Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
101 / 121
zargin wasu da shiga gidanka su ka kashe matarka" Ta sake kallonsa a tsanake ta ce "Ka na ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, eh ko a'a?" Viper ya yi shiru ya na bin idonta da kallo. Nabila ta nemi a dakatar da Bunkure, saboda ƙoƙarin sanya Viper amsa laifi ta ƙarfin tsiya, sai dai ba a karɓi ƙorafin ba, aka ce ga ci gaba. "Ko ba ka amsa da bakin ka ba, amsar eh ce.Ya mai girma mai shari'a duniya kowa ya shaida Al'amin Viper ko in ce mai zamani, gawurtaccen ɗan daba ne da ya gagari al'umma, har a bayan tserewarsa daga gidan yari, ya ci gaba da aikata miyagun ayyukansa, na sara suka da dillancin miyagun ƙwayoyi". "Objection my lord, barrister Naja'atu ta na kare waɗanda ake zargi ne, ko kuma ɗorawa mai ƙara laifuka da hanyar karkatar da shari'ar kan wani abu daban". Aka gargadi Naja'atu Bunkure, ta ɗaukko wani file ta ɗaga ta ce "A bincike da yan sanda su ka tattara, akwai binciken likitoci, da gwaje-gwajen da aka yi masa bayan mutuwar jauhar, wanda a jininsa aka gano sinadarin wata allura, da ake amfani da ita a asibiti, wadda sai da matakai masu tsauri ake amfani da ita. Bayan haka akwai sauran ƙwayoyin da aka gano sinadaransu a cikin jininsa, wanda hakan yake tabattar da shi ya sha ya bugu, ya kashe matarsa da kansa. Da wannan nake roƙon kotu ta wanke waɗanda ake zargi, a hukunta wanda ya aikata laifin" Tsit kotun tayi, wani irin gumi ya tsatstsafo wa Viper, ba shi ba hatta su Walid, sun shiga cikin matsanancin tsoro da fargaba, ga su Abbu da mama hatta Alhaji mu'azzam da duk wani majiɓancin shari'ar, suka shiga cikin damuwa da tashin hankali. Nabila ta kalli Bunkure, Bunkure ta kalli Nabila tana murmushi. Nabila ta ce "Zan so kotu ta banu dama, na gabatar da doctor Muktar sharfaɗi" Aka ba ta dama, sak Viper ya yi, ya na tunanin shi kuma me doctor Muktar zai yi a nan. "Doctor ka gabatarwa da kotu kanka" "Sunana doctor muktar sharfaɗi, ni ne likitan da na duba marigayiyya jauhar, na tabattar da inducing ɗin ta za a yi a asibitina, kuma ni aka samu na tabattar da mutuwarta a asibitin gwamanti na shiga asibitin safe. A report ɗin da na bayar, babu duka a jikinta ko kaɗan, faɗuwa ce, ta rasu ɗan cikinta ma ya mutu. Sai dai zan yi wani karambani, ban san wane irin bincike barrister ta yi akan allurar da take magana a kai ba, wannan allura ta na fara aiki ne mintuna biyar zuwa bakwai da yin ta, kuma tana tafiyar da ji da gani da consicous ɗin mutum gaba ɗaya, babu yadda za ayi wanda ya yi amfani da wannan magungunan ko alluran, ya iya sanin meyake yi, har ta kai ga ya yi kisan kai, kashe jiki suke yi gaba ɗaya Banbancin mutum da matacce numfashi ne kawai" Nabila ta numfasa, ta je gaban teburinta, ta ɗaukko wata envelope ta fito da wasu hotuna, ta ɗaga su ta ce "Mai girma mai shari'a, waɗannan su ne hotunan farko da jami'an tsaro su ka ɗauka, bayan ƙorafin da maƙwabta su ka shigar, na cewar sun ji ihun jauhar cikin dare, wayewar gari kuma sun yi ta bugu ba a buɗe gidan ba. Idan aka yi duba da