Viper, da cutar da shi zan yi, da tuni na yi so bakinki ƙanin ƙafarki" daga haka ya miƙe ya nufi in da suka baro su walid.
Aka fito da Viper a kan gado, aka ce za a ba su ɗaki, za a turawa likita result ɗin.
Kamar yadda Nabila ta yi tsammani, an biya bills ɗin, ta din ga yi wa ɗan mama kallon tuhuma, shi kuwa da sun haɗa ido, sai yayi mata murmushi, hakan ya ƙara jefata cikin tunani.
Likita ya shigo da file a hannunsa, suka sake gaisawa, ya tattaɓa cikin Viper, sai dai duk da an yi masa allurai ya samu bacci, da ya taɓa cikinsa ɓangaren dama, sai da ya zabura ya motsa.
Ya duba scanic ɗin hannunsa, ya ce "Hantarsa ce ta kumbura gaskiya, amma ƙodojinsa da sauran abubuwa lafiya ƙalau, amma duk da haka zaku yi x-ray na cikin, mu sake tabattarwa ko da wani abun"
A tsorace Nabila ta ce "Likita hantarsa ta kumbura kuma?"
"Eh, amma karki damu babu wani abu in sha Allah, idan aka yi x-ray ɗin, akwai likitanmu da zai zo ya duba shi, ba wani abun tayar hankali bane ba, zai samu sauƙi in sha Allah"
Walid ya ce "Allah ya sa"
Ɗan mama ya ƙurawa wayarsa ido, sannan ya kalli Nabila, yayi mata alama da su haɗu a waje.
Ya tashi ya fara fita sannan ta bi bayansa.
Ya ce "Ana bibiyarki, yanzu aka turo mini saƙo, zaki bani mukullin motarki, zan kawo miki ita gida a matsayin bakanike"
"Nifa ban fahimci duk wannan abun ba"
"Tsayawa dogon bayani, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki ga gaggauta muje na raka ki, na ɓulla da ke wata hanyar ki hau napep ki tafi gida, zan kawo miki motar gida".
"Kamar wani abun kake shiryawa a kaina" ya miƙa mata wayarsa, ta karɓa ta duba, message aka turo masa aka yi masa bayanin kar ta tafi a motarta, akwai yiwuwar a kamata, ko kuma ayi mata wani abu.
Bai bari ta yi wa su liti sallama ba, ya fitar da ita daga asibitin, ya tare mata abun hawa ta hau ta tafi tana mamaki.
Ta koma gida, duk a gajiye, abubuwa duk sun dame ta, tana ta tunanin ciwon Viper, tayi ta addu'a Allah ya bashi lafiya, sai ta ji ba ta kyauta ba maganganun da ta gaya masa, haɗuwarsu ta ƙarshe.
"Allah ka bashi lafiya, ka bani ikon cika masa alƙawarin da nayi masa"
"Arfa"
"Na'am" ta amsa tana daga zaune.
"Ina motarki?" Nasir yayi maganar yana shigowa cikin ɗakinta.
"Lalacewa ta yi, na bawa bakanike"
"Wane bakaniken?"
"Bakanike dai mai gyara mota"
"An ce an ganki da wasu maza a motar, a can ring road, sai dai ba a san in da ku ka yi ba, na saka jami'ai a arear in da ake tunanin kin bi, aka kama wani da motar yanzu haka yana tsare a wurina"
Ta miƙe tsaye ta ce "Wai dan Allah yaya me kake nufi da ni ne? Motata ta lalace zan yi gammo na ɗauketa a kaina ne, na kira masu gyara su tafi da ita sai ya zama laifi, na menene zaka saka a din ga bibiyata ma?"
"Saboda baki da gaskiya arfa, gaba ɗaya kin canza, kuma ba kya tsoron salwantar da rayuwarki"
"Kalli, kamar da gaske ka damu da rayuwar tawa, ba ta rayuwata kake yi ba, mafitar ka kawai kake nema Yaya Nasir, amma ai ramin ƙarya ƙurarre ne ka cigaba da bibiyata. Na roƙe ka ka saki bawan Allah, gyaran mota kawai na bashi, abun arziki bai kamata ya zama na tsiya ba" ta fita daga ɗakin gaba ɗaya ta bar shi.
