ɗan mama ya haɗa allura ya hau zuba masa a cikin cannula, a hankali viper ya fara buɗe idanunsa, amma kansa ya fara juyawa, ya kasa magana.
Ɗan mama ya koma gefe, ya kunna sigari yana sha, mintuna goma Viper ya tafi gaba ɗaya, ya ciro wayarsa ya danna, sannan ya saka a kunnensa ya ce "Hello sir, eh su yi sauri ya samu bacci, amma yana cikin ciwo sosai"
Ya ajiye wayar ya cigaba da shan sigarinsa, mintuna arba'in sai ga wata helux baƙa ta iso wurin, wasu narka narkan ƙarti suka fito, suka saɓa Viper suka saka shi a cikin motar, ɗan mama ya kama ya hau suka tafi.
Suna tafe a hanya su liti suna kiran ɗan mama a waya, ya gaya musu yana ina, da shi da Viper, ya din ga raina musu hankali yana yi musu kwana-kwana, suka din ga zaginsu amma ya ce "Oga walid ka yi haƙuri, wayar zata mutu babu caji" ya katse wayarz ya cire batirinta gaba ɗaya.
Wani Asibiti suka kai shi, likitoci suka rufu a kansa, suka dudduba shi, suka ce babu wata matsala zai warke, ba wata gagarumar matsala bace ba, sai dai dole ya nisanci shaye-shaye idan yana son zama lafiya.
Nasir jiki na rawa ya ɗaukko wayarsa, yana kiran Nabila, sai dai yayi mata missed calls, sun fi biyar, ko ɗaya bata ɗaga ba, hakan ya ƙara fusata shi ainun, ficewa yayi ya ɗauki mota ya bar Asibitin, yana ƙoƙarin gazgata zargin da yake yi wa Nabilan.
Yana ƙoƙarin sake kiran wayarta, sai ga kiranta, ya ɗaga zai yi magana ya ji muryar da bata Nabila ba, ta wani daban.
"Malam ina mai wayar?"
"Ta haɗu da hatsari, tana emergency na asibitin cikin gari" wani wawan burki ya ci a tsakiyar titi, wanda sai da ya kusa haddasa hatsarin shi ma.
"Ta mutu ne?"
"A'a, ana kula da ita, ni ɗan sanda ne, mu muka kaita asibitin"
"Nima ɗan sandan ne, ka gaya mini ta mutu ko?"
"A'a, muna dai jiran abun da likitoci zasu ce ne" ana tayi masa horn, amma hankalinsa baya kai, ya fizgi motar ya canza hanya.
***
Ramma kuwa bayan Abdul ya gama wayar ta ce "Ka ce mini mahaukaci ne ya yanke ka, kuma yanzu na ji yan sanda ne suka kiraka ana zancen ɗan ta'adda"
"Eh shi ne mahaukacin ai"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kamar na san sunan da ka faɗa fa"
"Wanne?"
"Mai zamani, amma kuma kamar ba haka ake ce masa ba, mama ta san shi"
Basar da zancen yayi ta hanyar cewa "Wayyo wuyana"
Cikin kulawa ta ce "Sannu, ka kwanta to"
"To ki zauna sai na kwanta a kan cinyarki"
"Gaskiya ba zaka takura mini ba, wai kai jinyarka sai ka ce wani jariri, ka yi ta ragwanci, ɗan wannan ciwon sai wash kake, wannan idan kaga fuska kuka zaka yi kenan?"
"Haba baby, ki tausaya mini mana, da na mutu fa"
Ramma ta ce "Haka nake fata dama"
"Ƙarya ki ke yi " yayi maganar yana janyota, yana ƙoƙarin kwanciya a jikinta, ta ture shi ta ce "Baka isa ba, idan ka gama sangartar ka watstsake, mutum ba juriya"
Shagwaɓe fuska yayi, yana kuma kwanciya a jikinta ya ce "Zafi"
"To sannu"
"Yauwwa baby, i love You, ki kula da ni sosai"
"To samo zani sai na goyaka ƙarewar kula, ka rabu da ni dan Allah" ƙarshe ta gama mitar ta rabu da shi.
