Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
23 / 121
san matar mutum kabarinsa, mu'azzam bai yi mini komai ba, dan Allah a bashi haƙuri" Suka ce "To shikenan, Allah ya tabattar mana da alkhairi". Suka amsa da "Amin" Baba ya ce "Ku bani account number, na mayar muku da kuɗin auren" Ɗaya daga cikin su ya ce "A'a, a bar wannan maganar sai ya dawo tukuna, Allah ya basu zaman lafiya" Ya amsa da "Amin". Bayan la'asar yara duk suna islamiyya, babu 'yan aike, ta ce bari ta fita ta sayo maganin sauro, idan ya dawo sai ta gaya masa. A ƙofar gida suka haɗu da maman su halimatu a waje da wata maƙwabciyar su, suka gaisa ta ce "Maman halimatu, ba ku shigo mini mun gaisa ba haryanzu". "Wallahi Amarya, ba ƙi muka yi ba, kin sa yanayin mijin naki sai a hankali, abun da tsoro, kar wani abu ya faru". Ranta bai yi mata daɗi ba ta ce "Haba dai, ina ruwansa da ku? Kawai dai a shigo a gaisa, shikenan a gaida su halimatu" tayi gaba zuciyarta babu daɗi, a duk lokacin da ta ji an aibata shi, sai ranta ya sosu. Har dare ba ta sake ganin Al'amin ba, gashi ita ba waya ba, wasa-wasa har dare yayi babu Al'amin babu dalilinsa har garin Allah ya waye, bai kwana a gida ba. Sai abin ya fara damunta, gashi ba ta san a ina za ta ganshi ba. Abu kamar wasa, aka sake shafe wuni, aka shiga kwana na biyu, babu shi babu labarinsa, nan fa hankalinta yayi mummunan tashi, gashi ba ta san wa za ta nufa ta gayawa ba. Maman halimatu ce tayi sallama, Jauhar ta saka hijjabi ta fito tana murmushin yaƙe ta ce "Maman halimatu, sannu da zuwa shigo" "A'a ba shigowa zan yi ba, abbansu yana nan bai fita ba, bai san ma na shigo ba na ce kin kuwa san an kama mijinki?" Gaban Jauhar ya faɗi ta ce "Yaushe? A ina? Waye ya gaya miki?" "A bakin Abban su halimatu na ji, cune suka yi masa aka kama shi, amma dan Allah kar ki gaya masa wanda suka saka aka kama shi ɗin dan Allah, na gaya miki ne na san baki sani ba". Tuni idon Jauhar ya cika da hawaye ta ce "Eyya, meysa abban su halimatu yayi haka? Wallahi babu abun da zai yi wa wani, ba ruwan shi da kowa idan ba taɓa shi aka yi ba, ina aka kai shi? Dan Allah ki gaya mini, ina gidan ban san ina zan nufa ba ma". Tayi ƙasa da murya ta ce "Yana anti daba can aka kai shi". "Menene anti daba kuma? Ina ne?". "Can in da ake kai 'yan daba, ki shirya ki je ki duba shi". Ta ce "To na gode" bayan tafiyar maman halimatu, take ta ji haushin malam lawan ya kamata. Tayi tunanin ko gidansu za ta je, ta faɗa, amma sai ta ga idan tayi hakan, kamar ta tozarta kanta ne, dan haka ta fasa ta ɗora girki, ta gama ta shirya, ta zuba a flask, ta bi kwatancen da maman halimatu tayi mata. Su kansu yanayin jami'an tsaron wurin, tsoro suka bata, ba ta taɓa zuwa police station ba, ta gaishe su cikin girmamawa sannan ta ce "Dan Allah wani nake nema" "Wa kenan?" Wani ya tambayeta. "Al'amin sunansa" Ɗan sandan ya ce "Anya, babu wani mai irin wannan sunan da muka kama". Ta ce "Dan Allah nan aka ce mini an kawo shi, dan Allah officer ka duba mini" Na kusa da