tuhuma".
Major ya ce "Haryanzu ina mamaki, da ka ce kai ne dai wada kankarofi, ni na zata suna ne kawai ya zo ɗaya"
Alhaji mu'azzam ya ce "A'a, ni ne dai, a rayuwata ina son 'yanci da walwala, dan haka ban fiye son takura ba, ko yawo da gayyar jami'an tsaro ba duk in da zani.
Na san ka ɗauki zafi a kan abubuwan da Nabila take aikatawa, na kasada, amma ni burgeni tayi, kuma daga ranar farko da na ganta a law firm ɗin su, nake bibiyarta, nake taimakonta, akwai ire-iren ta, brave citizens, da cin hanci da ƙarfin iko, ya sanya ake tauye su su kasa kataɓus, a kanta na ce bari mu jarraba ayi supporting ɗin ta, mu ga wace irin baiwa da gudunmawa zata bai wa ƙasa, and Alhamdilillah ko iya haka tayi rawar gani "
Major ya jinjina kai ya ce "Haka ne sir, amma abun da aka yi ya isa haka, ina son a dawo mini da 'ya ta, abun da tayi Allah ya amfana, ni aikin ma a haƙura da shi, tayi aure. Ba zan lamunci zuba mata ido, tana kare rayuwar ɗan ta'adda ba. Aikinta na neman kawo mini rabuwar kai a cikin iyali. Ga ɗan uwanta yana fafutukar neman mai laifi, ita kuma tana kare shi ba. Sunanta ya ɓaci a idon duniya ba, ina buƙatar ta dawo a haƙura kawai"
Alhaji mu'azzam ya ce "Am sorry to say sir, Nabila ta ɗaukko aikin da kammala shi ne kawai mafita, da ceto dubban al'umma, za ta aikata abun da da yawa sun yi yunkurin yi, amma ba su yi nasara ba. Bani da ikon dawo maka da ita, umarni ne na musamman kareta da lafiyar ta"
Abba ya numfasa ya ce "Na ji, amma Allah ya amfana haka nan, a dawo mini da 'ya ta, ban ga dalilin da zai sanya, a ɗaukar mini yarinya ba da iznina ba a ɗaga mini hakali har haka ba"
Alhaji mu'azzam ya ce "Na san an yi maka laifi, shiyasa muka zo har gida baka haƙuri, kuma ta ɗan samu mini attack ne mun kaita Asibiti, daga baya kuma muka lura da matsanancin haɗarin da rayuwarta take ciki, ka ɗan bamu lokaci"
Nasir kamar yayi maganar Viper, amma yayi shiru, kenan da gaske Viper yake shi jami'in sirri ne, ko kuma wata kitumurmurar ce?.
Abba suka yi ta jayya da Alhaji mu'zzam, haka ya haƙura, sai dai bai ji zai yi shiru da maganar nan ba, dole a dawo masa da 'yar sa.
Bayan tafiyar su, mutanen gidan suja din ga tambayar meyafaru, Abba ya gaya musu ba wani abu, a kan Nabila ne, tana wurin hukuma saboda tsaron lafiyarta.
Masu jiran su ji baƙin labari, duk ba haka suka so ba, baba magajiya kuwa addu'a ta cigaba da yi, tare da fatan Allah ya sa Nabila na cikin ƙoshin lafiya.
Sumayya ce ta zo gidan, cikin matsananciyar damuwa, ta tarar da Abba yana shirin fita, suka gaisa ya ce "Kin biyo sahu ko sumayya?"
"Eh Abba, hankalina ya kasa kwanciya, ni har a radio na sanar a tayamu addu'a bamu ganta ba, na kasa sukuni gaba ɗaya"
"Ki kwantar da hankalinki, yanzun nan baƙi suka tafi, wai tana wurin hukuma saboda tsaron lafiyarta, wai wani saurayinta da ya zo dubata kwanaki, wai mai bawa shugaban ƙasa shawara a kan harkar tsaro".
Take Sumayya ta gane waye, ta ce "To Abba ya tabattar maka tana lafiya?"
