ki, sai ku yi magana".
Nabila ta ce "Kai sumy, ban da ni ki bari na je na same shi, ni da nake nema?"
Sumayya ta ce "Ya zo ya same ki is more safe, ba wanda zai kawo wani abu, kin san yanzu rayuwa babu tabbas mussman irin aikinmu".
Nabila ta yi murmushi ta ce "Hakane masoyiyya, na gode sosai, saura ɗaya aikin"
"Wanne kenan?"
"Waye indabo?"
"Kin ga ki raba kanki da indabon nan, wai me ki ke nema a kansa ne? Ba dai kin yi masa wulaƙanci kin ƙi gaishe shi ba, menene na bibiyarsa"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ba zaki gane ba, ki taimaka kawai"
"Nabila kamar kina ɓoye mini wani abu fa".
"Ba abun da nake ɓoye miki, mamakinki kawai nake yi, duk kin canza kina abu kamar mara gaskiya kwanan nan sumayya"
Dummm gaban Sumayya ya faɗi ta ce "Ban gane ba"
Nabila ta yi dariya ta ce "Kar ki manta fa ni lawyer ce, idan na so zan gane idan ma baki da gaskiya, don't mind me kawai dai na ga kina ƙoƙarin kawar da maganar indabon nan ne, shiyasa nake tsokanarki, am about to do something big, zan gaya miki menene daga baya"
"Nabila Please, kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba, ki raba kanki da duk wani abu da zai sake haɗa ki da Aminu Vipern nan, kar ma a cetare ku ke. Ki bar DSP yayi aikinsa dan Allah"
"Ni ba maganar Viper nake yi miki ba, case ɗin dattijon nan nake magana a kai, amma ki binciko mini maganar indabon nan, ko na binciko da kaina".
Sumayya ta ce "To shikenan na ji zan yi, amma ki san in da zaki din ga zuwa da abun da zaki din ga yi kin ji arfan Abba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ji sai ka ce wata uwata, to na ji sai anjima" ta kashe wayar tana murmushi, a duniya bayan Abba ba ta tunanin akwai wanda ya kai Sumayya damuwa da ita, da tsoron ta aikata wani abu, da zai janyo mata matsala.
Bayan sallar magariba, Murtala ya kirata a waya, ya sanar mata da ya zo, yana ƙofar gidan su.
Ta saka hijjabi ta fita, suka gaisa ya ce "Sumayya ta ce "Ki na nemana"
"Au ba ta yi maka bayani ba?"
Murtala ya ce "Tayi mini, daga bakinki nake son ji".
"Haka ne, ka ga wani case na samu, na wani dattijo, an yi framing ɗin sa, wai yayi wa wata yarinya 'yar aikin da yake gadi fyaɗe, na je na yi magana da shi, yayi mini bayani, ya ce ba shi bane ba, ɗan yayan matar gidan ne, so abubuwa da yawa are similar to rahoton da ka bayar kwanakin baya, shiyasa na ce bari na neme ka, ka ƙara yi mini bayanin yadda abun yake".
Murtala ya numfasa ya ce "Kin san duk abun da aka ce, harka ta manya ce, sai dai a lallaɓa a yi komai a ɓoye ko ba haka ba, an ce yaron nan ɗan manya ne, kar mu je ki yi wani abun da zaki sakamu a matsala fa"
Nabila ta ce "Uncle murtala, ba zan saka kowa a matsala ba, dattijon nan nake son na taimakawa, kunna mini recording ɗin matar, na sake ji".
Ya kunna mata recording, ta saurara tiryan-tiryan, Nabila ta ce "Uncle murtala, case ɗin dai ai wannan, ba shi ne aka ce Naja'atu Bunkure ta shiga case ɗin ba, ai da na ce zan shiga case ɗin yarinyar".
Ya ce "Shikenan, faɗuwa ta zo dai-dai da zama, amma dan zatin Allah don't mention my name".
Ta jinjina kai ta ce "Kar ka damu in sha Allah ba zan yi mentioning ɗin ka ba. Naja'atu Bunkure ko da me take yawo a kanta, sai ta gaya mini in da case ɗin ya tsaya, ka san ina station ɗin da aka fara case ɗin, aka ƙwace file ɗin daga hannuna, wai ba zan duba ba".
