Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
63 / 121
ta yamutsa fuska ta ce "Ka sallame su kawai, babu buƙatar na gansu" "Kamar yaya, abu mai muhimmanci da ki ke nema, ki ce a sallame su" "To ai nayi nisa ne, yaushe na bar abun da nake yi na zo" "Ki bari koma menene ki taho yanzun nan" to kawai ta ce masa, ta ajiye wayar. Ta cikin niƙabinta, take ƙarewa asibitin kallo, wurin cashier ta sake zuwa, sai dai yau wata mace ce. Suka gaisa Nabila tayi mata bayanin abun da ya faru jiya, ta buƙaci ta dubo receipt ɗin da aka turo musu na biyan kuɗin, ta ciro ta bata. Ta shiga computer ta duba, ta kalli Nabila ta ce "Ban ga receipt ba, kawai an saka bill settled" "Ina ne ofishin MD, ko admin na asibitin nan, dole fa a nemo wanda ya biya kuɗin nan" Ta ce "Ba sa shigowa da wuri, amma maybe zuwa anjima" Nabila ta juya ta koma ɗakin Viper. Ya canza kaya ya zauna a kan gadonsa. Har walid ma ya zo, ya buɗe masa wainar shinkafa ta sha ƙuli-ƙuli, yana lallaɓa shi ya ci. "Barrister har kin zo ashe?" Ta ce "Eh oga Walid, na zo tun ɗazu, naje likita ya duba ni, allurar da master ya caka mini jiya, hannuna ya sage" da sauri Viper ya kalleta. Walid ya ce "Subhanallah, Allah ya sauwwaƙe ya ƙara afuwa" Ta kalli wainar gaban Viper, ta ce "Oga walid ɗauke wainarka, na dafo masa abinci. Ta janyo ledar viva daga ƙarƙashin gadonsa, ta buɗe food plask, ta ɗaukko mini tea flask ɗin ta, ta haɗa masa tea. Faten dankalin turawa ne, ya sha ganye sosai da nama, sai ƙamshi yake yi duk ya cika ɗakin da ƙamshi. Ta miƙa masa shayin ta ce "Bisimillah ranka ya daɗe, kaga tea ne, da ɗuminsa sai ka samu cikinka ya warware, kaga tun jiya baka ci komai ba, ina fatan Allah ya baka lafiya da wuri, mu cigaba da aiki muna addu'a, in sha Allah sai mun dangana da nasara" Ya ɗaga kai yayi mata wani irin kallo, ta ce "Ba danni ba, dan Allah idan baka ci ba ba zan ji daɗi ba, dan kai na girko na kawo maka. Lafiyarka na da matuƙar muhimmanci a wurina please mana, ka karɓa" ya miƙo mata hannu, ta saka masa kofin tana kallonsa tana murmushi. "To yi bisimillah ka fara sha". Ɗan mama ne yake ta ƙoƙarin yin dariya, amma yana jin tsoro, ganin yadda aka bar Walid da busashshiyar wainarsa. Liti kuwa ƙyaƙyatawa ya din ga yi ya ce "Walid, miƙo mana wainar nan, mu ƙaddamar mata" "Sannu maye, aikuwa ba zaku ci ba, ku ci kanku" Nabila murmushi ta yi, ta cigaba da yi wa Viper hira, cike da tausayawa, da bashi ƙwarin gwiwa a kan haƙuri da ƙaddara. Sannu a hankali yake cin abincin, har ya cinye tas, ya shanye shayinsa. Wani murmushin ta sake yi masa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin. Allah ya ƙara maka sutura da ingantacciyar lafiya, ya baka tsawon rai ya bamu nasarar ɗaukar fansar abun da aka yi mana. Har cikin raina nake jin zafin abun da ya faru da kai, but before then. Please promise me ka daina z1y ³y2ubar da hawayenka, wanda ka yi ya isa. Kuma kayi mini alƙawarin ba zaka sake shan ƙwayoyin da za su illata mini kai ba" Liti ya tashi ya ce "Nikam nayi waje, wannan wace irin fitsara ce?" "Ka kalleni mana dan Allah" ya ɗaga kansa