Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
27 / 121
ka caka masa, dan Allah ka yi haƙuri kar ka kashe shi". Viper ya ce "Kafin ɗayanmu ya bar duniya, za a ga waye ragon, ƙazamin kare kawai" Ya sake danƙar hannun jauhar, ya keta ta tsakanin yaran madaki yayi gaba, walid kuma ya tsaya a kan hanyar yana kallonsu, dan kar wani ya bi bayansu ya illata su. Madaki ya bi bayansu da kallo, ya din ga kallon wuƙar hannunsa yana murmushi, lallai yayi sake ɗan zaki ya girma, ya fara zama barazana a gare shi. Babban abun da ya ƙular da Al'amin, bai wuce yadda jauhar take ta rusa masa uban kuka ba a cikin a daidaita sahu, bayan koma menene ita ya janyo, kamar ya cillata kan titi ya huce, yana zaman zamansa an ƙaƙaba masa ita, yanzu dole duk in da zai yi sai yana tunanin kar a cutar da ita. Bai kulata ba har suka je gida,ga wani irin ciwo da kansa yake yi, ga zazzaɓi tun a hanya ya rufe shi. Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa ya bar ta. Bin bayansa ta yi, cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Master ka yi haƙuri, ban san haka za ta faru ba, nayi niyyar gaya maka dama idan na dawo, dan Allah ka yi haƙuri" Banza yayi mata, ya rufe idanunsa, saboda yadda sanyi yake ratsa shi, ga wani abu mai ɗaci da ya tsaya masa, ya ƙi wucewa, saboda yadda abubuwan da suka wakana a rayuwar sa, suke dawo masa cikin kansa a yanzu. Idan ya tuna abun da madaki ya faɗa a kanta, sai ya ji kamar ya kurma ihu, ya gama cutarsa, ko shi jai tsaya ya ƙare mata kallo, ya ga bakin nata ba sai shi. A marairaice ta ce "Master, Yaya Al'amin dan Allah ka yi mini magana, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, na san koma menene ni ce sila". "Get out from sight, ki tashi ki fita kafin ni na sassaraki a wurin nan" a tsorace ta tashi ta fita, tana waiwayen sa. Tana fita ya riƙe kansa, saboda yadda ya yi masa nauyi. Anty Zakiyya kuwa, Rahila ta kira a waya, bayan sun gaisa ta ce 'Ƙawata yau na ga tsiya da wasali" "Bani na sha meyafaru?" "Yau ɗanki ya zo gidan nan ai" "Wa kenan" "Sirikinmu mana, wai ashe yaran madaki ɗan dabar nan na unguwarmu sun ce idan ta sake zuwa unguwar nan, sai sun sassarata, ta zo gidan nan bai sani ba, a sukwane ya taho, yau mun ga bala'i, kin ga tijarar da ya yi ya ja hannunta suka tafi?" Rahila ta ce "Zai aikata fiye da haka ma, in dai Aminu ne ɗan banzan bawa kenan ake gaya miki" "Taɓ amma anya ba son yarinyar nan yake yi ba? Kin ga a yadda ya zo kuwa?". "To ke ina ruwanki, dama dai ba burinki ita wannan ta bar miki gida ba, shi ya sani ba mace ba ce ba? Luf zai yi ai, ni fa tun da aka yi auren ba mu sa shi a idonmu ba, na ce can ya ƙarata" Suka kwashe da dariya, Zakiyya ta ce "Taɓ amma ƙato ne, sai ka ce ɗan dambe, kuma wallahi ba wani abun gyara da muka yi mata, yau ne ma da ta zo maƙwabciyarmu ta bata, amma haka nan muka kaita" "Oho musu, in dai buƙata ta biya, ba shikenan ba, su ƙarata" Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Jauhar ta kasa zaune ta kasa tsaye, master ya ɗau fushi da ita, gashi ya ƙi