hotunan, Al'amin kwanciyar da yayi ruf da ciki, hannayensa a kan gadon bayansa, ya na nuni da cewa tabbas ɗaure shi aka yi. A wannan hoton kuma, idan aka duba wurin ƙafafuwansa kasancewar ba dogon wando ne a jikinsa ba, akwai shaidar an yi traumatizing wurin, akwai alamar shaidar ɗauri a wurin. Idan har binciken jami'an tsaro dai-dai ne, kamar yadda Barrister Naja'atu ta faɗa, to ya tabatta toxicating ɗin Al'amin aka yi aka kashe matarsa. Idan kuwa har shi ne ya kasheta, zai iya zama tsautsayi ne, dan idan niyyar kasheta ya yi, zai daketa ne, ko jikinta ya nuna wani nau'i na cutarwa. Amma daga bayanan doctor Muktar, da hotunan da na gabatar, ina fatan Al'amin ya fita daga zargi, kuma za ta hukunta waɗanda suka aikata laifin" Da ido kawai Viper ya din ga bin Nabila, dan bai san yadda aka yi duk ta tattara waɗannan shaidun da hujjojin ba, sai a yanzu ya ƙara jinjinawa basirarta da hangen nesa. Alƙali ya yi rubuce-rubuce Alƙali ya ɗauki lokaci ya na yi, daga baya ya ce ya sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda, domin yin zama na ƙarshe domin yanke hukunci. Kamar wata celebrity, haka Nabila ta fito daga cikin kotun, su Abba suka kewaye ta, kowa ya na tofa albarkacin bakinsa, su na jinjina wa ƙoƙarin da ta yi. Viper gefe ya koma ya tsaya ya na kallonta, yadda farinciki ya mamaye fuskarta. Sumayya ta saka mata abin magana, ta na tambayarta, yaya take ganin gudanawar shari'ar. "Babu abin da zamu cewa Allah sai godiya, muna sanya ran samun adalci,  a wannan shari'ar". Hatta su liti ma, kasa ɓoye farincikin su su ka yi. Viper bai tsaya ba, yau ma saboda Abbu ya na wurin, ba ya son duk abin da zai haɗa shi da shi. Daga nan duk su ka watse, Baba ya na ta son lallaɓa Nabila ta dawo wurinsa, amma yadda ta nuna ba ta so, ya sanya ya ƙyaleta. "Thank you very much, for standing by my side, and show me way, to live another life as a different person, a really appreciate Abla, thank you once again take care. Al'amin" Murmushi ne ya suɓuce mata, sai kuma ta ɗan tsuke fuska a hankali ta furta "Alaƙarmu za ta zo ƙarshe, da zarar na kammala wannan shari'ar" Ayshercool 08081012143 95 Duk da abin da ta ƙudurce a ranta, amma ta karanta message ɗin nan, ya fi sau ashirin. Haryanzu tana tantama a kan hukuncin da ta ɗauka, na rabuwa da shi da zarar ta kammala shari'a, amma itakaɗaice mafita a ganinta, saboda ta na ganin soyayya da Viper tamkar cin amanar 'yar uwatta ne, babban abin da za ta yi, a matsayin ba ta santa ba, shi ne ta tabbatar da an ƙwato mata hakkinta, kuma an wanke Viper daga zargi. Viper kuwa su na tafe, Liti ya yi wani irin ihu, ya ce "Kan uban nan, yarinyar nan ta yi bala'i, ashe haka kanta yake ɗaukar wuta, kamar me. Kai ka ga wata karakaina da shige da fice da ta yi, ashe ta san abin da take yi" Ɗan mama ya ce "Oga liti, ka manta lokacin da ka din ga korarta, Allah ne ya sa Oga walid bai yi saurin korarta ba, ya bari ta ci gaba da zuwa, ina ga a wannan gaɓar babban yaya za mu sarawa, Mikiya mai hangen nesa, amanar Oga Viper kuma babban yayan marigayiyya, an buga da kai