Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
120 / 121
ƙaramin tausayi take bashi ba, idan ta zauna shi ma cikin nasa zaman yake yi. Zama sai da dabara, tashi sai da dabara, haka bacci ma, gashi tun da ya ƙara tsufa, take fama da matsalar numfashi, dan ma ba ta da yawan complain, sai dai shi ya fuskanci akwai matsala. Sanin alaƙar da take tsakanin Sumayya da Nabila, ya sanya mijinta ba ya damuwa, da yawan zuwa gidan Nabila da take yi, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata. Duk shagwaɓa da rigimar Nabila idan ba ta da lafiya, yanzu babu, sai dai idan an yi mata sannu ta yi murmushi kawai, gaba haka kurum take jin ta sare, kamar mutuwa za ta yi idan ta zo haihuwa. Duk da ita ce abin tausayi, amma tana tausya wa Viper sosai da sosai, bawan Allah sai ya zauna ya zuba mata ido, duk motsinta tausayinta yake ji, da ta motsa zai tambayeta me take buƙata, me take so. Har nauyinsa take ji, ta ce tana buƙatar wani abu. Ana haka mama uwargidan baban su Nabila, Allah ya karɓi rayuwarta, duk unguwa ba in da zancen jinyar wulaƙancin da 'ya'yanta su ka yi mata bai je ba. Nabila tana ji tana gani, babu roƙo da magiyar da ba ta yi ba, Viper ya ce sai dai ta yi addu'a daga gida, ba zata je ko ina ba. Mutuwarta ta ƙara razana Zakiyya, ta din ga ganin saura ita. Watan jaririn Walid biyu, Nabila ta fara naƙuda, tun cikin dare suka tafi Asibiti, amma har garin Allah ya waye ba ta haihu ba. Tun da aka gaya wa Major da sassafe sai gashi a asibitin, ya zo ya tarar da su da Viper da baba magajiya, an fito da Nabila tana zagaya wa, ta samu wuri ta zauna a jikin Viper saboda ta gaji da zagayen. Viper na gaida shi, amma bai ji ba, hankalinsa na kan Nabila, ya riƙe hannunta ya ce "Sannu Arfa na, ya jikin?" "Da sauƙi Abba" "Allah ya rabaki da cikin nan lafiya, ki ci gaba da addu'a kin ji, muna taya ki" Ta jinjina masa kai, mai haɗe da yaƙe. Duk wanda ya wuce ya ga Nabila, sai ya sake waiwaiwayawa ya kalli cikin nan. Shahida ta kira wayar Nabila, dan tun yammacin jiya ta kirata take tambayarta, wai ya mutum yake gane naƙuda yake yi. Viper ne ya ɗaga ya sanar mata su na Asibiti. Shahida ta gaya wa Walid, lokacin bai fita kasuwa ba, ya cewa liti ya wuce kasuwa, zai fara biyawa ya duba Nabila, liti ya ce "Saboda ka rigani ganin ɗan mai zamani ko? To baka isa ba" A asibitin suka haɗu, Walid jikinsa yayi sanyi, dan bai manta yadda Shahida ta din ga fama ba. Liti ya zata abin wasa ne, ganinsu a zaune a harabar wurin a kan kujera, har tana shan shayi. Wata Nurse ta fito ta ce mata ta daure, ta tashi a mayar da ita labor ward a sake dubata. Da Nabila ta miƙe sai da gaban liti ya faɗi, tare da mamakin yadda aka yi tayi rayuwa da wannan cikin, duk da da hijjabi a jikinta. Su na tafe idan ciwon ya motsa sai ta rirriƙe Viper, tana yarfa hannu tana ambaton Allah. Liti ya ce "Walid gaskiya tafiya zan yi, idan ta haihu ka kira ni a waya,na ci gaba da zama a nan kuka zan yi, wallahi na zata haihuwar ba wahala" Walid zai yi magana ya ga da gaske hawaye ne a idon liti, wanda liti da bakinsa yake cewa shi fa sai a shekara ko ƙwalla bai yi ba. Wasa-wasa har Baba sai da