***
Nabila kuwa a emergency, aka gano gocewar ƙashi a hannunta, sai buguwa da tayi a ka, ta fasa goshi, ga jini na fita daga hancinta, in da Allah ya taƙaita abun, da seatbelt a jikinta take driving, dan Abba na yawan gargaɗinta a kan hakan.
Godiya Nasir ya din ga yi wa Allah, da ya tarar bata mutu ba, daga nan asibitin, ya ɗauketa ya canza mata wani.
Da ƙyar ya iya kiran Abba ya gaya masa, saboda yadda baya ɗaukar lamuranta da sauƙi.
***
Lokacin da aka kai Viper da ɗan mama gida, su liti basa nan, sun bazama nemansu, duk da a hanya, sai da jami'an tsaro suka tare motar, da son bincikar motar, amma ganin masu motar, ya sanya aka basu dama suka wuce.
Suka kwantar da Viper suka tafi, ɗan mama ya gyara gidan, ya nemi wuri yayi zamansa hankali a kwance.
Dare yayi sosai, su liti suka dawo, suka tarar da ɗan mama da Viper yana bacci.
Zabura liti yayi, zai kwaɗe shi, Walid ya hana shi, ya ce "Ɗan mama, wane irin wulaƙanci ne ka yi mana haka?"
"Oga Walid, wayata ce ta mutu fa, ɗan gidan indabo ne likitan da ya shiga duba shi, tona mana asiri ya so yayi, a kama mu, muka yi layar zana, muka dirge, muka samu wuri muka ɓuya, ciwon cikin ya sake tayar masa, na yi masa wata allura da na ga suna yi masa a cikin kayan magungunan sa, kawai naga ya ware, shi ne na samu abun hawa, na kai shi wani asibitin, da kyar na kawo shi gidan nan, hannunsa na saƙalo a kafaɗata muna tafe muna faɗuwa har gida".
Liti ya ce "Ɗan azzaluma, duk sai da ka azabtar da shi, ga ciwo yana fama, shegen taurin kai kamar jinjirin jaki, ka gaya mana kuna ina, ka ƙi da yake ɗan kut....ne kai, ɗan wahala kawai".
Walid ya ce "Dan Allah liti kayi haƙuri, tun da Allah ya dawo da su gida lafiya"
"Ai yaron ne, wasu lokutan yadda ka san rainon garke, gaba ɗaya rayuwar sa, babu lissafi"
Ɗan mama ya ce "Ayi haƙuri"
"Kai ni fa ban ma yarda kai kaɗai, ka iya kawo Viper gida ba, Allah ya sa ba wani haukan kayi, ka kawo mana wani ya ga in da muke ba"
"A'a oga liti, nikaɗai na kawo shi gidan nan"
"Ware maƙaryaci kawai"
***
"Abdul"
"Na'am daddy"
"Saura wata guda bikinka, babu wani alamar shirye-shirye da kake yi, kawai dai gaka nan, ta ƙarfi da yaji ka ke son salwantar mana da wannan damar"
"No daddy ba haka bane ba, ina shiri, amma yau ka ji news kuwa?"
"A'a wasu lokutan news ɗin nan, hawan jini yake saka mini, amma meyake faruwa?"
"Na haɗu da Viper fa" miƙewa tsaye Indabo ya yi ya ce "Wane Vipern?"
Abdul ya ce "Ya naga ka tashi tsaye? Viper dai naka, ya je ƙaramin branch ɗina, an kwantar da shi har ya kwana"
Indabo ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai da me yaron nan yake taƙama har haka, yawo ma yake yi a cikin gari har da zuwa asibiti? Anya ba harinka yake yi yayi maka wani abun ba, ya sanya ya je?"
Abdul ya girgiza kai ya ce "Bana tunanin hakan, unexpected muka haɗu, naje da daddare ban gane shi ba, yana bacci, sai yau da safe muka haɗu, amma dan Allah Daddy, meya haɗaka da Viper har haka, yake farautarka kai ma kake farautarsa?"
Indabo yayi wuƙi-wuƙi da ido ya ce "Ya gaya maka wani abun ne?"
"A'a, amma ya ce yana nan zai yi fitar burtu, yana nan tafe gareka, dan Allah mai ka yi masa ne?"