"Eh, ya ce suna bata kariya ne, ashe ba saurayin ta bane kawai, ni dai kam na gaji da wannan aikin, ajiye shi zata yi ta fitar da miji, na yi mata aure, ko ni na fitar mata"
Sumayya ta ce "A'a Abba ka yi haƙuri, aikin yana da muhimmanci, zan cigaha da kiranta, Allah ya sa na sameta"
"Allah ya sa, dan bana tunanin zasu bari ta ɗaga waya".
***
Ko da Abdul yayi parking a harabar gidan su, bai ko tsaya rufe motar ba, ya shiga cikin gidan kamar yayi fuka-fukai ya tashi, "Mummy" ya din ga ƙwala wa mahaifiyarsa kira.
"Menene wai ka ke kirana haka?"
"Ina Daddy?"
Ta kalleshi rai a ɓace ta ce "Ya tafi ya gurfana a gaban kwamitin da aka naɗa, na binciken kuɗin da kake neman ka janyo masifa a kansu"
"Mummy ba wannan ba, dan girman Allah ki gaya mini idan shi ne ya sa aka je aka ɗauke ramma"
Sheƙeƙe ta kalle shi ta ce "Wacece hakan?"
"Matata mana"
"Wai Abdul baka jin kunyar faɗar wannan maganganun ne? Har wani tutiya kake yi dan ka auri karuwa? Wannan aure da zaka yi alfahari da shi ne, kana wani matarka?"
Abdul ya ce "Mummy, meyasa a ƙasashen ƙetare, ko wasu sassan na duniya, idan suka lalata yarinya, ko su gama watsewar su, suke dawowa su aure su, mu kuma sai mu tafka ɓarna mu koma mu ce zamu yi wa Allah wayo, na san ba zan taɓa auren macen kirki ba, dole ragowar wani zan aura, gara wannan ragowata ce koma menene ni na janyo"
"Abdul, ka tsaya a gabana ka ke gaya mini wannan maganganun banzan? Ina uwarka"
"Ni dai dan girman Allah idan ku kuka ɗauke mini mata, ko dawo mini da ita, wallahi ba zan iya rayuwa mai daɗi babu rahama ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka je kayi duk abin da zaka yi Abdul"
"Mummy dan Allah Daddy ne ya saka aka ɗauke mini ita"
"Ban sani ba, ka bishi Abujan ka tambaye shi" ta juya ta koma ɗakinta, a matuƙar fusace.
****
Wata irin runguma, Ramma ta yi wa mahaifiyarta, suka fashe da kuka baki ɗaya.
"Ramma, kina lafiya bai cutar mini da ke ba?" Ramma ta jinjina mata kai tana kuka, suka ƙara ƙanƙame juna.
Barrister Habib ya ce "Kukan ya isa haka, a gode wa Allah, dan Allah ku yi wa Nabila Addu'a, da ita da malam garba, shi an bishi an kashe a prison ɗin, amma ita Nabila an kauwwameta, ana tsaron lafiyarta"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, sai da mutumin nan ya rasa ransa?" Maman ramma tayi maganar cikin tashin hankali.
Jiki a sanyaye ramma ta ce "Yanzu malam garba ya rasu? Wayyo Allana, Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi"
Suka Amsa da Amin.
Mama ta kalli barrister Habib ta ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, idan ka samu ganinta, ka ce mata na gode, na gode Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, ya jiƙan magabatanta, yadda ta share mana hawaye, ka da Allah ya bar nata su zuba"
Ya ce "Amin, amma ni kuma fa"
"Kai ma haka tare da Alhajin da yake ta ɗawainiya da ni"
Barrister Habib ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, bari zamu cigaba da magana da jami'an tsaron, za a kama ainihin mai laifin, za a hukunta shi da yardar Allah, duk wata shaida muna da ita a kansa" suka din ga yi masa godiya, ya wuce ya fita.
Suka ƙara rungume juna, mama ta ce "Lokacin da yarinyar nan take tabattar mini da zata dawo mini da ke, ban zaci da gaske take ba, da zan ganta har ƙasa zan durƙusa na yi mata godiya"
Ramma cikin kuka ta ce "Mama ina Sani?"
