da zai gusar masa da hankali, ko yayi ɓarna, yana ta iya ƙoƙarin sa a kan dainawa, kuma cikin ikon Allah ya rage kaso mafi yawa. Baba ya nuna masa jin daɗin sa a kan haka, tare da yi masa addu'a.
Ba ayi sati da zuwa gidan ba, tsautsayin nan ya faru, kuma ko a kotu, bai ga Baba ya je ba.
Viper cikin mamaki, ya ga Baba ya rungume shi, ya ce "Sannu Al'amin, sannu da zuwa" ya riƙo hannunsa, ya buɗe gate ɗin gidan, yana jan hannun Al'amin.
Saroro tijjani da saifu suka bi baba da kallo, duk tsawon lokacin da ya shafe, yana gaya musu bai yadda Al'amin zai kashe jauhar ba, ba su yadda da gaske yake ba, dan ya ce musu babu wata gamshashshiyar hujja a kan hakan.
Suka ankarar da shi cewa, yana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, dan haka ba abin mamakin bane ba, amma ya ce shi dai har zuciyarsa bai amince da hakan ba.
Har tsakiyar falonsa ya shiga da shi, cikin murna da farincikin ganin sa, ya ce "Zakiyya, ku kawo masa ruwa, sannu Aminullahi amintaccen Allah, dama zan sake ganin ka bayan na rasa Waliyiyya? Sannu Aminu" kawai Viper ya durƙusa a kan gwiwoyinsa, ya riƙe hannayen Baba, ya ɗaga ido ya kalle shi, ya ce "Wallahi baba ban kashe jauhar ba, ban kashe waliyiyya ba, me tayi mini me zai sanya na kasheta? Idan da wanda zai tafka asarar mutuwarta to ni ne, ni ne nan baba, zan yadda idan aka ce nine sila, amma da hannuna ban kasheta ba baba, ba ni na kashe maka jauhar ba, na san duniya ba kowa zai yadda da hakan ba, amma na san ko yaya, kai zaka yarda da ni Baba, wallahi ban kasheta ba, nayi burin kashe kaina nima, ko dan kaucewa sake haɗuwa da kai, ban san me zan ce maka ba, ban san da wasu kalmomi zan yi amfani ba, kawai dai ban kasheta ba"
Cikin rauni, da dattaku, Baba ya rungume Viper a kan kafaɗarsa, yana dukan bayansa cikin sigar rarrashi, ya ce "Ko kowa bai yadda ba, wallahi ni shaida ne Aminu, ni na san me na gani, na san me na ji daga bakinta a kanka, kar ka damu, na san me ka ke ji, na taɓa tsintar kaina a yanayi mai kama da naka, ina fatan Allah ya yi wa jauhar rahama, Allah ya sa halinta na gari ya bi ta"
"Nayi asarar mace Baba, ta bar ni da raunin da ba zai taɓa gogewa a zuciyata ba, ba zan fasa zargin kaina da ni ne silar mutuwar jauhar ba, taurin kai da jinkirta barin aikata laifi, shi ya janyo mini haka, ina kewar matata" tamkar ƙaramin yaro, haka ya kwantar da kansa a kafaɗar Baba yana kuka, kukan da ya daɗe yana fatan Abbunsa ne ya fuskance shi ya bashi wannan damar.
Baba ma kukan yake yi, ya ce "Haka Allah ya tsara, ka yi haƙuri, mu duka na haka ne, zaman jiranta muke yi. Bayan an kama ka, mijin yayarta hafsa da ya so ya aureta, shi ya zo ya same ni, ya ce mini in ci gaba da addu'a, Allah ya bayyana gaskiya, amma ba kai ka kashe jauhar ba, abin ne akwai sarƙaƙiya, duk da ni dama tun farko ban yadda zaka kashe mini 'ya ba. To kuma daga baya ita ma hafsan zaman yaƙi daɗi, suka rabu".
Viper ya ɗago ya kalli Baba cikin mamaki, ya ce "Shi ne ya zo ya ce maka bani na kashe jauhar ba?"
