ya saka miki da alkhairi"
Nabila suka gaisa da maman ramma, ta ce "Rahama ga masoyiyyar ku, Sumayya T ladan"
Ramma ta ce "Anty sumayya ya aiki?"
Sumayya ta ce "Alhamdilillah, ya fargaba kuma, Allah ya kiyaye gaba"
Maman ramma suka gaisa da barrister Habib ma, tana tayi masa godiya, ta ɗaukko wa Nabila takarda, an yi stapling ɗin ta, ta ce "Gashi aka kawo, tasatasan da aka yi wa ramma ne, da aka ɗebi jininta, bayan an kawota, aka ce kar a buɗe ke za a bawa, tun da ke ce lauyanta"
Nabila ta karɓa ta na faɗin "Ai yana daf da zuwa hannu, mun gama sbirya komai ta buɗe takardar tana dubawa, komai na ramma lafiya ƙalau, sai dai ga tes ɗin ciki ya fito rangaɗau".
"Ina fatan babu matsala dai ko? Babu ƙanjamau ko wani abu?"
Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Eh komai lafiya, amma rahama ɗan zo mana"
Ramma ta tashi suka koma gefe, ta kalli ramma ta ce "Rahama kin san kina da juna biyu?"
Ramma ta jinjina kai alamar eh.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
"Dan Allah anty kar ki gaya wa mama"
"Rahama dole a mata, dole ta sani fa"
Cikin kuka ramma ta ce "Dan Allah ki rufa mini asiri"
Ta kamo hannun ramma suka dawo falon, ta kalli mahaifiyar ramma ta ce "Maman ramma, da gaske kin tabattar ya aureta?"
Jiki a sanyaye ta ce "Haka wan babanta ya gaya mini, meyafaru?"
"Akwai matsala, sakamakon nan ya nuna akwai ciki fa"
Sosai Nasir yake gudu, cikin matsanancin tashin hankali, ganin hoton da Viper ya bashi, hotonsa shi da jauhar.
Ko rufe motar bai yi ba, ya fita ya faɗa cikin gida.
Sai da Abba baya nan, ya din ga kallon hoton, cikin fargaba, kenan wannan ce ake dambarwa a kan kisanta? Saboda yanayin yadda suka yi hoton, ya tabattar da mata da miji ne. Lallai akwai gagarumar matsala.
"Wai wannan wane irin mutum ne? Kenan ya san komai, shiyasa yake ziga Nabila? Akwai Matsala......
Ayshercool
08081012143
82
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
Nasir ya cigaba da jujjuya hoton, ya fita ya tafi sashen mama, ya tarar da ita tana cin abinci, amma ya rasa me zai ce mata.
"Lafiyarka kuwa?"
"Eh lafiya ƙalau, shigowa nayi kawai mu gaisa"
"Kuma sai na ganka a haka kamar mara gaskiya, gaisawar da muka yi da safe fa?. Amm ya ake ciki ne? Ka haɗu da ita ɗin?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh mama, mun haɗu ƙarewar rashin kunya, tare suka je da gayen"
"Hmm ai na sha gaya wa mahaifinku, gurbin ido ba ido bane ba, ai yanzu gashi nan ya fara gani. Ni dai ka yi iya yinka kar yarinyar nan tayi galaba a kan ka"
Ya jinjina mata kai kawai ya fita.
Wiwi ramma take kuka, mamanta ta ce "Ramma, kin munafunce ni, na ce miki babu abin da yaron nan yayi miki, ki ka ce mini eh, amma kawai sai na tsince ki da ciki? Baki kyauta mini ba"
Ramma cikin kuka ta ce "Dan Allah mama ki yi haƙuri, bana son ki shiga damuwa ne"
Barrister Habib ya ce "Hajiya, ina ga mu bi komai a hankali, Nabila menene watannin cikin, kuma kwana nawa da ɗaura musu aure, tun da an ce ai lokacin da ya saceta da ciki, ya ci ace zuwa yanzu ta haihu.
Ramma tayi wiƙi-wiƙi da ido tana kuka.
"Kiyi magana dan ubanki"
Nabila ta ce "Yi mata a hankali, rahama meyafaru da wancan cikin?"