"Mutumin nan da ya saka aka ɗaukkomu, ya kai shi makarantar kwana, ta kuɗi"
"Mama wai waye shi? Meyasa ya ɗaukko ki?"
"Yana da nasa dalilin, amma ban sani ba"
*MONTHS BACK*
Nabila sai sauri take yi, takalminta mai tsini yana ƙara, tana neman network, domin yin magana da sumayya, har ta dangana da rukunin ofisoshin da ba kowa a wurin.
"Hello, ke Sumayya T ladan, ba network ne, yanzu na samu wuri, ya ake ciki munafukan al'umma"
Sumayya ta ce "Nabila ki daina ce mana munafukai, aiki muke fa"
"Ba wani aiki, tsegumi wanda aka saka ku, da wanda ba a saka ku ba, duk ku ke samowa ku kwatsawa al'unma komai daɗinsa da ɗacinsa"
"Zan ɗura miki ashariya wallahi"
Nabila ta ce "Sorry T ladan, masoyiyyar Nabila, bani labari"
Da sauri Ramma ta ajiye littafin hannunta, jin an ambaci sumayya T ladan, da sauri ta ƙarasa gaban window tana zura kai.
"Baiwar Allah, baiwar Allah kin ganni ta nan baiwar Allah" Nabila ta hau waige-waige, taga ta ina ake magana.
"Baiwar Allah wadda take waya, dan ki ƙaraso wurin tagar nan"
Cikin dakewa Nabila ta ƙarasa, ta ragar jikin window Nabila ta ga ramma, ta ce "Lafiya kuwa?"
Ramma ta ce "Ki taimake ni, kamar yadda Allah ya taimake ki dan Allah, na ji kina faɗar sunan yar jaridar nan, mai aiki a radio"
Nabila ta ce "Eh ya aka yi, kin santa ne?"
"Ban santa ba, taimakona zaki yi, dan Allah ku sanar da jami'an tsaro idan kuna da dama, wani ne yayi mini fyaɗe, ya sace ni ya aure ni, ba da sanin mahaifiyata ba, ban san a wane halin take ciki ba"
"Yayi miki fyaɗe ya sace ki? Garin yaya?"
Nan ramma ta gaya mata komai, Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kin san irin neman da muke yi miki kuwa? Ni nake shari'a a kan case ɗin ki, har ya fita yana yawo da ke, amma baki yi masa ihu ba, a ƙwace ki?"
"Tayaya zan yi masa ihu yana aurena? Kuma idan nayi ihu tamkar na ƙara tonawa kaina asiri ne, wanda ya sanni, da wanda bai sanni ba, sai kowa ya san abin da ya same ni, shi ne mai asibitin nan, shi yayi mini fyaɗe, sai an bi a hankali idan ba haka ba, ba zai taɓa rabuwa da ni ba, dan Allah ki taimaka mini dan Allah, ina son na je na ga mahaifiyata"
Nabila ta ce "Tsaya, yana baki ci da sha, ko yana dukanki da cin zarafi?"
Ramma ta ce "A'a, baya yi"
"Yauwwa Alhamdilillah, a ina yake ɓoye ki?"
"Ban san ina ne ba"ta yi maganar tana kuka.
Samo abu na rubuta miki lambata, ki faki idonsa, ko saƙo ki turo mini, sai ki goge, nayi miki alƙawarin zaki kuɓuta in sha Allah"
Nabila ta bata lambarta, ta nufo hanyar tafiya, tana yi wa Allah godiya, yadda kayanta suka tsinke a gindin kaba, saboda tsananin addu'a da take yi.
Daga nan ta koma ƙofar ɗakin Viper, ɗan mama ya hanata shiga.
Kamar yadda suka tsara, Ramma ta yi mata message, Abdul na wanka, Nabila ta bawa Viper, ta ce masa wata lamba take so, a duba mata location ɗin ta.
Yana dubawa ya ce "Wannan ai lambar ɗan gidan indabo ce"
"Waye Indabo?"
