Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
102 / 121
mini. Shikenan dai makomar ɗan shaye-shaye ko ɗan daba. Ko ka kashe ko a kasheka, ko a kashe maka wani makusancinka, da zai bar maka mummunan tabo a zuciya, babu riba sam a wannan harkar". Ta gyaɗa kai ta ce "wannan haka yake, amma ka godewa Allah da ya sanya ka farga da wuri, har ka ke ta ƙoƙarin tuba ga Allah, ina fatan Allah ya karɓi tubanka" Ya amsa da "Amin ya Allah, kuma kema ina yi miki godiya sosai Abla, kema kin bayar da gudummawa sosai da sosai a cikin rayuwata, kamar yadda sisternki jauhar ta yi mini, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi" Tayi murmushi ta amsa da Amin, duk wannan basar da abubuwan da yake yi, ashe yane sane da duk alkhairin da ake yi masa. "Amm ya maganarmu ta zuwa asibiti, me ka yanke a kai?" Ya jinjina kai ya ce "Zani in sha Allah" Faɗaɗa murmushinta ta yi, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, amma na yi murna na ji daɗi sosai da sosai, Allah ya tabattar da alkhairi" "Amin" "To menene next, idan an kammala shari'a, sannan ya zamu yi da batun indabo? Shi Shikenan ya ci bulus kenan, idan aka hukunta su madaki shikenan?" Al'amin ya haɗiyi yawu, ya ce "Shi wannan iya jarrabawar da yake ciki ta ishe shi, ko iya yanzu ya san tasa ta ƙare, akwai jarrabawa a rashin mulki, tarwatsewar iyali kamar yadda na fuskanta. Bore daga magoya baya ga karayar arziki an kama kayansa a ƙasar waje da yaransa, ga tuhuma da yake fuskanta a cikin gida da sauransu, bana buƙatar wani ya hukunta indabo ni ne zan hukunta shi" Ta waro ido ta ce "Dan girman Allah mun kusa zuwa gaɓar ƙarshe, kar ka mayar da mu baya ka ɓallo mana wani babban aikin dan Allah". "Haba akwai bambanci tsakanin Al'amin ɗan daba da kuma jami'in tsaro, na san abin da nake yi, ki kwantar da hankalinki" Nabila ta ce "Anya kwanciyar hankalin nan kuwa?" "Trust me mana" yayi maganar yana murmushi. Ranar Litinin, Nabila da Viper da rakiyar Sumayya, suka kai Viper Asibitin ƙwaƙwalwa, domin ya ga likita. Ba su wani sha wahala ba, ya samu dukkanin kulawar da yake buƙata, hatta history na yadda ya fara shaye-shaye, sai da suka yi wa likitan bayani, aka tura shi yin wasu gwaje-gwaje. **** Kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, wasu daɗi wasu akasin haka, ana tsaka da alhinin mummunan kisan gillar da aka yi wa Abba, Rahila ba ta gama dawowa dai-dai ba, aka sake sanar da ita, an kama Nazifi a Lagos, tare da manyan 'yan fashi, hakan ya ƙara tunzura nutsuwar ƙwaƙwalwarta. Kwanci tashi asarar mai rai, aka sake shafe watanni guda curr, Ramma kullum cikin lissafi take, yaushe Abdul zai fito daga tsaren da yake. Yau kotu ta fi ko yaushe cika, ana jiran hukuncin da kotun zata yanke. Ƙarar su Viper ce ta uku da aka kira, bayan dogon rubuce-rubuce da Alƙali ya yi, da bayanai ya shiga karanto hukuncin da za a yanke wa su Lakwari. Shekarun ɗaurin rai da rai, kowannensu, sannan kotu ta yi umarnin a cigaba da binciken in da sauran waɗanda su ka tafka ta'asar tare suke. Wata irin ajiyar zuciya Nabila ta sauke, hawaye suka din ga zuba daga idanunta, ba zata taɓa manta wannan rana ba, domin kuwa wannan ita ce mafi ƙololuwar nasara da ta samu. Viper ma sunkuyar da kansa ya yi a wurin, hawaye ya kasa barin idanunsa, duk da Madaki yana can gadon Asibiti, bai san ma waye a kansa ba. Ana gama yanke hukuncin ta yi waje, da Sumayya ta fara arba, suka rungume juna, Nabilan sai kukan farinciki take yi. 