Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
95 / 121
ba, na je rigar su chubaɗo. Sai dai mummunan labarin da na iske ya kaɗa ni, wai major ya tafi da ita can in da yake, amma da ita da yaranta duk sun mutu. Ban kawo cewa 'yan biyu bane ku, na yi zaton kawai shirme ne, na mutanen karkara, mussaman su da ba hausa ce ta wadace su ba. Su ka tabbatar mini da chubaɗo ta rasu, dan maitama da kansa ya je ya sanar musu da mutuwarta. Tsananin tashin hankali ya sanya na yi hatsari a hanya, na samu karaya hannu da ƙafa, da raunuka sai da na yi jinya kamar ba zan rayu ba. Na yi kukan rashin chubaɗo, kuma na yi kuka da nadamar abin da na yi. Na bibiyi in da major yake aiki, amma duk wata kafa da zata sada ni da shi ya toshe ta, ban san adadin zuwana Jalingo ba, har a shekarun nan na je, suka ce mini tun da ya je su ka ce masa na je nemansa, har rana mai kamar ta yau bai sake zuwa ba. Waɗanda na ɗan sani a rigar ma duk sun rasu, duk aure-aure na, har yau ban samu mace kamar chubaɗo ba, ita na aura domin soyayya, uwargidana auren zumunta, ta biyu saboda aikina uwargidan da fari taƙi bi na, chubaɗo kuwa soyayya ce ta sanya na aureta". "Au to mu da ka auremu ba dan ka na sonmu ba, ai da sallamar mu ka yi tuntuni, ashe mu zaman kare a karofi mu ke yi" "Aifa tun da mu zaman 'ya'ya mu ka yi, ashe zaman larura ka ke yi da mu wadda ka ke so, zuciyarka take muradi daban" Saifu ya ce "Dan Allah mama menene haka? Duk wannan fa girmanku ba ne ba, abubuwan duk da ku ka aikata duk bai ishe ku ba?" Mama ta ce "Rufe mini baki, kafin na mangareka" Baba ya numfasa ya ce "Tabbas zaman larura, zaman 'ya'ya nake yi da ku, lokuta da dama ba na gane kaina, kawai dai rayuwa gata nan ne dai ina yi. Haka jauhar, akwai abokina sadis Allah ya jiƙansa, shi ya ankare da halin da nake ciki, duk soyayyar da nake yi wa jauhar, ba na iya kataɓus ko da za a dafata a sha romonta, ya ce yakamata na binciki rayuwata, kamar akwai abin da yake damuna. Na ce masa ni ba zan bi bokaye ba, ya ƙyale ni, ya ce mini ba bokaye ba, in nema wa kaina tsari, amma ko a jikina, ni lissafin matan da na tara, da yara yadda zan riƙe su na kula da su, shi ne kawai damuwata in nemi kuɗi. Ga kuɗin akwai su, amma ba na iya morawa jauhar, ina kallonta da yagaggen tufafi, ta na aiki kamar baiwa a cikin gidan mahaifinta amma ba na iya cewa komai. A cikin ƙannena, ɗaya da ta na cikin masu adawa da Chubaɗo, ta kwanta ciwo, na je dubata ta riƙe hannuna ta na kuka take neman afuwata, ta ce mini haushin rawar kan da nake yi a kan chubaɗo ya sanya ta haɗa kai da Maimuna, su ka yi mini asiri, da sunan chubaɗo bayan an yi mana farraƙu, aka zuba asirin a cikin toka, su ka kai cikin ruwa mai tafiya, wai yadda ruwan nan ya tafi da tokar ta ɓace, haka ya tafi da tunanin chubaɗo a kaina. Sannan su ka koma, su ka yi mini sihiri, aka binne a maƙera, yadda ake rura wuta a maƙera, haka zafin ƙiyayyar da na yi mata yake ruruwa a zuciyata duk