ta yi da file ɗin hannunta, ta faɗa jikin sumayya tana kuka.
Barrister Habib ya ƙaraso, ya ce "Haba Nabila, wannan ai sai ki saka ayi mana dariya, akwai appeal a gaba, dan Allah ki nutsu.
Cikin kuka ta ce "Sumayya mu tafi gida, ba zan iya sake haɗa ido da mutumin nan ba, i try my best, ai kun ga yanayin shari'ar da aka yi, dama haka aka koyar da mu, an bi Principles na law a wannan shari'ar?"
Sumayya ta din ga rarrashinta, suka sakata a mota, barrister Habib ya ce "Bari mu kaita gida, Bashir kai ka tafi da motata"
Suna tafe a mota tana cigaba da kuka, Barrister Kabir ya kira Habib, ya ce "Ya ake ciki ne?"
"Gamu zamu tafi, ba ta yi wining ba, sai kuka take yi"
Kabir ya ce "Ai dama na gaya mata, waye ya gaya mata jayayya da mutanen nan abu ne mai sauƙi?"
"Dan Allah kar ka saka ta sare gaba ɗaya, za mu yi appeal, kuma saboda ita nima zan yi abun nan kyauta fisabilillahi i really appreciate what she did" ya ajiye wayar yana cigaba da yi wa Nabila nasiha.
Bunkure ta ƙyaƙyace bayan kammala wayar da ta yi, ta kalli badi'a.
Badi'a ta ce "An kammala komai kenan?"
"Eh, an ƙarƙare shari'ar a yau, uba ya yi abun da ya dace, wallahi da bai yi wani yinƙuri ba, sakar musu zan yi su ƙarata daga shi har ɗan nasa, su ta shafa, amma a wannan karon dole na ɗauki mataki a kan yarinyar nan, da gaske so take yi sai ta tona mini asiri, dole zan tattauna da indabo, ya ɗauki mataki a kan ta"
"Amma kina ganin hakan zai yiwu, tun da abu ya shiga social media, kuma ta fara samun masu mara mata baya?"
"Iyayen gidanta ma, ba su kai ko ina ba, amma an ce mini an hangeta da barrister Habib, kuma ina kyautata zaton da saka hannunsa a wani abun da take yi, amma duk na san matakin da zan ɗauka akan dukkansu" ta ƙarasa maganar tana haɗiye ƙwayoyin da suke hannun ta, ta bi su da ruwa.
Nabila bayan sun kaita gida kuwa, ba ƙaramin kuka tayi ba, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya, komai ya fita daga kanta.
A ɗakin Nasir, ya sameta bayan ya dawo daga aiki, ko da ya tarar da Nabila ta sha uban kuka, tuntsirwa yayi da dariya, ya ce "Haba barrister, ina ƙwarin gwiwar ta ki? Har kin karaya haka?. Abun da na yi ta nuna miki kenan, nake gargaɗinki a kan ki fita daga sabgar nan, ba ke kaɗaice mai gaskiya a ƙasar nan ba, amma tun da ki ka ga kowa ya ja baki yayi shiru, to abun ya gagari kundila, amma ki ka ƙi ganewa ki ka cigaba da dagewa, ki gode Allah da ba su yi wani abu da za su taɓa lafiyarki ba ma" ya gama surutansa ya fita, ba ta ko kalleshi ba.
Yana fita ta mayar da ƙofa ta rufe, tana ƙoƙarin kiran Viper, wayar Alhaji wada ta shigo. Ajiye wayar tayi, ta ɗauki ƙaramar ta ta, ta kira Viper.
Bugu ɗaya ya ɗaga, kawai ta saka masa kuka.
"Meye ne?"
"Kana kallon wulaƙancin da aka yi mini a shari'ar nan, kaga wata irin shari'a da aka yi mai cike da wulaƙanci da zalunci, wallahi gaba ɗaya na karaya, na gaji da aikin nan, ina ji ina gani, mutumin da bai ji ba bai gani ba, zai tafi prison, zuciyata kamar ta fashe na gaji".
"To ni kuma wa zai tsaya wa tawa shari'ar?"