Indabo ya ce "Babu komai, kawai dai ka san yan daba, ba alƙawari ne da su ba, babu wani abu da nayi masa" yanayin yadda yake maganar, ya sanya Abdul gane akwai wani abu a ƙasa, amma ya ɓoye masa, Abdul ya jinjina kai ya sake cewa "Daddy"
"Na'am Abdul"
"Bayan na auri 'yar gidan party chairman, idan na kawo wadda nake so, zaka aura mini ita?"
"Wacece kuma a ina take?"
"A'a kafin in gaya maka, zaka yarda na zauna da ita, kuma ba zaka yi mini faɗa ba?"
Indabo ya ce "To ai haryanzu ba ka yi mini bayani ba"
"Amm yarinyar da nayi raping tana raye"
"What! Tana raye? Tana ina?"
Cikin sanyin jiki Abdul ya ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri ɓoye makan da nayi, tsawon lokaci, dan Allah ka yi haƙuri"
"Na ji, na ji, tana ina yanzu?"
Abdul ya girgiza kai ya ce "To ai daddy baka ce komai ba, dan Allah ka yi haƙuri, na san nayi kuskure, sai da na ce zan kasheta, na ga ashe kisan kai ba abu ne mai sauƙi ba, dan Allah ka yi haƙuri "
Indabo ya yi shiru sannan ya ce "Na ji, amma yanzu tana ina? An yi sara a kan gaɓa, hankalin mutane ya dawo kan appeal ɗin da waccan shegiyar yarinyar zata yi, dan haka dole zata bayyana a gaban kotu, amma da baka kasheta ba tana ina?"
"Daddy, abun da kawai zan iya gaya maka kenan ban kasheta ba, saboda ina tsoron matsala ta taso daga baya, amma ba zan iya barin rahama taje gaban kotu ba"
"Me kake nufi?"
Cikin damuwa ya ce "Ban san me zai iya biyo bayan hakan ba, rahama tana tare da ni a wuri daban, tsawon wannan lokacin" wani lafiyayyen mari Indabo ya ɗauke Abdul da shi, ya dafe kuncinsa ya ja da baya.
"Abdul yasar, yaushe ka yi girman da zaka yankewa kanka hukunci ba tare da sanina ba? Yanzu duk dambarwar da ake yi yarinyar nan na tare da kai? Audio da yake yawo aka ce muryar babarta ne, da gaske kenan zuwa ka yi ka ɗauke ta, saboda mahaukaci ne kai, sai ka je da kanka, ba ma turawa ka yi a ɗaukko maka ita ba, lallai ta tabbata baka da hankali dabba ne kai, wallahi ba zaka lalata mini siyasa ba duk wannan wahalar da nayi ta tashi a banza ba"
"Daddy, dan Allah ka fahimce ni".
"Shut up my friend, ubanka zan fahimta ka je ka kawo mini yarinyar duk in da ka kaita, kafin na casaka wallahi ba zan bari ka tona mini asiri ba, saboda hauka da wautarka ba, fice ka bani wuri kan na tattaka ka"
Abdul ya tsuke fuska sai hura hanci yake yi, ya fice, sam bai ji cewa ko indabo zai jajjaga shi, zai kai masa Ramma ba, ko ya yarda ta tsaya a gaban kotu ba, sai dai ayi duk wadda za ayi.
***
Bayan farfaɗowar Viper daga baccin da allura nan ta saka shi, ya din ga mamaki, wace irin allura ce haka, bai takura da kansa da dogon tunani ba, sai dai yadda ya din ga jin ina ma, ya yi wa Abdul mummunar illa, kan ya baro asibitin, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa, ba shi ne yayi masa laifi ba. Wata zuciyar kuma ta ce kai ma ba matarka ce tayi musu laifi ba, suka kasheta.
Ya tashi ciwon cikin da sauƙi, ya yi alwala ya rama sallolin sa, da daddare ya zauna yana jiran kiran wayar Nabila da daddare, dan ya san ba zata iya zuciya ba, sai ta kira shi ta ji ya jikinsa, amma shiru ba ta kira ba, har cikin dare idan ya juya, sai ya duba wayarsa ko ta kira bai sani ba, amma babu kiranta, shi ma kuma ya kasa kiranta.