lokacin da aka kira sunanta. Babu wani mahaluki da na sanar wannan maganar, na haɗiyeta a cikina. Na daina yawon aure-aure dan ba za a bari su zauna ba, sannan duk wadda na aura, ta na da tata kalar matsalar. Wasu abubuwan ba na sanin ana yi wa jauhar, Jauhar ba ta iya tambayata abu, ko kawo mini ƙara. Duk 'ya'yana su na rayuwa kamar yaran sarakai, pant wanda 'ya mace za ta saka, sai na saya, pad ɗin da za su yi amfani da ita ta jinin al'ada, ta na cikin budget ɗin da nake yi duk wata, amma ba na iya magantawa 'yar marainiyar yarinyar da duk cikin yarana babu wanda nake jin daɗinsa, babu mai tausayi da imaninta, amma ba na iya maganta mata komai. Ko da su ka rushe maganar auren jauhar, duƙufa na yi addu'a, haka kurum kuma na ji na karkata na aminta da aurawa jauhar Al'amin. Ko a lokacin da na amsa aura wa Alhaji mu'azzam ita, na amince ne domin ta huta ta samu nutsuwa a can, tun da ni na gaza samar mata da kwanciyar hankali a matsayina na uba, wallahi nauyin laifukan da na aikata ina jin su a tsakiyar ƙirjina Nabila, rayuwa kawai nake yi, amma babu abin da yake yi mini daɗi, mussaman idan na tuna laifukana ga chubaɗo da jauhar, na san ni mai laifi ne, ki nema mini afuwa a wurin Abbanki" Hafsa ta yi wuf ta ce "Wallahi lokacin nan, wani abu aka saka a bakin wata mage, aka binneta da ranta, wai ba zaka ce komai ba, idan aka ce a aura wa jauhar Mai zamani, da maman su saifu, da Anty. Sai kuma Anty da matar gidan su mai zamani, su ka din ga kai ni wurin wasu mutane, ana bani abubuwa wai saboda Alhaji mu'azzam ya aure ni, amma na gaya wa jauhar komai ai, kuma na ce ta yafe mini, jauhar ai na gaya miki duk yadda aka yi, ki ka ce kin yafe mini, amma kar in gaya wa kowa" tayi maganar tana kallon Nabila. Kamar ƙaramin yaro, saifu yake kuka. Zakiyya ta ce "Hafsa ki rasa wanda za ki yi wa sharri sai uwarki, a gidan uban... Maman saifu ta katseta da cewa "Uban waye bai san ki na biye-biyen bokaye ba?" "Idan ma na bi gara ni, a kan ku wanda ku ka haɗa kai ku ka yi wa chubaɗo ai" Nabila ba ta ce komai ba, ta miƙe, ta ɗauki jakarta da wayarta ta na wata irin tsuma, kafin Zakiyya ta yi yinƙurin ba wa Nabila hanya, tuni ta angijeta ta wuce. Saifu ya bi bayanta ya na kiran sunanta, Baba kuwa bai iya motsawa ba, ya dafe fuskarsa ya cigaba da zubar da hawaye. Hafsa zama tayi ta kwanta a jikinsa, ita ma ta na kukan. Zakiyya da maman saifu kuwa kamar za su dambace. Viper ya kawo kai, Nabila ta nufo barin layin, sojan da ya kawota ya biyo ta ya na yi mata magana, amma kamar ta kurmance. Shan gabanta Viper ya yi ya na tambayarta meyafaru. Saifu ne ya nufosu, Viper ya riƙe hannun Nabila. Saifu ya tsaya nesa kaɗan ya na kallon Viper, ya kalli Nabila ya kalli saifu, bai ce komai ba ya ce wa sojan ya ƙaraso da motar su tafi. Babu gardama ta shiga motar, sun fara tafiya ta ce "Wurin Abba za ka kai ni" "Meyasa? Meyasa ma ki ka zo ba tare da kin sanar da ni ba?" Shiru ta yi masa, yanayinta