Da daddare ta kira walid, ta ji ya jikinsa, ya tabattar mata jiki da sauƙi sosai, ya farka ma.
Nabila ta ce "Oga walid, shaye-shayen nan ne fa ya fara taɓa shi, ya janyo masa wannan matsalar"
"Ai bama sai kin faɗa ba, shi ne ba wani abun ba"
"Dan Allah oga walid ku daina wannan rayuwar, idan ba haka ba da ƙuruciyarku haka zaku rasa lafiyarku ku mutu, dan Allah" yayi murmushi ya ce"Karki damu, za a daina in sha Allah"
"Allah ya sa, ayi masa sannu dan Allah"
Ya ce "Zai ji in sha Allah" bayan ya kashe wayar, ya fita yana mitar ina ɗan mama ya tafi har wannan lokacin bai dawo ba.
A harabar Asibitin ya haɗu da ɗan mama, kamar ya kwaɗe shi, dan haushin abun da yayi, shi kuma bai gaya masa ainihin abun da ya faru ba, ya ce masa wani wuri yaje.
"Ka wuce ka je ka zauna da shi, liti ya je nemo wani magani, ni kuma zan je gida".
"Kar ka je gidan nan oga Walid, hanya babu kyau, cinnakun nan sun ɗana mana, akwai wani abu a ƙasa ka ɓad da sahu, ka lafe a wani wurin, akwaisu sosai a hanyar gidan nan"
Walid ya ce "Na fahimta, muddin kaga wani abu da baka yarda da shi ba, ka kira sanar mini" ya jinjina masa kai.
Nasir yana zaune ya gama cin abincin dare, aka kira shi a waya.
Ya ɗaga a take, ganin daga office ɗin su ne.
"Yallaɓai yaron nan fa, wasu sun zo sun yi belinsa"
"Wane yaron?"
"Wanda muka kama, kuma sun ɗauki motar ma"
Tashi tsaye yayi ya ce "What? Meyasa ku ka bari suka ɗauka? Waye ma ya ce a sake shi?"
"Manyanmu ne yallaɓai" mukullin motarsa ya ɗaukko ya fito da sauri, kawai ya tarar da motar arfa a gareji.
Bin motar ya din ga yi da kallo, dan ya tabattar ita ce, ko ba ita ce ba. Bai haƙura ba sai da ya dangana da zuwa ya dudduba ya tabattar dai ita ɗin ce.
Bai tsaya ba, ya shiga cikin gidan, ya tarar da ita a falo, suna kallo a falon ita da mutanen gidan.
"Arfa waye ya kawo miki motarki?"
"Ina ga bakanike ne, yaro ne ya kawo mini key ya ce an kawo motar" tayi maganar cikin ko in kula.
Ganin da mutane a wurin, ya sanya bai ja maganar ta yi tsawo ba, ya bar falon.
***
Liti yana zaune yana game a wayarsa, likita ya shigo, ya kalli likitan, likitan ya ce "Sannu ko, ya mai jikin?"
"Da sauƙi"
"Masha Allah, naga ya samu bacci ma, shi ne mai hepatitis ko? Yayi maganar yana duba file ɗin Al'amin. Kodayeke ma bacci yake yi, bari ba sai an tashe shi ba, idan aka yi x-ray ɗin na duba shi, idan ya farka gaba ɗaya" yayi maganar yana taɓa cikin Al'amin. Sai dai yayi shiru yana kallon Viper, yana ƙoƙarin ganin fuskarsa sosai, dan kamar ya san shi, sai dai yanayin kwanciyar da ya yi, bai bashi damar yin hakan ba.
Ya kalli file ɗin Al'amin, an rubuta Muhammad Ibrahim. Ya juya zai fita, ya tsaya ya sake waiwayowa ya kalli Al'amin ya ɗan yi shiru sannan ya fita.
Yayi iya ƙoƙarin sa wurin tuna a ina ya san shi, amma ya kasa dan haka dolensa ya haƙura.