shi ya ce "Ko viper take nufi?" Ta ce "Eh shi, mai dogon zamani" "Ya aka yi me zaki yi masa?" "Wurinsa na zo, maƙwabciyata ta ce mini cune aka yi masa aka kama shi, wallahi bai yi komai ba". "Ke ya aka yi ki ka san bai yi komai ɗin ba? Wacece ɗin sa ke, ni tun da muke kama shi ma, ban taɓa ganin wani ya zo wurinsa ba, idan ba ire-iren sa ba ko yaran ubangidansa ba" Ta ce "Mijina ne" Saroro suka yi suna kallon jauhar, kyakywar yarinya ƙarama da ita. "Ke kuma auren soyayya ku ka yi? Jama'a kun ga matar Viper, yaushe ne kuwa zuwansa na ƙarshe aka fito da shi aka ce aure yayi" waiwayowa suka yi suna kallonta, ta sunkuyar da kai tana fatan Allah ya sa su bar ta ta ganshi. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ku fito da shi, ta ganshi, amma dai Viper yayi asara, daga aurensa ya saka 'yar mutane fara sintiri saboda shi". Saroro yayi da ya hangota cikin hijjabi, 'yan sandan suna yi mata tambayoyi. Tana ganinsa tayi ajiyar zuciya, ya ƙaraso gaban kantar ya kalleta ya ce "Me ya fito da ke?" "Kwana biyu baka nan, ban san in da ka ke ba, sai yau ban san kama ka aka yi ba" Ya sake kallonta ya ce "To ware ki koma" Jauhar ta ce "To in koma, kai fa ba sakinka za su yi mu koma ba?" Al'amin ya ce "Ki tafi na ce, kuma kar ki sake zuwa wurin nan kina mace, ware" haushi ne ya kamata, yadda yake korarta, shi ba ayi masa abun arziki sai hantara. Ta ɗora leda ɗuake da flask ɗin Abinci ta ce "Gashi abinci ne na kawo maka" sai da ya ɗan yi shiru yana kallonta. Tun da ya fara rashin jin sa, babu mai tunawa da shi, ya kawo masa ziyara ko abinci, idan ba su walid ba, sai kuma ita yanzu. "Ahh yau zamu ci girkin amarya, amma hajiya sai kin fara ci kafin ya ci" Bai saurari ɗan sandan ba, ya ɗauki abincinsa ya koma gefe. Ya buɗe, ta yi sauri ta zagaya, ta huda ruwa pure water, ta ce masa "Ka fara wanke hannunka" Kamar ya shareta, sai kuma ta zuba masa ya wanke, ya saka hannu ya fara cin abincin. "Akwai sauro ne wurin? Na ga kamar ya cijeka, jikinka duk cizon sauro?" "Mmm" ya amsa yana cigaba da cin abincin. "To yaushe zasu sake ka, kar ka yi rashin lafiya, saboda cizon sauro" shi dai yayi shiru yana cin abun sa. Ya gama ci ta bashi ruwa, ya karɓa ya zuƙe, ta ƙara masa wani ya shanye. Ta ce "Officer, to zaku sake shi? Bai yi komai ba" "Ke, da wiwi muka kama shi da ƙwayoyi, sai kuma ki ce bai yi komai ba? NDLEA zamu kai shi". Jauhar ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba in sha Allah, Master ka basu haƙuri su ƙyaleka mu tafi" miƙewa yayi tsaye, ya nufi hanyar komawa cikin ceil. "Officer to, idan na sayo maganin sauro da ashana, zaku bar shi ya kunna?" Gaba ɗaya sai ta basu tausayi, ya ce "Sayo" Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya ya waiwayo ya bi bayanta da kallo. "Viper, wai dan Allah ka bamu labari, wurin wani bokan ka kai 'yar mutane da iyayenta, suka aura maka 'yar su?" Shi dai ya ƙarasa ya koma cikin ceil, yayi zamansa, ba a jima ba, sai gata da maganin sauro, da ashana. Suka karɓa a nan kan