Nabila ta ce "I give up, na karaya" tayi maganar tana kuka.
"Ke kin isa? Ai tun da muka fara, sai mun kai ƙarshe, tied your belt against next trial".
"Ni ba zan iya ba, ina ga ma ciwon zuciya ya kama ni, duk na tsani komai, haka zamu cigaba da tafiya, mai kuɗi ne kawai ɗan gata? Ƙiri-ƙiri fa aka murɗe komai".
"Sai ki gyara, kar ki gaji, sai kin gama da ni tukuna, anyway an hukunta wanda ya aikata laifin, saura kuma ki matsa ki gano in da ramma take da mahaifiyarta"
"Wai kai wane irin mutum ne? Na gaya maka dattijon nan ba shi yayi laifin nan ba, kuma ni ina zan ganta?"
Ko a jikinsa ya ce "Wannan matsalar ki ce ai, ki ƙarasa wannan ki zo ki yi nawa"
Katse wayar ta yi, ta ajiye ta cigaba da kuka.
*****
"Lakwari, ka je ka samu P.A ɗin Indabo, ka gaya masa ni na aikoka, ya uzzura mini da kiran waya, a kan lallai sai na je, wai mai zamani ya yi masa aike, dan haka dolena na nemo masa shi, haryanzu ban sanar masa da halin da nake ciki ba, amma ka je, idan ka je wurin P.A ɗin, ka kira ni zam yi masa bayani".
"Shikenan, amma kana ganin ba za a samu matsala ba?"
"Ba za a samu ba, daga nan ma sai ka samo mana kuɗin zuwa asibitin nan, dan na tattara kuɗin hannuna gaba ɗaya na aika a kawo mana ganye, shi ma kuma na ji shiru, idan ka dawo daga wurinsa ka biya ka duba mana".
"Shikenan an gama"
***
Nabila kuwa ba a iya Nasir ba, hatta yan gidan suka sakata a gaba da tsokana, suna yi mata dariya, bisa yadda ta shiga matsananciyar damuwar rashin nasarar da ta yi, a kotu. Ba ta taɓa yin shari'ar da ta shiga ranta ba kamar wannan, gashi dai kyauta take shari'ar babu ko sisi, amma duk ta bi ta damu, hatta hawa social media ya gagareta, saboda yadda ake yi mata dariya, ƴan koren Bunkure ke cigaba da nuna cewar Nabila hassada take yi wa bunkure, kuma kwangila ta karɓo a hannun wasu.
Sosai ta fusata, ta hau social media tayi posting, ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin faɗa ne. Kuma ko bayan shekara dubu, sunan gaskiya baya taɓa canzawa, a saurari fitowa ta gaba.
Ɓangaren Nasir ma, yana fuskantar matsin lamba sosai daga wurin Indabo, da kuma manyansa a wurin aiki, a kan kama Viper.
Gefe guda ga fargabar abin da Nabila za ta janyo musu, tun da ita ba ta so a zauna lafiya, yana matuƙar fargabar Indabo ya yi mata wani abun.
Gaba ɗaya ta daina walwala, ko fitowa ta daina yi, sai idan fita zata yi, sai dai a kai mata abinci ɗaki a ajiye.
Ganin ta takura kanta da yawa, Nasir ya sameta yana rarrashinta, da bata baki a kan ta jure ta karɓi ƙaddara.
"Ba wata ƙaddara da zan karɓa" tayi maganar tana hura hanci.
"Ke saɓo zaki yi kenan?"
Nabila ta ce "DSP, abun da Allah ya hukunta shi ne ƙaddara, ba abun da mutum ya ga dama yayi da son rai ko son zuciya ba, ko da me matar nan take yawo, sai na tona mata asiri wallahi, gara ma ka ƙyale ni da wannan nasihar"
"Na ƙyale ki, amma idan kin ƙi ji, ai ba kya ƙi gani ba, tun gashi yanzu kin fara ganin ma, amma ba wannan ba, wai haryanzu babu wani news da ki ka samo a kan Viper ne? Na ga duk kin yi sanyi, kin daina taimaka mini"
Ta kalleshi ta ce "Ba dole na yi sanyi ba, ai dama ka ce na daina saka kaina a abun da babu ruwana, dan haka wannan ma babu ruwana da shi"
Yayi murmushi ya ce "Haryanzu a fusace ki ke arfa, to ba ni ne dai Naja'atu Bunkure nan ba, amma yakamata idan da wani hints a taimaka mini"
Ta kalleshi ta ce "Babu wani hints, ban san komai ba"
"To shikenan, idan kin huce sai mu cigaba da maganar" ta harare bayansa har ya fice.
