a hankali, kanta na sara mata ga jiri saboda yunwar da take ji.
Tana daga kan kujerar a kwance, ya ɗage ɗaya kujerar da ƙadangaren yake ƙarƙashin ta, kawai ya saka hannu ya danƙi ƙadangaren ya jefa shi waje.
"Na shiga uku master, ƙadangaren ka ke kamawa da hannunka"
Tsaki yayi, ya wuce ɗakinsa, jikinta ya din ga rawa, tsigar jikinta ta din ga tashi. Ya dawo ya dire mata leda, ya ce "Ki ci ki sha magani" ya jefa mata wani kwali sannan ya fita.
Kwalin ne ya fara ɗaukar hankalinta, ta ɗauka da sauri tana dubawa, sabuwar mp ce kar 'yar ƙarama mai kyau.
Ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba, ta hau kukkunata tana dubawa, sai da ta gama, ta ajiye ta buɗe ledar.
Irin meatpie ɗin nan ne oasis manya kusan biyar, da ƙatuwar robar fura da nono.
Kasancewar a yunwace take kuwa ta hau ci, ta ji babu daɗi kwana biyu tana ciwo, amma bai iya yi mata sannu ba, dama magani ba ta saka ran ya saya mata ba, mutumin da bai ba ta abinci ba wane magani zai bata, ashe yana sane, sannu ce ko ya jiki ba zai iya ce mata ba.
Sai dai da tuna yadda ya ɗauki ƙadangare da hannunsa, sai tsigar jikinta ta tashi.
Ana yin sallar isha'i ya dawo, mp ɗin ta har da fitila.
Ta tashi tana yi masa sannu da zuwa, ya wani maze ya bata wata ledar, sannan ya zauna ya ce "Ki nemi wata ma'aikaciyar idan akwai a nan kusa, tayi miki, idan ki ka je wurin wancan ɗan iskan na bakin hanya kuma ni da ke ne"
Ta saka hannu biyu ta karɓa, allurar zazzaɓi ce mai tsada ya sayo ya kawo mata, amma bai iya cewa ya jiki ba.
"To godiya nake master, Allah ya ƙara arziki ya sa a fi haka, na ga saƙo ma na gode sosai da sosai Allah ya sa afi haka".
"Amin".
Ta ce "Ga naka na ajiye maka"
Ya ce "Idan zan ci ba sai kin ce na ci ba, ki daina kuma wannan mugun tsoron, komai ya baki tsoro, idan ba haka ba ki kashe kanki a banza"
Jauhar ta rausayar da kai ta ce "Nima ban san ina jin tsoron ba ne. Amma kai ba ka jin tsoron sa ka riƙe shi da hannu?"
"Ban sani ba? Rannan kwaɗo yau ƙadangare, meye abun tsoro a jikinsu, har da suma saboda ƙadangare" tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Sai da ya gama sannan ta ce "Ka yi haƙuri to, ban san ya ake yi nake jin tsoron ba".
"Idan ma kina sane ki cigaba da yi mini ihu a gida kamar gyare".
Sai da ta yi murmushi ta ce "Zan koyi jarumta, zan daina jin tsoro in sha Allah. Yauwwa master yaushe zamu je ka kai ni na gaida su mama? Ba su taɓa ganina ba, ban taɓa ganinsu ba, su hajiya kawai na taɓa gani, yakamata ka kaini na gaishe su. Sai ayi girki mu je mu gaishe su, na ga haka ake yi".
Shiru yayi, yana tuna Ummansa, tana yawan cewa Allah ya raya mini babana na ga aurenka, in ga mai sa'ar da zata auri ɗan autan mazana
Jauhar ta ce "Ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai ne maganar da na yi"
Ya tashi tsam ya ce "Yauwwa, Ina sake jaddada miki, idan ba zaki iya zama ba, ko kin gaji zaki iya komawa gida, babu takura, na ga shekaranjiya kina ta koke-koke, idan da takura you are free to go" daga haka ya nufi ɗakinsa.
Gabanta ya faɗi ta fara tunanin, me ta ce da zai ɓata masa rai har haka?.