kanta, suka ce ta tafi. "Dan Allah ku bari na sake ganinsa" "Ke wuce ki bar nan, da ki ka samu ma aka bari ki ganshi?" Ba ta karaya ba ta sske cewa "To ana bashi abinci? Ko ina kawo masa na dare ma" "Au uban wa ki ka ajiye da zai bashi abinci a nan? Ware ki tafi" Jiki a sanyaye ta ce "To, zan tafi ga wannan dan Allah officer ko buredi ku bashi" ta ajiye musu ɗari biyar sannan ta ce "Dan Allah kuma ku yi haƙuri, kar ku kai shi NDLEA, dan girman Allah in sha Allah zai daina, ba zai ƙara ba ma dan Allah" "Ki je ki kawo dubu hamsin, sai mu sakar miki shi" Tayi shiru, har ga Allah ba ta da ita, ba ta da dalilinta amma ta ce "To zan kawo, amma dan Allah kar ku kai shi, zan kawo muku in sha Allah" Ta fito daga wurin, tana tunanin ina zata nufa ta samo dubu hamsin a sake shi. Ayshercool 08081012143 23 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Tun da ta hau adaidaita sahu, tunani take yi, yaya za ta yi ta samu dubu hamsin ta kai, a sako shi. Ta san muddin aka kai shi NDLEA case ɗin tsayi zai yi, ba zata musa an ganshi da kayan maye ba, tun da yana sha. Ta koma gida tayi salla, amma abun duniya ya isheta, ta kasa ko cin abinci, tausayinsa duk ya cika mata zuciya, jikinsa yayi ruɗu-ruɗu da cizon sauro, gashi almu sun nuna ba abinci ake ba shi ba. Baba kuwa abun duniya ya dame shi, yadda ya ji kunya a idon iyayen Alhaji mu'azzam, ace sun kawo kuɗi sun gama magana, amma ya aurar da ita ga wani, ko gaya musu bai yi ba, ya rasa me yake yi masa daɗi, har sai da zakiyya ta fahimta ta ce "Baban su Saifu, wai lafiya kuwa? Tun da ka yi baƙi jiya, gaba ɗaya ka rasa nutsuwar ka" Ya sauke numfashi ya ce "'yan uwan Alhaji mu'azzam ne, suka zo suna bayar da haƙuri a kan jin su shiru da aka yi. Wai za ayi mata visa ayi auren a tura ta can" Waro ido tayi ta ce "Sai kuma ka ce musu me?". "Na aurar da ita" yayi maganar a sanyaye yana sake jinjina wautar da ya yi. "Ba a haka fa, sai ka ce musu Allah ne ya ƙaddara a hakan, amma akwai yayyenta, ko hafsa ba sai a maye gurbinta da ita ba, hafsa ba ta fi jauhar komai ba ma? Ai bai kamata a bari ya tafi haka ya tsallake gidan nan ba". "Zakiyya, kun saka na yi abun da yake damuna, na cuci 'ya ta ba gaira babu dalili, na aurar da ita ga mutumin da ba na kirki ba, na rasa yadda aka yi, lamarin nan ya faru, kunyar haɗuwa da jauhar ma nake yi, na kasa komawa gidanta, zuciyata zafi take yi mini" Zakiyya ta ce "Jauhar fa an gama babinta, sai a fuskanci 'yan uwanta, bai kamata a bari mutumin nan ya tafi haka ba" "Zakiyya, dan Allah ki bari na samu nutsuwa, ni ban san ma meyake damuna ba, dan Allah ki bari na ji da abun da yake damuna" Ta kwantar da murya ta ce "Babu wani abu fa da yake damunka, kai ne ka ke neman ɗorawa kanka matsala, amma komai mai sauƙi ne, idan ya dawo ba sai a lallaɓa shi a bashi Hafsa ba ya aura". Baba ya ce "Na ji, amma dai yanzu ki ƙyaleni" ya ɗauki hularsa ya saka ya fita. A tsakar gida ya tarar da su surayya, aiki duk ya kacame musu, aiki ba aiki, wanda da jauhar na