ya zo asibitin, Nabila ba ta haihu ba, Viper ji yake kamar ya tayata ciwon, tun da cikin nan ya samu a wahala take. Idan ta gaji, sai ta fashe da kuka, sai dai Viper ya yi ta rarrashinta, yana ba ta haƙuri. Har sai da ya cewa Abdul, ko ayi mata tiyata kawai. Abdul ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, lokaci ne zata haihu da kanta in sha Allah, haka kowace mace take ji. Babu tangarɗa a laborn dan haka a ƙara haƙuri. Sai da ta kusa daf, sannan aka ce Viper ya fita waje, ya din ga sintiri a bakin ƙofa, yana addu'a, sai dai ya din ga tuna Jauhar, yana fargabar Allah ya sa kar wani abu ya samu Nabila da yaran. Doctor Abdul Yasar, ma'aruf Indabo, shi ya karɓi haihuwar Nabila, ta sha wahala sosai da sosai. Dan bayan da jaririn ya faɗo, sai da ta kuma wani ciwon sannan ta biyun ta faɗo. Hamdala ta din ga yi, tana yi wa ma'aikatan godiya, saboda gudunmawar da su ka bata. Abdul ya ɗora mata jariran a kan ƙirjinta, ta rungume su, kawai ta fashe da kukan murna. "Ya haiyyu ya ƙaiyyum ya zuljalalu wal ikram, ya Ubangijin Al'arshi ya Allah duk mai neman haihuwa in dai alkhairi ce , Ubangiji Allah ka bashi yara masu albarka, Allah ka bashi yara masu jin ƙai ababen alfahari ga addinin musulunci, Allah duk mai nema ka bashi, kamar yadda ka azurta Annabi Zakariyya Alaihissalam a lokacin da ya roƙeka. Allah na gode maka da wannan ni'ima, Allah ka raya mini yarana, ka shirya mini su" Su ka din ga amsawa Nabila da Amin. Viper ne kaɗai a wurin da labor room yake, su Major su na can waje. Nabila ta sha ɗinki ciki da waje, ta ji yadda gaba ɗaya ɗakin ya cika da ƙarnin ƙazantar haihuwa, amma daga Abdul har Nurses ɗin, babu wanda ya nuna ƙyamar sa a gareta. Aka shirya yaran tsaf, ita ma aka shiryata, ya basu wuri, nurses ɗin suka ƙarasa taimaka mata, ta shirya, aka yi mata allurai aka fito da ita. Aka wuce da ita postnatal room, ana miƙo wa Viper yaran, amma bai bi ta kansu ba, ya nufi in da aka shiga da Nabila. "Abla" ya kira sunanta. Ta ɗago idanunta da suka yi jawur saboda wahala, ga bacci tana ji. Rungumeta ya yi yana shafa kanta ya ce "Sannu my love, Ubangiji Allah ya yi miki albarka, ya dauwwamar da farinciki a rayuwar aurenmu" Cikin shagwaɓa ta ce "Vi na sha wahala" "Na sani sweetheart, na gani, sannu Abla. Alhamdilillah ala kulli halin. Na gode, na gode my world" yayi maganar yana sumbatar goshinta. Hannunsa ta riƙe ita ma ta ce "Ni na gode da kasancewa tare da ni, ba tare da ƙosawa thank you very much" ya riƙe hannun nata sosai ya ce "Lokacin Jauhar na raye, ta din ga ce mini tsoro take ji, tana son na kasance da ita lokacin haihuwa. Allah bai amince ba, ban kasance da ita ba, amma na cika alƙawarin da na yi mata a kanki" Nabila ta yi murmushi ta ce "Na yi mata addu'a sosai da sosai, Allah ya jiƙan 'yar madararmu" "Amin my love" Abdul ne ya shigo da jariran a hannunsa ya ce "Wai ba kwa san yaran ne? Ana ta rawar ƙafa a baka su, amma ka ƙi kallonsu, ga su nan an yi musu rigakafi, BCG da HB kafin mutane su fara zuwa ɗaukar su" Viper ya yi murmushi ya ce "Sun wahalar mini da mata, shiyasa na ɗan yi fushi, amma tun da tana nan ƙalau, barakallahu