rabuwar su, kawai ya ji ya na matuƙar jin tausayinta, har ga Allah ya na son Nabila ma, sai dai ya san Viper ba zai taɓa barin sa ya aureta ba, ko da zai samu aurenta sai an kai ruwa rana, amma matuƙa tausayin hafsa yake ji.
Ya na ta bibiyar unguwar ko zai samu ya ganta.
Ranar da ya sake zuwa wurin Baba kuwa, Allah ya taimake shi, ya ganta ta dawo daga islamiyya, dan kuwa islamiyya ta koma, idan ta je makaranta ta na samun sassauci daga damuwar da take damunta.
"Baba na dawo"
"Sannu da zuwa" Baba yayi maganar ya na kallonta.
Ta saka kai za ta wuce, duk da yadda Alhaji mu'azzam yake ta kallonta.
Baba ya ce "Hafsatu ba ki ganni da baƙo ba ne?"
"Na ganshi"
"To ba zaki gaishe shi ba?"
Ta kalleshi ta zumɓura baki ta ce "Ina kwana?"
Baba ya ce "Kwana kuma da yammacin nan?"
Alhaji mu'azzam ya ce "Hakan ma na gode, lafiya ƙalau ya makaranta?" Ba ta amsa ba ta shiga cikin gidan.
Ya na so ya yi wa baba maganar hafsa, mussaman da ya samu labarin, ta samu matsalar ƙwaƙwalwa, amma ya kasa.
Bayan baba ya shiga gida ya hau ta da faɗan abin da ta yi kawai ta fashe masa da kuka ta ce "Baba ni ko son ganinsa ba na yi ne, amma ai na gaishe shi, ni na tsane shi ne"
Baba ya waro ido ya ce "Hafsatu, ba a cewa an tsani mutum, ko ba komai auratayya ta taɓa haɗaku, ba ki san mai zai faru gaba ba, ki daina haka"
But Zakiyya ta fito ta ce "Baban saifu, Alhaji mu'azzam ɗin ne ya zo, ko bikonta ya zo yi?"
Hararta Baba ya yi, kawai ya wuce turakarsa, daga ita har Babbar su saifu ya watsar da su, ko turakarsa su ka je korarsu yake yi.
Da yaransa kawai yake harkokinsa, shi ma kuma ba dukkansu ba, saifu ne sai Hafsa, mussaman hafsa da yake jin tausayinta.
Zakiyya ta saka Hafsa a ɗaki, a kan yadda za su lallaɓa a sasanta ta koma gidan Alhaji mu'azzam, A take ta ce Allah kar ta ko shi ne autan maza ba za ta koma gidansa ba, ita yanzu islamiyya za ta yi ta zuwa, ta zama malama ta din ga yi wa addini hidima har ta mutu.
"Wallahi baki isa ba hafsa, ka ji baƙar muguwar yarinya, yi wa addinin hidima ba sai ki yi a ɗakin mijinki ba, wallahi sai kin koma, ba zaki yi mini baƙin ciki ba"
"Wallahi ba zan koma na ci gaba da zaman boranci ba, ai tun farko dama ba so na yake yi ba, ki ka saka dole ya aure ni, wallahi ba zan koma ba"
Zakiyya ta rasa yadda za ta yi da ranta, ta shirya ta tafi gidan su Viper, wurin ƙawar cin mushenta rahila, dan lambar wayarta ba ya shiga, rabonta da ita, tun ta na Asibiti bayan Abba ya daketa.
Sai dai ta tarar da ita cikin damuwa da tashin hankali ita ma, shahida ta kashe aure, Amira an sake gwaji babu HIV sai ciki, ta zubar da cikin ta gudu, ga Abbu ya kori Abba daga gidansa, Naziru kuwa tun da ya tafi kudu ba ta sake ganinsa ba, sai labari da aka kawo mata ya zama riƙaƙƙen ɗan iska a kudun.