'yan jarida ne suka baibaiye ta, suna yi mata tambayoyi, amma Sumayya ta ce su ƙyaleta ba ta cikin nutsuwarta. Walid ne ya fito tare da Viper, yana ta rufe fuska da handkerchief, babu abin da yake iya sanya shi hawaye a take, sai tuna jauhar, 'yan jarida shi ma suka yo kansa, amma ya rufe fuskarsa, Liti ya ce "Ko me zaku tambaya ku tambayeni, ba zai iya magana ba" "A'a da shi muke son yin magana" "To ba zai yi ba, munafukai kamar baku ku ka din ga zuzuta lamarin baz da faɗar ƙarya da gaskiya, wallahi idan ba ku bi a hankali ba, sai aikin nan ya kai ku wuta, saboda yaɗa fasadi da sharrin da k... "Kai liti wai waye ya tambayeka ne?" Walid ya dakatar da shi. Baba yana tsaka da rarrashin Nabila, ta daina kukan da take yi, ya ga Viper ya fito, ya nufe shi, yana zuwa ya rungume shi ya na "Ina tayaka murna Aminullahi, Ubangiji Allah ya wankeka yau, ni dama na faɗa ba zaka iya kashe mini jauhar ba, Allah ya yi maka albarka". Abbu yayi tsuru daga gefe, yana son yin magana, amma ya kasa wata irin kunya ta mamaye shi. Alhaji mu'azzam ma gefe ya koma yana murmushi, amma bai tunkari in da Viper yake ba. Viper ne da kansa ya tunkari in da yake tsaye, ya je gabansa ya miƙa masa hannun sa. Sai da Alhaji mu'zzam ya waiwaya, ko ba shi yake miƙowa hannun ba. Ya ga dai shi yake bawa hannu, ya miƙa masa hannu suka yi musabaha. Viper ya rungume shi, ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gode, ina sane da dukkanin gwagwarmaya da ka yi a kaina, duk dan saboda soyyayar da ka ke yi wa jauhar, da kuma ƙoƙarin ɗaukar fansa ta hanyata. Ka yi amfani da ni, ka cimma burinka, ba butulu ba ne ni, da na rintse idanuna daga kallon abin da ka ke yi mini, ina matuƙar kishin matata ne. A karo na babu adadi, ina mai sake baka haƙuri, ka yi haƙuri da Nabila kamar yadda jauhar ba ta kasance taka ba, Nabila ma haka, mussaman da ake barin halak dan kunya, a wannan karon ma ita ma ɗin tawa ce. Na gode sosai da gudunmuwar ka". Alhaji mu'azzam kawai ya yi murmushi ya ɗan daddaki bayan Viper ya ce "Ina tayaka murna, maganar Nabila kuma, ba a sanin ma ci tuwo, sai miya ta ƙare". Nabila kuwa hankalinta ne ya kai kan Naja'atu Bunkure da take yi wa 'yan jarida bayanin cewa, za su ɗaukaka ƙara. Ta gama bayanin ta nufi motarta, Nabila ta nufi in fa take, Sumayya ta riƙe ta, amma ta fizge ta nufi Bunkure. Ayshercool 08081012143 96 Tsayawa Bunkure ta yi cak, tana jiran Nabila ta ƙaraso, Nabila ta ƙarasa gabanta tana wani irin huci, kamar fusatacciyar damusa. 