Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
21 / 121
sayo musu buredi. Suka sayo, suka zauna, suka ci tare da su, ta ajiye wani da niyyar idan mai gidan ya zo ta bashi. Mama kuwa bayan sun koma gida daga kai jauhar, duk 'yan biki sun watse, kowa tayi ta kanta. Suka ƙule a ɗaki ita da zakiyya ta ce "Zakiyya duk da gidan yarinyar nan babu gyara, amma yayi kyau sosai da sosai" "Eh ai hakan yayi, ma rage wani surutun, har ku ka taho kuwa kun ganshi ya je gidan shi angon?" Mama ta ce "Ina fa, itakaɗai muka baro, sai wasu 'yan uwan babarsa, su ma na san ba zasu jima ba zasu tafi ba. Nifa sunansa kawai nake ji, ban taɓa ganin sa ba". "Zaki ganshi ne, ba dai ya zama sirikinku ba? Ni na san shi, amma lokacin yana yaro, ai kin san daga baya suka dawo ƙofar na'isa da ba a nan suke ba, ni tsoro nake ji ma kar yaran nan su cigaba da kawo mana farmaki" Mama ta ce "Babu abun da za su dawo su yi mana, mun yada ƙwallon mangwaro mun huta da ƙuda, yanzu menene abun yi?" "Abun yi, shi ne mu jira dawowar wannan Alhajin, mu ga yadda za a ɓullowa lamarin ya haƙura gaba ɗaya da batun ta" "Haka ne, to Allah ya dawo da shi lafiya, sai ayi ta ta ƙare, jauhar dai an aurar da ita, sai mu jira mu ga yaya zai kasance da namu 'ya'yan. Gidan jauhar magariba na yi, yara suka watse suka bar ta itakaɗai kamar tsohuwar mayya. Sai fitila ta kunna, ta saka mayafinta ta din ga korra sauro daga ɗakunan, saboda yadda suke ambaliya kamar a barikin su. Ta rurrufe ko ina, tana jiran ta ga ta ina ango zai shigo, amma shiru. Har bacci ya kuma cin ƙarfinta ya kwashe ta. Wunin ranar kuwa, Al'amin zarya ya din ga yi, sai da aka sakar masa yaransa da aka kama a unguwar su madaki, har suka sanar masa iƙrarin da 'yan unguwar da suka yi, na idan suka kuma ganinta a unguwar sai sun sassarata. A ransa ya ce Allah ya ƙara, maganinsu kenan, da suka ga babu wanda ya dace su bawa 'yar su sai shi. Tare da su ya wuni yana shaye-shaye, Walid ya na son ya yi masa magana, amma ya san yana yi za su yi faɗa, dan haka sai dare ya sake lallaɓa shi, daga can unguwar ya goya shi a babur ya kai shi gidansa na ɗorayi chiranci. Sai dai kamar jiya, kafin gari ya yi haske, ya sake barin gidan, gashi ko brush ba ta da shi, ba ta da kayan girki, haka ta kuskure baki ta cinye biredin jiya, gashi ba ta son cigaba da taɓa kuɗin da aka bata, yakamata ta nuna masa kayan da aka bata, saboda 'yan uwan sa ne suka bata. Ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan tudu ta zauna, tana tunanin yanzu haka za ta rayu, wanda ya ajiye ta baya ko ƙaunar ganinta, kwana na biyu kenan haryanzu ba ta ga kalarsa ba ma. Tana son yin wanka da sauran buƙatu, amma ba hali, babu ruwa, ga rijiya a gidan amma babu guga, babu sauran kayan masarufi. Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ya dawo da ita hayyacinta, ta tashi ta ɗaukko mayafi ta saka, ta buɗe a hankali. Saifu ta gani a tsaye, hannunsa riƙe da kaya. Ta washe baki ta ce "Yaya saifu" yayi murmushi ya ce "Na'am Waliyiyya" Ta bashi hanya ta ce ya shigo, ta karɓi kayan hannunsa, suka shiga har falo. Ya kalleta ya ce "Yaya babu wata matsala dai ko?" Ta girgiza kai ta ce "Babu" "Ina mijin naki yake?" "Baya nan, ya su baba? Ya su mama?" "Suna nan ƙalau, gida yaƙi kyau ba kya nan, duk 'yan matan nan an rasa wadda za ta yi aikin da ki ke yi" tayi shiru tana murmushi. "Ga sauran kayanki na kawo miki, na harhaɗo da na ɗakinki duk na kawo miki, muddin ki ga ya yi miki wani abu da baki gamsu ba, ki gudo gida kin ji ko?" Ta jinjina masa kai alamar to. Ya ce "Kina buƙatar wani abun ne?" Ta ce "A'a" Ya miƙe ya ce "Na san ba zaki faɗa ba ai" ya shiga kitchen ɗin ta yana dubawa, babu alamar an dafa wani abu. Ya ɗauki gas ɗin ta, ya fita da shi, ya yo mata refilling, ya yi mata sayayyar kayan shayi da 'yan kayan abinci, ya dawo ya kawo mata. Ya ce "Ki yi haƙuri jauhar, bani da kuɗi, amma zan sake dawowa in sha Allah, kar ki yadda da wani haƙuri, na san zaman aure haƙuri ne, amma kar ki zauna ana zaluntarki, ko ya ce zai dake ki, zan sake dawowa in sha Allah kin ji ko" ta ɗaga masa kai alamar eh, ya sayo mata guga, ya janyo mata ruwa ya tara mata, ta din ga yi masa godiya suka yi sallama. Bayan tafiyar sa, tayi wanka ta canza kaya, yaran maƙwabtanta da suka shgo, ta dafa musu taliya, suka ci ba ta gaza ba, ta ɗebarwa maigidan nasa ta ajiye. Sai dai yaran da wuri suka tafi yau, ta samu wuri tana wanke-wanke, ta ji kamar an wuce ta bayanta. Tashi ta yi a firgice, tana addu'a da tunanin ko gane-gane ta fara yi. Sai dai ta ga takalmi a ƙofar falon, kasancewar gidan akwai gate, kuma akwai ƙaramar ƙofa, ƙofar a buɗe take. Ta lallaɓa ta leƙa, ba ta ga kowa ba, ta shiga falon tana tambayar waye?. Fitowa ya yi daga ɗaya ɗakin, hannunsa riƙe da baƙar leda, kallo ɗaya ta yi masa ta gane shi, ƙwala ihu ta yi, ta ruga da gudu ɗakin da gadonta yake, ta rufe ƙofar ɗakin. Ayshercool 08081012143 21 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya taɓa ganin fuskarta. A ransa ya ce "Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki" ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice. Jauhar kuwa durƙushewa tayi, ta ɗora hannunta a ka ta ce "Na shiga uku" a take ta fashe da kuka ta ce "Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ƙangin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba". Ta cigaba da addu'ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ƙara sakata da ta yi a ɗakin tana kuka. A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa riƙe da mutum da wuƙa a gefen cikinsa. "Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba" tayi maganar ƙasa-ƙasa tana kuka. Ko da wasa ba ta yi yinƙurin, sake buɗe ƙofar nan, a banɗakik nan tayi alwalar magariba da ta isha'i, ta kasa addu'a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba. Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye. Zaman ɗakin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta leƙa ta ga babu kowa a falon, bakinta ɗauke da addu'a ta fito. Ba kowa, ta leƙa tsakar gida, ya rufe mata ƙofar, babu taklmansa kuma a wurin. Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ɗan zube a ƙasa bai kwashe ba, jug ɗin ma daban kofin jug ɗin daban. Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan. Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu'a Allah ya ƙara nesanta ta da shi. Ta yi 'yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ƙadangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro. Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga. A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice. Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai. Wajen la'asar ta ji ana buga ƙofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru. Har zata haƙura da buɗe ƙofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ɗin maimakon ƙofar da ƙarfin gaske. A tsorace ta buɗe, aikuwa ya hankaɗo ƙofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ƙofa. Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice. Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata. Cikin kuka ta ce "Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata". Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ƙoƙarin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ƙara rikita ta. Suna dabarsu, Al'amin yana ta shan sigari, Walid ya ce "Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?". Al'amin ya rausayar da kai ya ce "Yarinyar Mahaukaciya ce ashe" Cikin rashin fahimta ya ce "Mahaukaciya kamar yaya?". "Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itakaɗai" Walid ya ce "Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?" Aminu ya ce "Da wa?" "Da amaryar mana" ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa. "Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya " Yayi masa shiru, yaƙi ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi. Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake haɗa shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba. Sai dai sun fara zancen a kawo 'yar aiki, dan duk yawan 'yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ɓatawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa. Baba kuwa ƙasan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya duƙufa yana yi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta. Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ɓarawo. Gaba ɗaya jauhar a zatonta, itakaɗai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ƙofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ɗora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu. Ta fara bin ɗakunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin. Kawai ta nufi ɗakin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita kaɗaice a gidan. Yana kashingiɗe yana zaune yana kaɗa ƙafa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ɗakin, ghana must go ɗin, ya cillar da ita a tsakar ɗakin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar. Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina. Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ɗiba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin da ta shiga, ya hankaɗa ƙofar ta faɗi jikinta na wata irin tsuma. Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro. Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi. "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi haƙuri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida" tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta. Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya taɓa ganinta. "Kin ganni na kashe shi?" Ta jinjina kai alamar eh. "Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya. "Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki" Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta. Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba. Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ɗakin da ta gano shi. Ɗakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buɗe dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ɗakin yake yi. Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta. Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ɗauki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ɗan ɗebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana. Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da 'yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi. Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ɗaya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan. Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata. Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su" Ta ɗan yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuɗin da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji. Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa. Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba. Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu. Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni". "Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana". Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni". Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?" Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?" "Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?" Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga ɗebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi" Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman kuɗi". Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka" Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan buƙatu. Jauhar ta ji daɗin hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi. Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai. Ta ɗebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ɗebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta. Tana aikinta, tana jin radiyo a mp. Ta bawa yara kuɗi, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi. Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo. Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi. Ba ya falo, ta shiga ɗaki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ɗakin da yake. Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banɗakin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa. Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba. 'yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama. A fusace ya ce "Meye ne?". Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka" Ɗan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daɗi da bai haɗu da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta. "Ga kuɗin" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi. "Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "Kuɗin fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ɗakin. Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuɗin, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo. "Kwashe kuɗin nan ki bar nan" jiki na rawa, ta ɗauka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ɗakin. Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi. Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba. Maimakon ya ɗebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buɗe flask ɗin, ya juye salad ɗin a ciki, ya ɗaga flask ɗin miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma. Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ɗaya, ɗaya kuma ta zuba masa ruwa. Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata. Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan. Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba. Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faɗuwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba. Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ɗaya, dama taliya leda guda yake cinyewa. Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ɗin ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin. A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet ɗina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta ɗebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ɗakinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar. Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba. Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke. Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta. Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce "Waye" Ya amsa da "Ni ne" ta saka mayafi, ta fita ta leƙa. Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al'amin ba ba. A ɗan tsorace ta ce "Sannu" Ya ce "Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?" Ta ce "Eh meyafaru?" "Ɗan je ki ce mata ana sallama da Boss" Ta yatsuna fuska ta ce "Waye hakan?" "Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?" Jauhar ta ce "Ba wani mai

Chapter 21 of 121