"Rahila yanzu ina zamu saka ranmu, maigidanmu fa duk ya yi watsi da mu, yanzu ya gano ɗaya yar ta sa hankalinsa ya na kanta, soyake ya lallaɓa ta dawo hannunsa, gashi daga gani ba ta da kunya. Ba na son Alhaji mu'azzam ya san da ita ya ce ita ma so yake yi, hafsa ta kasa komawa ɗakinta, ta ɓangaren ki babu wani zazzafan malamin ne?"
"Zakiyya da alama ruwa ya ƙare wa ɗan kada. Dan yanzu asirin ba cin mazajen yake yi ba, har su ma yaran. Gaba ɗaya yarana sun ɗaiɗai ce sun tsiyace babu wani mai ɗan dama-dama sai shahida, Abba ya ɓaci da shaye-shaye tuburan"
Zakiyya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan shaye-shayen ya zama bala'i. Ni fa da depression da shaye-shayen ne su ka haɗu su ka saka hafsa hauka" nan su ka ci gaba da jajanta wa juna.
***
Da daddare Nabila na shirin kwanciyar, take kallon wayarta, ji take yi tamkar ta kira Viper, dan ta san ta gama ƙular da shi, amma ta dake taƙi kiransa.
Washegari da safe ta tura masa message da "Mu haɗu a CID da ƙarfe goma, saura ka ƙi zuwa, wani abin ya biyo baya ka ce an bani cin hanci"
Jujjuya wayarsa ya din ga yi ya na kallon saƙon nata.
Gaba ɗaya su ka haɗu kusan lokaci guda, daga ita har Viper kamar ba su san juna ba, sai basar da juna suke yi.
Babar Abdul sai cika take ta na batsewa, kamar ita aka yi wa laifi, ta na kallon ramma da take ta rufe cikinta kallon banza.
Abdul kuwa satar kallon matarsa yake yi, kallo ɗaya ya yi mata ya tabattar da maganar Nabila na ƙarancin jini da kuma damuwa a tattare da Rahama, gashi duk ta rame ga pimples ƙanana sun feso mata saboda ciki.
Tausayinta da ƙaunarta su ka mamaye shi, ya ji ina ma su na tare, ya ciyar da ita da ingantattun abinci masu gina jiki, da kulawa ta musamman.
Ɗaya daga cikin lauyoyin Abdul ya sake gabatar da kansa sannan ya ce "Mu na godiya da amincewa da ku ka yi ku sake zama da mu, domin a duba a ga abin da zai yiwu na mafita da kuma masalaha a kan wannan case".
Mahaifiyar Abdul ta ce "Go direct to the point. Su faɗi ko nawa su ke so, idan ma kuɗin da ya ba su bai ishe su ba, zamu ba su kuɗi, su ƙyale mini ɗa a nema masa lafiya. Dan na gaji da wannan sintirin ba yau babu gobe ana wulaƙanta ni da ni da yarona saboda wata ba ƙauyuyiyar yarinyar"
Cikin ƙunar rai babar ramma ta ce "Uwa uwa ce, babu banbanci tsakanin abin da ki ke ji a kan ɗanki da wanda nake ji a kan 'ya ta.
Da mazajenku sun sauke hakkin da Allah ya ɗora musu na al'umma, mussaman na karakara da babu yadda za ayi yaranmu su fito birni aikatau dan nema mana abin da zamu rufa wa kanmu asiri, balle yaranku marasa kirki da tarbiyya su keta musu haddi. Da sai dai can su haɗu da watsatsu irin su su lalace, ba dai da yaranmu ba.
