Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
50 / 121
ki ka yi mini bayani, na saka aka kama, ta tabbata yaron Aminu Viper ne, amma riƙaƙƙen mara mutunci ne, ya ƙi magana, duk wani nau'i na tuhuma an yi masa amma ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi magana". Nabila ta ce "Ikon Allah, bai faɗi in za yaken ba kenan?" Ya girgiza kai ya ce "Bai faɗa ba. Amma muna nan muna trying, alamu sun nuna ya sani, ɓoyewa yake yi. Yauwwa yanzu gaya mini me ki ke son ki gaya mini lokacin bana nan" Tayi ajiyar zuciya ta ce "Nothing much, dama dai duk a kan case ɗin nan ne, na ce me zai hana ka bibiyi case ɗin daga tushe, misali daga gidansu, iyayensa mutanen kewayen da ya zauna da su". "Me hakan zai amfana?" Yayi maganar yana kallonta. Ta ce "Kawai ji nake kamar akwai lauje a cikin naɗi, a kan sha'anin Aminu Viper, kamar abun da aka baka a kansa is not complete, something is missing, yakamata a fara samo full details na abun da ya faru". Ya girgiza mata kai ya ce "Duk bani da isashshen lokacin yin haka, na yi ƙoƙarin yin hakan, aka ce ba shi aka sakani ba, kuma duk maganar nan da ki ke yi is a very long way, gara shortcut, idan ya zo hannu muka gama da shi, kotu zamu tura shi, a can ne aikinki yake idan ma tssya masa zaki yi" tayi murmushi ta ce "Hakan fa zai iya sawa na yi suna ko?" Yayi dariya ya ce "Ke dai kin damu da maganar yin sunan nan, gaba ɗaya kin canza, ko dai haryanzu jikin ne? Gaba ɗaya kin rage ɗokin case ɗin Vipern ma, ko akwai wani abu ne ki gaya mini " ta girgiza kai ta ce "Babu komai" Ya ce "Are you sure?" Ta jinjina masa kai, ya tashi tsaye ya ce "Ban yarda iya abun da ki ke son gaya mini ba kenan, akwai abun da ki ke son gaya mini ki ka fasa, amma da sannu zan gano menene da kaina" Shiru kawai ta yi tana murmushi ya fita, yana ƙoƙarin fita daga falon, ya ci karo da mama, sai da ya ɗan tsorata ya ce "Mama" "Me ka ke yi a ɗakinta da daddaren nan?" Tayi maganar rai a ɓace. Ya ce "Subhanallah, dan Allah mama kar ki kawo komai a ranki, muna magana ne a kan aiki... "Rufe mini baki, aikin banza da na wofi, sai ubanka ya farga ya fara yi maka terere a cikin gidan nan ko, kana zuwa ɗakinta da daddare, ka dai san ita ba zai tagayyarata ya nuna laifinta ba sai kai. Duk lokacin da na yi ƙoƙarin fahimtar da kai, irin wannan abun ba ka gani, daga dawowar ka, zaka fara sakani magana saboda wannan sheɗaniyar yarinyar ko Nasir? Ka cigaba ban ce ka fasa ba" ta nufi ɗakinta ta bar shi a tsaye a wurin saroro yana kallonta. *** Ramma tana kwance ta sha kuka har ta gaji, tunanin halin da mamanta take ciki kawai take yi, ta san tana can hankalinta a tashe, tana faɗi tashin neman in da take. Ta gaji da kwanciyar, ta ɗauki ruwan da yake ajiye, a kan side bed, ta sha fiye da rabi, saboda maƙogwaronta duk ya bushe, saboda kukan da ta sha. Ta kwanta tana jiran bacci ya kwasheta, amma bacci ya gagara, sakamakon wani irin yanayi da ya din ga bijiro mata, har wani irin gumi take yi, ta tashi cikin