***
"Rahama"
"Na'am"
"Zan fita da ke, zamu je asibiti, wallahi idan ki ka yi misbehaving, ke da ganin mahaifiyarki har abada"
"Idan da zan yi misbehaving, da tuntuni da kake fita da ni da nayi, amma na fara gajiya da ƙaryar da kake yi mini, na cewa gwargwadon bin umarninka da nake yi, shi zai sanya ka sada ni da mahaifiyata. Ina tsoron tonuwar asirina na wulaƙanta a idon duniya, shiyasa bana yi maka ihu, da neman agaji, sonake ka mayar da ni cikin sirri da rufin asiri, yadda ba zan tozarta da yawa ba, amma haryanzu na kasa gane in da ka dosa"
Ya ce "Zaki fahimta ne, muddin ki ka yi yekuwa, to ke zaki kunyata fiye da ni, kuma ni zan iya wanke kaina, ke kuwa zaki tozarta, dan sai kin samu masu ɗoraki a social media kowa ya ganki, kin san duk abun da namiji yayi ado ne"
Ta girgiza kai ta ce "Wannan wani banzan tunani ne, na waɗanda ba su san girman Allah ba, babu al'ada a batun saɓon Allah. Allah bai ware wutar mace ba, kuma bai ware ta namiji ba, bai ce zai sassautawa wani ba dan yana wani jinsi idan ya saɓa masa ba, dan haka babu ado da zunubi, idan al'ada ta nuna maka duk abun da ka yi ado ne, addini kuma ya koyar da kai tsoron Allah da tsoron azabarsa"
Wato ramma akwai baki, wasu lokutan duk abun da yake ji da shi, sai ta ƙure shi ta hanyar kafa mishi, hujjoji da addini, dan haka ya ja bakinsa yayi shiru, suka cigaba da shiri.
Tana sanye da niƙab, a kan dogon hijjabinta, yake nuna mata wurare a cikin asibitin, wai nan ma branch ne na Asibitin, ba shi ne main branch ɗin ba, sai dai yayi kyau ya tsaru sosai da sosai.
Washegari da safe Nabila ta je court ɗin da take da trial, tayi ta kammala, ta samu wurin parking, ta bayar da ajiyar motar, ta hau napep ta fita asibiti.
"Ki zauna a nan, zan je na fara zagaywa na duba marasa lafiya na, sai na zo na tafi da ke, in da zan duba ki"
Ta kalleshi ta ce "To ka tafi da ni mana, ni ba wani abun zan yi ba"
"So ki ke sai wani ya ganki wai?"
"Matsalar rashin gaskiya kenan"
"Eh na ji, ga kayan tea nan, fridge akwai lemuka, ga kayan kallo nan, ki yi duk abun da ki ke so, ban da fitina, zan rufe ki a nan, zan je na ga marasa lafiya, sai na yi ward round na dawo"
Ta ce "Saura ka daɗe"
Abdul ya ce "No ba zan daɗe ba in sha Allah" yayi kissing goshinta ya ce "I love you, ki yi mini addu'a na yi komai cikin nasara"
"To jeka, kar su gaji da jiranka" haka kurum ya din ga jin is no safe, ya bar ta nan, kamar wani abu zai faru, ya din ga waiwayawa yana kallonta, har ya fita ya rufeta a wurin.
Nabila ta shiga cikin Asibitin, tana saanye da hijjabin da ta ɗora a kan uniform ɗin ta da facemask, sai waya take yi, tun da ta taho, wata matashiya da ita ma tahowa take yi, suna facing ɗin juna, take bin ta da kallo. Ji take yi, tamkar ta je ta ɗage facemask ɗin fuskar Nabila taga wacece, har ta wuce hanyar da yakamata ta tabi.
Wayarta ce ta fara vibrating, ta ɗaga ta ce "Hello yaya"
"Dalla malama kina ina, gashi ya zo, zai fara ganin marasa lafiya, ki zo ya fara da ke na mayar da ke gida, amma kin tafi yawonki" kasa bashi amsa tayi, ta ɗaga kai tana dube-dube, ta nemi Nabila ta rasa.