Haka nan ta ji ba ta fatan abun da zai sake mayar da ita gida yanzu, da sunan zawarci ko ace ta kasa zama, saboda ta san dama mugunta ce ta saka aka aura mata shi.
A ranta ta ce 'Zan jure, in sha Allah zan bawa mara ɗa kunya, in sha Allah, Allah ba zai kunyata ni ba, ba zan tagayyara ba"
Lokaci-lokaci yake leƙowa falo, sai ya hangota tana aikin stone ɗin ta, tana jin radio a mp. Yana so yayi mata maganar ta je ayi mata allura, amma ya fasa.
Bacci ta fara, ji ta tafi ta je ta kwanta, har ta fara bacci aka kawo wuta, hasken lantarki ya hasketa, ba shiri ta tashi, sai a yanzu ta tuna ba ta kashe ƙwayayen ba, ta fita falo dan ta kashe, taga Al'amin ya fito daga ɗakinsa, yana soke wuƙa a ƙugunsa.
Ta tsura masa ido tana kallonsa, bai san tana falon ba, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu, ɗaure fuska yayi ya zo zai fice.
Ta ce "Master ina zaka je a daren nan, kuma?"
Ai ko sake kallonta bai yi ba, ya nufi ƙofar fita.
"Dan Allah kar ka je in da za a illataka, zuciyata ba ta yi mini daɗi in ga kana zubar da jini".
Bai tsaya ba, sai da ya dangana da tsakar gida, ya kama katanga ya dira, ita kuma ta zauna a wurin ta fashe da kuka mai taɓa zuciya.
Ko da ya fita titi, liti ya zo a kan babur ya ɗauke shi, suka tafi.
Unguwar shiru, kowa ya shige gida, suka maƙale a wani wuri su na shaye-shaye.
Can sai ga wanda suke hari, ya kwararo layin a kan babur, Al'amin ne ya fita da sauri, ya daki tayar gaban babur ɗin, aikuwa ya faɗi ƙasa da shi da babur ɗin.
Suka rirriƙe shi, Al'amin ya zagaya dai-dai kunnensa ya ce "Tijjani Faruk ko? Gargaɗi aka ce ayi maka, a kan rubuce-rubucen da ka ke yi a dandalin sa da zumunta, da waɗanda ka ke suka, da Switzerland na so na yi maka warning ɗin, amma a yadda ka ke ɗin nan, zaka iya ɗayewa idan nayi maka da ita, ko iraƙi na saka maka a jiki ba zaka shura ba.
Liti, duba bayana, ka ciro Russia ka yi masa rijiya a cinya, ka yi masa eleven da iraƙi a gadon bayansa".
Tijjani yana ihu, yana kururuwa, yana komai, liti ya caka masa wuƙa a cinyarsa, ya yage masa riga, ya yanke shi sau biyu a baya, ya watsar da shi a wurin yana kururuwa.
Can gida mama tana ta sintiri, har sha biyu saura, ba ta ji an ce Tijjani ya shigo gida ya ɗauki abinci ba, ta din ga kiran lambar wayarsa amma a kashe.
Tana ta mita, aka kira baba a waya, aka sanar musu, an tsinto tijjani a hanyar dawowa gida, an yanke shi da makami, an tafi kai shi asibitin cikin gari, sashen bayar da agajin gaggawa.
Ɗora hannu ta yi a ka, tana ihu tana ta shiga uku an kashe mata ɗa.
Baba ya ce 'Ba cewa aka yi ya mutu ba, an yanke shi aka ce, ƙila masu ƙwacen waya ne ki bari mu je mu gani mana"
Ya fita ya kira maƙwabcinsa, ya ce ya raka shi asibiti, domin su ga a halin da Tijjani yake ciki.
Ala'amin bayan ya koma gida, a falo ya tarar da jauhar, sauro yayi dandazo a kanta yana cizo, sai ajiyar zuciya take yi ta ci uban kuka.
Tsayawa yayi yana kallonta, tare da jinjinawa taurin kanta.
