ɗin da take faɗa a kanmu"
"Kaga P.A, dan Allah ka ƙyale ni haka, gaba ɗaya maganganunka ba alheri yau, tashi ka tafi dan Allah"
P.A ya ɗan yi shiru, sannan ya tashi ya fita.
***
Yanayin da Abba ya fito falo, ya tabattar musu da ba lau ba, fuskar nan a murtuke babu annuri.
Ya kalli baba magajiya ya ce "Kira wo mini Nabila" sai da suka kalli Abba, jin ya ambaci Nabila, maimakon Arfa da ya saba kiranta.
Nabila na kwance baba magajiya ta shigo ta sameta, ta ce "Arfa, babanki yana kiran ki" sai da ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, gani nan zuwa" baba magajiya ta fita daga ɗakin.
Da ƙyar Nabila ta tashi, ta nufi falon, ƙirjinta na ta bugawa da sauri.
Kusan kowa ya hallara a falon, ita kawai ake jira.
Ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Abba, ta ce "Abba gani"
Mama ta ce "Munafuka ga ladabin kura"
Umma ta ce "Ki yi shiru, karya haɗa da ke".
"Dama irin tarbiyyar da na baki kenan? Ki je ki dinga bibiyar 'yan iska a waje?"
Gabanta ya faɗi, ta ɗaga kai ta kalli Nasir ta koma ta sunkuyar da kai.
"Har muka yi zaman kudancin Najeriya, muka gama ki ka yi jami'a, duk baki lalace ba sai yanzu? Ina ke ina bibiyar ɗan daba, ɗan ta'adda kuma ɗan iska da hukuma take nema? Kin zama 'yar iska lalacewa ki ke so ki yi ko, ko ma in ce ki ka yi?"
Falon yayi tsit, baka jin sautin komai, ƙarar gudun A.C, sun yi cirko-cirko suna kallon Nabila.
Tuni ta fashe da kuka, jin yadda maganganun Abba, ke dukanta.
Abba ya ce "Nasir ya gaya mini komai, da duk bana yadda, yanzu sakamakona kenan a wurinki ko? Sakamakon tarbiyya da ilimin da na baki kenan, ki ƙare a ɓoye mai laifi, azo kama shi a haɗa da ke, ki tozarta ni ki zubar mini da mutunci"
Cikin ƙulewa mama ta ce "Wane sakamako ka ke saka ran samu daga tsintacciyar mage, ai ba zata taɓa mage ba, shiyasa nayi ta ƙoƙarin ankarar da kai tun a baya, uban wani ba ya zama na wani, yanzu duk da fifikon da ka nuna mata, bai hanata nuna maka, ita 'yar kunama ce ba, duk gidan nan babu wanda yake janyo maka magana sai ita, yayanka suna zaune lafiya amma ita kullum cikin ɗaga mana hankali take"
Baba magajiya ta ce "A'a fa, dan Allah ki sassauta maganganun nan, sun yi tsauri da yawa"
Nabila kuwa da a zahiri ta nuna tashin hankali da nadama, cikin zuciyarta kuwa babu alamar hakan, ta yakice gumin fuskarta da yake ta tsatstsafo mata ta ce ""Abba ba mummunan sakamako bane ba, abin da ka tarbiyyantar da ni a kai ne, gaskiya ita ce nake tsaye a kai. Yakamata ayi mini adalci aji ta bakina, ba a goyi bayansa kawai ba ace ni ce bani da gaskiya ba. Wallahi Abba ni ba bibiyar yan iska nake ba, aikina kawai nake yi".
Mama ta ce "Har wata gaskiya ce da ke....
Abba ya ɗaga mata hannu, ya dakatar da ita, ya ce "Ya isa haka, ki tashi ki je, bana ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin shi ne dai-dai, tun da a kan gaskiyar ki kike"
Cikin tashin hankali ta ce "Abba baka son ganina fa ka ce, me aka gaya maka har haka a kaina ya sanya ka yanke mini wannan hukuncin "
"Abun da ki ka aikata aka gaya mini, muddin kina neman zaman lafiya da gudun ɓacin raina, dole ki bawa ɗan uwanki cikakken haɗin kai, ya gudanar da aikinsa, ki fita daga wannan lamarin, kafin a saka ki cikin masu laifi a kama da ke.
