Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
71 / 121
ta shekaru ta tafi a banza ba, in ƙare a lalace, ƙaramar yarinya ta rusa ni ba, ko dai ka saka a dakatar da program ɗin nan, ayi abun da ya dace a kanta, ko kuma ni zan ɗauki matakin abun da ya dace" Indabo ya kalleta ya ce "Naja, wai yaushe ki ka zama haka ne? Duk wata matsala tare muke magance ta, amma wannan sai nema ki ke yi ki zame, ba fa wata babbar matsala bace ba" "A wurinka ne ba babbar matsala ba, kuma ƙaramar matsala ita ce take zama babba. Kana jin manyan lauyoyin nan da basu samu dama a kaina ba da, yanzu sun samu suna ta bata goyon baya, mutane sun fara farga da abun da take yi, ni na rasa wai waye uban ɗakinta ne waye ya tsaya mata?" Ya numfasa ya ce "Kankarofi ne" "What? Kankarofi kuma? Meya kawo shi cikin wannan maganar?" "So yake lallai sai ya ga bayana, ya rama abun da ya faru a baya, maimakon ya rama a siyasance, ba ta haka yake son yi ba, so yake lallai sai na tozarta" Naja ta ce "Ikon Allah, to menene ribarsa, alhalin kuna sirikai?" "Aurenma da ya auri jidda, duk cikin plan ne na siyasa, kin san ita siyasa babu maƙiyi na dindindin, kuma babu masoyi na dindindin, mun zauna jam'iyya ɗaya da shi a baya kamar yadda na taɓa gaya miki. A lokacin nan mutane suna matuƙar sonsa, duk da ba wani babba bane ba, kuma naga take-taken ana kiransa ya fito takarar kujerar da nake hari. Na shiga na fita da wasu mutane, sai da suka fita suka bar mana jam'iyyar, duk da a lokacin ba wani mayar da hankali yake a kan siyasar sosai ba, gidansu yan kasuwa ne, shi ne yake taɓa siyasa. Bayan sun bar jam'iyyar, aka bani takara, shi ma jam'iyyar da ya koma, suka bashi takara, nayi ta bita da ƙullin siyasa, da yi masa yarfe kala-kala. Ni da yan jam'iyyar mu, kasancewar muke da mulki a sama, muka shiga muka fita, aka murɗe zaɓen, ya ce shi ba zai kai ƙara ba, jam'iyyarsa suka kai ƙara, amma duk aka kori ƙarar, duk da haka mutane suka so yi mini bore, shi suke so. Na haɗa kai da shugabannin jam'iyyarmu, muka kunno masa wuta ta sama, EFCC suka zo har gida suka kama shi, aka yi seazing ɗin wasu kadarorinsa, da zimmar ya mallake su ba bisa ƙa'ida ba. Kasancewar ba shi da manyan iyayen gida, bai iya shige-shige da neman wurin zama da biyayya a wurin manya na wannan lokacin ba, ya sanya sai da aka tsare shi a prison, ana binciken sa, bayan an sake shi duk da haka aka ƙwace masa kadarori. A lokacin mahaifinsa ya ce, baya son sa da harkar siyasa, ko zai yi ya bari sai bayan ransa, sai ya cigaba da kasuwancinsa, kuma bai taɓa ce mini uffan ba, sai bayan rasuwar mahaifinsa ya dawo yake taɓa harkar siyasa, har aka yi masa muƙamin nan, ashe ya ƙwafe wannan abun a ransa, so yake sai ya ɗauki fansa ta ƙarfin tsiya yanzu" Naja ta ce "Taɓ, gaskiya kana ruwa indabo" "Ban gane ina ruwa ba?" "Au muna ruwa zan ce? Wannan rigimar ai ban san lokacin da aka yi ta ba, balle ace da ni aka ƙulla a nemi mafita, a kanka yake neman fansarsa, dan haka ni kar a saka ni a ciki ba zai yiwu ba, haka kurum ana nema ayi mini tsirara a idon