Abba kuwa godiya ya din ga yi wa Allah, da likitoci suka tabattar masa da ba wani abun tashin hankali ne ya samu Nabila ba, ta bugu ne a ka, kuma babu internal injury, sai hannunta da ta samu gocewar ƙashi shi kawai za a gyara.
Mama ta hau masifa, ta ce "Ba dai ita yar gata ba, an ɗauki mota an bata ba, Allah kaɗai ya san tuƙin gangancin da take yi, ko dan ma tayi burga a titi, gashi ta tayar da mutane tsaye"
Abba ya ce "bata tayar da kowa tsaye ba, babu wanda na yi wa dole ya zo ya zauna mini da ita, a da ma baku yi ba sai yanzu? Kuma tuƙin da take yi, ai masaniyar doka ce ita ma, ba wani tuƙi da take yi na ganganci, jarabta ce kawai Allah ya kawo, kuma ya taƙaita, Magajiya zata yi mini jinyarta, zuwa a sallameta, ban ce dole ayi mini ba" mama ta ja bakinta tayi shiru, jin abun da ya ce.
Ya cigaba da kallon Nabila, cikin tsananin tausayawa, kwanan nan abubuwa sai samunta suke yi, daga wannan sai wannan.
***
Nasir ne zaune a gaban Indabo, fuska babu walwala Indabo ya ce "Naga alamar aikin nan baka ɗauke shi da muhimmanci ba, idan har ba zaka iya ba, zan saka a canza mini kai, nayi abun da nake ganin shi ya dace".
"Ina mai baka haƙuri, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe"
"Idan ma baka kawo shi ba, ni zan kawo".
***
Hafsa ce zaune a gaban baba ta ce "Baba"
Ya ce "Na'am ƴar baba"
"Baba na san ai kai ba zaka ƙaryata ni ba ko?"
"Eh mana yaya zan yi na ƙaryata ki ma?"
Hafsa ta gyara zamanta ta ce "Ai dai ka san na warke yanzu, bana yawo, ba na shan komai, kuma na warke ai dai ko?"
Ya ce "Alhamdilillah kam, duk na sani hafsat"
"To yadda naga jauhar yau Allah ya nuna mini annabi haka, ta saka niƙab, da irin tafiyarta, da irin idonta, amma sai da na ganeta, na so na bi ta, yaya saifu ya kira ni, na nemeta na rasa"
Baba ya ajiye cokalin sa, ya ce "Anya kuwa warkewar nan hafsa? Yaya za ayi ki ga wanda ya riga ya mutu, kuma ta cikin niƙab ɗin ki ka iya gane ita ce?"
"Haba Baba, ka san dai yadda nake da jauhar, amma ko ina ga fatalwarta ce, amma dai da ko da ta zo mini a fatalwa, sai ta tsaya mu gaisa, bai kamata ta nuna kamar ba ta sanni ba, ina ga haryanzu haushina take ji, saboda na auri Alhaji mu'azzam yakamata ai ta yafe mini, ba ta ga irin wahalar da na sha ba, ai ko gaisawa sai ta tsaya mu yi. Ka ce na din ga yi mata addu'a, ina yi mata fa, amma duk ba ta ga wannan ba, ta share ni, ban san ya aka yi waliyiyyarka ta koyi wannan halin ba baba" tayi maganar tana kuka iya ƙarfin ta.
Ya share hawayen da yake shirin gangaro masa, ya ce "Bata kyauta miki ba, zan yi mata faɗa, amma ina ga zamu koma Asibiti ganin likita".
Hafsa ta ce "Baba da hankalina fa, ba hauka nake yi ba, ina sane da duk abun da nake yi fa" Mama ce ta shigo ɗakin ta ce "Ke mahaukaciya, tashi ki fita ki bashi wuri, ya gama cin abinci dan Allah, kin saka shi a gaba da sakarci"
Hafsa ta ce "Ni ba mahaukaciya ba ce ba, cutar damuwa nayi ba hauka ba"
Baba ya ce "Na sha gargaɗinki a kan kiranta da mahaukaciyar nan, wannan salon ki sake tunzurata ne ai"
"A'a dama ai a tunzuren take" Hafsa ta tashi rai a ɓace, ta fita tsakar gida tana kiran Anty.
