yi haƙuri dan Allah, ki fahimce ni, ya za ayi na so ki mutu, ba haka bane ba. Wallahi Mumm tsoro nake ji na fito da yarinyar nan, ayi mata wani abu na daban, dan Allah ki yi haƙuri, zan zo gida nayi miki bayani, na san zaki fahimce ni in sha Allah. Kuma yaya jafar zai fito in sha Allah, ki yi haƙuri dan Allah"
"Ai shikenan, ka yi abun da ka ke so"
"A'a ba za ayi haka ba, zan zo har gida nayi miki bayani" ta katse wayar, yayi ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa ya buɗe yana kallon ramma, da ta yi kamar ba ta jin me yake faɗa a wayar.
"Rahama"
"Na'am"
"An sakoni a gaba a kanki"
"An san ka sace ni kenan?"
Abdul ya ce "Ke fa ba a abun arziki da ke, ke da ban sace kin ba, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba"
"Ai ba da kyakywar manufa ka sace ni ba, kashe ni ka ce zaka yi"
"Amma ai ban kashe kin ba ko?" Tayi masa shiru ta cigaba da aikin ta.
****
Nabila ta fito daga banɗaki, kawai ta tarar da Nasir a tsaye a ɗakinta, ta kalleshi ta ce "Lafiya?"
Ya ɗago mata file ɗin Viper da yake hannunsa, ta bar shi a kan gadonta tana aiki, ya faɗo mata ɗaki.
"Menene wannan?" Ta ƙarasa gabansa ta saka hannu zata karɓa, ya janye yana sake tambayarta "Menene wannan Nabila?"
"Babu ruwanka da ko menene, ka bani file ɗina kuma ka daina shigo mini ɗaki ba tare da iznina ba"
Cikin tsawa ya ce "Ki yi mini bayani kin tsaya kina wasu kame-kame da wasu maganganun banza da na wofi"
Cikin dakewa ta ce "DSP aikina nake yi, ka fita daga harkata ka bani file ɗina"
"Nabila, ta tabatta goyon bayan ɗan ta'adda ki ke yi?"
"Ni bayan gaskiya nake bi, kawai, ka bani file ɗina"
"Nabila kina haɗuwa da mutumin nan, kin san in da yake"
"Ni ban san in da yake ba, ka bani file ɗina tun ina ganin mutuncinka"
Shammatarsa tayi, ta kafa masa haƙora a hannunsa, ba shiri ya sakar mata file ɗin, ta kwashe abun ta tayi waje, ya bi ta da kallo, ya kalli hannunsa yadda yake tsatstsafar da jini saboda iya ƙarfinta ta cije shi.
Cikin yarfe hannu, ya bi bayanta, sai dai ko sama ko ƙasa ya nemeta ya rasa a cikin gidan nan.
Zuciyar sa ta daɗe tana mamakin abun da ya gani, amma haryanzu ya kasa gazgata cewar Nabila tana haɗuwa da Viper, ta san in da yake, amma me zai haɗata da ƙasurgumin ɗan ta'adda haka tana ya mace, idan kuwa haka ne, duk hukuncin da doka tayi a kanta shi ba zai ce komai ba, amma ya yanke ya sake tuntuɓar Abba, ya kirata ya ja mata kunne, a lallaɓata a cikin gida idan da abun da ta sani, a sasanta abun, kar asiri ya tonu, dan shi kansa abun kunya ne a gare shi, ace yana can yana haƙilon neman ɗan daba, Nabila na zagewa ta haɗu da shi a ɓoye.
Da daddare Nabila na zaune a falon Abba, ga Nasir a gefe, sai kuma shi kansa Abban, tayi shiru ta sunkuyar da kai fuskarta babu annuri.
"Arfa" Abba ya kira sunanta a kausashe.
"Na'am Abba"
"Gaske ne abun da ɗan uwanki ya gaya mini?"