Baba ya jinjina masa kai, ya ce "Eh, shi ya gaya mini haka"
Viper ya sauke numfashi ya share gumin da ya haɗa da hawaye, da handkerchief ɗin sa.
Gaba ɗaya cirko-cirko mutanen gidan suka yi, suna mamakin baba, yadda ya sake da Al'amin, wataƙila ma ƙarya kawai yake ta zuba masa, dan kawai a tausaya masa.
Viper ya ce "Na zo da wata tambaya da nake buƙatar amsarta baba"
Baba ya ce "wace tambayar ce?"
"Baba jauhar mutum nawa ce?"
Cikin mamaki baba ya ce "Kamar yaya?"
"Tana da wata 'yar uwa ne, da suke ciki ɗaya?"
"A'a itakaɗai ce"
Ya jinjina kai ya ce "Akwai lauyata, da muka zo tare, zaku tattauna da ita, wadda ita ce tambayata da nake son ka amsa mini" ya tashi tsaye, ya nufi hanyar fita.
***
"Kankarofi, zuwa yanzu ina fatan hankalinka ya kwanta baka da wata damuwa ko?"
Ya kalli indabo ya ce "Ba ni da ita Indabo, kawo ƙarshenka, babbar nasara ce, da rage mugun iri a ƙasa ko ma na ce duniya baki ɗaya"
"A'a, bari murna karenka ya kama zaki, da saura tukuna baka kawo ƙarshena ba, kuma kawo ƙarshena tamkar kashe maciji ne, baka sare kansa ba"
Kankarofi ya ce "Ko ban sare kansa ba, ya tashi, na rage masa karsashi da ƙarfin mugunta da zalunci. Kuma in sha Allah wannan kujerar da ka cimmata, ta hanyar zubar da jinin mutane bisa zalunci, da amfani da rayuwar talaka ka cimmata, ka wofantar da su ka tagayyara rayuwar su, sai ka barota, sai ka kuma fuskanci hukunci.
Yanzu haka ana shirin tsayar da kadarorinka, a kai gaban shari'a bisa laifin sata wato cin amanar ƙasa, bayan babban tattalin arzikinka da aka kama, na miyagun ƙwayoyi a Italiya. Ka san Waye yayi maka aikin kama ɗanka da kama maka dukiya? Viper! Abin ya baka mamaki ko? Wani banbarakwai, da yake ce maka ya saka an kama ɗan sa ka daɗe kana mamaki, da ganin ƙarya yake yi. Dodo babban sarki ya fi ka lissafi, da shu'umanci indabo, sirrinka da ya sani, ya san zaka kashe shi, ba za ku bar shi da rai ba, da shi da tawagarsa, shiyasa ya ƙara jan Viper, ya sanar masa da duk wani abu da yakamata ya sanar masa. Duk tsawon lokacin da Viper ya shafe tare da kai... Yayi shiru yana kallon Indabo.
"Spy ne, hatta yadda ka ke samun return da kai da tawagarka, a kan tashe-tashen hankulan da ake yi a ƙasar nan, yadda ku ke safarar makamai ta ɓarauniyar hanya cikin ƙasar nan, Viper ya sani, dodo ya gaya masa, aikin contract rundunar tsaro ta bashi a kanka, kasancewar waccan gwamnati duk gayyar tsiya ce irinka, ya sanya ba su iya yi muku komai ba.
Sannan Viper bai shafe shekaru biyar a gidan yari ba, yana can yana karɓar horo na musamman a kan zama cikakken jami'in leƙen asiri. Idan ku kuna amfani da doka, wurin tozarta ƙasa yadda ku ka ga dama, mu ma muna iya amfani da ƙarfinmu ta ɓarauniyar hanya mu yi wa ƙasa aiki. Ina fatan yanzu ka fahimci BODMAS ɗin da Viper ya gaya maka. Kar fa ka zarge shi, sam shi ma wasu abubuwan bai san da su ba, tsuntsu biyu na jefa da dutse ɗaya.