"Mutumin da ya kashe mini jauhar"
Nabila ta rufe baki cikin tsananin mamaki.
"A ina ki ka sameta?"
Ta ce "Kar ka damu, manta kawai" sai da kanta ya sara, ta ina zata fara yi masa wannan mugun jawabin mara daɗin ji, indabo ya kashe Nura guduma, kuma yanzu ɗansa ya saceta, bayan yayi mata fyaɗe.
Wurin barrister Habib ta je, ta sanar masa da abin da ya faru, sun daɗe suna mamaki, barrister Habib ya ce "Wannan lamarin ba zamu miƙa shi kai tsaye ga 'yan sanda ba, dan bamu san a hannun wa zamu danƙa ba, yana buƙatar sirri sosai da sosai, kar wani yayi mana katsalandan ya ɓata mana aiki".
Bayan Nabila ta gano Alhaji mu'azzam, shi ya sama musu wanda suka cigaba da tracking in da ramma take, ta hanyar bibiyar lambar Abdul, har zuwa lokacin da aka yi nasarar gano in da take, jami'an tsaron Civil defense, suka je suka ɗaukkota
****
Nabila na tsaye na leƙen window, ta kasa gane a ina take, wurin shi ba jeji ba, shi dai gashi nan.
Ta koma ta nemi wuri ta zauna, Viper ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya je gabanta ya tsaya, ya ajiye mata ledar abinci ya ce "Gashi nan ki ci ki sha magani"
"Vi"
"Mmm"
"Dan Allah ka mayar da ni gida, ina da abubuwan yi da yawa, yakamata na je ta'aziyyar malam garba, na rarrashi iyalinsa na basu haƙuri, bisa ga gazawata, dama ni ban taɓa shari'a na samu nasara ba, kullum faɗuwa nake yi, bani da sa'a" ta ƙarasa maganar cikin damuwa.
"Dama yaushe masifaffen mutum zai yi sa'a?"
"Na ji, amma ka mayar da ni gida, ni ban san me ma zan cewa yan gidanmu ba, kwana biyu bana gida, dama ana yi mini iƙirarin bin maza, ban san me zan ce musu ba"
Viper ya ce "Na gaya miki, na fisu buƙatar ki, zaki cigaba da zama a nan, har sai kin kammala aikina"
"Wai na cigaba da zama kamar yaya? Sai in din ga keɓewa daga ni sai kai, ka san dai bai dace ba, idan mace da namiji suka haɗu na ukunsu shaiɗan ne, ka san bai kamata ba"
Ya sunkuyo dai-dai fuskarta, ya tsura nata jajayen idanunsa, da suke razanata wasu lokutan, zaro harshen sa yayi waje, wanda sai da ta tsorata, saboda ganin tsayin harshensa. Ya ɗan ja numfashi ya ce "Lokacin da ki ke sintiri a gidan da nake, kina neman suna, baki yi tunanin na ukunmu shaiɗan bane sai yanzu? Sai dai kece macen kuma shaiɗaniyar, idan zamu shekara dubu, baki isheni kallo ba, wadda take halalina ma, sai da.... Sai kuma ya yi shiru.
Ya cigaba da cewa "Kamar yadda na gaya miki, duk wata mace idan ba jauhar ba, namiji ce a idona"
"Katako kake gani ba namiji ba" tayi maganar cikin ƙunƙuni.
"Ban taɓa ganin abin da ya raina ni ba kamar ke? Amm dama zan gaya miki, ina ganin zan canza lawyer, saboda na lura baki da sa'a ko kaɗan, gashi baki wani goge ba, nafi son wanda zai din ga abin da nake so. Idan na biye miki, sai na koma prison, kuma ƙila nima a bini a kashe a can, kamar yadda aka kashe wannan mutumin, dan haka zan canza lauya".
Ɗagowa tayi tana kallon Viper, cikin tsananin mamaki da takaicin abin da yake fitowa daga bakinsa.
Fuskarsa a ɗaure, alamar da gaske yake yi.
