shi, idan ma haka ne, ai ɗan uwansa ne ba ruwansa.
Aka share zaman makoki, amma Al'amin ya kasa cigaba da walwala, tun jauhar na bin sa na tambayarsa ko lafiya? Ta yi rarrashin tayi ban bakin, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.
Zuciyar sa na ta azalzalarsa ya bi Indabo can Abujan, ya halaka shi kowa ma ya huta, amma ya daure ya jira ya dawo.
Sai da Nura yayi sati uku, sannan aka gaya wa Al'amin Indabo ya dawo.
Gaba ɗaya baya cin abinci yadda yakamata, idan ya fita baya iya zuwa wurin sayar da shayi, sai ya samu wurin da babu wanda zai takura masa ya kwanta yayi ta tunani, ya din ga jin da ma bai san Nura ba a rayuwarsa gaba ɗaya da duk haka bata faru da shi ba, ashe duk abun nan ma suna da alaƙa da juna.
Hatta jauhar yanzu ba ta iya samun kulawarsa yadda yakamata, dan ko in da take ya daina zuwa, ba ya dawo wa ma sai ta yi bacci.
Gashi ta shiga wata na bakwai, haki ya sakata a gaba, ga nauyin cikin ya fara damunta, da ƙyar take iya tafiya.
Indabo yana zaune a falonsa, yana ganin mutane, ya ga Al'amin ya faɗo falon kamar daga sama.
Cikin sauri ya sallami waɗanda suke tare da shi, ya miƙe tsaye ya ce "Mai zamani lafiya kuwa? Ya na ganka a haka?"
Kafaɗar Indabo ya daka ya hantsila kan kujera, "Me zamani distinguish senator kamar ni ka yi wa haka, dan na sakar maka na ba dama a kaina?"
"Zuwa na yi na gaya maka shukar da kayi tayi huda".
"Kamar yaya?"
Al'amin ya kalle shi da jajayen idanunsa ya ce "Ba na jin magana, amma wallahi ba na cin amana, kuma duk wanda ya ci tawa sai ya biya. Nura guduma ya mutu, na karɓi saƙonka ka jira amsar da za ta biyo baya".
Ras! Gaban indabo ya faɗi, dan ba haka suka tsara ba, ya aka yi ya san Nura ya mutu?.
"Ban gane Nura ya mutu ba"
"Shut up! Ka sam komai, tsohon munafuki algungumi, na san komai, ka lalata rayuwar yaron da nayi niyyar ingantawa. An dawo da shi rai a hannun Allah, na san baka san ya aka yi aka dawo da shi gida ba, bayan ka shirya yayi hatsari idan ya tashi dawowa yadda zaka ɓatar da abun da ka aikata. Wallahi ka ci amanar Al'amin kuma sai ka biya.
Ba ka yi mamakin yadda nake yi maka biyayya ba na yi duk abun da ka ke so?, ka zata kawai saboda kana bani kuɗi ne? Bari na tuna maka ni yaron dodo ne, dodo babban sarki doodn da yake ɗauke da makamin tarwatsaka, ka zata ya mutu da sirrin nan a cikin sa ne? Wallahi ma'aruf na sanka fiye da yadda ka san kanka, a Nigeria ko wajen Nigeria wuraren da ka ke tafka tsiyatakunka.
Wallahi na buɗe bakina a kanka, ka gama kaɗewa bar ganin kana da rigar kariya, kuma ku ne ku ke juyar ƙasar, dodo ya mutu ya bar ni da babban kundun da zan iya rusa ku.
Niyyata idan na zo na kashe ka, sai dai hakan ba zai saka na huce ba, saboda yanzu ba irin da ba ne, na ajiye wanda suke buƙata ta. Akwai dabarun da masu kimiyyar lissafi suke bi, wurin yin solving wato BODMAS. Bracket Open, division, multiplication addition sannan subtraction. To ni upside down nake yi indabo, sai na fara division nake multiplication na yamutsa komai sannan na saka a bracket na rufe.