ya kalleta. Duk da idanunsa sun yi mata nauyi, amma ta ce "Ka ce Nabila, nayi miki alƙawari ba zan sake shan miyagun ƙwayoyi ba, ba zan sake yi wa kaina allura ba, zan baki cikakken goyon baya in ɗauki fansata ta hanyar da ta dace" "Tashi zan kwanta" ya faɗa a taƙaice. Duk wannan zubar da ta gama yi, ba su ne a gabansa ba, kawai ta tashi zai kwanta. Ta fuskanci aiki ne jawur a gabanta, ba ta sare ba taƙi tashi, ta kuma ƙi magana. Ya ture ta, ya raɓa ya kwanta ya juya mata baya. "Allah ya baka lafiya ya jaddada rahamarsa ga marigayyiya jauhar". "Amin ya Allah, na gode" yayi maganar idanunsa a lumshe. Tayi murmushi jin ya amsa, ba ya wasa da duk abun da ya shafi Jauhar. Walid ne ya rakota, take ce masa "Ku yi haƙuri da wasu abubuwan da zaku ga ina yi, ina yi ne saboda sama wa ƙwaƙwalwarsa nutsuwa, idan ba haka ba zai iya rasa hankalinsa baki ɗaya" Walid ya ce "Karki damu na fahimce ki, ki rabu da liti, ba kan gado ya cika ba dama". *** Ramma na kwance a jikin Abdul, yana waya da mahaifiyarsa, tana yi masa magana a kan haɗa lefensa, ya ce su yi duk abun da yakamata, yau zai je asibiti ne, zai yi tiyata cikin dare, dan haka yayi busy. Ya kashe wayar, ramma ta motsa tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ta ya ce "Beb, ina zaki kuma?" Rai a haɗe ta ce "Na gaji da kwanciyar tashi zan yi" Ya tashi zaune ya ce "Haba rahama, nifa duk wani motsinki ina gane me kike nufi, ai na baki haƙuri, kin san dalilin auren nan..... "Ni cewa nayi na damu da aurenka? Ina ruwana ne ni damuwata na koma gaban iyayena" Abdul ya ce "Zaki koma, amma sai Allah ya sa kin samu ciki kin haihu, am doing this for your own benefits, saboda ke duk nake haka". "To bana so, ka daina" "Haba sayyada, ba fa zina zan yi ba aure zan yi, kin ce in yawaita istigfari Allah zai yafe mini, to ke kuma kin ƙi ki yafe mini, ki yi amfani da iliminki mana haba sayyada rahama" "Ba wata sayyada, sayaddar da ka kafawa ƙahon zuƙa sai ta haifi ɗan shege ko?" Kawai ya kama dariya, ya ce "Ke dai ba a iya miki, idan an yi nan sai ki yi can, anjima zan kai ki shan ice cream mu ɗan fita mu zagaya". "Ba zan je ba" Ya ce "Shikenan huta roro, na ɗauki amaryata mu je" Tayi tsaki, ta sauka daga kan gadon, ta nufi toilet. ***Bunkure ta fito daga shari'a kenan, ta nufi motarta, ta tarar da Nabila a tsaye tana jiran isowarta. Ta tsaya ta kalli Nabila, Nabila ta kalleta ta ce "Na je office ɗin ki sau biyu, an ce ba kya nan, kin yi balaguro, da ki ka dawo kuma, bani da isashshen lokaci. Ina son sanin in da ramma take, ita wadda aka yi wa fyaɗen, da shi kansa likitan da yayi documenting ya tabattar da an yi mata rape, ba wai takarda kawai ba. "Ke, kin fara wuce gona da iri fa, kar ki bari na waiwayeki, nayi yinƙurin ɗaukar mataki a kanki" "Wane matakin kenan? Harka ce ta aiki fa, idan kina da gaskiya menene na ɓoye-ɓoye. Nayi mamakin yadda kina mace, once a rape victim, amma ki zama tsanin kare masu laifi. Na san kin ga shaidar da na gabatar a kotu, ta sautin muryar mahaifiyar ramma, kuma ko sama ko ƙasa an nemeta an rasata yanzu. Shikenan idan kina