ka sha yau?"
"Wiwi"
Jauhar ta ce "Da me?"
Ya girgiza mata kai alamar babu.
"Ba ka saba ƙarya ba" ta saka yatsanta a bakinsa, ta ciro guntuwar ƙwayar da take ƙasan harshensa, laɓɓansa sun yi fari.
"Ƙwaya ko? Meyasa. Na ce fa idan an ɓata maka rai ne, ko kana cikin damuwa ka yi ta ambaton Allah, kana azkar, meyasa za aje a sha ƙwaya, ka ɓata mini shirina na yau gaba ɗaya"
Babu tsammani, ya miƙe da ita a jikinsa, ya tafi da ita ɗakinsa, rabi a buge yake, rabi a cikin hayyacinsa, yayi ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta ce "Ba zaka sumbace ni, da sauran ƙwaya a bakinka ba master, me aka yi maka?"
"Mhmmm bakomai, i need you"
Ta ce "A hakan, a buge fa ka ke"
"Ina hayyacina, kin yi mini kyau ne sosai" kasa hana shi tayi, ya gama ya cigaba da yi mata surutai.
Ta rungume kansa a ƙirjinta tana shafawa ta ce "Na san wataran zaka daina master, Allah ya shirya mini kai mijina"
"Madarata"
Ta ce "Idonka biyu"
"Mmm"
"Me zaka gaya mini?"
"In sha Allah zan daina, ki cigaba da yi mini addu'a" yayi maganar cikin muryar maye sama-sama.
"Addu'a kullum ina yi maka master, Allah ya nuna mini ka daina"
"Madarata"
"Master na"
Ya ja jikinsa, ya kai bakinsa saitin kunnenta, ta yi shiru, tana jiran ya yi mata magana.
Kawai ya fara murmushi, yana yi mata numfashi a kunne.
"Zaki koma makaranta"
"Allah ya ja zamaninka, godiya nake"
Cikin mayen ya sake cewa "Ki daina yawan kuka ba na so"
"To ka daina sakani"
"Allah ya bani kuɗi na kai ki makka"
"Amin Mijina, da alama ƙwayar nan nishaɗi take sawa"
"Ke ce nishaɗin nawa" yayi maganar yana dariya.
Ita ma murmushin ta yi masa, ya kwanta a gefenta, bacci ya ɗauke shi.
Da Asuba ya rigata tashi, ya tasheta shi kuma yayi wanka yayi alwala ya fita.
Da wani irin tashin zuciya ta tashi, kamar za ta yi amai, ta danganta hakan da awarar da ta yi wa cin ƙoshi jiya da daddare ulcer ta tayar mata.
A ɗakinsa ta yi sallar ta idar, idonta ya sauka a kan robar cocala da ke gefen katifarsa.
A take ta ji idan ba ta sha coke ɗin nan ba, akwai matsala.
Ta ɗaukko, ta buɗe ta kafa kai ta fara sha, sai da ta shanye tas, sannan ta ajiye jarkar, still ta din ga jin kamar za ta yi amai. Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki, ta yanke jiki ta faɗi, jini ya fara gangarowa daga hancinta.
Ayshercool
08081012143
41
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Al'amin a masallaci, magidanta suka tare shi suna ƙara bashi haƙuri, a kan abun da ya ce wa faruku tela.
Ya koma gida ya shiga ɗakinsa, yanayin kwanciyar da ya ga jauhar ne ya sanya ya tsaya yana kallonta.
"Wace irin kwanciya ce ki ka yi haka, ko baki da lafiya ne?"
Ya ga shiru ba ta motsa ba.
Ya ƙarasa gabanta, ya ɗagota, gabansa ya faɗi, ganin hancinta na ta zubar da jini, bakinta ma jinin ne yake fita haɗe da wata kumfa.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya furta cikin tashin hankali yana jijjiga jauhar.
Amma shiru ba ta amsa ba, ya ɗaga hannunta ya ga ya saki, ya kai hannunsa hancinta amma babu alamar numfashi a tare da ita.
"Jauhar, meya same ki haka? Meya sameki ne?"
Jijjigata yake iya ƙarfin sa, amma ba ta motsa ba, kawai idonsa ya sauka a kan robar cocala. Ya kai hannu ya ɗauka ta shanye komai tas.
