Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
80 / 121
mijina bane mama" "A'a ba Alhajin ba, Aminu" Cikin mamaki Nabila ta ce "Aminu kuma? Nifa ban taɓa aure ba, ba ni da aure" tayi maganar tana murmushi. Babar ramma ta ɓoye mamakinta, kar kwaɓarta tayi ruwa ta ce "Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke ta ƙoƙari a kanmu" Nabila ta ce "Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a rayuwarmu" Maman ramma ta ce "In sha Allah, addu'a yanzu aka fara" Nabila ta ce "Na gode sosai" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa. Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba. A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi. "Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an riƙa a gida babu aure, abun bai yi miki yawa ba kuwa Nabila" Sauda tayi maganar tana dariya. Ta sake cewa " An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda baƙin naci, kin liƙe mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da baƙin cikin ki a banza ba" Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaɓa mata magana. "Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ƙi karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ɗayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daɗin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki bayar nonsense" Sauda ta tashi a ƙufule, Nabila ta ce "Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki ka zauna" Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta. **** Cikin mamaki Abdul ya ɗago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaɗa masa. "Ina na kai mini kuɗi Abdul?" Abdul ya yi shiru yaƙi magana. "Ka gaya mini in da ka kai mini kuɗi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ɓacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai watsa mini ƙasa a ido ba, ina ka kai mini kuɗi?" Mahaifiyar Abdul ta ce "Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuɗin da ya zuba a account ɗin ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?" Abdul ya numfasa ya ce "Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a" ya faɗa kai tsaye. Salallami suka hau yi, da tafa hannu. Indabo ya ce "Abdul, kuɗin ka kwasa ka ƙarar a kan garin yar matsiyata da karuwa?" Ya girgiza kai ya ce "Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fyaɗe nayi mata, nayi hakan ne, dan na goge laifina" A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ƙiba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar P.A ya janye shi daga jikinsa. "Ƙarya ma kake yi, ka fito mini da kuɗina, sai na yi seazing ɗin asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita". "Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta" Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, kuɗin da suka yi sama da faɗi da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da kuɗin da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama kuɗin mutane ne na wasu hukumomi a ƙasa, ga balli na neman tashi, kuma Abdul ya yi masa hauka. P. A ya ce "Kayi haƙuri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara kashe case ɗin can na gaban kotu tukuna". "Na fara tunanin anya Abdul ɗa na ne? Ƙiriƙiri ya zaɓi mace a kaina, ni zai tozarta?" P.A ya ce "Jarabta ce da kuma ƙuruciya ke damunsa" "A shekara talatin da shidan ne ƙuruciya?" P.A ya din ga bashi haƙuri yana lalaɓa shi, Abdul kuwa tunu yayi ficewarsa. ***** Madaki na zaune a cikin ɗaki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ƙofar gidan da yake. Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce "Madaki, yan ƙofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta fama da su, sai ƙoƙari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka" Madaki ya tashi ya ƙwalalo ido, sai dai kan yayi magana, sun faɗo gidan, sun kai su bakwai, suka zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na faɗa da yaran madaki. Duk da akwai ƙarfin zuciya, yana ta ƙoƙarin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ƙwari, suka din ga saransa, ƙarshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ƙasa tamkar abun banza, duk da iya ƙoƙarin da yaransa suka yi, su ƙwace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon ɗaukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da saƙo, daga ƙarshe da ƙyar jami'an tsaro suka kawo masa ɗauki, suka tarwatsa matasan, suka ɗauke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti. ***** "My Abdul" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya ɗago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba. "Meyafaru ne? Gaba ɗaya na ganka a cikin tashin hankali?" "Rahama abubuwa sun ƙara cakuɗe mini, barin ƙasar nan zamu yi" Cikin mamaki ta ce "Mu bar ƙasar nan, mu je ina?" "Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria" "Ban gane ba, uwata fa?" Abdul ya ce "Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan da ke" "Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi haƙuri ka yi abun da mahaifinka ya buƙata mana" Ya kalleta ya ce "Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fyaɗe? Ba wannan ne ya dame ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai" Murmushi ta yi masa da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen. **** Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu ɗauke da damuwa, Bunkure tayi ƙwafa ta ce "Gaba ɗaya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, ɗan hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun. P.A ya ce "Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya ɓoye yarinyar nan" Indabo ya girgiza kai ya ce "Ban san in da Abdul ya koyi wannan baƙin taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ƙulla harƙallar kuɗaɗen nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe kuɗin nan, ya yi wa yan ƙauye ayyukan raya ƙasa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har haka" Bunkure ta sauke numfashi ta ce "P.A ya batun barrister Nabila?" "Kamar yadda na gaya muku, sponsiring ɗin ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba" Indabo ya ce "Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar buƙatar sa ya ga ya kai ni ƙasa, ya rama abun da nayi masa, kuma yayi kaɗan". ***** Nabila na zaune a ɗakinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo ɗakin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi. "Nabila" Ta ɗaga ido ta kalleshi. "Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper" "Eh" ta faɗa a nutse. "Nawa aikin ki ke burin ɓatawa kenan, me nayi miki haka ne?" Ta kalleshi ta ce "Ba kai nake fatan ɓatawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na ɓata masa aiki. Gaba ɗaya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me" tayi maganar tana tashi ta bar shi a ɗakin. Tana office ɗin ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar masa gida. Kenan Abba ya goyi bayan ɗan sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba. Turo ƙofar office ɗin aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingiɗar da tayi, tana tunanin ina ta taɓa ganin baƙon nata. Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce "Baki gane ni ba ko?" Ta jinjina kai ta ce "Gaskiya dai" "Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci" Nabila ta ce "Ok, ina jinka" "Saƙo ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke" Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa. "Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku" "Ɗan yi sauri, ina da wurin zuwa" P.A ya ce "Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye shari'ar nan ta batun fyaɗe nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai maƙudan kuɗaɗe muddin ki ka aikata abun da na ce" Nabila ta ce "Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case ɗina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ƙoƙarin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case ɗin nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su ɗora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu riƙe da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan talaka kawai ba, everyone is equal before the law" "Haka ki ka ce?" "Hala kurma ne kai?" Ya ce "To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka" "Na santa farin sani, tun da na ɗaukko ƘARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa" P.A ya kalleta ya ce "Me ki ke nufi?" "Zaka fahimta nan ba da jimawa ba" Yana fita tayi tsaki, ta ɗauki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan Viper. Yana tsakar gida, daga shi sai ɗan mama a gidan, suna hira. Sun daɗe suna kallon juna, sannan ta ƙarasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa uffan ba. Ya samu abu ya zauna, ya ce "Ya ake ciki, meye labari?" "Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka" Ya tsuke fuska ya ce "Menene?" "Vi" Ya Kalle ta, tare da ɗage girarsa ɗaya. "Ka dubi girman zatin Allah, ka tausaya mini, ina ga ciwon zuciya na daf da kamani, kowa ya ja da baya ya juya mini baya, Abba ya yayyaga hotunan nan ya watsa mini, ya ce naje na nemi ubana na bar masa gida, daga shi har yan gidanmu, babu wanda yake kula ni. Gashi a  tsakiyar program sumayya ta hau yi mini tambaya a kanka, yanzu ta ko ina mutane sai attacking ɗina suke yi a media, saboda case ɗinka, client ɗina malam garba wai ya yanke jiki ya faɗi na je na duba shi, na tarar wai ya samu stroke, yanzu P.A ɗin Indabo ya bar office ɗina da tashi barazanar, kuma haryanzu ka ƙi gaya mini dalilin da ya sanya Indabo yake bibiyata. Na rasa ya zan yi me zan yi ne? Kamar na gaza, ba wanda zan je na samu duk na gaya wa damuwata, dan Allah Viper ka gaya mini wacece ta jikin hoton nan, ina jin kamar ina da alaƙa da ita, tun da ni dai na san ba ni bace ba, dan Allah idan akwai wani abu da ka sani ka gaya mini, atleast na rage wata damuwar". "Na gaya miki ban san komai ba, 'yan gidanku zaki tambaya" "Na gaya maka ba zasu gaya mini komai ba, so kake sai na mutu ban san babana ba, idan kana da yadda zaka yi ka taimake ni dan Allah, ko hakan ne alfarmar da ya rage da zaka yi mini a rayuwa" tayi maganar tana haɗa hannayenta biyu cikin sigar magiya. "Ana kiranki a waya" "Ni ba ta waya nake yi ba, ka taimaka mini dan Allah" "Ki ɗaga wayarki " yayi maganar yana kallon ta. Ta ɗaukko wayar, ta ga lambar barrister Habib ce, ta ɗaga wayar ta ce "Hello" "Na duba office ba kya nan, Allah ya yi wa malam garba rasuwa yanzun nan" miƙewa ta yi tsaye, ta saki wayar, ta tashi za ta nufi hanyar fita, jikinta yana rawa. Cikin zafin nama, Viper ya tashi ya riƙe ta, gaba ɗaya ta gigice, ta ce "Sun kashe shi, wallahi kashe shi aka yi" Ya ce "Waye? Waye ya kashe shi?" "Malam garba, wayyo Allahna, meyasa na karɓi shari'arsa, na janyo ya rasa raywarsa a banza, bani da sa'a wayyo Allah zuciyata" wata irin miƙa tayi, kamar zata zare, ta fara kokowar ƙwace wa daga hannun Viper, tana kallon hanyar waje. Ya ƙara riƙeta ya ce "Abla, tsaya ki ji, ki nutsu" Magana take son yi, amma numfashinta ya din ga sama yana ƙasa, hannunta da ya riƙe, ya din ga jin bugun zuciyar ta da sauri-sauri. Ya ciro wani abu a jikinsa, ya saka mata a gefen wuyanta, gaba ɗaya jikinta ya saki. Ya kalli ɗan mama ya ce "Ka kira mutanen nan a waya, su aiko da mota, a kaita Asibiti" Ɗan mama yayi saroro ya ce "A ina ta ajiye motar tata?" Viper ya ƙura masa ido, ya ce "Au, ammm wasu mutanen?" "A tunaninka duk abun da ka ke yi ban sani bane? Zaka kira su ko ni na kira su?" Ɗan