matsananciyar damuwa, amma ta rasa takaimaimai meyakamata ta yi. Ta nemi wuri ta kwanta, ta takure, tana ta mamakin wannan wane irin abu ne haka. Abdul ne ya shigo yana fito, tayi shiru ba ta motsa ba, ya nemi wuri ya kwanta a bayanta. Ba ta yi masa tashin hankali ba, ko ƙoƙarin yin gardama ba, babban abun da ya ɓata mata rai, ya sanya ta ji tamkar ta kashe kanta, bai wuce yadda ta iya biyewa Abdul ba, ta tabatta mazinaciya!. Kuka take yi iya ƙarfinta, har da sheshsheƙa ko a jikinsa, kaɗa ƙafa kawai yake yi, daga baya ya tashi zaune yana kallonta, yayi dariya ya ce "Ba dai ke taurin kai ba, ai na san maganinki, you are very healthy and unique, zaki yi mana baƙin ciki. Ba kya buƙatar komai kan ki yi functioning lafiyayyiya ce ke, amma tsinanane taurin kai irin na ɗan ƙauye ba zai bari ki yi abun da ya dace ba". Ya ɗago wata ƙwaya ya ce "You force me to use it on you. Idan ki ka bari muka cigaba a haka ke zaki sha wahala, dan zata iya cutar da ke, aikin gama ya riga ya gama ba wani sauran amfani da zaki yi, ni ban ga abun ƙi ko damuwa ba. Na aika a gaya wa babarki ta daina nemanki na ajiye mata ke a in da ya dace". Cikin kuka ramma ta ce "Ba zan taɓa yafe maka ba, Allah ya isa, mazinaci mugu". Ya ce "Mazinata dai har ke" "In sha Allah ba zaka gama da duniya lafiya ba" Ko a jikinsa ya ce "Idan Allah ya nufa na gama da ita lafiyan, sai ki hana ai" ta cigaba da kuka, shi kuma ya juya ya hau bacci. Ta bi shi da kallo, ba ta tunanin ko wankan janaba yana yi, sai da tayi mai isarta, ta tashi ta yi wanka, ta saka wata jallabiya, ta leƙa fuskarsa, ta ga bacci yake yi sosai. Ta lallaɓa ta fita daga ɗakin, ta fara laluben ƙofar fita, sai dai ta nemi hanya ta rasa. Ko ina a rufe ta girgiza manyan ƙofofin, amma ko motsi ba sa yi, ta zauna a falo, ta cigaba da kuka, ta din ga jin haushin karnuka, tsoro yakamata, ta tashi ta koma bedroom ɗin, ta tarar da shi a zaune yana danna wayarsa. Ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa. "Idan ki ka kuma yinƙurin guduwa, sai na bar garin nan da ke, ba garin nan ba kawai, zan iya barin ƙasar nan da ke, babu wanda zai sake jin ɗuriyarki, gara ki shiga hankalinki". "Ai ba zan tabattar da kai tabattacen azzalumi bane, sai ka rabani da duniyar" ya kalleta, kamar ba daga bakinta maganar ta fito ba. Duk a yawon barikinsa, babu karuwar da ta isa ta ci masa mutunci ko ta zage shi, amma a garin kwashe-kwashensa, ya kwaso 'yar mitsitsiyar yarinya tana cin zarafin sa, yayi mata shiru, yana jin ta tana yi masa Allah ya isa ƙasa-ƙasa har da Allah ya tsine masa, amma ya shareta, tun da yau ya samu abun da yake so. Nabila tana office ɗin ta a zaune, tana ɗan danna system, sai dai hankalinta ba a kan system ɗin yake ba. Aka danna ƙarrarawar office ɗin, ta bada umarnin a shigo, matasan matan nan ne, wani masinja ya rako, ya ce "Hajiya Nabila, ga baƙi kin yi" Ta ce "To na gode sosai. Bisimillah ku zauna" suka zauna tare da gaida Nabila. A kallo ɗaya zaka ga Nabila ta yi kalar mata masu