nan, ita kaɗai take yi suna mimmiƙe kamar kifi a fridge. Suna ta yi masa a dawo lafiya, ya dawo da baya ya tsaya, ya kalle su ya ce "Surayya, kun je gidan ƙanwarku kuwa kun ganota?" Duk suka yi shiru, suka kasa amsa masa. "Yakamata ku je ku ga in da aka kaita, ita ma ta ji daɗ". Mama ta fito daga kitchen ta ce "A'a fa, ka san dai yadda mijinta yake, ba zuwa gidanta ne ba za ayi ba, kar mutum ya je ya illata shi". Yayi shiru bai ce komai ba. Jauhar kuwa kasa nutsuwa tayi, har sallar nafila tayi mussaman tana fatan Allah ya sa kar a kai Al'amin NDLEA. Duk yadda ta kai ga tunani, ta rasa mafita, bacci ya gagareta, a gidanma ya ta ƙare da sauro, ina ga shi da yake can, ta yi ta fatan Allah ya sa su saya masa buredin nan su bashi, sai kuma ta tuna ba ta bayar da kuɗin da za a saya masa ruwa ba, gaba ɗaya ta shiga damuwa, haka har garin Allah ya waye. Ta ji ƙarar babur ɗin malam lawan alamar ya fita, tana ta tunanin ko shiga za ta yi gidan, ta yi wa maman halimatu magana, ko akwai taimakon da za ta iya yi mata. Tana cikin tunanin, maman halimatu ta shigo, suka gaisa jauhar ta ce "Yanzu nake tunanin zuwa gidan wurinki". Maman halimatu ta ce "Yaya kin same shi ɗin?" "Eh yana can, sun ce na kai dubu hamsin a bayar da belinsa, amma wallahi bani da ita" "To yanzu ya za ayi?" Jauhar ta ce "Wallahi ban sani ba, shi nake ta tunani" "To ki kira gidanku mana ki faɗa" ta girgiza kai ta ce "A'a, daga yin auren sai na fara kai musu complain, a'a gara na rufa masa asiri na samu ya fito" "Aikuwa Jauhar sai ki yi tunanin in da zaki samo kuɗi". Tayi saurin cewa "Dan Allah ko akwai wanda zaki haɗa ni da shi, ya sai carfet ɗina?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh akwai wata dillaliya, kusa da titi gidanta yake" Cikin ɗoki jauhar ta ce "Mu je ki rakani maman halima". "Shikenan, amma Jauhar kina me ki ka auri mutumin nan, gashi daga aurenku kin fara wahala, da kyanki da ƙuruciyarki, kin auri wanda zai wahalar da ke". Jauhar ta yi murmushi ta ce "Maman halimatu ku daina aibata shi dan Allah, ku din ga yi mana addu'a" "To Allah ya kyauta" Jauhar ta saka hijjabi, suka tafi gidan dillaliya, sai dai bata nan, aka kirata a waya, ta ce sai yamma zata dawo, zata biya gidan maman halimatu, su je gidan Jauhar ɗin. Wunin ranar jauhar kamar ta yi hauka, saboda dillaliya ba ta zo ba, sai tunanin halin da yake ciki take yi. Sai wajen ƙarfe biyar sannan ta zo, ta ga carfet ta ce zata saya dubu goma. Maman halimatu ta ce "Haba sahura, wane irin dubu goma, bai fi sati biyu ba ca carfet ɗin sabonsa dubu kusan sittin ne fa". "To ku ɗauka ku mayar kasuwar mana, tun da an shimfiɗa ai ya zama taoho". Jauhar ta ce "Bakomai na yadda" ba ta da burin da ya wuce ta ga Al'amin ya fito. Sahura ta ce 'Saboda kin ban tausayi, na saya dubu sha biyu, bari na baki kuɗin. Maman halimatu ta ce "Wallahi sahura shiyasa da yawanku ba kwa arziki dillali, duk cuwa-cuwar ta ku, a tsiyace ku ke mutuwa" Sahura ta ce "Oho miki dai" Ganin ta fito da kuɗi da yawa, ya