"Abba ai ban san me ya gaya makan ba"
Abba ya gyara zama ya ce "Gaske ne, kin san in da wanda yake ta haƙilon nema yake? Nabila meye haɗinki da ɗan daba ne? Kina 'ya mace?"
Ta girgiza kai ta ce "Abba ya za ayi na haɗu da wanda yan sanda ma suka kasa kamawa, file ɗin shari'arsa kawai ya gani a ɗakina, kuma ba nawa bane ba, na barrister Habib ne, nima karɓa nayi na duba, ina dudduba yadda aka gudanar da shari'ar sa a wancan lokacin ne, an ce yayi shekara biyar a prison ba ayi masa shari'a, kwatsam kuma aka ce an sake shi, aka dawo ana nemansa sai nake jin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari, shi ne nake ta bibiya, ka san muna program da sumayya, so ina binciken cases makamantan nasa shi ne kawai, amma sai zargina yake yi, ni ban san meyasa ba"
Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce "To kai ka ji abun da ta ce, me zaka ce?"
Sam Nasir bai ji ya yarda da abun da Nabilan ta faɗa ba, amma ya ce "Shikenan Abba, tun da haka ta ce"
"Dan Allah ku daina wannan rigingimun, da ba haka kuke ba, naga tare kuke sharing working experience ɗinku, amma yanzu kuna nema ku lalata tsakaninku, ni ban ji dama arfa zata iya bin wani ɗan daba ba, tana ƙyamar irin wannan laifukan, dan haka dan Allah duk ku yi haƙuri Allah ya yi muku jagora, ya rufa muku asiri"
Nabila ce ta fara miƙewa ta amsa da Amin, ta fice tana hararar Nasir, shi kuma ya bi bayanta da kallo, sam bai yarda da ita ba.
Washegari aka dawo da motar Nabila, an gyarota fes har fenti an canza mata, ta ji daɗin dawowar motar nan, dama yawan zirga-zirgar nan ya isheta.
Ɓangaren sumayya ma, nata program ɗin da take gabatarwa a kan shirin siyasa, na an yi walƙiyya, yana ta jan dubban masu sauraro, sakamakon yadda take baje wa mutane komai, game da irin kuɗaɗen da gwamantin tarayya take bayarwa domin ayyukan raya ƙasa, ta kan ɗauki ƙananan hukumomin shiyya ɗaya, ta kawo kuɗin da suka samu na wata, na tarayya, na jiha da na ƙanan hukumomin, da iya ayyukan da aka yi musu.
Sai dai tun da ta zo kan na Indabo, a ƙalla tafi sati uku, program ɗin a kansa yake, dan sai da ta faro tun daga farkon tenure sa, yadda take hawa da sauka a kansa, zai tabattar maka akwai wata a ƙasa tsakaninta da shi. Yan siyasa da dama, sun kawo wa program ɗin hari, da neman a dakatar da shi, amma hukumar gudanarwa ta tashar suka tabattar da cewa an riga an biya su ɗaukar nauyin program ɗin, dan haka ba zasu dakatar ba, wanda bai gamsu ba, ko ya ji an yi masa sharri ko cin zarafin sa, to ya kai kotu.
Da safe Nabila ta fito da motarta, sai ƙyalli take yi, ta batta a kunne, ta shiga gida ta haɗo kayan breakfast ɗin ta, ta koma cikin mota, Viper ya kirata a waya.
Ta ɗaga ta ce "Hello V snake"
Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce "Kin fita aiki ne?"
"Ina ƙofar gida ne, yanzu zan tafi ka tayani da addu'a, yau zan kai kokenmi kotu"
Ya ɗan ja numfashi ya ce "Ki bi ta farkon layinku, wurin incomplete building ɗin nan, ina nan ina jiran ki"
"Ok sir, gani nan"
Ta ja motar ta ƙarasa in da ya ce mata, a wurin ta tarar da shi, ya tako a hankali, cikin nutsuwa. Ta zura masa ido tana murmushi ba tare da ta san tana yi ba.