kamar na mai shirin fita hayyacinta. Tsaki ta ja ta ce "Dan Allah ni kawai ka kai ni wurin Abba kawai". "Amma kin san halin da ake ciki ko? Ya za ayi a mayar da ke gida a wannan yanayin?" Cikin kuka ta ce "Ni wurin Abba kawai zan tafi, ji nake ma kamar haukacewa zan yi" Gaba ɗaya tausayi Nabila ta bawa Viper, ya ce "Me za ki je ki yi masa ne?" Ya gyara zamanta ta dube shi ta ce "Viper, shekara ɗai ɗai ɗai shekara ashirin da shida mutum ya na yawon asiri, could you imagine wai asiri aka yi wa baba ya manta da mahaifiyarmu, aka zo ta mutu aka koma kan jauhar, wai abin har da ƙanwarsa kai, jauhar ta yi haƙuri Allah ya sa ta na aljanna, wallahi da ni ce idan ban haukace ba, guduwa zan yi na bar gidan, ko ma na tsani baban namu, ina kallon ka na wahaltawa 'yan uwana amma ni ka tsane ni, Allah sarki manana da 'yar uwata, wallahi kamar haukacewa zan yi Vi, ni kowa ma ya kasa fahimtar halin da nake ciki" tayi maganar ta na kuka ta kasa zama wuri ɗaya. "Kin ga zauna sosai, ai na san me ki ke ji, ni ma ina ji ai" Ta na kuka ta girgiza masa kai ta ce "A'a ba ka ji" "Ina ji mana, ai na fiki sanin jauhar da wacece ita" "Har da matar gidanku wai aka yi asiri, a kan baba ya amince jauhar ta aure ka" Ya ce "Na sani" "To ita meya kawo ta cikin wannan maganar matar gidan naku?" "Ƙawar babar hafsa ce" ya ba ta amsa. Ta marairaice fuska ta ce "Dan Allah abubuwan nan ba su yi mini yawa ba? Gaba ɗaya na rasa me ma zan ce, ta ina zan yi wa major wannan bayanin, ba ma zai saurare ni ba, amma baba abin tausayi ne, gaba ɗaya matan nan sun raina shi, ba su da kirki kai wayyo Allana ni na Nabila, da ma tun ina jaririya tamowar ta kashe ni kowa ya huta" Sai da Viper ya ji kamar ya yi dariya, amma ya gimtse, tabbas Nabila ta na namijin ƙoƙari jaruma ce ta gasken gaske. Kamar yadda ta buƙata, gidan major ya kaita, duk da ya san ya saɓa doka, amma ta na buƙatar yin abin da zai sakata nutsuwa. Mamaki ne ya cika 'yan gidan, ganin Nabila a gidan. "Me kuma ya kawo ki gidan nan?" Ba ta saurare su ba, ta nufi ɗakinta, wasu daga kayan Sauda ta gani a ɗakin, har an gaje mata ɗakin. Kamar mahaukaciya, ta fara watso kayan waje ta na huci. "Ke Nabila wai meye haka ne? Ba an ce kin gano ubanki ba, uban me ya dawo da ke gidan nan kuma? Ko ba kin zaɓi wasu daban a kan shi wanda ya yi wahala da ke ba ne?" Mama tayi maganar ta na haƙiƙancewa. Baba magajiya ce ta shigo da sauri, ta rungume Nabila cikin farinciki. Nabila ta ce "Baba magajiya, finally na ga abbana, sai dai 'yar biyuna Allah ya yi mata rasuwa" Baba magajiya ta ce "Alhamdilillah, Allah ya ƙara tabattar da nasara" "Ki zo ki fice daga gidan nan, kin tafi mun huta, kin sake dawowa ki koma gidan ubanki mu ma mu sakata da mu huta da yaranmu" Nabila ta ce "Ai ni da ke samamkal, duk ba gidan ubanmu ba ne ba, har gara ni na da ke" Mama ta ce dole sai Nabila ta bar gidan, tun kan Major ma ya dawo ya ganta. Baba magajiya ta ce "Da dai kun yi