'yan jarida na ganin haka, abin nema ya samu, yuuuu suka ɗiba suka nufe su, da abin magana da camerori. "Ina fatan yanzu kin tabattar da jinin 'yar uwata ba zai taɓa tafiya a banza ba? Kuma matsayin da ki ke taƙama da shi, ki ka ce ba zan taɓa taka shi ba, ashe ba matsayin ba na arziki bane ba, na gode Allah da ki ka haska mini ko ke wacece, ban ci gaba da yi miki makauniyar soyyaya ba. Abin alfahari shi ne kayi amfani da damar da Allah ya baka, wurin kyautata wa mutane, yadda ko bayan ranka zaka yi alfahari da hakan, ba yin mugunyar shuka ba, da sharrinta zai ta bibiyarka har bayan ranka ba. Na ji ki na iƙirarin ɗaukaka ƙara, to baki da wannan lokacin, ga copyn ƙorafin da zan shigar a kanki nan, ga hukumar shari'a, kuma ina fatan ta soke lasisinki da na ƙungiyar ki, ta ƙwatowa al'umma hakkinsu da ki ke dannewa, ta hanyar rufe kura da fatar akuya, ki na kare yaran masu kuɗi, kina tozarta masu ƙaramin ƙarfi. Bakk da lokacin ɗaukaka ƙara, zai fi kyau ki mayar da hankali a kan yadda zaki karenki" Nabila ta dangwara mata wani file, tare da yi mata kallon banza. Tabbas tarihi ya maimaita kansa, domin kuwa sowa aka ɗauka da tafawa Nabila, yayin da ta bar Bunkure baki buɗe ta rasa abin cewa, ƙanƙanwar bayanta, da da auren wuri tayi, da ta kusa haifar Nabila, duk yadda ake girmamata kamar wata abar bauta, ita yau Nabila ta dizga kuma ta kayar a shari'a, wani malolon takaici ya ƙuleta, ta watsar da File ɗin, za ta shige cikin mota. Wani abokin aikinta ya ce "Kul, kar ki yar ki tafi da shi ki je ki duba, ki ga ta ina zaki ɓullowa lamarin". Nabila kuwa wurin Barrister Habib ta waiwaya, da ya kammala wata Shari'a ya fito, yana ta yashe mata baki, "Congratulations our legit barrister" Cikin murmushi mai haɗe da farinciki, ta ce "Na gode barrister, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Har duniya ta naɗe ba zan manta da kai ba, a lokacin da yan uwa abokan aiki suke yi mini kallon mara hankali, na ɗaukko dala babu gammo, ka tsaya tare da ni, tare da bani ƙwarin gwiwa da gudunmawa ta kowacce fuska" Yayi murmushi ya ce "Honorable Mu'azzam Wada kankarofi shi ya dace ki yi wa wannan yabon, duk ƙoƙarin sa ne ya kawo haka" Ta dubi Alhaji mu'azzam ta ce "Honorable, ban san me zan ce maka ba, sai dai ina fatan idan kujerar sanata alkhairi ce a gareka, Allah ya baka, ina kyautata maka zato, halacci da taimakon da ka yi mana, Ubangiji Allah ya shaida ya kuma biyaka, bamu da baki, ko wani kalami da zamu yi amfani da shi, da zamu yi gamshashshiyar godiyar da za ta wadaci hidimar da ka yi mana, mun gode sosai da sosai" "Babu komai Nabila, yi wa kai ne, kun cancanci hakan ne, daga ke har Al'amin" Walid ya ce "Shikenan Alhamdilillah, zaman rami ya ƙare, mun yi 'yanci, kumurcin cikin rami zai yi yawonsa freely a gari, Allah ya sa kuma kar ya addabi al'umma da sara" murmushi Viper ya yi. "Yaya" suka ji an faɗa daga nesa, suna juyawa Shahida ce ta taho da gudu, ta ruƙunƙume Viper tana kuka. "Yaya dama zan sake ganinka? Yaushe rabon da na ganka a rayuwata, ashe zan sake haɗuwa da kai?" Wani irin sanyi ne ya ratsa Viper, duk da ba wani good time yake yi da Shahida ba, amma atleast yar uwassa ce ta jini, kuma duk da irin cin kashin da aka din ga yi masa a gidan su, sosai take nuna masa tausayi da jin ƙai" Rungumeta ya yi, sai dai ya rasa mai ze ce mata. Ta ɗago tana kuma ƙare masa kallo, ta ce "Na je prison ban san adadi ba, ba a bari na ganka, ina yawan yin kuka, idan na tuna halin da ka ke ciki, ɗazu na