"Hafsa wane irin kira ne wannan? Menene?"
"Kin ga maman su surayya tana ce mini mahaukaciya ko? Ni fa ba mahaukaciya ba ce ba"
A fusace Anty ta nufi ɗakin Baba ta ce "Wallahi kar ki sake kiran ya ta da mahaukaciya, idan ba haka ba duk abun da nayi miki ke ki ka saya"
"Mecece idan ba mahaukaciya ba, ba dai auren cin amana ba, da son abun duniya ba, ta haɗu da babarta a makirci a matsayin kishiya ai, ga hauka ga ba auren, sai an yi magana ace depression ne, yarinya ta zama yar ƙwaya ta haukace"
"Eh bakomai, tun da har ta yi auren ai, ta shiga ta fito, da babbar budurwa ai gara ƙaramar bazawara, da kike maganar zama yar ƙwaya, naki ɗan uban menene ba ya sha? Ko kina tunanin bamu san komai ba"
Hafsa ta koma gefe tana kuka, saboda ta tsani taji an kirata da mahaukaciya, kuma haryanzu idan ta tuna jauhar, da cin amanar da aka yi mata sai ta ƙara shiga damuwa, tayi ta kuka, ta san hakkin jauhar ne ya sanya ta tsinci kanta a wannan mawuyacin halin da take ciki.
Baba yana jin su, ya fito a zuciyarsa yana Addu'ar, Allah ya sa jauhar da mahaifiyarta suna tare a aljanna. Ya fice ya bar musu gidan.
Walid yana ta lallaɓa Viper, ya ci abinci ya sha magani, gaba ɗaya jin sa yake yi wani iri babu daɗi, ya karɓi kofin shayi yana sha a hankali.
Ɗan mama ya kunna radion wayarsa, liti ya hau mitar ya cika musu kunne, ya ce "Dan Allah oga liti kayi haƙuri, labarin wasanni zan ji"
"Ai sai ka yi"
Tashar su Sumayya ya kai, a dai-dai lokacin da murtala yake sanar da hatsarin da Nabila ta samu a jiya, bayan kammala program da suka yi ta tafi, suna barar a sakata a cikin addu'a.
Buredin da viper ya haɗiya ne, ya tsaya masa a maƙogwaro, tamkar ya haɗiyi dutse.
Liti ya fizge wayar hannun ɗan mama ya ce "Ban gane hatsari ba, ji ya ma fa taje Asibiti duba Viper, har yaushe ta yi hatsari kuma?"
Walid ya ce "Babu kusa babu nesa ga Allah, amma dai dole mu san halin da take ciki"
Liti ya ce "Taɓ yarinyar nan tana shan azaba, dudu yaushe ta kusa mutuwa a gobara, yanzu kuma hatsari?"
Viper ya din ga murza kofin hannunsa, gumi yana tsatstsafo masa, amma bai tofa uffan ba.
Ɗan mama ya tashi ya ce "Bari nayi maza nayi wanka, na je unguwar su na jiyo, wane asibitin take? Ko kuma na je asibitin da ta kwanta lokacin da tayi gobara, yadda ake ciki dai zan kira ku"
"Saura kuma ka kira mu ka yi mana wannan gaɓancin naka, kayi mana wauta, ka tsaya ka nutsu, kuma saura ka ce baka da caji a waya"
Ɗan mama yayi murmushi ya ce "Ni na isa, in sha Allah ba za ayi haka ba"
Walid ya ce "Viper ka ƙarasa ci, in sha Allah babu wani abu, tun da ba su ce ta mutu ba, an ce dai ta ji raunuka ne kawai" shi dai bai ce komai ba, ya ajiye kofin shayin.
***
Yanayin yadda Abdul ya shigo, sai da ramma ta ɗan tsorata, maye yake yi sosai.
Ta tashi ta nufi in da yake, ta ce "Abdul giya ko? Baka ce mini ka daina shan giya ba?"