Ya shigo ya rufe ƙofar, ta kalleshi ta ce "Good morning"
"Morning" ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya ajiye mata baƙar leda.
Ta ɗauka ta ciro abun ciki, baƙar riga ce, da sunansa a jiki Viper, da hoton maciji.
"Wow masha Allah, har an yi mini? Na gode sosai, wai waye yake yi maka rigunan nan?" Yayi shiru bai amsa mata ba.
Sai kuma ta ce "Sanyin Ac yayi maka normal ko na rage?" Kawai ya jingina da seat ɗin motar ya zuba mata ido.
Sai ta ɗan rikice ta ce "Menene? Ko wani abun ne?" Still bai yi magana ba.
Ji tayi tsigar jikinta na tashi, ta ce "Dan Allah ka gaya mini menene?"
"Ina jin ƙwarin gwiwa a kan shari'ar nan, wanda ke ki ka bani shi, and at the same time scared, idan rayuwarki ta salwanta saboda ni, ba zan yafe wa kaina ba, dan rayuwar ki kika saka a haɗari saboda ni, na zo ne in ce miki good luck"
Duk da ta takura da kallon da yake yi mata, tamkar ta nutse, ga wata fargaba da bata san ta mecece ba, amma ta dake ta ce "Allah yana tare da mu, in sha Allah zamu yi nasara"
"Allah ya sa, ko mun yi nasara ko bamu yi ba, ina da kyakykyawan tukuici gareki"
"Ni zuciyarka kawai nake so, shi ne tukuicin da nake so" haɗe rai yayi ya ce "You are not serious, ba zaki daina wannan shirmen ba ko? Wahala zaki yi ta sha kuwa, ba na kallon kowace mace mace idan ba jauhar ba, ki je ki samu wani ku daidaita" yayi maganar ba tare da ya kalleta ba, yana ƙoƙarin buɗe ƙofa ya fita, jikinta har yayi sanyi, idonta ya cika da hawaye" yayi saurin ficewa, ba tare da ya sake kallonta ba. A guje ta fizgi motar, ta bar wurin, wanda hakan sai da ya bashi dariya, dan ya san fushi ta yi.
Nabila tana tafe hawaye na zuba daga idanunta, duk ta ɓata kwalliyar ta, sai taga kamar zata yi nasara, kawai sai ya buntsure, gashi ita kullum ƙara son sa take yi so mai zafin gaske.
Da haka ta ƙarasa court, ta tsaya ta ƙara gyara fuskarta, sannan ta fita ta shiga cikin court ɗin.
Nabila ta nemi kotu, ta hana hukumar 'yan sanda kama Muhammad Al'amin Ibrahim, da aka fi sani da Viper, har sai an yi cikakken bincike a kan kisan kan da aka yi wa matarsa shekaru biyar da suka gabata, hakazalika yana neman hakkinsa, na tsare shi shekaru biyar ba tare da yi masa shari'a ba, a kan laifin da ba shi ya aikata ba. Ta gabatarwa kotu kwafin shari'ar da aka yi masa a baya.
Duk da ba ma a fara shari'ar ba, amma haka nan ta din ga jin tamkar ta kama hanyar sauke gingimemen nauyin da yake kanta.
Abun da Nabila bata sani ba shi ne, tuni aka kira Nasir, aka sanar masa da an ganta da wani, a wurin sabbin gine-gine da ake yi a unguwar, kamar yadda ya saka CID ta ko ina a kanta.
Ya shiga kitchen ɗaukar lemo a fridge ya tarar da wayar Nabila a kitchen tana ringing, ita kuma bata kitchen ɗin, ya ƙarasa in da wayar take, kiran ya yanke. Ya kalli wallpaper ɗin ta Hoton sunan Viper ne, da maciji a kan wallpaper da wani heart.
Ya saka hannu ya ɗauki wayar, wani kiran ya kuma shigowa.
Kawai ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa ya ce "Waye?"
"Viper ne, mai zamani
Ayshercool
08081012143
73
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Ina ma'abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, ƘARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A BAKU LABARI.