ga text ɗin Abbu, wai na taho kotu an wankeka daga zargin da ake yi maka, ni ban san yana ganinka kuna haɗuwa ba, na yi kewarka sosai yayana" Ya riƙe hannayenta ya ce "Kin yi saurin girma Shahida, ƙarama ce ke fa, lokacin da aka tsare ni" Zata yi magana ta haɗiyeta ta ƙarfin tsiya, sakamakon arba da ta yi da Nabila, cakumar rigar Viper ta yi, tana nuna masa Nabila. Ya ce "Menene?" "Ba ta mutu ba?" Ya ce "Eh, amma ta dawo ne ta halarci taron kotu, ta ga yadda za a hukunta waɗanda suka kasheta, yanzu zata koma" Nabila ta ce "Kaiiii" Kiɗimewa Shahida tayi cikin matsanancin tsoro, Walid ya ce "Viper kai fa ka iya wasan banza wasu lokutan, ba fa ta san ainihin abin da ya faru ba, sai ka saka ta suma ai" Baba ya ce "Na ga alama ai, Shahida wannan ba Jauhar ba ce ba, twins sister ɗin ta ce Nabila" tayi ƙuri da ido, tana kallon Nabila. Liti ya ce "Ke kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo ne?" Ganin Nabila ta samu nutsuwa, 'yan jarida suka cigaba da addabarta a kan tayi magana, tambayar da ta fi ɗaukar hankalinta, har ta ji zata iya amsata ita ce "Wane irin farinciki ki ke ciki a yau, ganin kin yi nasara a wannan shari'ar?" Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, nayi farinciki sosai da sosai, dan wannan ce nasara mafi girma da na samu, tun bayan zamana cikakkiyar lauya mai zaman kanta, kuma in sha Allah yanzu aka fara. Sai dai na sadaukar da wannan nasara tawa kacokan, ga babana maganin kukana, abin alafharina baya goya marayu ginshikin da na jingina da shi, ya zame mini tsananin da na taka na cimma wannan nasara. Mutumin da ya saita ni a kan wani buri da ban taɓa tunanin ina da shi ba, kuma zan ci karo da shi ba, yau gashi wannan burin ya cika wato Major Yusuf maitama mai ritaya, ina alfahari da kai dattijon arziki matuƙa gaya. Ina fatan al'umma za su ci gaba da bamu goyon baya ɗari bisa ɗari wurin kawo gagarumin gyara da sauyi, a fannin shari'a da kuma harkar tsaro. Kuma ina fatan matasanmu maza da mata zamu nisanci shaye-shaye da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi". Yanayin yadda Nabila take magana, ya sanya Viper ya kalli Shahida ya ce "Jauhar zata iya magana haka doguwa a gaban mutane cike da ƙwarin gwiwa ba tare da tsoro ba?" Shahida ta girgiza kai ta ce "A'a" "To Nabila daban jauhar ma daban, wannan 'yar biyunta ce" "But how, ban taɓa sanin tana da sister ba ai" Viper ya ce "Is a long story" Abbu abin har mamaki ya bashi, yadda a wannan karon, Viper ya sake da Shahida, duk da a baya, duk da irin shishishigi da take yi masa, baya saurarar ta. Viper ya gabatarwa da Nabila Shahida, Nabila ta ce "Ai naga kamar haryanzu tsorona take ji, bari idan ta sake ta ƙara tabattar da ba jauhar ba ce, sai mu yi magana" Wata ƙatuwar helux ta shigo harabar kotun, baƙa ƙirin sai ƙyalli take yi. Ta yi parking a gaban su Nabila, da Abbu, wasu zaratan ƙarti ne suka saukko, su na sanye da riguna baƙaƙe da tambarin dragon, bayan rigar kuma hoton maciji ne da sunan Viper. Murmushi ne ya suɓucewa Viper, suka jeru suka din ga gaisawa sa shi ɗaya bayan ɗaya, suna yi masa congratulations da rungumarsa, yana amsawa cikin sakin