Kamar ya tsallaketa ya wuce, ya durƙusa ya kwasheta kamar tsuma ya nufi ɗakinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita a kan gadon, ta buɗe idonta tare da ƙura masa ido.
Tsaki yayi ya fita, ta mayar da kanta ta kwantar a kan pillow.
Al'amin sawun keke ne, Allah kaɗai ya san in da ya dosa, ɗazu ya gama cewa idan ba zata iya zama ba, ta tafi gida, amma yanzu ya tsinto ta a falo ya kawota ɗaki.
Da safe ta dafa tea, ta kawo masa da sauran meatpie ɗin da ya so jiya, yau bai yi rejecting ba ya karɓa ya fara ci.
"Master"
"Mmmm"
"Na iya irin wannan meatpie ɗin fa, idan ka na so ka sayo mini kayan, na iya sosai mai daɗi".
Ya ce "To".
Da tana jin kunyar cin abu a gabansa, amma zuwa yanzu ta saba, ta gama cin nata, ta je ta kwaso kayansa da suka bushe, tana ninkewa ta saka zare da allura, tana ɗinke masa waɗanda suka yage.
Yana kallonta tana yi, shi kuma ya karkace zai kunna sigari.
"Master, shan sigari yana cutar da lafiya fa, ka din ga ragewa dan Allah, kar ka yi rashin lafiya".
"Kin je an yi miki allurar?"
"Zan sha magani, ba na son allura ne tsoro nake ji"
Tashi ya yi zaune ya ce "Ƙadangare, kwaɗo yanzu kuma allura, sannu 'yar madara. Sai ki biyani kuɗin allurar da na saya" yayi maganar yana barsawa yana gyara gefen rigarsa.
Tayi dariya, jin yau ya kulata, har ya ɗan yi doguwar magana da ita.
"To nawa ne, sai na tara da kaɗan-kaɗan na biya ka" yayi shiru yana cigaba da sakin hayaƙi.
Ta sake gyara zamanta ta ce "Master Mp nan fa tayi kyau sosai, Allah ya ƙara maka buɗi"
Ya jinjina mata kai.
Tijjani kuwa ba ma ya hayyacinsa, saboda ya zubar da jini sosai da sosai saran da su Viper suka yi masa, da ƙyar aka samu ya farfaɗo.
Cinyarsa sun yi masa rami da ɗan buda, likitoci sai ƙoƙarin ceto ransa yake yi.
"Sai oga"
"Yaya na ji shiru fa, haryanzu kuna tsare da yarona".
"Na sani, trape ɗin muke setting, idan muka yi gaggawa aikinmu zai kwaɓe"
"Ok ina saurarenku".
Jauhar sai murna take yi, zata je registration makarantar su, dama tun da aka kawota ba ta je unguwar ba.
Da safe tana ta shiri, ya fito zai fita ya ajiye mata dubu ɗaya ya ce "Ki hau mota"
"Na gode sosai da sosai, Allah ya sa a fi haka, ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai" ba shiri ya kalleta, ya ga ba shi take kallo ba, sai jujjuya dubun take yi tana murmushi.
"Da ina da wata ba zan kasheta ba, ina son sabon kuɗi sosai" tayi maganar tana ƙara faɗaɗa murmushin ta.
"Sai ki ɗinka ta ki saka tun da riga ce"
"Kuma zata yi mini kyau fa, adawo lafiya, Allah ya tsareka"
Ya amsa da "Amin"
Jauhar ta ƙarasa shirinta, ta tafi makaranta, kamar yadda Baba ya ce mata ta je tayi registration, a nan ta haɗu da 'yan makarantar su, ta din ga murna sun haɗu da 'yan makarantar su, da malaman makarantar ma.
Ta din ga yi wa ƙawayenta mitar ba su je gidanta ba.
"Jauhar wa zai zo gidanki kina auren ɗan daba? Ba ma za a bar mu mu zo ba"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Ku daina fakewa da haka, ni da muke tare, ya aka yi bai yi mini komai ba?"
"A'a ai ke matarsa ce, mu kuwa fa"
Duk da ba ta gaya masa ba, haka kawai ta ji tana son ta je gida.