Ramma ta kasa magana, ta cigaba da kallon mahaifiyarta da ta hasala.
Nabila ta yi ta rarrashinta, amma taƙi magana fafur.
Sumayya ta ce "Nabila, ku bi a hankali, zata yi magana, amma yanzu yakamata a rabu da ita, zuwa lokacin da zata samu nutsuwa tayi magana"
Maman ramma ta ce "Har zuwa yaushe kenan, dan girman Allah ku yi mini rai a cire cikin nan"
Barrister Habib ya ce "Haba Hajiya, baki bari an cire na farko ba sai wannan, dan Allah kar ki takura mata, ki ce sai ta yi miki bayani ko makamancin haka, ki yi haƙuri"
Maman ramma ta dafe fuskarta tana hawaye, ta ce wannan wace irin wulaƙantacciyar rayuwa ce, an cutar da ni an wulaƙanta iyalina"
Nabila ta ce "Mama jarrabawa ce, kowa da yadda Allah ya tsara masa, muddin muka taɓa cikin nan, zamu iya shiga matsala, tun da da izinin wakilinta ya aureta, babbar damuwar mu a nan shi ne, ayi masa hukuncin abin da ya aikata mata, amma ki yi haƙuri dan Allah"
Nabila ta cigaba da rarrashin ta, tare da taimakon su sumayya.
Sai da suka gama da mahaifiyar ramma sannan suka fito, suna ta jajanta lamarin, Sumayya ta ce zata tafi gida, Barrister Habib kuma zai mayar da Nabila, Nabila ta ce "Sumy, ki turo mini lambar mahaifin Viper please"
Sumayya ta ce "Ok, amma ni haryanzu baki gaya mini tayaya ki samu alaƙa da matarsa ba"
Nabila ta girgiza kai ta ce "Ai ni yanzu na daina dagewa lallai idan na faɗi abu sai an yadda da ni, lokaci zai warware komai"
"Shikenan, ba zan matsa miki ba, zamu gani, amma Nabila nayi mamakin ganin Viper, lallai ya ci sunansa Viper, wallahi na zata zan ga wani karabutin mutum kawai, kalleshi masha Allah, lallai wannan su suke yin dabar gaske"
Nabila ta ce "Malama ya daina daba fa, ki daina zancen dabar nan Please, ya tuba"
Sumayya tayi murmushi ta ce "Allah ya baku haƙuri, sai mun yi magana"
"Ok, bye" suka yi sallama.
****
Sannu a hankali ta cigbaa da zaro kwalaban maganin tari, da satchet ɗin magungunan mura a ƙarƙashin gadonsa, kwalabe sun kusa ashirin, jikinta sai tsuma yake yi.
Da kyar ta iya amsa sallamar da Shahida take yi a tsakar gida, ta fito jiki a sanyaye tamkar munafuka.
"Mama ya dai? Na ganki kamar a tsorace meyake faruwa ne?"
Alama ta yi wa shahida da hannu da ta shigo, ta ƙarasa cikin ɗakin Abba, ta nuna mata tulin kwalaben maganin tari masau hatsarin gaske.
Shahida ta dafe kai ta ce "Mama kin gani ko? Na daɗe ina gaya miki amma kin ƙi yarda"
Rahila ta ce "Duk laifin babanku ne, tun da ya kore shi daga kasuwa shi da Nazifi, ya rasa abin yi ya shiga wani hali, ni da nake ta fatan nayi masa aure"
"Mama Abbu fa ba shi da laifi, yayi iya ƙoƙarin sa a kansa, ya zai zauna da su, suna cutarsa"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku ni Rahila"
"Ina Amira ne?"
Tamkar ta fashe da kuka ta ce "Amira yau kwananta biyu bata gidan nan, ban san in da take ba, na yi wa babanku ƙaryar tana gidan Yaya, Shahida na shiga uku"
Jiki a sanyaye ta ce "Mama baki shiga uku ba, ni fa daga kotu nake, na kai Anwar ƙara ya sauwwaƙe mini, ba zan iya ba na gaji" A razane ta ce "Ya sauwwaƙe miki? Shahida baki da hankali, a wannan ƙadamin da ake ciki zaki kaso aurenki, ya ki ke so nayi, sai duniya tayi mini dariya?"