duniya" "Naja" "Na'am" "Haka ki ka ce? Kin san bana tafiya da butulu?" "Babu in da nayi maka butulci, na bauta maka da ƙarfina da gangar jikina, abun da nake yi ba butulci bane, iya ruwa ne fidda kai" Ya jinjina kai ya ce, "Haka ne, na fahimta" *** Abdul ne a zaune, ya zubawa ramma ido, tamkar mahaukaciya, gaba ɗaya ta burkice masa, idanunta sun yi jawur saboda kuka, yana kallonta rabonta da abinci tun jiya, muryarta duk ta dashe saboda kuka, ya ma rasa ya zai yi mata, yayi tsawar ya zare idon, amma duk a banza. Ya kaɗa ya raya taƙi cin abinci. "Rahama" ta ɗago ta kalleshi kamar wata dodanniya. "Me ki ke so?" "Ka duba ni, wallahi ba zan zauna da cikin shege ba, idan shi ne ka cire mini, ka mayar da ni gaban uwata, na gaji da yi maka biyayya baka da niyyar cika alƙawarin da kayi mini, ban sani ba ko sai ka cika alƙawarin ka na kasheni sannan hankalinka zai kwanta". "Yanzu da kanki ki ke cewa a zubar da ciki? Alhalin lokacin da tsautsayin nan ya faru, mun nemi a zubar a rufe maganar amma ku ka ƙi" Kamar ta ɗura masa ashar ta ce "Wancan idan tsautsayi ne wannan fa? Wallahi Abdul zan kashe kaina in huta, na gaji" Ya ce "Is ok, shikenan yanzu ko cikin ne babu lallai na gani, ki bari zan tafi da ke asibiti na yi miki gwaje-gwaje sosai, amma sai kin yadda kin yi wanka kin ci abinci" Cikin rashin wayo ta jinjina kai, ya lallaɓata da kyar, ta yi wanka, ya dafa tea da indomie ya bata, sai dai tana gama ci, ta hau amai. Ya ce "Kin gani, ulcer ta kama ki, daga jiya zuwa yau da baki ci abinci ba, shiyasa kina cin abincin ki ka yi amai" Cikin kuka ramma ta ce "Wallahi ciki ne da ni, ni bani da wata ulcer " "In ji wa? Ulcer ai tana saka amai, baki ga nima yadda take yi mini ba ne? Ai rashin cin abincin ne ya janyo haka, kuma idan ki ka cigaba da ƙin cin abincin tumbinki ne zai ta rarakewa, komai ki ka ci sai kin yi amai". "Dan Allah da gaske kake, ulcer ba ciki ba?" "Zan yi miki ƙarya ne?" Yayi maganar yana tsuke fuska. "To ka rantse da Allah" "Ba zan rantse ba, ina likita zan yi miki ƙarya ne? Kuma kan nayi miki allura ban gaya miki allurar tsarin iyali na iya ɗauke miki al'ada ba, tun da artificial homones ne aka saka a jikinki ba?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh ka gaya mini" "Amma shi ne ki ke ta yi mini wannan borin ko rahama, ni ko?" "Da ka san me nake ji a zuciyata da baka ce ina yi maka bori ba, na gaya maka mamana mu biyu ne da ita, yayanmu ma ya mutu, ya za ayi hankalinta ya kwanta ina nan? Kalli tsawon lokacin da na ɗauka ban ganta ba, ka tausaya mini mana" Ya saka hannu yana share mata hawaye ya ce "Zan mayar da ke rahama, sonake sai na sanar da mahaifina komai tukuna, bana son sunanki ya ɓaci kamar yadda ki ke ta iƙrari" "Ɓacin suna na nawa kuma? Ai ya riga ya ɓaci" "Zan gyara shi da yardar Allah babyna" Sai da yayi ajiyar zuciya da yaga ta ɗan nutsu har ta ɗan saduda, sai da ta samu bacci, sannan ya tashi ya fita, ya kira saif a waya ya ce masa su haɗu. *** A harabar gida Nabila ta tarar da Nasir, tana gama parking ya fito daga cikin tasa motar ya tareta ya ce "Daga ina ki ke?" Kamar ta wanka masa mari, a hasale ta kalleshi ta yi shiru. "Ina magana kin tsare ni da ido" "Iska na fita sha" "Wa ki ka gaya wa, sai Abba ya dawo yayi ta faɗa ko? Kuma wace irin shan iska ne zaki fita ki yi nisa da gida, kukan me ki ke yi ma?" "Dan girman Allah ka ƙyale ni" tayi maganar cikin sauti mai ƙarfi, ta nufi cikin gida da sauri, kamar mahaukaciya sabon kamu. Ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofa ta wulwula jakar hannunta tayi jifa da ita, ta samu wuri ta zauna ta dafe kanta, da take jin tamkar zai rabe biyu. "Ya haiyyu ya ƙaiyyum, ya zuljalalu wal ikram" take ta maimaitawa, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi. Viper ya ƙular da ita, amma tafi jin haushin kanta, da ta iya buɗe baki, ta furta tana son shi, a da ko me za ayi mata, ko da wasa ba ta taɓa sakawa a ranta zata iya furtawa wani tana son shi ba. To saurayi ya ce yana sonta ma, wahalar da shi take yi, ko da tana sonsa, saboda ta ja ajinta, amma wai yau ita ta furtawa wani so, kuma yayi rejecting ɗin ta kai tsaye. Viper yana da qualities ɗin da ya cancanci a so shi,  ba ta taɓa zaton wasan da take yi zai zama gaskiya ba, dan ita da fari tsokanarsa kawai take yi, sai kuma matsanancin tausayin sa sa take ji, gashi tausayi ya juye ya koma mata soyayya shi kuma baya ta tata, ga wannan tsohon ciwon nata da ta fama. Zuwa yaushe Abba zai fuskanci gurbin ido ba ido bane ba, duk wani abu da ya faru a baya, bata san an yi shi ba, ba ta san maman nata ba dama wannan an tabattar mata da bata raye, to mahaifinta fa, komai lalacewarsa zata so ta ga abun ta, kuma komai ya yi wa mahaifiyarta, wani abu ne da ya wuce a baya, da ba ta nan ma aka yi shi, to na menene za a gadar mata da wani abu da ba shi da tushe balle cikakkiyar makama. Ta zabura ta tashi, ta watso drower littatafanta, ta ɗaukko hotunan mahaifiyarta, cikakkiyar bafulatanar yarinya ce ba wata babba ba, fara sol da ita mai dogon hanci, tayi ɗauri irin na mutanen da, ta zubo da dogon gashinta ta ƙarƙashin ɗan kwalinta, har ka kafaɗarta, dukkanin hotunan uku, fuskarta ɗauke da murmushi daga yanayin hotunan zaka fahimci ba ta da hayaniya, kuma mai yawan murmushi ce. Ta daɗe tana kallon hotunan tana kuka, ta gaji ta kwanta a kan gado, sai ajiyar zuciya take yi. Washegari da safe, ta shirya zata tafi wurin aiki, ta shiga wurin Abba ta gaishe shi, amma ya shareta yaƙi amsawa, sai gajiya tayi, ta tashi ta fita. Ko da taje wurin aikin ma, kanta ta kifa a kan teburin office ɗin ta. Barrister Habib har yayi knocking ya shigo, ba ta sani ba, sai da ya daki teburin, sannan ta ɗago. "Nabila ya dai? Na ji program ɗin ki ya ɗau hankalin mutane, ki zo a mayar da hankali wurin neman shaidu, kin shigo kuma kin zo nan kina bacci" Tayi shiru ba ta ce Komai ba. "Wai meyafaru ne?" "Ba na jin daɗi ne" "Yasalam, sannu kuma kika fito? Kina da tiral ne yau?" "A'a, na zo ne dama mu cigaba da aikin shari'ar nan, ai na sha magani, bari na biyoka office ɗin" Tare suke aikin, amma sam hankalinta baya kan aikin, ƙarshe