Haske su aka yi da fitilar mota, Nabila ta tura baki, tana kare fuskarta, Nasir ya gyara parking ɗin sa, ya fito ya nufo su.
Ta ce "Yaya sannu da zuwa" bai amsa mata ba, ya kalli murtala ya ce "Malam ya dai, ya aka yi?"
"Yaya idan saurayina ne, haka zaka yarfa ni dan Allah? Abokin aikin sumayya ne, muna tattaunawa ne a kan wani case".
Nasir ya sake tsuke fuska ya ce "Kuma da daddaren nan?"
"Eh, saboda shi ɓoyayyiyar shaida ne, da ba zan bayyana shi ba, ba na kuma son a samu trace, na wani ya ganshi, shikenan uncle murtala ka gaida gida"
Yayi wa Nabila sallama ya tafi.
Ta cigaba da yi wa Nasir mita, "Gaskiya yaya na fuskanci saboda kai wasu samarin namu suke tafiya, da haka za a aure mu, kana zare musu ido, kamar wasu 'yan ta'adda".
"Eh, gara a zare musu idon, su san nan ba wurin da za su zo su kawo wargi bane ba" kawar da zancen ta yi, ta hanyar bashi labarin case ɗin dattijon nan, da yadda aka ƙwace file ɗin.
Sosai ya din ga mita, har yayi alwashin rakata sake komawa station ɗin, a bashi tun da tana lawyer, dole a bata dukkan haɗin kan da take buƙata.
Bayan ta koma ɗakinta, ta din ga murmushi itakaɗai, abu zai case zai haɗa ta da Naja'atu Bunkure, "Sai na ga abun da ya ture wa buzu naɗi kuwa" sai dai walwalarta ta ɗauke, bayan tuno wa da Viper, kar ta shagala da ramuwar gayya a kan Bunkure ta sakankance ta gaza samo mafita a kan nasa case ɗin.
Tana buƙatar wanda zata tattauna case ɗin da shi matuƙa, amma ba ta ga wanda ya dace tayi maganar da shi ba. Dan ko da wasa ba zata tunkari DSP ba, balle sumayya tsfa zata ce za ta gaya wa Abba, dama ban da su biyun nan, ba ta wanda ya dace, ta sanarwa wannan gangancin da take shirin yi ba.
Sai dai kwana ta yi, tana tunanin ko yaya Viper, ya farfaɗo gaba ɗaya ya warware ko kuma yaya?
Washegari da safe, da DSP suka tafi station ɗin nan, a hanya yake sanar mata da an yi belin Liti, ta tambaye shi waye ya yi belin Litin, ya ce mata bai sani ba, waya kawai aka yi masa aka ba shi umarnin ya sake shi.
Nabila ta ce "Nigeria ƙasata"
Suka isa police station, Nasir ya nuna musu id card ɗin sa, sannan ya nemi su bashi file ɗin da Nabila ta nema, amma suka tabattar masa da an zo an karɓi file ɗin an mayar da shi babbar headquarter.
Nabila ta ce "No wonder, hakan ya sake tabattar mini da lallai wanda ya aikata laifin, ɗan manya ne, kuma ba dattijon nan ne yayi ba" ta cewa Nasir kawai su tafi dama ta san a zaman farko sai an aike da baba prison, kafin ta gama tattara hujjojinta.
Sai dai duk da haka, Nasir ya nemi a ba su in details, statement ɗin, da Asibitin da aka kai yarinyar, amma suka ce ba a ba su wannan umarnin ba, komai da komai yana babbar headquarter.
Suna tafe take ce masa "Kar ka damu yaya, zan baka mamaki ƙoƙarin da zan yi a kan lamarin nan, zan tattara hujjojina na shiga kotu" yayi murmushi tare da ccigaba da ba ta ƙwarin gwiwa, ya biya ya ajiyeta a wurin aiki sannan ya tafi.
Cak ta tsaya a harabar wurin, tana ƙarewa motocin kallo, ta tsayar da idonta a kan baƙin motocin da ta gani guda uku, sai dai ɗayar ita ce motar da ta din ga bin ta, har ta tsaya tayi knocking ɗin glass. Ta ƙarasa ta zagaye motar, ta sake tabattar da ita ce, ta jinjina kai ta shiga.
Ta je office ɗin ta, ta ajiye jakarta, ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib, a hanya ta ci karo da MD barrister Kabir da wani babban mutum, da ta taɓa haɗuwa da shi a office ɗin sa.