Ganin ko ta fita ba hanata yake yi ba, ya sanya ta nufi hanyar gida.
Gaba ɗaya sun yi mamakin ganinta, Anty ta ce "Yaya, ya na ganki yanzu meyafaru?"
Jauhar ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau anty, registration na zo na ce bari na biyo, tun da kun ƙi zuwa".
Kallon jauhar suke yi, su ga ko akwai wani abu na tashin hankali a tare da ita, ko alamar duka ko makamancin haka, amma ba su gani ba, sai ma wata nutsuwa ta mussaman da suka gani a tare da ita.
Mama ta ce 'm"Jauhar kin kyauta, wato miji daɗi, ki ka kasa zuwa ki duba ɗan uwanki, ya kusa mutuwa"
Cikin tashin hankali jauhar ta ce "Subhanallah, mama ban sani ba ba shi da lafiya ne?"
"Ina fa, ya dawo daga aiki, aka samu wasu suka sassare shi".
Abun ya ɗagawa jauhar hankali, ta ce musu ba ta sani ba.
Al'amin yana can wurin su Walid, kansa yana yi masa ciwo, ga yana jin yanayin jikinsa kamar zazzaɓi yana son kama shi.
Yana jin wayarsa na ta vibrating yayi banza.
"Viper wayarka fa ta cika mini kunne, dan Allah ka ɗaga"
"Ƙyale ni, kamar zazzaɓi ne zai kama ni"
"To ka kashe wayar mana".
"Ba zan kashe ba"
"Ka duba mana ko beb ɗin ka ce take nemanka, yarinyar nan ta na kula mana da kai yasin".
Viper yayi tsaki, ya sake gyara kwanciyar sa.
Walid ya miƙa hannu, ya ɗauki wayar ya ɗaga ya ce "Ya aka yi?"
"Ka gaya wa uban gidanka, na ga cikarsa ta shigo mana arear, duk da kashedin da na yi kar ta sake zuwa, tun da ya kwasheta. Yayi ganganci mafi girma da muni, tun tun da ya bari ta shigo, ya zo ya ɗauki gawarta a dabata!.
Ayshercool
08081012143
26
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Walid ya kalli Al'amin, ya lumshe idanunsa, wasu irin jijiyoyi suka fito raɗa-raɗa a goshinsa.
Yayi shiru ya ƙi ko motsawa.
"Mai zamani, ba ka ji me ya ce ba ne, matarka fa yake maganar ka je ka ɗauki gawarta"
"Na aiketa ne?"
"Ban gane ka aiketa ba? Kai kut....." Ya ɗura masa ashar.
"Idan da gaske ya kasheta fa?"
Al'amin ya tashi zaune, ya ɗauki wayarsa, ya danna ya kira wata lamba.
"Yeah maza"
Ya ce "Ina aikin da na saku?"
"Ai ta gama ta tafi ma"
Ya ce "Ba tafiya a ta yi ba, gidansu ta tafi, ba ka kira ni ka gaya mini ba. Wancan garan ya ce in je in ɗauki gawarta a dabarsa, wallahi ya kashe 'yar mutane sai na kasheka kai ma"
"Haba maza, cewa ka yi mu saka ido, ta shiga ta gama abun da take yi ta tafi, kuma min bi ta ba ta sani ba, ta gama ta tafi ba ka ce mu bi ta mu ga ina zata tafi ba"
"Wallahi liti ka bari muka haɗu sai na saka maka ƙarfe, ka ji na rantse. Ya ajjye wayar ya yinƙura, Walid ya ce "Ina zaka je, ka ce ba ka jin daɗi, ka zauna bari ni na je"
"In zauna sai ya kasheta, sannan zan je?" Yayi maganar a zafafe.
Walid ya bi shi da kallo, yana son gano haƙiƙanin in da ya dosa, amma bai gane ba, Al'amin ya sake birkicewa ya ce "Ya kasheta ko ya bar ta da rai, ba shi ne a gabana ba, tun da ba ni na gayyato ta rayuwata ba, abu mafi muni shi ne ace madaki ya kuma yi mini illa, idan haka ta kasance, kan mai uwa da wabi, zan ɗauki matakin da ya dace".
