Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
110 / 121
ramma, komai normal sai palpitations, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, suka din ga rarrashinta, suna kwantar mata da hankali. Aka yi mata abin da yakamata, aka kwantar da ita, aka ce ta ɗaga ƙafafuwan ta, ta ce ba zata iya ba, suka rufe yadda zata ga me suke yi, ta miƙa hannu ta riƙo na Abdul. Doctor Muktar ya ce "Anya ba korarka zamu yi ba, malam ka nutsu ka mayar da hankalinka mana" Ramma ba ta san me ake yi ba, ta ji kamar ana yi mata shocking dai, kuma ana jijjigata. Gashi sai surutu suke yi mata, suna mata hira mai ma'ana da mara ma'ana. Ta ce "Doctor Abdul" "Yes my dear" "Ban taɓa ganinka a cikin kayan tiyata ba, sai yau da Allah ya yi kai zaka yanka ni" Ya ce "To ya ki ka ga, sun yi mini kyau?" Ta ce "Sosai ma, duk sun fi yi maka kyau". Muktar ya ce "Ban da son kai fa, tsakani da Allah na fishi kyau" Ramma ta ce "Anya kuwa? Doctor ashe doctor Muktar ne ya yi wa Anty Jauhar matar Yaya Aminu awon ciki, kuma shi ya tabattar da rasuwarta" Abdul ya ce "Haba dai?" "Wallahi tambaye shi ka ji" Muktar ya ce "Baka ga yana ta lallaɓa rahama ba, gayen nan na tausaya masa, ko yanzu kafin mu shigo, naga damuwa a tare da shi, ana gobe za a kashe ta, na gaya masa ya tanadi kuɗi, idan inducing bai yi ba, yayi failing C.S ne, gayen nan ya ce ko nawa ne, zai nemo su, na daɗe ban ga zunzurutun so da ƙauna ba sai a wurin su, kuma kalli ikon Allah ga 'yar uwatta nan da take kawo Madam awo, kamar su ɗaya sak" Shiru Abdul yayi, bayan da Muktar ya ciro jaririn cikin rahama, jibgegen yaro, fari ƙal alama ya daɗe ma da mutuwa, fatarsa ta fara macerating, sai dai kyakykyawan gaske ne, ga gashi cunkus a kansa, har goshinsa zuwa girarsa gashi ne. Abdul ya kalli doctor Muktar, amma ya girgiza masa kai, yayi masa alamar yayi shiru. Ramma ta ci gaba da magana, doctor Muktar yana bata labarin Viper da Jauhar. Ta ce "Wai haryanzu ba a ciro ɗan ba?" "Babyn naki ne, ƙato to, amma yanzu za a ciro shi in sha Allah" Ta ce "Allah ya fito mini da shi lafiya, na bi na ɗaga hankalina, ashe CS ɗin ba abin tashin hankali bane ma" Maman ramma na can waje, tana jera salloli tana addu'a, Allah ya sa a fito mata 'yar ta da lafiya. Viper kuwa kamar ya haɗiye Nabila, sai satar kallonta yake yi, duk da ta basar da shi, amma zuciyarta azalzalarta take yi, ta kula shi, ta yi kewarsa sosai amma ta maze, ta kira Sumayya ta gaya mata suna Asibiti wurin ramma. Ramma ta ji shiru-shiru, ba a ce mata ga ɗa ba, ta ce "Nifa ban ji yayi kuka ba, idan kun ciro shi, ku nuna mini shi mana" Muktar ya ce "Ai sai mun gama, an kai ki ɗakin hutawa sannan zaki ganshi" Ta ce "Ka haɗa kai da abokinka sai ya rigani ganinsa, shikenan ai" "Wai dama kina magana haka? Kullum idan aka kawo ki awo, kanki a ƙasa kina ɓuya" Tayi murmushi ta ce "Idan na yi shiru, zai shiga damuwa ne, shiyasa nake magana" Muktar ya girgiza wa Abdul kai, saboda yadda ya karaya jikinsa yayi sanyi, ya ƙallafa ransa da ɗora buri a kan abin da ramma za ta