ya ce, su bari sai ta samu sauƙi tukuna. *** A wani wurin cin abinci saifu suka haɗu da Abdul, suka zaune saifu ya ce "Mutumina harkar siyasar nan duk ta ɓoye mana kai, wurin chilling ɗin ma duk ka daina zuwa. Hafsa ta ce tana son ta zo ta ganka, na ce ko ta je asibiti baka zama, ayyuka sun yi maka yawa, asibitin ma ba wani zama kake yi ba" Yayi murmushin ƙarfin hali ya ce "Ya jikin nata?" "Da sauƙi sosai Alhamdilillah, likitanta ma sun sallameta, sun ce ta warke, ina ga wani abun ne yake damunta, ta ce kafi dubata sosai, na rasa wani siddabarun kake yi wa patient suke liƙe maka" "Saif, mu bar wannan maganar, akwai damuwa fa" "Ta me?" "Haryanzu babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi kuma ta matsa mini, kullum cikin kuka take" Saifu ya ce "Ai fa Abdul ka yi mugun ganganci abun da ka aikata, ka mayar da ita wurin iyayenta, tun kafin asirinka ya tonu, sunanka ya ɓaci" "Saif, ni fa ba ta sunana ya ɓaci nake yi ko akasin haka ba, ni wallahi burina kawai na cigaba da ratuwata da ita, wani irin abu nake ji a kanta, da rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne" "Kai Abdul, ba ka gama ɗibar abun da kake so ba, ko haryanzu bai isheka ba?" "Ba wannan nake yi wa ba, ita nake so, tun bayan da na ɗaukota take bani tausayi, ka san ban taɓa raping ba, sai a kanta, wallahi son rahama nake yi, so mai tsanani". Cikin mamaki Abdul ya ce "Taɓɗijan, aurenka ne fa yake gabatowa, yanzu yaya kenan, gashi ana ta fitina a kan ainihin wanda ya yi mata fyaɗen, wata lauya ta kafe, sai an fito da ita ta bayar da shaida a kotu. Ina ga fa dolenka ka gaya wa mahaifinka gaskiya, ya ɗauki matakin da yakamata a rufe abun nan". "Ina son gaya masa, amma ina tsoron abun da zai iya yi, ba zai ɗauki maganar da sauƙi ba" "To ai kuwa ko da yaya zai ɗauki maganar, haka ne kawai mafitar" Abdul ya yi shiru yana zancen zuci. *** Viper yana zaune, ya tsurawa hoton jauhar ido, yana hararo kamannin Nabila a cikin kansa. Walid ya dafa shi, ya ɗaga kai ya kalle shi. "Ya ake ciki ne? Mutuniyar kwana biyu, yakamata ace fa shirye-shirye sun yi nisa a kan shari'ar ka, ta ina za a fara?" Viper ya ce "Fushi take yi " Walid ya ce "Fushin me? Wani abun ya faru ne?" Ya girgiza kai ya ce "Akwai magana a bakinta da yakamata na saurara, wataƙila zai haska mini abun da kake gaya mini, sai dai ta bijiro da abun da dole na taka mata burki" "Wane abu ne?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Bakomai" "Mai zamani, yakamata ka din ga bin komai a sannu, mata fa dukkansu ba irin jauhar bane, jauhar one in million ce, ba kowace mace ce zata iya juriyar da ta yi ba, kar ka yi treating ɗin Nabila yadda kake treating ɗin Jauhar, suna da banbanci" Yayi shiru, ya cigaba da kallon hoton hannunsa. "Allah ya jaddada rahama a gareki, ya kyautata makwancinki my wife " yayi maganar yana shafa haƙoranta na jikin hoton da yake da shi da ita ne, fuskarsa da ƙuruciya sosai lokacin. Walid ya ce "Amin" ya karɓe hoton, ya ajiye shi a wani wurin. Yayi shiru yana tunanin ko me Nabila take son ta gaya