Ya fita da sauri, Walid ya bi bayansa, bai ma san ina ne gidan na su ba, sai da walid ya yi masa jagora, yaran madaki suna ganin Al'amin ya shigo musu unguwa da rana tsaka, amma aka rasa mai tunkararsa, dan ba su fiye galaba a kansa ba, sai sun yi masa taron dangi.
Suna tafe a hanya, liti ya kira Walid ya ce masa "Ka ce ya kwantar da hankalinsa, na yi waya tana lafiya tana cikin gidan su, zamu fito da ita lafiya in sha Allah"
Walid yana gaya wa Viper, ya ce "Ka ce masa bana so" ya yi maganar yana ƙara sauri.
Jauhar kuwa na can, har ta ɗora musu girki, sai zungurarta suke yi, su ji a wani hali take ciki a gidanta, da irin zaman da take yi da Al'amin, amma ta dinga waskewa, taƙi gaya musu komai.
Hafsa har da tambayarta, wai wuri ɗaya suke kwana?.
Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "To zai kwana a waje ne yana da mata?".
Surayya ta ce "Iyee zama da maɗaukin kanwa, wato har bakinki ma ya buɗe haka?"
Jauhar ta yi dariya ta ce "Kai Anty surayya tambayata fa tayi, bari na ƙarasa na je gida ma na yi girki, kar ya dawo".
A tunaninsu za su ga jauhar cikin mawuyacin hali, amma sam ba su ga alamar hakan ba.
Ta shiga suka gaisa da anty lubabatu,ta din ga murna yadda ta ga jauhar, babu alamar wahala a tare da ita, ta aika 'ya'yan anty lubabatu su je gidan kakannin su, su karɓo mata shirin dutse a wurin ƙanwar anty lubabatu. Da yake duk a unguwar ne.
Anty lubabtu har da harhaɗawa jauhar 'yan kayan gyaran aure na mata, ita dai ba ta ce komai ba, ta karɓa ta ce ta gode.
Da ta fito daga gidan, ta lura da wasu matasa da ba ta san suwaye ba, a layin amma ba ta damu ba ta shige gida.
Walida ta tare ta ta ce "Me Anty lubabatun ta baki?" Suka karɓi ledar hannunta, suka ga kayan mata da turarukan wuta da humra masu kyau da ƙamshi.
Suka din ga yi mata dariya cikin izgilanci surayya ta ce "Wai nan ba ki yadda ba ke matar aure ko jauhar? Dan Allah ya ki ke yi ke kuwa da shi, ga 'yan shaye-shaye da ƙazanta, kuma har kiss ku ke yi?"
Jauhar ta yi wani irin murmushi ta ce "Yaya surayya kenan"
"Gaya mana man"
"To ni me zan ce? Annabi ya hana faɗa, sirrinmu ne ai"
Surayya ta ce "Lallai, yau na ga illar ƙani ya rigaka aure, ni ki ke gaya wa baƙar magana jauhar?
"A'a ki yi haƙuri, ba baƙar magana ba ce"
Ta karɓe kayanta, ta saka a jakarta, ta cigaba da aikinta.
Ta zauna tana yanka salak, sai mita take yi ba ta haɗu da yaya saifu ba, kuma baba ma baya nan"
Tijjani ya fito yana ɗan tattakawa, ta din ga yi masa sannu.
Tun da ya shigo layin yake ganin yaran madaki tsilla-tsilla, alla-alla yake yi ya ƙarasa ya tabattar da abun da madaki ya faɗa gaske ne ko akasin haka, idan gaske ne bai san iya adadin haukan da zai yi masa ba.
Walid ya ce "Ga gidan nan" dai-dai lokacin ɗan gidan anty lubabatu ya zo zai shiga gidan su jauhar, hannunsa riƙe da ledar viva, an zubo mata dutsen shiri da kayan yi kala-kala, babar anty lubabatu ta ce a bata kyauta a matsayin jari, shi ne gudunmawarta na biki.