Ka rubuta ka ajiye daga yanzu, ni ne babbar barazanar rayuwarka
Daga yanzu duk motsin da zaka yi, zaka yi shi a tsakanin tarkunan da zan saka maka, ka daina shan ruwa cikin kwanciyar hankali, ni ne magajin dodo kuma zaka biya cin amanar da ka yi mini" ya juya ya fita yana huci.
Cikin tsananin tashin hankali, Indabo ya tashi, ya ɗauki wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa.
Cikin tashin hankali ya ce "Ya aka yi Nura guduma ya bar gidan nan, garin yaya? Waye ya dawo da shi kano ban sani ba wane munafukin ne ya rusa mana plan?"
Jifa yayi da wayar, ya hau safa da marwa, cikin tashin hankali "Kenan kallon biri yake yi mini duk tsawon lokacin da muka yi tare? Amma Allah ya tsinkewa dodo albarka, ya ƙara tsine masa cin amanar da ya yi mana kenan?" Ya kuma ɗaukko wata wayar ya kira P.A ya ce "Maza ka ƙaraso gida ina nemanka".
Ya ajiye wayar ya cigaba da kaiwa yana komowa.
Afujajan P.A ya ƙaraso, ya ce "Yallaɓai ya ake ciki ne, meyafaru na ganka cikin tashin hankali?"
"Dodo"
P.A ya ce "Me dodon yayi?"
"Dodo ya daɗe da kashe mu, kafin mu kawar da shi ashe ya gaya wa mai zamani komai? An dawo da yaron nan Nura kano, ya san komai, na yi waya wai an nemi obi an rasa, ya gudu yanzu ya san komai, na kaɗe idan yayi magana ya gama rusa ni, Allah ya tsinewa dodo albarka"
"Ka kwantar da hankalinka, honorable wai waye wani mai zamani, me aka yi aka yi shi ne? Mutum nawa ka kawar kan mu zo in da muke yanzu? Ba zai tayar mana da tarzoma ba, bayan mun yi nasara kawar da shi kawai zamu yi"
Indabo ya ce "Tayaya wannan yaron mai shegen taurin rai, da ƙarfin tsiya, ashe tsawon lokacin nan kallona kawai yake yi"
P.A ya ce "Kwantar da hankalinka akwai abun yi, zan yi maka bayani".
Cikin dare jauhar na zaune tana lazumi, tayi sallar dare, ta ji shigowar Al'amin, ta ɗan jira wasu mintuna, sannan ta bi shi ɗakinsa.
Ƙwayoyi ta tarar da shi ya haɗa zai sha, cikin azama, ta durƙusa ta kwashe ƙwayoyin, ta dube shi ta ce "Akwai abun da ka ke ɓoye mini master, ba iya mutuwar Nura ce take damunka ba, akwai wani abu a ƙasa ka gaya mini. Baka saba ta'amalli da ƙwayoyi haka ba".
Yayi shiru bai ce komai ba.
"Master ka yi mini magana dan Allah ka gaya mini " tayi maganar cikin matuƙar rauni.
"Ki yi haƙuri ki je ki kwanta, dare yayi"
"Ka san kwana nawa nayi bana iya bacci, saboda damuwar da ka ke ciki? Kallonka kawai nake yi kar na takura maka ina jiran ka yi mini bayanin menene amma shiru, haba master ka gaya mini dan Allah"
Ya juyo ya riƙe hannun jauhar, yana murzawa cikin matsananciyar damuwa, ya sunkuyar da kai ya ce "Duk da abun a ɓoye ne, amma bai kamata na ɓoye miki ba, bai kamata na bar abun a raina nikaɗai ba".
Sai a lokacin ya gaya wa jauhar abun da ya faru.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" tayi ta maimaitawa cikin matsanancin tashin hankali.
"Master, ka ga irinta ko? Yana ɗaya daga abun da ya sa nake ta fatan ka nesanta kanka da mutumin nan, ya cucemu amma kansa ya yi wa. Baka yi da niyya ba, Allah ya jiƙan Nura ya saka masa"
Al'amin ya kifa kansa a kan cinyar jauhar, sai a lokacin ya ji wasu irin hawaye suka zubo masa.