masa? Ko yanzu tana wani hali? Da gaske son shi take yi, ko kuwa dai still da wasa take yi? Kukan da tayi ya tabattar mata ba wasa take yi ba. To su mata babu wuya sun fara son mutum kenan? Ya ga damuwa sosai da sosai a cikin idanunta da suka haɗu, ya so ya ji menene damuwarta, amma ta zo da lamari mai girman gaske, son da take yi masa wahalar da kanta kawai zata yi, yana cikin wannan halin na ɓoye-ɓoye, idan ta fara son shi yaya zata yi, tun da ba aurenta zai yi ba, kuma shi ba ma wannan ne a gabansa ba gaba ɗaya. *** Kusan kwanaki huɗu, amma Abba baya saurar Nabila, fushi yake yi da ita sosai, gajiya tayi da fushin da yake yi da ita, ga habaici da yar da magana da ake yi mata a gidan. Ta shirya tafiya aiki, ta shiga ɗakinsa, ya na karyawa. "Abba ina kwana" yayi mata shiru ya cigaba da karyawa. Ta tashi ta je gabansa ta zauna cikin kuka ta ce "Dan Allah Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, in sha Allah ba zan sake maganar babana ba, idan raina ne ya ɓaci aka yi mini gori, duk sai na ji babu daɗi amma dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini ba zan sake ba" da fari yayi mata shiru, amma daga baya ya numfasa ya shafa kanta ya ce "Kukan ya isa haka, na ji na yafe miki, duk da kin sha yi mini wannan alƙawarin amma ba kya cikawa, yau da mahaifinki wani abun kirki ya tsinanawa mahaifiyarki, rabuwar arziki aka yi, babu yadda za ayi na nesanta ki da shi har haka, na yanke duk wata alaƙa tsakaninki da shi. Ki yi haƙuri na san kina haƙuri da abun da ake yi miki, da zarar kin yi aure shikenan kin wuce wurin, ki yi haƙuri ki cire maganar mahaifinki a zuciyarki" Nabila ta jinjina kai, amma ƙasan zuciyarta ba ta ji zata iya daina maganar mahaifinta ba. Ta tashi ta fita ta tafi aiki, ita ma ta fita daga harkar Nasir gaba ɗaya. Yau ba ta da shari'ar da zata halatta, dan haka tana office tana ta nazarin shaidunta, da za su yi appeal. Wayarta ce tayi vibrating, ta ɗaga ta duba "Mu haɗu a restaurant ɗin da ki ka je, zamu yi magana mai muhimmanci" ta zubawa wayar ido tana kallonta, ta ajiye wayar. Har mamakin kanta take yi, yadda take abu babu tsoro take wannan kasadar haka. Ta ajiye wayar ta kifa kanta, can ta miƙe, ta tattara system ɗin ta da kayanta, ta tashi ta fito, suka yi karo da barrister Habib. Ya ce "Yauwwa wurinki zan zo dama, ina son mu je unguwar da abun nan ya faru ne, ko da wani abu da zamu kuma samu, da bamu haske a kan shari'ar" Ta ce "Amm ganin likita zan je ne, ko mu bari sai gobe in Allah ya kaimu?" Ya ce "Subhanallah, jikin ne dai?" "A'a ba wani abun damuwa ne sosai ba, zan dai je na ga likita ne, yau yakamata na koma dama" "Ok, to Allah ya ƙara afuwa" Ta amsa da Amin. Ta je wurin cin abincin, ta kira wayarsa ya ɗaga. "Gani na zo ina wurin" "Ki miƙe sosai ciki, ki tambayi Vip 2" ta ƙarasa ta tambaya, aka nuna mata, ta buɗe ta shiga. Yana zaune, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana sanye da facemask da facing cap ya rufe fuskarsa. Fuskarta babu annuri, ta ƙarasa ta ja kujera ta zauna, ta ajiye jakarta da wayarta, da