izza da jin kai, amma kuma kana zama da ita zaka ga saɓanin hakan. Suka gaisa ta ce "Jiya ina sauri zan fita, mun fara magana bamu ƙarasa ba, duk da yau ɗin ma ina son fita ne" Ɗayar ta ce "Ai mun gode ma saurarmu da ki ka yi. Lauyan gwamantin sai yawo yake yi mana da hankali, aka ce mu ɗaukar wa baban lauya mai zaman kansa kawai, mun zata abun mai sauƙi ne, ashe yafi ƙarfinmu". Nabila ta yi musu tambayoyi, ciki har da in da aka ajiye mahaifinsu, ta yi musu alƙawarin za ta je da kanta, ta tattauna da shi, za ta bibiyi komai, kafin a shiga zaman kotu. Suka yi ta yi mata godiya, ta ce "Kar ku damu, ku bani lamabar wayar da zan iya samunku" Suka bata, ɗayar ta ce "To ƙanwata nawa ke zamu baki?" Nabila ta ce "Karku damu, ku yi mini addu'a kawai, akwai abun da na saka a gaba, Allah ya sa na yi nasara baki ɗaya, da case ɗin ku da ɗaya abun da na saka a gaba" da suka fara yi mata addu'a, sai da ta fara jin nauyinsu, dan tamkar ta yi musu bushara da mahaifinsu ya fito, suka hau yi mata hira da labarin yadda sunan mahaifin na su ya ɓaci, a cikin unguwa. Tayi ta basu ƙwarin gwiwa, da tabbacin da yardar Allah za su yi nasara. Bayan tafiyarsu, kawai ta yi wani tunani, ta ɗauki jakarta ba ta zame ko ina ba, sai wurin aikin sumayya, ba ta tarar da ita ba sai Lawisa, sai zuba iko take tana hura hanci. Nabila ta yi murmushi ta ce "Anty lawisa, Sumy ta shigo kuwa?" Ta ɗaga kai da ƙyar ta kalli Nabila ta ce "Eh" "Tana ina?" "Recording take yi". Ta ce "Ok, bari na jirata a nan" tayi maganar tana ƙoƙarin zama. "No please, ba na son takura, ko zaki jirata a reception?" Nabila ta ce "Ba zan iya zaman reception ba, kujerun ba su da daɗin zama a nan zan zauna" tayi maganar tana zama a kan kujerar office ɗin. Baki buɗe lawisa take kallon Nabila, ta maze ko a jikinta, ta na danna wayarta. Ta kalli lawisa ta ce "A kan kujera kawai na zauna, ba hira na ce mu yi ba, 10-20 minutes, ai is not that much da zaki ce ba kya son takura" ta cigaba da danna wayarta. Bayan mintuna goma sha biyar, Nabila ta ji yo muryar sumayya, ta ɗauki jakarta ta fice, ba tare da ta sake kula lawisa ba. Sumayya na ganinta ta harareta, Nabila tayi murmushi ta ce "Haba masoyiyya daina hararata mana" "Matsa ko na make ki, ni ki ka yi wa wulaƙanci ki ka daina ɗaga wayata" "Ba haka bane ba, ayyuka ne suka yi mini yawa, daga nan ma wani wuri zan je na ce bari na biyo mu yi magana" Suka shiga wani office da babu kowa suka zauna, Sumayya ta ce "Wai ni me zaki gaya mini last week ne? Ki ka shanya ni da yake ba mutunci ne ya ishe ki ba, wayarki ma gaba ɗaya ta daina shiga, har gida na je ina nemanki" Nabila ta kaɗa kai ta ce "Aiki ne ya zo mini unexpected, mun je court ne, ina da shari'a kuma zan ga wasu clients ɗina. Dama a tsakanin lokacin nayi tunanin zan iya squeezing time ɗina, mu haɗu, kuma bai yiwu ba". Sumayya ta ƙare mata kallo tayi murmushi ta ce "Ko dai kin sake komawa wurin Aminu Viper ba?" Nabila ta yi murmushi ta ce "Kina zargin na koma ne?" "Na san