"Sadik ya mutu a sanadina, Nura yayi wulaƙantacciyar mutuwa a dalilina, na zama annoba kenan? Mahaifiyar Nura har ta mutu ba zata manta, ni na kai yaron ta, in da ka yi dalilin gurɓata masa rayuwa ba"
Jauhar ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka daina faɗar haka master, kowa abun da Allah ya rubuta masa yake riska ba kaine sila ba" tana kuka tana rarrashin sa.
Tun da Allah Nura ya mutu, Al'amin ya ƙara nutsuwa, babu abun da yake yi masa daɗi. Ita kanta jauhar ta kasa daina jin ɗacin rashin Nura, dan tun da Al'amin ya ce masa an samo masa aiki a Abuja yake murna, yake bata labarin shi wata yarinya ya gani yake so, kullum sai ya je ƙofar makarantar islamiyyar su idan an taso su ya ganta, yanzu yana fara aiki, idan ya ginawa mama gida a cikin kano, ta dawo sai ya nemi auren yarinyar, amma kar ta gaya wa master.
Take yi masa dariya ta ce masa ai mamansa aure take yi sai dai ya haɗo da mijinta, ya ce ya fasa zai yi aure ya ɗaukko ramma ta dawo cikin gari, ta baro ƙauye.
Ta ce "Ban da abunku Nura haryanzu fa da sauran ƙuruciyarka, ɗawainiyar aure da yawa fa".
Ya ce "Ni dai kawai ki yi mini addu'a, da na dawo, zan fara zuwa wurin yarinyar nan zance"
Da haka tayi ta tuna ire-iren hirarsu, da barkwancinsa, ta kasa mantawa da shi.
Al'amin har tofa ya sake zuwa, ya yi wa mahaifiyar Nura gaisuwa, ya kai mata abun alkhairi, ya biya ya gaida Hajiya ya dawo gida.
Jauhar cikinta yayi girma sosai, kamar kana fita ka dawo zaka tarar ta haihu, ƙafafuwan ta duk suka kukkumbura, saboda girman cikin, aka ce yana shiga wata tara ayi inducing ɗin ta ta haihu ta huta, dan bayan nauyin cikin kullum cikin haki take, a haka kuma take lallaɓawa ta je makaranta.
Wurin shayin Al'amin kuwa, wasu irin kuɗi ne suke shiga suna fita, dan tun safe ake aikin ɗorawa da saukewa, ya zama chamber matasa sosai da sosai, duk da suna sayar da kayan shaye-shayen su a wurin, ba sa cutar Al'amin shi kuma ba ya yi musu mugunta.
Da safe su yi shayi, da rana indomie shayi, taliya haka suke wuni saye da sayarwar abinci.
Juahar sun gama haɗa kayan haihuwa, dan washegari ne ya kama ranar da za su je ayi mata inducing, tana ta jin tsoro yana kwantar mata da hankali.
Ta ce "Master"
Ya ce "Mmm"
"Ka ji sai motsi yake yi, kamar ya san gobe in Allah ya kaimu za a fara inducing ɗin nan"
Ya ce "Ya ƙagu ya ga daddynsa, Nuradeenin daddy, in sha Allah sunan Nura zan saka, kamar yadda na yi masa alƙawari".
Ta ce "Allah ya jiƙan Yaya Nura ya sa ya huta"
Ya ce "Amin".
Cikin shagwaɓa ta ce "Amma a gabanka zan haihu master, tsoro nake ji, an ce haihuwa akwai wahala fa"
"Ba wata wahala in sha Allah, ina kusa da ke, ina yi miki addu'a zaki haihu, Ni zai fara gani kafin ya ganki " yayi maganar yana sumbatar cikin nata.
"Ni dai na fuskanci ba a so na, ta babynka kawai ka ke yi" tayi maganar cikin shagwaɓa.
"Ni na isa? Dukkanku ina sonku madarata"
"Ba wani, ni baka taɓa cewa kana so na ba".
Yayi murmushi ya ce "Amma kina gani a aikace ai".