Duk wahalar da yaron nan yake yi, kina ji kina gani, amma kika ja bakinki ki ka yi shiru, har barazana ake yi masa na kora, muddin bai kama mutumin nan ba, amma ki ka zagaye ki ka je ki ka ƙulla alaƙa da shi, kin fara bani tsoro Arfa"
Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata? Yakamata ka ji ta bakina abba, na karɓi aikin nan ka fahimce ni Abba"
Bai tsaya sauraronta ba ya ce "Sai dai kin nuna mini ba ni na haife ki ba, na gode" yayi gaba zai bar falon.
Cikin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta ce "Haba Abbana, idan har zan rayu kana fushi da ni, me yayi mini saura a duniya? Ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce" ta yi maganar tana kuka mai ratsa zuciya, tana sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa yayi gaba.
Yana bari falon, tamkar su cinyeta ɗanya, suka yi kanta da surutu, kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.
Ɗakinta, ta shiga ta buɗe drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ɗin ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ɗauki wayarta tana dannawa.
Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri.
A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri.
Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, Nasir ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kin shirya aikata abun da Abba ya umarce ki ko kuwa? Ina zan kama Viper"
Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce "Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada,ka je can ka neme shi, yaya Nasir ka fita ka rabu da ni dan Allah".
Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, "Yanzu duk kukan da ki ka yi a falo, ƙarya ki ke yi kenan?"
A hasale ta ce "Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa. Ba dai ka je ka gaya masa ƙarya da gaskiya abun da ka ke so ba? Shikenan, amma kar ka sake yinƙurin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki ka taka a hankali kar ka faɗo cikin aikina"
Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce "Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa Nabila? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka? Sai da na zauna na nutsu, nake tunani, kenan duk hanyoyin da nake bi, dan na samu na kama mutumin nan, ke ce ki ke toshe su ko? Ki ke taka doka yadda ki ke so Nabila"
Ta waro masa idanunta ta ce "Doka ko? Ni iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙarin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba. Ka rabu da ni muje a kan Sharrin da ka yi mini, ina bin ɗan daba a waje" hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita.
Yana fita ta dafe kanta, saboda yadda yake wani irin sara mata, ta kira Sumayya a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga.
"Salamu alaikum"
"Wa'alaikum Salam, sumayya dan Allah kina ina ne?"
"Gida, ban daɗe da dawowa ba ma"
"Dan Allah idan kin huta ki zo gida, ina son na ganki, ina cikin matsala ne, ba zama a bari na fito ba"
"Subhanallah, wace irin matsala kuma?"
"Ni dai ki zo dan Allah"
"Shikenan, bari na canza kaya na zo kawai"
***
Tamkar an ɗora masa gingimemen dutse a kansa, haka ya buɗe idanunsa da ƙyar, ya na ƙoƙarin tashi, ya ce "Masa oga kar ka tashi, ka huta tukuna"
Madaki ya ɗaga kai da kyar, ya ganshi a dabarsa ya ce "Ya aka yi na zo nan?"
"Yaran mai zamani ne, suka kawo ka, suka ce wai gaka nan ajiya, zai waiwayeka, amma oga ya na ganka da ƙafa ɗaya, sai nemanka muke yi da kai da lakwari babu wanda ya san in da kuka shiga?"
Ya kalle shi ya ce "Akwai wanda suka san na dawo?"
"Eh mana, su fidda na kogo, duk suna nan aka kawo ka, labari ma ya fara zagawa cewar an cire maka ƙafa ɗaya"
"Wani taimako nake so ka yi mini, amma bari sai na wartsake, kaina kamar an kunna wuta a cikinsa, kamar ana narka mini ƙwaƙwalwa, bari abun nan ya sake ni"
"To shikenan, sannu"
*****
Sosai Nabila take yi wa sumayya kuka, tana gaya mata abubuwan da suka faru.
"Nabila, shiyasa tun da fari na ja miki kunne, babu wanda zai tsaya ya saurareki balle ya fahimce ki, gaskiya ina bayan Nasir, ko dan rayuwarki, yakamata ace kin ajiye wannan shirmen da ki ke yi, ni babban tashin hankalina haukan da ki ka yi wai son shi ma ki ke yi".
"Laifi ne dan ka tsayawa wanda aka zalunta?"
