cire saifu, shi ma suna gaisawa.
Tare suka ta shirye-shirye, Hafsa tana cewa ita babu wani gyara da zata yi, lokacin da aka yi na farin ma, bai yi mata amfani ba balle yanzu.
Amma Nabila da taimakon sumayya suka ce, sai ta yi gyara da da yanzu ba ɗaya bane ba, zamani ya riga ya canza.
A lokacin Shahida ma Walid ya kai kuɗin aure, kuma Hafsa ƙawar Shahida ce, kasancewar iyayensu aminai ne. Watanni biyar aka saka, saboda babu yadda Viper bai yi da Walid ba, ya dage ya ce shi sai yayi mata lefe ko yaya yake, kuma sai ya kama gida. Shi ba ruwansa da bazawara ce, ba zai so ace shi aurensa na fari, ace ya naɗe hannu komai sai dai ayi masa ba.
Viper ya ce masa ya gyara nasa gidan, su zauna sai ya din ga biyansa kuɗin hayar.
Walid ya ce "Ai sakankancewa zan yi, na san naka ne, idan ma ban biya hayar ba, ba zaka damu ba, kuma zan ta damuwa gidan zai din ga tuna mini ƙanwata Jauhar, kuma kai a ina zaka zauna, idan ka yi naka auren?"
Viper ya ce "Ina da wurin zama ai ni, ko ka ƙi, ina wani gidan, na ji ba zan saka maka hannu ba, ka gyara shi da kanka, kayi lefen, amma ba zaka kama haya ba gaskiya ba"
Da kyar Walid ya amince da hakan, sai dai Liti ya zage kamar kayan lefensa zai tara, kuma Nabila suke turawa kuɗi take haɗa kayan, ita kanta Shahidan ba ta san da haka ba"
Sai dai daga Hafsa har Shahida sun dawo daga rakiyar iyayensu, na shirmen bin bokaye, domin sun tabattar da ba hanya ce mai ɓullewa ba.
Kasancewar Sumayya na ta'amalli da mutane daban-daban, a dalilin harkar aikinta, ya sanya ta nemi lambar maman dr., Domin haɗawa Alhaji mu'azzam da kuma ango Walid amayarsa. Tun da ita mace duk in da take sai da gyara. Kuma masu iya magana suka ce, idan kana da kyau ka ƙara wanka.
A cikin wata gudan nan, ba ƙaramin kyau Hafsat tayi ba, sai sheƙi tayi gwanin sha'awa, duk da ba ta da jiki, amma maman dr. Ta tsatsota, ta cika tayi fam, tayi ƙiba dai-dai misali, amma duk lokacin da Alhaji mu'zzam ya zo sai sun yi faɗa. Gashi can gidansa uwargidansa ta sako shi a gaba a kan ya ce zai dawo da hafsa, rashin mutunci na yau daban na gobe daban, gaba ɗaya ta ƙaurace masa, yadda Jidda ma ta fita, so take ta rayu itakaɗai a gidanta, shi kuma ya ce bata isa ba, yana da wadata da lafiyar da zai auri mace fiye da ɗaya.
Ya din ga ganin tamkar ranaku ba sa sauri, duk lokacin da ya je wurinta, da kyar yake saita nutsuwarsa, saboda kyan da tayi, da wani irin sihirtaccen ƙamshi da take yi. (Domin gyara da kankaro naku mutuncin kuma a naku gidajen auren, ku garzaya ku tuntuɓi maman dr. Likktar mata domin kar ayi babu ku 07069711327)
Viper yana zaune yana duba status ɗin sa na waya, yana son ya halarci ɗaurin auren hafsa, dan haka yana saka ran ana idar da sallar asuba zai nufo Kano, duk da ɗaurin auren na azahar ne sai an saukko daga masallaci.
Status ɗin Nabila da ya yi muting ya shiga, na farko Addu'a ce, kamar yadda ya zame mata ɗabi'a, yawan sanya addu'oi da shot videos na malamai.
Na gaba kuma, videonta ne, an yi mata lalle ja da baƙi, sumayya tana cewa our dear barrister marasa galihu, jin ki yafi ganinki, our anti serious beb" ta kwaɓe fuska tana harar Sumayya.