an barka" Walid ya yi murmushi, ya ce "lokuta da dama, abin da haƙuri bai bayar ba, akasinsa ba ya bayarwa. Kai yanzu da mun koreta, da idan Allah ya ƙaddara za ta tsaya masa, sai mun je mun nemota, idan kuma lauya zamu ɗaukar masa babu lallai mu samu yaƙinin ba za a saye shi da kuɗi ba ya cutar da mu ba. Wallahi hardwoker ce Nabila, gashi babban abin da yake burgeni da ita da Jauhar, sun iya kwantar da kai, su yi galaba a kan abu, Nabila ba ta da tsoro da ni wani ne, sai na karrama yarinyar nan. Kuma kai yanzu ka ji kunya, irin abin da ka din ga yi mata" Liti ya ce "Na ji ɗin, amma duk da haka ai ba ta da kunya muguwar fitsararirriya ce" "Liti ka daina rinjayar da laifukan mutum a kan alkhairin sa mana, kowane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Ita jauhar ɗin ce maka aka yi ba ta tsiwa, ka tambaye shi ka ji to, ba ta yi wa kowa amma ta na yi masa, ko ƙarya nayi?" Yayi maganar yana kallon Viper. Viper ya yi murmushi ya na tuna yadda ya sha jifa da kwanuka a hannun Jauhar. Nabila kai tsaye take abubuwan ta, babu ɓoye-ɓoye ko kara, Jauhar kuwa cikin ruwan sanyi, a ɓoye take ladabtar da shi. Walid ya ce "Ko ma yaya ne, ni Jauhar tawa ce, Nabila ma haka, kowacce ta taimaki rayuwarmu. Ba dan Allah ya kawo Nabila ba, da tuni mai zamani ya samu taɓin hankali, ko kuma ya kashe kansa, kalli yadda muka din ga fama da shi, saboda yi wa kansa allurai. Amma tana faɗowa rayuwarsa, ta saita shi, kai ba iya lauya ba ce ba, har role ɗin likita tayi playing, kalli multiple attempts na kasheta, da intimidation da ta din ga fuskanta, amma ta dage ta jure, ko yau ta barka, ta biya Jauhar ina yin ta sosai, ina yi mata fatan iyayenta su samu fahimtar juna, ita ma ta samu nutsuwa, a zo ayi bikinku mu huta" yayi maganar yana kallon Viper da bai ce uffan ba. Liti ya ce "Ba wani nan, ba fa zai sake yin aure ba, kawai ya haƙura ya shiga ittikafi da yi wa addini hidima har ƙarshen rayuwarsa, saboda wani takaici nake ji, idan na ji an yi zancensa da wata ba jauhar ba. Dama ba damuwa yayi da wata sabgar mata ba, zai iya lallaɓa rayuwarsa a haka, ko mai girma Al'amin" Kawar da kai Viper ya yi yana dariya, iya shege ɗan liti yake ji, wai ya shiga ittikafi. *** Yau aka ɗaukko ɗan uwan ramma Sani daga makarantar kwana da yake yi a Dutse, kamar su haɗiye juna da shi da ramma. Ya ce "Yaya na kasa gane yaya ki ke ma, rama ki ka yi ko ƙiba, kin wani goge, ashe zan ƙara ganinki, nayi kuka sosai har na fid da ran sake ganinka ma" Tayi murmushi ta ce "Nayi kewarka sosai da sosai da kai da mama, na yi kuka iya yi na, ban taɓa zaton zan sake ganinku ba, amma Alhamdilillah ala kulli halin, ya makarantar?" "Lafiya ƙalau, ni fa kusan shekara ban dawo kano ba, idan an yi hutu a gidan wani abokin honorable nake zama, wanda ya saka aka kawo mu nan aka ajiye, wannan karon na saka aka roƙe shi tun da an ce mini an ganki, kin ga kayan alatun da ake bani ramma, A dalilinki kalli daɗin da muke ciki, da muna ƙauye muna fama har da cin dafaffiyar tafasa mun sha wahala sosai" ramma tayi murmushin yaƙe. "Yaya bayan