"Aka zalunce shi a gidan uban wa, mutumin da ya yi kisan kai? Kisan kai fa yayi. Kuma babban tashin hankalin son sa da ki ka fara yi. Ba zaki taɓa ganin laifinsa ba, mutuncinki ya zube a banza, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza, wallahi hukuncin da Abba ya ɗauka a kan ki, yayi dai-dai duk wani abu na shaida ko hujja, ki tattara ki ba wa Yaya Nasir, a kama shi kowa ya wuce wurin, kan ki janyo wa mutane magana, ni ba a kyauta mini ba, da bai haɗa woyoyinki ya ƙwace ba, ya bar ki da su" Ta ƙura wa Sumayya ido, yadda ta ɗauki zafin nan, babu alamar za ta tsaya ta fahimce ta, kawai ta yi mata shiru, ta gama masifarta, ta tashi ta fita.
Tayi shiru, gaba ɗaya ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ta ji gaba ɗaya duniya tayi mata zafi, rana zafi inuwa ƙuna, ta rasa ina zata kama, wurin wa za ta je taji sauƙi.
Gari ya waye, Nabila ta shirya tayi ficewarta wurin aiki, ba wanda ta kula, ta yi ficewarta ta tafi.
Ofishin barrister Habib taje, ta jira shi, ta samu wuri ta zauna, tana jiransa.
Kallo ɗaya yayi mata, ya buɗe ofishin sa, ya ce mata "Taso"
Ta tashi ta shiga, suka zauna, ya kalleta ya ce "Ina jinki yau kuma menene?"
Nan ta kwashe komai ta zauna gaya masa.
Ya ce "Ai dama na gaya miki, dole ki fuskanci ƙalubale, ki yi haƙuri, komai zai wuce, gobe in Allah ya kaimu kotu zata zauna a kan case ɗin su rahama, sannan zan cigaba da duk wani ƙoƙari na baki dukkanin goyon bayan da ki ke buƙata, amma mu cigaba da addu'a"
"To yaya Habib, kai kaɗai ne ka fahimce ni, kotu na yanke hukunci zamu shigar da ƙarar kotu ta tilasta wa bunkure foundation fito da ramma, tare da gurfanar da ainihin wanda ya aikata laifin".
"Ki yi haƙuri ƙanwata, nasara na tare da ƙalubale, ina yi miki fatan alkhairi da fatan nasara".
A sanyaye ta ce "Na gode"
"Amma Nabila, a ina zaki yi generating shaidun da zaki shiga kotu da su, a kan case ɗin Viper? A ina zaki ganshi?"
"Na ma ganshi, na riga na tanadi duk abun da nake buƙata, domin fuskantar shari'a"
"You can do it my dear, kuma in sha Allah za ki yi nasara, akwai yiwuwar zan je na samu major da kaina, nayi masa bayani"
Ta girgiza kai ta ce "No need, kar ka je, hakan ba zai sauya komai ba"
Ta miƙe ta nufi hanyar fita, tana duba message ɗin da ya shigo wayarta.
"Mu haɗu a garden, idan baki da aiki"
Tayi masa reply da "On my way".
Yanayin yadda take tafe, tana jefa ƙafa, ya tabattar masa da a cikin damuwa take.
Tana zuwa gabansa kawai ta nemi wuri ta zauna, ba tare da ta ce masa uffan ba.
Ya samu wuri ya zauna a gefenta ya ce "Ya aka yi ne?" Ta girgiza masa kai alamar babu komai.
"Akwai mana, fuskar ki ta nuna"
"Kowa yaƙi fahimta ta, Abba yayi zazzafan fushi da ni, wai sai na bawa yaya Nasir haɗin kai ya kama ka, ya je ya gaya wa Abba ƙarya da gaskiya, sam Abba yaƙi saurarara ta, sumayya taƙi fahimta ita ma, barrister Habib ne kawai ya fahimce ni, Vi na rasa ya zan yi, zuciyata zafi take yi mini, Nasir ya cuce ni, ya haɗa ni da Abba"
"Yanzu zaki ba shi haɗin kai ya kama ni kenan?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba, ba zan iya bari a kama ka ba".
"Meyasa?" Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Ka sani ai"
"Ban san komai ba"
Cikin basarwa ta ce"Kawai ina so ayi wa matarka adalci ne, kuma a hukunta wanda suka yi maka laifin"
Ya ce "Gwargwadon yaya ki ke son yar madara?"