Ɗaya Videon kuma, Ita da sumayya ne da amarya hafsa, da wasu daga cikin yayyen su mata.
Haushi ne ya kama shi, ya san wataƙila duk mazan da suke cikin wayarta sun ga status ɗin, doguwar riga ce a jikinta, ta ɗora mayafinta a kanta, shigarta decent amma shi abin da idonsa yake gani, gani yake kowama ya gani.
A irin fitinarta, duk abin da Hafsa take amfani da shi na gyara, sai ta ce sai ta sammata.
Nabila kuwa tana saurar tashar su Sumayya, At the same time tana chatting, Sumayya na shirye-shiryen rufe tashar, ta fara sanar da ɗaurin auren hafsa, sannan ta ambaci na Nabila da Al'amin, a babban masallacin juma'a na BUK wanda za a ɗaura bayan an idar da sallar juma'a.
Ayshercool
08081012143
105
Miƙewa Nabila ta yi tsaye, tana tunanin kamar ba ta ji sosai ba.
"Wane irin wasan banza ne haka sumayya take yi mini?" Tayi maganar tana mamaki.
Wayar Sumayyan ta hau kira, amma wayarta a kashe, jikinta na rawa ta fito falo, amma ta tarar kowa ya kwanta, ko ina a rufe.
Ta koma ta hau kiran Umman Sumayya, amma ita ma ta ta wayar a kashe.
Ta saka wa zuciyarta zolaya ce kawai Sumayya take yi mata, dan tun da aka yi musu lallae take cewa tayi kyau kamar ranar tarewa a gidan Viper.
Sai dai wannan ya wuce wasa, ta rasa meyakamata tayi, ta din ga fatan Allah ya sa mafarki ne ba gaske ba.
Gaba ɗaya ta kasa bacci, sai dai yadda ta kasa baccin nan, haka Nasir ya kasa, da yayi juyi ya kalli invitation ɗin auren Nabila, sai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, cike da baƙin ciki da damuwa.
Ya so Nabila tun tana 'yar ƙarama, tun tana yawo ba riga, ba ta san ciwon kanta ba, yana matuƙar tausayinta, yana taya major ƙaunarta, saboda maraicinta, ga rashin lafiya ga kuma ƙiyayyar da mutanen gida suke yi mata.
Wahalarta babu wadda bai sha ba, kaita makaranta, yawon visiting kaita Asibiti idan Major baya nan, duk wata gudunmawa da ya san zai iya bayarwa domin ta ji daɗi yana yin su.
Duk rashin jin ta da karaɗinta baya damunsa, babban burnsa ya ganta tana cikin faranciki, mussaman idan yayi la'akari da hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da suka yi magana a kan kula da maraya, idan ya tuna mamanta ta rasu, ba ta san waye babanta ba, sai matsanancin tausayinsa ya ƙara shigarta.
Bayan Major ba ta da wasu da yadda da su take ƙaunar su, sama da shi da Sumayya, koma Yaya Nasir ko Sumayya, duk wata wauta da taɓara da zata yi, baya gajiya, da hakan matsanancin son ta ya shiga ransa, sai dai mama ta riga tayi masa kandagarki da Allah ya isa a kan Nabila, tsawon lokacin nan baya iya kula kowacce mace, saboda Nabila, sai dai duk wannan son da yake yi mata, lokaci ɗaya kuɗi suka rufe masa ido, ya tafka mummunan kuskuren da ya rushe waccan kyakkyawar alaƙar da take tsakaninsu, har ta kai tana yi masa kallon maƙiyinta a yanzu.
Da Asuba Viper ya nufo Kano, Abbu ya kira shi a waya, suka gaisa ya ce "Ka taho ɗin ne, zaka halarci ɗaurin auren?"
"Eh in sha Allah Abbu, ai ina hanya ma, na biyo sojoji mun taho"
"Akwai kuɗi a wurinka ne?"
Viper ya ce "Eh, amma kamar nawa?"
