ne, kema baki fahimce shi bane"
"Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga siraɗin gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini"
Walid ya ce "Ki yi haƙuri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke"
"A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?" Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta.
Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ɗaga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar aljihunsa ya yi gaba.
***
"Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse" Sumayya ta yi maganar tana ƙare mata kallo.
Baba magajiya ta ce "Gara dai ki yi mata, ko ta ji, taƙi gaya mini meyake damunta, sun samu saɓani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ƙarewa take yi kamar kuɗin guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta" Sumayya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Wallahi kuwa baba magajiya, da 'yar ƙibarta tafi kyau, haba jarumar mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ƙwarin gwiwar? Muje mu zanta na ji menene ya faru".
Suka tafi ɗakin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce "Gaya mini menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi faɗa da Abba, me ki ka yi?"
Ta kalli sumayya ta ce "Sumayya haka soyayya take dama?"
"Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya.
Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ƙarƙashin ƙasa da kaina"
"A'a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ɓaci"
"Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani abun ba za ayi mini shi ba"
"Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya"
Ta numfasa ta ce "Ƙaddara ta kaini ta baro sumayya"
Sumayya ta waro ido ta ce "Kamar yaya?"
"Son abun da ba zan samu ba nake yi"
"A'a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ɗin tukuna ma dai"
Nabila ta tashi, ta saka key, ta buɗe wardrobe ɗin ta, ta ɗaukko file ta zo ta ajiye a gaban Sumayya.
Sumayya ta ɗauka ta fara bubbuɗewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin matsananciyar kiɗima da tashin hankali ta ce "Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila"
Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Ta daki kafaɗar Nabila ta ce "Kin san in da mutumin nan yake, da gaske haɗuwa ku ka cigaba da yi da shi, har ki fara son ɗan daba?"
"Ɗaga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya"
"Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta haƙilo yana fama, ko ɗazu an kawo mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ɓaɓatu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya ne?"
"Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka faɗa tabbas ina haɗuwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan taɓa bari hukuma ta kama shi ba"
Sumayya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila? Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ɗan daba mashayi, dan ta'adda?"
Ta girgiza kai ta ce "Sumayya ƙaddara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da zaɓin yin wanda ya dace". Ta tashi ta nufi wardrobe ɗin ta, ta mayar da file ɗin.
"Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba"
"Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne dai-dai"
Sumayya ta ɗauki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan bata taɓa tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ɗin ba.
Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ɗin jami'an tsaro, ta ɗauki, jakarta ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan.
Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce "Sir dan Allah ka yi wani abu a kai, rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ɗan ta'adda take shirin kasadar karewa"
Yayi murmushi ya ce "Sumayya ƙawarki ba ta ji, bar ta ai ɗaukaka take nema, mu yi mata fatan nasara"
"A'a sir, dan Allah ba zata iya ba"
Kankarofi ya ce "Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ɗin sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu'a, in da ki ka ga ana buƙatar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi ƙoƙarin dakatar da ita, wannan gargaɗi nake yi miki" ya kashe wayar.
Sumayya ta ce 'Naga ta ta kaina ni sumayya"
***
Suna zazzaune a ɗakin, suna ta shan sigari, ya ɗaga kai kawai ya ganta a tsaye a ƙofar ɗakin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba.
Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask.
Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye.
Liti ya ce "Su 'yar anace ce da yamaccin nan ashe"
Walid ya ce "Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da hayaƙi, gashi ke ba kya son hayaƙi"
Viper ya yinƙura ya tashi, ya ce "Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta jagwalgwala ki" yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a jiki ta fito da harshenta.
Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ɗin sa, irin ina saurarenki.
Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara gajiya, yana zuƙar sigarinsa, yana fesarwa a gefe.
Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ƙasa, ya kalleta amma ta haɗe rai.
"Ina jinki ya aka yi?"
"Alhaji mu'azzam da ku ka haɗu, dama ka san shi ne?"
"Haka ya ce miki?"
"A'a, tambayarka kawai nake"
"Ki bar maganar sa kawai"
"Saboda me?"
Ya ce "Saboda haka na ce"
"Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda zan ɓullowa lamarin, ka gaya mini shi menene alaƙarka da shi?".
A hasale ya ce "Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ɗin ba shi da wani amfani".
"Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam" tayi maganar tana kallon ƙwayar idon Viper.
