Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
47 / 121
ƙirjinsa yana murmushi ya ce "Ke dai ki ke kallon hakan, ga al'umma na zama mara amfani, saboda ɗan daba ne ni" "To ni dai kana da amfani a wurina" Yayi murmushi ya ce "A ɓoye fa rigima kawai ki ke so ki yi na rarrasheki, to na ji sannu yi haƙuri" "Yauwwa mata da yawa ba ayi mus irin yadda ka ke yi mini ɗin nan, zuciyar zinare ce da kai master, kana da tausayi sosai da sosai" ta kara kunnenta a ƙirjinsa ta ce "Zuciyarka sai kiran sunana take" Al'amin ya ce "Ni dai yi magana a hankali, na ji babyna yana motsi, kar kwanciyar da ki ka yi ce kika takura masa, tashi zaune" Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Master, zaka dawo ka tarar da ni, ina 'yar gala-gala da cikin nan, duk sai nuna banbanci ka ke yi" Shi ma kallon fararen idanunta yake yi yana dariya, ya ce "To breakfast fa, me zamu ci?" Ta tashi zaune ta ce "zan dafa maka wani abun, amma ni anty wasila nake jira, za ta kawo mini wainar gero" Ya tsuke fuska ya ce "Roƙo ko?" Ta ce "A'a geron da ka kawo na ɗiba na bata tayi mini, idan ni na yi ba zan iya ci ba" Ya ce "Ok" Har azahar yana gida, jauhar ta hana shi fita, sai azahar yayi shiri ya fita, saboda sallar azahar, yanzu jauhar ta daina fama da shi a kan yin salla a kan lokaci. Sai ga anty lubabatu, ta zo maƙwabciyar su mai ba ta aikin bead a gida. "Oyoyo anty lubabatu, yau ke ce a gidan". "Yau gani na lallaɓo, an ce mini kin kusa juyewa, na ce bari na zo ga ya kike" Jauhar ta ce "Ohh ni zahra'au in ji wa? Ba a gaya miki daidai ba" "Eh ba a gaya mini ba, ni na gani yanzu ai" Da sauri jauhar ta kalli cikinta ta ce "Haba dai dan Allah a na gani" Anty lubabatu ta kwashe da dariya ta ce "Lallai yarinya, wannan uwar ƙibar da ki ka yi ma da haka ki ke? Kin zama uwar mata" Juahar ta yamutsa fuska ta ce "Na yi muni ko?" "A'a babu wani muni, wallahi kin yi kyau, kallo ɗaya mutum zai yi miki ya san a kwanciyar hankali ki ke. Jauhar gyaran gida aka yi miki haka, lokacin da na zo gidan nan kina amarya tsurar bulo ne fa, ikon Allah har da sola, wato a duniya idan Allah yana yinka ko wa ma yaƙi ka. Ga Alhaji mu'azzam can Allah ya bar su da shi, matarsa na ta gana wa hafsa azaba, abu har da 'yan sanda, ya ce idan ba zata zauna da matarsa lafiya ba tayi mata biyayya ta tafi gida. Gidanku kuma ana ta tashin hankali, Anty zakiyya ta ce mama ke yi mata asiri" Cikin damuwa jauhar ta girgiza kai ta ce "Bari kawai Anty lubabatu, lamarin gidan nan namu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma wasu lokutan har da laifin baba, kodayeke shi ma sun mayar da shi sai yadda suka yi da shi, ai da ni aka ce ina yi wa hafsan asiri. Ko gidan ya hanani zuwa, sai idan da daddare ya kaini na gaida baba na dawo gida" "Allah ya taimake ki, ke da suka so su tozarta rayuwarki Allah ya rufa miki asiri, ɗan daban da suka aura miki dan ki wulaƙanta, hakan ba ta faru ba" "Tababs babu abun da zan ce wa Allah sai godiya, Anty lubabatu mijina a maza ɗari