haƙuri ya dawo ɗin, tun da babu wanda ya san abin da ya dawo da ita". Sauda ta ce "Ki rufewa mutane baki, 'yar karere kawai, ke ma kamata yayi ai ki tattara komatsanki ki bar mana gida, tun da amfaninki ya ƙare" Sosai faɗa ya kacame, Nabila ko a jikinta, ta gyara ɗakinta tas, ta nemi mukullin motarta ta rasa, kai tsaye sashen Abba ta nufa, ta nemo mukullin motarsa ɗaya, ta fito. Duk yadda su ka yi ƙoƙarin hanata ɗaukar motar su ka kasa, saboda yadda su ka lura da fuskarta babu mutunci. Gidan Gonar Major ta nufa, ta na ta zabga addu'a domin ta yi nasara a kansa ta samu ya saurareta, dai dai su ka yi saɓani, domin kuwa baya nan. Su na tsaye su na ta mayar da yadda aka yi, su ka saka baba magajiya a tsakiya, su na kiranta da munafuka. Cikin rashin jin dadi Walida ta ce "Bai kamata ba baba magajiya fa dattijuwa ce, kuma ba ta san komai ba" "Dalla rufe wa mutane bakinki a wurin" Sallamar Major ce ta sanya su ka yi shiru. "Meyafaru ake waye munafuki menene?" Cike da ƙwarin gwiwa mama ta ce "Wai Nabila ce ta dawo gidan nan" Ya ce "To sai aka yi yaya?" "Ai abin ne da mamaki, duk dambarwar da aka yi babu kunya ta dawo gidan nan, motarka fa t ɗauka ta fita, ni dai na ce bar gidan nan kafin ma ka dawo ka tarar da ita". Ya kalli mama da ta haƙiƙance, ya ce "Saboda tare mu ka haɗa kuɗi mu ka gina gidan?" Turus ta yi ta na kallonsa. "Ina ruwanku da ita?" Sauda ta ce "Amma Abba, abubuwan da ta yi maka fa, kuma kai ka ce kar ta dawo maka gida, muddin ba ta yi abin da ka ce ba... "Ni na gaya miki haka? Idan ma hakan ne na naɗa wani wakili a cikinku ne da na ce idan ba na nan a yanke hukunci makamancin wannan?" Su ka yi tsuru-tsuru. "Duk in da za ta je ta san ba ta da kamar nan, ciki har da gidan uban na ta, ni nake da ikon sallamarta ko na ƙyaleta a gidan nan, duk in da za ta je ta dawo, babu ruwanku da ita" Sauda ta ce "Amma Abba ta ɗauki motarka" "Eh ta wace ai, ba wani abu" yayi maganar dai-dai lokacin da Nabila ta shigo. Su ka yi kallon kallo da Abba, ya wuce ya nufi ɗakinsa, bin bayansa ta yi ta na kiran sunansa, amma ya yi mata shiru. Sai da ta dangana har bedroom ɗin sa, wanda a nan ya tsaya, ya juyo ya kalleta bai ce komai ba. "Abba" ya kalleta. "Abba dan Allah ka yi mini magana mana, ko zan samu ƙwarin gwiwar sanar maka da abin da na zo maka da shi. "Kin gama fushin kenan?" "Abba ka fahimce ni, ka yi mini uzuri dan Allah. Na kasa sarrafa zuciyata ne a wannan lokacin, ka yi mini uzuri ni ma 'yar uwata na rasa. Na je wurin baba mun yi magana ne, dan Allah Abba. "Stop it please, in dai maganar mahaifinki ce ba na son jin komai menene, sannan ki je ki cigaba da kare wanda ya kashe 'yar uwakki saboda rashin kishin kai". "Abba ba shi ya kasheta ba... "Ba shi ya kasheta ba ke ce kenan? Azzalumin mutumin nan, bayan kashe mini 'yar uwa, yar da ta bar masa ma, ya kasa riƙeta babu abin da za ki gaya mini a kan mahaifinki na yarda Nabila, Kodayake laifina ne, da na kai masa