"Mama, kin kasa gane in da na dosa, wai so ki ke sai na halaka ne, saboda kawai yana da kuɗi, nayi haƙuri fa iya haƙuri, ke fa uwata ce, haƙurina ya ƙare, Allah da zan iya tunkarar Abba, da sai na tunkare shi na sanar masa".
"Shahida uban naki zaki tunkara da wannan maganar? Saboda baki da kumya?"
Cikin tsiwa ta ce "Idan ba irin Amira ki ke so na zama ba ki ƙyale ni dan Allah"
Rahila ta kwantar da murya ta ce "Ki rufa mini asiri Shahida, shi wannan ya fara shaye-shaye, waccan bin maza, shi Nazifi ya gudu kudu neman kuɗi, ban ma san a duniyar da yake ba, ke kaɗai ce a ɗakin aure nake jin daɗi, kar ki gurguɗe auren nan, ki ƙara tona mini asiri, ba ya ce miki yana neman magani ba? Baki san me Allah ya ɓoye a lamarin nan ba, ga tarin dukiya yana da ita, sai ki ga ke kin haihu da shi, ki haifi namiji, wannan dukiyar ta zama tamu"
Ta kalli Rahila cikin takaici ta ce "Na haihu ta yaya, mama shekara uku fa, wane irin magani ya kasa nema a kan sauran matan da ya rabu da su? Ashe aurensa tara ni ce ta goma ya ɓoye mana, ga shaye-shaye ga cin mutunci har da duka wasu lokutan, wallahi ba za a kashe ni da raina ba, gara na auri talakan tulus in samu nutsuwa da kwanciyar hankali" Rahila ta ɗora hannu a ka, ta din ga kurma ihu, tana kukaz Shahida ko a jikinta, ta tashi ta shige ɗaki ta bar ta.
***
Abin duniya duk ya damu liti, da yayi juyi ya ga babu ɗan mama sai yayi ta tsaki, da daddare ma kasa bacci yayi, sai tsaki yake yi.
Walid ya ce "Sarkin gida"
"Mai laya"
Walid ya ce "Wai ya ne?"
"Wallahi tunanin yaron nan nake yi, Allah ya sa ba suna can suna jibgarsa ba, ka san ba imani ne da su ba, kuma ga sauron wurin nan"
Walid ya yi dariya ya ce "Allah liti, kai ne kake tunanin halin da ɗan mama yake ciki? Dama ka damu da shi har haka?"
Liti yayi tsaki ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ya shiga raina haka ba, ka san ya iya ladabin makirci, wallahi da ya dawo wurinmu, rashin Nura ya sanya nake yin sa"
Viper ya yi gyaran murya ya ce "Ka yi haƙuri duk laifina ne, amma in sha Allah ba zai wulaƙanta ba zai fito"
"Idan ma cewa kayi ba zai fito ba, ya tafi kenan dai-dai ne Ogana"
Viper ya ce "Zai ma fito, ni kaina nayi mamakin yadda ya shiga raina, Allah sarki ɗan uwana Nura, Allah ya sanyaya makwancinsu da shi da mahaifiyata, da Sadik, da uban gidana dodo, da kuma matata a bar ƙaunata, da dukkanin wanda muka rasa" suka amsa masa da Amin.
Liti dai bacci gagararsa yayi, sai tsaki ya din ga yi yana juyi.
Gidan da Nabila take, aka gabatar mata da wata macen soja, a matsayin mamallakiyar gidan, ba ta gari ne ya sanya Nabila take zaune a gidan tare da masu aikinta.
Nabila ta zata zata ga matar masifaffiya, kasancewar an ce soja ce, amma taga ba haka ba, tana da matuƙar kirki da sauƙin kai.