Cikin girmamawa ta risuna, ta gaishe su, suka amsa, Barrister kabir ya ce "'yar ƙwalisa in ji habib, an shigo kenan?"
"Eh sir, na biya neman wata shaida ne, ban samu ba ma, na taho"
Ya ce "Sai haƙuri, haka lamarin aikin dama yake, wataran nasara wataran sai haƙuri, na ji daɗi da na ga kina mayar da hankali yanzu kin rage kwalliya".
Mutumin ya zuba mata ido, yana ta murmushi kamar an yi masa kyautar kujerar makka, dan sai da ta faki idon Barrister kabir, ta galla masa harara, sannan ta yi gaba.
"Yaya Habib"
Ya ce "Yau kuma?"
Ta ce "Eh mana, yau baƙi muka yi ne?
Ya gyaɗa kai ya ce "Dama wurin nan ai kullum cikin baƙi yake"
"Wasu motoci na gani, wata farar mota ta waye?"
Ya ƙura mata ido sannan ya ce "Hala na samu demotion ne zuwa mai gadi?"
Tayi dariya ta ce "Am very sorry, ka san wani abu?"
"Sai kin faɗa"
"Ka san shi Allah, mai son bawansa ne, da kuma jin ƙan sa"
Barrister Habib ya ce "Wannan haka yake".
"A wannan karon, ba tare da na yi tsammani ba, akwai yiwuwar case ya haɗani da Najar bunkure, to kuma ka san ni yanzu kai ne mentor ɗina, na zo mu yi magana "
Yayi dariya yana mayar da wasu files, drower gabansa ya ce "Nabila 'yar ƙwalisa, haryanzu ba ki san wacece Bunkure ba ko?"
"And ba na buƙatar na sani, kawai i need your support, i want expose her hidden face to the world "
"How?"
Nan ta bashi labarin duk abun da yake faruwa, da case ɗin da yake hannunta.
Ya ce "Nabila"
"Na'am barrister yaya Habib"
Yayi murmushi ya ce "Zaki ga yaya, aradu ki ke shirin tara da ka fa"
"Na shirya mata".
"Tana da wanda suka tsaya mata matar nan "
"Ni ma Allah ya tsaya mini"
Ya jinjina kai ya ce "Kin gama magana"
Nabila ta ce "Yauwwa barrister, and i want you to support me, dan Allah ka taimaka mini"
"Ba ƙi nayi ba Nabila, matar nan manyan mutane da manyan ma'aikata sun kasa ja da ita, ke kin san ba haka nan take ba"
Nabila ta sake gyara zamanta ta ce "Support me, you will be proud of me"
Ya sauke numfashi ya ce "Duk abun da ki ke buƙata na taimako, ki yi mini magana kamar yadda na taimaka miki ki ga file ɗin Viper, zan cigaba da taimaka ki, amma ya zama sirri tsakanina da ke" tayi shiru tana kallonsa, ji tayi kamar ta yi masa zancen Vipern, sai dai a zuciyarta ta ji, ba ta gama amincewa da shi ba, kuma ba kowa za ta yi wa magana a kan case ɗin sa ba, dan haka ta yi murmushi ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi ya raya maka zuriya. Amma yanzu ya kake ganin za ayi? Office ɗin ta zan je, a kan ina son bayanai daga gare ta, da bakin yarinyar?"
"Eh mana, go as a barrister, ke ma lawyer ce, go with your full confidence"
Tayi murmushi ta ce "Na gode sosai ranka ya daɗe" ta juya ta fita cikin farinciki.
Sai dai kuma tunanin Viper ya cika mata zuciya, ko yaya jikinsa? Ya warware gaba ɗaya ko kuwa?
Ba tare da dogon tunani ba, ta ɗau jaka ta fita, ta samu mai sayar da fruit, ta sai uban kayan marmari ta tari abun hawa ta tafi.
Sai dai ta sha wahala, tana ta bulayi, ga uban kaya a hannunta, ta kunna Google map, yau sai ya fara yi mata hauka ta ce "Wai shi wannan ma anya ba aljani bane ba?"
Har ta fitar da rai, kawai ta hango roofing gidan, haka ta cigaba da tafiya, har ta isa ƙofar gidan.