A wurin Nura guduma ya ƙwace, ganin yadda ya haɗa uban ƙwayoyi a ciki zai sha, ya ƙwace ya ƙare masa zagi, ya ce idan yana wannan haɗin kashe kansa zai yi. Ya taho da shi gida ya ajiye a bayan katifar, ya kai kwana uku a ɗakin, shi ya ma manta da ita a ɗakin.
Da sauri ya ɗaukota ya fito da ita falo, ya kwantar da ita, ya fita da gudu, ya rasa wani gidan ma zai dosa, saboda ba shiga harkar mutanen layin yake ba, amma kasancewar a kiɗime yake, ya saka ya nufi gidan wasila, dan maigidan ya sai mota.
Wani irin mahaukacin bugu ya din ga yi wa gate ɗin gidan, ba shiri mijin wasila ya fito daga shi sai gajeren wando, ya buɗe yana rarraba ido.
"Ɗaukko mota matata babu lafiya" ya ce "To" dan a yanayin fuskar Al'amin ko ba'asi ya tsaya tambaya, bai san me zai yi masa ba.
Jin bugun gate ɗin, ya sanya wasu daga maƙwabtan su fitowa, su ji ko lafiya.
Mijin Wasila ya fito da mota, yanayin halin da ya fito da jauhar, ya sa gaba ɗaya jikinsu yin sanyi, dan babu alamar rai a tare da ita.
Mijin wasila ya ce "Bari ya taso matarsa a tafi da ita, asibitin"
Cikin ikon Allah suka yi wa Al'amin kara, mussaman da jauhar tana girmama su da jan yaransu a jiki, maƙwabcin mijin wasila ma ya shiga motar ya ce su tafi tare.
Asibitin da ya taɓa kaita aka buɗe mata file suka tafi.
Suna tafe yana girgizata yana ta tashi.
"Malam Al'amin ka yi haƙuri, ka daina jijjigata kar ka ƙara gajiyar da ita"
Al'amin bai bi takansa ba, ya riƙe hannun jauhar, "Dan Allah ko motsi ki yi Zahra, dan Allah ki tashi" su dai duk suka yi shiru, yanayin tashin hankalin da yake ta tattare da Al'amin ya ƙara bayyanar da tsantsar soyayyar da yake yi wa jauhar.
Suna zuwa Asibitin, Al'amin ya nufi emergency da ita, sai da aka bishi aka tambaye shi file numbern ta.
Mijin wasila ne ya biya kuɗin ganin likita, dan ba ya cikin nutsuwar da za a tambaye shi kuɗi.
Likita ya ce "Malam, meyasame ta?"
Al'amin ya rasa ta ina zai fara.
"Guba ta sha"
"Guba kamar yaya? Wannan ma ai kamata yayi sai an zo da 'yan sanda, ya aka yi ta sha guba?"
"Ka fara ceto mini ranta, duk wani bayani na yi maka daga baya, ka ceto rayuwar ta tukuna".
Likitan ya ce "Ai sai ka fara gaya mini meyafaru?" Ya juya kan jauhar, ya duba pulse ɗin ta, tana bugawa a hankali.
Aka samo bandage, aka toshe hancinta, saboda jinin da yake fita, aka ɗagota ƙirjinta a sama a kan gadon.
Likitan ya ce "A cire mata hijjabin nan"
Al'amin ya riƙe hijjabin, ya yi shiru.
Nurse ɗin ta ce "Malam ranta za a ceto, ka yi haƙuri"
Mijin wasila ya cewa maƙwabcinsa su fita.
Suka fita daga emergency, kayan bacci ne kawai a jikinta, doguwar riga iya gwiwarta.
Halin da take ciki, bai hana shi jin matsanancin kishinta ba, likita kuwa aikinsa kawai yake yi, zuƙe jinin da yake bakinta, da kumfar da take fita.
Sannan suka fara yi mata CPR, a hankali take ajiyar zuciya, zuciyarta na ƙoƙarin responding.
Wasila ta ce "Likita wani jinin na bin ƙafarta"
Wani likitan aka kuma kira, aka tafi da ita scanning room, nan suka ga akwai ciki, sai dai shi ma ya fita.
Al'amin ya rasa in da zai saka ransa, Nurses suna aikinsu, likitoci na nasu, aka ce Al'amin ya fita ya ce wallahi ba zai fita ba.