mama yayi wiƙi-wiƙi da ido, cikin tsoro da mamaki". "Am talking to you, and you are looking at me" ba shiri ɗan mama ya ciro waya yana kallon Viper. **** "Abdul yau ka addabe ni, kamar nayi maka dukan tsiya haka nake ji" "Sorry baby, kin san kullum ke ta musamman ce, i so much love the natural you". Ramma ta ce "Wallahi ka isheni, duk ka dame ni" "Wallahi wani mafarki nayi da bai yi mini daɗi ba, ya bani tsoro". Ramma ta ce "Maganin wanda baya addu'a" "Wallahi ina yi, har karatun Alqur'ani nake sakawa fa" Ta ce "To Allah ya bada lada, yanzu ka bani wuri na je nayi wanka, zan yi salla". Ya tashi zaune ya ce "Mu je, daga nan sai ki ɗan dafa mana wani abun, yunwa nake ji" Yayi maganar yana ɗagota, daga kwancen da take. A tsakiyar gado suka din ga ciye-ciye da shi da ramma, suna yi yana tsokanarta, tana gaya masa baƙar magana yana dariya. Tamkar ya mayar da ramma cikin sa haka yake ji, kuma ya kasa ɓoye mata hakan, suka kwanta ya gama damunta, bacci ya kwasheta. Juyi ta yi zata gyara kwanciyarta, ta ga Abdul a zaune, ya saka wayarsa a gaba, ya ɗora hannu a ka, yana wani irin kuka tamkar ɗan ƙaramin yaro. Ayshercool 08081012143 76 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN *BRIGHT PENS SECOND BATCH* Ku kasance da littatafan bright pens, second batch. *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)* Tashi ramma tayi, ta ce "Abdul, wai menene meyafaru ne?" Yayi mata shiru ya cigaba da kuka. "Dan Allah kayi magana mana, ko mutuwa aka yi muku?" Yayi mata shiru bai yi magana ba, ta kai hannu zata ɗauki wayar, amma ya janye wayar ya kashe. Kawai ya yinƙura, ya ɗauki mukullin motarsa, ramma ta miƙe ta riƙe shi ta ce "Ina zaka je ne?" "Fita zan yi" "A wannan yanayin da ka ke? Idan wani abu ya sameka fa, dan Allah koma menene kayi haƙuri, zuwa Allah ya kaimu gobe, dan Allah ka haƙura da fitar nan" jifa yayi da mukullin, ya koma ya zauna ya cigaba da kuka. Ta zauna a kusa da shi, cikin damuwa ta cire masa hannunsa da ya rufe idanunsa ta ce "Abdul, kalleni menene wai?" Ya sake sunkuyar da kai, kamar ita ce baya son haɗa ido da ita. A hankali ya kwanta a jikinta kamar ƙaramin yaro, ta rungume shi sosai, tana shafa kansa ta ce "Koma menen kayi ta nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un, zaka samu sassauci in sha Allah" wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, wanda sai da ya bata tsoro. "Rahama" ya kira sunanta da kyar a galabaice. "Dan Allah ko na fuskanci hukunci, kar ki manta da ni, na san koma menene zuwa ki gama karatunki, zan fito" "Tom" ta faɗa a sanyaye, dan wasu lokutan har tausayi yake bata, gaba ɗaya Abdul ya saduda, duk wannan iskancin da rashin mutunci ba ya yin su. "Rahama kin ce mini kina da yaya da ƙani ko? Har su ina son in ɗauki nauyin su" Ramma ta ce "Ba na gaya maka yayana ya mutu ba, sai ƙanina sani" "Da gaske ki ke fyaɗe aka yi masa ya mutu?" Ta ce "Oho ina na sani, ba ka ce mini ba a yi wa maza ba, ni kamar haka na so na ji an ce, wai za a samo masa aiki, yaje Abuja aka yi masa, amma mama ba ta taɓa zama ta gaya mini yadda abun ya faru ba, ko tunawa ba ta son yi, idan ta tuno da shi tayi ta kuka" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ban san me zai faru ba, amma dan Allah duk tsanani kar ki rabu da ni, ki zama mai yi mini uzuri da tausaya mini dan Allah, Allah ma baya kama wani da laifin wani" Ramma ta ce "Da bana yi maka uzuri, da bana tunanin zamanmu zai zo i yanzu, ka daina wannan kukan dan Allah kunya kake bani" tayi maganar da sigar tsokana. Ya ƙanƙameta ya cigaba da sheshsheƙar kuka. "To ɗan jariri, ya isa haka, cikin dare kawai mutum ya tashi yana kuka, ko ka je ka yi alwala kayi salla". "Ba zan iya ba, ba zan yi karatun sallar dai-dai ba" "Kaga amfanin ibada ko, idan bawa ya tuna da Allah, lokacin da yake cikin