hali zaki aikata ai, ina gargaɗinki a kan kasada da rayuwarki Arfa" Tayi murmushi ta ce "Ina ma zan iya jin maganarki" Sumayya ta ce "Baki yadda ba kenan?" Nabila ta ce "Mu bar maganar nan, ni wani taimako nake son ki yi mini " Sumayya ta ce "Ina jinki" "Ke ce uwar neman labari, bincike nake son yi a kan honorable ma'aruf Indabo" Sumayya ta kalleta ta ce "Kamar yaya?" "Kamar yadda na gaya miki, taimaka mini nake son ki yi, ki binciko mini duk wani labari da yakamata a kansa" "Me ku ke so ku mayar da ni ne daga ke har shi?" Nabila ta ce "Shi wa?" Sai kuma sumayya ta farga da katoɓarar da ta kusa tafkawa. "Indabon yayi miki wani abu ne?" Sumayya ta ce "No kar ki damu, haushi ki ka bani ne, kin ce Naja'atu Bunkure, kin ce Aminu Viper yanzu kuma kin ce Indabo, Nabila me ki ke son ki zama ne?" Nabila ta tashi tsaye ta ce "Zan je wani wuri yanzu, Ina jiranki dan Allah sumayya, da tarihinsa da tarihin siyasarsa komai da komai da yakamata ina son sani a kansa" Sumayya ta ce "Wai me zaki yi da shi to?" "Amfani mai muhimmancin gaske, sai anjima, ki gaida umma zan zo har gida na gaisheta, kwana biyu ba mu gaisa ba. Ina jiranki dan Allah" ta ɗauki jakarta ta yi waje. Kamar ta tafi gida, sai ta fasa ta ɗaukar mai napep, ta tafi police station ɗin da aka ce mata dattijon nan yana tsare, da ta je ta tarar an canza masa wuri, an mayar da shi sashen kula da manyan laifuffuka. ID card ɗin ta kawai ta nuna, aka bata damar ganinsa, aka fito da shi, dattijo ne amma ba tsoho cancan ba. Suka gaisa ta ce "Baba ni ce, wadda 'ya'yanka suka same ni, a kan maganarka, yaya meyafaru?". Nan ya ba ta labarin duk abun da ya faru, ta ce "To baba yaya sunan shi ɗan yayar matar?" Yayi shiru ya ce "Wallahi ban sani ba, yana dai zuwa gidan da yake ban daɗe da fara aiki a wurin ba" Ta ce "Yanzu ina ne gidan da ka ke aikin, sannan ina yarinyar take, dole zan ganta " Ya share hawayensa ya ce "Wallahi ban sani ba" Nabila ta tambayi 'yan sandan suka ce sai dai ta koma can in da aka fara binciken case ɗin" Ta ɗauki bayanan da zata ɗauka, ta yi musu sallama ta tafi. *** Kasancewar Abdul da wuri ya fita, solomon ma baya nan, Ramma ta din ga yawo tana neman hanyar fita tana kuka, amma ta rasa, tayi-tayi ta samu hanya ta rasa, ƙarshe ta koma falo ta zauna tana kallon Tv. Wata magazine da tarin takardu ta gani, ta ɗauka tana kallo, signing ɗin sa mai kyau, Abdul yassar ma'aruf Indabo. Shiru ta yi tana tunanin, kamar ta san sunan nan. Ƙofar falon ya saka key ya buɗe ya shigo, yayi sallama ta amsa a hankali, sai dai yayi kissing ɗin kumatunta sannan ya zauna, ta tsuke fuska tana matsawa. Ya kuma matsawa kusa da ita ya ce "Kin ci abinci kuwa?" Ta yi masa shiru. Ya ɗago mata jakar hannunsa ya ce "Yakamata ki san menene a jakar nan" taƙi kula shi. Ya buɗe jakar, ya zazzage mata, kayanta ne a ciki, da kuma wasu sababbin kayan ya sayo mata. "Babarki tana gaishe ki" Ta kalleshi idonta fal hawaye ta ce "Me ka ke nufi?" "Na ce ta sallama mini ke, ba sai ta