Haka aka din ga ɗaga jikinta, ana ƙoƙarin tsayar da jinin da yake fita ta ƙasanta, allurai kuwa tsira mata kawai ake yi, ban da wanda ake zuba mata a cannula.
Al'amin ya ji da ma shi tsautsayin nan ya faɗawa ba jauhar ba, ko a iya haka ta galabaita.
Sakamakon gwajin jini, ya fito jininta ya yi ƙasa matuƙa ana neman a ƙara mata wani.
Ya fita hankali a tashe, mijin wasila ya ce "Al'amin ya ake ciki?"
Idonsa jawur ya ce "Jini za'a bayar, ku bani aron waya dan Allah, na kira a kawo mini kuɗi, da kuma wanda za su bayar da jinin".
Ɗaya maƙwabcin na su hadi ya ce "Ai sun ce sai an yi depositing dubu hamsin za su ganta, mun je reception mun biya, yanzu jinin a fara dubawa a namu, ko za a dace".
Ya ce "To, amma a bani aron wayar dai, na yi kira".
Walid ya fara kira ya ɗaga da ƙyar ya ce "Maza"
"Kana ina ka nemo kuɗi ka zo asibitin da nake kai Ƴar madara cikin hanzari ba ta da lafiya"
Tuni Walid ya ware ya ce "Meya same ta?"
"Ka zo kawai".
"Gani nan"
Likitocin suka kira Al'amin, suka zauna da shi suna tambayar sa meyafaru da ita.
"Ƙwaya na ajiye a cikin cocacola ta ɗauka ta sha ba ta sani ba"
"Kwanakin baya fa, haka nayi ta counselling ɗin ka, a kan ka daina yi mata abun da yake saka jininta ya hau. Yau kuma ka bari ta sha ƙwaya wannan sakaci ne baka kyauta ba, idan ka yi silar rasa yarinyar nan, Allah ba zai barka ba"
Al'amin jikinsa yayi sanyi matuƙa.
"Ko ka san cewa tana ɗauke da juna biyu? Yanzu dai ciki ya zube babu shi, kuma a shawarce, idan Allah ya bata lafiya, yakamata tayi tsarin iyali, mahaifarta ta sake hutawa, dan ƙwayoyin sun yi wa jininta ƙarfi fiye da kima"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba zata sake ɗaukar ciki ba kenan?"
"A'a zata iya ɗauka, amma a shawarce, mahaifarta ta huta, dan ya yi affecting ɗin mahaifar, akwai buƙatar ta huta kan ta sake wani cikin "
Daga shi har jauhar babu wanda ya san da cikin, tsananin son da take yi wa yara, ya sanya ta mayar da boti kamar ɗan da ta haifa, dan ma kwanan nan ya hanata ɗaukko yaran mutane, tayi ta fama da su tana yi musu hidima.
Ya tashi jiki babu ƙwari ya fita, su Walid suka ƙaraso Asibitin, a kiɗime suka nufe shi "Mai zamani ina take? Meyafaru?"
Bai ɓoye musu komai ba, ya gaya musu.
Cikin tashin hankali Walid ya ce "Amma wallahi ɗan kutm..... Ne kai, wane irin hauka ne zai sanya ka ajiye abu in da zata ɗauka ta sha, kuma ba ka gaya mata menene ba? Ka san jikinta ba zai iya ɗaukar abun da yake ciki ba wannan ai hauka ne"
"Mai laya" yayi wa Walid tsawa.
Sai dai walid ya kuma narka masa ashariya ya ce "Ba za a kiyayeka ɗin ba, idan ka ji haushi ka saka mini ƙarfe, idan ta mutu kai ka yi asara, wannan ai ganganci ne da wauta"
Wata irin zuciya ta yinƙuro Al'amin, ya nemi ya huce takaicin sa a kan Walid, amma Walid ma ya hayyayaƙo masa, dan ba ƙaramin mutunta su Juahar take yi ba, yarinyar was very simple and innocent.
Security ne suka shigo, suna ƙoƙarin korar su Al'amin, suna nema su tayar da hayaniya a cikin Asibitin.