Kasa samun nutsuwa ta yi, ta sake ɗaukar wayarta ta yi posting, "Idan har mahaifiyar ramma ba ɓata tayi ba, kuma da gaske Bunkure foundation na kula da ramma ne, to tana ina, al'umma yakamata su samu update a kan halin da take ciki, kuma shin suna da masaniya a kan ɓatan mahaifiyarta? Idan eh to ina tafi? Tana tare da 'yarta ne ko kuwa?" Tayi posting ta nemi wuri ta zauna, lissafi da tunani daban-daban suka din ga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Nabila.
***
"Indabo, yakamata fa ka sake matsa Abdul, ya gaya maka in da yarinyar nan take, hankali ya fara dawowa kanmu, yarinyar nan fa ta matsa, kuma ban ga alamar, zaka ɗauki wani muhimmin mataki a kan ta ba"
"Ya ce mini ya kasheta"
Bunkure ta ce "Ya kashe ta ta yaya? A binciken da na yi, an tabattar mini uwar yarinyar ba ta garin nan, tafiya ta yi babu shiri, kuma Abdul ya je gidan fiye da sau ɗaya, bayan ya ɗauke yarinyar, me ya je yi, ni fa ba na son a din ga gaba ana baya, kar asirinmu ya tonu fa"
Indabo ya numfasa ya ce "Abubuwa sun fara caza mini kai Naja, ga takarar Abdul da nake ta fafutuka, ga auren nan da ake shirin yi na shi. Ga ɓangaren ki taki matsalar, duk is a minus case, bababr damuwata yanzu Viper, aiken da ya yi mini ya tayar mini da hankali, idan ba a kama shi an kashe ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ga ƴan adawa sun sako mu a gaba, ga tunanin jafar da yake tsare na rasa wane tunanin ma yakamata na yi"
"Ai wanda ya fi muhimmanci shi zaka yi, wallahi idan aka cigaba da ƙyale yarinyar nan, muna raina abun da take yi zata bamu mamaki fa"
Ya jinjina kai ya ce "Na ga alama, kuma ba zan taɓa bari hakan ta faru ba".
P.A ne ya kaste su, ta hanyar yin sallama, suka amsa duk suka ɗago suna kallonsa.
Ya kalli indabo ya ce "Akwai matsala fa"
"Again?"
"Ƙwarai kuwa, madaki ne ya yi aike, wai ya samu rauni a ƙafarsa, yanzu haka ko iya tafiya ba ya yi, ɗazu ya turo yaronsa har ya buƙaci a bashi kuɗi ya je asibiti, amma wai duk wani abu da yakamata, yana da yaran da za su iya yi maka"
Indabo ya buga tsaki ya ce "Maganar banza kenan, zuwa yaushe zan cigaba da rarraba sirrina, wannan yayi mini aiki wancan yayi mini, kalli yadda haryanzu jarabar ɗan tahaliki ɗaya take ta ɗawainiya da rayuwata. Na gaji ya je Allah ya kyauta, na nemi wata mafutar"
"Amma kana ganin watsi da shi, ba zai zame mana wata ɓarakar ba ko barazanar ba?"
"Babu abun da zai zame mana sai wahala, tun da ba shi da wani amfani yanzu, Viper da na bari ya ci karensa babu babbaka, saboda yaron dodo ne, ina matuƙar jin tsoron abun da ya sani a kaina, kuma kamar yadda na yi tsammani, ya san abubuwan da idan yayi magana kashinmu ya bushe, dole fa a nemo Viper akwai matsala wallahi" yayi maganar yana zazzaro ido cikin tashin hankali.