fuska. Suka gaggaisa da su Abba, sai dai girmamawa ta musamman suka yi wa Alhaji mu'azzam. Viper ya ɓalle rigar jikinsa, rigarsa ta ciki irin ta su ce. Ɗaya daga cikin su, ya ce "Oga yana son ganinka, shi ya ce mu zo mu tafi da kai we need to celebrate with you" Ya jinjina kai ya ce "Ok to" ya kalli Baba ya ce "Baba bari na tafi, Nabila za a mayar da ita gida, idan na nutsu za ayi maganar in da yafi security ta koma, idan kuma za ta ci gaba da zama da madam shikenan. Shahida, zan zo gida zan yi miki gaisuwa ban in sha Allah. T ladan ina godiya sosai da sosai" ya ƙarasa maganar yana jinjina musu hannu, ya ce "Mai laya zamu yi magana, mu haɗe a chamber" yayi maganar yana danƙar kwalar ɗan mama ta ƙeya ya tura shi cikin motar" Liti ya ce "Wai yaushe zaku daina munafurtarmu daga kai har ɗan maman, waɗan nan jibga-jibgan kamar kai su kuma suwaye, menene alaƙarka da su?" "Tambaye su mana" Viper ya yi maganar yana nuna masa su. Ya kalli Nabila, yayi mata alama da hannunsa na zai kirata a waya, tare da kashe mata ido ɗaya. Murmushi ta yi ta ɗaga masa hannu, a daidai lokacin ya rufe motar suka ja, suka bar wurin. Nabila ta kalli Abbu jikinsa duk a sanyaye, Baba yana ta bashi haƙuri, ta ce "Baba da kai da honorable, yakamata ku shiga cikin lamarin nan  mussman kai, a sasanta Viper da Abbu, wallahi nayi nayi da shi yaƙi, da na fara maganar yake haɗe rai" Abbu ya ce "Na san kin yi iya ƙoƙarin ki Nabila, ki daina matsa masa, kin san murɗaɗɗen mutum ne, mai taurin kai, amma mai raguwar zuciya, duk wannan abin da yake yi, zai saukko, zan ci gaba da haƙuri, har zuwa lokacin da Allah zai sanya ya saukko". Viper ne a tsaye a wani katafaren office, wani narkeken mutum ya miƙe, ya ƙarasa wurin Viper, suka yi musabaha, ya rungume Viper ya ce "Congratulations my man" Viper ya ce "Thank you Sir" "Congratulations once again Al'amin" "Thank you very much sir" "Yarinyar nan fa ta bamu mamaki sosai da sosai, bamu taɓa zaton za ayi wining case ɗin ba, saboda case ne mai hatsari da sarƙaƙiya, amma thank God, Congratulations once again" Ya kalli ɗan mama ya ce "Anas" ɗan mama ya ɗan ɗago yana risunawa. "Yaushe zaka tafi training ne?" "Dan Allah sir ka yi haƙuri, ni ba sai na yi training ɗin nan ba, a bar ni kawai" Yayi murmushi ya ce "Viper ka ji abin da ya ce?". Viper ya ce "Bai isa ba sir, dole ya tafi" "To kai Anas, ko Viper bai faɗa ba, dolenka Anas, ai ka riga ka yi aiki da mu, you can leave, zan ganka" ɗan mama ya fice. Ya mayar da idonsa kan Viper ya ce "Viper, komai ya zo ƙarshe, yaushe zaka koma bakin aiki gaba ɗaya?" Viper ya ce "Ina son a ɗan ƙara mini lokaci, tun da ina gudanar da aikina daga nan, ina da abin da nake son ƙarasawa ne" Ya ƙaraso ya dafa kafaɗar Viper ya ce "Kamar haryanzu kana cikin pain Viper, amma yakamata ka tattara hankalinka wuri guda, a baka abin da za a baka ka cigaba da rayuwarka, amma duk abin da ka yanke shikenan, ina yi maka fatan alkhairi, zamu cigaba da baka dukkanin gudunmuwar da ka ke buƙata" Suka sake gaisawa da Viper ya fita. ***** Bayan Nabila ta koma gidan madam Halimaz tayu wanka ta canza kaya, madam sai murna take tayata saboda nasarar