Liti ya kalli security ya ce "ko dai ka ƙyale su, ko abun ya ƙare a kanka"
Walid a fusace shi ma yake yi wa Al'amin martani "Saboda ka ga ba ta da baki, iyayenta ba tuhumarka za su yi ba, shi ne zaka yi musu ganganci da rayuwar 'ya, wallahi daga nan gidan su zan je na faɗa, idan ma kashe auren za su yi, su ɗauke 'yar su" Al'amin kawai yayi shiru, dan da makami a jikinsa sai ya yi wa Walid illa.
"A ina za a duba jinin?" Yayi maganar yana kallon Al'amin.
Yayi masa banza yaƙi magana.
"Wallahi sai dai ka fashe, gaskiya ce sai na gaya maka" ya ce "Liti zo mu duba ina ne za a ɗauki jinin".
Mijin wasila da suka koma gefe suna kallon sarautar Allah, suka gaya musu in da lab yake.
Ba a samu irin jinin Jauhar ba, sai dai sun bayar da jinin su leda biyu, aka tafi da shi babban asibiti, za a canzo da kalar nata jinin.
Suka shiga dudduba in da Al'amin ya shiga, aka nuna musu ɗakin da jauhar take.
Suka yi sallama suka shiga, an lulluɓe ta da green ɗin bedsheet, idonta a rufe hannunta biyu duka an saka mata ruwa.
Al'amin na durƙushe a gaban gadon, ya riƙe hannunta idonsa yayi ja, fuskar jauhar ta yi yellow sosai alamar ƙarancin jini.
Walid ya ƙarasa ya dafa kafaɗar Al'amin ya ce "Mai zamani, ka yi sakaci da wauta, amma ka kwantar da hankalinka in sha Allah za ta tashi, ka yi mata addu'a. Ba a samu irin jininta ba, amma mun bayar da jinin za a canzo, likita ya ce a kira ka"
Ya miƙe a hankali, suka fito, Walid yana ta cigaba da rarrashin sa, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ce "Wallahi ka ga dubu ɗari da hamsin aka samu, shi ma jarin kaya ne, na ɗebo su kawai, kuɗaɗenmu na hannun mutane, kana ganin za su isa kuwa?"
Al'amin ya haɗiye yawu ya ce "Ban sani ba, maƙwabcinmu ya bayar da dubu ɗari, sai a cire a bashi, in gani idan sauran za su isa".
Walid ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ka yi haƙuri za su isa in sha Allah, yanzu me ake buƙata kuma?"
Ya ce "Jinin dai muke jira a saka mata"
"To shikenan, zan je na sake lalubawa ko za a samu kuɗi, ka yi haƙuri ka nutsu. Amma dole a sanar da iyayenta"
Al'amin ya ce "Wallahi babu wanda ya isa ya rabani da matata, ka ma daina wannan tunanin"
"Nima ban ce a rabaku ba, haushi ka bani ne, Allah ya taimake ka, na kiyayi mai zamani" yayi maganar cikin sigar girmamawa ga Al'amin.
Al'amin ya daki kafaɗarsa ya ce "Get out"
Yayi murmushi suka fita da liti.
Mamaki sai da ya kama mutanen da suka gansu suna faɗa ɗazu.
Al'amin ya bawa mijin wasila kuɗinsa, amma ya ce kyauta ya biya ba sai an biya shi ba.
Babban burin Al'amin bai wuce ya ga ta farka ba, da ya tuna abun da aka ce na game da mahaifarta sai ya ji ya tsani kansa, sai kokowa yake da zuciyarsa yaƙi bari haushin Nura guduma yayi tasiri a zuciyarsa.
Wasila ta koma gida, ta dafo musu abinci ta dawo asibitin.
Har la'asar Al'amin ya rasa nutsuwa, aka kawo jini aka saka mata.
A gigice Nura ya zo asibitin jin abun da ya faru, sai dai ko kallonsa Al'amin ya ƙi yi.
Ya rasa in da zai saka kansa, mussaman da ya ga juahar a kwance ana saka mata jini, duk da tsananin kishi irin na Al'amin, Nura yana good time da jauhar, mussaman yake zuwa idan tana da aike, ya karɓa yayi mata, har kasuwa yake zuwar mata, sayen kayan beads da stone work.
Ta dafa abinci ta bashi, duk da yaron mijinta ne, kuma tana aikensa, hakan bai hanata girmama shi ba, da yi masa nasiha wasu lokutan.
