Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
22 / 121
irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba" Ya ce "Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?" Ta tsuke fuska ta ce "To shikenan idan ba ka yadda ba"ta mayar da ƙofa ta rufe. Walid ya koma gefe ya kira Al'amin ya ɗaga ya ce "Ya mai laya". Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata 'yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa" "Wacece ya aka yi?" "Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da 'yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne" Al'amin ya ce "Ita ce matar gidan fa" "Kai haba maza, wannan ɗin?" "Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti" Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata 'yar caras beauty ka ji muryarta". "Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme". Walid ya ce "To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka" katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce "Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba" yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan. Kamar ba zata buɗe ba, ta sake buɗewa cikin mamaki ta ce "Malam lafiya?" "Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani" "Shi wa?" Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce "Maigidan" "Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba" Ya ce "Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?" Ta marairaice ta ce "Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa". Ya ce "Gaskiya ne, shikenan" ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe. Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su. Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ɗaukko masa ta ce "Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?" Ta ɗauka ta mayar masa ɗakinsa Al'amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi. Walid ya je ya samu Al'amin, ya  din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya ci a hannunsa. "Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure 'yar yarinya ta hana aiki yau?" Al'amin ya kalle shi ya ce "Ƙila" Yayi tsaki ya ce "Yauwwa, na haɗa maka da mp ɗina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba" Al'amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa ɗakin, ya tabattar ɗauka tayi ta kunna. A ransa ya ce 'Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba' "Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp ɗina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?". Aminu ya miƙe ƙafa ya ce "Sai ka dawo" Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al'amin, ba zai koma gidan nan ya ɗaukko kayan ba. Ƙarfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye. Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari. Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera. Ta durƙusa ta ce "Yaya ina kwana" waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba. Har ta fitar da ran zai amsa ya ce "Lafiya" Ta miƙo masa leda ta ce "Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ɗiba na dafa mana tea?" Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce "Da me zaki dafa tea ɗin?" Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce "Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ɗin taliya ce?" "Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?" Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji daɗin mahaukaciya da ya kira ta da ita ba. "Dan Allah ka yi haƙuri, ban sani bane". "Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami'an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki" Shagwaɓe fuska ta yi zata yi kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah ka bashi haƙuri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa" Ya saka hannu ya ɗauki ledarsa ya tashi zai fita ta ce "To karin kumallon fa" ko waiwayowa bai yi ba, ya fita. Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ɗakinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ɗaya da zai saka, ta ɗaukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wuƙa. Gabanta ya faɗi wuƙar kawai abun tsoro ce. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta ɗauka" "Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani". A razane ta ɗago jikinta na tsuma. "Fita ki bar mini ɗaki, bincike ki ke yi mini ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba" "Fita to" Ta ce "To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka". Ya sake tsuke fuska ya ce "Ki fita na ce" Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin. Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntuɓe, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton. Ta lallaɓa ta fita ta kunna gas, ta ɗora shayi. Buga gate ɗin gidan ake yi da ƙarfi, ba shiri ta tafi ta buɗe. Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa. Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce "Ina matar gidan?" Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta. "Lafiya?" "Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke" Jauhar ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini". "Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ƙararsa muka kai" Ta ce "Subhanallah, laifin me yayi muku?" "Au jira zamu yi sai ya yi kan mu ɗauki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana 'yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen ɗan daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala'i. Gara aje a zauna da mai unguwa da 'yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi". Jauhar ta ce "Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin 'yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina". "Ke rufe mini baki kan na kwaɗe ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba" Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke faɗa. Da sauri ta leƙa ta ce "Ka tafi kar ka bari ya ganka"ta waiwayo ta rufe gate ɗin tana kallonsa. "Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa". Ayshercool 08081012143 22 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Kafin ta yi wani yinƙuri, ya janyeta daga jikin gate ɗin, sai dai kasancewar ba ƙwari ne da ita ba a kansa, sai da ta kai ƙasa. Ya buɗe ƙofar ya lelleƙa, bai ga kowa ba, tuni malam lawan ya ɓace. Ya dawo ya kalleta, ta sunkuyar da kai, sai murza yatsan ƙafarta take yi, da yake yi mata zafi, saboda faɗuwar da ta yi. Ƙwafa ya yi ya wuceta, ta lallaɓa ta tashi, ta shiga kitchen ta ɗora tea, ta ɗebi miyar nan da su Anty lubabatu suka kai mata, ta ƙara gyarata ta zuba ta kai masa falo. Ya wani maze yana basarwa, nan kuwa jira yake yi, tayi ta kawo masa ya ci. Sai dai yadda yake cin abinci ya goge mata a jikin kujera, ko carfet yana damunta, sai dai idan ya gama ya tashi ta goge. Dan haka ta sayo toilet paper, take haɗo masa da ita, amma ko kallonta ba ya yi, idan Allah ya taimaketa ne, wani lokacin sai ya goge a jikin kayansa kamar wani ƙaramin yaro. Da daddare kuwa kullum, sai ya cika gidan da warin sigari, wasu lokutan ba zai dawo ba, sai sha biyu na dare, ya shige ɗakinsa yayi ta shaye-shaye, da safe kuma idan ta ajiye abinci zai ci, idan ba ta ajiye ba ba zai tambaya ba, kuma ba zai sayo ya kawo ba. Idan za ta gyara masa ɗaki sau goma a rana kuwa, muddin ya shiga sai ya watsar da komai ya ɓata, yayi shaye-shayensa ya bar mata toka da sauran karan sigari duk a ɗakin. Wasu lokutan sai su shafe kwana biyu ba su haɗu ba, gashi zai kwana a gidan, amma ba zai shigo ba sai ta yi bacci, duk da wataran ba ta baccin sai ta ji shigowarsa, asubar fari kuma sai ya fice, ranar da ya ga dama kuma, sai ya bari gari yayi haske, ko za ta bashi abinci, dan sai yanzu ya fuskanci abincin waje wasu lokutan ga ƙaurin hayaƙi gashi ba sa jin sinadaran ɗanɗano, nata kuwa har cikin kansa yake jin su. Yau ma dawowa