Jiki a sanyaye ta shigo office ɗin, saifu kamar ya mareta ya ce "Wai ina ki ka tafi, yazo ya zauna yana jiranki?" Bata amsa ba, ta zauna jiki a sanyaye.
Abdul ya ce "Dan Allah ka daina yi mata tsawa, ka san mara lafiya ce, ba na son naga ana kyarar mini patient, Hafsat ya aka yi ne?"
"Doctor Abdul, jauhar fa na gani ta saka niƙab ta wuce"
Ya ce "Wacece haka?"
Saif ya ce "Na fuskanci ba ta warke daga depression ɗin nan ba, likita ya sallameta, ƙanwarmu da ta mutu fa take magana a kai"
"Wallahi yaya, ka taso mu bi hanyar da ta bi, ka ganta kaima, ta saka niƙab"
"Kuma da niƙab ɗin ki ka ga jauhar ce?"
Ta ce "A'a, gani nayi kamar na santa, kuma wallahi irin idonsu ɗaya, ai naga idonta"
Abdul ya yi murmushi, ya fara bin hanyoyin su na likitoci, wurin daidaita tunanin hafsa, da saka mata nutsuwa.
Nabila tayi sallama. Al'amin yana zaune, ya jingina da jikin gadon, yana ɗan yamutsa fuska.
Suka gaisa da ɗan mama, shikaɗai ne a wurin, ta ƙarasa gabansa ta ce "Sannu ya jiki?" Ya jinjina mata kai alamar da sauƙi.
"Kaga ɗaya daga cikin illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ko? Kodayeke zuwa yanzu ai ba illa ɗaya ka gani ba, illoli daga dabar shaye-shaye da bangar siyasa wanne yayi maka rana a cikinsu? Daba da bangar siyasar a dalilin su, ka rasa makusantanka, ka rasa soyayyar mahaifi da ta ƴan uwa, illar da aka yi maka, ka kasa karɓar ƙaddararka, ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ya sanya, ka nemi ka rasa imaninka, ka halaka kanka, yanzu gashi lafiyar ka ta taɓu, gaba ɗaya abubuwan nan babu wanda zaka ɗaga na ce ga ribar da ka samu a dalilin su, dan Allah ka cikawa yar madara burinta, duk da bata duniya, ka zama mutumin kirki, ka zame mata sadaƙatul jariya, ya zamana bata raye, amma tana da kamashon ayyukan alkhairin da zaka yi idan ka zama mutumin kirki, tun da ita ta ɗaukko hanyar saita rayuwarka bisa hanya mai kyau" kamar ba zai yi magana ba, sai ya buɗe idonsa ya zuba mata ido.
Ita ma shi take kallo, amma ta yi ƙoƙarin janye nata idanun daga nasa.
Ya zuba mata ido kamar zai haɗiyeta, hatta maganarta wani abun idan tayi, kamar Jauhar.
"It all depends on you" ya furta yana cigaba da kallonta.
Ta ɗago ta kalleshi, "Ke zaki ƙarasa abun da ta yi niyyar yi, ta hanyar cika mini alƙawarin da ki ka yi mini. Na gode da ki ka taimaka mini, ban rasa imanina gaba ɗaya ba, tabbas a duniya daba da shaye-shaye basu tsinana mini komai ba, sai asara kashi-kashi wata na bin wata. Abu ɗaya nake fata, ko da ba zan rayu ba, naga an hukunta wanda suka kashe mini mata ba tare da hakkinta ba, shi ne babban fatana, ke ki ka cusa mini aƙidar in ɗauki mataki ta hanyar shari'a ba hanyar da nake so nake ganin ita ce dai-dai ba. Ba wai ina roƙonki bane ba, kina da zaɓin yin abun da ki ke ganin shi ne dai-dai a gareki"
A ƙasan zuciyarta ta ce 'Ai ba zaka canza ba"
Kiran sumayya ta gani a waya, ta ajiye ledar kayan marmari da ta shigo da su, ta fita amsa waya.
Ba ta san dalilin kiran sumayyan ba, dan haka ta nemi hanyar da zata nesanta ta, da wurin shige da ficen mutane.