fitowa, kuma ya korota daga ɗakinsa. Da canjin hannunta, ta haɗa ta sayo fulawa, ta kwaɓa alkubus, da wata irin miya ya 'yan dabaru, sai dai har ta yi ta gama bai fito ba. Sai ta kasa ci, ta sake lallaɓawa ta leƙa ɗakinsa, ta ga yana banɗaki, ta cigaba da tsayuwa ya fito, ta tsaya tana sallama a bakin ƙofa. "Idan ki ka bari na zo na sameki a wurin nan, sai na ɓata miki rai" Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri master, na tuba ba zan sake ba" Kwanciya ya sake yi, ya juyawa ƙofar baya. "To in kawo maka abinci?" Kamar ya ce eh, amma yayi mata shiru. Abun da ya ɗaure mata kai, bai wuce har dare kwanciya yake yi ba, yaƙi fitowa, cikin tsananin fargaba ta shiga da kwanukan abinci ta ajiye masa. Ƙamshin miyar da ya cika masa hanci, ya sanya ya buɗe idonsa. Gwiwoyinta ta saka a ƙasa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ni ko wani hukuncin ka yi mini dan Allah ka daina yin fushi da ni, bana son na ga na yi laifi dan Allah" hawayenta ne yake ɗiga a kan katifarsa, ya gyara kwanciyar sa ya juya mata baya. Ya tsani kuka, ba ta san ƙara ƙular da shi take yi ba. Tashi ta yi ta sake zagayawa kamar mayya, tana yi masa magiya. Ya buɗe jajayen idanunsa yana kallonta, sai dai yaƙi magana. Yarrrr haka ta ji tsigar jikinta tana tashi, ba ta san kallon ma yake yi mata ba. "Ka yi magana Please, ka ce ka haƙura" tayi maganar tana jan majina. Ƙafarsa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa, saboda ciwon da kansa yake yi, amma a zahiri abun da yake yin, kamar yana yi ne da gayya da nuna mata iko da izza irin ta ɗa namiji. "Kin cika mini kunne" yayi maganar a hankali, duk da buɗɗaɗiyar murya ce da shi irin ta jaruman maza. "To ka ce ka haƙura mana" tayi maganar cikin shagwaɓar da ba ta san ta yi ba. "Kai mini ruwa zan yi wanka" cikin sauri ta ce "To" Tunani yake yi daban-daban a ransa, ya ma rasa wanne zai yi, yana shiga wankan, ta sake gyara shimfiɗar katifarsa, ya yi wanka ya fito yanzu ma jikinsa babu riga, yana ƙoƙarin mayar da kayan da ya cire, da sauri ta ce "Ai kana da wankakkun kaya, na wanke maka ka saka wannan" ta yi maganar tana miƙo masa kayan da ta ciro masa. "Ɓace zan canza kaya" ta fita da sauri,mintuna goma da ta dawo, tuni ya kusa rabin abincinsa. Garin ta miƙa hannu ta ɗauki jug ta zuba masa ruwa, hannunta ya taɓa ƙafarsa ta ji zafi sosai, ta kalleshi ta sake kai hannunta ƙafarsa. "Master zazzaɓi ka ke yi?" Lomarsa ya cigaba da yi, cikin tsoro ta sake kai bayan hannunta ta taɓa hannunsa. "Na shiga uku ba ka da lafiya ai, duk ni na janyo ko?" Ya karɓi jug ɗin hannunta, ya cire murfin, ya kafa kai ya sha fiye da rabin ruwan, sai ka ce tsohon raƙumi. Ya gama ya jingina da jikin bango ya sake lumshe ido. "Master, akwai allurar nan da ka sayo mini ba ayi mini ba, mu je in raka ka ayi maka to" Gyatsa ya saki, maimakon ya yi hamdala, sai ita ta ce "Alhamdilillahilazi aɗa'amana haza, Ubangiji Allah ya ciyar da mu kullum, ya bawa wanda bai samu ba" "Amin" ya faɗa ƙasa-ƙasa zai kwanta, a sukwane ta ce "Dan Allah kar ka