Ganin shi ne sila, a ƙoƙarin hana shi illata lafiyar sa da Al'amin yayi tsautsayi ya faɗa kanta, ya sanya ya koma gefe yana kuka, saboda ya firgita da yanayin da ya ganta kamar gawa.
Al'amin cikin tsawa ya ce masa ya fita ya bashi wuri.
Nura ya fita wajen ɗakin ya tsaya cikin damuwa.
Al'amin ya je gida, ya bar jauhar da wasila, ya je ya yi wanka, ya ɗaukko mata kayan da za a canza mata.
Sai bayan sallar magariba ya dawo, ya tarar da Baba tare da mama Anty zakiyya da kuma saifu a ɗakin, wasi ta goge mata jikinta, da taimakon Nurses ta saka mata kaya.
Tsayawa yayi yana kallonsu, yana tunanin ma a ina ya san su.
Sai daga baya, ya tuna Baba, ya durƙusa ya gaishe shi, ya amsa masa tare da faɗin ya mai jiki.
Ya amsa da "Da sauƙi" yana tunanin me Walid ya je ya gaya musu.
Baba ya ce "Meyafaru ne? Wani ya je ya ce mana abokinka ne shi, wai ka turo shi an kwantar da jauhar a asibiti, hankalinmu duk ya tashi"
Al'amin ya ce "Ɓari ta yi"
Anty ta ce "Amma shi ne aka je aka ɗaga mana hankali, ni wallahi na zata wani abun ne ya same ta ma".
Mama ta ce "Duk da haka, tun da aka kai ga ƙarin jini tana jin jiki, Allah ya sa ba wani abun ne ya faru ba tayi ɓarin"
Al'amin bai ce komai ba, ya ajiye kayan hannun sa, dai-dai lokacin Jauhar tayi wani yinƙuri zata faɗo daga kan gadon tana kiran "Master kana ina?"
Cikin hanzari ya ƙarasa gaban gadon, suna rige-rige da shi da Saifu.
Yayi hanzarin riƙe ta ya ce "Zahra"
"Master"
"Na'am sannu"
"Meyasame ni ne? Kaina fa zai tarwatse ciwo master"
Babu kunya ya rungumeta ya ce "Zai daina, ki daina ɗaga muryarki"
Cikin kuka ta ce "Master bana gani, duhu nake gani bana ganinka" tayi maganar tana tittirza ƙafarta a kan gadon.
Ya ce "Zaki ganni in sha Allah, ki daina magana"
Al'amin ko a jikinsa, ya ttatara hankalinsa a kanta, Baba ya ce "Waliyiyya, sannu kin ji"
Ta ce "Baba"
"Na'am jauhar"
"Baba kai ne ka zo bana ganinku, duhu nake gani, makancewa na yi?"
Saifu ya ce "Baki makance ba, bacci ki ke ji, ki yi shiru"
"Yaya saifu, bana gani fa"
Saifu ya ce "Bacci ki ke ji ne"
Cikin fita hayyaci ta ƙanƙame Al'amin ta sake cewa "Master"
"Na'am madarata"
"Kaina zai fashe, ka riƙe mini shi da ƙarfi, marata ma ciwo take yi mini sosai" tayi maganar numfashinta yana fita sama-sama.
Yayi ƙasa da muryarsa yana yi mata raɗa ya ce "Kina jina" ta ɗaga masa kai.
"Ki daina magana, ki yi shiru baki da lafiya"
"To meyasame ni?"
"Zazzaɓi ki ke yi"
Ta ce "To, ka je sallar asubar ne?"
"Na je mana, har na yi mana addu'a"
"To ka riƙe kaina da ƙarfi ka yi mini addu'a, jikina ma kamar an jona mini shocking nake ji"
Nurse ɗin da ta shigo ta ce "Malam ya ka ɗagata ana ƙara mata jini, so ake ta kwanta"
Mama ta ce "Faɗowa zata yi daga kan gadon, fizge-fizge take yi"
Nurse ɗin ta ce "Kwantar da ita, sai ayi mata allurar bacci"
Ta rirriƙe Al'amin ta ce "Kar ka ajiyeni, idan na kwanta bana iya numfashi".