fihum" yayi maganar yana karɓar su, cikin wani irin maɗaukakin farinciki mara misaltuwa. Abdul ya ce  "Wannan boss ɗin da kai yake kama, fuskarka ce wannan" Viper ya yi dariya. Su Major ne su ka shigo, shi ma sai da ya fara nufar gadon Nabila, ya tabattar tana lafiya. Kan ka ce kwabo, Asibiti ya ɗinke da mutane, 'yan barkar Nabila. Da liti ya zo duk jikinsa a sanyaye, ya din ga jerawa Nabila sannu, halin da ya ganta a ciki ɗazu, ya ƙara sanya masa tausayin mata. Ya ja gefe aka miƙo masa jarirai. Bai san lokacin da ya ce "Kan uba, kumbo, Viper wannan fuskar ai taka ce, ka ga jariri yadda ya haɗe fuska kamar zai kai duka. Allah ya baki juriyar tarbiyya, wannan zai yi taurin kai kamar babansa" Ba wanda bai yi dariya ba, macen ce take ta tsotsar hannunta, tana buɗe idanunta tana lumshe su a hankali. "Allah ya raya mana ke 'yar madara, Allah ya sa ki ɗaukko halin mai sunanki" Viper ya ce "Har ka saka mata suna?" "Eh gaskiya, na saka mata suna fatima zahra, 'yar madara" Viper ya yi murmushi ya ce "Babanki ya saka miki suna, Allah ya raya ki bisa tafarkin addinin musulunci" Bayan awanni shida aka sallami Nabila, gida ma da suka tafi, ana ta zuwa barka. Washegari hafsa su ka zo Kano da Hafsa, Hafsa kamar a bar mata jariran nan. Alhaji mu'azzam ya ce "Wannan dai na san 'yar madara ce, shi kuma ogan fa ya sunansa". "Takwara na yi muku kai da Abbu, Ibrahim ace masa mu'azzam ko Khalil" Ita kanta Nabila ba ta zaci haka zai yi ba, ta ɗauka sunan Nura yayan ramma zai saka" Alhaji mu'azzam bai taɓa zaton Viper zai yi masa kara haka ba. "Masha Allah, amma na gode sosai da sosai, idan ina da rabo nima Allah ya bani ɗa namiji, Allah ya raya khalil" Viper ya ce "Mu ke da godiya, har duniya ta naɗe, ba zamu taɓa manta abin da ka yi mana, Allah ya saka da alkhairi" Kankarofi ya ce "Kar ka damu Viper, yi wa kai ne" An sha shagalin bikin suna sosai, Alhaji mu'azzam ne ya yi wa jariran Viper hakika, sun samu tarin kyaututtuka, ta in da suka zata da in da ma ba su zata ba. Sai dai Nabila ta fara fama da ɗawaniyar raino, Khalil ba shi da afuwa wurin tsotsotso, 'yar madara ba ruwanta idan an ba ta ta sha, idan ba a bata ba, sai tayi ta tsotsar hannunta. Viper ya ce "Ba fa zai yiwu ka hana mini 'ya kumari ba" Haka zai tsigo shi daga jikin Nabila yana tsala kuka, ya bata 'yar madara ta shayar. Baba magajiya ce take yi wa Nabila wankan jego. Watan Nabila ɗaya da haihuwa, aka yankewa Indabo hukuncin kisa a ƙasar saudiyya. Ko a iya haka Viper ya ɗan ji sanyi a ransa, duk da ba za a taɓa wanke masa zuciya ba, haka ma maman ramma. Bunkure kuwa ana ta jan shari'ar ta, saboda tuhume-tuhumen da ake yi mata da yawa. Abdul ya sha tashin hankali, saboda yadda maganar kashe Indabo ta karaɗe ko ina a ciki da wajen ƙasar nan. Nabila ta fara mayar da hankali a kan ƙoƙarin ta, na fito da hanyoyin taƙaita shaye-shaye, a tsakanin al'umma. Ta fara da rubutun ƙanan litattafai, masu ɗauke da zane-zane, da suke ankarar da illar shaye-shaye da 'yan makaranta tun daga primary zuwa secondary za su iya amfani da shi. Aka gudanar da babban zaɓe na ƙasa, gwamnati ta canza bara gurbi daga cikin muƙarabbanta, yayin