Abbu ya ce "Dubu ɗari biyu"
"Eh ba za a rasa ba"
"To da ka dawo ka taho gida da kuɗin, ina son ganinka"
"To in sha Allah, ina nan tafe"
"Allah ya kawo mini kai lafiya"
Viper ya yi murmushi ya ajiye wayar.
Sai dai babu daɗewa Walid ma ya kira shi, ya ɗaga ya ce "Mazaje ya ne?"
Walid ya ce "Mai zamani"
"Mai laya?"
"Za ka zo ɗaurin auren yayar Nabila ne?"
"Eh in sha Allah"
Walid ya ce "To ka yi sauri"
"Me zaka bani, ba sai bayan juma'a ne ɗaurin auren ba?"
"Eh kawai dai ka yi sauri"
Viper ya ce "To aiko mini da fuka-fukai na tashi sama"
Walid ya yi dariya ya ce "To in dai zaka yi sauri ai shikenan"
*****
Wayewar garin Allah, Ana idar da sallar asuba, Nabila ta tafi ɗakin Abba, ta tarar bai ma dawo daga masallaci ba, ta samu wuri ta zauna tana jiran dawowarsa.
Yana yin sallama ta tashi tsaye, ta ce "Abba, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?"
"Abba ni fa ban yi bacci ba, Sumayya ce ta yi mini wani wasan banza da ya ɗaga mini hankali, wallahi ido biyu na kwana cikin zullumi da fargaba, na zata mafarki ne ma zan farka, amma dai na ga gaske ne"
Ya zauna yana faɗin "Subhanallah, wane irin wasa ne haka, da ya hana barrister bacci?"
"Ɗaurin auren hafsa ta sanar, kuma sai na ji ta faɗi sunana da na Viper, wai za a ɗaura mana aure"
Major ya ce "Ikon Allah, kuma kin kira wayarta?"
Ta ce "N kirata wayar a kashe, na kira ta Umma ma, amma ba ta shiga duka"
Abba ya jinjina kai ya ce "Abin da mamaki gaskiya, bai kamata ta yi miki wannan wasan ba gaskiya, amma ki je ki samu ki yi bacci, na san da wasa take yi miki, wurin ƙarfe goma sai ki shirya ki tafi can gidan naku wurin bikin, na ji Antynki da su Magajiya duk suma za su je"
Ta ce "To Abba" sai ta ji ƙwarin gwiwa, ta je ta nemi wuri ta kwanta, sai ta samu bacci ya ɗauke ta.
Tana farkawa, Sumayya ta fara kira, wayar ta shiga amma Sumayya taƙi ɗagawa, hakan ya ƙara fusata ta.
Ta fita kitchen, tana gaya wa baba magajiya abin da tayi mata cike da takaici.
Baba magajiya ta ce "Kun fi kusa, ina fatan Allah ya tabattar mana da alkhairi"
"Ba amin ba, ba da shi ba alkhairin"
Baba magajiya ta ce "Au zaki ga ba da shi ba, ni dai ina yin sa, duk da ya ce kar na gaya miki, ranar da suka zo, dubu goma ya bani, ya ce na sha lemo, a samarinki waye ya taɓa saurarata"
A shagwaɓe ta ce "Ni fa ba saurayina ba ne ba"
"Oho miki dai, ni dai Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi"
Nabila ba ta sake cewa komai ba, ta hau bubbuɗe kwanuka, ta buɗe fridge ta ɗauki gasarar alkama, ta dama kunu da ita, ta ɗebi doya ta dafa ta ɗebi miya ta koma ɗaki.
Ta fara karyawa, ta shiga facebook, saboda tana buɗe data, notifications suka din ga shigowa ba ƙaƙƙautawa.
Ai tana shiga da invitation ɗin ta fara cin karo, ana ta yi mata Allah ya sanya alkhairi, ba ta san lokacin da ture kofin kunun ba, ta tashi da sauri, har tana tuntuɓe, ta shiga ɗakin major tana zazzare ido.
Ta tarar da shi tare da telansa, ta ce "Abba ka ga fa" tayi maganar tana haska masa fuskar wayarta.