haifa, daga fitowarsa ya sai sa da rago, saboda ya ce ko me za ayi, ko a faɗa sai dai ayi, amma babban shagalin bikin suna zai yi. Ya nananɗo jaririn a zani, ya fita daga cikin tiyatar jikinsa a sanyaye. Gaba ɗaya suka nufo shi, suna jera masa tambayoyi. Maman ramma ta ce "Yaya ina rahaman? Mutuwa tayi?" Ya girgiza musu kai alamar a'a. Viper ya ce "Kayi magana mana menene?" Yayi maganar yana ƙoƙarin karɓar jaririn. Ya karɓe shi, ya buɗe shi, ya ga bashi da rai. Take jikin Viper ya sanyi ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Yaron ba shi da rai, kamar ma ya kwana biyu da rasuwa, amma mama da wa yaron nan yake yi miki kama" yayi maganar yana nuna mata fuskar jaririn. Ta ce "Kaii, kamar Nura ce ai wannan, wallahi kamar su ɗaya sak, bani shi na gani, ina ma yana da rai, wayyo Allana" ta karɓi jaririn tana kallonsa, hanci har baka ƙato mai kyau, amma babu rai. Abdul ya koma ya jingina da jikin bango yana kallonsu kawai, jikinsa gaba ɗaya ya yi sanyi, yama kasa komawa ɗakin tiyatar. Sai da Nurse ta fito ta ce masa, ana nemansa, sannan ya shiga, ya tarar an gama ɗinketa, har an sakata bacci, aka fito da ita daga tiyatar, suka nufeta, suka tarar bacci take yi, dan yadda aka fito da ita kamar matacciya. Aka kaita post-op room, aka kwantar da ita. Doctor Muktar ya kalle su ya ce "Haƙiƙanin gaskiya, tun da ku ka zo na yi mata scanic, naga yaron ya mutu, bana son ɗaga muku hankali ne, ta ƙara karaya kafin ayi aikin, rashin sanar da batun zubar ruwan nan ne, da wuri ya ƙara ta'azarra lamarin. Amma Alhamdilillah ita tana nan ƙalau, mun tura lab ayi post-op pcv, mu gani idan jinin jikinta ya isheta normal ne, idan kuma akwai buƙatar a ƙara shikenan, amma dan Allah a rarrashe ta, a bata baki" Mama da su Nabila suka yi ta yi masa godiya. Viper ya ce "Yakamata ka zo mu je a binne shi ko" Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah a jira ta farka, ta ganshi, idan aka rufe shi ba ta ganshi ba, za ta ji babu daɗi" Viper ya jinjina kai, mama ta miƙa wa Viper yaron, ta tafi gaban gadon ramma da take ta bacci, tana kallonta tana shafa kanta cike da tausayawa. Viper ya riƙe yaron sosai, ya zuba masa ido, ya tuna shi ko gawar masa ɗan ma bai gani ba, kamar dai Abdul ɗin nan haka ya din ga zumuɗi a kan haihuwar da yake saka ran ayi masa, amma a ƙarshe duka biyun ya rasa su. Shirun da ya yi yana kallon jaririn, Nabila ta san me yake tunawa, saboda yadda ya tattara nutsuwar sa kacokan a kansa, yana ta sauke numfashi. Nabila ta miƙa wa Viper hannu, ta ce "Ba ni shi nima na ganshi" Mugun kallon da ya yi mata sai da ta ja da baya, ya koma gefe ya zauna, rungume da gawar yaron. Alhaji mu'azzam ba ya gari, ya aiko yaronsa da yake yi wa su ramma hidima, idan da wani abu da ake buƙata. Nabila idan idonta dai-dai yake gane mata, har da harara Viper yake ta aika mata. Abdul kuwa sai da ya zubar da hawaye, a cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar yaronsa, gashi dai babu rai ya zo, amma sosai yake jin son sa a ransa. Mummy ce ta addabe shi da