kwanta, mu je a duba ka, kar ka sha wahala, sauro ne yayi yawa a unguwar nan shiyasa muke ta zazzaɓi, dan Allah ka zo mu je a duba ka" "Kai wallahi kina addaba mini, kin dame ni" Jauhar ta kwantar da murya cikin sigar rarrashi ta ce "To na sani, amma ka yi haƙuri, na daina, dan Allah mu je a dubaka ka ji Mijin 'yar madara, ba ka ji yadda jikinka yayi zafi ba?" Ya kalli yadda ta dafe kafaɗarsa, tayi saurin sakinsa, ya ce "Sai an yi sallar magariba" "To mu koma falo, sai na saka maka maganin sauro a ɗakin, idan ka cigaba da kwanciyar jikinka mutuwa zai yi" Da ƙyar ta lallaɓo shi, suka dawo falo, ta kunna maganin sauro. Ana idar da sallar magariba, ta ɗaukko allurar, ta ce su tafi, ya ce ya fasa zuwa, shi ba zai iya tafiya ba. Da ƙyar sai ka ce ɗan goye, ta lallaɓa shi suka fita. Ta rufe ƙofar gidan, ta riƙe hannunsa ta ce "To mu je, kar ka ji jiri idan ka gaji ka yi mini magana sai mu tsaya ka huta". Kallonta kawai yake yi, ɗan hannun nata ɗan mitsitsi a cikin nasa. Suna tafe tana ƙara ba shi haƙuri, a kan laifin da ta yi. Nasiru mai chemist na ganinsu ya ce "A'a jauhar, kin warware shi ne shi ma ya kwanta" tayi murmushi ta ce "Allura na kawo shi, ayi masa mai sanyi dan Allah" Da jauhar ta san yadda yake ji a zuciyarsa idan ya ga tana tankawa mai chemist da ba ta yi ba, sai dai bai san dalilin hakan ba, kawai ba ya son ya ga wani yana kulata. Aka gama yi masa suka fito za su tafi, ta tsaya tambayar mai ɗanyen dankali nawa kwano. Al'amin ya zaro kuɗin ya bayar, suna tafe tana godiyar dankali. Da safe ta soya musu dankali da tea, ya gama karyawa, ya kalleta ya ce "Wannan matar da na gani a gidanku wacece?" Ta ce "Wacce?" "Mai baƙaƙen kayan nan" "Anty zakiyya ce, matar Baba ce" ya jinjina kai bai sake cewa komai ba. "Ka santa ne?" Yayi shiru bai amsa ba, daga haka ta ja bakinta tayi shiru. Babu yadda ba ta yi ba, a kan ya je a ƙarasa allurar nan, amma ya ƙi. Da ya ji ƙwarin jikinsa ma, fita ya cigaba da yi. Jauhar na zaune a falonta, tana tunanin ƙirƙirar sabbin styles na abun hannu da jigida, ta fara sayarwa. Aka bubbuga mata gate, ta tashi ta je ta buɗe, ta ga wani mutum da ba ta san shi ba, fuskarsa sanye da facemask ya ce "Mai zamani yana nan?" Ta girgiza kai ta ce "Ya fita" "Ga wannan ki ajiye masa". Ya bata leda mai baƙi da fari. Ta karɓa ta ce "In ji wa zan ce?". "Idan ya zo zai gane, ki ajiye masa a ɗakinsa, zan kira shi" Ta ce "To shikenan" Ta rufe ƙofa, kamar ta buɗe, sai ta fasa ta kai masa cikin drower sa, ta ajiye masa ta cigaba da sabgoginta. Kayan da anty lubabatu ta bata ta ɗauka tana duddubawa, ta ɗan ɗanɗana abun, tayi shiru tana tunani, ita sam abun da ake faɗa a auren, ba ta ga alamar sa ba, dan shi ba ta tata ma yake yi ba, ya ƙule a ɗakinsa yayi shaye-shayensa ya ci abinci ya fita yawonsa shi ne kawai a gabansa. Ta ɗan taɓe baki, ta ɗauki turaren wutar, ta tirara na gidan, ta turara na jikinta, ta ɗora girki. Da daddare da wuri ya dawo gida, gidan sai ƙamshi yake yi na musamman, giftawar farko da tayi, sai da ya ɗaga kai ya kalleta, ƙamshin