Ayshercool
08081012143
72
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
*Ina ma'abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, ƘARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A BAKU LABARI.
Waro ido suka yi waje, jin abun da Nabila ta yi wa Viper, liti ya doko tsalle yana faɗin "Ke! Saken da ki ka samu har ya kai haka, mai zamanin ki ke yi wa tsawa?"
"Nayi ɗin, kai kuma a suwa?" Tayi maganar cike da son huce takaicinta a kan liti.
Walid ya yinƙuro ya fito, amma Viper tuni ya danƙi ƙeyar Nabila, Walid ya yinƙuro, amma Viper ya ɗaga masa hannu, ya yi waje da Nabila.
Sai da ya yi nisa da ita, sannan ya saki ƙeyarta, ta ja da baya, tana ƙifta idanu.
Ya taka a hankali ya ƙarasa gabanta, ya tsaya ya kalleta ya ce "Ni ki ke wa tsawa a gaban jama'a ko?"
Ta sunkuyar da kai, tana yamutsa fuska tare da tura baki.
"Karki yi ƙoƙarin tsallake iyaka, ki kaini bango, idan na yi magana bana son jayayya, ki ƙyale wannan maganar, ki tafi da id card ɗinki zan tura miki adress ɗin da zaki je, a asibiti ne kiga shaidan da nake da shi, wato madaki.
Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Kai ba zaka je ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Tsoro nake ji, na samu labarin yayanki ya ƙara tsananta nemana kar ya kamani"
Nabila ta ce "Hotonka yake nema, ya ce a samo masa hotunanka, ina tunanin hotunanka za ayi sharing ace ana nemanka"
Ya ce "Duk neman da yake yi mini ma bai sanni ba, a confused blind man" yayi maganar tare da yin murmushi. Sai da ta kuma kallonsa, ganin yana murmushi, murmushin ma a nutse yake yi.
Kallonta da ya yi, ya sanya ta daina kallonsa, ya ce "Amm kwanaki, kamar akwai maganar da ki ke son ki yi mini, something like wani abu yana damunki"
"Baka tambaye ni a lokacin ba sai yanzu, ka manta ba wani abu bane, ya wuce" tayi maganar cikin tsiwa, tana kawar da kanta gefe.
Kallonta yayi, bai ce uffan ba, ya zira hannu a aljihunsa, ya ciro wayarsa, ya danna ya saka a kunnensa, ya ce "Kawo mini abun nan, na ƙasan katifata, ina wajen bishiyar kalgon nan"
Shiru ya wanzu a tsakaninsu, sai ga ɗan mama ya ƙaraso, ya miƙawa Viper envelope, ya saka hannu ya karɓa ya ce "Zaka iya tafiya"
Ya kalli Nabila ya ce "Gashi, wani abu ne daga aikinki ne na fara biyanki wani abu, idan komai ya kammala, in sha Allah zan yi miki kyakykyawan biya"
Ta karɓi envelope ɗin ta jujjuyata, ta saƙala masa a hannunsa ta ce "Da dan kuɗi zan yi maka aikin nan, da ba zan yi shi ba, bana buƙatar kuɗinka, a wurin Allah nake neman ladan abun da zan yi maka, ba wai dan halinka ba"
Shi ma ya jujjuya envelope ɗin, ya ce "Rashin sani, ya fi dare duhu, abun da yake ciki yafi kuɗi muhimmanci a wurinki, zaki dawo ki nema da kanki, shikenan a sauka lafiya"
Ta shagwaɓe fuska tana kallonsa, shi ma ita yake kallo, ji yake kamar ya tambayeta me yake damunta, ta rame, amma ya kasa.
"Kayi haƙuri"
"Da me?"
"Kayi haƙuri ka bani"
Ya zira aljihunsa ya ce "Ai kuma kin yi wa kanki, maganin mara kunya, wuce ki tafi gida, kan a fara nemanki"
Ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah"
Viper ya ce "Kar ki ɓata mini rai, wuce ki tafi"
"Korata ka ke yi ko? Dan Allah meyasa ka tsane ni ne? Me nayi maka?, Kalli duk rashin lafiyar nan da nayi, ko sannu fa Viper, sannu kawai baka iya yi mini ba, abun yayi mini zafi fa"
"Really?"