Sai da aka kusa sati da yanke hukunci, sannan Nabila ta tafi wurin iyalan dattijon nan, tare da sake rarrashin su, a kan su yi haƙuri su ƙara mata lokaci, zata ƙara shiryawa sosai a appeal ɗin da za su yi, tana saka ran za su yi nasara in sha Allah.
Suka yi ta yi mata godiya, sai da zata tafi, ƙaninsa ya keɓe da ita, ya ƙara yi mata godiya, sannan ya ce "Dan Allah ki ƙara bincikar ɗan uwana, kamar fa ya san wanda ya yi laifin, barazana aka yi masa Shiyasa ya kasa gaya miki komai"
"Barazana kuma, wace irin barazana?"
Ya ce "Eh, akwai ziyara da na kai masa, ya gaya mini amma ya nemi kar na gaya wa kowa, ya san sunan wanda yayi laifin, da alaƙarsa da matar gidan, amma bai san ɗan waye ba"
Ta ce "Ya salam, to amma meyasa ni bai gaya mini ba, babu yadda ban yi da shi ba a kan idan ya san wani abu, ya sanar mini, amma ya ce mini babu abun da ya sani, sunansa ma bai sani ba, kawai dai ya san ɗan yayan matar gidan ne".
Ta ce "Subhanallah, shikenan zan san abun yi, a cigaba da yi mana addu'a"
Ya ce "In sha Allah, kullum cikin yi muku ake, Allah ya jiƙan magabata mun gode sosai da sosai".
Tana kan hanya saƙon Viper ya shiga wayarta, a kan yana son su haɗu.
Ji tayi kamar ta maze taƙi zuwa, amma ina, ba ta ji alamar zuciyarta zata bari ta aikata hakan ba.
Garden ɗin da suke haɗuwa, a can ta same shi, ta tsaya tana kallonsa ya rage sumar kansa, yayi kyau sosai.
Wata tab ta gani a hannunsa, cikin basarwa ta ce "Ina wuni?"
"Wayarki zaki bani"
Ta kalleshi ta ce "Wai baka san meya same ni bane? Baka jajanta mini rashin nasara da nayi ba, abu duk ya dame ni"
"Yanzu ki ka fara, idan har rashin nasara ba zai saka ki ƙara jajircewa ba, sai dai ki yi kuka"
Nabila ta ce "To idan ban yi kuka ba ya zan yi?"
Ya kalleta ya ce "Babu"
"Waye ya sai maka waya?" Yayi mata shiru.
Ta sake cewa "Haryanzu fa ina da tarin tambayoyin da baka amsa mini ba"
"Wanne daga ciki?"
"Meyasa Indabo ya ce zai yi maka tarko da ni ya kama ka? Ni meye haɗina da kai?"
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Wataƙila ya san kina zuwa wurina"
"To amma ya aka yi haryanzu bai kama ka ɗin ba? Kuma ni haryanzu kana ɓoye mini wasu abubuwa"
Ya saka ƙaramar wayarsa a kunnensa, ya ce "Ɗan mama ya ake ciki?"
"Oga Viper, mun ƙwamuso Lakwari fa, yanzu duk in da madaki yake, dole ya bayyana, tun da babu mai taimaka masa ko ya kula da shi"
Viper ya ce "Good job, zan gaya muku what next"
Cikin zaro ido Nabila ta ce "Viper kidnapping?"
"Eh ina son na sauƙaƙa miki aiki ne, shaidu na fara tattara miki, kafin a fara shari'ata, Madaki yayi jigatar da ba zai iya musa laifin da ya aikata ba"
"Amma ka gaya mini me ka ke yi da wayoyi? Ka daina yi mini ɓoye-ɓoye. Sai kin zo kan shari'ata zaki ji koma me ki ke buƙatar ji"
Kamar shashasha haka take kallonsa, gaba ɗaya ta ma rasa me za ta ce masa.