Yayi shiru yana ta numfarfashi.
"Kai dai ba zaka taɓa gyara rayuwarka ba, idan ka yi kamar zaka nutsu, sai ka ƙara fanɗarewa, kayi ta yi mini alƙawari baka cikawa".
Ya kama hannunta ya rirriƙe, ya ɗaga jajayen idanunsa da ƙyar ya kalleta ya ce "Rahama"
"Meye?"
"Dan Allah karki rabu da ni, ban san me zai iya faruwa a gaba ba, ina sonki, ina sonki....Ai zaki yafe mini ko rahama" yayi maganar cikin maye yana kallonta.
Ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana shafa sumarsa a hankali ta ce "Kana so na amma ka je ka sha giya, kafi bawa soyayya muhimmanci a kan tsoron Allah ko?"
Ya girgiza kai alamar a'a.
"Ga lokacin Sallah yayi, amma babu damar ka yi saboda kana maye, idan ka mutu a haka fa, zan yafe maka ne kawai, ranar da ka mayar da ni gaban mahaifiyata ka nemi afuwarta"
"Idan nayi hakan, zaki yafe mini, mu cigaba da zama tare?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.
"Wallahi rahama, komai zai faru sai dai ya faru, idan aka yi ƙoƙarin raba ni da ke, zan ɗauke ki ne na yi gaba da ke, muje mu cigaba da rayuwarmu tare"
Ta ce "Mhmm Abdul yasar rigima, kayi shiru ka daina wannan surutun ka samu ta sake ka, kayi salla ba na son ka mutu kana rashin ji, wasu lokutan dai kayi ta abu kamar mutumin kirki, amma zunubanka da kake tafakawa ne, sun wuce misali"
"Rahama"
"Abdul yasar"
"Wallahi ba zan yadda a rabani da ke ba, ina sonki sosai"
"To likita, amma na ce kayi shiru ai"
Ya ce "To na yi" da haka ya din ga sauke numfashi, yana bacci.
****
Ƙarfe biyu da rabi na dare, Viper yana cikin asibitin da Nabila take, sawu duk ya ɗauke, yan dubiya babu kowa, daga majinyata, sai marasa lafiya da ma'aikatan da za su kwana.
Ya jinjina ƙofar ɗakin da Nabila take, ya tura a hankali, bai ji an yi magana ba, ya sake turawa ya ga duhu, an kashe fitilar ɗakin, ya shiga ya rufe ƙofar, ya kunna fitilar wayarsa ya haska, baba magajiya na ƙasa kan carfet tana bacci.
Ya haske Nabila tana kan gado, ita ma baccin take yi, ana ƙara mata jini.
Ya taka a hankali, ya je gaban gadonta ya durƙusa, an naɗe mata hannu ɗaya da bandeji wanda ta samu gocewar ƙashin.
Hular kanta ta zame, tun daga farkon goshinta, a cike yake da gashi mai santsi, kasancewar ba gwanar yin kitso bace, gashin nata a tsefe yake.
Ya kai hannunsa goshinta, in da aka rufe da plasta, da alama rauni ne a wurin, ya dawo ya riƙe hannunta ya ce "Get well soon, Allah ya baki lafiya"
"Viper" ta furta a hankali kamar mai raɗa.
"Angry bird"
"Ya jikinka?"
Ya ce "Na ji sauƙi"
"Yanzu ma na san ba zaka kira ni a waya, ka yi mini sannu ba, ka tsane ni"
Ya girgiza kai ya ce "Ban tsane ki ba Abla, ina so ki rayu ne, in cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin taki"
"Viper"
"Mmm"
"Zan cika maka alƙawarin ka in sha Allah, duk wuya duk rintsi, zan tsaya maka sai ka yi 'yanci, duk girman barazanar da zasu yi mini, zan tabattar da an yi maka adalci da kai da matarka"
"Allah ya baki iko"
Ta sake cewa "Viper"
"Mmm Abla"
"Dan Allah kar ka tafi daga mafarkina yanzu, na san idan na tashi, ba zan iya zuwa asibiti na dubaka ba"
Yayi shiru bai kuma ce mata komai ba, ta ƙara riƙe hannunsa, da yafi nata girma sosai.