"Baka taɓa faɗa ba"
Yayi dariya ya ce "Ai ke da ruwan zinari aka rubuta sunanki a zuciyata. Ina sonki madarata, ina ƙaunarki ƙauna mai tsanani ya fi ubban shadidan"
Ta ce "Wayyo Allah daɗi. Wallahi har cikin tsakiyar zuciyata na ji kalaman nan, ba ka taɓa gaya mini ba, ka cigaba da gaya mini, da daɗi"
Ya ƙara rungumeta ya ce "I love you madarata"
"I love you too babyna, kuma baban babyna, masterna abun ƙaunata"
Har mamakin irin kalaman soyayyar da suka din ga musaya take yi, da ba ta taɓa tsammanin jin su daga bakin mastern ba.
Cikin matsanancin shauƙin so da ƙauna, suka kasance cikin farin ciki. Suka yi wanka, ya rungumota daga toilet tana takawa a hankali da ƙaton cikinta a gaba.
Ya taimaka mata, ta saka rigar bacci, sannan suka kwanta, ta kwanta a jikinsa, tayi balance da ta motsa sai yayi mata sannu.
Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da ita.
Ji tayi kamar ana kokowa a falo, ta laluba ba ta ga Al'amin ba, ga wani irin ƙaurin taba ya cika ko ina.
Hasken fitila ta hango an kunna ƙwan falo, ta saukko ta fito falon tayi arba da wasu matasa hannunsu riƙe da miyagun makamai, madaki ta fara ganewa gabanta ya faɗi.
Sun rirriƙe Al'amin, suna shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki yana ta layi.
Madaki ya bushe da dariya ya ce "Ka ce baka ji, dama ka ce da ni da kai sai wani ya kawo ƙarshen wani, to ni zan kawo naka ƙarshen yau ina dodon da kake taƙama da shi? Duk da zuwan ba nawa bane ba, na uban gidanka ne Indabo, amma ya jaddada mini in tabattar ka tafi da wani mugun miki a zuciyarka".
Cikin tashin hankali jauhar ta janyo jikinta ta nufi in da Al'amin yake tana kiran sunan sa "Al'amin me ka yi musu ne? Dan Allah ku yi haƙuri mana".
Al'amin ko harshensa ya kasa motsawa, balle wata gaɓa ta jikinsa.
Madaki ya riƙo gashin jauhar, ya kalleta ya ce "Yanzu kin zama ragowa, ni kuma ba zan ɗana abun da yake ragowar maƙiyina ba, gashi kin zama cuus" ta riƙe ƙasan gashinta da Madaki ya riƙe.
Cike da mugunta, ya saka ƙafa ya kawashe na jauhar ta gaba ya saketa, ta faɗi a kan cikinta, ta ƙwala wata irin razananiyar ƙara ta ce "Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah" ta faɗa sau uku, take jini ya fara malala daga jikinta, harshen ta kawai take motsawa a hankali tana kiran sunan Allah, ta din ga ɗaga hannunta tana son kiran sunan Al'amin. Ya ƙura mata ido yana kallon ta, cikin buguwa da mutuwar jiki, tun tana ƙoƙarin magana a hankali har ta daina motsi.
Madaki ya samu wani ƙarfe ya bugawa Al'amin a ka, shi ma suka sake shi a wurin.
Ayshercool
08081012143.
46
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Wayar Walid ce ta fara ringing, yayi shiru ya cirota daga aljihunsa ya kara a kunnensa ya ce "Ya aka yi?"
"Oga walid ka yi sauri ka dawo dan Allah, ya fara dawowa hayyacinsa, kar ya dawo gaba ɗaya ka san ba zan iya da shi ba".
Walid ya ce "Gani nan, ka yi iya ƙoƙarinka, kar ka kuskura ya fita, idan ya fita akwai ƙura ka sani, gani nan zuwa" ya katse wayar ya sakata aljihunsa, ya kalli matasan ya ce "Ku mayar da ita kawai" ya juya zai tafi.