Ya sallami telan sannan ya ce "Zauna mu yi magana"
Ta zauna jikinta yana tsumar rashin sanin abin yi.
"Nabilatul arfa, tun da mahaifiyarki ta rasu ta bar mini ke, nake kula da ke cikin ikon Allah, tamkar ita nake kallo, ban taɓa yi miki wani abu da zai cutar da ratuwarki ba. Kuma na daɗe ina baki dama na aikata duk abin da ki ke so, muddin ba gani nayi zai cutar da ke ba, babu irin ƙalubale da bamu fuskanta ba daga ni har ke, amma na toshe kunnuwana, domin ganin kin rayu cikin farin ciki da jin daɗi.
Wannan hukuncin mahaifinki ne ya yanke shi, duk yadda na kai ga nuna miki so da ƙauna, ya fi ni iko da ke, ko da a gaban shari'a ne, na ce ya bani dama na tattauna da ke a kan yaron nan, ya bani amma ki ka nuna ke fafur ba kya son sa.
Kafin na amince da maganar Al'amin, na yi bincike a kansa fiye da yadda ki ke tunani, wurin aikinsa, wurin mahaifinsa, duk wani motsi na rashin jin sa sai da aka bani labari. Na zauna da abokansa, sun bani labarin yadda ki ka shiga rayuwar sa, da duk abin da ki ka din ga yi, rayuwarsa da yar uwakki, wanda shi kansa bai sani ba.
Irin rayuwar da ya yi da 'yar uwakki, duk na bincika, gefe guda babansa na ta bi na yana yi mini magiyar a shawo kanki, Allah ma'aiki kar ya koma rayuwarsa ta baya.
Honorable Mu'azzam Wada kankarofi, shi ma bai ɓoye mini komai ba, shi ya ƙara ƙarfafa lallai ayi auren nan, zaku zauna yana sonki kina sonsa, ke kuma naga gaba ɗaya shirme ne a kanki da wauta, dan haka muka yanke wannan hukunci.
Sumayya ba wasa ta faɗa ba, katin aurenki ne, kuma ina fatan zaki yi mana biyayya baki ɗaya"
Ƙurawa Abba ido ta yi, ji take kamar almara, kawai kuma ta fashe da kuka "Abba ka fa ce ba zaka yi mini auren dole ba, haba Abba"
"Wannan ai ba na dolen bane ba"
"Haba Abba, na dole ne mana, ba sai an tambayi mutum yana so ko ba ya so ba, kuma ka tambayeni na ce a'a kawai kuma sai a ɗaura"
Ya ce "Eh gaskiya ne, ban kyauta ba, za'a kai ƙarata kenan, na taɓa masu shari'a"
Yanayin yadda yayi maganar ya sanya ta gane zolayarta ma yake yi, bai ɗauki hakan serious ba. Hakan ya saka ta ƙara sautin kukanta har da sheshsheƙa.
Abba ya ce "Maza yi ta yi, in dai kukan banza ne, dama tun kina zanin goyo halinki ne, idan ki ka isheni kuma, na zane miki jikinki"
"Abba ba na son shi fa, gaba ɗaya baya so na, ai an baka labarinsa da Jauhar, ya ce duk duniya itakaɗai ce mace, ba fa ya so na ko kaɗan, Wannan auren dole ne Abba"
"To Arfa a kaini gaban me Shari'a a tuhume ni da laifin child abuse, na yi wa barrister auren dole, amma sai ki haɗa da ni da ubanki duk ki kaimu ƙara. Kai waye a nan wurin ku kira mini magajiya ta zo ta ɗauki yarinyar nan daga gabana, kafin na casata a wurin nan"
Ƙarshe ya tashi ya bar ta a wurin, tana ta gursheƙen kuka, kamar an sanar da ita mutuwar tsohuwarta.
****
Ƙarfe sha ɗaya Viper ya shiga gida, Abbu ya ce "Dama tuntuni kai nake jira, ka ƙaraso mu karya"
Viper ya yi murmushi, yana jin daɗin tattalin nan da Abbun yake yi masa.
Ya ce "Abbu ya su Walid kuma?"