Nabila ta din ga jujjuya lambar mahaifin Viper tana son ta kira, amma tana tsoron tijarar Viper, kasancewar ya gargaɗeta a kan haka, tana cikin tunanin, sai ga kiran Viper sai da ta kusa katsewa ta ɗaga ta ce "SPY"
"Idan ki ka sake suka ji abin da ki ke faɗa, zasu iya kashe ki, ban da ogana da ya zo wurnki da su Walid, babu wanda ya san kin san ni waye"
"Yanzu har su Oga Walid basu sani ba"
Ya ce "Mmmm"
"Taɓ, sannu"
"Yauwwa, ya rahama da mamanta? Ina son zuwa da gaske kamar yadda ki ka ce, na ga halin da suke ciki"
Nabila ta ce "Akwai matsala, ciki ne fa da rahama"
"What ciki ta yaya?"
"Ya za ayi in sani, ciki dai, maman hankalinta ya tashi sosai da sosai, ta ce sai an zubar, wallahi na rasa yadda zan yi, gashi ta ƙi magana rahaman, muna son mu ji, kafin ya aureta cikin ya samu ko bayan ya aureta, amma na fi kyautata zaton bayan auren ta samu cikin, duk da bamu san meyafaru da wancan cikin ba da ta samu bayan ya mata fyaɗe"
Viper ya haɗiye takaici, ya tsani ya ga an ci zarafin mace, mussaman mahaifiyar ramma da aka watsa mata yara gaba ɗaya babu wani wanda ta amfana an watsa rayuwar su, kuma abin mamakin uba da ɗa ne suka lalata mata rayuwar yara"
"Bani adress ɗin in da suke zan je" yayi maganar a kausashe cikin damuwa.
"Ka bari muje tare, ina ga idan rahaman ta ganmu tare, ta yi magana, kayi haƙuri na san ranka a ɓace yake, amma babu yadda muka iya da ƙaddara" yayi shiru yana huci.
A raunane ta ce "Viper"
"Mmmm"
"Idan na mutu baka sadani da mahaifin jauhar ba, wanda nake kyautata zaton ina da alaƙa da ita ba, ba zan yafe maka ba"
Dummm haka ya ji maganar Nabila ta dira a tsakiyar zuciyarsa.
Viper "Kin san me ki ke faɗa kuwa? Ta ina ki ke da alaƙa da jauhar?"
Tuni ta fara kuka ta ce "Abubuwa da yawa, na fara sarewa, tun kan na ganka nake mafarkinka, bayan ban sanka ba, ban taɓa ganinka ba, ina da ciwon Athma da take gada nayi daga mahaifiyata, ita ce take da ciwon, familyn su na Jalingo da yawansu, Asma ciwonsu ne, ita ma ka ce ciwonta ne. Akwai abubuwa da dama, ba zan ɓoye maka ba, Wallahi idan Allah ya karɓi rayuwata baka sada ni na mahaifina ba, ba zan yafe maka ba" ta ƙarasa maganar tare da kashe wayarta.
***
Abba ya kalli Nasir ya ce "Nasiru, ya aka yi ne, an ce tun ɗazu ka ke nemana, na je wani wuri ne, ya aka yi?"
"Na haɗu da Arfa"
Abba ya ɗan yi sak, sannan ya ce "Tana lafiya" ya jinjina masa kai alamar eh.
"Haryanzu ba ta yi regreting abin da tayi ba kenan, shirun da nayi mata da zuru duk bata saduda ba kenan?"
"Babu alama, tare da ɗan daban suka je CID jiya"
"What? Aka ce mini tana barrack wurin yarinyar nan Halima goza, ina sane da duk halin da take ciki ai"
Nasir ya ce "Tare dai na gansu, tare da wasu 'yan daban ma, da sumayya"
Abba ya yi shiru cikin takaici, wai 'yan daba.
"Nabila ba ta da hankali, kuma bana tunanin zata yi shi, zan je na taho da ita, duk wadda za ayi sai dai ayi, basarwa kawai nake yi, amma hankalina yana kanta"
"Abba" ya kalli Nasir.
"A harabar wurin, ga abin da shi wanda take karewar ya bani"ya miƙawa Abba envelope.
Cikin matsananciyar faɗuwar gaba, ya kalli Nasir ya ce "Hoton da ta kawo mini wancan karon dama ba Photoshop bane?, Har na fara tunanin waye ya gaya mata wani abu"
"Abba ka san babu wanda ya isa yayi fatali da umarninka a cikin gidan nan"
Muryar Abba har rawa take ya ce "Shi wannan ɗin waye a jikin hoton?"