taƙama da kun saye lawyoyi da alƙalai, ki shirya motsi na gaba da zan yi. Sai na bankaɗo duk wani shu'umanci, da zalunci da ki ke yi, kuma ko a ina kuka ɓoye ramma, sai na tona muku asiri, na tonawa wanda yayi mata fyaɗe asiri. Kar ki manta ɗan hakin da ka raina....... Bata sake cewa komai ba ta tafi ta bata wuri. Wayarta ta ɗaukko ta tura wa Indabo message. "Yakamata ka motsa a kan yarinyar nan, ta fara wuce gona da iri" Kasancewar ta sha zirga-zirga, a gajiye ta ƙarasa office ɗin su. Wurin Barrister Habib ta fara nufa, tana zuwa ta tarar da Sumayya da wasu mata su biyu, a Office ɗin Barrister Habib suna jiranta. Suka gaisa da Habib, ta juya ta fice, zai yi magana, Sumayya ta ce "Bari na je na same ta. Ta iske Nabila a office ɗin ta, ta ce "Arfa, tun safe fa bayin Allah nan suna jiranki, har na zo nima, baki zo ba ina ki ka je ne haka?". "Sumayya wai baki da zuciya ne, alaƙa da ke ce bana so, na menene zaki din ga bibiyata kuma?" "Nabila, dan Allah ki tsaya mu yi magana, mu fuskanci juna dan Allah" "Babu wani abu da zan fuskanta, ni kin riga kin sire mini, ki fita ki bani wuri, ko ni baki wuri" Sumayya ta tsaya tana kallon Nabila. Nabila ta zo zata fice, Sumayya ta riƙe ta, ta ce "Ni yakamata na fice na baki wuri, na san nayi kuskure amma yakamata ace ko sau ɗaya kin saurare ni. Tabbas ina bayar da duk wasu bayanai, da aka nema a kanki, amma ni baki san a wani hatsarin rayuwata take ciki ba, domin kare taki. Ni 'yar halak ce, zan daina binki dan ki saurare ni, amma zan cigaba da aikin da aka bani a kanki. Idan kin ga dama, ki saurari matan can, idan kuma kin ga dama, ki kore su, matsalarki ce ba tawa ba" ta ja da baya, ta buɗe ƙofa ta fita. Ta so bin bayan sumayya, amma sai ta fasa, Sumayya ta faɗi maganganu masu muhimmanci, da yakamata ta tsaya ta ji menene, amma sumayya ba ta fushi, idan kuma tayi tana da wahalar sha'ani, dan haka bata bi bayanta ba ta koma wurin barrister Habib da wannan matan. *** Ƙarfe biyar Al'amin ya koma maɓoyarsu, bayan su Walid suna ta fama da shi, ya ce a sallame shi, sun ce sai ya gama warwarewa, shi kuma ya san akwai hatsari zamansa a asibitin, suna fita salla ya fice daga ɗakin, ya bar Asibitin. Sai dai yana shiga ɗakinsa, ya tarar da wata baƙar rigar, irin wadda aka ajiye masa da safe a asibiti, ya ɗaga ta ya juya, irin waccan ce sak. Ita ma a take ya yayyagata, ya watsar, ringing ɗin waya ya ji a ɗakin, ya duba ya ga wata ƙaramar waya keypad, wata lamba ce ke kiran wayar. Ya ɗaga ya saka a kunnensa. "Al'amin Viper, ka daina jayayya da ƙaddararka, bin wannan ƙaddarar itakaɗaice mafitar da ta rage maka, ka karɓi kayan da muka baka, ka dawo gida Viper" aka katse kiran, ya bi lambar, amma aka ce lambar dose not exist. Yayi jifa da wayar ya ja da baya ya tsaya yana huci. Ayshercool 08081012143 60 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Ya cigaba da zazzare ido, yana kallon ɗakin, ya ɗauki wayar da ya watsar, ya sake haɗata, ya kuma kiran lambar, amma a sai ace masa lambar dose not exist. Ya fita waje, ya zagaye gidan yana dube-dube amma bai ga kowa ba, ya