da Alhaji mu'zzam ya ɗare kujerar sanata. Jidda babu yadda ba ta yi ba ta koma gidansa, amma yaƙi. Zakiyya kuwa sai abin ya zame mata ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, ga kuɗi iya kuɗi hafsa na cikin daula, amma bata nutsuwar ƙwaƙwalwar da za ta ci, kullum a zabure take cikin tashin hankali. Ba a rufa watanni uku ba, shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu, a kan sauya shugabannin da za su jagoranci rundunonin tsaro na Nigeria. Viper mamaki ne ya cika shi, ganin matsayin da aka ɗauka aka ba shi. Sumayya gwamantin kano, ta buƙaci su yi aiki da ita, ayi mata S.A daga ita har Nabila, amma suka ƙi hakan, saboda ƙungiyar da suke son kafawa, ba sa son siyasa ta shiga ciki, su na so tayi hannun riga da irin ta bunkure. Nabila ta fito daga wanka ta na shirya, ta tsaya tana kallon kanta a mudubi, Viper yana ta rarrashin Khalil yayi bacci, ya ga ta tsaya ta yi shiru tana ƙarewa jikinta kallo a mudubi. "Madam ya dai?" "Vi, kalli duk na yi wani iri, kalli tumbina yadda yaƙi komawa gaba ɗaya, kalli stretch marks duk ya ɓata mini jiki, kalli yadda cikin yayi, kalli breast ɗi na ma, duk stretch marks, ni Allah ya sa kar su yi sagging ma idan na yaye su" tayi maganar cikin damuwa. Ya tashi ya ƙarsa in da take, ya tsaya a bayanta, yana kallonta ta jikin mudubi. Ya zagaya hannunsa a cikinta, yana shafa cikin a hankali ya ce "This is motherhood abla, yara biyu ne fa suka kwanta wata tara a cikinki, ta yaya ki ke expecting ki zauna a yadda ki ke?" "Vi zan daina yi maka kyau, kalli tumbina fa, ji nankarwa, kalli breast ɗina, duk yadda ya cika maybe da na yaye su ma zubewa za su yi" Ya kwantar da kansa a kafaɗarta ya ce "Idan na ce zaki daina yi mini kyau, ban yi wa kaina adalci ba ko kaɗan abla. Ba zaki taɓa komawa yadda ki ke a da ba, kar ki damu kanki, ki ce sai kin yi abin da zai cutar da ke, sai nankarwa ta tafi, sai breast ya koma yadda yake a da, ban ƙi ba ki yi gyara, amma ban da cutar da kanki, ki yi alfahari da wannan nankarwa tambarin zama uwa kenan, ni kyau take yi mini ma, ba na cikin mazan da zan damu da sauyin da jikin matata ya samu, alhalin na san ba a haka na aureta ba, dan duk wanda yake a haka, zai zama mai yawan zalama da hange kuma ba zai taɓa samun yadda yake so ba. Ina sonki a duk yadda ki ke ablana, ni kullum mai kyau ce ke a idona." Juyowa ta yi suka rungume juna tana murmushi, ko ba har zuciyarsa yayi maganar nan ba, ta ji daɗi a ranta, balle ma Viper da ba ya abu dan a so shi, idan abu bai yi masa ba faɗa yake yi. A lokacin da aka shirya walimar karrama Viper, ɗan mama ya zo, Liti ya rungume shi cikin murna da farinciki ya ce "Ɗan mama kai ne ka zama haka? Ni da tsulai, kai in da aka kai kan, tsotsarka suke yi ne, ka ga yadda ka koma kuwa? Ni da takanɗa" Ɗan mama ya ce "Oga liti kenan, ai gara ace garin mayu aka kai ni, ake lasata da azabar da ake gana mini" Kamar Liti ya haɗiye ɗan mama dan murna, har Abdul sai da yaje wurin walimar nan, a ransa yake ta ƙara jinjina lamarin Allah, ɗan daba mara galihu, yau ya zama daga cikin manya a jami'an tsaro. Ramma da tsohon ciki ta kammala WAEC ɗin ta, sun