sanya jauhar shiga kitchen ɗin ta, ta ɗauko blender da set na tukwanenta masu kyau, ta cewa dillaliya su ma ta saya. Maman halimatu ta ce "Jauhar, idan 'yan gidanku suka gane kin sayar da kayanki fa?" Sahura ta ce "Wallahi uwar su halimatu ke 'yar baƙin ciki ce, ke kika saya mata?". Jauhar kamar ta yi kuka ta ce "To ya zan yi maman halimatu, bana son zamansa a wurin nan, sauro ma kawai ya ishe shi" Sahura ta ce "Allah sarki yarinya, Allah ya mayar da alkhairi, idan an tashi sayar da wasu ma ki kira ni" Da ƙyar ta bawa Jauhar dubu ashirin da huɗu gaba ɗaya. Wanda a ƙalla sun kai kayan dubu ɗari da wani abu. Ƙoƙarin nemo wani abun take, maman halimatu ta hanata, ta ce ta bari gobe ta je station ɗin, ta basu haƙuri ta ce musu abun da take da shi kenan. Jauhar ta ce "Ki na ganin za su karɓa kuwa?" "Za su karɓa mana, ai kin yi ƙoƙari" kamar ta janyo wayewar gari, ta din ga addu'a Allah ya sa su karɓa su sake shi. Da wuri ta gama komai, wurin ƙarfe goma da rabi ta fita, shi ma maman halimatu ce ta hanata fita da wuri, ta ce mata ba da wuri suke zuwa ba. Suna ganin Jauhar suka ce "Madam ya aka yi ne? Kin sake dawowa ganinsa ne?" Ta ciro kuɗin ta ce "Gashi dan Allah yallaɓai ku sake shi, sukaɗai na samo dan Allah ku yi haƙuri" Ya zuba mata ido ya ce "Shekarar ki nawa ne?" Ta ce "Na kusa shiga sha bakwai, dan Allah ku yi haƙuri" "To ai ba zamu iya baki belinsa ba, kin ga mace ce ke, kuma yarinya, Allah ya sa ya daina abun da yake ko dan saboda ke, karɓi kuɗinki, ba zamu sake shi a kan wannan ɗan kuɗin ba, kotu ma zamu kai shi" Kawai ta saka kuka, "Dan Allah ku yi haƙuri, ba zai ƙara ba dan Allah kar ku saka a kai shi prison" Ɗaya daga 'yan sandan ya ce mata "Yi haƙuri ki daina kuka, da wasa yake yi miki, an zo belinsa ma, ke ki ke tayar da hankalinki, ko mun kama shi zamu sake shi" Kasa daina kukan tayi, hannunta riƙe da kuɗin, wani ɗan sanda ne ya fito, da alama babba ne, bayansa kuma walid ne da Al'amin da wani mutum. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta zubawa fuskarsa ido, da take a ɗaure babu walwala. Walid ya ce "Kai Viper, wannan ce yarinyar da na tarar a gidanka, tayi mini rashin mutunci" "Wannan fa me aka yi mata take kuka?" "Sir, matar Viper ce" ya kalleta ya ce "Hajiya me aka yi miki ki ke kuka?". "Ce mini suka yi na kawo dubu hamsin za a sake shi, na kawo kuma suka ce mini wai kotu za su kai shi" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka cike da yarinta. Ya kalli 'yan sandan ya ce "Waye ya ce ta kawo dubu hamsin" "Sorry sir, dan ta daina zuwa aka gaya mata haka" Nan ya hau yi musu faɗa, suka din ga bayar da haƙuri, Al'amin kamar bai santa ba, yayi gaba. Da sauri ta bi bayansa, tana ta yi masa magana yayi shiru. Walid ya ce "Haba mai dogon zamani, ka tsaya ka saurareta mana" A fusace ya waiwayo ya hau ta da masifa "Ban ce miki kar ki sake zuwa wurin nan ba? Kin san suwaye ake kawowa wurin nan? Mutuncinki ne a ganki a nan?" Sai da ta ja da baya a tsorace ta rufe fuskarta, saboda razana