"Shi ne gayen, matarsa ce, ita ce ake shari'ar a kanta ai, ake zargin ya kasheta"
A zabure Abba ya tashi tsaye jikinsa yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma Nabila saboda mahaukaciya ce, ta tsaya masa take fafutukar a wanke shi, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nasir kira mini Nabila a waya yanzun nan".
Nasir ya ciro wayarsa daga aljihunsa, ya kira lambar Nabila, amma line busy.
Ya ce "Abba line busy" Abba jikinsa na ta ɓari, ya ciro ta sa wayar, ya jefawa Nasir, ya ce "Kira ta maza" sai dai tun tana cewa line busy, aka ce wayar a kashe take.
"Abba ta kashe wayar"
"Nasiru, tashi ka ɗaukko mota mu tafi barrack"
"Abba a daren nan, wajen gari ne wurin"
"Ka tashi na ce!" Yayi maganar cikin tsawa.
"Abba dan girman Allah kayi haƙuri, ka san ba zasu bari mu shiga yanzu ba, dan Allah ka yi haƙuri sai Allah ya kaimu gobe da wuri sai mu tafi.
Anty da ta fara bacci, a bedroom ɗin Abba ta fito ta ce "Major lafiya kake ɗaga murya a daren nan?"
Nasir ya ce "Bakomai"
Har Abba zai bar falon, ya dawo ya nuna wa Nasir hoton ya ce "Waye wannan ɗin ne wai?"
Nasir ya ce "Abba, na ce maka shi ne ɗan daban da nake nema, aka ce na kama, yarinyar jiki ya kashe.... Abba ya ɗaga masa hannu ya dakatar da shi, ya shige ɗaya ɗakin nasa ya kulle ƙofa.
"Nasir meyake faruwa ne?" Anty ta sake tambayar Nasir cikin damuwa.
"Bakomai"ya sake bata amsa a taƙaice ya fice.
Abba ya ɗaukko wani hoto tun Black and white, da hoton wata matashiyar budurwa a jikin bukka ta buɗe haƙora tana dariya, aka yi mata hoton.
Ya haɗa da hoton da Nasir ya bashi, gabansa ya tsananta faɗuwa ya ce "Anya ban tafka kuskure ba kuwa? Hukuncin da na yanke bai yi muni ba? Kana naka Allah ya na nasa. Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na yanke hukunci cikin fushi, bayan shekaru Allah ya jujjuya ƙaddara yadda yake so, ki yafe mini mairamu" yayi maganar cikin matsanancin rauni.
Kwana Abba yayi a zaune, yadda ya ga rana haka ya ga dare, cikin tashin hankali da rashin sanin abin yi, ya din ga jinjina girma da ƙudurar Ubangiji.
***
Sojar nan sai mita take yi wa Nabila, ta ƙi sakin jiki ta karya.
Ƙarfe bakwai da rabi, Viper ya je gidan, suka gaisa da Madam, ya ce "Nabila ta shirya, za su fita"
Madam Goza ta ce "Ka karɓo permisson ne?"
"Eh sun sani, wurin aiki zata je, muna ta shirin shiga court"
Ta jinjina kai ta ce "Best of luck"
Ya amsa da thank you.
A wata haɗaɗiyar mota helux mai fentin sojoji, aka ɗauke su.
Da ƙyar Nabila ta iya ce masa "Ina kwana"
Shiru yayi bai amsa ba, ita ma ta ja bakinta ta tsuke.
Gaba ɗaya fuskarta mamaye da damuwa, kamar ma ba ta samu isasshen bacci ba.
"Meyasa ki ce ba zaki yafe ba, idan ban haɗaki da iyayen jauhar ba, Allah ya isa fa ki ka yi mini kenan"
Cikin rauni ta ce "Ya ka ke so na yi, ka ƙi fahimta ta, Allah ke da yau da gobe, balle ka ce akwai lokacin da ka zaɓa, ka nuna mini iyayenta".
Ya numfsa ya ce "Kalmar tayi mini nauyi sosai, kasa bacci nayi" ta yi masa shiru, tana kallon window tana share hawayenta.
Ya kamo hannunta ɗaya, ta kalleshi da sauri, ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta.