"Bayan duk wannan wahalar da na riga na sha? Ka san zaka ɗauki wani lauyan, amma ka wahalar da ni, nake ta dagewa ina ƙoƙari a kan shari'ar ka na kasa zaune na kasa tsaye?"
Viper ya ce "Eh, muddin zaki cigaba da yi mini rashin kunya, tabbas zan sake saka miki ƙarfe wataran, kamar yadda na saka miki da farko, na gaji kin kasa kawo ƙarshen lamarin, kullum sai surutu da shirme ki ka iya"
Tamkar ta kwaɗe shi, haka wani abu ya cunkushe mata ƙirji, kawai ta kifa kanta a kan gwiwarta.
"Abla, ɗago ki ga" banza tayi masa taƙi ɗagowa.
"Kin san magana ɗaya nake yi" ta ɗago idanunta, da suka yi sharkaf da hawaye.
Ya ajiye mata takarda a gabanta, takardar umarnin kotu ce, da ta hana kama shi, ɗagowa tayi ta kalleshi, ta rasa ihu zata yi na murna ko kuma me? Kawai ta cukuikuye takardar, ta jefa masa a ƙirji, ta sauka daga kan gadon tana cigaba da kuka"
Murmushi ya yi ya tashi ya bi bayanta, cikin kuka ta ce "Amma a haka kake cewa zaka canza lauya?"
Ya ce "Sorry, am just kidding"
"A haka ake wasa Vi?, fuska a ɗaure ana zare ido? Tayaya zan gane wasa kake yi?" Tayi maganar tana kuka cike da shagwaɓa.
Ya ce "Viper baya manta halacci, ba kuma ya saɓa alƙawari, ko da zaki yi failing sau dubu, ba zan taɓa barin ki ke kaɗai ba, alƙawari ne da na ɗauka"
Nabila ta ce "Look at you, i even save your life, amma da haka zaka yi mini albishir da 'yar ƙaramar nasarar da nayi" ya girgiza kai ya ce "Ba ƙaramar nasara ba ce Congratulations, and barrister Habib ya yi miki message, Civil defense sun ɗaukko rahama" a take ta waro ido ta ce "Dan Manzon Allah, da gaske?" Ya jinjina mata kai, alamar eh.
Rikicewa tayi, ta durƙusa tayi sujudu shukur, ta tashi, ta shiga kaiwa tana komowa ta ce "Alhamdilillah, ko yanzu na mutu, na cika wani sashe na alƙawarin da nayi, Allah sarki malam Garba, Allah ya yi masa rahama, ni me ma zan yi ne dan daɗi Vi?"
Murmushi take yi, tana kuka, tana ta zarya a ɗakin, kamar zata zare, shi kuma sai bin ta yake da ido. Ta je ta tsaya a jikin bango, ta jingina tana sauke numfashi.
Ya sake takawa, ya ƙarasa in da take ya saka hannunsa ɗaya ya dafe bango, yana cigaba da tsareta da ido.
"Thank you for saving my life 'yar suga" duk da ta takura, amma bai hanata yi masa murmushi ba.
Kallonta yake yi, yana tunanin a yaya zata ɗauki ƙaddarar da take bibiye da ita? Ko zata iya jurewa, ko zata gaza kamar yadda yayi? A hankali ya ce "Wannan babbar nasara ce ki ka samu, kamar yadda nayi tsammani, ba kya gori, kamar yadda Jauhar take, na zata da na ce zan canza lauya, zaki yi mini gori, amma ba ki yi ba.
Akwai tambayoyi da ki ka yi mini a baya, da wasu wanda nake son na yi miki.
Da fari meyasa nayi yinƙurin kashe ki karon farko da na ganki? Meyasa ki ka ga ruɗewa a fuskar liti da walid da suka ganki? Meyasa na din ga korarki idan ki ka zo wurina, nake yi miki barazanar mutuwa? Meyasa su liti suka amince su kawo ki wurina, duk da babu mahalukin da suke bawa damar hakan? Meyasa Indabo ya ke ƙoƙarin yi mini tarko da ke? A yanzu ko a baya, ba za a rasa mutanen da suka nuna miki sanayya ba, alhalin baki san su ba right?" Ta tsare shi da ido tana jiran amsohin tambayoyin.