har cikin ƙwaƙwalwarsa ya ji shi. Yau  faten dankalin ta yi, dan shi ne kawai da su, sai dai yayi masa daɗi bai taɓa sanin ana faten dankalin hausa ba, sai yau da ta bashi, har mamakin yadda take sarrafa abinci yake yi. Ya gama cin abincin ta ce "Master yanzu allurar nan dai ba za a ƙarasa ba ko?" "Eh" ya faɗa kai tsaye. "Ai shikenan, thank God tun da ka warke ai. Ka yi mini addu'a mun kusa fara WAEC, Allah ya sa result ɗina yayi kyau". "Sai ki yi karatu" "Ina yi ai" ya kalleta ya ce "A hakan, kina shirme dai" ta gane da kayan beat ɗin ta da stone yake, tayi murmushi jin yadda yau yake yi mata doguwar magana. "Ina karatu sosai da sosai fa". "Akwai kwaɗo a ƙarƙashin kujerar nan da ki ke" da sauri ta kalli kujerar, sai kuma ta yi dariya ta ce "Ai na daina jin tsoron" wai nan tsokanarta yake yi, amma fuskar nan a haɗe. Har wajen ƙarfe goma suna tare, yana ta danna wayarsa, mai madannai, ita kuma tana jin radio tana aikinta, ba hira suke yi ba, amma kasancewar su a hakan ma, daɗi take yi mata. Ya yi miƙa ya tashi zai tafi ɗaki ta ce "Tafiya babu sallama" Ba tare da ya yi Magana ba, ya ɗaga mata hannu, murmushi ta yi ta ce "Asuba ta gari mijin Angela" ɗan rausayar da kai ya yi kamar zai yi murmushi ya shiga ɗakinsa. Ya kwanta yana shaƙar ƙamshin da bedsheet ɗin sa yake yi, bai taɓa tunanin zai yi aure ba, dan babu wannan lissafin a gabansa, ba dan albarkacin auren ba, da a cikin tsummokara zai kwana a can gidan da suke tare da su Walid. Tsakar dare jauhar ta ji motsi, kamar ana watsi da kaya. "Malam kar ka shiga wannan ɗakin ba komai a ciki, mata ta ce a ciki, kuma babu in da shari'a ta baka damar shiga in da matata take" Jin muryar Al'amin, ya sanya ta saukko daga kan gadon da sauri, wata irin dalleliyar fitila aka saka ana haske gidan. "Shut up, kar ka sake magana, kar na sake jin bakinka" Cikin ƙaraji ya ce "Sai na yi magana, wallahi ka shiga ɗakin nan, zan illataka". Da gudu ta fito dan ta ga meyake faruwa, ma'aikata ta gani, har da jami'an tsaro, sun saka wa Al'amin ankwa sun durƙusar da shi a kan gwiwoyinsa. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai me yayi muku? Laifin me ya yi?" "Ki koma ɗaki Ki nemi hijjabi ki saka" yayi maganar cike da takaici. "Oya ku yi searching ko ina a gidan nan, kar ki motsa daga in da ki ke" Wani jami'in ne ya fito daga ɗakin Al'amin, da wannan ledar da aka kawo aka ce a ajiye masa, ya ce 'Ga abun da muka samu sir" Shugaban operation ɗin ya karɓa, ya zazzage sai ga ƙwayoyi, da allurai da wiwi da sauran tarkace sai kuma wata 'yar leda mai ɗauke da wani farin gari. Ya ce "Good, mu tafi da shi mun samu abar" "Yallaɓai, wallahi wani ne ya kawo su ɗazu, ba shi ya kawo su ba, dan Allah kar ku tafi da shi.  Ko kallonta ba su yi ba, suka tasa ƙeyar Al'amin. Ayshercool 08081012143 27 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Biyo bayansu tayi, tana wani irin kuka mai ban tausayi, tana yi musu magiyar su sake shi, ba shi da laifi, amma babu wanda ya saurareta a cikinsu. Maƙwabta na jiyo kukanta, amma babu wanda ya iya ko leƙowa ya ga abun da yake faruwa. Shi kuwa Al'amin ko a jikinsa, kukan da take yi ne kawai ba ya so. Suka saka shi a mota, ta ce "To Yallaɓai ina za ku kai shi dan Allah" "NDLEA, daga nan zamu miƙawa 'yan sanda shi, su kai shi gaban kotu". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu dai sai kun kai shi NDLEA ɗin kenan? Wancan karon baku kai shi ba sai yanzu, dan Allah ku duba lamarin nan" Suka saka Al'amin a mota, suka tafi da shi, a falonta ta zauna, ta fashe da kuka, ta daɗe a wurin tana kuka, ganin hakan ba mafita bane, ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala ta koma ɗakinta, tayi ta sallar da ba ta da tabbacin tana karanta ayoyin daidai saboda tashin hankali, ta ɗaga hannu tayi addu'a, amma ta kasa kawai ta mayar da kanta sujuda ta fashe da kuka. Har asuba ta yi idonta biyu, ta yi sallar asuba ta idar, ta zauna tana karanta duk abun da ya zo bakinta, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya. Bayan sallar asuba magidantan layin suka tsaya suna salallamin, jiya da daddare ma'aikatan sun shigo layin, amma babu wanda ya fito. Malam lawan ya ce "Har kwa tambayi lafiya? Ai tun da ɗan daba ya tare muku a unguwa, sai abun da Allah ya yi, wurinsa suka zo, wataƙila ma wata ta'asar ya je ya tafka, suka zo suka yi masa ɗaukar amarya tsakar dare". Suka yi ta salallami da fatan Allah ya kyauta. Har rana ta yi haske, jauhar tana zaune a wuri ɗaya, idanun ta sun yi ja, duk sun kumbura fuskarta tayi ja ta kumbura saboda kuka. Maman halimatu da wata mata mai kallon gidan na jauhar suka shigo, sai da suka yi ta sallama, da ƙyar ta iya amsawa sam ba ta ji sallamar ta su ba ma, ta fito falo ta ce su shigo. Maman halimatu ta ce "Jauhar, lafiya kuwa? Wai meyafaru ne jiya mun ji hayaniya, babu damar mu fito. Take wasu hawayen suka ziraro mata ta goge su ta ce "Jami'an tsaro ne suka  zo suka tafi da shi" "Subhanallah, laifin me yayi?" Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba" "To ki yi haƙuri, ki samu ki ci abinci,  sai ki nutsu a san abun yi, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba" Ta amsa musu da to ta gode. Kai ka ce takaba take yi, duk ta fita hayyacinta, ba ta san wurin wa za ta nufa da maganar nan ba, kuma ba ta san ina hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin take ba ma, balle ta je, ba kuma ta san ta tambaya a gano wani abun, gashi ko gidan su Al'amin ɗin ma ba ta sani ba, balle ta je ta gaya musu, ko da wani abu da za ayi a kai. Ta dudduba ta tattara ɗan kuɗin da take da shi, ta fita, ta samu mai napep ta tambaye shi idan ya san ina ne hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. Ya ce mata ya sani, ya ɗauke ta ya tafi da ita. Ta din ga yawo a cikin hukumar, aka ce mata ba ya wurin, ba a kai shi ba, sai da ƙyar aka ce mata yana nan, amma ba zata ganshi ba, babu irin magiyar da ba ta yi ba, amma suka hanata ganinsa, ƙarshe sai gida ta koma a matuƙar galabaice. Ta rama salollin da suke kanta, ta din ga addu'a da fatan Ubangiji Allah ya fitar da