Ya miƙa mata wayarta ya ce "Angry bird"
"Am confused"
"Sorry"
Kamar ta sake fashewa da kuka ta ce "Zuciyata kamar a kurku, haka nake jin ta, mai laifi daban yana can yana rayuwarsa, mai karɓar hukunci daban, wane irin abu ne wannan?"
Viper ya gyaɗa kai ya ce "Kamar dai ni a kwanakin baya, idan aka kama mai laifi, sai ayi musanye a saki wancan saboda ɗan gata ne, ni kuma a tsare ni a matsayin mai laifin"
Ta ce "Kuma dai? Wani yayi laifi kai kuma a tsareka?"
"Mmm, a saka matata tayi ta yawo tana wahala ba, wata Shari'a sai a lahira, duk rintsi kar ki yadda ayi amfani da ke ki ci amana, ba kowa ne yake da zuciyar yafiya ba"
Jiki a sanyaye ta jinjina kai, ya ce "You can leave".
Kusan a tsukin lokacin, Nabila ta zama topic of discussion a social media, sai dai ba ta karaya ba, wurin cigaba da posting a kan bunkure foundation.
***
"Abdul tun muna shaida juna, ka gaya mini ina yarinyar nan take? Ka kashetan ko kuwa? Sannan uban me ya sake mayar da kai gidansu, bayan ka je ka ɗauki yarinyar, kuma saboda hauka maimakon ka saka ayi? Kawai sai ka wanke ƙafa ka tafi da kanka ka je ka ɗauki yarinyar, kamar baka san matsayinka ba? Idan ka san uwar yarinyar nan ma, tana tare da kai, ka gaya mini, na san matakin da zan ɗauka a kai"
Ya girgiza kai ya ce "Ni ban ɗauki uwar yarinyar ba, ban san in da take ba"
"Da ka kashe yarinyar yaya ka yi da gawarta?"
Abdul ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Ruwa na jefa ta"
Indabo ya ja guntun tsaki ya tashi, maganganun da bokansa ya gaya masa ne suke ta yi masa kai komo a zuciyarsa, wai dutsen da ya gaya masa zai ci karo da shi, lokaci yayi da shi bai san ya za ayi ba, dole ayi ɗayan biyu, ko dutsen yayi nasara a kansa, ko kuma su yi mutuwar kasko, amma babu yadda za ayi, ya iya maganin dutsen nan da kansa.
Nabila fa ta sake jajircewa, da cigaba da ƙoƙarin gano bakin zaren matsalolin da take tunkara.
Bayan shari'ar ramma, akwai shari'oi da dama a gabanta, amma wannan c ta fi ci mata tuwo a ƙwarya, sai kuma ta Viper da zata fuskanta.
Kasancewar da sassafe ta je wurin aikin, duk babu mutane, ta shiga office ɗin ta, ta ajiye jakarta, ta yi addu'a ta zauna, ta buɗe computer ta fara aiki.
Ƙaurin wayar wutar lantarki ta fara ji, ta ɗaga kanta, ba ta ga komai ba, ta sunkuyar ta cigaba da aikinta.
Wata irin ƙara wearing ɗin office ɗin ta yayi, ya fara ci da wuta, a razane ta tashi cikin tashin hankali, ta nufi ƙofa zata buɗe, ta ji an kulleta ta waje, ta jijjiga iya ƙarfin ta, amma a ƙofar a kulle gam, ga wuyar wuta sai cigaba da ƙara take yi wuta na kamawa tana tarwatsi.
Da ƙyar ta iya ɗaukko jakarta, ta ciro wayarta, tuni ta fara gani dishi-dishi, saboda hayaƙi, tari ya turnuƙeta.
Hannunta na rawa, lambar Viper kawai ta iya gani, ta danna.
Ya ɗaga wayar sautin tarinta ya fara ji, tana ta yi haɗe da haki, da ƙyar ya iya fahimtar ta ce "Wuta" daga nan ya ji ɗif
Ayshercool
08081012143
64
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin hanzari Viper ya tashi ya tsaye, yana cewa "Kina ina ne? Meyake faruwa?" Sai dai still shiru ba ta ce komai ba.
Su Walid ma duk suka miƙe tsaye, suna kallonsa.