Al'amin ya ce "To shikenan, ba zan kwantar da ke ba"
Anty Zakiyya ta ce "Wannan wane irin ɓari ne, zai saka mutum yayi ta surutai kamar mahaukaci?".
Nurse ɗin ta kalleta ta ce "Jini ta zubar sosai da sosai, dan haka jikinta yayi weak, alluran da muke yi mata kuma, sune suke burkita ta, dan haka ba abun mamaki bane ba".
Al'amin yayi ajiyar zuciya, jin yadda Nurse ɗin ta rufe musu ainihin abun da ya faru.
Ita kuwa tayi hakan ne, dan tausayin yadda tun da ya kawo jauhar yake ɗawainiya, ko da ganganci a lamarin yayi nadama.
Sai wurin sha daya suka tashi za su tafi, dan bayan allaurai ƙarancin jini ya saka ta fara haki, athma kuma ta tashi, sai da aka sakata a kan oxygen.
Sai dai daga baya ta zama stable, baba ya din ga yi mata addu'a kan su tafi ya ce tsakanin mama ko Anty Zakiyya wani ya kwana da ita Al'amin ya je gida.
Al'amin ya ce "A'a baba, zan kwana da ita ba wani abu" dama yanayin fuskarsu ya nuna ba su yi niyya ba.
Baba ya din ga yi masa addu'a, sannan suka tafi.
Har suka je gida, suna mamakin kulawa da tashin hankalin da suka gani a tatatare da Al'amin.
Su Walid ma a reception suka kwana, da an ce a nemo abu, za su fita su sayo, shi kuma yana tare da ita yadda ya ga rana haka ya ga dare.
Lokaci -lokaci tayi ta surutu, duk a dalilin mugun ƙarfin da ƙwayoyin suka yi mata.
Daf da asuba ta sake farkawa, sai dai ba ta zaburar, wannan karon tana gani, sai dai daga kwance ma jiri take yi.
"Master" ya ɗago daga kifa kan da yayi, ya ce "Sannu zahra ya jikin?"
"Alhamdilillah, jiri nake ji".
"Ki yi haƙuri, kin ga jini ake ƙara miki. Zaki daina ji in sha Allah, sannu" yayi maganar yana shafa kanta, yana yi wa Allah godiya da ta farfaɗo.
Da sassafe Nura ya sake dawowa, har da guzirin bredi da madara da suga, ya dawo sake duba Jauhar, amma al'amin ya kore shi.
Liti ne ya dawo da shi ya ce "Haba maza, Nuranka ne fa, waye ba ya kuskure? Kar ka yi masa haka dan Allah, kuma sakacin naka ne ba na sa ba, daka karɓa kamata yayi ka zubar ai, dan Allah ka yi haƙuri"
Nura har da kuka ya ce "Dan Allah yaya Aminu ka yi haƙuri, dan Allah wallahi ban ji dadin abun da ya faru ba"
Daga kwance ta ce "Master, laifin me ya yi ka ke korar ƙaninka, ayi haƙuri dan Allah, kalli ka saka yana kuka"
Al'amin ya ce "Ki daina magana kar hakin ya dawo"
"To ka ce masa ka haƙura, ka ga kuka yake yi"
A hankali ya furta"Ya wuce"
"Yauwwa mai zamani, Allah ya ja zamanin maza" tayi maganar tana ɗaga hannunta da ƙyar ta taɓa fuskarsa.
Cikin jin daɗi yadda take ƙarfin hali, yayi murmushi ya ce "Ban hana ba?"
Murmushi ta yi masa ba ta ce komai ba.
Da nurse ta shigo ta tarar da ita, tana magana, ga su liti a gefe ta ce "Zahra gawa taƙi rami, sannu kin ji"
"Yauwwa Anty na gode "
Ta kalli Al'amin ta ce "Congratulations, na tayaka muranr farfaɗowarta, dan wallahi mun sare bamu zaci zaki tashi ba"
Walid ya ce "Sannunku da ƙoƙari, Allah ya biya ku"
"Amin, bari mu gyara mata jikinta, a bata abinci " su liti suka fita, ya taimakawa nurse ɗin, ta gyara jauhar, ta zaunar da ita, duk da tana ta kuka da jiri da ciwon kai da na mara.