da suka samu, kai tsaye gidan Abba ta tafi, ta nufi benensa cikin matsanancin farinciki da murna, suna tare da Nasir, da wasu daga cikin yaran gidan da matansa. Gaban Abba taje ta zauna, tana ta murmushi bakinta yaƙi rufuwa, gaba ɗaya suka tattara hankalinsu a kanta. Dogon skirt ne a jikinta, da over size t-shirt ta Viper, tayi rolling da veil, ta ƙarasa gaban Abba ta durƙusa ta ce "Major Abba, na samu nasarar da ban yi zato ba, Alhamdilillah kotu ta wanke babban mai laifin da nake karewa, bayan da aka gano ba shi da laifin da ake zarginsa" Fuskar Major babu yabo babu fallasa ya ce "Na tayaki murna" "Abin da nake ta gaya maka kenan Abba, tun farko ba ka tsaya ka fahimce ni, nayi maka bayani ba" Ya girgiza kai ya ce "Nabila, ni fa duk wani abu da ya shafi mahaifinki ba ƙaunarsa nake yi ba. Da bai aura mata ɗan daba ba, da duk haka bata faru ba, ai yana da wasu yaran, meya hana su ya aura musu shi, sai ita, saboda ba ta da galihu, ni fa mutuwar yarinyar nan, ƙara mini ƙiyayyar mahaifinki ta yi, and na baki zaɓi idan zaki zauna a nan ne ki zauna, idan kuma wurin mahaifinki zaki koma, ki sauka lafiya ki yi abin da ki ke so, you are allowed to make decision" Jiki a sanyaye Nabila ta saki hannunsa, ta kalleshi ta ce "Abin har ya kai ga haka Abba? Ban taɓa tunanin akwai ranar da za ta so, ka sanya na ji wani abu a raina, mai kama da ba kai ne mahaifina ba" Ya dubeta a tsanake ya ce "Amma ke kin tabattar da duniya ba ni na haife ki ba" Ta girgiza kai ta ce "Ban nuna wa duniya ba kai ka haife ni ba, amma ina neman afuwarku baki ɗaya" ta tashi gwiwa a saɓule ta bar ɗakin. Ta sha kuka sosai da sosai a ɗakinta, sam ba ta ji daɗin abin da Abban ya yi mata ba. Ta koma ɗakinta ranta babu daɗi, tana jin kamar dan ba Nasir ne yayi nasarar ba, shiyasa Abban yake yi mata haka, ba wai dan yana jin haushin Babanta ba kawai" Baba Magajiya ce ta din ga rarrashinta, tana ba ta haƙuri, wayarta ce ta fara ringing, ta duba taga Viper ne. Ta ɗaga tare da goge hawayen da yake kwance a fuskarta. "Hello vi" "Ina waje" "Ai ba na barrack ina gida" Ya ce "Na sani, location ɗinki ya nuna mini, am tracking you ai" Ta ce "To ina zuwa" "Baba Magajiya, bari na je waje ana nemana" "To shi sirikin nawa ne?" Nabila ta ɓata fuska ta ce "Wane siriki kuma? Ai wallahi baba magajiya duk kallonku kawai nake yi, babu wanda ya yi mini kara a gidan nan, na zuwa in da mahaifina yake gaba ɗaya ma kamar kowa gaba yake yi da ni" Magajiya ta ce "Haba dai Arfa, wallahi dan babu yadda zan yi ne, amma ina matuƙar son yin hakan, amma kin ga ga a halin da ake ciki ne, kar nima na yi wani laifin" Nabila ta ce "Shikenan" ta tashi ta fita. "Vi snake" ta faɗa tana murmushi. "Kukan me ki ka yi kuma? Wai dan Allah ke a rayuwarki ba kya gajiya ne?" Ta girgiza kai ta ce "Ni kaina na san saurin kukan nan yana cutata, ba yadda zan yi ne" Ya ɗage kafaɗarsa ya ce "Ya gajiya kuma?" "Alhamdilillah, babu gajiya" "Bangajiya na dawo na yi miki, kuma na ƙara jaddada godiyata a gare ki" Ta numfasa ta ce "Kar ka damu, kaina na yi wa ai" "Gaskiya ne, gobe in Allah ya kaimu zamu koma wurin likita ko?" Ta jinjina kai ta ce "Eh gobe in Allah ya kaimu ne" Viper ya ce "Ina son 1hr kacal a lokacinki idan mun dawo" kawai ta gyaɗa masa kai. "Wai ya na ga jikinki a sanyaye ne, kamar ba wannan ranar ki ke jira ba? Meyafaru ko wani abin kuma nayi?