Walid ya ce "Yaya meyafaru Viper?"
"Ki yi mini magana, kina ina meyake faruwa ne?"
Liti ya ce "Mai zamani menene wai?"
"Yarinyar nan tana cikin matsala"
"Subhanallah, to tana ina ne yanzu?" liti yayi maganar yana kallon sa.
"Safiya ce yanzu, ko tana gida, ko hanya ko wurin aiki. Babu yadda za a yi ace a gida ne wani abu ya same ta ta kira ni, da hanya ne kuma da tuni an kai mata ɗauki, ko dai an ɗauketa ne ko kuma tana wurin aiki, wuta na ji ta ce"
Hanyar fita Viper ya nufa, Walid ya riƙe shi ya ce "Ina zaka fita ka je? Ba kai yakamata ka fita ba, liti ko ɗan mama, ɗan maman ma dai, ka san wurin aikinta ai in da kuka ɗaukkota?"
Ya ce "Eh oga Walid"
"Je ka gano mana menene yake faruwa"
Ya ce "To bari na canza kaya"
Viper ya cigaba da bin layin Nabila yana kira, amma shiru ba ta ɗagawa.
Nabila kuwa tuni ta fice daga hayyacinta, ba ta sake sanin in da kanta yake ba.
Masinja ne da shigowarsa kenan, ya ga wurin ya turnuƙe da hayaƙi, ya shiga dudduba daga ina hayaƙin yake fitowa.
Cikin tsananin tashin hankali, ya nufi ƙofar office ɗin Nabila, ya din ga bubbuga ƙofar, amma ya ji ta a rufe gam, ya girgiza ya girgiza amma a rufe, ya fito ya nufi wurin masu gadi, ya na sanar da su wuta.
Suka tashi gaba ɗaya suka rankaya a guje, ɗaya daga cikin su ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nabila fa ta shigo aiki, tana ciki jama'a ku taimaka".
Nan da nan wuri ya cika da mutane, ana ta ƙoƙarin a ɓalle ƙofar a cirota, a daidai lokacin barrister Habib ya ƙaraso cikin tashin hankali, kasancewar an kira shi a waya an sanar masa.
Da kyar aka ɓalle ƙofar, wani irin huci mai ɗauke da hayaƙi ya buso waje suka ja da baya, wani matashi ne ya kutsa kai, ya na nemanta, ya hangota a yashe a cikin office ɗin ga jakarta da system ɗin ta, da wayarta a wurin.
Wutar ta mutu ba ta cigaba da ci ba, iya wadda ta kama ce ta haddasa hayaƙi, da huci mai zafi.
A kafaɗarsa ya saɓo Nabila, yana fitowa barrister Habib ya karɓi wayar da system ɗin, yayi waje da ita. A motar barrister Habib aka saka ta, suka nufi asibiti.
Barrister Kabir ma hankalin sa yayi mummunan tashi, ya din ga kiran waya, Habib ya ce masa sun tafi da ita Asibiti.
Gaba ɗaya hankalin ma'aikatan wurin ya tashi, dan duk jin kan Nabila da gayunta akwai girmama mutane, ga yawan kyauta da take yi musu.
Viper ya kasa zaune ya kasa tsaye, Liti da Walid ne suke ta rarrashin sa, amma ya kasa nutsuwa, sai cewa yake tafiya zai yi ya gano halin da take ciki, suka din ga kiran wayar ɗan mama, amma bai ɗaga ba.
Viper ya ce "Walid, ba zan lamunci a wannan karon wannan ita ma ta rasa ranta ba, dole fa na gano halin da take ciki"
Walid ya ce "Mun sani, amma ka fara bari mu ji daga bakin ɗan mama"
Suna tsaka da maganar ya kira waya, Viper ya fizge wayar daga hannun liti, ya ɗaga ya ce "Kai ana ta kiranka ka ƙi ɗagawa, yaya aka yi ka sameta?"
"Wuta ce ta kama fa a ofishin ta, lokacin da na je an buɗe ƙofar an fito da ita, za a tafi asibiti"
"Dalla ba wannan na tambayeka ba, tana ina yanzu a wane hali take ciki?"