"And as my lawyer, akwai abubuwan da yakamata na sanar da ke, but before then, Abla ni da ke ƙaddara ce mai ƙarfin gaske ta haɗa ni da ke, dan haka dole mu yi haƙuri, mu karɓeta a yadda ta zo mana, saboda pain ɗin da zaki shiga, zai iya fin wanda ni na tsinci kaina a ciki"
Tayi tsuru tana kallonsa.
Ya zaro wani hoto a aljihunsa, ya miƙa wa Nabila.
Hannunta na rawar rashin sanin wace ƙaddarar ce, ta sanya hannu ta karɓi hoton, wata 'yar ƙaramar ƙara ta saki, ta saki hoton a ƙasa, jikinta yana rawa, ta kalleshi ta ce "Soka ke sai na haukace sannan zaka daina yi mini wasa da hankali, menene wannan? Ni bani bace wannan, ni yaushe na sanka har muka yi wannan hoton tare?" Tayi maganar a firgice, tana neman ta raɓa shi ta wuce, amma ya riƙeta a jikin bango, idanunsa suka cika da hawaye ya ce "Matata ce a jiki, ita ce jauhar, 'yar madarata, mace mafi soyuwa a gare ni, matar da ba zan manta halaccinta ga rayuwata ba, matar aljanna da kullum nake fatan na farka daga mummunan mafarkin da nake yi, na farka na ganta a kusa da ni, Nabila meyasa ki ke kama da matata?" Jikinta ne yake wata irin rawa, ta zazzaro ido tana kallon sa.
Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, suka waiwaya gaba ɗaya suna kallon ƙofar, Alhaji mu'azzam ne ya shigo tare da barrister Habib, da kuma ɗan mama, da yake laɓewa a baya, yana leƙowa.
Cikin mamaki Viper yake bin Alhaji mu'azzam da kallo, ba tare da ya saki Nabila ba.
Ayshercool
08081012143
78
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
Cak Viper ya tsaya yana bin kankarofi da kallo, zuwa kan ɗan mama da yake ta zazzaro idanu.
Kankarofi ya haɗiye wani abu mai ɗaci, saura ƙiris ya yi loosing control ɗin sa, saboda yanayin da ya ga Viper da Nabila.
Viper ya a janye hannunsa a hankali, ya tsaya a tsakiyar ɗakin, su kankarofi suka shigo.
"Meya kawo ka in da nake?" Yayi maganar a kausashe.
"Haba ƙanina, mayar da wuƙar mana, abun rabo ya ƙare, miƙa hannu na menene, bai kamata ace zuwa yanzu muna cigaba da wannan abubuwan ba, ko da ran jauhar, ko babu mallakinka ce, matarka ce dan haka ba zan din ga bibiyarta ba, balle yanzu da babu ranta, ka sassauta wannan kishin dan Allah. Ga Anas, wato ɗan mama yaronka na hannun damanka, da duk wani nasarar aiki da muka yi a kanka, ya faru ne saboda ƙoƙarin sa, sai dai kan mu kai ga bayyana maka komai, ashe ka gano shi, ya gudo wurina hankali a tashe, ya ce na taimake shi, ba zai iya jure hukuncin da zaka yi masa ba, na zo on his behalf, na bayar da haƙuri kuma nayi maka bayanin komai"
Viper ya bi ɗan mama da wani irin kallo, ɗan mama ya ce "Na shiga uku, dan girman Allah Oga Viper kayi haƙuri, tursasa mini aka yi, wallahi bani da niyyar cin amanarka, ban taɓa cutar da kai ba, ka san ina yinka, kamar yadda ka ke yi na, kayi mini rai saboda Allah"
Alhaji mu'azzam ya ce "Ya isa haka Anas, ni yakamata na wanke ka" duk maganar nan, Viper idonsa na kan ɗan mama, ɗan mama ya sake maƙalewa a bayan Kankarofi ya ce "Gaskiya daga nan kayana zan tattara na gudu Cadi, kallon nan da yake yi mini, tsoro yake bani, bana tunanin zai yafe mini, da ƙyar idan bai saka na gana da Russia ba"
Kankarofi ya riƙo hannun ɗan mama, suka ƙarasa gaban Viper, ya numfasa sannan ya ce "Lokacin da uban gidanka yana raye, Dodo, ka fi ni sanin waye shi, ka fini sanin hatsarinsa da imaninsa. Babu wanda ya bawa damar sanin sirrikan da yake da su, kuma ya sani sai kai.