Sosai ƙafafuwan Indabo suka fara karkarwa, saboda mamaki da tashin hankali.
"Ka hanzarta, ka je ceil ka duba ɗanka, kar wahala ta kashe shi, dan ya saba da hutun da aka samar masa ta hanyar zubar da jinin dubban matasa, a kan harkar daba bayan ka basu miyagun ƙwayoyi, ka gina ɗanka, gashi dai ka bashi ilimin, yana amfanar mutane, gefe guda kuma ya gado duk miyagun halayenka, kuma a haka ka ke ƙoƙarin ɗora shi a kujerar mataimakin gwamna, shi gwamna kai senator, ku cigaba da azabtar da mutane, tun da shi mulkin gadon gidanku ne, you are not serious, Allah yana son bayinsa. Kuma ina tayaka murna, saura wata guda kacal ayi recall election, mutanen yankinka za su yi maka kiranye, abin da ba a taɓa yi a tarihin ƙasar nan ba, sai a kanka" ya ɗauki glass cup ɗin ya bar falon.
***
Mamaki ne ya kama Nabila, ganin idon Viper yayi jawur, gidan da ya shiga bai yi kama da na mutanen banza ba, balle ta ce ko shaye-shaye ya shiga yi, hakan ya tabbatar mata da kuka yayi.
Ya kama hannunta, ya ja ta zuwa cikin gidan, kasa yi masa magana ta yi, ta cigaba da bin sa.
Tijjani da saifu da suke tsakar gida, darewa suka yi, suka ja da baya suna zazzaro ido, ganin wadda Viper ya shigo da ita.
Zakiyya kuwa iya ƙarfinta ta saka uban ihu, ta zura da gudu ɗaki, tana dambe da ƙofa taƙi rufuwa, saboda razani da tsoro.
Nabila tsaywa tayi tana kallon dattijon, wanda shi ma ya ƙame wuri guda yana kallonta, tun daga sama har ƙasa.
Ta baya Nabila ta ji an yi mata wata irin runguma da ƙarfi.
Hafsa ce, ta ce "Jauhar, sai da na gaya musu na ganki rannan a asibiti, da na je ganin doctor Abdul yasar, amma suka ce bani da hankali"
Jiki a matuƙar sanyaye, Nabila ta rungumeta ita ma, duk da ba ta san wacece ba.
Hafsa cikin kuka ta ce "Kin haihu? Ina jaririn naki yake? Mastern ne ya kai ki asibiti? Kin ga aurena ya mutu ko? Na sha wahala a gidan Alhaji mu'azzam".
Nabila ta ɗaga kai ta kalli Viper, ta mayar da idonta kan dattijon, amma ta kasa magana, sai lumshe idanunta take yi, tana rufewa tana fatan jin amsar tumulin tambayoyin da ke bakinta, ba tare da ta iya furta ko tambaya ɗaya ba, dan ji take yi, tamkar an kanannaɗe mata harshenta.
A tare Major da Nasir suka fito daga mota, cikin ikon Allah suna fitowa, suka yi arba da liti da walid a tsaye a jikin motar da suka zo.
Nasir ya ce "Yauwwa Abba gasu nan, ina Viper yake, ina ku ka kai Nabila?"
Liti ya ce "Ba a sani ba, kai a wa zaka zo kana yi mana tsawa?"
Ya kalli liti ya ce "Ni ka ke gaya wa haka?"
"An gaya maka ɗin"
Major ya ture Nasir ya ce "Ina 'ya ta take, waye shi yaron a cikin su?"
Nasir ya ce "Abokansa ne"
"Shi yana ina? Meya kawo mini 'ya nan yayi mata?" Major ya yi maganar a matuƙar hasale.
Walid ya ce "Suna cikin gidan can" yayi maganar yana nuna musu gidan da Viper ya shiga da Nabila.