Ta haɗiye wani abu mai ɗaci, ta gyaɗa kai ta ce "Shikenan, bari na tafi, in sha Allah zan yi duk abun da ya dace" ta juya zata tafi ya ce "Amm meye ma sunan naki? Abla ko?" Ta waiwayo ta kalleshi, ta fara tunanin a ina ma aka taɓa kiranta da wannan sunan?.
Ta girgiza kai ta ce "A'a Nabila"
"Ohh, sunan yayi mini tsayi, just accept it Abla"
Kamar ba yanzu ya gama yi mata wulaƙanci ba, ta ce "Nice one, na gode sosai" tayi maganar tana ɗaga masa hannu.
***
"Hello, Salim kana ina ne?"
"Bokan turai, ya aka yi ne?"
"Dan Allah gida nake son ka samo mini"
Salim ya ce "Gida kuma?"
"Eh salim, amma ba na son kowa ya sani, a wajen gari kuma, saboda na san daddy zai saka a fara bibiyata, sun dage lallai sai sun gano in da rahama take".
"To kai yanzu hakan da ka ke yi kana ganin shi ne dai-dai?"
Abdul ya ce "Shi ne, dole zan danƙata a wurin iyayenta, na kai ta makaranta kafin su san in da take"
"Abdul, ina tsoron abun da zai biyo bayan abun da kake yi ne?"
"Salim, rayuwar rahama nake ƙoƙarin karewa da ingantanwa, dan Allah ka taimaka mini, kar a kuma cutar da yarinyar nan a wannan karon"
"Shikenan, babu damuwa za a duba in sha Allah"
"And sirri ne Please, ko saif ba na son ya sani"
"Haba mutumina, ba sai ka jaddada mini ba, you are safe"
"Thank you"
***
Kankarofi yana zaune a kan gadonsa, yana daddana wayarsa, ya ci karo da lambar Hafsat. Ya yi shiru yana kallon lambar ta ta, ya shafi saman lambar yana tuno ta, yarinyar ta nuna masa so, kuma shi kansa ya san ba dan yana son ta ya aureta ba, amma beside his wealth, ta so shi, ta yi iya ƙoƙarin ta a kansa, amma ya kasa sakewa da ita, yayi mata adalci, har auren ya mutu.
Amma ita jidda bai ji haka a kanta ba, hasali ma sosai suke gogawa ita da Safiyya, duk da dama Jidda tsohuwar budurwarsa ce, lokacin tun suna jam'iyya ɗaya da Indabo, kuma za su yi sa'anni da Safiyya, ita kuwa hafsa yarinya ce dama. Ya ji ciwon rashin samun auren jauhar da bai yi ba, amma duk da haka yana yi wa Allah godiya, da ba jauhar ya aura ta wahala suka rabu ba.
Shiyasa ko zai ƙarar da duk abun da ya mallaka, sai ya tabattar da indabo ya girbi abun da ya shuka, ba ƙanwarsa yake aure ba, ko babarsa yake aure, bai ji zai iya ɗaga masa ƙafa ba, kisan mummuƙe zai yi masa, kamar yadda shima indabon yake yi.
Jidda ta ce ta shigo ɗakin, sanye cikin doguwar riga, ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi, ya ce "Ya dai?"
Ta yi guntun tsaki ta ce "Nifa gaskiya na gaji"
"Da me?"
"Haryanzu ana yi mini sintiri a kan rashin mutuncin da Abdul yayi, yau wannan ya zo, gobe wancan ya zo, duk security ɗin nan, gaskiya ni kawai ka canza mini gida, mu bar estate ɗin nan, na gaji wallahi"
"Mu bar estate ɗin nan, amma ɗaya gidan kin san na sister ɗinki ne, a nan suke zama idan sun zo hutu"
"So find another one mana, am tired hell of all this, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, tun da abun ya faru ban sake ganin Abdul ba, ga babarsa ta kira ni tana nema ta gaggaya mini magana, wallahi rashin ramma a gidan nan, gaba ɗaya bana samun komai yadda nake so, khalifa da ansar haryanzu suna tambayata, yaushe yarinyar nan zata dawo, sun saba da ita, Abdul yayi mini hauka wallahi " har ta gama surutanta, murmushi kawai Alhaji mu'azzam yake yi, bai ce mata uffan ba.
***
"Hello Ambassador Tahir Arabi"
"Distinguish, ya aiki ya Nigeria?"
"Alhamdilillah"
"Masha Allah, dama maganar yaron nan ne"
Indabo ya ce "Na wurina? Jafar?"