ya yi rana tsage-tsage, walid ya sayo musu abinci, yana fara ci ya ji babu daɗi, ya ajiye ya ce gida zai tafi. Walid ya ce "Da ranar nan tsaka zaka fi gida?" "Eh" ya amsa a taƙaice. "Lallai, na fuskanci lamari yana ta daidaita to Allah ya sa mu ji alkhairi ya kawo zuriya ɗayyiba" Ya haɗe rai ya ce "Mai laya" Walid ya ce "Sorry maza, na kiyayi mai zamani" ya fice ya tafi gida. Jauhar tana ta lissafin kuɗin hannunta, sun kusa ƙarewa, girkin ma duk da dabaru take yin sa, ga gogan babu ruwansa sai dai ta dafa ya lashe. Da 'yan dabaru take yin ɗan wake yau, ta aiki almajiri ya sayo mata kabeji da cucumber, tana jiran dawowarsa, Al'amin ya dawo, a duk lokacin da za ta ganshi sai ta razana, gashi ba sallama yake yi ba, ya hangota da tukunya a kan gas, ya yi ajiyar zuciya ya san zai ci abinci. Ya shiga ɗakinsa, ya tarar ta sake wanke masa kaya, ta gyara ɗakin tsaf. Tsaki yayi ya ce "Ita dai wannan an yi 'yar wahala" Ya daidaici lokacin da ta gama girki, ya dawo falo ya zauna, aikuwa sai ga ta abinci bakinta ɗauke da sallama. Bai amsa na sai Alla-alla ta kawo ta ajiye, saboda yadda ƙamshin manjan, ya cika masa hanci. Ta ajiye masa ya haɗa abun sa ya fara ci. Ta zauna a gefensa, cikin fargaba ta ce "Yaya" shiru ya yi mata, yana haɗiye ɗan wakensa da hurhuɗu biyar-biyar. Ta sake cewa "Yaya magana nake dan Allah abu zan tambayeka". "Malama sunana Aminu, kar ki sake ce mini wani Yaya" a ranta ta ce 'Ai na san a rina' A zahiri kuma ta ce "Ai ba zan iya faɗar sunanka ba, ya za ayi na faɗi sunan mijina kamar mara ɗa'a" sai ya ji abun wani banbarakwai wai mijinta. "To me zan din ga ce maka?" Ba ta jira amsar sa ba, dan ta san ba zai amsa ba, ita kuma zaman kuramen nan da suke yi ba son sa take yi ba, ace kana zaune a ƙarƙashin mutum, amma ba zai kulaka ba. "Na ji abokanka suna ce maka boss, ni kuma sai na ce maka master, idan na ce master zaka amsa, ko nima boss zan ce? Tun da ba ka son yaya?" Ta tambaye shi tana murmushi ba tare da ta kalli in da yake ba, saboda kwarjinin da yake yi mata, yanzu haka ma ƙarfin hali kawai take da take yi masa magana. Kallonta yayi, tana murmushi dimple ɗin ta na side ɗaya ya lotsa, ya gane dakiya kawai take yi, amma a tsorace take yi masa magana. Duk da bai bata amsa ba, amma matsern da ta ce zata din ga kiransa da shi, ya so yayi murmushi, amma yaƙi ya sha kunu, yana suɗe kwanon ɗan wakensa. Cikin hikima ta ce "Da da sauran garin ɗan waken nan, da na dafa maka wani, ko na ƙaro maka?" "A'a" ya ajiye kwanon, cikin sauri ta miƙa masa wani tsumma mai kyau, ta ce "Gashi ka goge hannunka, manjan yana da kamu, sai mu je waje na zuba maka omo ka wanke sosai" ya karɓa ya goge, ya koma ya kashingiɗa yana duba wayarsa mai madannai. "Na ce, dan Allah sonake na shiga maƙwabta na yi musu sallama na tare, wai haka ake yi, ka ga mu bamu cewa kowa mun tare ba" "Sauka lafiya" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Yauwwa na gode sosai master, bari ayi la'asar, sai na je. Yauwwa mutumin ɗazu ya ce wai mai unguwa na nemank..... Ba ta ƙarasa ba ya tashi, dan surutunta ya fara isar sa. Bayansa ta bi da kallo, 'Da sannu wataran zaka tanka mini ne, ni ba zan iya rayuwar zaman kurame ba' tayi maganar a hankali. Huɗu da rabi, bayan ta yi la'asar, ta leƙa ɗakinsa ta ce masa za ta fita, ta tarar yana salla. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, tare da hamdala a zuciyarta, ba ta taɓa tsammanin yana kai goshinsa ƙasa ba. Ta zauna a bakin ƙofar tana kallonsa, duk da shaf shaf yake yi, kuma azahar da la'asar ya haɗa a lokacin, amma ta ji dadin ganin yana salla. "Master bari na je, idan ka idar ka sani a addu'a, Allah ya sa ka daina jin haushina, ban san me nayi maka ba" dama ta san ba amsawa zai yi ba ta fita. Matasan 'yan mata ne su biyu a gaban rahila suna cin abinci, da alama daga makaranta suka dawo, domin kuwa bayansu jibga jibgan akwatuna ne, na 'yan