Major ya tunkari gidan, liti ya ce "Wallahi bin su zan yi, kar wannan mai kunnuwan ya je yayi musu wani abu"
Viper ya ce "Baba wannan ita ce tambayar da na zo maka da ita, nake neman amsarta"
A hankali baba ya fara takowa, yana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, subhanallah wa bi hamdihi, adada khaliƙihi, wa rida nafsihi, wa zinatu arshih" yana miƙa hannun sa, yana ƙoƙarin taɓa Nabila.
Da ƙarfin tsiya, Nabila ta ji an ja ta baya, har ta na ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, major ya nuna Baba da ɗan yatsansa ya ce "Kar ka kuskura, baka da wannan ikon, babu wanda ya baka wannan damar, tsohon macuci ma ci amana"
A hankali baba ya ce "Yusuf maitama"
Major ya ce "Bashir lamiɗo" suka kalli juna.
Baba ya ce "Bai kamata haɗuwarmu ta kansace a haka ba"
"Babu wani abin kirki da yakamata a tsammata daga azzalumin mutum, mara imani da tausayi irinka, haɗuwar da ta fi wannan muni ita yakamata muyi. Ke kuma wuce mu tafi, da kin san wanenen wannan tsohon najadun da abin da ya aikata wa babarki, da baki yi marmarin ganinsa a rayuwarki ba, wuce mu tafi kafin nayi ƙasa-ƙasa da ke. Kuma da na san kana garin kano, da da nayi retire ban zo kano na zauna ba"
Baba ya sha gabansu ya ce "Maitama, babu in da zaka je sai ka gaya mini ita kuma wannan wacece, duk da ko baka faɗa ba, na san 'ya ta ce, amma nauyin laifin da nayi maka bai kai zunubin da aikata mini ba, wacece wannan?"
Major ya ce "'ya ta ce ta halak, wadda ba ta da uba, ba ta da wani gata sai na Allah sai nawa, ni ne uwa kuma ki ni ne ubanta, babu uba a tarihin rayuwar ta, na cireka a rayuwarta gaba ɗaya, dan haka kar ka sake saka wa zuciyarka wannan 'yar ka ce".
"Amma maitama ka san zan iya shari'a da kai a kan abin da ka aikata mini. Ka san me ka ce mini shekara ashirin da shida da suka wuce"
A fusace Major ya ce "Ka daɗe baka yi ba, ni yakamata na yi shari'a da kai, shekaru ashirin da shida baya, bisa cin amana da kisan kai, zan iya cewa kai ka kashe 'yar uwata, dan haka ba abin da zaka tsinana wa rayuwar Nabila, wanda ban yi mata ba"
Ƙara Nabila ta saki, ta silale ƙasa, nufarta suka yi gaba ɗaya, Nasir ya durƙusa zai kai hannu kan Nabila, amma Viper ya hankaɗe shi gefe, ya ɗagota.
Galala ya buɗe baki, ganin yadda ya kusa kai wa ƙasa saboda hankaɗewar da Viper ya yi masa.
Baba ma kan Nabila yayi, amma major ya durƙusa, zai karɓi Nabila daga hannun Viper.
Nabila kuwa kanta ne ya juye, wani irin jiri ya ɗebeta, ta faɗi ƙasa, wani irin kuka take yi daga cikin zuciyarta.
Viper ya riƙe ta gam, ya kalli major ya ce "Yallaɓai a ganina, kamata yayi ku yi wa Nabila bayanin wacece ita, meyake faruwa, bai kamata ta shiga cikin saɓanin da ku ka samu ba, abu ne da yake a tsakanin ku, da ya faru shekarun da suka gabata.
"Wanene kai?"
"Mijin ta jikin hoton da na bayar a kai maka".
"Mmm mijin wadda ka kashe" major yayi maganar yana kallon idanun Viper.
Su Saifu da suka fara leƙowa ɗaya bayan ɗaya cikin tsoro, saifu ya ce "Baba ka yi mana bayani meyake faruwa ne? Mu da kai mun san jauhar ta mutu, to wannan kuma wacece?"