Cikin azama Nabila da idanunta suka yi ja saboda kuka ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, kar ka tafi, ka ƙarasa mini labarin nan, yaya aka yi Viper ya tafi prsion? Shi aka ɗorawa kisan matarsa? Ta mutu ne ma ko kuwa yaya aka yi, ya kuma aka yi ya fito yanzu? Ni abubuwa da yawa ban gama fahimtar su ba, sun cukurkuɗe mini sun shige mini duhu, dan Allah kar ka tafi baka ƙarasa mini ba"
Walid ya ce "Ba zan ƙarasa ba ɗin, ba dai ke mara mutunci ba, na ɗauka haɗuwarki da shi, zai zama alkhairi amma ki ka yi mana halinku na mata, laifina ne da na kawo masa ke, Al'amin ya daɗe da cire mata a rayuwarsa, sai zuwan jauhar cikin rayuwarsa daga kawo ki a tashin farko kin mayar mana da hannun agogo baya, Viper ba zai taɓa zama ya bar liti a tsare ba, saboda shi ɗan halak ne"
Cikin matsananciyar damuwa ta ce "Na ji, na yi kuskure amma dan Allah ka yi haƙuri ka ƙarasa mini"
"Ba zan ƙarasa ba, ki je shi ya ƙarasa miki"
Cikin hanzari ta sake tarar Walid ta ce "Dan Allah ka sake yi mini jagora, ka kai ni wurinsa na nemi afuwarsa, na yi kuskure kaina ne ya riga ya gama kullewa na faɗawa lamuran a gaggauce cikin duhun kai, amma a shirye nake na gayara kuskuren da nayi"
Walid ya ƙare mata kallo ya ce "Kin riga kin aikata abun da ba zai gyaru ba, kuma kar ki sake yin gangancin zuwa in da yake, idan ba haka ba, ko bai kashe ki ba ni zan kashe ki. Ku ɓatar da ita daga gabana".
Suka saka Nabila a gaba, suka tasa ƙeyarta zuwa cikin napep ɗin da suka kawota, tana ta kallon walid tana yi masa magiya, amma suka ja babur ɗin suka tafi da ita.
Suka mayar da ita hanyar law firm ɗin su, suka bata wayarta suka tafi, wani abun hawan ta tare, ta nufi gida, zuciyarta sai bugawa dake da sauri da sauri, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ga matsanancin tausayin Al'amin da ya mamaye zuciyarta, lallai an yi wa rayuwarsa yankan ƙauna mafi munin da har ya mutu ba zai manta da shi ba.
A falo magajiya take ce mata sumayya ta zo har gida tana nemanta, duk an kira layukanta ba sa shiga, ko akwai matsala ne, gashi yau ta daɗe sosai ba ta dawo ba.
Ai har baba magajiya ta gama maganarta, ba ta fuskanci komai ba, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, wayarta na ta ringing ta duba, missed calls ɗin sumayya sun fi ashirin, ga na Nasir, ban da barrister Habib, ta kashe wayar, ta cillata kan gado, ta shiga banɗaki tayi alwala ta fito ta yi sallar azahar da la'asar.
A kan daddumar ma haɗa kai da gwiwa ta yi, ta din ga kuka, za ta iya cewa tun da ta buɗe ido a duniya, ba ta ji labari mai ban tausayi da tsayawa a zuciya ba kamar na Al'amin.
"Why Nabila kin yi garaje, why would you judge the book, according to cover? Why?" Ta tambayi kanta cikin tsananin takaicin abun da ta aikata.
Ta kifa kanta a kan gadonta, wani abu tsananin ɗaci yana yi mata zafi a tsakanin ƙirjinta. Gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, wani mugun haushin kanta ya isheta.
"Ko yaya yake ji a zuciyarsa yanzu? Dole ya zama bugagge gaba ɗaya, amma idan aka bar shi ya cigaba a haka, to tabbas zai haukace, amma yanzu yaya za ayi na samu ƙarashen labarin nan? Ta haihun ko mutuwa tayi, kuma wa ya kashe aka kai shi prison? Wait, to yaya ma aka yi aka sake shi daga prison ɗin, yana yawonsa idan ya ga dama har ya je yayi ɓarna, kuma still a haka wai nansa ake yi. Wai wannan wane irin lamari ne mai sarƙaƙiya haka? Kar na je na haukace a banza mana" tayi maganar kamar za ta haukace ɗin.