Cak Nasir ya ƙame, a daidai lokacin da Nabila ta dawo kitchen ɗin.
"Wa ka ce?"
"Sarai ka ji abun da na ce, kar na sake kiran waya, ka ɗaga mini, ka bawa mai wayar, zan yi magana da lawyer ta"
Hakan yayi daidai da shigowar Nabila da take tsaye a bayansa, ya waiwayo ya kalleta, ya miƙa mata wayar yana tsareta da idanunsa da ya zazzaro su, tamkar zasu faɗo ƙasa.
Ta saka hannu ta karɓi wayar, tayi ƙasa da murya, ta ce "V ka kashe ni"
"Shhh ki tsaya ki saurare ni"
Ta ce "Tom"
"Yaya zaki yi da batun shaidun nan? kin ce gayen nan yaƙi magana, ina so zan je in da yake da kaina"
"To ai ka ga ni ban san me ma zan ce ba, ban san wace hukumar ta ce ta kama shi ba, dole yan sanda zamu shigarwa koken su kama shi".
"Na fahimta, na san abun da zan yi, dama na zata zai yi magana ne, ki samu wani abun as shaida, amma na san abun da zan yi masa, zai yi magana ta ƙarfin tsiya. And am sorry for what i did, na san zan saka ki a matsala, amma hakan ka iya zama maganin wasu matsalolin naki, dole za a zo wurin nan, cigaba da ɓoye-ɓoye ba zai haifar da ɗa mai ido ba, no matter what it takes, duk tsanani da ƙalubalen da zaki fuskanta ki jure, da Allah na dogara, amma kekaɗai ce ƙwarin gwiwa ta, Please don't give up"
"Kar ka damu, in sha Allah I won't, i promise you that"
"Thank you" ya katse wayar, hankali kwance ta kammala wayar, Nasir ya zuba mata ido, yana jiran ta gama, ya ji wace ƙaryar za ta yi masa, kawai ya ga ta basar, ta cigaba da abun da yake gabanta.
Da ƙarfin tsiya, ya janyo kafaɗarta ya tsayar da ita tana fuskantar sa, ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari ya ji muryar Baba magajiya "A'aaa lalalalaaaaa me zan gani haka, a kul ɗin ka, kar ka kuskura fara me yayi zafi zaka dakar mini 'ya Nasir" tayi maganar tana nuna shi da yatsa, Nabila kuwa da gudu ta gudu ta ɓuya a bayanta, tana ƙifta idanuwa.
"Ammm baba magajiya, ki fita daga cikin maganar nan"
"Ban gane in fita daga maganar nan ba, zaka kassara mini ƴa ka ɗaga hannu zaka daketa, ƙarfin ka da nata ɗaya ne?" Ai tana rufe baki, ya ture baba magajiya ya danƙo Nabila ya fara janta.
Tirjewa ta din ga yi, tana zunduma ihu, tana a taimaketa zai kasheta.
Baba magajiya ta sake biyo su, tana yi masa masifar ya saki Nabila. Sai da ya kaita tsakiyar falo, sannan ya kalleta cikin ƙunar rai ya ce "Nabila umarni nake baki, a yanzu yanzu cikin gaggawa ki sanar mini ina wannan ɗan iskan ɗan daban yake, kafin na tafi da ke na kulle ki, Nabila wace irin mahaukaciya ce, kina iƙirarin ke mai gaskiya ce, amma kina take doka kina ɓoye mai laifi?".
"Ni ban taka kowace irin doka ba, bisa doron doka nake gudanar da aikina"
"Shut up, ki gaya mini in da yake, kafin na saka ankwa ke na tafi da ke, na je na kulle ki"
Nabila ta ce "Ka kulleni a nayi maka laifin me?"