***
Chubaɗo tun tana sanya ran dawowar Bashir, har ta fara sarewa, ta fara tunanin ko wani abin ne ya same shi, ba ta iya yi wa kanta komai sai da kyar, saboda nauyi da girman cikin da yake jikinta, abu kaɗan sai haki, gashi babu wanda ta sani a garin, ko ta san wani ma, babu yadda za a yi ta iya magana da su, ita ba yarensu take ji ba.
Cikin ta ya shiga wata na tara, ba ta iya cin komai sai dai ta wuni a kwance, salla ce kawai take tayar da ita.
Kwanan cikin bakwai da shiga watanni tara, ta fara jin alamun ciwon naƙuda, ga ƙuruciya, gashi ba ta san kan abin ba, dan haka ba ta gane meyake faruwa ba.
Ciwo ya ci gaba da ƙaruwa, tamkar zata bar duniya, sai da ta kwana biyu a haka, babu mataimaki sai Allah.
Cikin dare abu ya ta'azarra, ta rasa in da zata sanya ranta, tana jin yadda abu ya tokare ƙasan mararta, amma yaƙi fitowa, tayi kukan ma abu ya gagara ta tashi tsaye, ta durƙusa, ta kwanta kowanne ya gagara ta rasa abin da za ta yi ta ji daɗi.
Ta ji fitsari ya matseta, ta tafi banɗaki amma ya fara zuba a tsakar gida ashe faya ce ta fashe, ga ta ga banɗakin ta kasa shiga, ƙafafuwan ta suka sage a wurin, dolenta ta durƙusa a wurin, ta fara nishi.
Tana jin kan jariri ya fito, amma gangar ciki ta ƙi fitowa, ta yi iya yin ta abu ya gagara, ga numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa, kawai ta nemi wuri ta kwanta daga durƙushen da take, ta zubawa sarautar Allah ido.
Ayshercool
08081012143
86
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_GYARA SHINE MACE_*
*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327
*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,
Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍
Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍
Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃
Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata💃😍
Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃
Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃
Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima
KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻
Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi
Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu
Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra
Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa
Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka
*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻
07069711327 Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍
Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊
Wani irin nishi ne ya fara taho mata, ta yinƙura zata tashi, amma ta kasa tashin, tun tana yi kaɗan kaɗan, har ta fara yi da ƙarfi, da tayi wani ƙwaƙƙwara, santaleliyar jaririya ta faɗo jawur da ita, duk da mairamu a galabaice take, haka ta yinƙura, ta tashi zaune, ta kalli jaririyar yadda take ta wutsul-wutsul tana ƙoƙarin yin kuka, amma ruwan da yake fitowa daga bakinta, ya hanata yin kukan yadda yakamata.
Ta janyo zaninta, ta fara goge wa jaririyar cikin bakinta, tana kuka yarinyar na kuka, ta rasa yadda za ta yi da ita, ga zaren mabiyiyya a jikinta, bai faɗo ba, gashi ba ma ta san ta yadda zata raba yarinyar da zaren ba, wani irin mugun ɗaurewa, mararta tayi, tare da bayan ta, a take ta fara sabon nishi, ciwo ya dawo sabo, tana tsoron tayi muƙursusu, ta danne jaririyar hannunta, amma da masifa tayi masifa, ajiye yarinyar ta yi a gefe, ta cigaba da jijjiga kanta, jin da gaske wani abu ne yake ƙoƙarin sake fito wa daga jikinta, ya sanya ta tashi ta durƙusa, ga mamakinta wata yarinyar ce ta sake fitowa tare da mabiyiyyar da suke ciki da komai, tayo waje, sai dai ita wannan tana ta tsanyara uban ihu, kamar ana cire mata idanu.
Ta zauna da kyar, da zuba musu ido cikin tsananin so da ƙauna take ce wa "Yanzu Allah duk nawa ne wannan? Allah na gode maka, Allah na gode sosai da sosai Allah ka raya mini su duka, ka shirya mini su, duk wannan nawa ne" tayi maganar tana murmushi tana kallonsu, sai dai kuma ta fashe da kuka rashin sanin yadda za ta yi da su.
Ƙoƙarin jan jikinta take yi ta tashi, ta ɗauke su, amma abu ya gagara saboda uban jinin da yake zuba daga jikinta.