tafiyarki fa, kin ga kwaltar da aka shimfiɗa, tun daga tasha har cikin tofa an yi tituna aka gyara makarantu, amma dai kin je ƙauye ko da ki ka fito, kamar yan birni, har da fitilun sololi aka saka mana, ga ruwa" Ramma ta girgiza kai ta ce "Ban je ba, tun da na fito ina nan" Suka din ga hira da ita. Dawowar Sani, ba ƙaramin daɗi ta yi wa ramma ba, sosai yake zama su yi hira ya saurareta, saɓanin mama da yanzu sama-sama take da ita. Shi dai tun yana kallon ramma, yana mazewa har ya magantu ya ce "Yaya wai aure ki ka yi ne da gaske, kamar yadda kawunmu ya ce ya aurra da ke?" Ta kalleshi ta ce "Me ka gani?" "Gani na yi kin kusa haihuwa" ya bata amsar da ta kusa sanyata nutsewa, yanzu duk ɓoye-ɓoyen nan da take yi, sai da Sani ya ga cikin nan. Ta ce "Eh da gaske ne" "Ikon Allah, to ina mijin naki yake, ni gaskiya ban so yayi miki irin wannan auren ba, na ci buri da yawa a kan aurenki" Ramma ta katse hirar, ta ce masa za ta je ta kwanta, bacci take ji. Ta je ta haye kan gado ta kwanta, ta din ga kallon ɗakin, duk albarkacin abin da ya faru da ita ne, ta samu wannan ni'imar, da tana rayuwa a ƙasƙance cikin talauci, amma yanzu tana cikin ni'ima duk da ƙaddarar da ta kawota wannan bugiren ba irin wadda ake fata ba ce. Ta ji yadda abin da yake cikinta yake motsawa, ta shafi cikin a hankali, tana tunanin Abdul. Da tunanin halin da yake ciki yanzu, ko ciwonsa ya warke Allah masanin gaibu, dan ba ta da wata hanya ta ganinsa, idan ba Nabila ce ta wayance da kaita awo, ta kaita wurinsa ba. *** Nabila ta halarci program ɗin su, da su ka saba yi da Sumayya, Sumayya ta din ga yi mata tambayoyi a kan shari'ar da take gudanarwa ta Viper, nan Nabila ta din ga fito da wasu bayanai da mutane da yawa ba su san da su ba, iya abubuwan da suka ji a kan sa a bakin Mutanen gari, da na jamu'an tsaro kawai da shi suke amfani su yi masa hukunci. Har tarihin yadda ya shiga daba a dalilin kisan ɗan uwansa da rashin ɗaukar mataki, sai da ta bayar, duk da ta ɓoye duk wani abu da ya shafi familynsa. Abbu yana tafe a mota, yana driving yake sauraren shirin, sai tsananin mamakin abun ya kama shi, mussman ɓangaren shekara biyar da ya yi a prsion, ba tare da an yi masa shri'ar ba, aka sake shi, kuma aka koma wai ana nemansa wai an sake shi ba bisa ƙa'ida ba. To zaman me ya yi na shekara biyar ba ayi masa shari'a, a ƙaddara yanzu a yanke masa hukuncin laifinsa, da lissafin waccan shekara biyar ɗin za ayi, ko banda ita? Haka ya tafi gida, ya na ta lissafi daban daban a cikin zuciyarsa. Ji yayi kamar ya nemi Nabila, amma sai ya rabu da ita, gaba ɗaya topics ɗin da suka yi discussing sun ɗauki hankalinsa sosai da sosai, tare da mamakin yadda fannin shari'a da tsaro ya lalace ya taɓarɓare da cin hanci da rashawa, kawai wa ka sani waye ya sanka. Maganganunta suka ci gaba da ɗaukar hankalinsa, da take kira ga iyaye, da al'umma da hukumomi su guji watsi da yaransu dan suna rashin ji, idan yaro yayi laifi, iyaye su bar hukuma ta hukunta shi, idan an sako shi, su rungumi abin su, su ci-gaba da addu'a da yi musu nasiha, ta