cigaba da nemanki ba" Ta sake kallonsa ta ce "Waye indabo?" Ayshercool 08081012143 48 Ya kalleta ya ce "Meye alaƙarki da sunan? Kin san shi ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To a ina ki ka ga sunan?" Ta ɗago masa takardar ta ga signing ɗin sa, da full name ɗin sa. Ya ce "Well babana ne, ba abun mamaki bane dan kin san shi, ɗan siyasa ne" Cikin rauni ta ce "Me ka ce wa mamana da ka je?" "Ba na gaya miki ba, na ce kar ta sake nemanki, kin zama mallakina" "Saboda ba ka da tausayi da imani ko? Wallahi idan baƙinciki ya kashe mahaifiyata ba zan yafe maka ba" "Ikon Allah, me zai sa baƙin ciki ya kasheta, na kai mata kayan buƙata a matsayin ina tare da 'yar ta. Ku ne haryanzu ku ke wannan kidahumancin, kun ƙi ku waye, turawa duk in da mace ta kai 18yrs tana da ikon zuwa in da take so tayi rayuwa, amma ku da an yi magana sai ku ce aure aure, in anjima kuma ku yi ta surutun wahala ku ke sha a auren" Ramma ta ce "Saboda yahudanci ko? Mu ai ba turawa bane, musulmai ne baƙar fata, hausawa masu riƙo da addini da al'ada. Ni ban shekara sha takwas ɗin ba, idan ma na yi ai sai da yadda ta da amincewa ta. Kawai saboda bamu da kuɗi ka yi mini fyaɗe ka je har gidanmu gaban uwata ka ɗaukko ni, ka rabani da ita, kuma ka koma ka karɓo kayana ka ce mata ta daina nemana kai ba aurena ka yi ba, kai ba wani abu ka yi da zaka taimaki rayuwata ba, ka ɗauki hakkinmu ba ka yi mana adalci ba" Ya ce "Ke kin isheni, sai ka ce ke kaɗai ce 'ya? Ni fa ban taɓa ɗaukar wata mace na ajiye ina lallaɓata ba sai ke, kuma ma ku da ake haihuwar ku barkatai babu tsari, har wani damuwa za a shiga dan an ɗauki ɗaya? Kashe ki fa na yi niyyar yi na ƙyale ki". "Mu ba ai haife mu barkatai ba, mu uku ne, yayanmu ya rasu, ƙanina ba shi da cikakkiyar lafiya, ni kuma ka ɗauke mata ni, ban da dalilin maraici babu abun da zai saka ka ganni a birni aikatau, har ka keta mini haddi, bayan ka turo mana wata azzaluma, da fari ta ce zata taimaka mini, ta koma gaya mana yahudanci, ka ɗauke ni a gaban uwata, ka zo ka mayar da ni karuwa ka yi wa kanka adalci dan Allah kuma nima ka yi mini?" "Naja'atu Bunkure ba ƙarya ta gaya miki ba, tun a lokacin da ba ku nuna taurin kai ba, da ba a zo nan ba, ku ku ka janyo koma menene ai" Ramma ta haɗa hannayenta biyu, ta rufe fuskarta tana kuka ta ce "Ka cuce ni, ka lalata mini rayuwa, dama kasheni ka yi na huta, ka wulaƙanta rayuwata a matsayina na 'ya mace musulma da addinina ya suturta. Da ƙanwarka ce ni ko 'yar ka, ba zaka zuba mini ido ka ce na je na yi tarayya da wani ba aure ba, kayi amfani da kuɗi, ka wulaƙanta ni dan ni 'yar talaka ce ba ka kyautawa rayuwata ba" ga ta yarinya ƙarama, sai iya tsara magana. Abun da bai taɓa ji ba sai a wannan karon, kukan ramma a cikin zuciyarsa, maganganun ta suka tsaya a zuciyarsa, amma a zahiri ya nuna ko a jikinsa, ya tashi ya bar ta a falon ya tafi ɗaki. *** Ɗan mama yana ta kaiwa yana komowa, tsakanin ɗakin Viper da tsakar gida, yana jiran Walid ya fita, amma ya ƙi