"Ki daina kuka, jauhar ɗina nake gani, kar nayi ɓarna dan Allah"
"Cika ni, ni ba ita ba ce, ni maganin kukana Allah"
Ko a jikinsa ya ce "Kar ki ce zaki yi kishi da ita, wahala zaki sha"
Shiru ta sake yi masa, tana duba wayarta.
Nasir ya turo mata message "Ki ɗaga wayata, zamu zo ni da Abba" kasje wayarta tayi, saboda a jikinta ta ji Nasir ƙarya yake yi.
****
A rikice maman ramma ta tashi, ganin Nabila tare da Viper, ta nufe shi da sauri ta fashe da kuka.
Riƙeta yayi, jikinsa a sanyaye yana tuno Nura guduma, ya ɗagota yana share mata hawaye ya ce "Mama, ki daina kuka dan Allah, na san ni mai laufi ne, rabona da ke na daɗe, amma ƙaddara ce ta janyo duk hakan".
Cikin kuka ta ce "Murnar ganinka nake yi Aminu, ashe zan sake ganinka? Ni da Hajiya mun zo wurinka sau uku, tun daga ƙauye amma ba a bari mu ganka, Allah bai ƙaddara zaku sake ganawa da ita ba"
Aminu ya ce "Allah sarki, ki yi haƙuri ke gashi Allah ya ƙaddara ganawarmu ai" yayi maganar yana zaunar da ita a kan kujera.
Nabila ta gaisheta, ta amsa tana kallon Nabila tana kallon Viper, gashi an hanata magana.
"Jauhar a ina ki ka gano shi? Ya aka yi ki ka san muna da alaƙa da shi?"
Viper ya ce "Nabila ce wannan, ita ce lauyar da zata tsaya mini nima, kuma take ta ƙoƙari a kan shari'ar rahama. Komai da ake ciki tana gaya mini, ina son na zo na ganki na gaishe ki, amma kin san jami'an tsaro nemana suke yi, kuma ina tsoron ki yi mini kallon ɗan ta'adda da ya kashe matarsa"
Cikin ɗaurewar kai ta ce "Wai ni fa na rikice, tayaya Jauhar ta koma Nabila kuma?"
Viper ya ce "Zancen dogo ne, yanzu mu fara gamawa da batun rahama" yana maganar ramma ta fito cikin hijjabi.
Mammaki ne ya kama shi, har ya tafi prison yarinya ce ƙarama sosai, amma yanzu ta zama wata uwar mata, tayi ƙiba, tayi haske sosai.
Cikin matsanancin tsoro, ta gaida Viper, ita gaba ɗaya taoro yake bata tun lokacin da ta taɓa ganinsa a asibiti da kuma lokacin da ya zo gidansu"
Viper ya yi mata alama da ta zo.
Ta ƙarasa gefe kusa da Nabila ta zauna.
"Maganar me ake so ki yi ki ka ƙi yi? Sai kin yi magana za a iya ƙwatar miki hakkinki"
Jiki na rawa Ramma ta kalleshi, amma ta yi shiru. Tsura mata ido yayi ba tare da yayi magana ba, babu shiri ta fara bayani tiryan-tiryan.
Nabila ta ce "Taɓɗijan, wannan case ɗin akwai sarƙaƙiya, cikin jikinta na halal ne ai"
Maman ramma ta ce "Dan girman Allah ku taimake ni a zubar da cikin nan, yaron nan ba shi da tarbiyya ko kaɗan, babu ɗan da zai yi alfahari da shi a matsayin uba, ni dai bana buƙatar sa".
Viper ya ce "Na goyi bayan haka, yakamata ta koma makaranta ne, ta fuskanci rayuwarta da ƙalubalen rayuwa"
Ramma ta fashe da kuka, Nabila ta ce "A'a dan Allah ku yi haƙuri, laifi ne na kisan kai, ko kin yadda a zubar?" Tayi maganar tana kallon ramma.
Ramma ta girgiza kai ta ce "Mama dan Allah ki yi haƙuri, nayi masa alƙawarin ko an kama shi, ba zan zubar da cikin ba, dan Allah ki bari na haihu, ya ce mini mutuwa ake yi idan aka zubar da ciki" tayi maganar cike da yarinta da wauta.