din ga bankaɗo illar da watsar da yaron da ba ya ji da iyaye suke yi, a waje kuma su samu mai rungumar su, komai munin halinsa dole su yi masa biyayya. Gaba ɗaya Abba bai taɓa tsammanin Nabila ta na da hankalin da za ta yi bayanai masu muhimmanci har haka ba. Jikin Nasir ya fara sanyi, mussman yadda ya ga ko ina zancen Nabila ake yi, da yadda shari'a ta fara karkata, ƙoƙarin haifar da abin da bai yi tsammani ba. Abba ya samu Nasir a gida, ya ce "Nasiru, ka ji program ɗin Arfa kuwa?" Ya ce "A'a Abba, meyafaru?" "Maganar yaron nan ɗan daba da ta ƙallafa ran kare shi, alamu fa sun nuna kamar yana da gaskiya. Koma dai ba shi da gaskiya, akwai zalunci a cikin abin da aka yi masa". Nasir ya ce "Haka ne, amma duk da haka mu jira a kai ƙarshen shari'ar, tun da yana da iyayen gida, maybe akwai masu tallafa musu har da Nabilan a kan shari'ar" Abba ya ce "Haka ne, amma duk da haka, ɓangarorin shari'a a ƙasar nan da gyara, yaya za ayi a ajiye mutum shekara biyar babu Shari'a, to zaman meyake yi ba a yanke masa hukunci ba? Kai Allah ya kyauta" duk jikin Nasir ya bi yayi sanyi. ***** Viper yana ta son ya kira Nabila, amma bai san me zai ce mata idan ya kirata ba, dan haka ya din ga jujjuya wayar, yana kallon lambarta. Babu tsammani, ya kalli liti ya ce "Abdallah" "Na'am mai zamani" "Yaushe rabonka da gida ne?" Jin tambayar yayi wani iri, "Kusan shekara ɗaya da rabi" "Yakamata ka je ka gaishe su, mussaman kai da iyayenka suke a raye, ba kamar ni da Walid ba". Liti ya ce "Kai ma ai Abbu yana da rai" "Ina magana kana mayar mini?" Viper yayi maganar yana tsuke fuska. "Easy maza, ni wallahi wannan munafukar tsohuwar ce ta saka na daina zuwa gidan, tayi ta hantarata tana ziga Alhajinmu, shi ma fa korata yayi, maminmu na kallo, ba ta ce komai ba. Ai ni da gidan nan idan ba wannan algungumar tsohuwar ce ta baje tayi bacci ba, gaskiya na daina zuwa, ga tsinuwa da take yi mini, dan ma Allah ya sa Alhaji ta haifa ba ni ba, da sai na kwashe ƙasusuwan ƙafarta na watsar da ita" "Yakamata mu buɗe wani sabon babi na rayuwa ne Abdullahi, mu gyara wasu daga cikin kura-kurai waɗanda za su iya gyaruwa, akwai yiwuwar idan mu ka yi nasara a kotu, na koma can kudu da aiki, koma na bar ƙasar gaba ɗaya, ba zan taɓa tafiya na bar ku ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran madogara ba" Walid da tun ɗazu yake wanki bai ce komai ba, ya ce "Aikin me ka ke yi wai? Kuma meyasa zaka tafi kudun?" Viper ya yi murmushi ya ce "Zan yi muku bayani a gaba, amma dole muje ka gaida iyayenka, ka ba su haƙuri liti" "Dan Allah maza ka bar zancen nan, nima fa yakamata su nemi yafiyata fa, mussman algungumar tsohuwar nan" "Ba zaka daina ce mata algungumar nan ba ko?" Liti ya ce "Saboda fa Alhaji ya yi mata biyayya ta saka ya kore ni, wai zan lalata mata sauran jikoki, lokacin ma fa ba wani nisa nayi a shaye-shaye ba, amma wani ƙanin babanmu ya ce wai alhakin yaransu ne, da babanmu bai haɗa da su, ya kai ƙasar waje karatu ba, shegu kamar su suke tara masa kuɗin. Ni Allah yasa ma ba asiri suka yi mini na je na dawo ban