"Gwargwadon yadda nake son ka"
"Ki ke son wa?" Yayi maganar ƙasa-ƙasa.
Kasa jurewa tayi, duk jikinta yayi sanyi, ta kasa kallonsa, gashi ya matso daf da ita sosai.
"To ungo share hawayen" yayi maganar yana bata handkerchief ɗin sa.
Ta karɓa, amma ta kasa gogewar, ta cigaba da kuka.
"Dan Allah kar ki karaya, ina ƙara jaddada miki, da Allah na dogara da ke na dogara, amma idan kin ga matsin yayi yawa, ki bayar da kai bori ya hau, ki bashi dama ya kama ni" ta girgiza kai ta ce "A'a, ba zan iya bari a kama ka ba" tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.
"To ya isa haka kukan, ga wata 'yar ƙaramar kyauta zan baki" yayi maganar yana sake bata envelope ɗin da ya bata wancan karon.
Ta saka hannu ta karɓa, tana goge hawayen, tana buɗewa ƙananan hotuna ta ciro guda biyu, wadda ta yi tozali da ita a jikin hoton ce, ta sakata razana, ta kalli hoton, ta kalli Viper ta shafa fuskarta ta ce "Wace wannan?"
"Ni ma ban sani ba"
"Yaya zaka bani abu ka ce mini ka ce baka san wace ba? Wannan....wann... Kai wannan ba ni ba ce ba, bani ce a jiki ba, yaushe aka yi wannan hoton ban sani ba? Kai wallahi bani ba ce ba, wacece wannan meyasa take kama da ni" ta yi maganar tana kallonsa, idanunta yake kalla, amma bai yi magana ba.
"Kayi mini bayani, ka yi magana wacece wannan" tayi maganar kamar zata zare, tana riƙe rigarsa tana zazzaro masa ido.
Ayshercool
08081012143
74
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
KU KASANCE DA LITATTAFAN BRIGHT PENS A SECOND BATCH, NA ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL).
MUTALLAB (NIMCYLUV)
ZAYTOON (ZEE KUMURYA) DA HADARIN GABAS (NAZEEFA SABO NASHE)
Idanunta yake kallo, jikinsa a sanyaye amma yayi shiru bai yi magana ba.
"Kayi magana, ka gaya mini wacece wannan? Bani ba ce a jiki, amma meyasa take kama da ni? A ina take?"
Still bai yi magana ba, ƙara tsananta riƙon da tayi masa ta ƙara yi, cikin matsanancin kuka tashin hankali da ƙaraji, take jijjiga shi ta ce "Ka yi magana, ka gaya mini wacece meyasa take kama da ni? Kuma a ina take?"
Viper ya ce "Ban santa ba, tsintar su nayi, naga ya dace kema ki gani, ban taɓa jin kin ce kina da yar uwa da ku ke ciki ɗaya ba, amma kamarku ta ɓaci da ita, shiyasa na ga ya dace na baki ki gani"
"Ka san wacece, ka saba yi mini wasa da hankali wasu lokutan, Please na roƙe ka, don't play with my emotions, ka gaya mini dan Allah" tayi maganar tana kallon ƙwayar idonsa.
Ya ɗan jima yana kallonta, kan ya saka hannu ya cire hannunta daga riƙon da tayi masa, yana riƙe da hannunta ya ce "'yan gidanku yakamata ki tambaya bani ba"
"Tayaya zan tambaya? Alhalin a duniya babu abun da Abba ya tsana sama da nayi masa zancen mahaifina, ban san dalilin wannan mummunar ƙiyayyar ba, sun yi abun su ya riga ya wuce, amma ya nesan ta duniyata da mahaifina, duk wata hanya da zata saka na san in da yake, Abba ya tosheta wai ba wani abu da zai tsinana mini. Wani abu ne mai ciwon gaske da yake addabar zuciyata, ka fama mini ciwon da yake zuciyata, kuma ka bar ni a duhu, ka taimaki rayuwata wallahi ko Wacece wannan tana da alaƙa ta kusa da ni"
Viper ya ce "How, an ce kowane mutum akwai irinsa guda uku a duniya...