"Tambayata ki ke sake yi saboda kin raina mini hankali, ko bayan wannan hujjar wata ki ke nema? Am disappointed on you, kin bani kunya Nabila, ban taɓa tunanin duk wannan haƙilon da ki ke yi, zaki iya cin amanar ƙasa ba, kuma ki ci amanata ba"
"Ban ci amanar kowa ba, ni ba maciyiya amana ba ce ba"
"Ba zaki yi mini shiru ba, sai na tattakaki tukuna? Ki na ɗiya mace daga gidan daraja da mutunci, amma ki zubar wa da kanki kima, dan ba zan ce mu ki ka zubar wa ba, ki gaya mini ina ce maɓoyarsa, kafin ke nayi arresting ɗinki"
"Kayi arresting ɗina like how, DSP lawyer ce fa ni, lawyer ma mai zaman kanta, ina da ikon kare duk wanda ya zo gabana ya nemi hakan, duk girman laifin da ya aikata kuwa, balle wannan da makauniyar shari'a kawai ake yi. Ba ka da ikon kama ni, dan ban aikata laifin komai ba"
Tuni yan gidan suka tattaru a falo, domin jin meyake faruwa, suke ta wannan uwar hayaniya da yammacin Allah.
Sai dai jin turka-turkar da ake yi, ya sanya su mamaki ba kaɗan ba, jin abun da Nabila ta aikata, gaba ɗaya sai suka haɗe mata kai, suka din ga jifanta da miyagun maganganu, na cin zarafi.
Mama ta kada baki ta ce "Ai na san a rina, an saci zanin mahaukaciya, ba dai major ya ɗaukaketa ya nuna ita ce ya a gidan nan ba, an zo dai-dai in da nake son a zo, ɗan sa da ya haifa bai ja masa abun kunya ba, wata a banza gashi ta jawo masa, Allah ya sa ba yawon ta zubar take yi ba da sunan aiki, ban da haka, ya za ayi ta din ga hulɗa da ɗan iskan gari da ake nema ruwa a jallo, ta ce shi zata kare mutumin da yayi kisan kai ɗan ta'adda".
"Allah ba zai nuna mini yawon ta zubar a rayuwata ba, da ni da 'ya'yan gidan nan, in Allah ya yadda, babu wanda zai yi yawon ta zubar"
"Maman ki ke gaya wa haka Nabila?" Yayi maganar yana nuna ta da yatsansa.
Ko a jikinta ta ce "Zata iya kallon sauda, ko su siyama, ta ce suna yawon ta zubar? Ko yi suke na san ɓoyewa zata yi ba zata faɗa ba, sai ni 'yar Allah ba ni da ba ita ta haife ni ba, ai na daɗe ina yi mata kawaici kai ma ka sani" Baba magaji sai haƙuri take bayarwa, Nabila kuwa bakinta yaƙi mutuwa, da sun faɗa take mayar musu, mama ta ce wa Nasir, ya rabu da ita ya jira major ya dawo, ya ɗauki duk matakin da yakamata a kanta, kar ya matsa tayi masa wani Sharrin amma duk abun da yakamata ayi mata na doka, a ɗauki mataki a kanta.
***
"Abdul, so kake sai baƙin ciki ya kashe ni, ya kashe mahaifinka, mu bar maka duniyar ka rayu kai kaɗai ko? Tun da aka ce masa an mayar da jafar amurka, hankalinsa yaƙi kwanciya, wataƙila hukuncin kisa ne a kansa, jininsa yayi mummunan hawa, an bashi hutu ma zaman majalisar nema yake ya gagare shi, kai ana ta fama ka samu ka zama deputy governor ɗin nan, yanzu ko maganar bikinka ka daina yi, yau an ƙara watanni uku a kan lokacin bikin, amma ko ka bibiya meyafaru ya ake ciki? Babu ruwanka saboda ka ajiye yar mutane kana lalata da ita, so kake sai asirinka ya tonu mu shiga uku baki ɗaya, da wanne ka ke son mu ji? Wancan case ɗin ko kuma naka da ake ta bibiyarka ana lallaɓaka ka ke rashin mutunci?"