gama babu jimawa ta haihu, ta haifi ɗa namiji, ana haifarsa Abdul ya ce Nuradden ya saka wa jaririn. Ba ramma ba hatta mamanta, sun ji daɗin abin da Abdul ya yi. Mamansa dole ta zubar da makaman adawa da ramma, ganin kaf iyalinta sun tarwatse, sai Abdul, shi kuma ta matarsa yake yi, a dolenta ta sassauta ƙiyayyar da take yi mata, mussaman da ta haifi Nuruddeen. Viper ya ba wa jaririn kyaututtuka daban-daban. Bayan yi wa Viper ƙarin girma, sai da aka bashi motar hawa, da gidan zama. Abin da ya fara yi, ya je unguwar su, ya samu mai unguwa aka zauna da manyan unguwar, ya ce a tattara masa duk yaran da suke harkar daba, waɗanda suke da sha'awar aikin soja, a ɗauki sunansu a bashi. Sannan a duba mutum biyar, za a kai su kasuwa, wurin su Walid, masu son komawa makaranta ma, a ɗauki sunayensu, a kai wa distinguish senator Mu'azzam kankarofi, a ga ta ina za a taimaka musu. Amma duk wanda aka samu da cin amana, sai ya ɗaure shi, kuma babu wanda ya isa ya karɓe su, bisa yarjejeniya za a rubuta komai. Ya haramta daba a yankin unguwar da kewayenta, ko dai mutum ya rungumi zaman lafiya, ko kuma zai ɗauki matakin da ya dace a kansa. Major bai saka lokaci mai tsawo ba, na auren Walida da Abdallah, liti kamar ya janyo lokacin mussman idan ya ga 'ya'yan Viper da kuma na Walid. Khalil rigimamme ne, baby jauhar kuwa babu ruwanta, bayan nono da madara ake haɗa musu, saboda shayarwar na ba wa Nabila wahala, Khalil kaɗai idan ya sakata a gaba, sai ta fara jiri. Nabila ta dage a kan ƙungiyar ta, da gaske take son yaƙi da daba da shaye-shaye, tare da yaƙi da bangar siyasa. Tare da sumayya suke faɗi tashin su, ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta da kuma kafafen watsa labarai, wurin bayyanar da manufar su. Suka samu goyon bayan manyan lauyoyi, da 'yan jaridu, Nabila ta na yawan nanata su ƙungiyar su ba ta siyasa ba ce ba, kuma ba ta gwamnati ba ce ba, dan haka duk ta kan wanda aiki ya biyo za su yi aikinsu ne, ba tare da sani ko kuma sabo ba. Ta kuma samu cikakken goyon bayan mijinta Al'amin, ɗari bisa ɗari. Tare da amincewar gwamnati, aka bibiyi rubuce-rubucen da ta yi, aka yi gyare-gyare, aka fara rarraba su kyauta a cikin makarantu, wanda suka haɗa har da ƙanan labarai, masu kama da tatsunuyoyi, wurin nuna illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da bangar siyasa. Haka nan mawaƙa sun bayar da gudummawa, wurin waƙoƙin yara, da suke nuni da illar waɗannan miyagun ayyukan. Misalin ƙarfe takwas na dare, Viper yana zaune a katafaren falonsa, za ayi hira da Nabila, a babbar tashar talabijin a Kano, kuma Sumayya ce za ta gabatar da program ɗin. Khalil sai tsalle-tsalle yake yi, ya faɗa nan ya tashi can, kamar ɗan aljani. Jauhar kuwa na jikin Viper a kwance, tana ta tsotsar hannunta. Viper ya fi shiri da 'yar madara, babu ruwanta, ba rigima ba rikici, ga ta da haƙuri, Khalil kuwa ɗan gidan Nabila ne, ita kaɗai take iya masa, ba ya ji ko kaɗan, ga wasan kasada, duk wani wasa da zai yi ya cutar da kansa shi yake yi. Ga miskilancin tsiya da kukan banza, gashi abu kaɗan Jauhar za ta yi masa ya maketa, ko ya cijeta. Sai dai idan Viper ya gani, ya