Tabi wata hany, ta ɓulla wani wuri da babu kowa, ta tsaya a wurin ta ciro wayarta ta ɗaga ta ce "Hello, Sumayya T ladan baki abun magana, maƙogwaron kakaki radio".
Gaban ramma ya faɗi, jin muryar mace a wurin office ɗin, sunan wadda aka ambata ne ya daki zuciyarta, Sumayya T ladan, tana jin program ɗin ta, sai dai a rufe take a cikin office ɗin babu hanyar fita.
"Ba shakka Nabila Yusuf maitama, ni kike kira da ni da sunan ubana ko?"
"To ai kin rama, ya ne ya ake ciki, ya gidan radio?.
Abdul ya shiga ɗakin da Viper yake, da shi da wata Nurse da take on duty.
Ya kalli ɗan mama ya ce "Ina mara lafiyan?"
Ɗan mama ya ce "yana banɗaki"
Ya ce "Ok, sister je ki room 4 ki duba mini temperature yaron nan, kafin na zo" ta ce "Ok sir"
Ya tsaya yana dudduba medication ɗin da aka yi chatting, ya juya baya yana amsa waya Viper ya fito, ya nemi wuri ya zauna a kan gadonsa, ya gama amsa wayar ya juyo, idonsa suka shiga cikin na Viper.
Ƙiris ne ya rage bai yar da wayar hannunsa ba, an kusa shekara bakwai rabonsa da Viper, tun wata haɗuwa da suka yi, ya zo hutu suka kusa faɗa P.A ya gargaɗe shi a kan hakan, Viper ya ƙara girma, kwarjini ya ƙara baibaiye shi.
Shi bai san abun da ya faru ba, shi dai ya daina ganinsa a wurin mahaifinsa, ya ji labarin kisan kai yayi, aka rufe shi, sai kuma yaji mahaifinsa yana nemansa, kasancewar shi ba mai shiga abun da babu ruwansa bane ba, sam bai damu da sai lallai ya ji meyake faruwa ba.
Da ido Viper ya yi wa Ɗan mama magana, ɗan mama ya taso, ya zo, Abdul bai gama tunanin ba, Viper ya zare wuƙar da ke ƙugun ɗan mama, ya fuzgo labcourt ɗin Abdul, ya zauna a gabansa. Ya kalli ɗan mama ya ce "Ka gindaya katanga, ba shiga babu fita" ɗan mama ya jinjina kai ya fice, ya rufe su ta waje.
"Ka yi mamakin ganina ko? Nima mamakin ganinka nake yi, haka mahaifinka ya adana rayuwarka, ni kuma ya tagayyara tawa, ya bar ni da yawon ramuka ina ɓoye kaina, tamkar maciji, kodayek macijin ne ni, ina nan zan yi fitar burtu daga ramin, zan yi masa sara mafi muni, da zai yi ajalinsa"
"Da mahaifina kake yi, ni meye nawa a cikin abun da ya haɗaku?"
Viper ya saka masa kaifin wuƙarsa a jijiyar wuyansa ya ce "Kai likita ne, na san ka san ma'anar wannan jijiyar, kuma ka san mai hudata yake nufi ga rayuwar ɗan adam, idan ka yi wani yinƙuri da bai gamshe ni ba, zan yi wa jininka magudana zuwa doron duniya. Ya saka hannu ya ciro wayar Abdul daga gaban labcourt ɗin sa, ya ce masa "Buɗe ta"
Ya karɓa ya buɗe masa, Viper ya karɓa yayi danne-danne a ciki, sannan ya miƙa masa ya ce "Gashi nan, zan tura masa saƙo mai muhimmanci ta hanyarka, kafin nan ka gaya masa, zan cigaba da farautarsa babu dare babu rana, sai na ɗaiɗaita farincikin sa, ni ƙarfen cikin wuta ne, hannun da yake ƙoƙarin sakawa dan ya kamani, idan nayi masa illa, sai ya nakasa, nakasa kuma ta har abada. Ƙarfen da yayi yinƙurin yin amfani ya ɗaukko ni, wutar tayi masa zafin da na riga na narka shi, ba kowane irin ƙarfe ne zai ciro ni ba. yana gama maganar ya hankaɗa Abdul da hannu ɗaya, sai da ya faɗi ƙasa.