irnsa ɗaya ne tak. Daba da shaye-shaye su ne ƙaddararsa amma, ya ci sunansa amintacce rauninsa mutane suke kallo, basa kallon nagartarsa" sun daɗe suna hira sosai kafin ta tafi. Kusan duk bayan kwana biyu zuwa uku, sai hajiya kakar Al'amin ta kira Jauhar ta yi mata ya jiki, dan tun wani zuwa da tayi ta fuskanci hakan. Tun da ya fita da azahar har bayan magariba bai dawo ba, sai da ta kira shi a waya, ya ce mata gashi nan. Hnakali a tashe ya dawo mata, dan sai da gabanta ya faɗi ya ce "Master lafiya?" "Nura aka kawo daga Abuja, wai ba shi da lafiya, tun lokacin nan da ya ce mini ba shi da lafiya, yake kwance" Ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka?" Ya ce "Ban sani ba, an dai kai shi asibiti, na je na ganshi a galabaice, yayi magana ya faɗi meyake damunsa ya ƙi, na ga a galabaice yake sosai, an saka masa ruwa da sauran abun da yakamata gobe in Allah ya kaimu dai zan koma". Jiki a sanyaye ta ce "Allah sarki Nura, sai da ka ce idan ba zai iya ba ya dawo, wataƙila dan kar ka yi masa faɗa ne ya zauna bai dawo ba. Allah ya bashi lafiya" Ya amsa da Amin. Ya ciro mata envelope ya ajiye mata. Ta ce "Menene wannan?" Ya ce "Duba ki gani mana" Hotunasu ne shi da ita, wanda galibi a wayarta suka yi, ya kai aka ciro su, sai kuma ƙatuwar viva, da aka yi frame ɗin hoton da suka yi na sallar eid ɗaya an rubuta musu happy marriage life, ɗaya kuma an rubuta first eid with habibi. Tayi murmushi ta ce "Kamat yayi a rubuta Master weds madara" duk da a cikin damuwa yake sai da yayi murmushi, ya ce da safe zai kafe a falo. Ta kalleshi tana murmushi, bai taɓa ce mata yana son ta ba, sai dai actions ɗin sa, yana tabattar mata da hakan. Da fari kai ba ka ce ya iya duk wani abu da yake da alaƙa da kulawa ba, saboda he's always serious, sai dai a hankali ainihin halayensa suke fitowa. Jikin Nura yayi tsananta, kullum Al'amin cikin sintiri yake, jauhar ce mai lallaɓawa tayi musu girki, mahaifiyarsa ce take zaune da shi a asibiti tana kula da shi, gashi an rasa gane abun da yake damunsa, Al'amin har gona ya saka aka sayar masa a ƙauye, saboda kula da Nura, dan asibitin kuɗi ya saka aka mayar da shi. Da daddare babar Nura ta fita, Al'amin ya zo, cikin ƙarfin hali ya ce wa Al'amin "Yau ina Antyna ba ta zo ba?" Ya ce "Eh, ni na hanata zuwa, tayi nauyi. Nura yakamata zuwa yanzu ka gaya mini menene yake damunka, ana ta kashe kuɗi an rasa gane abun da yake damunkaa yayi maganar cikin damuwa" Nura ya ce "Idan na gaya maka ba zaka yi fushi da ni ba?" "Ya za ayi na yi fushi da kai? Ka gaya mini in san ta in da zan kamo bakin zaren". Ya riƙe hannun Al'amin ya ce "Na san ba lallai na rayu, amma ba ka da laifi ka taimaki rayuwata ne. Na gayawa mama na ce kar ta gaya maka. Lokacin da na ce maka na fasa tafiyar nan, Honorable ne ya ce sai ya yi ɗabi'ar mutanen annabi luɗ da ni, na ƙi yarda, ni kuma na kasa gaya maka, dan ya ce idan na gaya maka, kashe mai unguwa zai yi, amma idan na amince shikenan, ba wanda zai san an yi kuma zai