Duk da tsoro da fargabar waccan shaƙar da ta sha, na neman kashe mata gwiwa, ta tsananta addu'a tare da neman kariyar Ubangiji.
Jin sallamar mace ya sanya gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, liti ya zabga ashar ya ce "Ke uban me ya kawo ki nan, munafuka macuciya?"
Ta ce "Ashe kuma ka fito"
"Ban sani ba, uban me ya kawo ki?"
"Wurin Viper na zo" ta bashi amsa kai tsaye. Ya tashi tsaye zai zare wuƙa, Walid ya hana shi, ya ce mata "Me zaki yi masa, kin manta abun da yayi miki ne? Ki bar taƙama da baya kisan kai, zai iya farawa a kanki, dan yanzu ƙwaƙwalwarsa sai a hankali "
Nabila ta ce "Shi ne dalilin sake zuwana, in ji ya jikinsa kuma na ji ƙarshen labarin nan"
Walid ya ce "Jiki yayi sauƙi mun gode, amma ki tafi kar ki sake zuwar mana, saboda zuwan da ki ke yi zamu canza wuri"
Liti ya fusata ya ce "Ke dalla fita"
"Ka daina hantarata, ba wurinka na zo ba. Ni dai ku taimaka ku haɗani da shi, yakamata na ji da bakinsa ya yafe mink"
"Ke! Ni ki ke gaya wa haka?"
Walid ya ƙara dakatar da Liti ya ce "Ya riga ya yafe mikin ai"
Ta girgiza kai ta ce "Ban ga alama ba, akwai buƙatar sama masa nutsuwar ƙwaƙwalwa kafin tunkarar duk wani abu, a ɗan zuwan da na yi, na fuskanci kuna amfani da ƙarfi wurin tursasa masa karɓar abun da ya zo masa a yadda yake.
Baku da raunin, da zaku tausasa masa yadda yake buƙata"
Walid ya ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda nake faɗa yanzu, a fara samo ƙwaƙwalwarsa, ta hanyar daidaita gangar jikinsa, da hana shi ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, a saita tunaninsa da tunatar da shi shi wanene, ko ba duka ba, ayi ƙoƙarin samar masa da wani abu na farinciki ko yaya, a gwada canza masa tunani ba ta ƙarfin tsiya ba, kuma a sama masa likitan da zai din ga duba ƙwaƙwalwarsa"
Walid ya ce "Taɓ, ke zaki iya duk wannan ɗin?"
Cikin ƙwarin gwiwa Nabila ta ce "Ku bani dama, na san kuma a ba a karon farko ya karɓe ku ya saba da ku ba".
Kafin wani ya kuma magana, ya turo ƙofa ya shigo.
Walid ya ƙure shi da ido, dan kar yayi wa Nabila wani abu, ko nuna ya ga mutum a wurin bai yi ba, balle ya yi wani abu, ya shige ɗakinsa ya nemi wuri ya zauna a kan katifa.
Babu fargabar komai, ta bi bayansa, tare da yin sallama a ɗakin, bai amsa ba kuma bai ɗago ba.
Ta je gabansa, ta durƙusa da gwiwoyinta a ƙasa, ta ce "Ranka ya daɗe, wurinka na zo fa" ya cigaba da 'yan dube-dube.
"Duk da na san, ba zaka amsa mini ba, amma na san kana ji na, wannan zuwan da na cigaba da yi, ina yi ne don neman afuwar kuskuren da na tafka bisa duhun kai, da rashin sani, amma dan Allah ka yafe mini ka yi haƙuri dan Allah" tayi maganar muryarta na rawa.
"Dan Allah ka yi magana, wallahi na kasa sukuni, a dalilin jahiltal abun da ya sameka, ban san haka abun yake ba, ka yi magana ka ce ka yafe mini please"
Still bai yi magana ba, sai dai ya ɗago ya kalleta, hakan ya sanya ta saurin cire idonta daga nasa.
Ya miƙa mata hannunsa ya ce "Bani"
Jakarta ta ɗaukko ta buɗe, ta ɗaukko wayarsa, ta miƙa masa, ya saka hannu ya karɓa, sannan ya ce "Sai da nayi kaffara a dalilin rantsuwa da na yi zan kashe ki, ban kashe ki ba, ki ka sake na sake rantsewa sai na aiwatar"
"Da kuwa ka ci amanar 'yar madara"
Ayshercool
08081012143
50
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin hanzari ya kalli Nabila, yana mamakin a ina ta san wannan sunan, dan sam bai san Walid ya gaya mata labarin sa ba.