mukullin motarta, amma ba ta ce komai ba. A yanayin yadda ta tafi wancan karon, bai zaci da ya ce ta zo zata kuma zuwa ba. Tayi masa shiru, tana danna ƙaramar wayarta. Ya ɗan daki teburin ya ce "Attention, magana zamu yi" Ta ajiye wayar ta ce "Ina ji" Ya ja babbar wayarta, ya buɗe ya ɗaukko tab ɗin sa, ya fara daddanawa. Mai kawo abinci yayi knocking, ya kawo ruwa da lemo. Ya sauke facemask ɗin sa ya ce "Yaya ake ciki da maganar wancan case ɗin, zuwa yaushe zaku yi appeal ɗin? Sonake ki kammala da wancan shari'ar, sannan ki mayar da hankali a kan tawa, already ina da shaidu guda biyu a ƙasa" har yayi maganar ya gama, bata ɗago ta kalleshi ba, wasa kawai take yi da zobunan hannunta. "Magana fa nake yi" "Ina ji ai" "Ba jin nake buƙata ba, hankalinki zaki bani" iya idanunta ta ɗaga ta kalleshi tana yi masa wani irin kallo. "Ina magana a kan yaushe zaki yi appeal, ki zo ki fara processing tawa, ina da shaidu biyu a ƙasa" still ba ta ce komai ba ta cigaba da kallonsa. Zubawa sarautar Allah ido yayi, ya saka mata nasa idon shi ma, ta gyara zamanta, ta kwantar da hannunta a kan teburin, ta ɗora kanta ta kwanta ta yi masa shiru. Ƙasa yayi da muryarsa ya ɗan matsa ya ce "Meyake damunki ne?" Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru, tayi iya yin ta, ta ɗago ta share hawayenta ta ɗauki jakarta, ta ɗauke wayarta daga gabansa, ta juya za ta fita. "Ina miki magana zaki tafi? Ina zaki je ina yi miki magana?" Yayi maganar cikin tsawa da sai da ta firgita, ta ja da baya tana kuka. "Talk" yana mata tsawa tana ƙara sautin kukan nata. "Meyake damunki? Kin san haka zaki yi mini, ki ka yi mini tayin dawowa normal rayuwata? Ki ka ce zaki taimaka mini" "Ina amfanin tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani kuma yake so? Ba cewa kai baka so na ba? Rashin amsa tayina bai yi mini ciwo ba, irin halin ko in kula da ka nu na wa rayuwata, hakan na nufin duk da risk ɗin da na saka rayuwata baka damu ba ko da zan rasa rayuwata. Saboda kana ganina a haka do you know what am going through ne? To an fasa taimakon naka, i destroy the deal and i am out of it, ka je kayi duk abun da ka ga dama" Murmushi ya yi, sai da haƙoransa suka fito, abun da ba ta taɓa gani ba. "Angry bird, always angry for no reason, duk saboda na ce bana sonki, ki ke wannan abun? Ba zan taɓa sonki ba, zuciyata ta jauhar ce itakaɗai" "Ai baka burgeni ba, da aka zauna baka bi ta lahira ba" Viper ya ce "Ai nayi niyyar bin nata, ki ka hanani, wannan deal ɗin sai an kai ƙarshensa da ke" "Komai zaka yi, ba zan sake zuwa in da kake in dai ni yar halak ce, babu amfani tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani" ta raɓa shi ta wuce ta bar wurin. Ajiyar zuciya yayi, ya koma ciki ya zauna. Gida ta tafi, abun duniya duk ya dameta, tana ganin kiran sumayya, amma ta share ba ta ɗagawa, gaba ɗaya ta zama so silent. *** Abdul ne yake kallon ramma, yadda take ya shiri, ya ce wai shirin me ki ke yi haka ne? "Asibitin ka zaka tafi da ni, ni dai mu je ka duba ni na tabattar" "Rahama haryanzu tunaniki