da masifar da yake yi mata. "Wai Aminu meyasa ka ke yin haka? Da uban waye ya damu da kai, yake ta taka? Macen kenan haka zuciyarsu take, ko dan matar gidanku ba ta da kirki kowa ma haka yake?" Tsaki ya yi yayi gaba. Walid ya ce "Yi haƙuri mu je, rabu da shi ya ƙarata, kar ki sake tayar da hankalinki saboda shi" suka tari a daidaita sahu suka tafi gida. Da suka je gida, ta shiga gidan ta bar shi da Walid. "Aminu, dan girman Allah ka rage jaraba, kalli yadda duk ta rikice saboda kai, kar ka yi wasa da damar da ka samu, ka saka ta tsaneka dan Allah" Ya tsaya ya ƙarewa ƙofar gidan malam lawan kallo, yayi ƙwafa ya shiga gidan, ba tare da ya tanka Walid ba. Jiki na rawa ba tare da ta yi fushi ba, ta kawo masa tea da buredi. Ya gama baccinsa ya tashi, ya yi wanka, ya gama ya ga ta kafa masa ƙusar rataye soso a banɗakin, har zai rataye yayi tsaki ya yar da soson a kan sabulun ya fito. Ya canza kayansa ya fito falo, Satar kallonsa take yi, kamar ya ƙara kyau, kwana biyun da ya yi a tsare ba ya shan komai, kamar ya yi kyau sosai. Sai murna take yi ya dawo gida. "Ke!" Ta ɗago ta kalleshi. "Meye sunanki ne?" "Jauhar" Ya kalleta ya ce "Me? Angela?" Murmushi ta yi ta ce "Angela kamar wata mage,  sunana Jauhar" Guntun tsaki ya yi ya ce "A saka muku normal suna, sai dai a saka ƙaƙale-ƙaƙale da iyayi, ni ba zan iya ba" "To ka kirani da fatimata fatima zahra" wani irin zirrrr ya ji a jikinsa, fatima zahra, sunan mace mai girma da daraja a idonsa, Ummansa abar ƙaunarsa, duk da ba ta duniyar, amma idan ya ji sunan har wata tsuma yake yi. Ya maze ya ƙarewa falon kallo, ya fita tsakar har zai wuce ya kalli kitchen ɗin ta sannna ya ce "Zo nan" Ta fito ta ce "Gani" "Wa ki ka sayar wa carfet ɗinki da kwanukanki?" Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, yaya aka yi ya gane ko ya sani? Sai ka ce aljani? Ya ƙare mata kallo ya ce "Ina jinki, ya aka yi ki ka samu wannan kuɗin da ki ka kai? Ina kuma abubuwam da na tambayeki? Ki ka yi mini ƙarya kuma jikinki ya gaya miki" Kamar munafuka, haka ta zayyane masa komai. Bai ce mata komai ba, ya fita. Sahura na tsakar gida, tana hira ita da wasu coustomominta, kawai ta ga wasu irin zaratan matasa su uku, a tsakiyar tsakar gida da manyan gorori kamar za su farauta. Ta tashi ta ce "Lafiya malam? Me ku ka zo yi mini a gida. Wannan ai.... Haɗiye maganar tayi, da ya sako ƙafarsa cikin isa tsakar gidan. Yana shigowa idonsa ya sauka a kan carfet ɗin, a shimfiɗe a falonta. Ya ce "Liti, ku naɗo mini carfet ɗin nan" Ta waro ido ta ce "Malam lafiya?" Walid ya zaro wuƙa ya ce "Ki ka kuma magana, sai kin ɗaware daga sararin nan yanzun nan" daga ita har sauran matan, suka hau tsuma. Kamar abun banza, suka din ga yi mata cilli da kujeru, suka naɗo carfet. Viper ya ce "Dubu sha biyu ki ka saya ko?" Ta jinjina masa kai. Ya ce "Ɗaukko mini sauran kayan da ki ka karɓa a wurinta" jiki na tsuma ta shiga ta kwaso su. Ta ajiye masa a tsakar gidan, ya ce "Ɓarauniyar zaune, daga yanzu ki san abun da zaki din