Nabila kuwa babu yadda ba ta yi ba, ta shiga, ɗan mama ya hanata, ya ce likita ne yake duba shi, ya ce su fito waje.
Ita kuma ga sumayya na jiranta, tana ta tuna mata lokacin program ɗin su ya kuss, ga barrister Habib yana ta kiranta shi ma, dan haka kawai tayi masa sallama, ta ce za suyi waya.
Ɗan mama ya ce "Jiya bayan fita ta da motarki yayanki da kansa ya kama ni fa"
"Ina ta son na yi maka magana, ya aka yi kuma ya sake ka".
"Waɗanda nake yi wa aiki ne suka karɓo ni, na kawo miki motar ki gida, na bayar da mukullin aka kai miki ciki"
Nabila ta ce "Suwa ka ke yi wa aikin kenan?"
"Ai sauri ki ke yi, kuma ya saɓa dokar aikin da nake yi, ki kula sosai yayanki tarko yake yi miki ko ta ina, siled mistake zai iya kama ki" ta ɗan yi shiru sannan ta jinjina masa kai ta ce "Na gode"
Cikin ɗakin kuwa da sauri Abdul ya tashi, ya shafo wuyansa da wuƙar Viper ta fara yankarsa, ya ga jini, ya ja da baya a hankali yana kallon Viper, ya nufi hanyar fita ya jijjiga ƙofar da ƙarfi, ɗan mama ya buɗe, ya fice cikin matsanancin hanzari, ɗan mama kuma ya shiga.
Wuyansa ya cigaba da tsatstsafar da jini, ya fita gate wurin security, ya ce su hanzarta, su shiga amenity 2, su kama wanda yake cikin ɗakin, babban ɗan ta'adda ne, da jami'an tsaro suke nema" nan da nan suka tashi da gudu, suka yi cikin Asibitin.
Ma'aikatan suka ce, ya tsaya ayi masa treatment ɗin wuyansa, ya ce musu a'a, ya je ya buɗe Office ɗin sa, ramma na ciki ta kwanta a kan couch ɗin ɗakin tana bacci, ya danƙota daga kan kujerar, sai da ta razana, ya fita da ita da sauri, ta ce "Abdul lafiya kuwa? Menene wai?"
"Akwai matsala ne" ya faɗa lokacin da ya sakata a mota ya rufe.
Suna tafe a hanya ta ce "Meyasame ka a wuya ne? Wai me yake faruwa?"
"Wani patient ne mahaukaci, ya yanke ni a wuya"
Cikin tausayawa ta ce "Subhanallah, sannu Allah ya sauwwaƙe, kuma baka tsaya ka saka magani ba"
"Bakomai, idan muka je gida na saka"
Security kuwa suna zuwa suka tarar da ƙofar ɗakin a buɗe hanhai, sai dai babu kowa a ciki.
Suka dudduba har cikin banɗaki, amma babu kowa.
Suka je suka rufe gate, aka hana kowa shiga da fita, tuni aka sanar da jami'an tsaro, Viper kuwa da ɗan mama tuni suka dire katanga, ya kira su walid ya ce kar su dawo, asibiti babu lafiya, Viper ya haɗu da ɗan gidan indabo.
Liti ya ce "Maganar banza kenan, kuna daidai ina mu zo mu same ku?"
Viper ya ce "Ba sai kun zo ba, zamu zo mu same ku"
Sai da ya kai ramma gida, ya zauna ya yi wa kansa dressing, aka kira shi a waya, aka ce ya je yan sanda za su ɗauki report ɗin abun da ya faru.
"Kai ba zan sake dawowa wurin nan a yau ba, sai an tabbatar da security wurin"
Ɗan sanda ɗaya ya karɓi wayar, ya ce "Doctor, to ko zaka gaya mana wani ɗan ta'addan ne?"
"Aminu Viper ne, wands ake cewa mai zamani da".
"Mai zamani kuma, yallaɓai Viper fa"
"Eh shi fa"
Ɗan sandan ya ce "Ok to" Nan da nan suka kira DSP Nasir a waya suka sanar masa.