Haka ta koma ta kwanta cikin ƙazantar da haihu a ciki, tun tana ƙoƙarin ɗaukko su, har ta daina gani hankalinta ya gushe.
Ba ta da maƙwabta in da take, wani mutum ya wuce ƙofar gidan, ya shiga daji ya yi itace, ya ɗoro a kan keke, da zai wuce ya ji kukan jariri, da ya dawo ma haka. Har zai wuce ya fasa, ya sauka ya tsaya ya hau bubbuga ƙofar gidan, amma shiru, ga kukan yana ji, ɗaya da sauti mai ƙarfi, wani kuma yana tashi kaɗan-kaɗan kamar kukan jaririn mage.
Ya gaji da bugu, kawai ya kutsa kai cikin gidan, ja yayi ya tsaya, yana kiran yesu, ganin mace kwance dama-dama a cikin jini ita da yara har biyu ɗanyar haihuwa.
Da gudu ya fita nesa da gidan kaɗan, in da yake da mutane, ya tattaro mutane, suka tafi gidan.
Sai a lokacin mata suka yanke cibiyar, aka naɗe yaran da ita uwar, aka tafi da su Asibiti.
Likitoci suka buƙaci jini, a tsakanin mutanen, suka yi voulanteer suka bayar, aka din ga saka mata, yara kuma aka ce madara, nan ma ba su yi ƙasa a gwiwa ba, aka nemo madarar ba wa yaran, a lokacin duniya na kwance, babu ƙabilanci da gudun taimako.
Sai da ta kwana uku a asibiti, ba ta san in da kanta yake ba, dan daga baya jijjiga tayi, bayan an kaita asibitin.
Ga yaran aka ce dukansu su biyun, pnuemonia ce da su, dan ta ɗaya har ta fi muni ma, taƙi yin kuka yadda yakamata.
Bayan chubaɗo ta farfaɗo, da kyar, ana so ayi magana da ita, babu hali, ita ba ta jin yaren su, su ma kuma ba sa jin nata, gashi sai dai tayi ta bin su da kallo, kamar tana son gane wani abu.
Sai da tayi sati biyu a asibitin cif, aka sallameta, suna ta tambayar ta, ina ne gidan su, ina mijinta, amma ba baki sai kuka, har suka fara tunanin ko yaran dakan kuka ne, wato marasa uba.
Suka mayar da ita gidanta, suka cigaba da kula da ita, wannan ya kawo mata abinci, wannan ya kawo mata kayan sakawa ita da yaranta, da safe da yamma haka mata suke zuwa, ayi wa yaran wanka, da ruwa mai zafi, sai dai tsakaninta da su ido, sam ba ta jin yarensu, su ma ba sa jin nata.
Suka daina damuwa da sai sun san wacece, kawai suka cigaba da hidima da chubaɗo, ta zauna cigaba da jiran Bashir, tana tunanin ko wani abin ne ya tsare shi, ta dawo ta fara jin tsoro ko ya mutu ne a hanya ba ta sani ba, gashi ba ta da kuɗin mota, ba ma ta san hanya ba, balle ta koma gida.
Ita kanta ta ƙi lafiya, ga damuwa ga kewar gida ga raino, ba ta san kan abubuwa ba, ga jijjigar da ta yi, ta taɓa mata ƙwaƙwalwa.
Kusan duk sati sai an kai yaran nan asibiti, saboda yanayin jikinsu, mussaman ta farkon, duk zuwan matan nan ba sa gane su, sai ta wajen kukansu, ɗayar ba ta da kuzari sosai, amma ita chubaɗo tana kallon abinta take banbance su, ta san wadda ta fara haifa.
Sai dai da daddare ta kan ɓuya tayi kuka, dan har da wata dattijuwa, da take tayata kwana, tana tayata kula da jariran.
A haka tayi arba'in, a danginta dana Bashir babu wanda ya sani, shi ma kuma a can, matansa babu wadda ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 90 Chapter of 121