Ba komai kuɗi zai iya saya ba, an riga an cuceni, ko a hukunta ɗanki ko ba a hukunta ɗanki ba, ya riga ya cuce ni, ubansa ya kashe mini ɗa, ɗanki ya keta wa ya ta haddi, ya dawo ya nemi nima ya keta mini haddi, ya jaddada mini shi ya yi wa 'ya ta fyaɗe na yi abin da zan yi ya ɗauke ta ya tafi da ita. Ubansa kuma ya ci gaba da bibiyar mu da yinƙurin sakawa a kashe ni, dan na nemi hakkin 'ya ta, uwa ce fa ni sukenan yaran uku, uba ya salwanta mini rayuwar ɗa, ɗanki kuma ya kassara rayuwar 'ya ta, kuma ki na gaya mini nawa zaki bani, ki je can da tsiyarki, ɗa ne na ji ɗan sunna ne, za ta haife shi a kawo muku tsiyarku, amma ba zan bar wurin nan ba sai ya sakar mini 'ya" ɗif kowa ya yi yadda maman ramma take kuka mai ƙarfi, wanda yake fallasa asirin zunzurutun baƙin ciki da takaicin da yake cikin zuciyarta.
Ramma ta ƙanƙame mama, ta na jin tamkar ba ta yi wa kanta adalci ba, ba ta yi wa mahaifiyarta ba.
Nabila ma gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, a hankali Abdul ya saukko daga kan kujerar da yake, ya je gaban babar ramma ya durƙusa a kan gwiwoyinsa sai dai ya kasa ɗaga kansa, kuma ya kasa magana.
A hankali kuma ya ce "Tabbas ahalina sun zama tamkar wata muguwar kibiya, da ta rusa miki dukkanin ginin rayuwarki da ta yaranki.
Idan rahama za ta iya tunawa kwanki kaɗan su ka rage na nemeta na rasa, ta farka ta ganni ina kuka cikin dare. Na yi kuka ganin abin da mahaifina ya aikata, abin ya bani tsoro. Sai dai ina neman afuwarku, dan Allah kar a hukunta ni da laifin da babana ya aikata, a hukunta ni da iya wanda na yi, ba zan iya ɗaukar hukuncin laifukansa ba.
Dan girman Allah mama ki yi haƙuri, yadda ki ke iƙirarin ke ma uwa ce, ko sau ɗaya ki kalle ni a matsayin ɗanki, idan ya tsinci kansa a halin da nake ciki, ya tuba yayi nadama, watsar da shi za ki yi, ko kuma rungumarsa za ki yi ki ci gaba da yi masa addu'a da fatan shiriya?.
Na cutar da ku, kuma na san jarrabawa ce, Allah ya jarabce ni da matsanancin son rahama. Ina nan a kan bakana, a hukunta ni, zan karɓi hukuncin da duk aka yi mini, amma dan Allah kar ku ce na saki rahama wallahi ba zan iya ba. Sannan dan Allah mama kar ki tsani abin da rahama za ta haifa, wallahi ɗan halala ne, kar laifina ya shafe shi, shi ma ya zama lalatacce".
Ya kalli in da Viper ya ke ya sunkuyar da kai ya ce "Duk da ina ganinka tare da mahaifina, ban san iya girman alaƙar da take tsakaninku ba, ban san laifukan da ya aikata maka ba, babu sanya hannuna, ban sani ba. Amma duk da haka kai ma ina baka haƙuri, dan Allah kar ka hukunta ni da laifukansa, dan Allah kar ka ce na saki rahama. Ka san me nake ji, tun da ka taɓa tsintar kanka a makamancin halin da nake ciki, ba ƙarya nake yi ba da nake nanata muku, ina son rahama, dan Allah ku daina cewa na rabu da ita, ko in saketa, idan ciwon na bai kashe ni ba, tsana da tsangwamar da ku ke yi mini zai iya halaka ni"
"Amma Abdul ka yi asara ka bani kunya, yanzu duk a kan mace ka ke wannan abin? Yanzu halin da mahaifinka yake ciki da ɗan uwanka bai sanya ka yi kuka ka kira wa kanka mutuwa ba sai a kan mace?"
"Mummy waye silar shigata wannan halin, laifukan waye su ka ƙara yi wa rayuwata ƙawanya, daddy mahaifina ne, ya yi iya ƙoƙarin sa a kaina, amma laifukan da ya aikata sun shafe kimarsa, babu abin da zan iya yi a kan abin da ya aikata face na yi masa addu'a, kuma ya saduda ya nemi yafiyar waɗanda ya zalunta"
Shiru Viper ya yi ya juya ya fice, haushi ne ya kama Nabila, wace irin zuciya da Viper hake ne.