"Kai shiga nan gidan ka ce.... Sai kuma ya yi shiru dan ya manta sunanta, sai Fatima yake iya tunawa.
Walid ya ce "Ka faɗa masa sunan"
Tsaki yayi ya ce "Na manta sunan, sunan wani iri ne dai haka kamar Angela"
Walid ya ce "Amma kuwa ka yi asara"
Al'amin ya ce "Ka ce 'yar madara ta zo in ji Master"
Walid na son yin magana, ya maze ya ce "Na san ƙarya fa madaki dama yake yi bai kasheta ba".
Yaron ya shiga ya fara ba ta saƙon hajiya kakarsa, na bata kyautar dutse, ta karɓa tana murna da godiya, sannan ya ce "Wani a waje ya ce wai 'yar madara ta zo" take gaban Jauhar ya faɗi.
Walida ta ce "Wace wata 'yar madara, babu ita a gidan nan, in ji wa ya ce maka?"
Yaron ya ce "Wai in ji Master "
Jauhar ta ce "Na shiga uku, master ne, ban gaya masa zan zo nan ba, waye ya gaya masa?".
Ta ce "Bari na ɗaukko jakata"
Anty ta fito ta ce "wannan aikin kuma wa zai ƙarasa shi? Ai sai yayi haƙuri ta gama, kai je ka ka ce masa aiki take yi, ya dawo an jima"
Buɗe baki jauhar ta yi ta ce "A'a anty kar ya gaya masa haka, kaga haidar ka ce masa...
Anty ta katse ta ta ce "Fita ka je ka gaya masa haka, waye shi ba gidan sirikansa ba ne ba".
Gaban Jauhar ya tsananta faɗuwa, ba ta san me hakan ka iya haifarwa ba.
Mama ma fitowa ta yi ta ce "Ba zaki zauna ki cigaba da aikin ba"
Viper kuwa wani marurun takaici ne ya ƙule masa a wuya, jin irin saƙon da aka aiko masa da shi, kamar shi za a aikowa da wannan banzar maganar. kawai ya sai kai zai shiga gidan, walid ya riƙe shi ya ce "Mai zamani gidan sirikanka ne fa, dan Allah kar yi wani abu mara daɗi, ka zubar mata da mutunci"
"Tun da suka zaɓi su aura mini ita, sai na tabattar musu da maganata ce gaba da ta su a yanzu" kawai ya saka kai cikin gidan.
Cak ta tsaya, jikinta yana tsuma, ganinsa ya shigo yana wannan takun nasa, ya ƙureta da ido, tun kafin ya ƙaraso.
Tsit suka yi suna kallon ikon Allah, ya ƙaraso, ta wutsiyar ido ya kalli yaya tijjani da ke zaune a kan farar kujera, ya sauke idonsa a kan mama, su surayya sannan Anty Zakiyya ta ƙarshe.
Yana ganinta ya ƙara tabattar da Rahila ce ta saka aka yi masa aure, bai ga alamar akwai mahaifiyar jauhar a cikin su ba.
Ya kalli Jauhar ya ce "Ni na aiko ki zo ki ka ce mini ba zaki zo ba?"
Ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri"
"Shut up!" Yayi maganar cikin ƙaraji, tare da ball da bokitin da aka kawo markaɗe, da kwanon salak ɗin duk suka tarwatse a wurin, ta zabura ta ƙanƙame jikinta. Ai ba ita ba, har sauran matan gidan da 'yan matan.
Tijjani kuwa ɗimaucewa yayi, dan kuwa ba zai manta muryar nan ba, duk da yana tantama amma kamar muryar wanda suka yi ma aika-aika.
"Dama mun yi da ke zaki zo nan? Kin zata ƙarya suke yi da suka ce za su saraki idan suka kuma ganinki a unguwar nan?" Ɗago ido ta yi cikin tsoro tana kallonsa.
Ganin yadda duk ta rikice ya sanya ya saki muryarsa ya ce "Zo ki wuce mu tafi"
Ta ce "Bari na ɗakko hijjabina"
Mayar da idonsa yayi kan Anty Zakiyya, ko ƙiftawa ba ya yi, babu shiri ta juya da sauri ta shige ɗaki.