shi lafiya, da ta san abun da zai faru kenan, da ba ta karɓi abun da ba ta san ko menene ba ta ajiye masa. Ɗaya maƙwabciyar ta ta wasila, wadda mijinta ya taɓa raka su wurin mai chemist ta shigo gidan. Ta ce "Jauhar yaya ake ciki, kin same shi kuwa, kin je wurin 'yan sandan?" Ta ce "Eh na je, ba su bari na ganshi ba" "Kuma ba su gaya miki abun da yayi suka kama shi ba?" Ta jinjina mata kai alamar eh, wasu hawaye masu ciwo suna zubo mata. "Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki jauhar, in sha Allah komai zai wuce kamar ba ayi ba, kuma in sha Allah zai fito" Ta ce "To Allah ya sa". Yau ma haka ta kwana salloli, da kai wa Allah kukanta, da fatan Allah ya saka mijinta yana lafiya ya kuɓutar da shi. Da safe ta sai ƙosai da buredi, ta dafa tea, ta kuma wanke ƙafa ta koma wurin nan, amma suka sake ce mata ba za ta ganshi ba, tayi magiyar har ta gaji, ta basu abincin ta ce su bashi. Ta koma harabar wurin, ta nemi wuri ta zauna, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, rabonta da abinci tun a jiya, gaba ɗaya tunanin halin da Al'amin yake ciki, da wanda zai shiga a nan gaba ya dame ta, ta gaji da zama ta tashi ta nufi gida. Ɗakinsa da suka shiga duk suka watsar da kaya ta shiga, dan damuwa ba ta bari ta shiga ta gyara ba. Duk sun watsar da komai na ɗakin, ta tattare masa kayan, tana cikin gyarawa ta gano wayarsa, ta ɗauka tana duddubawa sai ta ga tarin kiran walid da liti, cikin hanzari ta kira lambar walid. "Ya ne maza? Tun shekaranjiya ban sake jin ɗuriyarka ba, na zo gidanka ba kowa ka kuma ƙi ɗaga waya". "Assalamu alaikum" tayi masa sallama. Ya ce "Ahh madam ke ce ashe? Ya ake ciki yana ina?" Muryarta na rawa ta ce "Shekaranjiya da daddare jami'an tsaro sun zo sun tafi da shi" "Kamar yaya? Me yayi?". "Abu aka kawo aka ce na ajiye masa, su kuma suka zo da daddare suka ga kayan a leda, suka tafi da shi na je sun hanani ganinsa" tayi maganar cikin kuka. Walid ya ce "Ya isa haka yi shiru, bari na zo gidan gani nan" Sai ta ɗan ji sanyi a ranta, tamkar yana zuwa zai fito mata da Al'amin ɗin. Kusan awa ɗaya da rabi, ta ji ana knocking gate. Da sauri ta tashi ta je ta buɗe, liti ta gani da Walid, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su. Walid ya amsa ya ce "Ya aka yi, meyafaru?" "Yadda dai na gaya maka, wani ne ya kawo wata leda ya ce a ajiye masa, na manta ban nuna masa ba, kawai suka zo cikin dare suka tafi da shi, naje na je hukumar sun hana ni ganinsa" Liti ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina kukan haka, kuma kin tabattar bai yi wani laifin ba?" "Ni dai a iya sanina bana tunanin yayi wani abun, duk da ba tare muke yawo da shi ba, amma dai sun ce a kan kayan da suka gani a gidan nan ne" Walid ya ce "Ki kwantar da hankalinki, in dai Viper ne, mutum ne mai sa'a koma menene zai fito, amma ki kwantar da hankalinki, yanzu idan muka je babu lallai su sauraremu, amma in sha Allah gobe in Allah ya kaimu da wuri zamu je mu ga yadda za ayi". Ta ce "To shikenan na gode sosai, bari na kawo muku ruwa" "Kar