Duk da shi ma mai aikata laifi ne, amma yana yi wa hukumomi amfani sosai wurin kama masu laifi, daban-daban.
Ya baka horo na musamman, ta yadda yake gane masu laifi, komai kamalarsu, yadda yake iya gane idan akwai kayan laifi a wuri, bai tsaya nan ba ya saka aka baka horo na musamman, a kan fasahar na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Manyan ƙasar nan na mu'amala da shi sosai da sosai, dan ya san duk wasu hanyoyi da za a iya shiga da fitar da kayan laifi, ciki da wajen ƙasar nan, ba tare da ta an kama kaya ba, sukan haɗa kai da shi, su bashi dukiyoyin su, ya yi musu kasuwancin ƙwayoyi da sauran kayan laifi, ya ruɓanya musu riba a shekara".
Viper ya ce "Duk meye amfanin dawo da abin da ya riga ya wuce, abin da na riga na sani, kar ka aibata gawar uban gidana"
Kankarofi ya ce "Ba aibata shi nake yi ba, kayi haƙuri na sadaka da gaɓar da nake son na kai ka. Dodo yayi shirin yin murabus, bayan ya koyar da kai manyan abubuwa, da ka iya zama makamin rusa wasu daga cikin manyan hanyoyin aikata laifuka da ba kowa ya sani ba.
Daf da zai mutu, ya danƙa amanarka ga manyan mutane da ya yarda da su, ciki har da shugaban hukumar NIA na wancan lokacin, ya basu tabbacin zaka iya basu gudunmawa ta kowane ɓangare, sukaɗai ne hukumar da ya yarda ya damƙa amanarka a hannunsu, duk da kasancewar baka ji, amma kai babban makami ne, ka san manyan sirrukan da bayan shi babu wanda ya sani.
Bayan mutuwar dodo, sun buƙaci kaje su baka horo, kayi aiki da su, amma ka ƙi, saboda zuciyarka da tunaninka na kan ɗaukar fansa a kan madaki, kuma rashin yadda ya sanya ka sake cewa ba zaka je ba, dan baka da tabbacin ta wace hanya zasu yi amfani da kai.
Bayan aurenka da jauhar, bayan na shiga damuwar rashinta, wataran muna hira da cousin ɗina, wanda shi ne aka danƙa amanarka a wurinsa, muna hira, yake bani labarinka, a nan na gano cewa lallai kai ne ake magana a kai, na cigaba da matsa masa, a kan lallai suyi ƙoƙarin su ga sun ɗauke ka, zaka yi musu amfani sosai, a lokacin ina fatan silar aikin, ka daina wani abun, kuma ka samu hanyar kula da Matarka.
Har bincike na saka aka kuma yi mini sosai a kanka, a nan na gano kana aiki da Indabo, abin ya ɗaure mini kai ya bani mamaki.
Bayan wani lokaci, ban san meyafaru ba, na samu labarin ka je ka basu haɗin kai, an kama ɗan gidan indabo a Mexico, da laifin safarar cocaine, duk da babu wanda ya sani, amma ni ina da hanyar samun bayanai na a kanka.
Na cigaba da fatan Allah yasa daga haka su hilace ka, ka amince da aikin nan, amma sam baka da intrest a kan haka.
Wasu lokutan Hafsa kan bani labarin, irin soyayya da ƙaunar da ka ke yi wa jauhar. Kwatsam na samu labarin mutuwar ta, wai ka sha miyagun ƙwayoyi ka kasheta, sai dai sam ban ji na yarda ba.
Daga yadda na bibiyi case ɗin silently, naga sam babu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 82 Chapter of 121