Ya ƙureta da ido, ta kawar da kanta gefe, ta ce "Eh, idan ka kashe ni, ka ci amanarta, ta barka ka kusa dawowa hanya, amma ka koma ruwa fiye da baya. Zan so na ji ƙarshen labarinta, amma kafin nan bari na tafi yanzu, ga kayan dubiya nan na kawo maka, Allah ya ƙara sauƙi" sai da ta gama maganar sannan ta ɗago ta kalleshi, still ita yake kallo.
Ta sake cewa "Ina fatan zaka yafe mini laifin da nayi, rashin sani ne" ta tashi a hankali ta ɗauki jakarta ta fita, tana yi wa Allah godiya da wannan karon, ba ta sha shaƙa ba, hakan ya sa ta ƙara kin ƙwarin gwiwar cigaba da gwagwarmayar da ƙuduri aniya.
Bayan fitar Nabila, Viper ya ɗaga kai yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Walid ya ce "Ko ba ka yi magana ba, na san menene a ranka, ba kowa bane ba, ni ne nan na gaya mata labarinka".
Ya tsayar da idonsa a kan Walid ya ce "Saboda me?"
"Saboda dalili mai ƙarfi, cigaba da cusa kanta a lamuranka cikin duhun kai, tamkar ƙara yawan matsalolinka ne, zuciyar mace ta na da rauni, fiye da dukkaninmu, ina ganin hakan zai iya yi mana am..... Bai ƙarasa ba, viper ya katse shi ya ce "Ta yaya? Na ce ta yaya? Meye amfanin gaya matan, na gaya maka bana buƙatar cigaba da ganin yarinyar nan, sai an haɗa baki da ita an ƙara rusa ni kenan? Da raunin na su ake amfani a sarafasu a cuci mutum, halittu ne su marasa imani....
"Raunin 'ya mace, da tausayinta irin na halitta, kar ka manta shi ya jefa ka a cikin halin da ka ke ciki, idan mace ɗaya zuwa goma sun cutar da kai, ɗaya zuwa biyu sun yi maka abun da ba zaka taɓa iya biyansu ba, wanda tausayi da soyayyar da mace ta nuna maka, giɓin da ta bar maka ne, ya ƙara assasa tunzura zuciyarka ka ke fama da jinyar da muka rasa bakin zaren yi maka maganinta. Idan zaka yi adalci, ka yi musu hukunci da halin ƙanwata, Jauhar ko ba dukkansu ba. Yarinyar nan gaskiya ta gaya maka, idan ka yi kisan kai ka ci amanarta, wannan miyagun ƙwayoyin da ka ke ƙara ɗurawa kanka, su ma ba ka yi mata adalci ba".
Al'amin da ya ji maganganun Walid sun ishe shi, sai ya miƙe tsam ya sake ficewa.
Walid ya yi wa Ɗan mama inkiya ya bi bayan sa ya ga ina zai yi.
***
Ramma ce take dukan gefen fion da Abdul yake "Abdulyasar Abdul yasar" ya buɗe idonsa da kyar ya kalleta.
"Ka tashi ka yi sallar asuba, gari yayi haske, sallar ma baka yi" ya ja tsaki ya sake juyawa.
Ta sake cewa "Ka tashi gari fa yayi haske"
"Kin san jiya da daddare fa ban yi bacci ba, ki ƙyaleni"
Ramma ta ce "Haka ne kam, dama ba ka da lafiya, wataƙila a cikin baccin za a zare maka rai, ban sani ba ko kana da abun da zaka gaya wa Allah a kan rashin salla" kan ta rufe baki ya tashi zaune yana ƙifta ido.
Ta girgiza kai ta ce "Kai yanzu baka shirya wa mutuwa ba, ka ke rashin mutunci? Allah sarki ɗan Adam abun tausayi" ji yayi jikinsa yayi mugun sanyi, kamar mutuwar ce ke tunkaro shi, ya je ya yi alwala, ya fito ya tarar tana gyara gadon da ya tashi.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi da sauri, ya ɗauka, ya saka a kunnensa "Hello mummy"
"Kana ina ne?"