Nabila bata san abun da yake faruwa ba, ta ƙarasa gidan radion su sumayya, sai da suka yi faɗa da sumayya, saboda lokacin shirin ya ɗan ja sosai, sai itakaɗai ta fara program ɗin.
Sai da ta nutsu, suka gama faɗan dai-dai lokacin aka dawo daga talla, sumayya ta gabatar da ita suka ɗora da program.
Yau ma dai program ɗin na su, a kan abun da ya shafi harkar shari'a ne, kanta tsaye take bayyana ƙulle-ƙulle da rashawar da ta yi katutu a harkar shari'a.
Nan ta tabattar da cewa zasu yi appeal, a kan shari'ar ramma, kuma tana fatan hukumar shari'a zata sanya ido sosai a kan yadda shari'ar zata gudana.
Sumayya ta ce "Yanzu dai kina da hope kenan, a kan appeal ɗin da zaku yi?"
"Sosai kuwa sumayya, kuma ina nan a kan bakana, lauyoyin gwamnati da bunkure foundation su gabatar da victim a gaban kotu, kuma ina da kyakykyawan fata a kan wannan shari'ar, sannan bayan haka akwai tarin ƙulle-ƙulle da zan warware a wannan zaure, masu tarin ban mamaki"
"To shikenan, da ni da masu sauraro muna dako, duba da yanayin lokaci, baki samu shigowa da wuri ba, da haka da haka nake cewa muna nan muna saurarenki, domin jin wane irin ƙulli zaki warware mana.
The lady of her words, the young capacitated barrister, gugan ƙarfe sha kwaramniya iron lady, kuma boss lady, voice of voiceless Barrister Nabila Yusuf maitama ayi sallama da masu sauraro"
Dariya Nabila ta din ga yi ta ce "Kirarin nan naki dariya yake bani Sumyya, ai ke ce voice of voiceless, baki abun magana, a sayar da a tsage gaskiya, the lady of the century Sumayya T ladan, Allah ya ƙara kiyaye mana ke, masu sauraro Assalamu alaikum" suka ƙarƙare shirin cikin nishaɗi da dariya.
Tuni Nasir ya isa asibitin, ya fara investigation, aka ɗaukko masa file ɗin Viper da aka buɗe, sai dai babu lambar waya a jiki, ya ce meysa babu lambar wayar mai file, record suka ce, emergency aka buɗe file ɗin, kuma ba su ne a shift ɗin da aka buɗe file ɗin ba.
Ya saka security su kawo masa littafin da masu shiga da fice suke rubuta sunan su a ciki, aka kawo masa yana dubawa, babu wani sanannen suna a ciki, sai dai ya tsaya cak, ganin sunan Nabila a cikin book ɗin.
Nabila kuwa ta ɗauki hanyar titi, bayan ta ɗauki motarta, tana tafe yau jinta take sakayau, kwanakin da ta yi cikin takaici, zuciyarta tamkar an wanke mata ita.
Ta kalli glass ɗin motarta, ta ga wata babbar mota ta taso ta a gaba, idan ta kauce, ta bar hannun ta bawa motar dama ta wuce, sai motar ta rage gudu, ganin ba zasu bata damar tafiya cikin kwanciyar hankali ba, ya sanya ta ɗauki titi sosai, ta wuce su, amma suka cigaba da binta by fire by force ita suke hari!.
(Am sorry for delayed posting, am sick ayi mini addu'a please)
Ayshercool
08081012143
69
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Al'amin da ɗan mama suna kwance a cikin ciyayi, in da suka ɓuya nesa da Asibitin sosai.
Suna ta jin kai komon motocin yan sanda, ɗan mama ya kalli Viper, ya ga yadda yake rintse idanunsa, yana damƙar ciyayin wurin, ya ce "Sannu oga Viper, cikin ne? Ko wani asibitin zamu tafi?" Ya girgiza masa kai alamar a'a.
"To tun da da cannula a hannunka, kaga magungunanka da na kwaso, naga suna yi maka wannan allurar, ina ga ita ce ta ciwon cikin, bari na yi maka"
Viper bai ce masa komai ba,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 72 Chapter of 121