"Ba wani guda uku, wannan kamar nice a jikin hoton, kamannin nan sun yi yawa, ka wayar mini da kai dan Allah"
"Me ki ke so na ce, duk abun da zan faɗa miki ƙarya zan yi miki, ki je gidan abun da suka ce miki shikenan"
Ta fizge hannunta, ta yinƙura zata tashi, jiri ya kwasota ta hau tangaɗi, ya riƙe ta, ta ɗan yi shiru ta samu nutsuwa, ta juya ta bar wurin.
***
Ramma kuwa kwana suka yi, Abdul yana juye-juye, ciwon cikinsa ya tashi, ko baccin kirki ba su yi ba, sai bayan sallar asuba ya ɗan lafa masa, ya din ga tofa fatiha da bisimillah tana bashi yana sha.
Yana kwance a kan cinyarsa, tana ta shafa masa ruwan tofin a kan cikin, tana shafa masa, ya riƙe hannunta yana mayar numfashi.
"Sannu Abdul" ya jinjina mata kai alamar yauwwa.
"Wai wannan ciwon cikin, ka dudduba kanka sosai mana, kana likita amma ka din ga wasa da lafiyarka, kalli yadda ka ke shan wahala dan Allah"
"Tausaya mini ki ke yi?"
Ramma ta ce "Duk rashin imanina, idan ban tausaya maka wannan wahalar ba, ya zan yi, idonka har ja yayi saboda wahala".
"Rahama ina ga ciwon cikin nan ne zai yi ajalina, har ƙasashen waje na je, an kasa gano menene"
Dummm ta ji ƙirjinta ya buga, jin abin da ya ce, amma ta ce "Dan Allah ka daina wannan maganar, ka din ga addu'a ka cigaba da shan magani"
"Rahama baki san me nake ji ba ne, ina shan wahala fa" yayi maganar yana miƙa, tare da lanƙwashe yatsun ƙafarsa, hawaye na bin gefen idonsa, saboda azabar ciwo"
"Dan Allah ni ka daina wannan maganar" ya juya yayi ruf da ciki.
"Idan na mutu zaki yafe mini?"
Ta ce "Wataƙila, ai ni dama bana fatan na je gaban Allah ina neman hakkina a wurin wani, ko wani yana nema a wurina, a duniya nake fatan Allah ya saka mini abun da ka yi mini, da kai da wannan jakar matar"ya yi murmushi ya ce "Hakan ma na gode, alfarma ɗaya da zan nema, dan Allah rahama kar ki zubar mini da cikin nan, ina matuƙar son abun da yake cikinki"
"Wallahi sai na zubar tas, sai ya bi rariya, ni ka daina yi mini magana kamar wasiyya wasiyya, dan na tausaya maka"
Sai da yayi dariya ya ce "Abubuwa ne suke ta hargistewa Rahama, komai ya cukurkuɗe, ban san ya abubuwan za su kaya ba, ina ta ƙoƙarin baki kariya ne iya yi na, duk da ni mai laifi ne" yayi hamma ya ce "Idan ya lafa sai na ji daɗi, gashi bacci nake ji, ke ma na hana ki bacci"
Yayi maganar yana shafo fuskarta, ta saka hannu ta sauke hannunsa, ta shafa kansa ta ce "Kayi baccin, ko ka samu relief" ya juyo yana fuskantar cikinta, da yake shafe a jikinta ya ce "Bari na yi magana da yarona" maganar ta sa tayi daidai da jin motsi a ƙasan mararta.
A haka bacci ya kwashe shi, ta zuba masa ido, tana jin tausayin sa, gaba ɗaya ya rikice saboda ita, ta ƙara lura da shaye-shaye da rashin tarbiyya ne kawai yake ingiza shi yake rashin mutunci.
"Kayi haƙuri Abdul, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah"
*****
Walid ne ya magantu, dan tun shigowar Viper ya lura kamar yana cikin damuwa, ya ce "Mai zamani, ya ake ciki ne? Jikin ne ko wani abun ne ya faru?"
Ya numfasa ya ce "Na yi abun da ka ce, Nabila"
Walid ya ce "Masha Allah, ya ake ciki?"
"Ba ta da masaniya a kan hakan, things are complicated, ta shiga matsala daban daban, ta samu matsala da gidansu, an ce lallai ta bawa ɗan uwanta dama ya kama ni, she's almost alone, kamar ban kyauta ba, na ɗora mata abun da ya fi ƙarfinta"
Walid ya girgiza kai ya ce "Ƙaddara ce ta haɗa ku, kuma she's not alone, tana tare da kai, muna cigaba da addu'a in sha Allah, komai zai dai-dai ta, ba ta gaya maka komai game da labarinta ba?" Viper ya girgiza masa kai.