Jikinta ne ya ƙara saki, ta cigaba da bacci, tana yi tana surutai, a hankali har ta yi shiru. Ya sake haskata da fitilar sa, irin innocent face ɗin jauhar ta bayyana a fuskar Nabila. A hankali ya zare hannunsa daga nata, ya yinƙura ya tashi ya fita daga ɗakin.
Washegari da safe, sai tunanin mafarkin da tayi jiya take yi, tana tunanin gaske ne, ko kuma kawai mafarki ne?.
Da safe ana ta zuwa dubata, wajen ƙarfe sha ɗaya Nasir ya zo, lokacin babu kowa kasancewar ranar aiki ce, sai baba magajiya. Suka gaisa, ya aiki baba magajiya ya rage saura daga shi sai Nabila a ɗakin.
Ya zauna daf da ita a kan gadon, yana kallonta ya ce "Sannu ya jikin?"
Ta amsa da "Jiki Alhamdilillah, da sauƙi, zuwa gobe in Allah ya kaimu nake so na tafi ma, i have a lot to do"
Ya ce "Well, tambayarki zan yi, kuma bana buƙatar ki yi mini ƙarya, saboda zargina ya tabatta gaskiya ne a kanki"
"Wane zargin?"
"Nabila kin san in da Viper yake, kina haɗuwa da shi!"
Ta kalleshi ta ƙura masa ido amma bata yi magana ba.
"Ina magana kina kallona, na samu rahoton an ganshi a A.I hospital, naje bamu sameshi ba, amma naga signing ɗin ki, kin je asibitin me ki ka je yi?"
"Ni ganin likita naje, ka daina zargina tun da baka da wata hujja, mai asibitin aka tura ni wurinsa follow up, saboda lokacin da aka sallame ni, bai zo ba"
"Ƙarya ki ke yi Nabila"
"Ni ba ƙarya nake yi ba, ka fara samo tabattaciyar hujja, kafin ka ƙaryata ni"
Ya jinjina kai ya ce "Zamu gani ai, bayan duk wannan abubuwan hujja ki ke so na kawo miki? Shikenan zamu gani, amma ki sani aikinki ba zai baki kariya ba, muddin aka kama ki da laifi, sunanki yar ta'adda kema, mai ɓoye mai laifi"
"Abun kunya ne ga hukumar yan sanda ace sun gagara kama mutum ɗaya, da yake iya yawonsa a cikin gari, sai ma a din ga bibiyar wanda bai ji ba, bai gani ba, ana yi masa baranaza" tsananin fusatar da yayi, ya sanya kawai ya tashi ya bar ta a ɗakin.
Ta dafe ƙirjinta, saboda yadda yake tsananin bugawa, ta yanke a ranta dole tayi gaggawar fara shari'ar Viper, kafin ta kammala ta ramma.
Ya fita babu jimawa, baba magajiya ta dawo, ta karɓi aron wayarta, ta shiga banɗaki, ta kira wayar Walid, Allah ya taimaketa ya ɗaga.
Ya ce "Barrister ashe tsausayi ne ya faru haka, ya jiki?"
"Jiki da sauƙi, meyake faruwa ne? Yayana ya ce mini ya samu labarin Viper ya je asibiti, ina yake ina fatan babu wata matsala?"
"Eh, Yana nan cikin ƙoshin lafiya mun koma gida ma, haɗuwa yayi da ɗan Indabo a matsayin likitan da ya duba shi, shi ne ya sanarwa security"
Ta ce "Haba dai? Likitan da ya duba shi kuma? Garin yaya dole mu ƙara taka tsantsan amma ba abun da ya faru?"
Walid ya ce "Babu abun da ya faru, mun bar Asibitin ma, muna gida"
"Dole na haɗu da shi, nan kusa Allah ya ƙara afuwa" ta katse wayar ƙirjinta na cigaba da bugawa.
***
Indabo yana ta sanya ran ya ga ta ina Abdul zai ɓullo, ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda matsalolin da suke kunno kai, ya rasa wanne yakamata ma ya fara ƙoƙarin kawarwa.
Kwanaki biyu kenan, ko
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 73 Chapter of 121