Ya ce "Ina gidana"
"To zuwa anjima ka zo gida, zaka yi magana da babanka, shugaban jam'iyya ya ce ka je ka ga 'yar sa, ku daidaita kanku, ayi magana dan ba za su yadda a baka takara ba, baka da aure".
"Haba mummy, aure kuma? Ni wai dole ne auren nan, a haƙura mana"
"Ban gane a haƙura ba, waye zai yadda ka yi deputy governor ba ka da aure, lallai ka zo anjima ku yi magana dama yana cewa ni nake hure maka kunne"
Abdul ya ce "Ba ni da lafiya fa"
"Ka sha magani ka zo, ulcer ce?"
Ya ce "Eh, kuma wallahi ina jin jiki, dan Allah ki bashi haƙuri zan zo ne"
Cikin damuwa ta ce "Ko na turo a ɗaukko mini kai, ba na son ciwon cikin nan naka fa"
Ya kashingiɗa ya ce "A'a, zan warware, idan na ji sauƙi zan zo, sai anjima zan ɗan kwanta" ya ajiye wayar. Tun da ya fara wayar, ramma ta ƙura masa ido har ya gama.
Ta ce "Ka ga banbancin rayuwar mace da ta namiji ko? Kaga duk abun nan da ka ke yi, kai an samo maka mata ni mecece makomata?"
Ya kalleta ya ce "Kishi ki ke yi ne?"
"Allah ya rufa mini asiri, na rasa a kan wa zan yi kishi sai kai, ka wulaƙanta mini rayuwa ka cuce ni, kai ka yi aure ka tara iyali, ni kuma babu wanda zai kalleni, ka yi mini fyaɗe ka mayar da ni ƙaramar karuwa, har ciki na ɗauka duk ta ƙazamar hanya ka wulaƙanta rayuwata"
Abdul ya zauna sosai ya ce "Ke ki ka fara wulaƙanta rayuwarki, da ku ka yi yinƙurin cewa zaku nemi hakkinku a kotu, alhalin ba zaku iya ja da ni ba"
"Sannu tsohon azzalumi, dama mai kuɗi shikaɗai Allah ya ce ya ji daɗi a duniya? Yanzu duk wannan abun taƙamarka kana da kuɗi ni 'yar talakawa ce? In sha Allah sai Allah ya ƙasƙantaka da kai da masu goya maka baya, suka tsaya maka kake rashin mutunci. Na san akwai ire-irena da yawa yaran talakawa da kuka zalunta, Allah ya na kallonku. In sha Allah sai Allah ya nuna maka iyakarka tun a duniya Abdul yasar"
Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi "Ko wanda ya raɗa mini sunan nan, bai kai ki iya faɗar sunan ba Rahama, Abdul yassar"
Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta ɗauka ba zata iya operating ɗin ta ba, kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira.
***
Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingiɗe, ya tashi zaune yana murmushi ya ce "Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni"
Tayi murmushi ta ce "Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki sosai da sosai, na san addu'a ka ke yi mini"
Ya ce "Kullum Addu'ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan lamuranki".
"Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba" Umma tayi maganar tana harar Nabila.
Nabila ko a jikinta ta ce "Abba dan Allah abu na zo roƙonka"
Ya ce "Ina jinki ƴar albarka"
"Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta haɗani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe kuɗin mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client ɗina charges mai yawa"
Yayi dariya ya ce "Nawa ki ka tara?"
Tayi shiru sannan ta ce "Ina da 400k"
Ya kwashe da dariya ya ce "400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta"
Cikin shagwaɓa ta ce "Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please"
"Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da sharaɗi ba na son yawon babu gaira babu dalili, kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba"
Cikin takaici Umma ta ce "Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin rashin adalci ne?"
Ya kalleta ya ce "Da walida zan saya wa mota, ba zaki faɗi haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da 'yar cikinku? Ku daina haɗa kanku da ita, kun san abun da nake nufi".
Arfa ta tashi ta ce "Abba sai da safe" ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce "Saura ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu".
Ta koma bedroom ɗin ta tana murna, ta ɗauki wayarta, Viper ya faɗo mata a rai.
Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a kunnenta.
Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ƙaƙƙautawa, har sai da ya hasala, ya ɗaga wayar, amma bai yi magana ba.
"Har na kusa fushi sannan ka ɗaga, na san da 'yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata ɗaga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 121