Maman ramma ma shirun tayi, ya riƙe hijjabin rahama, cikin marairaicewa ya ce "Dan Allah ki saka baki rahama, ki ce su yafe mini, kar su rabani da ke ba zan iya ba"
Ban da uban tsaki, babu abin da take yi.
Nabila Viper ta bayan Viper ta biyo ta na mita.
"Haba Vi, abin da ka ke yi ba ka kyautawa, haba dan Allah, ai atleast ko ba zaka amince ba ka tofa wani abun ko" shiru ya yi bai yi magana ba, bai kuma waiwayo ba.
Nabila ta zagaya, sai ta ga ya na share hawaye da handkerchief, ta fuskanci duk lokacin da za ayi maganar abin da ya shafi jauhar, ƙarara yake karaya, wasu lokutan sai ya zubar da hawaye. A kullum ta na jinjina girman ƙaunar da yake yi mata.
"Vi menene kuma? Kukan me ka ke yi"
"Leave me" ya faɗa ya na kawar da kansa gefe.
"Amma atleast yakamata ka ce wani abu ai"
"I say you should leave me, muddin ina kallonsa ina tuna Indabo ne mahaifinsa, ba zan taɓa aminta ayi duk wani abu da zai sanya ya samu sassauci ba. Sai dai ya yi gaskiya na san abin da yake ji, dan har gara shi da ni, ni abin da nake so ɗin ubansa ya yi mini silar rasa shi, ba na fatan ya shiga mawuyacin halin da ni na shiga a silar rashin abin da yake so. Ba kuma zan iya watsa wa mahaifiyar rahama ƙasa a ido ba, dan haka ba zan sake cewa komai ba, abin da mahaufiyarta ta yanke shikenan"
Jikin Nabila ya yi sanyi, hakan ya na nufin ya saukko, ya sassauta abin da ya ƙudurta a kan Abdul, sai dai ba kowa zai gane hakan ba, sai wanda ya san shi ya saba zama da shi.
A hankali ta koma ofishin, ta tarar still maman ramma ba ta ce komai ba, sai kuka da take ta yi.
Nabila ta ce "Ina ga, yakamata a bamu ko 3days ne, mu yanke shawarar ƙarshe"
A haka su ka watse, Abdul ya so yayi magana da ramma amma sai haƙura ya yi.
Bayan Viper ya koma gida, ya din ga tunani, sosai ya ga tsantsar nadama da damuwa a idon Abdul, wanda da mutane mai izza da jin kansa, ga gayu da hutu, amma shi ne duk ya koma haka saboda soyayya.
Ɗan mama kuwa an sako shi, kawai sai ganinsu su ka yi ya dawo, liti ya saka shi a gaba, ya na tambayarsa waye ya sako shi?.
Ɗan mama ya ce "Dama ni ai ba laifin komai na yi ba, kawai shaida ne ni dan mugunta aka garƙame ni".
"Ɗan mama ka ji tsoron Allah, ko waɗanda ka ke kai wa munafuncin ne su ka karɓo ka"
"A'a sakina kawai aka yi"
Nabila kuwa Alhaji mu'azzam kankarofi ta kira, ta gaya masa halin da ake ciki a kan lamarin ramma.
Ya ce "To ke ya ki ke gani barrister?"
"Sonake ka yi wa Viper da maman ramma magana, su yadda aje shari'a court kawai, tun da ya yi nadama, ko dan ɗan da yake cikin ramma"
Kankarofi ya ce "Ni a su wa zan yi wa Viper magana, taɓ babar rahaman dai wannan gayen ai sai dai ke ɗin, haka kurum ya din ga yi mini kallon banza ba zai yiwu ba"
"Na sani ya na da zafi, amma mutum ne mai sauƙin kai"
"A'a ban ga alama ba, ke dai ki ji da shi, zan yi wa mahaifiyar rahama magana" suka yi sallama a kan haka.