bani aikin. Na ɗauka daga haka shikenan, sai dai tun da ya tafi da mu, a wani gida aka ajiye mu, abun da suke yi mana kenan, yana da masu kula da mu, babu ta in da mutum zai gudu, kuma ba shikaɗai ne yake yi mana hakan ba, akwai wasu manyan mutane a ƙasar nan, da duk zan gaya maka sunayensu. Kuma kamar tsafi suke yi ta hanyar amfani da mu, bana iya riƙe bayan gida, mama ce take gyara mini kafin mutane su zo dubiya, Indabo ya lalata mini rayuwa amma ka rufa mini asiri dan Allah, kuma kar ka zargi kanka! Ina da hujja mai ƙarfi da zan baka a kan haka! Ayshercool. 08081012143 45 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Gaba ɗaya fuskar Al'amin ta sauya takmar ta horo, ta koma Al'amin ɗin sa na ainihi, tamkar bai taɓa sanin wani abu wai shi dariya ba. Wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, jijiyoyin goshinsa zuwa kansa suka miƙe suka kukkumbura, idonsa yayi wani irin ja mai ban tsoro, bugun zuciyarsa ya ƙaru da saurin gaske, jikinsa ya fara ɗaukar wani irin zafi saboda tashin hankali da tsananin ɓacin rai. Ba tare da tunanin halin da Nura yake ciki ba, yayi wa hannun guduma wani irin mugun riƙo, da sai da ƙasusuwansa suka yi ƙara. Nura ya ɗora ɗaya hannun a kan na Al'amin ya ce "Yaya, kai ɗan uwa ne da Allah ya bani rana tsaka a titi, duk wannan abun ka yi ne dan inganta rayuwata, ba ka taɓa yin wani abu da zaka cuceni ba, na san da ka san abun da zai faru da ni kenan, ba zaka bari na je ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka, ni na san ba zan rayu ba, abun da suka yi mini ya fi na kowa muni da tashin hankali, ban san yaya zan misalta maka ba, amma dan Allah kar ka yi yinƙurin yin wani abu, idan ba haka ba za su yi maka illa. Na bar su da Allah ka tayani Addu'a Allah ya yafe mini laifukana, idan na mutu dan Allah ka yi mini wanka kar asiri na ya tonu, ba na son a zargeka da abun da mutane ba su san menene ainihin abun da ya faru ba. Wurin bayan gidana ya riga ya ɓaci, kowa ya gani zai gane meyafaru dan Allah kar wani ya je kan gawata idan ba kai ko mama ba" Al'amin ya riƙe hannun Nura gam, amma ya kasa magana sai wani irin numfashi mai haɗe da huci, ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi. Yanayin yadda mahaifiyar Nura ta tarar da Al'amin, ya sanya ta gane ya gaya masa. Ta ƙarasa gaban gadon, jiki a sanyaye ta ce "Al'amin, ka kwantar da hankalinka dan Allah, zan iya dafa Alqur'ani na rantse, ba zaka kai mini nura in da za a cutar da shi ba, na san da ka san me zai faru kenan ba zaka yadda ya je ba, a irin yadda yake bani labarin zamanka da shi. Iya ɗawainiyar da ku ka din ga yi da mu kai da matarka ya ƙara tabattar mini da haka. Cuta ce an riga an cuce mu, amma mun bar wa Allah, ni ba zan zargeka ba" Ya saki hannun Nura a hankali, ya tashi ya juya ya fice. Nura yayi ajiyar zuciya ya ce "Allah ya sa kar ya ce zai ɗauki wani mataki, dan mutanen nan sun wuce duk yadda yake tunani, ni dai ku cigaba da yi mini addu'a da fatan cikawa da imani" Duk da