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya sake kallon fuskarta yadda take ƙifta ido cikin damuwa. "Abla" ta ɗaga mayanyan idanunta ta na kallonsa. "Menene kuma?" "Abba ba zai yadda su sasanta da Baba ba, na rasa wace irin zuciya ce da shi, wai haushin sa ya ƙara ji, da ya aura maka jauhar, meyasa a cikin yaransa bai aura wa wata a yaransa ba, sai ita, saboda marainiya ce babu mai tsawatar masa. Shikenan haka zan zauna a tsakiya gaba ɗaya komai ya fita daga raina" ta yi maganar tana ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata. "Yanzu ni ne dai matsalar kenan?" Ta ce "A'a, ba kai ba ne ba, ya ma ƙi saurarata balle in yi masa bayani. Yanzu a haka zan ci gaba da zama a gidan nan, Abba ya kware mini baya a gaban mutanen gidan da ba sa so na, ko kuma can gidan mahaifina zan koma, na zauna a cikin waɗanda suka muzgunawa mahaifiyata da 'yar uwata. Zamana a cikin barrack na ɗan lokaci ne, kuma saboda kai ne, da komai ya kammala dole na bar zaman wurin, gaba ɗaya zuciyata a cunkushe take na rasa mai ma zan yi, na zata da an kammala shari'a komai zai zo da sauƙi, ashe tsugunno ba ta ƙare ba" Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ni ne matsalar a nan, zan kuma san abin yi na warwareta in sha Allah, ki yi haƙuri komai zai daidaita" Ta ce "Tayaya kenan, ka san halin Abba kuwa?" "Eh mana, hali mai kama da nawa ko? Zan san abin yi, ki je mu haɗu gobe in Allah ya kaimu" **** Nasir ya rasa abin da yake yi masa daɗi, mussaman yadda Nabila tayi nasara a kotu, duk sai ya sha jinin jikinsa, gashi sai ya ga kamar Abba ya sauya masa. Da asuba Abba yana sauraren labaran asuba, aka sako Muryar Nabila, tana murna da godiya ga Allah, bisa nasarar da suka yi a kotu, tare da sadaukar da nasarar ta ta gare shi baki ɗaya. Yayi shiru yana saurarenta, ƙasan zuciyarsa yana cike da farinciki, sai dai haushin mahaifinta, ya hana shi sakewa ya ji daɗin hakan. **** Ramma ta ɗauki wayar mama ba ta sani ba, ta kira Nabila, suka gaisa Ramma ta ce "Anty Nabila, mama ta ce wai kun yi nasara a kotu ko?" "Eh rahama, Alhamdilillah" Ta ce "Masha Allah, ina tayaku murna sosai da sosai Allah ya ƙara nasarori" "Amin rahama, mun gode sosai ya jikinki, lokacin zuwa awo bai yi ba ai ko?" Ta ce "Eh saura sati biyu" Nabila ta ce "To Allah ya raba lafiya" Sai kuma tayi shiru, ta kasa faɗar abin da ya sanya ta kiratan" "Rahama ko akwai wani abu ne" Jiki a sanyaye ta ce "A'a dama...." "Dama me? gaya mini babu wani abu" "Cewa na yi kin je wurin doctor ne? Ya warke?" Nabila ta yi murmushi ta ce "Allah sarki ƙanwata, na fahimce ki, ki yi haƙuri sai Allah ya kaimu lokacin awonki, daga nan sai mu je ki ganshi, kin san halin yayanki, daga ni har ke sai ya tijaramu ba ruwansa" Ta ce "To na gode sosai Anty Nabila" "Kar ki damu, ki cigaba da addu'a, da kula da kanki da cin abinci da shan magani, in sha Allah komai zai wuce" Ramma ta ce "Ina yi, na gode

Chapter 102 of 121