Abbu ya ce "Yaran kirki, Abdallah babansa ya kai shi kasuwa, wurin sayar da sarƙoƙi da kayan shafe-shafen mata, ya ce a kama masa shago, idan ya gane kan harkar sosai, yaƙi zama muna tare da shi a kasuwarmu, wai shi ba ɗan daudu ba, me zai yi da wani kayan shafe-shafen mata. Na daɗe ban ga rigimammen mutum kamarsa ba, yanzu haka ma suna kasuwa ne kayanmu zasu iso, daga nan za su yi mini wani aiki, da yanzu ka gansu a nan. Na je gida mun yi magana da mahaifinsa na ce yayi haƙuri ya ƙyale shi, tun da ga in da hankalinsa ya karkata".
Viper ya ce "Liti akwai rigima, wanda bai san halinsa ba ba zai iya zama da shi ba"
Abbu ya ce "Ai naga alama, akwai barkwanci"
"Idan yana yin mutum kena ba, amma ga wanda bai san shi ba, goga ne, a lokacin muna mazaje, muna ji da rashin ji, ya fi Walid karsashi, 'yan daba idan sun kai goma, zai ratsasu shikaɗai ba ya tsoro ba kuma ya san wargi"
Abbu ya rausayar da kai ya ce "Na so ace tuntuni na farga, na ja ku a jiki ku duka, da kai ɗin da su, na riƙe ku na kula da iliminku, na kaiku kasuwa, da yanzu Allah kaɗai ya san me zaku zama, su waɗanda nake kallon su ne shiryayyun na ɗauki ɗawainiyar su, gashi a ƙarshe ba wanda ya more su, na yarda da ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta, yanzu gashi ku ɗin da ake kallon marasa ji, yanzu al'umma sun fara amfanar ku, ba zan manta da honorable wada kankarofi ba, bawan Allahn nan ɗan halak ne, gashi ka zama soja kana aikinka, Allah ya ƙara dafa muku"
Viper ya ce "Amin"
Abbu ya ce "Amma ya aka yi ka ke da kuɗi tsakiyar wata, ai ni da na ce ka taho da 200k da idan ka ce babu, zan ƙara nuna maka amfanin haɗa kasuwanci da aiki ne, an ce albashin naku, ba shi da yawa".
Viper ya yi wata irin dariya ya ce "Ko a cikin sojoji, irin aikinmu na musamman ne, kuma mai hatsarin gaske, ina da salary mai kyau, zan zaɓi garin da nake so a bani gida, kuma za a bani abin hawa, ba a buƙatar rashin gskiya ko a samu irinmu da halin cin amanar ƙasa, idan aka kama mu da haka, babu shari'a kisan kai ne kawai. Shiyasa irinmu a sojoji ba su da yawa ko kaɗan"
Cikin mamaki Abbu ya ce "Wai bayan fitowar ka har ka yi training ɗin ko kuwa? Kuma wane iri ne aikin naku a sojoji?"
"Ina gaya maka kashe ni za ayi, ba a faɗa kawai dai ka saka a zuciyarka ɗanka soja ne, mai muhimmancin gaske ga ƙasarsa, kuma a kowane lokaci zaka iya rasa shi, dan haka ka yi mini addu'a kawai"
Abbu ya ce "In sha Allah sai ka yi retire da kanka daga aiki, ba za a kashe ka ba" haka Abbu ya din ga jan sa da hira, har lokacin salla ya ƙarato.
Abbu ya ɗaukko masa sababin kayan kar, dark blue ɗin shadda, riga da wando, da hula. Ga sabon agogo da takalmi.
Ya ce "Wannan fa?"
Abbu ya ce "Wurin ɗaurin aure zamu je, ba na son yawon da ku ke yi da ƙanan kayan nan, kamar ba yaran hausawa ba, dan haka su zaka saka"
Shafa kayan ya yi, yana tuna abar ƙaunarsa, Jauhar, a lokacin da ta bashi kyautar kaya ranar sallar idin ƙaramar salla.
Su Walid ne suka yi sallama a waje, Abbu ya ce ace su shigo, suka shigo sanye da fararen kaya, liti ya riƙo hularsa a hannu.