juriya da mahaifiyar Nura take yi, sai da ta kasa ta zubar da hawaye, cike da karaya, dan magana kawai Nura yake yi, amma komai sai an yi masa, gashi buni-buni jininsa ya ƙone, sai an saka masa wani, dan bayan bayan gidan, har da jini ne yake zuba daga wurin, jini sosai ba kaɗan ba, a tunaninsa da na mahaifiyarsa ɓoye wa likitocin ainihin abun da ya faru shi ne rufin asirin su, dan babu wanda zai fahimce su, cewa za a yi shi ya kai kansa, saboda kwaɗayi da son abun duniya, dan Nura ya yi girman da ya fi ƙarfin ace dole aka yi masa. Ikon Allah ne kawai ya kai Al'amin gida, dan ko me za ayi masa bai san ya aka yi ya isa gidan ba. Jauhar har ta yi bacci, dan 'yan kwanakin nan bacci take yi sosai da sosai, duk in da ta ji kwanciya ta yi mata daɗi sai bacci. Ba ta farka ba, sai bayan sha biyun dare, shi ma dan taji ta gaji da kwanciyar ne, a hankali ta tashi jikinta duk yayi tsami, ta kalli ƙofar ɗakin Al'amin, ta tashi ta nufi ɗakin, ta ɗaga labule ta shiga. Yanayin kwanciyar da ya yi, ya tabattar mata da yayi shaye-shaye ya bugu, dan wata irin kwanciya yayi. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban katifarsa ta zauna a hankali ta ce "Haba master yau kuma?" Dan bai fiye shan abun da zai gusar masa da hankali gaba ɗaya har haka ba, yana yi amma ba sosai ba, ya fi ganewa busa hayaƙi. Kuma kwanakin nan da Allah ya taimaketa tayi galaba a kansa, bai fiye shan abun buguwa ba sai shan sigari, wiwin ma ya rage shan ta sosai, amma ta zo ta tarar da shi a wannan yanayin. Da ƙyar tana haki, haka ta gyara masa ƙafarsa da hannunsa, ta shafi sumar kansa, sai wani irin gumi yake yi, naman fuskarsa yana ɗan yi rawa lokaci zuwa lokaci ga ajiyar zuciya da yake ta yi a kai kai. Ganin ba ya hayyacinsa, balle su yi magana, ya sanya ta tashi ta tafi ɗakinta, cikin zullumi da tunanin me aka yi masa?. Kiran sallar farko ya farka, sai dai zuciyarsa cike da tsananin baƙin ciki da ɓacin rai, ya san ko ya je gida ba zai samu indabo ba yana Abuja, kuma ba zai iya tafiya Abuja ba, cikin fargaba zai tafi kar yana matsawa wani abun ya samu Nura. Alwala yayi ya fice, a hanya yayi sallar asuba, ya ƙarasa Asibitin, maman nura na ta kokowar yadda zata ɗaga shi, ta saka masa pampers, yayi mata girma. Al'amin ya bubbuga ƙofar, ta ce "Waye?" Da ƙyar ya iya magana ya ce "Al'amin ne" Nura ya ce "Mama buɗe masa" Ta buɗe masa ya shigo, Nura ya gaida Al'amin, jinjina kai kawai yayi, suka gaisa da maman Nura, da ƙyar yake iya magana, saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali. Ya taimaka mata, suka canzawa Nura pampers, jinin da Al'amin ya gani a pampers ɗin ya ɗaga masa hankali, gaba ɗaya halittar duburar Nura ta fito waje, babu ƙyanƙyami babu komai, ya taimaka mata suka gyara shi, suka saka masa pampers uku, kamar yadda take saka masa, sai kuma ta kawo zannuwa ta tuttura masa ta toshe ko ina, ta fesa masa turare, ta kunna turaren wuta, ta shiga banɗaki ta wanke kayan da aka cire mas. Al'amin ya rasa me ma zai cewa