Salati suka hau yi, Viper kawai ya jinjina kai.
Ya tashi ya ƙarasa gaban Ramma, ta sake takurewa gabanta na tsananta faɗuwa.
Ya ce "Kin san yayanki Nura ko da ya mutu?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Baban wannan mutumin da yayi raping ɗin ki, ya ci mutuncin ki, shi ne ya yi sanadiyar mutuwar sa, bayan ya yi masa fyaɗe ta wurin bayan gidansa, idan kin zaɓi ki rufa masa asiri ba zaki bayar da haɗin kai ayi abin da ya dace ba, ba kanki kawai ki ka cutar ba, har da marigayi ɗan uwanki"
Toshe baki ramma tayi, tana bin Viper da kallo, jin maganar tasa kamar almara, sai yanzu wasu abubuwan suka din ga dawo mata.
Nabila ta ce "Vi da ka sani baka gaya mata a haka ba"
"Muddin aka tafi a haka, zata baki kunya a wurin Shari'a, alamu sun nuna zata iya ruf masa asiri"
Ya kalli maman ya ce "Mama, zamu tafi, akwai uzururruka da zamu yi amma zan dawo, ki yi haƙuri, na san na fama mana wani ciwo mai wuyar warkewa.
Ta jinjina masa kai ta ce "Gara da ka yi mata hakan, na gode Aminu, Allah ya kula da kai ya tsare mana kai. Kema Allah ya rufa miki asiri duniya da lahira". Tayi maganar tana kallon Nabila, bakinta fal maganganu, da tambayoyi, sai dai gargaɗin da aka yi mata ya hanata tambayar, amma har a wannan lokacin zuciyarta na bugawa cikin tsananin tashin hankali da mamaki, a duk lokacin da ta ga Nabila, mussaman a yanzu da ta gansu tare da Al'amin, kuma ya ce mata ba Jauhar ba ce.
****
Abdul yana tare da su Salim, ya sha ya bugu yayi mankas, dan abin da yake yi kenan ya samu sassauci, gaba ɗaya nema yake ya haukace saboda rashin sanin in da ramma take.
Salim ya miƙe yana ƙoƙarin kama shi su tafi, kawai suka ga an kewaye su, wasu mutane sanye da kaya personal.
Ba su yi musu wani dogon jawabi ba, suka kama su gaba ɗaya suka tafi da su.
Indabo yana Abuja, zuwa kano ya gagare shi, duk da zaman Abujan ba daɗi yake yi masa ba, kotu ta yi seazing ɗin passport ɗin sa, babu damar fita ƙasashen waje, har sai an kammala bincike, kwamiti biyun da aka kafa, na binciken kuɗaɗen da aka karkatar, duk sunansa ya fito a ciki, ga kuma tuhuma daga ɓangaren EFCC.
Gefe guda kuma, a Kano mutanen yankinsa na shirin yin abin da ba a taɓa yi ba a Nigeria, shi ne yi masa kiranye, ya dawo daga Abuja ba su gamsu da wakilcin da yake yi musu ba, ya rasa wane tunani yakamata ya yi, wace mafitar yakamata ya fara nema.
Ana tsaka da haka aka kira shi a waya, aka sanar da shi an kama Abdul, ba a ma san wace police station ɗin aka kai shi ba, abokansa ne suka sanar da kama shi.
Hakan ya ƙara gigita shi, da tayar masa da hankali, ya fara shirin tahowa Kano.
****
An so a kai ruwa rana kafin a bawa Abba damar ganin Nabila, sai dai kasancewar shi ma retired solder ne, aka bashi damar hakan. Sai dai suka tarar da Nabila bata nan. Gaba ɗaya Abba ya rikice, ya din ga faɗa ya ce "Shi ba haka aka yi masa bayani ba, an ce za a riƙe masa 'ya ƙarƙashin kulawar hukuma, dan me zai zo ace bata nan"
"Sir, bawa yarinyar nan kariya baya nufin mu yi ta ɓoyeta, akwai ayyukanta da take gabatarwa na aikinta. Sun fita an yi mata rakiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 86 Chapter of 121