Jauhar ta fito, da jakarta da ledojinta, ya danƙi hannunta, suka yi waje.
Suna fita Surayya ta ce "Bala'i dama wannan ne mai dogon zamanin? Jaraba jauhara na cikin bala'i".
Hafsa ta ce "Ni kuma abun da na gani daban, kut wallahi na ɗauka zan ga wani gardin mummuna, ji mutum hanci har baka, kai amma yayi kalar tsoro da yawa, haka yake yi mata wannan tijara"
Mama ta ce "Dalla ku yi mana shiru, kalli asarar da ya yi mana, abincin ranarmu ya mayar da mu baya" mama tayi maganar a ƙule.
"To mama aikin gama ai ya riga ya gama, ni wallahi na zata dukanta zai yi ma. Anty har an gudu ɗaki, bayan ita ta bayar da saƙon da aka gaya masa"
Daga ɗaki ta ce "Haka kurum in tsaya ya kasheni a banza, kin ga wani huci da yake yi kamar kumurci, gashi sai kallona yake yi, ya ƙara girma fiye da yadda na san shi".
Jauhar kuwa suna fita, walid ya rufa musu baya, Viper ya din ga jan ta, gashi saurinsa ya ninka nata, kamar ta hantsila, Alla-Alla yake yi su ƙarasa titi ya saka ta a abun hawa, sai dai suka yi karo da madaki da yaransa.
Wata irin muguwar dariya madaki yayi, wadda ta ƙara fito da ainihin muninsa, baƙi ne wuluk kuma gabjeje, yana da jajayen idanuwa, wanda yake rambaɗa musu farin kwalli, ga wani ƙaton sara a fuskarsa a kaikaice da ya raba fuskar in to two equal parts.
Sai ta ga Al'amin ɗin ta nutsatstse ne mai kyan gani, a kan madaki, ta san gidansu ta san sunansa a unguwar su, amma ba ta sanshi a fuska ba.
Jikinta ya hau tsuma, Al'amin ya sakata a bayansa, ya tsaya yana fuskantar madaki, Walid ya tsaya a gefensa.
"Tun da aka gaya mini matarka ta shigo unguwar nan, na ce bari in auna adadin son da ka ke yi mata. Ka san bikin ma bana nan aka yi, labari na samu ban haɗu da kai na yi maka Allah ya sanya alkhairi ba. Ƙarfin halinka ya kai, tun da ka iya ratso cikin unguwarmu ka auri 'ya. Shiyasa na so ka zama ɗaya daga yarana tun a wancan lokacin amma ka ƙi.
Ya leƙa ya kalli fuskar jauhar ya ce "Ashe 'yar gidan Alhaji faruku ce, rabona da ita tun tana 'yar mitsitsiya, ashe haka ta girma ta ƙara kyau, ka bani kunya ma, wannan ai ba ta wani gama nuna ba, wannan ai ka yi mata girma, kodayeke ba a nan take ba an danne bodari ta ka, bakinta mai kyau ɗan ƙarami zai yi daɗin sha, anya wannan ba....
Wani wawan mari Al'amin ya ɗauke madaki da shi yana huci, Walid ya riƙe shi ya ce "Viper ka san me ka yi kuwa?"
Al'amin ya hankaɗe shi, ya kalli madaki cikin ido ya ce "Ka daɗe da kashe Al'amin ɗin da ka raina, ka mayar abun nishaɗinka, Kar ka sake ka shiga shingena, duk wala-walar da zaka yi, kar ka ƙetare iyaka".
Yaran madaki suka yinƙuro, Madaki ya ɗaga musu hannu, ya ciro wata muguwar wuƙa a jikinsa, ya ce "Bari in nu na wa duniya kai rago ne, a gaban matar taka, da ka yi dan ka burgeta"
Wani irin ihu jauhar ta ƙwala, ta rirriƙe Al'amin tana kuka ta ce "Dan Allah kar ka caka masa, zaka kashe shi idan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 121