kiran waya, ya gaji ya ɗaga ta ce "Kana ina ne?" "Ina Asibiti Mummy" "Na ji muryarka ƙasa-ƙasa wani iri, menene?" "Rahama na yi wa C.S, ta haihu ɗan babu rai". "To kuma shi ne me? Ba zaka raba kanka da harkar mutanen banza nan marasa mutunci da suka ɗaureka ba ko? Ka dawo gida babanka yana hanya zai shigo Kano, yana son ganinka, tun da kai ba ka ga dacewar ka je in da yake ba" "Mummy, ɗa na fa na rasa, an yanka 'yar mutane, haryanzu ba ta farfaɗo ba, kawai na kama hanya na tafi na bar su, anya na yi musu adalci kuwa?" A fusace ta ce "Ni ka ke gaya wa haka Abdul?" "Ki yi haƙuri, ba wai rashin kunya bane ba, ko gaya miki magana ne ba, amma duk fa abin da ya samu rahama ni ne sila, zuwa anjima in sha Allah zan dawo, ina jiran ta farfaɗo ne" Ya katse wayar, yana mamakin son kai irin na iyayensa. Ramma ta farfaɗo daga baccin da take yi, suna ta jera mata sannu, kafin ta amsa ta kalli Nabila ta ce "Anty Nabila ina jaririn ne?" Nabila ta ce "Bari a kirawo Abdul ɗin" Aka kirawo Abdul, ya shigo cikin kulawa yana yi mata sannu. Ta ce "Ina babyn?" Ya zauna a gefen gadon ya ce "Ki na ji rahama, ki yi haƙuri da duk abin da Allah ya hukunta mana, babyn bai zo da rai ba, da alama ya ma kwana biyu da mutuwa a cikinki, sai mu yi haƙuri" "Wayyo Allana, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu duk wannan wahalar da na sha amma ya mutu" Mama ta ce "Ke ramma, ba musulma ba ce ke? Ba za ki yi tawakalli ba?" "Mama na sha wahala fa, amma ya mutu" ta yi maganar tana kuka. "To dan ubanki sai ki dawo da shi, ke da ki ka samu kanki lafiya ƙalau ba zaki gode wa Allah ba?" Ramma ta kasa jurewa ta fashe da kuka, Abdul ya yi shiru ya ma rasa me zai ce mata, shi kansa kukan yake son yayi, saboda ya saka rai sosai da sosai. "Rahama" Viper ya kira sunanta. "Na'am" ta faɗa tana ɗaga kanta ta kalleshi. Ya ƙarasa gaban gadonta ya ce "Ba a jayayya da ikon Allah kin ji ko? Mamanki da ta rasa Nura haƙuri tayi, nima na rasa ɗa na da matata da tsohon cikin da na ƙallafa rai a kansa, amma ko ganinsa ban yi ba, na rasata na rasa ɗan, dan haka ki yi haƙuri ki yi masa addu'a" Ya nuna mata jaririn nata, ta kai hannu ta taɓa fuskarsa ta ce "Shikenan, Allah ya jiƙansa ya sa ya huta" Abdul ya ce "Amin, ki yi haƙuri kin ji madam, Allah ya kawo mai amfani, ki kwantar da hankalinki, dan a samu ki warke da wuri" ta jinjina masa kai. Viper ya saka yaron a kwali, ya ce wa Abdul, "Mu je a binne shi ko?" Abdul ya jinjina kai, har magariba Nabila na tare da su rahama, ana ta rarrashinta, daga baya tayi musu sallama ta tafi gida. Sai da Viper ya tabattar da su mama basa buƙatar komai, sannan ya tafi. Muktar ya daɗe yana ba wa Abdul labarin Viper da matarsa, da yadda aka liƙa masa kashe matar ta sa, har yake gaya masa yaje kotu ya bayar da shaida a kan shari'ar, tare da nanata Naja'atu Bunkure ba ta da imani. Abdul ya yi shiru yana tunani, tabbas duk abin da Viper yayi, tirsasa masa aka yi, an cutar da shi da yawa, dole ya tsane shi. Jikinsa a sanyaye ya koma gida, yana hasko cewa shi ɗansa