Alhaji mu'azzam da kansa ya je gida, ya din ga rarrashin maman ramma ya ce "Na san an yi miki laifi, amma yanzu sai mun so za a cigaba da yayata abin da ya sameta. Wasu lokutan sai an jarrabaka ka ke samun ni'ima. Ba dan abin da ya faru ba da babu lallai na sanku, balle na taimaka muku.
Da babu lallai garinku su samu albarkacin rahama, ta na son mijinta, idan har ki na son farincikin rahama, ki daure ki yi haƙuri, an san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an cuce shi ne.
Amma abin da zai sanya namiji ya yi wa mace fyaɗe ta dawo ta na sonsa ba ƙarami bane ba, su suka zauna da juna, Allah kaɗai ya san irin zaman da su ka yi ta fara son abin ta.
Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ki yafe masa kamar yadda ya nema, yayi nadama na je na ganshi ai, saboda na taimaka muku, matata ƙanwar ubansa yanzu ta bar mini gida, wai na tozarta ɗan uwanta, kuma rahama mai aikinta ce, ba irin bautar da ba ta yi mata ba, kuma ban tsaya muku dan ina son ɗaukar fansa a kan ubansa ba, na tsaya muku ne a matsayina na uba, wanda na haifa nima, ba zan so ayi mini haka ba, amma ki yi haƙuri, ba kuma dole zan yi miki ba ba a yafiya dole, amma ba ki san me Allah zai yi miki ba albarkacin yafiyar ba. Abin alfahari ne a sanadin rahama Allah ya shiryi Abdul" ya daɗe ya na yi mata nasiha mai ratsa zuciya.
Ta amince da a kai ƙarar shari'a Court, dan Abdul ya samu sassauci.
Amma hakan bai yi wa babar Abdul daɗi ba, a gaban Alƙali aka karantawa Abdul laifinsa, a chamber alƙali a ka yi shari'ar, domin privacy ɗin rahama da identity ɗin shi kansa Abdul ɗin.
Ana karanta masa laifin, Abdul ya amsa, Alƙali ya ce a kai masa shi prison, bayan sati uku a dawo ya ci gaba da saurarar ƙarar.
Waro ido Rahama ta yi, ta san Abdul ba zai iya zaman prison ba, babu yadda lauyoyin Abdul ba su yi ba, a kan a bayar da belin Abdul, amma Alƙalin nan ya murtuke ya ce babu wannan.
Babarsa ta ce "Shi ya janyo wa kansa, dama haɗa baki aka yi, aka zo shari'a court, dan a kulle shi a tozarta shi"
Aka taso ƙeyar Abdul, Rahma ta kasa damuwarta da ruɗewa, ya kalli maman ramma ya risunar da kansa.
Ta bakin lauyoyin sa, suka yi wa su Viper godiya, bisa alfarmar da aka yi musu, aka gabatar da shari'ar kotun addinin Muslunci.
***
Nabila na office ɗin ta a zaune, Sumayya ta turo ƙofar ta ce "Suprise"
Nabila ta ce "Ko ma ki yi mini sallama malama"
Sumayya ta ce "Ba zan yi ba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ki ci kanki"
Sumayya ta ce "Nabila ana ƙoƙarin hana gudanar da recall election, an kuma sake ɗagawa ba ki ji raina ba"
Nabila ta kwaɓe baki ta ce "Mhmm, ai na san a rina, sai dai idan ba a ƙasar nan muke ba, na ji ana maganar EFCC za su sake shi, amma haryanzu babu wani tartibin bayani a kan laifukan da ake tuhumarsa da shi"
Sumayya ta ce "Za kuwa mu yi raising alarm a social media, lallai ayi mana bayanin meyake gudana ina kuɗin al'umma suke?"