makaranta. "Umma, nifa haryanzu na kasa daina mamaki, wai yaya ne yayi aure? Wai dan Allah ya aka yi aka samu aka bashi 'ya a yadda yake? Kuma ba a bari mun dawo ba aka yi bikin?" Rahila ta ce "Ke dallacan, waye ya ce miki abun na shiri ne shahida? Neman mafita nake ba shiri faka-faka na saka aka samo wata yarinya ya je can ya ƙarata, ya ƙara sako mini yaro a gaba, irin kallon da yake yi mini, tsaf zai halakka ni, cikin ikon Allah tun da aka yi auren, ban sake ganinsa a gidan nan ba, ya samu mace yayi luf" Shahida ta ce 'Ni wallahi mai tsautsayin da aka aurawa nake jin tausyai, yaya za ta yi da shi dan Allah dan Annabi?" Amira ta ce "Ke ina ruwanki ne shahida, ina ruwanki da ko ma wa ce ta aure shi, ba dai an samu ya tafi na, case close". Shahida ta yi murmushi ta ce "Ina ne gidan nasa ne?" "Yana can gidansa na ɗorayi, ba kuma cewa na yi ki je ba, kar abun da ya kai ki gidansa, balle ya lallaɓa ya dawo mana nan ya je can su ƙarke". "Ahh haba umma, sai mu yanke alaƙa da shi duka kenan? Yayi aure muna school kuma mun dawo ba zamu ganshi ba?" Amira ta ce "Wallahi a garin shishshigin nan da ki ke masa, zai kassara rayuwar ki, ki yi ta shige masa yana yarfaki" "Wallahi ki ka je gidansa ma sai na ci ubanki shahida, na gaya miki, ke baki san sai ku kasa auruwa ba saboda mugun halinsa da mummunan tabon da yake da shi ba a unguwar nan?" Shahida ta ajiye cokalin hannunta ta ce "Umma, shi fa jini ya fi ruwa kauri, the only male brother i have, sai ki ce sai na yanke alaƙa da shi?" "Au jayayya zaki yi da ni? Shi Abban uban meye idan ba yayanki ba?" Ta tashi ta ce "Ai ba babanmu ɗaya ba, Yaya Al'amin kuma babanmu ɗaya, kowane ina son sa" Rahila ta ce "La ila ha illalahu Shahida " Amira ta ce "Dan Allah umma bar shashasha, za ta gane kurenta ne" Rahila ta cigaba da salallami, a kan yadda ke adawa da ita wasu lokutan a kan Al'amin. *** Juahar gidan malam lawan ta fara shiga, wato gidansu halimatu da walida, yaran da suke zuwa tayata hira, suka gaggaisa da maman, sannan su halimatun, suka rakata sauran gidajen maƙwabta, tayi musu sallama. Har wurin masu kayan miya, da masu shaguna suka nunnuna mata da wurin makarɗe. A bayan gidan suka je har gidan wata tela, da har da yaranta, su na shigarwa jauhar, suka gaisa jauhar ta tarar da yaran suna stone work a jikin ɗinki, har ta karɓa tana taya su, saboda a rayuwarta tana son sana'oin hannu suna matuƙar burgeta. Take cewa matar, idan an samu stone work ta din ga aika mata da shi tana yi mata. Matar ta ce 'To nawa zan din ga baki, dan kuwa ina samun aikin su sosai da sosai" Cikin tsananin murna, da jin cewa ta samu abun yi, ta cewa matar, ko nawa ne ta bata, tana son za ta din ga yi, nan hira ta ɓarke, take gaya wa matar, ta iya shirin dutse, har adon da ake yi da shi a jikin ɗinki, duk zata iya, suka yi yarjejeniyar matar zata din ga bata ta yi mata. Ganin hadari ya fara haɗowa, ya sanya ta yi mata sallama, ta koma gida, sai dai tana komawa, ya zura takalmansa zai fice, ta ce masa kar ya fita, hadari ne a garin, amma ba ta gama rufe baki ba, ta ji ya buɗe ƙofa ya fice. Ta kawar da abun da zata kawar, ta rurrufe ko ina, ta laluba ta ɗauki mp a in da ta ajiye, ta tarar ya ɗauke kayarsa, ta ce "Da sauƙi, tun da ba ka yi mini faɗa ba". Ruwan sama aka yi, kamar da bakin ƙwarya, ga wata irin iska da ta jefa jauhar, cikin razani da tashin hankali, yadda kwanon yake ƙara ji take tamkar zai kwashe ne, saboda ƙarfin iskar da ruwan. Ta takure wuri guda, tana ta addu'a, kasancewar lokacin da ake ruwan sama, lokaci ne na karɓar addu'a, mafi yawan addu'arta a kan Al'amin ne, da take masa fatan shiriya. Ko da ruwan ya tsagaita, ta fito falonta, ruwa ya shigo sosai, ya jiƙe ɗakin, ta buɗe ƙofar falon, rashin kyakykyawan magudanan ruwa, ya sanya kwatocin layin yin ambaliya, duk suka shigo mata gida, gashi ba ga da rariyar kirki, sai ta banɗkuna, dan haka babu wurin da ruwan zai fita, tsakar