Abbu ya ce "Abdallah, ya ka cire hular ka ga yadda ka yi kyau a cikin kayan kuwa?"
Ya ce "Abbu, hular ce ta ɗame mini ƙeya nake ta gumi shi ne na cire"
"Ai fa rashin sabo ne"
"Mai zamani, Abbu ne fa ya ɗinka mana kaya" liti yayi maganar yana nuna masa kayan jikinsa.
Walid ya ce "Mai zamani haka ka ke kyakykyawa, rabon da ka yi kyau kamar haka, tun ranar aurenka da marigayyiya"
Abbu ya gyarawa Walid zaman tasa hular, ya ce "Yauwwa ko ku fa 'yan samari, Allah ya nuna mini aurenku duka" suka kasa cewa Amin.
Wani farinciki ne ya mamaye zuciyar Viper, ganin yadda Abbu yake nuna wa su Liti ƙauna, wanda ya san duk dan saboda shi ne, shi yanzu a duniya abin da zaka yi masa, ka saka shi farinciki, ka so mutanen nan uku kamar yadda yake ƙaunar su, ya san a duniya ba shi da abin biyansu.
Haka suka ɗinguma a mota, suka tafi masallaci, domin yin salla da halartar ɗaurin Alhaji mu'azzam.
A sahu ɗaya suka yi salla da Alhaji mu'zzam, suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.
Bayan an idar da salla, babban abin da ya ba wa Viper mamaki, bai wuce ganin abokan Abbu da yawa a wurin ba, da kuma wasu daga cikin 'yan uwansa, bai kawo komai a ransa ba, suka gaggaisa, suna taya shi murnar wanke shi da kotu tayi, wasu kuma na zuzuta kyan da yayi, wasu kuma suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, shi dai duk bai gane kan abin ba, ana ta ɗaura aure, aka zo kan na Alhaji mu'azzam, aka ɗaura aurensa da Hafsa.
Bayan an kammala na su, aka nemi waliyayyan Al'amin, saroro yayi yana kallonsu, ganin Baba yana kallonsa yana murmushi, haka Major.
Ya waiwaya, har da su doctor Muktar, da Abdul yasar a wurin.
Sai da aka ɗaura aurensa da Nabila, sannan ya fuskanci abin da yake faruwa.
Walid ya cire hular Viper, ya shafa kansa ya ce "Angon Nabila ka sha ƙamshi, yau dai Allah ya yi Allah ya sanya alkhairi"
Yayi saroro yana kallonsu, liti ya ce "Mun iya Suprise ko? Sai ka bamu tukuci yasin, idan ka cire kayan nan ni zaka bawa, in saka ranar auren Walidi, ko Allah ya sakani a damshinku"
"Mai laya yaushe aka shirya wannan abin, ita Nabilan ta amince ne?"
Liti ya ce "Oho muku, mu dai an haɗa kai da mu, an ƙulla sunnar ma'aiki, ai yanzu rumfar shayi har da banner dalilin aure zan saka. Idan aka biye muku, wahalar da mu kawai zaku yi ta yi, yanzu sai ku ƙarata ku sasanta kanku"
Aka fito daga masallaci, Viper sai jin sa yake tamkar ba shi ba, abin kamar almara.
Alhaji mu'azzam ya ƙarasa ya miƙa wa Viper hannu ya ce "Na haƙura na janye, na kuma yarda Jauhar taka ce, Nabila ma taka ce, ba a takara da kai Viper, duk da ka fuskanci ƙalubalen rayuwa da yawa, amma ina da yaƙinin Allah yana sonka, yadda yake tafiyar da lamuran rayuwarka. Ina yi maka fatan alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa"
Viper ya riƙe hannun Alhaji mu'azzam, amma ya kasa magana sam.