fita ya zauna ba shi da niyyar fita. Viper kuma sai bin ɗan mama yake yi da ido. Walid ya ce "Kai ɗan mama, kamar ba ka da gaskiya" Ɗan mama ya ce "Haba Oga walid me ka gani?" "Ba sai na gani ba, alamun hakan na gani, wallahi na ga abun da bai yi mini ba, sai ranka yayi mugun ɓaci" Ɗan mama ya ce "Kar ka damu Oga walid, babu wani abu da zaka gani wanda zai ɓata maka rai" Walid ya jinjina kai, ya cigaba da shan sigari. Al'amin ya yinƙura ya tashi, Walid ma ya tashi ya ce "Ina zaka?" Al'amin ƙura masa idanunsa da suka yi wani irin mugun jaa. "Ba wai tuhumarka nake yi ba, ko wani abu ba, kawai dai ba na son ka yi wani abu da zai wargaza mana shiri ne" "Iska zan je sha, ko yau ma yinƙurin kashenin zaka yi?" Walid ya girgiza kai ya ce "Last time ɗin ma, ni ba niyyar kasheka na yi ba, ƙoƙarin hanaka abun da ka yi niyya na yi, a dawo lafiya" Al'amin ya nufi ƙofar fita, ɗan mama ya ce "Oga Viper, bari na zo mu je na taka maka" Walid ya riƙe rigarsa, ya tsare shi da ido. Ya sosa kai ya ce "Dama raka shi zan yi" Al'amin bai waiwayo ba, kawai ya fita, Walid ya fara saka hannu a aljihun ɗan mama yana caje shi, Ɗan mama ya riƙe hannunsa ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri zan yi maka bayani". "Sakar mini hannu, ko na kwaɗa maka mari" Ɗan mama ya sakar masa hannu ya ce "Amma dai da ka tsaya na yi naka bayani" Walid ya ciro baƙar leda a aljihunsa, ya buɗe, ampoules ɗin allura ne da sirinji, sai baƙin capsule. Walid ya kalleshi, ɗan mama ya ce "Wallahi cewa yayi sai na nemo masa su, idan ba haka ba, ba ya iya bacci, kansa zai fashe ni kuma sai ya bani tausayi, daga ƙarshe kuma ya ce wallahi idan ban samo masa ba sai ya kashe ni" "Sai ya kashe ka, kai ka taɓa ganin ya kashe wanin?" Ɗan mama ya girgiza kai. "Wallahi idan ka kuma sayo wannan hard drugs ɗin ka kawo masa, sai na saka maka ƙarfe ka ji na rantse" ɗan mama ya ce "To, amma dan Allah shi ma ka gaya masa, ka san idan na ce masa a'a ba zai yi mini da daɗi ba". Walid ya ce "Idan ya ce ka kawo masan, ka ce masa to, ka gaya mini" ya jinjina masa kai. Viper yana zaune a kan dutsen, ya zubawa wuri ɗaya ido, kansa kamar ya tarwatse haka yake ji, ga ƙirjinsa kamar an ɗora masa dutse, da ƙyar yake iya numfashi, ga jikinsa sam babu ƙwari, banda kashe masa jiki babu abun da ƙwayoyin nan suke yi, soyake yayi bacci mai sunan bacci, ko ya manta komai da yake cikin ƙwaƙwalwarsa amma abu ya gagara. "Madaki! Indabo!" Ya faɗa a hankali yana sunkuyar da kai, ya ɗaga kai kamar a mafarki ya hangota, ta sauka daga adaidaita sahu, sai waige-waige take yi, yana saman dutsen sosai, dan haka yana hangota. Ta tsaya tana kallon hanya, in da yake take facing, amma ita ba ta ganinsa. Dogon hijjabi ne a jikinta yau, a hankali take tafiya tana cigaba da waige-waige, mamaki ne ya kama shi, me kuma ya dawo da ita wurin nan yau? Zuciya ce ta tinziro shi, ya ji kamar ya sauka ya je ya naɗa mata shegen duka. Mata halin su ɗaya, cin amana 'yar madarar sa ce kawai ta fita daban sai