Ya girgiza kai ya ce "Mummy, ba haka bane ba, wallahi tsoro nake ji na fito da rahama, na san babu lallai abun ya tsaya a iya bayar da shaida a kotu, ina tsoron daddy ya yi mata wani abun, kin san halin sa, idan kuwa aka kuma cutar da ita, ba zan iya yafewa kaina ba, saboda nayi nadamar abun da na aikata"
"Ka yi nadama amma ka ajiye musu yarinya, ka ke lalata da ita? Wace irin nadama ce haka?"
Ya ɓata fuska ya ce "Ni ajiyeta kawai nayi, ba lalata nake da ita ba"
"To yanzu dai na ji, amma tana ina? Ni ka gaya mini, nayi maka alƙawarin babu wanda zai cutar da ita, har mahaifin naka ma, ba zan bari ya cutar da ita ba"
Ya ce "Gaskiya Mummy na san lallaɓa ni ki ke yi, kiyi mini wayo, amma na san tsaf zaki bayar da ita"
Ta ce "Laaa ƙarya nake yi maka kenan Abdul?"
Ya girgiza kai ya ce 'To, zan dai dawo in gaya miki, amma ba yau ba, bari na tafi Asibiti zan je"ya tashi ya ɗauki jakarsa.
"Ba zaka je ka duba mahaifin naka ba?"
Abdul ya ce "Zan je, yanzu na kusa makara ne, kuma ina zuwa zai yi mini zancen yarinyar nan, sai na dawo tukuna" ya fice daga ɗakin.
***
Viper ya ƙurawa madaki ido, da duk yayi wani iri, babu wannan kwarjinin da ban tsoron da yake da shi, babu shaye-shayen ƙwayoyin da ya saba, gaba ɗaya sai tsufansa ya fito sosai da sosai.
"Madaki, yanzu na tabatta har labarin madaki ya shafe, Viper ba zai bar zuciyarka ba, ko dan wannan ƙafar da aka yanke, kodayeke taimakonka nayi, ni na fika imani, ba dan haka ba, wannan ƙafar cin jikinka zata cigaba da yi.
Na turo lawyer ta, ku yi magana, amma ka ƙi, ni ba ta taka nake yi ba, kai ka san kasheka ba wahala zai bani ba, da kai da muƙarabbanka, amma ba ta kai nake yi ba, zan yi amfani da kai ne, na dangana da Indabo, dan haka ka shirya yin magana ko baka shirya ba?"
"Ban shirya ba, kuma ba zan shirya ba, kayi kaɗan mai zamani, haryanzu ba ka kai in da zaka ga bayana ba, maƙiyina bai isa ya ga bayana ba"
Viper ya ce "Baya kuwa na riga na ganshi, tun da da hatimin sunana zaka mutu a gadon bayanka, na san duk abun da zan yi maka, ba zan huce ba madaki, ni zuciyata ka yi wa illa, amma zan iya kamantawa. Kar ka manta lakwari ma yana hannuna, sannan shi ya ji wuyar da ya shirya yin magana, dan haka ko ka yi magana, ko kar ka yi tare zata kwaɓe muku, idan yayi tamkar ka yi ne"
Ya ciro wani jan gari, mai fatsi-fatsi a cikin yar leda, ya ɗago wa madaki shi, ya ce "Da irin wannan, ku ka yi amfani wurin hanani kataɓus, ku ka yi mini illa ko?" Madaki yayi shiru, yana bin hannun Viper da kallo.
"Bari na yi maka amfani da ita, na ga wani irin hali na shiga kuma wane irin nishaɗi ka ji, lokacin da kake cin zarafina" Viper ya miƙe tsaye, Madaki ya zazzaro ido, amma Viper haka ya sheƙawa madaki garin nan.
A take kansa ya fara juyawa, ya shiga girgiza kansa.