Major ma zagayo wa yayi, ya dafa kafaɗar Viper, ya ce "Yadda na samu labarin ka riƙe Jauhar amana, dan Allah ga 'yar uwatta nan ma, Allah shi ya san dalilin da ya sanya ya karɓi jauhar a lokacin da ka ke matsanancin son ta, ya musanya maka da 'yar uwatta, wataƙila da bai ɗauke Jauhar ba, babu yadda za ayi Nabila ta ga mahaifinta, komai sila ne, kuma duk abin da Allah ya yi dai-dai ne, ba a tambayarsa dan me? Allah ya baku zaman lafiya"
Viper ya risunar da kai ya ce "In sha Allah Abba, na gode sosai"
Abbu ma ƙarasowa yayi, ya ce "Al'amin, a karo na biyu na sake nema maka auren 'ya, kuma Alhaji Bashir ya sake bamu, a rana mai kamar irin ta yau aka ɗaura maka aure da jauhar, yau ba ta raye, an sake ɗaura maka aure da Nabila, dan Allah Al'amin ka riƙe musu 'ya da mutunci da amana"
Kawai ya fara zubar da hawaye, duk da yayi iya ƙoƙarin sa wurin mayar da hawayen, amma abu ya gagara, kawai ya lumshe idanunsa ya basu damar su zuba.
Major ne ya ce "Ya haka kuma? Amare ke kuka ba angwaye ba, dan Allah kar ka bayar da mazaje mana, soja ne fa kai".
Jiki a sanyaye Walid ya ce "Ai a duk lokacin da za ayi wani abu da zai tuna masa da Jauhar duk taurin zuciyar sa da ƙarfin halinsa sai ya yi kuka, haryanzu ya kasa jurewa, duk yadda za a bayar da labarin yadda suka rayu, idan ba wanda ya gani ba ba zai gane ba"
Major ya ja shi ya bashi handkerchief ɗin sa, yana duddukan kafaɗarsa yana rarrashinsa, Abbu ya ce "Al'amin dole fa ka yi haƙuri, kayi haƙuri, duk lokacin da ka tuna Jauhar ka yi mata addu'a. Sannan dole ka koyi danne zuciyarka, idan ba haka ba, zaka iya sanya wa Nabila kishin 'yar uwatta, zuciya ba ta da ƙashi".
Kallonsu kawai yake yi, idan ya ce ba ya murna da farincikin wannan auren, ƙarya yake yi, amma zuciyarsa ta tsinke, da yaga yana sake ɗaura wani auren, Jauhar ɗin sa ba ta duniya, a lokacin da yake tare da ita, gani yake duk wani leƙe-leƙe da ake faɗa na namiji a kan mace, itakaɗai ta ishe shi rayuwa.
Suka kewaye shi suna ta rarrashin sa, abin da ya ƙara yi masa daɗi da sanya shi farinciki, bai wuce yadda shi da ake ƙyama a da, amma aka tara wannan mutanen saboda shi, kuma duk suka kewaye shi, kowa yana ƙoƙarin rarashin sa, lallai babu abin da ya fi zama mutum na gari.
Alhaji mu'azzam ya ce "Ko sai mun dangana da wurin amaryar za ta rarrashe shi? Dan naga tafi kowa iya shawo kansa"
Major ya ce "A'a bar amaryar nan, ka san ba ta san da bikin ba sai jiya da sumayya ta sanar da daddare, can na baro ta a falo tana kuka, fushi ma take da ni, ina ga ranar Litinin za a kawo mini sammaci daga kotu, na taɓa masu ƙasa na yi wa barrister auren dole, amma na gaya mata ni da kai zata kama, tun da tare muka yi laifin" yayi maganar yana nuna Alhaji Bashir .
Suka yi dariya baki ɗaya. Duk da a ƙurarren lokaci Sumayya ta sanar da ɗaurin auren Nabila, Auren ya samu hakarta ɗaruruwan jama'a, manya da ƙananan mutane, mussaman waɗanda suke supporting ayyukanta, har da wakilai daga gidan gwamnati, manyan lauyoyi da baristoci, har da kwamishinan shari'a, da alƙalin alƙalai na jiha. Da yawa saura kwana biyu uku suka samu invitation ɗin, kuma an halarta sosai da sosai.
Ba ƙaramin daɗ Major ya ji ba, ganin irin jama'ar da Nabila ta tara, a ransa yayi mata addu'a Allah ya sa yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 111 Chapter of 121