iya komai ba, sai holewa" Walid ya ce "Ko ba komai, ai ka hau jirgi" Liti ya kwashe da dariya ya ce "A banza amma" Ɗan mama ne ya faɗo cikin gidan, suka kalle shi gaba ɗaya, liti ya ce "Menene kuma?" Yayi tsuru-tsuru yana kallonsu. "Kai dalla menene wai?" Ya numfasa ya ce "An kashe brothern Viper, wannan na gidan na su Abba" sai da Viper ya zabura, ya kalli Ɗan mama ya ce "What? How?" Ɗan mama ya ɗan girgiza kai ya ce "Faɗa su ka yi da wasu a can unguwar bello wai a kan kare, shi ne suka ƙyale shi, sai da ya dawo daga yawon cajinsa, suka sassara shi, suka saka shi a buhu, suka kai shi gefen Black ocean kududdufin nan na cikin unguwa suka watsar. Ashe kwana uku ana nemansa ba a ganshi ba" Miƙewa Viper ya yi, jikinsa yana tsuma, kamar zai fita daga hayyacinsa ya ce "Yaushe ya fara shaye-shaye har yake bin yara marasa ji? Kuma jiya a kotu, ban ga alamar akwai Matsala a tare da Abbu ba" Ɗan mama ya ce "Taɓ ai an kwana biyu, yana zuwa rumfar shayinmu, wurin su ɗan kada ai, yana shaye-shaye". Takalmansa ya shura zai fita, cikin matsanancin tashin hankali, Walid ya riƙe shi, ya ce "Ina zaka je?" "Meye haka, cika ni mana na je na ji meyake faruwa? Kuma suwaye suka yi masa wannan zaluncin" Walid ya ce "Babu in da zaka je, a sabga irin tamu, duk wani ɗan gang, ya san irin haka na iya faruwa da shi, muddin bai tuna ba, ko ma mutum ya tuba, ko a kashe ne ko kuma a kashe shi" "Walid, Abba ba zai iya daba ba, ina ganin shaye-shaye kawai yake yi, wane irin kisan zalunci ne wannan da rashin imani? A sassara mutum a zuba a buhu aje a zubar?" Liti ya ce "Ni ku matsa mini, na yi sujudar godiya ga Allah, gabasa ake kallo ko daga nan Arewa ma zan iya yin ta? Daɗina da kai wasu lokutan kana da wani ɓoyayyen rauni, da ya kan kusa cutar da kai Viper. Matar da ta rufe muku ƙofa, aka hallaka ɗan uwanka, shekarun da suka gabata, sharrin da ta aika ne, ya dawo mata kanta a kan ɗanta ita ma, cin amanar da ta yi, ita ma Allah ya ɗanɗana mata, Allah Allah ne, dan haka babu ruwanka". "Liti kai mahaukaci ne? Ko kaza aka kashe wa mutum bisa zalunci, abin tashin hankali ne, mai rai a sassara shi, a saka a buhu, a kai a yar fa" Walid ya ce "Yanzu idan ka je gidan me zaka yi musu? Salon ta ce kai ne ma ka saka aka kashe shi, ka san halinta ai, babu in da zaka je, taje Allah ne ya kamata". Fafur suka hana Viper fita, ya koma cikin ɗaki, ya ɗaukki wayarsa ya kira Nabila. Ta ɗaga tayi sallama ta ce "Vi ya ne?" "Amm ki tambayi ƙawar nan taki Sumayya, ko labarin kisan da aka yi wa wani yaro Abba a unguwarmu, ya je mata dan Allah ina son a ɗan bikcika". Ta ce "Subhanallah, ban sani ba, bari na kirata na ji" "Yauwwa yi sauri, dan Allah idan gaske ne, Joseph ya kai ku station ɗin da case ɗin yake hannunsu, ku jiyo mini ya ake ciki?" Ta ce "An gama ranka ya daɗe, amma ya sunan wanda aka kashe ɗin?" "Ɗan matar Abbu ne, sunansa Abba idan ya kama ku je gidanmu, ku ƙara tabattar mini". Mamki ya cika Nabila, amma ta ɓoye mamakin nata ta ce "In sha Allah zamu je" ya katse wayar cikin matsanancin jimami. Walid ya ce "To wai meye