ita, ni dama ke na kai". Jiki a sanyaye ta ce "Abba... "Get out Nabila, ba na son ganinki ma, fita ki bani wuri" ta haɗiye wani abu mai mugun ɗaci, ta fice daga ɗakin nasa. Ɗakinta ta tafi, kawai ta nemi wuri ta kwanta, baba magajiya ta kawo mata abinci, amma ta ce ba zata ci ba. Washegari da sassafe, Viper ya isa ƙofar gidan su Nabila, ya tsaya ya na kiran wayarta, Nasir ya fito da motarsa. Bai kula shi ba ya ci gaba da kiran Nabila, ta ɗaga ya ce "Ina waje" mintuna kaɗan ta fito cikin shirinta na fita aiki. "Ina kwana" "Lafiya ƙalau, ba wata matsala dai ko?" "Akwai mana, meyasa za ka tambayeni, kai ma ka san akwai muje kawai" Wani irin azababben kishi, ya turnuƙe Nasir, ya fito daga motarsa ya tunkaro su. "Nabila, ki na nufin kin fifita son zuciyarki a kan abin da Abba ya gaya miki?" Nabila ta ce "Mu ƙaddara haka ne, meye naka a ciki?" "Mutumin da ya kashe 'yar uwakki, haryanzu ki na kan bakanki na kare shi kenan?" "Kai ma da ka samu dama, kashenin za ka yi, domin cikar naka muradin. Yaya Nasir kallonka kawai nake yi, kuɗin da aka baka domin ka kama shi, wasa da rayuwata da ake yi, ba tare da ka sanar mini ba, ko ƙoƙarin bani wata cikakkiyar kariya ba, duk fa kallonka nake yi" saroro ya yi ya na kallon Nabila. Viper ya riƙe gefen kwalar Nasir, ya risunar da muryarsa ya ce "Kar ka manta, ni ba karabutin ɗan daba bane kawai, hatta evidence na kuɗin da aka baka, ina da shi. Dan haka ka ajiye kishi a gefe sauran mutuncin da ka ke da shi a idonta ya zube. Nabila ta wa ce, ko da kuwa ita ma zan kashetan ne" Nasir ya kalli idon Viper, Viper ya kalle shi. "Na fi ka gwagwarmaya da ganin wahalar rayuwa, dan haka ba wani zare ido, da wani abu makamancin haka da zaka yi mini da zai tsorata ni. Ka daina shiga harkata dan ka ganni tare da ita, idan ka ci gaba kuma abin da zai biyo baya ba zai yi mana daɗi ba". Tsagwaron kishi ne yake damun Nasir, kamar zuciyarsa zata tarwatse haka ya na kallonsu, suka hau mota su ka tafi. *** Abbu ya na zaune ya na ta lissafi na shekara, nawa zai fid da zakka da sauransu. Hankalinsa ya yi zurfi sosai a tunanin. Rahila na gefe ta na ta yi wa shahida masifar, an raba auren su, ta dawo gida su na haɗa kafaɗa. Shahida ta ce "Auren da da shi, gara babu, ni wallahi ba na dana sani". "Ai dama ba zaki yi ba, nan gaba za ki fahimci abin da nake gaya miki" Wayar Abbu ce ta fara ringing, sai da ta yi sau kusan uku, sannan ya ɗaga. Jin muryar babban mutum ya sanya ya nutsu, su ka gaisa. "Daga nan hedkwatar hukumar hisba ne, mun kamo 'yarka a cikin sabon gari, shekranjiya da daddare, kuma a binciken da aka yi, an gano ta na ɗauke da juna biyu, kuma ga cutar ƙanjamau, dan haka mu na buƙatar ka zo mu na son ganinka" Abbu ya ce "Ba ni ne mahaifinta ba, ta baku lambar babanta ba ni ba ne ba" ya gama wayar, Rahila ta ce "Na ji ana maganar hisba, ka ce ba kai ne babanta ba" Ya ce "Eh, 'yar ki da ki ka ce mini ta na gidanku, ita aka gano a sabon gari, da