ki damu a ƙoshe muke, ki kwantar da hankalinki idan da wani abu ki kira lambata" Ta ce "To na gode" Ta rufe ƙofa suka tafi, liti ya ce "Ikon Allah" "Menene?" "Kawai rayuwar Mai zamani nake kalla, yadda yake gararambarsa da kamar babu mai so, idan muka faɗa cakwakiyarmu, iya mu muke warware kayarmu, babu wanda ya damu da mu, shi kalli Allah ya kawo masa mai kula da shi". "Haka ne, amma tausayi ta bani wallahi, yarinya ce sosai. Yana ta buyagi da rashin mutunci an yi masa aure, amma sai da ya mari madaki saboda ya tankata". Liti ya kwashe da dariya ya ce "Kai mace fa aka ce maka, na raba ka" Walid ya kwashe da dariya ya ce "A ƙi faɗinsa, da madaki ya ce ya kashe ta, mazewa yayi ba zai motsa ba, wai ba shi ya aiketa ba, amma ka ga wasu jijiyoyi da suka tashi a goshinsa, ga wani gumi da yake a iya karan hancinsa, bai san yana wasu abubuwan ba" suka sake kwashewa da dariya. Liti ya saka su guduma ɗan gidan mai unguwa, su din ga kaiwa sun komowa, suna ɗan zagaywa a layin gidan viper, idan suka ga wani abu da ba su yadda da shi ba, su sanar masa. Suka cigaba da kaiwa suna komowa a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma su ma ba su samu ganin Viper ba, suka ce sai dai idan sun kai shi wurin jami'an tsaro su je can su ganshi. Hankalin Jauhar ya ƙara mummunan tashi, ta rasa in da za ta saka ranta ta ji daɗi. Ta sake amfani da wayarta, ta kira walid a waya, da yake sun ce kar ta sake zuwa hukumar, ta bari za su din ga zuwa su. Ta duba wayar kaf, babu sunan wani mutumin kirki a ciki, balle tayi tunanin akwai lambar wani ɗan gidansu,  ta kira duk sai sunayen su Liti da ire-iren su. Sai kuma ta fara tunanin ko ba shi da kowa ne? Amma da ba shi da kowa ai ba zata ga kakarsa ba, kuma an nuna mata Rahila ranar da aka yi bikinsu Anty Zakiyya ta ce mata wai babarsa ce, amma tana tantama tun da aka yi auren, bai taɓa kai ta gidansu ba, kuma babu wani wanda ya zo daga gidan. Walid suka Kuma dawowa suna rarrashin ta, a kan suna ta ƙoƙarin ganin ya fito, ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah to ina ne gidansu, yakamata ace sun sani" Walid ya ce "Taɓ ke 'yan gidan na su da suna ta tashi, da baki gansu ba, ki manta da maganar su kawai ki cigaba da addu'a". Ta ce "Amma kamar yakamata a gaya musu halin da yake ciki, ko ba za su yi komai a kai ba". Walid zai yi magana, liti ya ce "Bari na kwatanta miki gidan na su" yayi mata kwatance sannan suka yi mata sallama suka tafi. Liti ya ce "A irin wannan yanayin da take ciki, idan ba ka kwatanta ba sai ta tsaneka ai, idan ta je ta ganewa idonta shikenan" "Haka ne, amma ka san wannan matsiyaciyar matar gidan na su ba mutunci gareta ba, kar ta ƙara mata zafi". Suka cigaba da tattaunawa. Kusan kwanaki bakwai da kama Al'amin, idan ka ga jauhar sai ka ce tayi jinyar shekaru, duk ta ƙare ta fita hayyacinta. 'yan sana'oin ma ba ta iyawa, saboda tunani da damuwa. Liti ya zo da safe, tana falo tana karatun Alkur'ani, ta ga kiran waya a wayar Viper, ta tashi ta fita ya ce "Sako hijjabinki mu

Chapter 27 of 121