murɗe masa kunne, ya tafi wurin Nabila yana kuka. Yanzun ma Viper ne ya kalle shi, yana ta hawa kan kujera yana dirowa da ka. "Ko ka zauna ka bar abin da ka ke yi, ko kuma ka fita, maminku ce za ta yi program zan kalla" Da sauri ya saukko ya zauna a ƙasa ya ce "Mamina ce nikaɗai" "Eh an ji taka ce, ni ma jauhar ɗi na ce nikaɗai" "A'a daddyna ne" "A'a kai ɗan mami ne, ni kuma 'yar madara ce tawa" Tasowa yayi yana kuka yana cewa "Daddyna ne, mamina ce" shi ma ya zauna a jikin Viper" Jauhar ta sake gyara kwanciyarta a jikin Viper, ba tare da ta kula Khalil ba. Fara program ɗin ya sanya, gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu kan TV. Bayan gabatarwa, Sumayya ta tambayi Nabila, menene dalilin da ya sanya ƙungiyar ta, ta fi mayar da hankali a kan harkar daba da shaye-shaye, da kuma bangar siyasa?" Nabila ta ce "Saboda tun da ake yi, bamu taɓa cin ribar abin ba, sai koma baya, da kuma lalata goben matasanmu, lalacewar goben matasa kuma lalacewar al'umma ce" "Ta yaya? Kuma wasu hanyoyi ki ke ganin za a bi a magance wannan matsalolin da ku ka sako a gaba" "Saboda su ne shugabanninmu na gobe, waɗanda za su jagoranci al'umma. Muddin bangar siyasa abin arziki ne, yan siyasarmu ba za su nemi ɗan talaka yayi musu ba, 'ya'yansu za su ka su yi musu. Meyasa ba sa kai yaran talakawa, ƙasashen waje su yi karatun injiniya lauyoyi, likitoci da makamantansu, ko kuma ɗan talaka ba shi da ƙwaƙwalwa da zai yi ilimi ya zama likita, ko injiniya?. Hannu ɗaya baya ɗaukar jinka, kuma hannu da yawa maganin ƙazamar miya. Dole ne iyaye, malamai, gwamanti, hukumomi, mu haɗa hannu mu kawo ƙarshen shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma bangar siyasa. Mu ba wa yaranmu kulawa da ilimi kamar yadda Allah ya ce mana masu kiwo ne mu, kuma ababen tambaya a kan kiwon da aka bamu. Kar ka haifi ɗan da ba zaka iya ɗaukar nauyinsa ba, dan jin daɗinka kawai. Sannan iyaye su din ga bawa hukumomi damar hukunta yaransu, a duk lokacin da aka masu da laifuka. Sannan su kansu hukumomin da 'yan siyasa su ji tsoron Allah, wurin kama masu laifi, da sakinsu ba bisa ƙa'ida ba. Babu wanda ya taɓa zama wani abik alfahari, a dalilin ta'amalli da miyagun ƙwayoyi. Ba hujja ba ce matashi ya zauna ya ce sai gwamanti ta bashi aikin ba shi da aikin yi. Masu kuɗin duniya babu wanda yayi kuɗi da aikin gwamnati. Ina kira da matasa, ku tashi ku nemi na kanku, ku nemi ilimi, duk wanda ku ka zaɓa, bai yi muku abin da ya dace ba, ku ɗaura ɗambar dawo da shi, ta hanyar recall election, ko  kuma ku canza shi a lokacin zaɓe. Kuma za ku iya zama likitoci, injiniyoyi da makamantansu, ku ba bayin 'yan siyasa bane ba, da za su yi amfani da yau ɗinku, su lalata gobenku, domin ku dauwwama ku na yi musu bauta da yaransu. Su daina ba ku miyagun ƙwayoyi, ku na sha ku na kashe kanku, alhalin sun kauwwame yaransu, sun tura su in da za su yi ilimi, sun kwashe dukiyoyinku sun tara wa iyalansu arzikin da ba za su yi talauci ba, sun bar ku da bauta musu, da zubar da jininku yadda suke so, alhalin iyalansu su su ka fi cancanta su yi musu wannan aikin ba ku ba. Ina fatan nan gaba kaɗan in ga matasa 'yan