ciki da kuma ƙanjamau, dan haka na ce a nemi mahaifinta ba ni na haifate ba" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace, ciki da ƙanjamau kuma? Wayyo Allana" Tashi ya yi ya fice ya bar mata falon. *** Garden ɗin da suke haɗuwa da Nabila a da, can su ka tafi. Ta kalle shi ta ce "Meyasa ka kawo ni nan" "Ina jin nishaɗi idan na zo irin wurin nan, sannan wuri ne mai sanya nutsuwa, ki ɗan huta kawai" wani irin daɗi ne ya ratsa Nabila, ganin yadda ya nuna damuwarsa a kanta ƙarara, sai dai ta basar da ta tuna alƙawarin da ta ɗauka. Hannunsa riƙe da leda su ka ƙarasa cikin garden ɗin, ta zauna ƙamshin furannin wurin na ratsata, haka kurum ta ji zuciyarta na narkewa da ƙaunar mijin 'yar uwatta ta, da take ganin kamar ba ta kyauta ba cin amana ne yin hakan. "Vi" "Abla" "Abba yaƙi fahimta ta, ya kore ni, ya ce muddin ina son zaman lafiya, to sai na bar shari'arka, na rabu da mahaifina". Viper ya gyaɗa kai ya ce "Ya ɗauki zafi da yawa ne, amma zai saukko, ba ya bari kin kwana a gidan ba?" "Eh, jiya da na dawo ma na tarar ya na faɗan babu ruwansu da ni, ina ga so su ka yi ya kore ni ma, duk sun gaje mini kaya, har da motata" Ya ce"Sorry" Ta numfasa ta ce "Ka na addu'a kuwa, a kan Allah ya bamu sa'a?" Ya ce "Eh, ina yi" "Masha Allah, amma fa dole mu ƙara, kuma ka yi haƙuri dole za mu yi exposing wasu abubuwan da ka yi a kotu" Ya ce "Kamar yaya? Ba dai aikina ba?" Tayi murmushi ta ce "Ba wannan ba, rashin jin da ka yi, da alaƙarka da indabo, ka san babban kuskuren da ka yi? Biye wa Nura guduma da ɓoyewa likitoci ainihin abin da ya same shi. Da sun yi documenting hakan zai bamu ƙwarin gwiwa da cikakkiyar hujjar dalilin da ya sanya rigima tsakaninka da Indabo. Yanzu dole abin ɓoye ya fito fili, muddin lakwari ya kuma denying kashe jauhar, shaidar ɗan mama kaɗai ta yi rauni, dole duniya ta san da videon nan". "Ki na nufin Videon Nura? No ba zai yiwu ba, cin amana kenan da karya alƙawari". Ayshercool 08081012143 90 Ta girgiza kai ta ce "Ba ina nufin lallai sai videon ya fita ba ne ba, ka fahimce ni. Indabo sun san me muke shirin yi, ba fa za su ƙyale mu ba, bar ganin hankalinsa ya na kan ɗan sa da kuma tuhumar da ake yi masa, ya na da muƙarrabansa, ya na da iyayen gidansa da waɗanda siyasarsu ta dogara da shi, ba za su taɓa zuba ido su na kallonmu ba. Duk wani tanadi da shiri da yakamata mu yi, dole mu yi shi, ko da kuwa ya na nufin faɗar abubuwan da ka aikata. Dan ba kowa ne zai ɗauki cewar akwai wata alaƙa tsakanin ɗan daba da mutum kamar sanata ba, har ta kai ga ya kashe maka mata ba. Dole sai mun shirya da shaidu da hujjoji fa, ba da ƙanan lauyoyi zan kara ba, na sani manyan lauyoyi ne iyayena a harkar aiki, muddin aka kai ga gaɓar da sunan Indabo zai fito a cikin shari'ar nan. To fa tsuguno ba ta ƙare ba, dan  haka kurum su lakwari ba za su kashe maka mata ba, kuma dole za su yi ƙoƙarin kare kansu, ko mu bamu faɗa ba, su za su iya faɗar wasu abubuwan da suke