gidan ya shafe da ruwan kwatami, falonta ma duk ruwan ya shigo, gashi idan aka yi ruwan, tsigar jikinta tayi ta tashi. Haka ta samo kwano, ta din ga ɗibar ruwan tana zubarwa, ta naɗe carfet ɗin ta, ta jingine, sai zallar buhun da aka shimfiɗa a ƙasa, ta din ga kwarfe ruwa a falon nan. Ta je ta yi sallar magariba, Allah ya sa ruwa bai shigar mata bedrooms ba. Ana sallar isha'i sai gashi ya dawo, ya tarar da ita, fitilarta babu batirin kirki, duk tayi duhu, sai kwashe ruwa take a falo. A ransa ya ce "Iyayenki ne suka ja miki" tayi masa sannu da zuwa, ta cigaba da aikinta, har zai wuce ya dawo ya karɓi kwanon, ya haɗe mata kujerunta wuri guda, ya kunna fitilar ƙaramar wayarsa, ya ƙarasa kwashe ruwan. Shi kansa ya san gidan nan kango ne, yana buƙatar gyara sosai, bai ci ace har an saka mutum a ciki ba, amma da iyayensa da na ta, ya rasa wannene uban garajen da ya saka aka yi haka. Ya ɗaɗɗaga labulayen, saboda ɗakin ya sha iska, daga nan ya tafi makwancinsa, ta tafi nata. Da safe ruwan duk ya tsane, amma sai ƙanƙame jikinta take yi, ƙarnin ruwa da ya kwanta ya din ga damunta. Haka nan ta daure, ta gyara gidan, ta zuba miya ta yi jallof ɗin macaroni, kasancewar falon a jiƙe yake, da danshi, da sauran Lipton ɗin jiya, ta dafa shayi har da su citta ta yi sallama a ƙofar ɗakinsa, bai amsa ba dama labulen a ɗage yake ta shiga. Ta ajiye masa ta ce "Ina kwana?" Ba ta jira ya amsa ba, ta haɗa masa tea, ta tashi ta fita. Aka jima ta dawo, ta shiga banɗakinsa ta wanke, ta ɗauki bokiti ta dawo, ta haɗo ruwan zafi na wanka, ta kai masa banɗakin ta ce "Master ga ruwan wanka nan na kai maka, mai ɗumi ne" idan ta ce mastern nan, sai ya ɗaga kai ya kalleta. Ta ce "Yauwwa, master zan kafa ƙusa a toilet ɗin ka, idan ka gama wanka, ka dinga saƙale soson, idan ba haka ba sabulun narkewa yake yi, sai ka ga ya ƙare da wuri" Ta zagaye shi, ta fara tattare kayan duk da ya watsar a ɗakin kamar ƙaramin yaro. Ya gama cin abincin sa, ya fara shan tean, yana jin yadda ƙamshin da yajin citta yake ratsa shi yana yi masa daɗi. Yana zaune ta gyare ɗakin, ta kukkuna masa turaren wuta, sai dai kafin ta ƙarasa, ya kunna sigari a ɗakin. Sai da ranta ya sosu, akwai sauran warin ta jiya da daddare ma da ya sha, ta gama aikin ɗakin, ta kunna turaren wuta, ya kuma kunna wata sigarin. Ta maze ta ce masa "Ruwan wankanka, kar ya huce fa, na ga garin da sanyi haryanzu, idan ka yi wanka da na sanyi, zaka yi mura" A hasale ya ce "Ke, fita ki bar mini ɗaki, kin gama tsegumin ai, kin sakani a gaba kin ga abun da nake yi, to fita ki bar min ɗaki, ba zan wankan ba" Ba ta sake cewa komai ba, ta juya ta fice, ta cigaba da ayyukan ta, tana tsaka da wanke-wanke, ya fito da sauri, hannunsa riƙe da waya yana cewa "Kar ku raga musu, gani nan zuwa" ta miƙe tana kallonsa, amma ta kasa yi masa magana. A haka yana ƙaurin sigarinsa da komai, ga kayan da su ya wuni jiya, ya wayi gari da su, amma bai canza wasu ba, ya fice cikin matsanancin sauri. Ta koma ta cigaba da aikinta, tana addu'a Allah ya sa ba wani rashin jin zai je yayi ba. Baba yana gida, aka aiko ana sallama da shi. Yana fita ya tarar da 'yan uwan Alhaji mu'azzam da suka kawo kuɗi. Suka gaggaisa, ƙanin mahaifin Alhaji mu'azzam ya ce "Gamu mun dawo, ɗanka ne ya dawo da mu, ya ce a bayar da haƙuri, kar a ji mu shiru, ayyka sun yi masa yawa, ba zai samu dawowa nan kusa ba, shi ne ya ce mu zo ayi magana, a ƙarasa shirye-shirye kawai, ayi auren a tura masa ita can". Gaban Baba ya faɗi jikinsa a sanyaye ya ce "Alhaji dama ko da baku zo ba, zan neme ku ni na zo, an sami matsala ne, zan dawo muku da kuɗin aurenku". Suka yi turus gaba ɗaya suka ce "Wace irin matsala ce haka?" "Yarinyar nan, yau ta kusa sati biyu, ina mai baku haƙuri, a bashi haƙuri dan Allah. Zan kawo muku kuɗin aurenku" "Amma wani abun yayi ne, ko wani laifin shi mu'azzam ɗin yayi?". Baba ya ce "Ko ɗaya, ka

Chapter 22 of 121