kawai ya rasa, duk ya damu ya shiga cikin tashin hankali, amma shi Viper da matar da ɗan ya rasa, kuma aka ɗaure shi aka tauye masa hakkinsa. Da haka ya ƙarasa gida. Yana zuwa gidan ya shiga falon Mummy, suna tare da Indabo, yana cin abincin dare. Ko zama bai yi ba, ta hau shi da faɗa, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, tana kiransa mara zuciya da bai san ciwon kansa ba. Cikin takaici da mutuwar jiki, ya ce "Mummy ɗa na fa na rasa, haihuwa aka yi mini ɗan ya koma, kuma ɗa na halal ɗan sunna. Mummy idan iyayen rahama sun saka an rufe ni, meye na ɗa na a ciki? Yadda ki ke jin so da ƙaunarmu, haka nake ji a raina, ɗa na ne ya zo babu rai, amma baki tausaya mini ba, baki jajanta mini ba sai faɗa ki ke yi mini ya zan yi ne?" Indabo ya ce "Abdul" Abdul ya kalle shi ya ce "Zo nan" Abdul ya ƙarasa gaban digning ɗin ya ce "Gani" "Zauna mu yi magana" Abdul ya ja kujera ya zauna yana sauraren indabo. "Yanzu Abdul duk abin da ka haddasa, duk bai dameka ba ko? Ka wulaƙantar mini da kuɗi, a kan shashashar 'yar ƙauye, ka yi asarar takarar da nake ta fafutukar na tsayar da kai, dan na san ina tsayar da kai, za ayi caa a tona asirinka, a sake ɓata mana suna, yanzu ni na riga na san na yi asarar takarata duk saboda wawancinka, kuma still baka yi regreting ba, kana faɗar maganganu kana cikin hayyacinka kuwa Abdul? Tun wuri tun da ta haihu, shikenan ina son lallai ka rabu da yarinyar nan, ka fita harkarta, ka zo ayi settling maganarka da yar party chairman haryanzu muna da sauran chances, a next tenure za a iya baka minista, ni kuma in san abin yi. Dan haka lallai ka saketa tun da dama ba wanda ya san ka aureta" Ya kalli mahaufinsa cikin matsanancin takaici ya ce "Daddy, yadda Jafar yake Mexico a tsare, ranka yake maka zafi saboda an tsare maka 'ya, haka maman rahama take ji, koma fiye a duk lokacin da ta tuna na keta wa 'yar ta haddi. Ba dan na zaɓi rahama a kan ku iyayena ba, amma sai da rahama ta shigo rayuwata, na fuskanci gaba ɗaya rayuwata jarrabawa ce, kasancewarku iyayena, babu wanda ya tsawatar mini da shaye-shaye, ko sauran laifuffukan da nake aikatawa ba, kuna kallon hakan a abu ne da zan daina a gaba, rayuwar cikin turawa ya sanya na zama haka. Ban ƙara tabattar da zamanku iyayena jarrabawa ce ba, dai da na nuna maka videon mummunan aikin da ka aikata, amma hakan bai wani dame ka ba, kuma bai girgiza Mummy ba, saboda duniyar ce kawai a gabanku, ni kuwa tuni rahama ta ankarar da ni fifikon Lahirata a kan duniya saboda ita ce dahir. Na miƙa lamurana ga Allah, la'akari da Annabin Allah ma, Annabi Ibrahim alaihi salam, Allah ya jarrabe shi a kan mahaifinsa, haka an jarabci Annabi nuhu da ɗansa, kowane bawa da irin ƙaddararsa, wallahi ku ka ci gaba da matsa mini, zan bar gidan nan, zan je na ci gaba da rayuwata kawai" Indabo ya kwantar da murya ya ce "Haba Abdul, duk wannan abubuwan da kaga ina aikatawa, duk dan mu yi surviving ne, na inganta rayuwarku, kuma abin da ka gani abu ne da ya riga ya wuce, na daina aikatawa, kowane ɗan Adam akwai