da alaƙa da ka yi daba da kuma dillancin miyagun ƙwayoyi, wanda laifi ne ga dokar ƙasa, da za na iya fuskantar tuhuma" Viper ya yi shiru jikinsa a sanyaye ya ce "Da sauran rina a kaba kenan? haryanzu ban gama karɓar sakamon laifukana ba kenan" yayi maganar cikin damuwa ya na ɗan murza zoben hannunsa. Cikin kulawa da matsanancin tausayin sa ta ce "In sha Allah komai zai warware, ai babu abin da ya fi ƙarfin Allah, kuma shi mu ke gaya wa. In sha Allah abubuwan da su ka faru, kaffarar laifukan ka ne, in sha Allah sai an tuhumi indabo a kan mutuwar jauhar, muddin sunan sa ya fito a kotu, to shi ma za mu yi ƙararsa ne, fatana Allah ya bamu nasara" yayi shiru ya na tunani. "Vi" ta kira shi a hankali. Ya ɗaga kai ya kalleta amma bai yi magana ba. "Ka ce wani abu mana" "I have nothing to say" "Idan ka karaya ni fa? Dan Allah ko yaya na ga alamar ƙwarin gwiwa a tare da kai mana, kar ka saka na karaya mana Please" ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Duk mai nema, dole ya sanya rai a samu ko rashi, duk wanda ya riske ni, zan karɓa da murna na gode wa Allah" "Duk da haka, yakamata bawa ya kyautatawa Allah zato, burina ɗaya tak ya rage a duniya da nake fatan cika shi, shi ne ƙwato muku hakkinku, da kai da jauhar, ko da hakan ya na nufin ƙarshen rayuwata. Ina ta gudanar da bincike na a ɓoye, ina tattara bayanai, hatta report ɗin likitoci a kan mutuwar ta, ina processing na karɓa. Alhaji mu'azzam ya na taimaka mini sosai da sosai" Nan da nan annurin fuskar sa ya ɗauke, rai a ɓace ya ce "Shi kuma me ya kawo shi cikin wannan maganar?" "Komai ma mana, ka san abubuwa da yawa ban da taimakon Allah, ya sanya ya na tare da mu ya na taimaka mana, da tuni an kaimu ƙasa an ga bayanmu, bawan Allah nan ya cancanci yabo wallahi" banza ya yi mata yaƙi yi mata magana. "Ni idan Allah ya sa aka kammala shari'ar nan, lallaɓawa zan yi na yi aure, su Baba idan za su shirya da major to, idan sun ƙi ina ɗakin mijina ina yi musu addu'a Allah ya yafe musu ya sanya su gane" "Amma kin manta mijin 'yar uwakki ne?" Nabila ta ce "Na sani mana, dama ba jauhar ya fara so ba? Kuma ai yanzu ba ya tare da hafsan idan ba zai mayar da ita ba ni sai na aure shi, ko na auri barrister Habib, ko ma duk wanda Allah ya sa ya samu, Allah ya zaɓa mini mafi alkhairi ya bani wanda zai kula da ni" ta na cikin maganar ya miƙe ya bar wurin. Tashi ta yi ta bishi, amma har su ka shiga mota su ka fara tafiya bai kulata ba. "Vi ka yi haƙuri idan laifi na yi maka mana, ka wani haɗe rai ka sha kunu kamar boss" gefe ya ci gaba da kallo. "To ni dai yanzu ba tsoronka nake ji ba duk muzuran da za ka yi mini, da dai na fi jin tsoronka" ya juyo ya yi mata wani irin kallo, take ta tsuke bakinta ta ce "Am sorry". *** Ramma laulayi ya sakata a gaba, ba ta iya cin abinci, komai ta ci sai amai, duk da ƙasan zuciyar mahaifiyarta babu daɗi ta na tausaya mata, amma a zahiri yadda rammar ta fifita abin

Chapter 95 of 121