"Bata bani ba, amma na bata hoton, na ce taje ta tambayi yan gidansu"
"Ina jin alamun nasara, in sha Allah ka kwantar da hankalinka"
Viper ya amsa da Allah ya sa.
****
Nabila kamar mara laka, ta fito daga wanka, jikinta ɗaure da towel, ta jiƙo kanta da ruwa, idanunta sun yi jawur, saboda ta yi kuka sosai da sosai.
Kawai ta ɗaga kai ta ga Nasir a tsaye a ƙofar ɗakin, ta ƙara haɗe rai, ta ƙarasa tsane jikinta.
"Nabila, lokaci yana cigaba da ja, kuma ke nake jira, haryanzu baki ce mini komai ba, ki gaya mini in da zan samu mutumin nan, ina ɗaga miki ƙafa ne saboda Abba, kuma nima ina jin nauyin aikata miki hakan"
Buɗe wardrobe tayi, ta ɗaukko phant da breziar ta jefo kan gado.
"Magana fa nake yi miki"
Tayi masa banza, ta ɗaga breziar tana ƙoƙarin fara sakawa.
"Nabila wai baki da hankali ne? A gaban nawa zaki saka kaya?"
"Ni na kawo ka? Ko ka manta bin maza nake yi? Ba abun da zai hanani saka kayana, ai yanzu ba kunyar wani nake ji ba"
Galala ya bi ta da kallo, jakar da ta fita da ita, ta janyo, ta ciro ƙaramar wayarta da take vibrating ta ciro ta ɗaga ta ce "Hello V"
"Are you safe?"
"Yes Alhamdilillah"
"It seems you are bit disturbed"
"No at all"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Kin tambaya ɗin?"
"A'a, ai bai dawo ba, yayi tafiya ne, ni yanzu ina jiran abun da zai kasance a kotu ne gobe in Allah ya kaimu, and su oga Walid su shirya, zasu kasance cikin shaidun da zamu gabatar a kotu fa"
"Shikenan, zan gaya musu"
"Yauwwa, gobe in Allah ya kaimu daga kotu zan wuce wurin 'yan sanda, a kan case ɗin ka, Allah ya sa......
"Nabila, wai me ki ka zama ne?" Nasir yayi maganar yana tunkararta zai fizge mata waya, ta ja da baya ta ce "Wallahi ka zo in da nake sai na saki towel ɗin nan, na saki ihu ai kai ka zo in da nake, get out from sight, wallahi Nasir ko me zaka yi ina kan bakana, ni, ko wani kaga zai yi mini ƙazafin da ka yi mini, yakamata ka tare mini, amma ka ɓata ni a wurin mutumin da bani da tamkarsa, wallahi ka cigaba da matsa mini kai ma sai na ɓata maka suna a gidan nan, ka fita daga rayuwata ba ɗan daba ba, ko uban wa zan kare ni naga zan iya. Ka je ka yi aikinka nima na yi nawa, kai ma ai amfani ake yi da kai, ake son kama shi ba dan taimkon al'umma ka ke son kama shin ba, get out please" yadda jikinta yake rawa take nema ta saki towel ɗin, muddin ta saki ba shi da kalaman da zai kare kansa da su.
****
Indabo ya kalli Abdul da yake zane yana wasa da mukullin motarsa ya ce "Wai meye ne, na ganka kamar wani mara lafiya?"
Ya ce "Bakomai, ka yi haƙuri na san maganar yarinyar.....
"A'a, ai ba maganar yarinyar nan zan yi maka ba Abdul, ka yi abun da ka ga dama, yau saura sati biyu ɗaurin aure ko wurin yarinyar da zaka aura duk ka kyauta. Magana ce zan yi maka a kan kuɗaɗen da nake sanya wa a account ɗin ka, balli na nema ya tashi, an naɗa kwamiti bincike a kan kuɗaɗen nan, shi ne nake son ka dawo mini da shi, na mayar kan balli ya tashi asiri ya tonu"
Abdul ya yi sororo yana kallon Indabo .
"Kake kallona kamar shashasha, ka dawo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 78 Chapter of 121