Nura, abun duniya ya ishe shi, ya ji ya tsani kansa, komai baya yi masa daɗi. A hankali ya kalli Nura ya ce "Zan gaya wa likitoci, su duba idan da abun da za a iya yi, ayi maka babu dabara a ɓoyewa likitoci wannan lamarin" Da sauri Nura ya ce "Dan Allah kar ka yi mini haka, ka rufa mini asiri, wallahi babu wanda zai yadda dole aka yi mini, na san ba zan rayu ba, lokaci kawai nake jira, dan Allah yayana wannan ce alfarmar ƙarshe da zan nema a wurinka, dan Allah kar ka gaya wa kowa" Cikin matsananciyar damuwa Al'amin ya ce "Nura ka yafe mini, wallahi ban san abun da zai faru ba kenan, na zata hakan zai taimaki rayuwarka ne... Sai ya kasa ƙarasawa muryarsa ta fara rawa. Guduma ya ce "Wallahi na sani, kai mutumin kirki ne yayana, dan Allah idan na mutu ku din ga yi mini addu'a, na san sauran jama'ar gari babu lallai su yi mini, saboda ban shuka alheri ba, amma na san kai zaka yi mini kai da mama, da Antynmu. Dan Allah idan ta haihu, idan namiji ne, ka saka masa Nuraddenni ka din ga tunawa da ni" yayi maganar yana murmushi. Al'amin ya haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci, ya kalli Nura, amma ya kasa magana. Nura ya sunkuyar da kai, yana share hawayen karaya. Maman Nura ta fito ta gama wanke kayan Nura, muryar sa na fita a hankali, ya kalli maman Nura ya ce "Me za a sayo muku ne? Da me zaku karya ba ta tashi ba na taho" Mama ta ce "Kar ka damu Al'amin, ƙanwata suna nan tafe, da wuri za su zo, ai da ƙannensa ma su duba shi, baiwar Allah ai tana ƙoƙari Allah dai ya raba ta da cikin nan lafiya, ta sauka lafiya ƙalau. Ai ta ce tuwon dawa zan yi mata, da miyar ɗanyar kuka da man shanu idan ta haihu, in sha Allah kuma ana ce mini ta sauka, zan dafo na taho kano, yajin daddawa ma ni zan yi mata". Nura ya ce "Mama ni dai ki tayani roƙo, na ce a saka sunana idan an samu ɗan saurayi" Suna yin hirar ne, dan Al'amin ya kwantar da hankalinsa, sai dai fuskar nan tamau ya kasa yin fara'ar. Ƙarfe takwas da mintuna, wata yarinya ta shigo ɗakin, 'yar baƙa mai kyau, da siririn billenta, a gefen fuskarta. Babu ko sallama ta faɗo ɗakin ta ce "Mama mun zo" "Baki iya sallama ba ne?" Ta ce "Assalamu alaikum, yaya wai da gaske ka je Abuja?" Tayi maganar tana ƙarasawa gaban gadonsa. Nura ya ce "Eh ramma, ya gida ya makaranta?" Ramma ta ce "Lafiya ƙalau, yaya wai to ka ga shugaban ƙasa?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. "To idan ka koma zaka ganshi? Ka ce masa dan Allah a gina mana burtsatse, wurin ɗebo ruwa da nisa sosai" Ya shafa kanta ya ce "To zan gaya masa, ina Sani?" "Babanmu ya ce ba za a zo da shi ba, ya tafi makarantar Allo, nima da ƙyar ya bar na biyo innar su jafarun muka taho". Mama ta ce "Ke baki iya gaisuwa ba, balle ki yi wa yayan naki yaya jiki ba?" Ta kalli Al'amin ta durƙusa ƙasa ta ce "Ina wuni?" Ya jinjina mata kai kawai, ta ce "Yaya sannu ya jiki?" "Jiki da sauƙi Alhamdilillah" "To Allah ya baka lafiya" Wata mace ce tayi sallama, tana faɗin "Ke kuwa ramma an yi ƴar bantan uba, ina