Nabila ta kwashe da dariya ta ce "Ɗansa ya wawushe fiye da rabi, ya yi wa matarsa hidima, Ai Allah ba azzalumin sarki bane, kuma wani ikon Allah yaƙi faɗar ɗansa ne ya wawushi kuɗin"
"Ya za ayi ya faɗa, dama fa ware su aka yi dan yayi campaign, shi kuwa yayi campaign a in da ya dace. Wai ina mutuniyar ki Naja'atu Bunkure ne?"
"Oho mata na daina jin ɗuriyarta, ina nan ina tattara ƙorafe-ƙorafe a kanta, zan kai ma'aikatar Shari'a, she's not suppose to practice law at all, her licensed must be seazed in sha Allah"
Sumayya ta duba wayarta ta ce "Ke ni fa tare nake da baƙo, bari na yi masa magana ya shigo".
Babu tsammani Sumayya ta shigo tare da wani mutum, da ko ba a gaya wa Nabila ba, kamaninsa ya bayyanar mata da waye.
Babu in da Viper ya bar kamanin mahaifinsa, shi ma haka yake dogo mai jiki, akwai alamar hutu a tare da shi, daga yanayin suturar jikinsa.
Babu shiri Nabila ta miƙe, ta ce "Abbu sannu da zuwa, Sumayya ai da ni ki ka yi wa magana sai mu je mu same shi.
Ta gyara masa kujera, ta ce "Bisimillah" sai dai ya daskare a wuri guda ya na kallon Nabila.
"Jauhar ya na ganki a nan kuma?"
Sumayya ta ce "Ba jauhar ba ce ai, wannan Nabila ce"
"Ya za ki ce mini ba jauhar ba ce ba?"
Nabila ta ɗan yi murmushi, ta ce "Abbu ni sunana Barrister Nabila Yusuf maitama, ita kuma sunanta Fatima Bashir Azare. Ka zauna dan Allah" ya zauna a hankali ya na bin Nabila da kallo.
Ta kawo masa ruwa, ta nemi wuri ta zauna ta ce "Abbu ya gida ya iyali?"
"Alhamdilillah, amma idan ba jauhar ba ce ba, ya aka yi ki ke kirana da sunan da iyalina suke kirana da shi?"
"Saboda na san tarihin rayuwar Viper, an sanar da ni komai"
Ya jinjina kai ya ce "Kin yi abin da ya tabattar mini da be ke ce Jauhar ba"
Nabila ta ce "Me na yi?"
Ya ce "Jauhar ba za ta taɓa kiransa da sunan da ki ka kira shi ba na Viper"
Nabila ta ce "Afuwan Allah ya sa ba laifi na yi ba?"
Abbu ya ce "Ko kaɗan, ba ki yi laifi ba, amma ina cike da mamakin yadda ya zamana ba ke ce jauhar ba, duk da a zahiri ban ga bambancin naku ba"
Nan Nabila ta labarta masa kaɗan daga abin da yakamata ya sani, game da alaƙarta da jauhar. Ta numfasa ta ce "Abbu, duk da mu yaranku ne, kun fi mu tunani da hangen nesa, amma iyayenmu maza kuna tafka kuskure.
Da mahaifiyar Viper ta na raye, ko a gabanta ya kashe jauhar, da ya dawo ba za ta kore shi ba.
Har mahaifin jauhar ya ce bai yarda zai kashe masa 'ya ba, amma Abbu kai ka kasa karɓar Viper. A lokacin da ƙaddara ta kai ni cikin rayuwar Viper, ya fid da ran samun sassauci a rayuwa. Ga ƙwaƙwalwars ta taɓu ga shaye-shaye fiye da da da ya din ga yi.
Allah ne kawai ya bani sa'a a kansa, daga shi sai abokansa da su ka riƙe shi, su ka karɓe shi su ka sadaukar da ta su rayuwar, saboda su rayu da shi.
Na yi iya ƙoƙarina a kansa ya dawo in da kake, amma yaƙi sosai yake fushi a kan abubuwan da su ka faru"
Abbu ya yi shiru, cike da jimami da kaico a kan wasu abubuwa da ya aikatawa rayuwar ɗan sa.