koma cikin gidan ya ɗauki wayar da rigar da ya yayyaga, ya shiga banɗaki, ya watsa su a masai ya fito. *** Nabila kuwa bayan tafiyar sumayya, ofishin Barrister Habib ta koma, suka sake gaisawa da matan nan, ya ce "Ina sumayyan?" "Ta tafi gida ne, na ce gani me yake tafe da su ne?" Ya kalle su sannan ya kalli Nabila ya ce, maganarki da ki ka yi, su sumayya T ladan suka saka a radio, a kan Barrister Naja'atu Bunkure, shi ne ya sanya suka zo, su sanar miki da wasu abubuwa da zai taimaka miki". Nabila ta ce "Masha Allah, bari na aika baba masinja, ya sayo musu ruwa da lemo, naga azahar ta wuce, kafin nan nima nayi salla" Ya ce "To babu laifi" Tayi salla ta dawo, suka zauna da matan, ɗayat ta fara bata labarin abun da ya faru "Ni 'ya ce da ni, mun rabu da mahaifinta, tana wurin babanta, yayi mata auren dole, take ta guje-guje saboda ba ta san mijin. Ake ta fama har tayi yinƙurin kashe kanta, magana har gidajen rediyo, ta turo wakilanta, suka tafi da mu can office ɗin ta, ta ce aure ba dole bane ba, dan haka dole a kashe auren nan. Da fari na so ayi sulhu yarinya ta koma ɗakinta, tun da bama tare da ubanta. Na din ga yi mata nasiha, a kan tayi haƙuri, tun da babanta yana ta tsine-tsine a kan ta bujire masa, ta haƙura ta yarda, amma matar nan ta ce sai an kashe auren, zata kai ni ƙara hukumar kare hakkin ɗan Adam, ta ɗauke mini 'ya, ta tafi da ita, sai da aka yi sati biyu sannan ta dawo mini da ita ga babanta da mijinta suka ƙara matsa mini lamba, bayan ta dawo da ita, yarinya ta ƙara tuburewa ba ta san zancen aure ba. Tamkar an canza mini ita, idonta ya buɗe, har mijin 'yar tawa ta saka aka kama aka rufe, aka kashe auren nan. Yanzu maganar da nake yi miki, shekru uku kenan, yarinyar nan ta ce aure wani abu ne al'ada da muke takurawa kanmu a kai, addini bai wajabta mana ba, haka take rayuwarta, sai ta shafe kwanaki ba ta gida, tana yawonta. Babanta ya sallama mini ita, bayan ya gama tsine mana daga ni har ita. Har a cikin unguwa ta cigaba da yi wa sauran ƙasayenta mummunar huɗubar adawa da aure, wai ana tauye musu hakki, kuma wallahi Naja bunkure ce ta mayar mini da 'ya haka,tana fakewa ne kawai da taimako, tana zaluntar mutane". Ɗayar ta ce "Nima kusan hakan ne, wani yaro ɗan masu kuɗi, ya lalata mini yarinya daga aikenta gidan, jami'an tsaro suka ƙi kama yaron, uban ɗan ya ce in dai arziki yana rana, zai kare ɗan sa, ba wanda ya isa ya kama shi ya hukunta. ni kuma jin shirye-shirye da ake yi a kanta, na taimakon marasa galihu, ya sanya nima na je neman ta taimaka mini. Da farko abu kamar gaske zata taimaka mini, ƙarshe abun ya juye, aka nemi a mayar da case ɗin wai sharri muka yi wa yaron. Wallahi ƙarshe yarinyata fiya-fiya ta sha ban sani ba, yar shekara goma sha huɗu ta mutu. Wallahi matar nan azzaluma ce, bamu da wurin da zamu je, mu nemi hakkinmu sai wurin Allah, haryanzu idan zance yayi zance a kan tayar da maganar abun da ya faru da yarinyata, wanda hakan ba ƙaramin tsaye mini yake yi ba" tayi maganar tana kuka mai ban tausayi. Nabila ta tashi ta rungume matar, tana rarrashinta ta ce "Ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, Allah ya jiƙanta, kuma in sha Allah da ikon Allah sai mun kai matar nan ƙasa, zan yi iya yi na, in bankaɗo duk wani mugun abu da ta aikata muku, kuma sai ta girbi abun da ta shuka, ku yi haƙuri. Yanzu duk zaku bani adress ɗin ku, zan bi cases ɗin ɗaya bayan ɗaya, na tabattar da abun da ya faru kafin na san abun yi" Jikin Nabila yayi sanyi sosai da sosai, da jin abubuwan da Bunkure take aikatawa, tamkar ba 'ya mace musulma ba, da matan ke iƙrarin ciwon ƴa mace, na 'ya mace ne. Har kuɗin mota ta basu, bayan tafiyarsu ta kalli barrister Habib ta ce "Yaya habib, ka ji wani yahudanci? Ina laifin ta tsaya a kan iya kashe auren an yi wa 'yar auren dole?" "Ke ce baki san wacece ita ba sai yanzu, wannan wata ɓoyayyiyar aƙidarta ce, na bawa mata damar ƙin zaman aure da lasisin karuwanci. Tana saye yaran da kuɗi, da abun duniya wurin cusa musu wannan mummunan ra'ayin, da koyar da su daidaiton jinsi tsakanin su da maza". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma duk da haka Alhamdilillah, na samu hints a kan yadda zan bankaɗo asirin matar nan, and one more thing kuma" ya kalleta ya na jiran me zata ce. "Maganar da muka yi da kai kwanakin baya, a kan case ɗin Aminu Viper" "Ina jinki" "Naja'atu Bunkure tana cikin tawagar lauyoyin da suka tsaya kai da fata a kan shari'ar da aka yi masa. Kuma ka san ita ungulu ce ba ta jewar banza, dan haka akwai manufa a cikin shiga shari'ar da tayi. Viper ba ɗan siyasa bane ba, kuma ba shahararren mai kuɗi bane ba, balle ace tsaya masa tayi a shari'ar. Dan haka akwai ayar tambaya a kan charges ɗin da aka yi masa na kisan kai. Take a look at it barrister, an tsare mutum shekara biyar, an yi masa shari'a sau biyar kawai, an kai shi prison an ajiye babu conclusion na shari'ar, is je guilty or innocent? Kwatsam an ce ba a ganshi a prison ba, kuma an cigaba da nemansa, ruwa a jallo, anya akwai gaskiya a lamarin nan kuwa?" Ya tsura mata har ta gama, yayi murmushi ya ce "Haka kwanyar nan take cike da basira, amma aka ƙarar da ita a wurin iyayi da kwalliya?. Maganarki gaskiya ce Nabila,  amma ina rabaki da case ɗin Vipern nan, akwai badaƙala sosai a kan case ɗin". Nabila ta ce "Me da me ka sani a kai?" "Nothing much, kawai na san dai akwai bita da ƙulli ne a ciki sosai" Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, bari na tafi gida, yau a matuƙar gajiye nake" tayi masa sallama, ta tafi office ta ƙarasa shirinta, ta tafi gida. Ta sake karo da file a office ɗin. Cikin mamaki ta ɗauka, ta fara buɗewa. Aka rubuta continuation a ciki. Cigaban tarihin Naja bunkure ne, bayan rape da aka yi mata, cousin brother ɗin ta, aka rufe case aka ce abu ne na dangi, bayan ta ƙara girma tayi aure, ta sha wahala sosai a hannun mijinta na farko, ya azabtar da ita tamkar baiwarsa, ko haihuwa ba ta yi ba auren ya mutu. Yayanta ne ya taimaka mata, ya mayar da ita makaranta, tayi candy, ta shiga jami'a, sai dai bayan rasuwar yayanta, aka rasa mai sponsiring ɗin ta, ta cigaba. Mahaifiyata na can wani garin tana aure, babanta kuma