Ta cigaba da sintiri, tana ƙirga yatsunta, tana lissafi.
"Kai dole na samo ƙarashen labarin nan, ko da kuwa me zai yi mini, ko dai wanda ya fara ya ƙarasa mini, ko kuma shi Vipern ya ƙarasa mini, no matter how and what it takes sai na ji ƙarshen labarin nan, kuma sai na yi wani abu a kai. Haba dan Allah What a pitful life of his? Kai, to ita meye nata ma da za ayi mata haka? Me ta yi she don't deserve this at all" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.
Bugun ƙofar ɗakinta ake yi, amma ko gezau, da ta gaji da jin bugun ma, sai ta tashi ta tafi banɗaki, ta rufe ƙofa ta kunna fanfo, ta cigaba da kuka da tunani.
Ƙarfe takwas na dare Abba ya dawo gida, Nabila ya fara tambaya tana ina, Mama ta yamutsa baki ta ce "Ta dawo"
Ya jinjina kai, ya tafi sashensa, har ya fara cin abincin dare, ya ajiye cokalin ya kalli mama ya ce "Kirawo mini ita, ina ga ba ta san na dawo ba"
Haushi ya ƙule mama, ta tashi ta fita, ta je ɗakin Nabila, ta tarar da ƙofarta a rufe, ta din ga jijjiga ƙofar tana bugawa, amma ba ta buɗe ba.
Magajiya ta ce "Hajiya tun da ta dawo fa ta rufe kanta a ɗaki, taƙi buɗe wa, ba yadda ban yi ba taƙi buɗewa"
Mama ta yi tsaki, ta koma ta ce wa Abba, "To ka ji tun da ta dawo, ta rufe ƙofa taƙi buɗewa"
"Kuma lafiyarta ƙalau?"
"Ƙalau take, tsagwaron iskanci ne"
Ya girgiza kai ya ce "No, ko an ɓata mata rai ne, a wurin aiki ko a gida, ƙyaleta na ganta da safe na ji menene, ko kuma rigimar ce ta motsa" yayi maganar yana murmushi. Wani malolon takaici, ya ƙule mama, yadda yake lallaɓa Nabila, yana bin ta kamar wata uwarsa.
***
Abdul kuwa ganin ramma taƙi mayar da hankali ta ci abinci, hakan ba ƙaramin ƙular da shi yayi ba.
Ita kuwa jikinta ne babu daɗi, ga kewar gidansu, tana tunanin mama, ga baƙin cikin abun da yake aikata mata, gashi ya sakata a gaba duk sai ta kasa cin abincin.
Tana cikin zancen zuci, ta ji hannunsa a kan fusarta, ta tsorata ta ja da baya, ya tsuke fuska ya ce "Meye haka ne?" Ya buɗe idonta, ya ga she's still pale.
"Solomon" ya ƙwalawa kukunsa kira.
Solomon ya fito tare da cewa "Yes sir"
"Kana da kayan miya ko?"
Solomon ya jinjina kai alamar eh.
"Kawo mini tumaturi manya guda uku, da wuƙa ka haɗo mini da Apple ja guda biyu"
Ya ce "Ok sir" ya cigaba da kallon ramma, da ta ajiye cokalin, ta hau jan rigarsa da take jikinta, tana rufe ƙafafuwanta.
Mintuna kaɗan solomon ya dawo, da plate biyu, ɗaya ɗauke da tumatir, ɗaya kuma Apple sai ƙaramar wuƙa guda ɗaya.
Ya karɓa, ya matsa kusa da ita, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan cinyoyinta, ta ɗago cikin rauni idanunta sun tara hawayen takaici, ya yanka tumatirin ya miƙo mata. Ta tsaya tana kallonsa tana kallon tumaturin.
Miƙa mata yayi bakinta, ta kawar da kanta ta ce "Ni ba zan iya cin tumatur a haka ba"
"Zaki karɓa ko sai na burma miki wuƙar nan a ciki?" Yayi mata maganar cikin tsawa. A tsorace ta buɗe baki, ya din ga bata tumaturin nan, tana taunawa da kyar.