ƙarya nake yi kenan?" "To wa ya sani, tun da haryanzu ban ji na warke ba, amai yaƙi tsayawa, muje idan ma shi ne kawai ka zubar da shi" Ya girgiza kai ya ce "A'a ni ba na zubar da ciki gaskiya" Ta kalleshi sheƙeƙe ta ce "Yaushe ka fara tsoron Allah, har ka ke cewa ba ka zubar da ciki?" "Ai lokacin da zan kama aiki, rantsuwa nayi, ba zan ci amanar aikina ba" "Kai har wata darajar rantsuwa ka sani? Ni ka daina yi mini wasan kwaikwayon nan, kawai mu tafi" "Rahama mutuwa fa aka yi a wurin zubar da cikin nan" "Na ji, bakomai, Allah ya yi mini rahama". Ya sauke numfashi ya ce "Na ji, zamu je, amma wallahi ki ka takura mini ba zamu je ba, kuma kar ki dame ni" Ta haɗe rai ta ce "Zan baka nan da sati ɗaya, idan na ji shiru zan kuma magana" ta cire mayafinta, ta bar ɗakin. *** Unguwar gidan aikin ramma take son sake zuwa, kamar yadda barrister Habib ya buƙata, take ta yi masa yawo da hankali. Tana daf da shiga mota, ta tsaya tana amsa kiran waya. "Salamu alaikum, Barrister, walid ne" Ta ce "Oga walid, ya kake?" "Lafiya ƙalau, mutumin ne babu lafiya fa, ko zamu haɗu a wani wurin mu kai shi asibiti a motarki, saboda yanayin tsaro" Gabanta ya faɗi ta ce "Subhanallah, wani abun ya je ya sha?" "A'a, ai rabon da ya sha wani abu, an kwana biyu, ciwon ciki yake yi, tun yana yi sama-sama, tsakanin jiya da yau har suma yake yi" A rikice ta ce "Ya salam, a ina zamu haɗu to? Ina wurin aiki gani nan" Da gudu gudu, ta ƙarasa ta hau motar, ta ja, tana tafe tana waya da su, har suka haɗu, sun ɗaukko shi a adaidaita sahu. A sume suka saka shi a motarta, hankalinta yayi mummunan tashi ta ce "Oga walid yana numfashi?" "Eh yana yi, Suma dai yake ta yi" "Yanzu wane asibitin zamu nufa? Ka ga wancan ga matsalar da aka samu" Suka tattauna suka yanke shawarar kai shi wani asibitin daban. Asibitin shi ma a wajen gari yake, amma yayi kyau ya tsaru, ko ina tsab da shi. Nan da nan aka shiga da shi emergency, aka fara yi musu tambayoyi a kan meyasame shi. Su walid suka yi musu bayani, aka tafi da shi wurin yin scanic. Nabila ta fita da sauri, dan ta je ta ji ya tsarin Asibitin yake, da biyan kuɗin, taga ɗan mama yana ƙoƙarin komawa in da ya baro su. Ta ce "Sannu ɗan mama" Ya ce "Yauwwa, an gano meyake damun nasa?" Tayi murmushi ta ce "Suna ƙoƙarin yin hakan dai, wannan karon ma ka je ka sanar da su ne su zo su biya bills ɗin asibitin nasa?" Yayi turus yana kallonta, ya ce "Kamar yaya?" "Kamar yadda wancan karon kayi, kai ka yi waya aka biya bill ɗin Viper, dan babu wanda ya san mun je asibiti, yanke muka din ga yi, mu ƙaddara ma wani ya sani yana bibiyarmu, ana tsaka da treating ɗin sa hankalinmu yana kansa, ka zame ka fice. Kana kawo masa miyagun ƙwayoyi a duk lokacin da ya buƙata, abubuwa da yawa idan ba na kusa da shi ba babu yadda za ayi a san su, wa ka ke yi wa aiki?" Ayshercool 08081012143 68 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Ɗan mama yayi murmushi, ya ƙara taku biyu gabanta, ya kalleta ya ce "You better count yourself out of this. Ba ni da niyyar cutar da

Chapter 71 of 121