yalwa, Ubangiji yana tuna wa da shi lokacin da yake cikin ƙunci, ka cigaba da addu'a, Allah ya yaye maka damuwar ka doctor Abdul yasar" yayi lamo kamar kyanwa a jikinta, ba tare da ya kuma magana ba. **** A hankali Nabila tayi juyi, tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta kawai ta ga Viper a zaune a kan kujera, yana danna waya. Ta ƙura masa ido tana kallon sa. "Wannan kallon haramun ne, ki daina yi mini wannan kallon" yayi maganar ba tare da ya kalleta ba. Ko ƙifta ido ba ta yi, ta cigaba da kallonsa. Ya waiwayo sosai yana fuskantar ta, ya ce "Ya aka yi ne? Ya jikin?" Ta ɗaga hannunta, ta kalli drip ɗin da yake shiga, ta ce "Vi" "Mmm" "Ina ne nan?" "Wurin sayar da mutane" yayi maganar yana cigaba da danna wayar. Ta lumshe idanunta ta buɗe, ta ce "Kamar bacci nake yi, kuma kamar a zahiri ne, dan Allah da gaske malam garba ya mutu?" Viper ya ce "Eh, ya mutu" Ta girgiza kai, tana kuka daga kwance ta ce "Ai shikenan, ya mutu bai shaƙi iskar 'yanci ba, ban cika masa alƙawarin da nayi masa ba, da yaya zan kalli iyalinsa? Kullum da shi nake kwana nake tashi a zuciyata, ya mutu da mummunan tabo a zuciyarsa da rayuwarsa, ban cika masa alƙawarin da nayi masa ba, na gaza na kasa" tai maganar tana fashewa da matsanancin kuka. "Ke, wai baki da tawakalli ne? Shikenan ke ba zaki mayar da lamarinki ga Allah ba? Wani ya ce ke ki ka kashe shi ne?" Ƙara sautin kukan ta yi, ta ce "Ya ka ji da aka kashe matarka, ya zuciyarka tayi da aka ƙala maka laifin kisanta? Haka iyalan malam garba suke ji, da wannan ɗacin da baƙin cikin ya mutu, kuma ni ban yadda da wani stroke ne ya kama shi ba, wani abun suka yi masa" Viper ya janyo kujerarsa gaban gadon sosai, ya matsa daf da ita, ya ce "Ki yi haƙuri" ta kalli cikin idonsa ta ce "Kai yakamata na bawa haƙuri nayi alƙawarin saka kotu ta wanke malam garba, a gurfanar da ainihin wanda yayi laifin, amma ya rasa rayuwarsa ina kan ƙadamin aikin, na fara tsorata kamar ba zan iya ba Vi" Ya girgiza kai ya ce "Zamu cigaba da ƙoƙari, ba zamu gaza ba, ba zamu sare ba, zamu yi nasara in sha Allah, idan kina cewa kin karaya, nima karaya nake yi" ta ja wata irin ajiyar zuciya ta kalli rigar jikinsa. "Vi" "Mmm" "Me kake ɓoye mini ne? Ba irin wannan rigar ka yaga lokacin kana Asibiti ba, mai tambarin dragon ɗin nan ba?" "Ki daina saka ido, kina ƙirga mini kaya, son rigar nake yi" hararsa tayi ta ce "Am not kid" "You are" yayi maganar very serious. Wani ne ya shigo ɗakin Nabila, yana shigowa ya ce "Viperrr" ya kira sunan yana jan sunan, tare da dunƙule hannunsa, ya miƙawa Viper, Viper ya dunƙule nasa suka haɗa. Ya ce "Ya madam, ta tashi? Barrister ya ƙarfin jiki?" "Ba sauƙi" ta faɗa tana tura baki. Duka suka kalleta, ya ce "Subhanallah, ba sauƙi fa, garin yaya meyafaru?" Ta nuna Viper, ta ce "Baya son na warke, bai iya jinya ba sam" dariya ya yi ya ce "Maza gumbar dutse, ina Viper zai iya jinya dama, ki manta da shi, zaki samu sauƙi in sha Allah, meyake damunki yanzu?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai, ƙirjina ne yake nauyi kawai" "To ki cire damuwa daga ranki, zai daina in sha Allah" Ta ce "Ok sir, na gode sosai" yayi rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa ya fita. "Vi" "Mmm" "Wai ina ne nan? Kuma waye wannan ɗin?" "Asibiti da likita" Nabila ta ce "Ai na san asibitin ne, ina son tafiya ne, zan je na ga malam garba" Viper ya kalleta ya ce "Kina da abun gaya wa iyalinsa ne?" Jiki a sanyaye ta girgiza masa kai. "To sai ki daina maganar zuwa" "To ina son na gaya wa yan gidanmu ina Asibiti, kar a neme ni" "Wa zaki kira? Wanda ya ce ki bar masa gida ki je ki nemi babanki, ko kuma yayanki da yake yi miki bita da ƙulli? Ko kuma sauran yan gidan da suke yi miki kallon yar hana ruwa gudu? Ba wanda ya damu da ke, mutum ɗaya

Chapter 80 of 121