"Ba zan sake zuwa ba, but smile mana dan Allah, kar mu tafi ka na huci, na ga ka ɗauki zafi da yawa"
Viper ya sake tsuke fuska ya ce "Tashi mu tafi" kamar yarinyar goye, ta maƙale kafaɗa ta marairaice ta ce "Dan ka yi murmushi Vi, ba na son wannan mood ɗin naka" tashi ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 99 Chapter of 121