amfanin hakan da ka yi? Meye naka a ciki Viper?" Al'amin ya girgiza kai ya ce "Yaya ku ke abu kamar ba tsoffin 'yan hannu ba? Yanzu faɗan ɗaukar fansa zai ɓarke a tsakanin unguwannin, kuma ina gudun abin da ya faru da ni, ya sake faruwa a kan wani, ina son na bibiyi abin a kama waɗanda suka kashe shi, na tabattar da an hukunta su, domin ya zama izina. Kuma ko ba komai, musulmi ne, kuma mahaifina ne ya riƙe shi, an yi masa kisa mai muni, abin da taɓa zuciya" Sai kuma suka yi shiru, liti ya ce "Haka ne, maganarka dutse, amma gaskiya ba zaka je ba, ba ruwanka daga nan kayi masa addu'a, idan komai ya lafa sai a san abin yi" Viper ya ja tsaki, tare da girgiza kai. Walid ya ce "Menene kuma?" Yayi ajiyar zuciya ya ce "Walid, babu wani alfanu ko jin daɗi a rayuwar daba da shaye-shaye, duk kalle mu dai, babu wanda wannan rayuwar ta amfana da komai, face tabon baƙin ciki da tsantsar nadama. Akwai tarin ƙalubale, muddin za a ci gaba da tafiya a haka" Walid ya ce "Haka ne, sai fatan Ubangiji Allah ya yafe mana ya shiryar da mu baki ɗaya". Kamar yadda Viper ya buƙata, Nabila tare da Sumayya, suka tafi binciken da ya ce, jami'an tsaro suka tabbatar da faruwar Al'amarin. Sumayya ta je har gidan su Viper, kamar sai dai ba su tafi tare da Nabila ba. A rumfar zaman makoki, ta hangi Abbu, ta ƙarasa tayi musu gaisuwa, Abbu ya taso, suka sake gaisawa, ya ce "Sumayya ya aka yi ne?" "Nabila ce ta kirani, Viper ya ce lallai mu zo a tabattar da abin da ya faru, ban san dai dalilinsa na yin hakan ba" Ya ɗan yi shiru ya ce "Shi da kansa?" Ta ce "Eh" nan ya sake yi mata bayanin abin da ya faru, maganar da yake yi mata ma, mahaifiyarsa na Asibiti allurar bacci kawai ake yi mata, tamkar zata haukace, saboda yadda aka kawo gawar Baba, jikinsa ya fara zagwanyewa, jikinsa ko ina sara, hannunsa ma daban aka kawo shi. Sumayya ta tattara rahoton abin da ta samu, ta sanarwa Nabila, kuma ta samu na sanarwa a gidan rediyo. Sosai batun ya ɗauki hankalin jama'a, Duk ita kanta Nabila, sai da ta ce Alhakin Viper ne, amma ta kaɗu matuƙa jin irin kisan tozarcin da aka yi wa Abban duk a silar ƙwaya. Kamar yadda ta wallafa a shafinta, suna nan suna zuba ido, su ga matakin da jami'an tsaro za su ɗauka, wurin cafke waɗanda suka aikata laifin. **** Rahila dai abin da ya samu Abba ya zame mata masifa, ta daina magana ta daina cin abinci, ba ta gane kowa sai kuka, idan aka jima kuma ta yi ta kurma ihu, tana kururwa tana kiran ɗana Abba, Abba bai mutu ba, sai dai a daddaneta ayi ta yi mata allurar bacci. Haka Shahida zata rungumeta, tayi ta kuka, ga Amira ta shilla ta yi nata wuri, tun da Abbu ya ce ba zai karɓeta a gidansa ba. ***** Yau da yamma Viper ya je barrack wurin Nabila, sai dai tun kafin yayi magana, ta fuskanci matsananciyar damuwa a tattare da shi. Ta ce "Vi meyafaru ne?" "Abin da ya faru da yaron nan Abba ne ya yi bala'in tsaya mini Abla" "To yaya za ayi, sai addu'a, amma in ganin kamar har da hakkinka abin da ya same su" Viper ya girgiza kai ya ce "Ba na tunanin haka, haka kurum abin ya tsaye

Chapter 101 of 121