irin laifin da yake yi wa Allah, kuma Allah mai rahama ne da jin ƙai" "Amma Allah ba abokin wasanmu bane, da dan muna taƙama da mai rahama ne da jin ƙai, zamu din ha aikata zunubai yadda muka ga dama, mu ce gafurun rahimu ne ba. Kuma ace ɗan Adam baya kunyar saɓawa Ubangiji, Daddy har kisan kai fa ka ke saka wa a yi" Indabo ya ce "Wa na ce a kashe?" "Matar Aminu Viper, dan ɗan uwan rahama ne matata, aka kashe matarsa da ɗansa, ita laifin me ta aikata?" "Shi ne yake hure maka kunne kenan? Shiga gonata yayi, na ce aje a koya mass hankali, tsautsayi ya faɗa kan matarsa" Hawaye na bin fuskar Abdul ya ce "Kun samu ssɓani saboda yayi barazanar tona maka asiri na abun da na yi wa yayan rahama, ka tura a kashe shi, aka kashe matarsa, kuma sai aka ɗora masa laifin. Daddy su iyaye ba a canza su, kuma ba a wulaƙanta su, ko da kuwa mushirikai ne, shiyasa tun a wancan lokacin na yi shiru na ci gaba da yi muku biyayya, kamar yadda Annabi Ibrahim alaihi salam yayi. Amma muddin ku ka ci gaba da takura mini, a kan rabuwa da rahama, zan bar gidan nan gaba ɗaya. Allah ne ya tashi kama ni, ya sanya na keta mata haddi ya jarrabe ni da son ta. Allah ne ha so ni da rahama, na haɗu da rahama, kuma shigowarta rayuwata ta zo mini da tarin alkhairi, ni duk abin da suka yi mini, ban ji haushi ba, domin kuwa ma sassauta mini suka yi, dan Allah ku bar ni na ji da zafin da zuciyata take yi mini dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa alamar magiya. Har Mummy za ta yi magana, Indabo ya ɗaga mata hannu, Abdul ya wuce yana share hawaye, yana jin zuciyarsa na wani irin zafi saboda tuna wasu abubuwan. ***** Viper ya tafi tare da Abbu ya duba ramma a asibiti. Abbu sun yi hira sosai, dan sai da hirar ta tuna masa da marigayiyya matarsa babbar su Viper zahra'u. Abdul yana ta zarya a kan rahama, baya damuwa da shan ƙamshin da mama take yi masa, hatta medications ɗin ta, shi yake serving. Duk abin da ake buƙata haka yake yi mata, baya nuna gazawa, dama yana zuwa mama ke bar musu ɗakin. Ranar da Abbu ya zo duba ramma, Nabila ma tana nan, yana ankare da su daga ita har Viper, babu wanda yake kula wani, yayi musu shiru bai ce musu komai ba. Sai da Ramma ta kwana biyar a asibiti, sannan Abdul ya yadda a sallameta, babu wani abu da yake damunta, ta samu sauƙi sosai da sosai. Nabila na zaune a ɗakinta, a kan gado, ta baje takardu tana duddubawa tana nazarin shari'oin da take da su. Abba yayi sallama a ɗakinta, ta amsa masa ta miƙe tana faɗin "Abba Allah ya sa ba laifi nayi ba?" "Saboda kin saba da aikata laifuffuka ba" ta ɗan yi murmushi. Ya zauna a gefen gadonsa ya ce "Maganganu ne da ni nake son mu yi" yayi maganar yana kallon jikin wardrobe ɗin ta, duk ta liƙe shi da hoton maciji da stickers na Viper. Ta ce "To Abba ina jinka" "Yanayin alaƙarki da ɗan uwanki Nasir, dan Allah ina son komai ya wuce, ba na son gabar da ku ke yi sam" "Abba ba gaba nake da shi ba, kawai ika mamakin yadda ya din ga kware mini baya ne, yana haɗa ni da kai" Major ya ce "Na sani Arfa, amma Nasir