"Eh, sun tafi kaita Asibiti, na bi bayansu a adaidaita sahu, an kaita wani ɗaki an hana kowa shiga, haryanzu dai ina asibitin, likitocin dai ba su ce komai ba, amma dai kamar fa ba ta da rai"
Ashar Viper yayi masa, ya ce "Yaya aka yi ma wuta ta kama a iya ofishin ta kawai? Me hakan yake nufi? Likitoci sun ce ta mutun ne?"
Ɗan mama ya ce "A'a ni nake tunanin hakan, bata motsi ko numfashi a yadda naga an sakata a mota wallahi da ƙyar idan ba mutuwa za ta yi ba"
Liti ya ce "Ɗan mama ko ɗan shegiya, gaba ɗaya yaron nan gaɓo ne, ya za ayi ka gaya masa wannan maganar?"
Walid ya karɓi wayar daga hannun Viper, ya saka a kunnensa ya ce "Ɗan mama kana ji na?"
"Eh oga Walid"
"Duk abun da ka ke ciki, ka din ga sanar da mu"
"To oga walid in sha Allah"
"Jikinta wutar ta taɓa ta ne?"
"A'a, ba ta ƙone ba, hayaƙi ne ya yi mata illa, wutar ma ba ta kama sosai ba"
"To shikenan, muna saurarenka"
Walid ya kalli idon Viper, yadda ya bayyanar da matsanancin tashin hankali.
"Viper, ka kwantar da hankalinka dan Allah komai zai zo da sauƙi, in sha Allah ba zata mutu ba, sai ta cika maka burinka"
Jiki a sanyaye ya ce "Walid yanzu shikenan duk wanda ya raɓe ni, rayuwarsa sai ta shiga hatsari, idan ita ma ta rasa ranta fa, jikina yana bani set up ne abun nan"
Liti ya ce "Kar ka zargi kanka, dama can wannan ba ta ji, kuma haryanzu ai bata fara shari'ar ka ba, balle ace saboda kai ne"
Walid ya ce "Ya isa haka liti, kai abu ba ya wucewa a wurinka"
"Yaushe zai wuce, tun da ta munafurce ni, ta saka aka kamani"
***
Abba kuwa Allah ne ya tsare bai yanke jiki ya faɗi na, bayan sanar masa da cewar, gobara ta kama a ofishin Nabila tana Asibiti.
Haka Nasir ma, cikin gigita da tashin hankali, ya nufi Asibitin da aka ce an kai Nabila.
Likitoci sun hana kowa ya shiga, an cire mata kaya an saka mata wata gown, ana duba jikinta ko da in da ta ƙone, amma babu, sai dai ga zuciyarta na bugawa, amma babu numfashi, idan tayi kamar zata yi numfashi, sai tayi ta tari, hayaƙi na fita ta hancinta da bakinta, sai tayi ɗif.
Gaba ɗaya Abba a rikice ya ƙaraso asibitin, cikin matsanancin tashin hankali Abba ya ƙarasa asibitin, zuwansa babu daɗewa Nasir ma ya ƙaraso, Abba ya nemi a bar shi ya ganta, amma aka ce ba a shiga likitoci na aiki tukuna.
Abba ya ce " 'ya ta ce, ko me za ayi mata ayi a gabana, idan ma ta mutu ne a bari na ganta, ai ni musulmi ne na kuma yadda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau" suna ƙoƙarin lallaɓa shi ya haƙura kar ya shiga, ya burkice musu, babu shiri aka bashi damar shiga wurinta.
A kwance ya tarar da ita, ana ta allurai, ya ƙarasa gaban gadon ta ya zuba mata ido, dama ya lafiyar kura balle ta yi hauka, an sha wahalar ciwonta na asma sosai da sosai, sai da ta girma ta ɗan samu sassauci, tayi gado mai wahala, dan mahaifiyarta ce mai ɗauke da ciwon ta gada.
Ya kalleta a kan gado, sai ya ga ta koma masa kamannin mahaifiyarta sosai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 67 Chapter of 121