Ya haɗa mata shayi, da buredi, sai dai ta kasa ci, sai lallaɓata yake yi.
Wasila tayi sallama, suka amsa.
Ta ce "Alhamdilillah anty jauhar jiki yayi kyau, ikon Allah"
Nan suka ƙara gaisawa, ta ajiye abincin da ta zo da shi, jauhar ta ce za ta sha kunun gyaɗar da ta kawo.
Ana haka su Baba suka zo, suka tarar da Al'amin yana ba ta abinci an zaunar da ita.
Gab ɗaya zamansu a wurin, bai hana shi tattalin matarsa ba, dan gani yake yafi kowa sa'a farfaɗowar da ta yi.
Babban abun da ya yi wa jauhar daɗi, bai wuce ganin 'yan gidan su, sun zo dubata ba, ko ba komai sun nuna damuwar su da ita.
Duk saifu na ta zuga Baba ya bi diddigin yadda aka yi tayi ɓarin, ko dukanta Al'amin yake yi, amma yanayin yadda suke mu'amala ita da Al'amin ya sanya kowa yin wani tunanin daban, dan saɓanin abun da ake tunani ake gani.
Har Abbu sai da ya zo duba jauhar, su shahida ma duk sun zo, Baba sai da ya yi ta yi wa wasila godiya da Addu'a, tana ta ƙoƙari da jauhar, maƙwabtan su ma na ta zuwa dubata.
A kwana na uku, da daddare take tambayar Al'amin "Master wai dan Allah meya same ni ne? Na san kawai na ga lemo a ɗakinka na sha, daga nan ban san meyafaru ba, kuma na ji ana cewa nayi ɓari, ya aka yi na yi ɓari ai bani da ciki, ko kuma ina da shi ban sani bane? To yaya aka yi ya zube?"
"Ki yi haƙuri, likita zai yi miki bayani in sha Allah"
"To kai ka yi mini mana, wai shikenan babyn yanzu babu a cikina" tayi maganar tana shafa cikin ɗauke da damuwa.
"Ni likita ne?"
"A'a amma ka gaya mini, haryanzu ina da cikin?"
Al'amin ya ce "Wai abun da baki san da shi ba ma, zaki bi ki damu, ki yi haƙuri za su yi miki bayani"
Ta ce "To shikenan, yi mini addu'a na yi baccin".
Ya ce "To"
Gari ya waye, su surayya ma suka zo dubata, saifu ya kawo su, take tambayar ina yaya hafsa, aka ce mata ta tafi umara.
Jauhar ta ce "Dan Allah ku ce ta yi mini addu'a sosai da ni da master"
Suryaya ta ce "Wai ke kowa na gaya wa miji sunan 'yan gayu ke kina master"
Tayi murmushi ta ce "Baki ga mastern ne ba? Kuma ai mu ba 'yan gayu bane"
Kasancewar Al'amin ba ya ɗakin ya sanya saifu cewa "Ke, ki faɗa mini gaskiya, wani abun yayi miki ko?"
Ta ce "A'a me ka gani?"
"Wallahi ki ka rufa masa asiri sai kin daku, har likita na saka baba ya tambaya, ko dukanki yayi ya ce babu alamar duka a jikinki da aka kawo ki"
Jauhar ta ce "Master ba ya duka, bai taɓa dukana ba".
"Na san halinki da shegiyar gwaninta ne, da kare mai laifi ki gaya mini gaskiya"
"Wallahi babu abun da ya yi mini"
Dawowar Al'amin ya sanya su yin shiru, ya ƙarasa gaban gadonta ya ce "Me zaki ci?"
"Bakomai, kawai a sallame ni"
Ya zauna a gefen gadon ya ce "Ba na son rigima, wace irin sallama kuma?"
"Kai ka koya mini ai, kai fa har guduwa ka ke daga asibiti"
Yayi murmushi ya ce "Zaki gudun kenan?"
Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kashe kuɗin yayi yawa, ina iya tashi ai"
Rarrashin ta ya din ga yi, dan shi kansa ya san zaman asibiti da gundura.
Sai da ta kwana shida, an saka mata jini ya kai leda biyar, sannn aka fara zancen sallamar ta ranar.
Daga likitan sai ita da Al'amin a ɗakin, yayi mata bayanin abun da ya faru, tare da gaya mata akwai buƙatar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 121