can ina bulayin in da aka kwantar da ku, kawai na nemeta na rasa shashasha ba zaki yi hankali ba" Ta zauna suka gaggaisa, Mama ta nuna mata Al'amin ta ce "Atine ga uban gidan Nura, shi ya samo masa aikin nan, yake ta ɗawainiya da mu" Atine ta ce "Allah sarki, ni wallahi kama yake yi mini da mai gyaɗa, yana kama da 'yar nan ta ta da ta rasu wadda tayi aure a birni, zahra'u" da sauri Al'amin ya kalleta Mama ta ce "Wallahi kuwa, mun yi waya da ita ma, ta ce zata zo duba Nura". Taɓ yana da alaƙa da Nura ne, ko kuwa kawai dai hasashe ne, ko abun su na mutanen ƙauye, da kowa ma ɗan uwan su ne? saboda tsabar miskilanci bai yi musu magana ba, ya tashi ya tafi. Ya je gidansa ma, ya kasa kawai ya tafi ya samu wani kango, yayi zamansa, abun duniya ya ishe shi, bai ma san ta ina zai fara ba. Bai koma gida ba sai can bayan la'asar sannan ya koma gida, ba ta ce masa uffan ba, tayi masa sannu da zuwa, ita babbar godiyarta ga Allah, dawowarsa lafiya, ba tare da wani abu ya faru da ita shi ba. Sai dai ta haɗa abinci ta bashi, amma ta ga ya daɗe bai motsa ba, daga baya ya ɗauki cokali ya din ga tura abincin da ƙyar, kamar mai tura magani, ya gama ya nemi wuri ya kwanta bai ce mata uffan ba. Duk da yanayin hakan bai yi mata daɗi ba sam, amma ta daure ta ɗan bashi lokaci, amma taga a jere, kusan kwana uku, ba ya ce mata uffan, kuma kullum sai ta yi bacci zai dawo, da asubar fari kuma yake ficewa. Idam ya fitan nan, asibiti yake tafiya ya taimakawa babar Nura ta gyara masa jikinsa, sai dai kullum jikin nasa babu sauƙi. Ranar na haɗu, da ya fito zai fita ta tare shi ta ce "Master, wai dan Allah laifin me na yi maka har haka ne? Meyake faruwa yakamata ka sanar da ni" Ya ce "Zan gaya miki idan na dawo" daga haka ya fice ya bar ta. Abun duniya ya ishi jauhar, ta kasa gane meyake faruwa haka yake ɓoye mata. Yana zuwa asibiti ya tarar da mahaifiyar Nura a gefen gadon Nura, ta rufe shi, idanunta sun yi jawur. Cikin matsanancin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon, ya yaye zanin, ya tarar Nura ya cika. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya furta cikin matsanancin tashin hankali, ya zauna yayi shiru shiru, ya kasa zubar da hawaye sai wani abu da yake yi masa zillo, tsakanin maƙogwaronsa da ƙirjinsa. Ya saka gwiwoyinsa a ƙasa a gaban mahaifiyar Nura ya ce "Ki yafe mini saboda girman Allah, ban taɓa tunanin abun da zai faru da Nura kenan ba, da na san haka zata kasance wallahi ba zan tura shi ba" Ta share hawayenta ta ce "Wallahi na sani, kuma ni ban zargeka ba, Yanzu fatana Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, Allah ya yafe masa kai ma ɗawainiyar da ka yi da mu, Allah ya baka lada". Ya ɗauki waya ya sanar da su liti su samo mota, a asubar su zo a tafi da gawar Nura Allah ya yi masa cikawa. Sun girgiza sun kaɗu matuƙa da mutuwar Nura, da asubar aka tafi da gawarsa gidan mai unguwa, ta ce ita za ta yi wa Nura wanka, Al'amin ya tayata ya ce ban da su biyu, kar wanda ya je kan