ba ƙashin yarwa bane, kin san kowane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kuma abin da ya aikata shi ake kira da rauni, irin na ɗan Adam" Nabila ta jinjina kai ta ce "Haka ne" "Yauwwa dan Allah ya wuce ki yi haƙuri" "To Abba, in sha Allah ya wuce, Allah ya yafe mana baki ɗaya, yanzu ka yarda gaskiyar da ka tarbiyyantar da ni a kai a kanta nake dagewa, shiyasa wasu lokutan ake ganina kamar mara ji, ko mara ɗa'a ko" Yayi dariya ya ce "Na yarda, Allah ya ci gaba da dafa miki" Ta amsa da "Amin" "Abu na gaba, babanki ya ce na gaya miki, An tsayar da ranar auren sisternki, ƙarshe watan nan, za a sake ɗaura aure, ta koma gidan tsohon mijinta, Alhaji mu'azzam" Nabila cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na ji daɗi sosai da sosai nayi farinciki, Allah ya sanya musu albarka ya daidaita su" ya amsa da "Amin, to ke ya naki batun ne? Kin ce ba kya son yaron nan, babansa sai magiya yake yi yana roƙo, ga Sumayya mamanta ta yi mini magana, wani ya fito ya ce shi kuɗin aure zai kawo, ke kuma kin ja bakinki kin yi shiru, baban yaron nan ya damu lallai a ba wa ɗan sa ke" Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Haryanzu Abbu bai haƙura ba? Wallahi ina jin nauyinsa sosai da sosai, amma ba zan iya auren Vi ba" "Meye kuma vi?" "Au Al'amin" "Haryanzu yana shaye-shayen ne da harkar daba?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai yanzu soja ne, kuma yana zuwa asibitin ƙwaƙwalwa, duk ya rage yin wasu abubuwan, kawai dai ba na son sa ne" "Ita kuma wallpaper ɗinki, da wannan liƙe-liƙen na ɗakinki, duk cikin tsanar ta sa ne?" Cikin jin kunya ta ce "A'a Abba, kawai dai ina sakawa ne, a lokacin ina da hope na ganin na saka kotu ta wanke shi daga zargi" Abba ya tashi ya ce "Gaskiya ne, to ni dai duk hukuncin da babanki ya yanke ba ni da ta cewa, tun da na ga shi ma yana yin yaron, ni na fita sai na dawo" "A dawo lafiya" "Allah ya sa" ***** Rahila ta ɗaga hankalinta sosai, ganin da gaske Walid da ba shi da komai zai aura wa Shahida, babu irin zagin da ba ta yi wa shahida ba, amma tayi bore ta ce ba ta so, amma Shahida ta ce ita ta ji ta gani. Abbu ya ce "Ke dama ban isa sa ke ba, Shahida kuwa 'ya ta ce, dan haka ina da ikon zartar da duk wani hukunci a kan ta, idan bai yi miki ba, zaki iya tattara kayanki ki ƙara gaba, dan albarkacin ta kawai ki ke ci ki ke zaune a gidan nan" haka suka yi faɗa kaca-kaca, ƙarshe Shahida sai komawa tayi cikin ɗaki tana kuka. Da daddare da Viper ya je gidan, ya ga Shahida kamar ba ta walwala, yake tambayarta ko lafiya. Cikin damuwa ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙa mini Abbu, na ji ya ce saboda ni mama take zaune a cikin gidan nan, dan Allah ka ba shi haƙuri, na san tun ba yau ba, yana matuƙar haƙuri da ita, amma dan Allah yayi haƙuri, ba ta da cikakkiyar lafiya kuma idan ya rabu da ita, babu in da za ta je, dan Allah yayi haƙuri" Viper ya ce "Kar ki damu, barazana yake yi mata, kin san shi da tausayi, da kuma fushi wasu lokutan, amma in sha Allah ba zai rabu da ita, duk