shekara talatin zuwa ƙasa a majalissu, in gansu a cabinet ɗin shugaban ƙasa. Mu ga matasa ɗanyen jini, sun gaji manyan malamanmu, irin su marigayi Albani zariya, Sheikh ɗahiru usman bauchi, dr. Isa Ali Ibrahim fantami, malam umar sani fagge, malam Aminu Ibrahim daurawa, malam Ahmad guruntum, Sheikh Ahmad bamba rahimuhullah, malam Nasiru kabara. Ina fatan na ga mun samu ire-iren ɗangote da dama, in ga natasanmu sun zama dactoci da profesoshin ilimi da duniya za ta yi alfahari da su. 'yan daban nan 'ya'ya ne, kuma za su amfani al'umma idan aka tsaya wa rayuwarsu" Sumayya ta ce "Sannu da ƙoƙari, kin kwararo bayanai, masu matuƙar ma'ana, kin ƙara ƙarfafa mini gwiwa, kamar na fito takara nima, duba da yanayin lokaci, bari mu waiwayi masu sauraro, mu ji gudunmawar da za su bamu" Bugowar farko, muryar Viper ta yi amsa kuwwa a cikin wayar tarhon. "Ina yi wa baƙuwa barka da zuwa, haƙiƙa ta yi bayani masu ma'ana, amma tayi tuya, ta manta da albasa, ba ta tofa komai a kan iyaye mata ba" Murmushi Nabila ta yi, domin kuwa muryar Khalil ta jiyo yana kiran mami ta cikin wayar. "Mata iyayen al'umma, mata iyayen giji, a basu ilimi, a kula da su, kar ayi musu fyaɗe a ɓoye, domin gudun zubewar mutunci, a ƙi ɗaukar musu mataki, kar a ɗora musu talla, kar a tura su barace-barace, kuma kar ayi musu auren dole, kar a zalunce su. A wadata su da ilimi, a tausaya musu a ba su damar cika burikansu. Babu wata mace da zata iya rayuwa ta tsaya da ƙafarta, ba tare da ta jingina da namiji ba. Kamar dai ni, babana ya share mini fagen cikar burina, mijina kuma ya bani dama kuma ya tsaya mini, hakan baya nufin lalacewar macen. Ni 'ya ce, matar aure, uwa kuma lauya mai zaman kanta, ina fatan nan da shekaru kaɗan na ga mata ire-irena sun yawaita, kuma matasa sun kama hanyar gyara rayuwarsu, domin samar da kyakykyawar gobe ga al'umma da ƙasata baki ɗaya." Nabila ta sha tambayoyi daban-daban, kuma sosai ta ƙara zaburar da al'umma, mutane da dama su ka nuna sha'awar su, a kan ƙungiyar, sai dai ta nanata cewar ƙungiyar ta ba ta siyasa ba ce ba, kuma ba ta neman kuɗi ba ce ba. Hankalin Nabila ya kwanta sosai da sosai, Allah ya dafa wa lamarinsu, ga Alhaji mu'azzam sosai yake tallafawa matasa, yake tafiya da su, tare da bankaɗo masu ilimi da himma a cikinsu, ya samar musu aiki, da sama musu appointments a ƙasa. Kankarofi na daga cikin yan majalisa da suka kawo wa yankin arewacin Nigeriya cigaba sosai da sosai. Liti tuni ya angwance da Walida, cikin ikon Allah kuma ya rage rawar kai, saboda daraja da kamala ta aure, da ta hau kansa. Bayan shekaru uku, Abbu ya basu damar tsayawa da ƙafafuwan su, ta hanyar ba su jari aro, da kuma kama su musu wurin gudanar da sana'a. Nabila sai da ta haifa wa Viper yara biyar, sau biyu tana yin twins, sai kuma Namiji a tsakiya guda ɗaya, sai dai Khalil shi ya ɗaukko halin Viper gaba ɗaya babu abin da ya bari. Abdul ya tsaya wa ramma, sai da ta zama cikakkiyar Nurse, shi ma ta hayyafa sosai da shi. Rahila daga baya Allah ya yi mata rasuwa, jikinta yaƙi daɗi haka ta koma ga Allah. Hafsa kuwa haihuwar dai Allah bai bata ba, amma Kankarofi

Chapter 120 of 121