Amb Tahir ya ce "Eh shi, wallahi distinguish sai haƙuri, sun bawa America shi, kuma yana daf da fara fuskantar shari'a, kuma na lura babu wani abu da embassy ɗin mu zasu iya yi a kai, duk da dai haryanzu muna cigaba da ƙoƙari"
Indabo ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ambassador ba wani abu da za a iya fa ka ce?"
"Wallahi kuwa, ka san kisan kai yayi a amurka ya gudu Mexico ya cigaba da harkar ƙwayoyi da hodar iblis tsakanin Nigeria da mexico, yadda aka shirya kama shi, akwai ƙwarewa sosai da sosai, bisa ga wata yarjejeniya da haryanzu bamu san ta mecece ba tsakanin Amurka da mexico suka basu shi, wataƙila musayar fursunoni suka yi"
Jiki a sanyaye Indabo ya ce "Na gode sosai da sosai"
Ya katse wayar ya dafe goshinsa ya rasa abun da yake yi masa daɗi.
*****
Da daddare Nabila na kwance, tana ta tattara bayanai a kan shari'ar Viper, sai ƙarfe ɗaya na dare, sannan ta samu sukunin kwanciya.
Ta janyo wayarta, tana duddubawa, ta ga lambar Viper, kawai ta danna kira.
Bisa ga mamakinta kawai ta ji ya ɗaga.
Ta ce "Viper"
"Mmm"
"Ba ka yi bacci ba?"
"Mmm"
Tayi murmushi ta ce "Me ka ke yi ba ka yi bacci ba?"
Muryarsa ƙasa-ƙasa kamar mai jin baccin ya ce "Abun da ya hanaki bacci ne hana ni"
Ta ce "Wai ni? Ai ni soyayya ce ta hana bacci" tayi maganar tana murmushi.
Viper ya ce "Nima haka, tunani da kewar matata ne ya hana ni bacci"
"Ai addu'a zaka yi mata"
"Ina yi mata, zafi ya dame ni, ina missing fankata" yayi maganar very serious yana lumshe idanunsa.
Nabila ta ce "Fanka? Wace irin fanka kuma?
Ya ce "Fankar solar ce, iskarta daidai ba mai cutarwa ba"
Nabila ta ce "To ko sayo fankar za ayi, ban zaci ana zafi a wurin nan ba ai"
"A'a nikaɗai nake jin zafin ai"
Tayi dariya ta ce "Ko ƙiba ka yi ne? Zan sayo maka fanka in sha Allah"
Viper ya ce "Ki ƙyale maganar fankar nan, ba ki da kuɗin sayenta, ba irin wadda nake buƙata zaki saya ba" yayi maganar yana juyi tare da gyara kwanciyar sa.
"Ka gaya mini, zan sai maka in sha Allah, wace iri ka ke so i promise"
Ya ce "Ba zaki iya sayenta ba"
"Ka gaya mini, zan nemota in sha Allah"
Viper ya ce "Ita fankar?"
"Eh mana"
Kawai ta ji yana dariya, har da gyaran murya.
"Kai, dama kana dariya?" Tayi maganar tana tashi zaune.
Yayi shiru bai ce komai ba.
"Viper"
"Mmm"
"Dan Allah me ka bani a envelope ka ce zan dawo ina nema da kaina?"
"Ki manta, ya wuce kawai, zan baki address ɗin nan, ki je ki samu mutumin nan"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "To, kayi bacci mai daɗi"
"Zafi ya dame ni, ba zan iya bacci ba"
Ta ce "Ka tashi liti yayi maka fifita"
"Na gaya miki fanka nake so ai, sai da safe"
"Ai ka ƙi gaya mini wace iri ce, dan dai fanka sai na saya maka, shikenan yau na ci pass an yi mini dariya"
"Hmm" kawai ya ce.
Ta sake cewa "Viper"
"Kar sunan ya ƙare"
Tayi murmushi ta ce "Sunan daɗin faɗa, Viper, in shot kuma V.Snake" ta faɗa tana murmushi.
Ta sake cewa "Wai a ina aka yi maka rigar nan, nima ina so"
"Wacce?"
"Wadda aka rubuta sunanka a jiki"
"Nawa zaki saya?" Gyara zama tayi, jin yana kulata yau.