Ya numfasa ya ce "Haka ne, haƙiƙa ni mai laifi ne a rayuwar Al'amin, duk da ni na haife shi, na cancanci na nemi gafararsa, dan sai daga bayan nan na fuskanci a lokacin da ya lalace, watsi da na yi da shi, ba shi ne masalaha ba.
Amma dan Allah babu yadda za ayi ku taimaka ku haɗa ni da shi. Zan yi duk mai yiwuwa na ga na gyara kuskuren da na aikata a baya. Sannan duk wani support da ake buƙata in sha Allah zan bayar".
Nabila ta numfasa ta ce "Ina haɗaku zai sauke mini kwandon masifa, duk wani ƙoƙari da nake yi a kan shari'ar ku, zai iya mayar mana da hannun agogo baya. Ranar da na haɗaku a waya ma, sai da muka yi faɗa da shi sosai.
Sannan duk da ka na mahaifinsa, idan na haɗaku na saɓa yarjejeniyar privacy ɗin sa, da aka ja mini kunne a kai. Abu ɗaya zan iya ce maka, shi ne ka din ga halartar kotu wurin gudanar da shari'ar sa, kuma a sakamu a addu'a, sannan in sha Allah zan cigaba da ƙoƙarin shawo maka kansa"
Abbu ya yi shiru sannan ya ce "Na yi kuskuren biye wa zigar mace, da hawa dokin zuciya na wofantar da ɗa na, na riƙe na wani, ƙarshe na zama mara kima a idanunsu. Ki ba wa Al'amin haƙuri, ki gaya masa abbu ya na kewarsa".
"In sha Allah zan sanar masa, kuma komai zai dai-dai ta, na yi maka alƙawarin bibiyarsa da ci gaba da tausar sa, kamar yadda ya jagoranci haɗa ni da mahaifina"
Ya jinjina kai ya ce "Na gode muku sosai da sosai, Ubangiji Allah ya biya ku da gidan aljanna, 'yar jarida ke ma na gode sosai"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai Abbu"
Nabila ta tashi ta ce "Abbu ba ka sha ruwan ba, na saka order ma a kawo maka abinci"
Yayi murmushi ya ce "A'a Alhamdilillah, bari na sha ruwan dai, kasuwa zan tafi"
Nabila ta ce "Allah ya tsare hanya, in sha Allah za mu zo har gida mu gaishe ka"
Ya ce "Da kuwa na yi farinciki da haka. Ai daga ke har Sumayyan, na zata zan ga manya, na ganku duk 'yan yara matasa, Ubangiji Allah ya dafa muku yayi muku jagora baki ɗaya, Allah ya raya mana ku, ya tsare ku daga Sharrin mai sharri"
Su ka raka shi har gaban motarsa, sai sanya musu albarka yake yi, ya buɗe motar, ya ɗaukko kuɗi ya ce "Ga wannan kwa sha ruwa, na gode sosai"
Nabila ta ce "Haba Abbu, ai Addu'ar da ka yi mana ma ta isa, mun gode sosai da mu da Viper a cigaba da sanya mu a addu'a"
"Addu'a kullum cikin yin ta ake yi, amma sai kun karɓa, sai dai idan kyautar Abbun ce ba kwa so" da kyar su ka karɓa, ya yi ta yi musu godiya ya tafi.
Bayan sun koma ofishin Nabila, Sumayya ta ce "Ohh su Abla sai ɓare-ɓare ake yi, an ga siriki"
Nabila kawai ta girgiza kai, ta din ga jinjina maƙudan kuɗin da ya basu kyauta, mutumin da zai iya bayar da wannan kyautar kuɗin, lallai mutum ne mai rufin asiri.
***
Laraba ta bawa ranar samu in ji hausawa, ta kasance ranar da za a ci gaba da sauraren shari'ar Viper.
Kotu ta cika iya cika, da masu ƙara waɗanda ake ƙara, lauyoyi 'yan jaridu ƙungiyoyi kotun cike fal.
Bayan an kira ƙarar su Nabila, aka fito
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 98 Chapter of 121