gawarsa. Mai unguwa ya din ga bala'i, yana yayi asara kuwa, ya rasa wanda zai gayyato kan gawarsa sai ɗan daba. Maman Nura ta ce "Ɗa na bai yi asara ba wallahi, kai ka yi asara, dan da ka kula da shi ka riƙe shi da mutunci da amana, ba zai faɗi haka ba. Kuma ba in da aka ce ɗan daba ɗan wuta ne, ko an haramta masa zuwa kan gawa". Haka suka yi wa Nura sutura, aka sanar da rasuwar sa. Duk da ana ganin Nura baya ji, amma ya tara mutane, saboda daga baya duk wani aikin gayya na cigaban unguwa da shi ake yi. Sai ƙarfe goma na safe, Al'amin ya dawo gida, yana zullumin yadda zai gaya wa Jauhar mutuwar Nura, ga zuciyarsa da take wata irin tafasa take raya masa kashe Indabo ya huta da baƙin cikin da ya jefa shi a ciki. Cikin matsananciyar damuwa ta ce "Master wai meyake faruwa dan Allah?" "Allah ya yi wa Nura rasuwa" Gaba ɗaya sai ta manta waye ma Nura, ta ce "Waye kuma Nura?" Ya ce "Guduma ɗan gidan mai unguwa" kamar shashasha haka ta bishi da kallo, daga bisani wani irin jiri ya ɗebe ta, cikin azama ya riƙe ta, jikinta ya hau wata irin tsuma, ta saka hannu iya ƙarfin ta, ta toshe bakinta, dan hana kukan da yake ƙoƙarin taso mata fitowa amma ta kasa, iya ƙarfinta ta din ga maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Allah ya sa ba Nuran da na sani ka ke faɗa ba" Jiki a sanyaye ya zauna da ita a jikinsa ya ce "Ba kyau yi wa mamaci kuka fa kin sani, ki yi masa addu'a" Cikin kiɗimewa ta ce "To me zan ce?" "Ki ce Allah ya jiƙan Nura yayi masa rahama" Tari ta fara yi, ya ɗaga ta yana yi mata fifita, tare da yi mata sannu. Sai da ya tabbatar ta ɗan samu nutsuwa, sannan ya riƙe hannunta, suka tafi gidan mai unguwa, idanunta sun kumbura sun yi jawur, fuskarta ma tayi ja sosai da sosai. Sai dai suna shiga ɗakin da mahaifiyar Nura take karɓar gaisuwa, suka tarar da hajiya a ciki a zaune, a kusa da Maman Nura. Hajiya ta ce "Al'amin, yanzu nake cewa zan kiraka na ga kamar unguwarku ce nan" Maman Nura ta ce "Ai wannan ne ubn gidan nasa da ya ɗauke shi kamar ɗan uwa da nake gaya miki" "To ai ɗan wurin Zahra'u ne, jikana ne" "Iko sai Allah, Al'amin da kakarka da mahaifiyata uwar su ɗaya uban su ɗaya, Allah bai saka mun san juna ba" Ya zaunar da jauhar, ta zubawa mahaifiyar Nura ido, amma ta kasa magana sai sheshsheƙar kuka, maman Nura ta rungumeta tana ƙoƙarin rarrashinta, amma ta kasa sai suka cigaba da kukan tare gefe ga ramma da ƙaninta sani, da suke uwa ɗaya da Nura, suma su na ta kuka, hakan ya ƙara karya zuciyar Al'amin. Har aka gama zaman makoki, Al'amin yana cikin damuwa da tashin hankali, Hajiya da su ramma, a gidan Al'amin suke kwana, har zuwa kwana bakwai, sai dai kafin a gama zaman makoki, mai unguwa ya fara yada maganganu cewar Al'amin ne yayi silar mutuwar ɗan sa, Allah kaɗai ya san ina ya kai shi, idan abun gaskiya ne, meyasa shi bai je ba ya tura shi. Kafin a ƙare zaman makokin, sai da maman Nura suka yi kaca-kaca da mai unguwa, ta ce Al'amin babu yadda za ayi ya kai shi in da za a cuce

Chapter 47 of 121