Viper ya ce "Ina son ku ɗauke shi, ku kai shi kusa da tsohuwar dabata, in da yaran nan da yake cin zarafi yake yi wa kisan gilla, wanda ya sanya tsananin tsoronsa a zukatansu, idan dare yayi ku yasar da shi a can, gari ya waye su ganshi a wurin, da ƙafa ɗaya su tabattar da cewa alkadarin sa ya karye, ƙaryarsa ta ƙare.
***
Nabila na kwance, ƙirjinta na ta bugawa, jiran dawowar Abba kawai take yi, ba ta san me Nasir zai gaya masa ba, ba ta san a yaya zai karɓi maganar ba. Tana ta maimaita "la haula wala ƙuwwata illa billah" bacci ne ya fara fizgarta, ta ji tsayuwar motar Abba, wajen ƙarfe goma na dare, zumbur ta tashi ta tsaya, ta tafi window tana leƙe-leƙe, har wurin goma na dare, shiru ba ta ji an kira ta ba.
Ta ɗauki wayarta, ta kira Viper, bugu ɗaya ya ɗaga, ya ce "Ya ake ciki?"
"V am scared" tayi maganar tana fitar da numfashi cike da tsoro.
"Meye yake baki tsoron?"
"Ban san me Abba zai ce mini ba, tsoro nake ji, Abba bai iya fushi ba, bana tunanin zai fahimce ni cikin sauƙi, na shiga uku" tayi maganar tana fashe masa da kuka.
"Shhhhh, Abla" ta ji kiran sunan har tsakiyar zuciyarta.
"Mmm"
"Shi ramin ƙarya ƙurarrre ne, duk yadda ki ka kai ga ɓoyewa, dole sai ya fasu wataran, shiyasa na kawo ƙarshen zargin da yayanki yake yi miki. Haɗuwar da muka yi da ke, sai da aka gaya masa, yana bibiyarki ko ta ina tasa mafitar kawai yake nema. Ki nutsu ki cigaba da addu'a, babu abun da zai faru in sha Allah, you are my only hope as i told you before, idan ki ka karaya ni ya zan yi?" Yayi maganar cikin rarrashin da bata taɓa tunanin ya iya ba.
"Ba zaka gane ba, amma zan cigaba da addu'a, sai da safe" ta kashe wayar tana dafe ƙirjinta, saboda yadda yake bugawa.
***
P.A ne ya shiga bedroom ɗin Indabo, bakinsa ɗake da sallama, ya amsa masa ya ƙarasa ya zauna, ya ce "Barka da wannan lokaci"
"Barkanka dai P.A"
"Ya ƙarfin jiki kuma?"
"Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai, maybe gobe in Allah ya kaimu zan shiga Abuja"
P.A ya ce "Yakamata ka ɗan dakata da shiga Abujan nan?"
Ya kalli P.A ya ce "Saboda me? Hutuna ya ƙare ai"
"Ƙishin-ƙishin na ji, maganar kuɗin scholarship ɗin da na harkar sadarwa, balli na daf da tashi, EFCC zata bincike ku" zumbur indabo ya tashi zaune ya ce "Kai a ina ka ji?"
P.A ya ce "Majiya mai ƙarfi, amma ka kira shugaban marasa rinjaye, a wurin P.A ɗin sa na ji maganar, kuma ba jita-jita bane ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, P.A wai ya aka yi abubuwa suke ta taɓarɓarewa ne haka?"
P.A ya ce "Nima abun ya fara bani tsoro, amma ka dudduba ka bincika mu ji"
"Ai ni har bana son kiran waya, duk wanda na kira akwai kalar masifar da zai gaya mini. Kuɗin nan fiye da rabi duk a kan ƙoƙarin ganin jafar ya fito ne, idan ba hali sai na lallaɓa na mayar, amma zan yi magana da ministan sadarwar da na ilimin, mu tattauna, koma dai na saka su bincika mana".
"Bayan nan, mutane fa suna ta surut a kan program ɗin da yarinyar nan take yi, na walƙiyya wallahi mutane sun fara dawowa daga rakiyarmu, na rasa uban da yake ba ta wasu information
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 77 Chapter of 121