A zatonta zai bata tuffar, ta washe bakinta da ta ci tumatur, amma ya hau yanka tuffar yana ci, yana yi mata tauna a fuska, yana kallonta ga ƙafarsa a kan cinyoyinta da tayi musu nauyi.
Ya gama cin Apple ɗin sa, ya taɓa wuyanta ya ji babu zazzaɓi, ya ce "Haryanzu kina zubar da jinin ne sosai?" Tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ya harzuƙa ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari, ya ga ba ta motsa ba, sai hawaye da yake bin kuncinta.
Ya janye ƙafarsa daga kan cinyarta, ya ce "Ki cigaba da ina yi miki magana kina kallona, ki yi mini banza kashe ki zan yi a banza" tayi shiru ba ta tanka masa ba.
Jin ana knocking ɗin ƙofar falon, ya sanya ya tashi tsaye, ya ce "Tashi ki tafi ɗaki, za a shigo". Ga mamakinsa ko gezau ba ta yi ba, ta cigaba da zama tana zubar da hawaye.
Zuba mata ido yayi, cike da tsananin mamakin shegen taurin kai a wurin kucakar 'yar ƙauyen yarinyar.
Tashi tsaye yayi, ya fizgi hannunta, amma ta faɗi a wurin, saboda dama jikin babu ƙwari, ga jiri tana ta fama.
Ya durƙusa ya ɗauke ta, ya nufi bedroom ɗin da ita, a bakin ƙofa ya dungurar da ita ta ciki, ya ja ƙofar ya rufe, ya koma ya buɗe ƙofar falon.
Wata matashiyar budurwa ce a tsaye, sanye cikin doguwar rigar material, sai hula a kanta, hannunta riƙe da Jakarta.
"Ko wata ce a ciki ne? Ina ta bugu amma baka buɗe ba?" Bai yi magana ba, ya bata hanya, ta shigo ta ajiye jakarta ta nemi wuri za ta zauna ta ce "Abdul, staining ɗin jini nake gani a kan kujerar nan"
Cikin ko in kula ya ce "And so?"
"Mace ka kawo gidan nan?"
"Eh, akwai magana ne?"
Cikin takaici ta ce "Abdul don't try me, ka sanni ka san halina, ba zai yiwu nayi dumping guys ɗina just because of you ba, and ka din ga rough play da ni ba"
Yayi murmushi ya ce "Nina, ki na da matsala, saif ne ya yanke hannu da wuƙa, yana cin Apple, yayi bleeding sosai, amma ba abun da ki ke tunani bane ba" tayi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa ko kai fa, har hankalina ya tashi, i so much miss you" tayi maganar tana rungume shi.
Gaba ɗaya sai ya ji banbarakwai, kamar ranar ya fara rungumeta, haka ya lallaɓata suka tafi ɗaya ɗakin sheƙe ayarsu, sai dai hankalinsa na kan ramma, kuma gaba ɗaya ya ji bai samu abun da ya samu a tattare da 'yar ƙaramar baƙauyyiyar yarinyar ba.
Duk yadda ya so mazewa, sai sa Nina ta fuskanci hankalinsa a ba a kanta yake ba da tayi magana sai ya ce mata ba shi da lafiya ne.
***
Har washegari, Nabila ba ta ci abinci ba, ta dai buɗe ƙofar cikin dare da zafi ya isheta, ta fara numfashi da ƙyar.
Ta ɗaukko wayar Viper, ta din ga kallo, kamar shi ne a gabanta, ta rintse idanunta tana tuno kamanninsa, a zahiri suffarsa ta ban tsoro ce, amma a baɗini abun tausayi ne.
Ƙarfe takwas na safe, yaran gidan na ta zuwa gaida Abba, sai da sauda ta shigo ta gaishe shi, ya ce "Sauda duba mini Arfa ko ta buɗe ƙofar, ki ce mata ina bata haƙuri idan laifi nayi mata, da ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 121