ya ce ba ruwansa da ita, tun da taƙi zaman aure. A lokacin har wurin ɗan majalisar su, ta je neman kuɗin makaranta, lokacin yana tare da Indabo, indabo ya ce zai bata, amma sai dai ayi bani gishiri na baka manda. Ta amince tun daga nan, ta zama tamkar matarsa su watse ya biya mata kuɗin makaranta, babu wani sirri nasa da bata sani ba. Ta nemi ya aureta, bayan tayi graduation, amma yaƙi, ganin haka ya sanya, ta samu wani suka daidaita ya aureta, sai dai Indabo ya cigaba da bibiyarta. Ta fara aiki a matsayin lawyer mai zaman kanta, Naja tana da burin yin luxry life sosai, sai dai mijinta yana da rufin asiri amma ba irin wanda take hange ba, Indabo yayi mata alƙawarin haɗa ta da manyan mutane, lokacin ya zama ɗan majalisa, wanda zata din ga samun alkhairi da damarmaki. Kwaɗayi da buri, ya sanya suka koma ruwa da aurenta, ya din ga kashe mata kuɗi, yana kuma haɗata da manya. A wurinsa ta koyi shaye-shaye. Tsakanin ta da mijinta babu ragayya ko kyautatawa, duk son da yake nuna mata da kulawar da yake bata sam baya gabanta. Ta fara tashe sosai tana shahara, ana programs da ita a kafafen watsa labarai, ta buɗe ƙungiyar ta ta kanta, bayan joining ɗin ƙungiyoyin yahudawa, masu da'awar daidata jinsi, reshen Nigeria, ta cigaba da yi musu aiki ta ƙarƙashin ƙungiyar ta. Sai dai a haka take miyagun harƙallarta, na yi wa manyan mutane safarar mata a birnin tarayya, musamman ƙananan yara, da akan yi amfani da su saboda asiri. Red handed mijinta ya kamata, chats ɗin ta da wani minista, na ƙazanta, yayi kuka, amma ko a jikinta, ta ce idan ba zai iya ba ya rabu da ita. Haka ya saketa, ta samu cikakken gashin kanta. Ba ta taɓuwa, ko da kuwa tayi laifi, yanzun nan ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam zasu shiga lamarinta. Ta din ga binne mutane ta hanyar bayyana musu kyawawan ayyukanta, da ɓoye na laifin. Bayan mutuwar aurenta labari ya bazu, mutane suka din ga tsinewa mijinta, wai ya saki macen kirki, aka yi hira da ita, ta din ga kuka tana yi tsohon mijinta sharri kala-kala. End the story.... Aka rubuta a ƙarshen page ɗin. Wani irin gumi, ya din ga tsatstsafowa Nabila, ta ma rasa abun yi, da tunanin da yakamata tayi, ba ta bari ta takura ƙwaƙwalwarta wurin hasaso waye ya kawo mata file ɗin a karo na biyu ba, kawai ta ɗauki jakarta ta fita. *** Sumayya ce a tsaye tana kuka wiwi, shi kuma ya zuba mata ido, ko ƙiftawa baya yi, sai da tayi mai isarta sannan ya ce "Kukan ya isa haka, meyafaru?" Ta share hawayenta ta ce "A gaskiya sir, ni na gaji da aikin nan, na samu matsala da ni da Nabila, ni Nabila ba ƙawata ce kawai ba, ƴar uwata ce, ta riga ta yi fushi, ba zata saurare ni ba, ni ban san wanda ya gaya mata ina bibiyarta ba, ga wancan honorable ɗin ya addaba mini, duk motsina sun sani, sai kuma sun tambaye ni, me tayi me take ciki, banda barazana da suke yi mini ba yau ba gobe, ni dai dan girman Allah ka yi wani abu a kai, kar ni ko ita ayi wa wani illa, indabon nan fa ba imani ne da shi ba" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka. Yayi murmushi ya ce "Haba ƴar jarida, ya da kuka