umminsa, ta sace masa waya ta gudu, ta saka an kama liti, saboda tsagwaron rashin kunya ta sake dawowa, ko uban me ta dawo yi oho?. Hakan ya ƙara tabattar masa he's not safe, za ta iya kawo jami'an tsaro su kama shi, sai dai kash, shi ba ya fargabar a kama shi, a kama shi ko a ƙyale shi, shi ba wannan ne a gaban shi ba yanzu. A yau ma ba ta iya gane hanya ba, bulayi take ta yi, tana nema, amma ta kasa ganewa. Babu tsammani suka yi kiciɓis da ɗan mama, ya kalleta ta kalle shi, ya ce "Ke! Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ce "Yauwwa, kai ne wanda na gani a gidan Viper ranar ko?" "Ke, ki ka kuma kama sunansa, sai na ƙara wa ƙofar bakinki faɗi wallahi, kar ki sake ambatar sunansa ko ki kama sunansa". Nabila ta ce "Tom, ba zan sake ba, dan Allah taimakona nake son ka yi, ganinsa nake son yi dan Allah" Ɗan mama ya ce "Ka ga wata mayyar kuma, baki ji kashedin da yayi miki ba kenan? Kin ɗauka da wasa yake yi da ya ce "Ya sake ganinki zai kashe ki, kin san waye Viper kuwa?" "Ba zai kashe ni ba, muhimmiyar magana nake son mu yi da shi, na san na yi muku laifi, ku yi haƙuri dan Allah, ka taimaka mini ka haɗani da shi dan Allah" Ɗan mama yayi mata wani irin mugun kallo ya ce "Ya aka yi ki ka san ba zai kashe ki ba?" "Viper ba ya kashe mutane, mussaman mata da ƙanan yara, dan Allah ka haɗa ni da shi na kasa gane gidan". "Ke bar nan wurin, na haɗaku ki saka a kama shi ko, to ta Allah ba taki ba, wuce ki bar wurin nan" Ta sake marairaicewa za ta yi magana. Ya zaro wuƙa ya ce "Idan shi ba ya kisa ni ina yi, ware ko na zaro hanjinki yanzun nan" wuƙar sai ƙyalli take yi, ya fara tunkarota, yana wulwula wuƙar, ba shiri ta juya, gwiwa a sanyaye ta bar wurin. Har ta miƙe ta ɓacewa ganin Al'amin yana hangota, ya miƙe ya kwanta a kan dutsen, ya lumshe idanunsa rana tana dukansa, yana jin yadda zafin ranar ke ratsa shi, yana ƙara masa ciwon kai, amma ba shi da niyyar tashi. *** "P.A" "Na'am honorable" "Ka tabattar binciken da ka yi a kan yarinyar nan daidai ne, babu kuskure a cikin sa?". P.A ya jinjina kai ya ce "Babu fa, ka san ba na yadda a samu kuskure a irin wannan lamarin, mussaman a irin wannan ƙadamin, ba a samu kuskure ba, yadda na gaya maka hakan ne" Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, ina ita ƙawar ta ta, ana cigaba da bibiyarta?" "Eh, a wurinta muka samu wasu abubuwan ma" Indabo ya ce "Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ta ce ayi mata bincike a kaina ne, shiyasa nake ta tantama anya ka yi binciken a kanta dai-dai?" P.A ya ce "Haba honorable, ya ma za ayi wannan ƙaramar alhakin ta yi wani bincike a kanka, wataƙila hakan yana da alaƙa da harkar siyasa ne kawai, ko kuma sakata aka yi". "Ba ita ce a gabana ba, Viper mai zamani, shi ne babbar barazanata, shi ne damuwata, ku cigaba da aikinku kawai, duk abun da ake ciki, ka din ga sanar da ni " P.A ya ce "In sha Allah, ai yaronsa ɗaya yana hannu, sai dai na bincika an ce Haryanzu bai yi magana ya

Chapter 50 of 121