a kan maganar aurenki ne ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Ba zigaki nake ki bijire mata ba, amma ki samu miji irin Walid, sai kin daɗe kina tonawa, tun da ki ka ga Abbu ya amince shi ma, ba mutumin banza bane ba" Shahida ta ce "Haka ne Yaya, ni dan Allah ma ka yi masa magana, wai ba zai yadda a bashi aurena, kuma a bashi wurin zama ba, wai haya zai kama, kuma ya dage sai ya yi mini kayan lefe ko babu yawa. Naga ba ƙarfi ne da shi ba, kuma ni ina duk abin buƙata. Budurwa ce ni ba bazawara ba, amma yaƙi yadda" "Muhsin bai yarda da gazawa ba, wannan wata aƙida ce da muke da ita, ko zamu yi a raina, mun fi son mu ƙoƙarta, amma ki kwantar da hankalinki, zan yi magana da shi in sha Allah, kuma da mun kammala shiri, ba jira zamu tsaya ba da an kawo kuɗin aure lokaci za a tsayar, duk abin da ki ke buƙata ki gaya mini" Shahida ta amsa da "To yaya in sha Allah " Wasa-wasa girma ya hau kan Viper, ɓangaren ramma shi ne, haka gidansu, ga liti ga Walid, kowa Viper. Al'amin sai da ya fara tausayawa Abdul, Abdul bai furta a bashi ramma ba, amma yadda yake sintiri kullum a tafe, ya ƙara tabattar da gaisuwa yake gami da roƙon iri, a kan a bashi matarsa. Ita kanta mama ta ɗan fara saukkowa, ta zuba musu ido. Dan kuwa duk da jaririn ya mutu, sai da ya yanka san da ya saya ya ce idan ta haihu za ayi mata amfani da shi. Duk da kayan da take da su, sai da yayi mata sayayya fal, na kayan sakawa. Ranar da ya kawo, ta din ga yi masa godiya, ya tambayeta, me take so ta karanta zai yi processing komawarta makaranta. "Nurse nake son zama" Yayi murmushi ya ce "Shikenan, sai mu ƙarfafi asibitocinmu, mu kula da su sosai da sosai, amma rahama zaki dawo gidana sai ki yi karatun?" Ramma ta ce "Ai ka san wannan ba maganata ba ce ba, maganar mama ce da yaya Aminu, amma kuma idan na dawo gidanka ai ba zan samu yin karatun ba, an ce ba a ɗaukar masu ciki" Abdul ya ce "No, sai mu yi planing zuwa lokacin da zaki kammala" Ta ce "Anya kuwa, yadda ka ke son yara, kar in je ka canza shawara" "Haba rahama, kin fi kowa sanin halina, ni ɗan Adam ne, amma ban fiye yi wa mutum ƙarya ba dan ya yarda da ni, duk son yarana dolena na jure, kema na ga na inganta rayuwarki na kafa ki" "To ka bari yaya Aminu ya dawo, ya koma wurin aiki ne, amma ka fara yi wa Daddy magana tukuna" "Waye daddyn?" "Alhaji mu'azzam mana, ko da nayi aiki a gidansa, ai haka ake ce masa" "To shikenan, zan yi masa magana in sha Allah, kin san za a mayar da aurensa da yayar Nabila Hafsa". "Ai ban santa ba, ni lokacin anty Jidda na fara aiki a gidan" Abdul ya ce "Ok haka ne, ta koma gida ma, wai sai ya saketa duk a kan case ɗin mu, ni kowa ya ƙarata, a bar mini matata kawai" Tayi murmushi suka cigaba da hira. Nabila sai da tayi ta rarrashin Hafsa, a kan tayi haƙuri ta koma gidan Alhaji mu'azzam, dan fafur cewa tayi ba ta sonsa. Kasancewar duk ƙarshen wata, sai tayi sayayya taje ta gaida Baba, hakan ya saka sun shaƙu sosai da hafsa, sai dai sauran mutanen gidan babu ruwanta da su, idan aka

Chapter 110 of 121