wiwi haka da karaya nan da nan? Da kin sanni, kin san zan taimake ki? Baki san ya aka yi na gane Indabo yana yi miki barazana ba. Har na shigo lamarin ba, dan haka ba zan bari a cutar da ku ba, dukkaninku a kan gaskiya ku ke, sai dai ita naga buyaginta yayi yawa. Ki yi haƙuri ku daidaita, da haka zan cigaba da yi mata supplying abubuwan da take buƙata a harkar shari'ar nan" "Sir yanzu fa ka gama cewa buyaginta yayi yawa, sai ce mini munafuka take yi, babu yadda tsakanunmu yanzu" Ya ce "No, tayi fushi ne kawai, and ki ƙara kiyayewa sosai da sosai, ki daina bari tana gane kina bibiyarta". Sumayya ta ce "Yanzun ma, wallahi ina kiyayewa, ban san yadda aka yi ba" Ya din ga rarrashinta, sannan ya saka aka ɗauke ta a mota, aka mayar da ita gida. *** Nabila da ƙyar ta isa gida, ta watsar da kayan a kan gadonta, ta fara kiran wayar Viper, amma a kashe, ta kira ta Walid amma baya ɗagawa, haka ta haƙura ta shiga banɗaki tayi wanka ta yi alwala ta fito. Har washegari da safe, Nabila tana neman layin Walid, hankalinta ya ƙara tashi, tayi tunanin ko wani abun ne ya same shi. Tana saka kayan abinci a motarta, Nasir ya fito. Ta ce "Yaya ina kwana?" Ya amsa da "Lafiya ƙalau, wai ina ki ke zuwa da kwanukan abinci kwana biyun nan ne?" Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ci nake yi mana, wataran ai wuni nake yi bana gida" Ya ɗage kafaɗa ya ce "Ban sanki da dakon flask ba, saboda haka kin gwammace ki ci biscuit da sauran kayan ciye-ciye" "Haba yaya, yanzu ba mota ce da ni ba? Kuma zan je in ta cin abinci nikaɗai duk ga mutane ne a wuri?" Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma yanzu ƙarfe bakwai saura kwata, har shida da rabi kin fita, saɓanin da har goma saura sai ki kai a gida" Ta tsaya sosai ta dube shi ta ce "Yaya me kake nufi ne? Ka daina ɓoye-ɓoye ka fito fili ka sanar mini cewar, tuhumata kake yi, da aikata rashin gaskiya mana" Yayi murmushi ya ce "Ai ba a tuhuma sai an tabattar da zargi my dear" "Da ka daina zargin, dan wahalar da kanka kawai zaka yi, ko kuma irin abun naku zaka yi mini na masu kaki" tayi maganar tana murmushi. Shi ma murmushin ya yi, ya ce "A sauka lafiya" Ta amsa da Amin ta tafi. Tana tafe a hanya sai ga kiran wayar Walid, ta ɗaga wayar ta ce "Oga Walid, sai kiranka nake yi a waya, shi wayarsa ba ta shiga, wayarka kuma baka ɗagawa" Walid ya ce "Bari kawai, kin san halin mutumin naki sai a hankali ai, jiya bayan tafiyarki, ya kafa mitar sai an sallame shi daga Asibiti, da mu da likita muka din ga rarrashin sa, yayi mana banza, mun fita salla ya gudu, baki ga yadda hankalinmu ya tashi ba, na ce musu kawai mu koma gida, dama ya saba irin haka, ko lokacin da ƙanwata take raye, haka take fama da shi, idan aka kwantar da shi, da ɗanyen ciwo haka zai bar asibiti sai dai ta ƙarasa masa dressing a gida ya warke". Nabila ta ce "Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, shi kuma ya bashi juriya. Kana ji na, zan shigo dan ga abinci ma nayi, yayana ya fara saka mini ido ne, dole na canza takuna, zuwa azahar zan bar motata a chamber, zan

Chapter 63 of 121