ga saya, ban da a nutse na zo miki, sai na saka an zana miki awarwaro a hannu, yadda gobe ba zaki sake zalunci ba. Liti ba ta kuɗinta". Liti ya zaro kuɗi zai bata, Al'amin ya ce "Wait, ta riga ta shimfiɗa a ɗakinta, ka cire dubu uku a kai, sannan ka sake cire dubu biyu zan cika ku wanke mini carfet ɗin ku kai mini gida. Haka kuwa aka yi, suka cilla mata kuɗi, suka kwashe kaya suka tafi. Jauhar ta na yi wa wasu stone work, dan kuwa matar ta fara kawo mata kayan tana yi, hakan yana ɗebe mata kewa. Ba ta yi aune ba, ta ganshi a tsakiyar falo, hannunsa da kaya, ya dungurar mata da su a tsakiyar wurin ya ce "Daga yau, ko cokali ki ka kuma sayarwa, saboda ni sai na ɓata miki rai, fiye da yadda ki ke tunani" Baki buɗe ta ce "Master, karɓowa ka yi, kuɗinta suna wurina fa, Allah zai kaman..." "Na ba ta kuɗinta, ko tsintsiya ki ka sake sayarwa, zan gane kuma ranki sai ya ɓaci". A hankali ta ce "Na shiga uku". *** Matasa ne a ƙalla su biyar, dukkanin su, babu wanda ya gaza ko ya wuce shekaru ashirin da biyu, suna sanye da tufafi masu nuna datti, gashin kansu da yanayin fuskarsu kuwa, babu tambaya sun bayyanar da tsantsar rashin ji a tattare da su, sai bushe-bushe suke yi, suna shewa. Wani matashin ne ya diro ta saman katanga, gaba ɗaya suka nutsu, suna yi masa sannu da zuwa. "Kai gayu akwai matsala wallahi" gaba ɗaya suka tattara masa hankalinsu suna sauraren sa. Ya ce "Kaii, wai ashe mai zamani ne ya tare a unguwar nan kusan sati biyu bamu sani ba?" Ɗaya daga cikin su ya miƙe ya ce "Ƙarya ne wallahi, me yake yi mana a unguwa". "Nustu, ni ma ban sani ba sai ɗazu, mai unguwa na ji yana maganar, sai za su je police station, ko a sasanta ayi zaman lafiya da shi, ko ya bar unguwar nan". Ɗayan ya yada sigarin hannunsa ya tashi ya ce "Guduma gaskiya kar dagus ɗin ka ya janyo mana matsala, ya san waye mai dogon zamani kuwa?". "Guys mafita ɗaya ce wallahi, kun san ba a sarki biyu a zamani ɗaya ko?" "Me ka ke nufi?" Guduma ya ce "Dole ɗaya ya bi ɗaya" "To waye zai bi wani?" "Kwanciyar hankalinmu da nustuwarmu, shi ne mu yi mubayi'a, samunsa ma a unguwar nan wani security ne, zai sa a din ga jin tsoranmu" Wani matashi ya ce "Ƙarya ne wallahi, babu wanda ya isa ya zo unguwarmu mu yi masa mubayi'a ba a isa ba". "Kai Kwano, bari na yi maka wani lissafi, duk sarkin da ya zo garinka ba da ziyara ba, ya shafe awanni arba'in da takwas, a irin harƙallarmu, to ɗayan biyu, ko dai ɗaya ya bi ɗaya, ko kuma a yaƙi juna, a kama sarki ɗaya da mutanensa a matsayin ganimar yaƙi, mu rayu a matsayin bayinsa, harƙalar da Mai zamani yake yi, ta ci uban tamu, ba sa'anmu bane ba, mu yi abun da ya dace, idan kuma mu ka bari rigima ta ɓalle, wallahi a unguwar tamu, zamu rayu kamar bayi ne amma ku yi tunani". Can Al'amin kuwa yana zaune a station, ga mai unguwar da yake da sauran mutanen unguwa. Yana zaune yana kallonsu, suna ta ɓaɓatun gaskiya ya tashi ya bar musu unguwa, saboda bad record ɗin da suka samu, a kansa daga in da ya baro, kuma

Chapter 23 of 121