"Ayi mata kuɗi, zan saya ko nawa ce, ka san wani abu, idan Allah ya sa muka yi wining a court, rigar nan zan saka in yi ta yawo ina murna"
"To, Allah ya bamu sa'a"
"Amin V snake"
Wasu lokutan simple da shi, wasu lokutan kuwa, sai ka rasa gane kansa gaba ɗaya.
Ta ce "Sai da safe"
"Hmm" kawai ya ce, ta katse kiran.
***
Sanarwa ko ta ina, a kan tsananta neman Al'amin Viper, tare da alƙawarin kyauta mai tsoka ga duk wanda ya nuna ko ya bayar da information a kan in da za a same shi.
Nabila ta damu sosai, ga Sumayya ta daina ɗaga wayarta, dan haka ta shirya tsaf, ta tafi wurin aikin sumayya.
Sumayya na ganinta ta haɗe rai, Nabila ba ta yi fushi ba ta ƙarasa in da take ta ce "Sumayya ba kya ɗaga wayata meyasa?"
"Ban sani ba, na gaji da wahalar da ki ke saka mu ne, babu dalili Nabila, daga wannan sai wancan? Gaba ɗaya kin hanamu nutsuwa da sukuni, ki jijjigo mana wannan masifa muna zaune, wane irin kallo ki ke so ayi miki, idan aka ga kin koma bawa ɗan ta'adda kariya, hukumar yan sanda na nemansa ruwa a jallo, ke kina tare da shi"
"Sumayya, baki yi mamakin yadda na sauya lokaci guda ba? Har kin manta huci da haƙilon da nake yi a kan a kama shi, kwatsam ki ji na koma na ce zan tsaya masa na bashi kariya, ayar tambaya yakamata ki fara saka mini, meyafaru?"
Sumayya ta ce "Ba wani in tambayi meyafaru, kawai ki cire kanki daga wannan sabgar"
Nabila ta ce "Wallahi ba zan ajiye ba, ko me za ayi mini" kawai ta saki baki tana kallon Nabila.
"Ko dai ki tayani a wannan karon ma, ko kuma ki ƙyale ni ki zuba mini ido, yanzu ya maganar program"
Sumayya ta ce "Mhmm yana nan, Nabila ni yanzu kin daina bani mamaki tsoro ki ke bani, yanzu duk bala'in nan, kin san in da Viper yake"
"Ƙwarai ki gaya wa uban kowa da ki ke so masoyiyya"
"To, Allah ya taimaka"
"Amin, gama mu tafi ki rakani wani wuri"
Sumayya ta ce "A'a ba zaki kai ni in da za a kashe ni ba"
Nabila ta ce "Wane irin kashe ki kuma, mu je dan Allah"
"To ki tsaya na kammala abun da nake yi, sai mu tafi"
Ta kammala abun da take yi, suka fita, tare da sumayya.
Tiryan-tiryan suna tafe, har ƙofar ɗakin da Viper ya rubuto mata, wasu masu sanye da kaki, suka tarar a ƙofar ɗakin a tsaye, Nabila suka gaisa, ta ciro id card ta nuna musu.
Suka ce ta shiga, amma ban da sumayya, Nabila ta ce "Ita ma ma'aikaciya ce, yar jarida ce"
Suka ce "A'a kekaɗai aka ce mu bari ki shiga".
Sumayya ta ce "Ba damuwa, zan jira ki a nan"
Nabila ta shiga, ta yi sallama ta tarar da mutum a zaune a kan gado, hannunsa ɗaya an saka masa sarƙa, ƙafarsa kuma ɗaya an yanke ta.
Ta ƙarasa gaban gadon, ta ja kujera ta zauna, ta kalleshi ta ce "Sannu malam"
Ya ce "Yauwwa"
Ta ciro id card ta nuna masa ta ce "Sunana barrister Nabila, na zo ne a kan case ɗinka da Al'amin mai zamani.
Ya ɗago ya kalli Nabila amma bai yi magana ba.
"Ka yi magana, dan ka sauƙaƙa wa shari'a, me ka sani game da kisan da aka yi wa matar mai zamani?"ya yi shiru ya ƙi magana.
Tayi tayi, amma yaƙi cewa komai, ƙarshe haka ta fito bai yi magana ba.
Sumayya suna ta hira da security ɗin wurin, Nabila ta fito, tana ganin Nabila ta tashi ta ce "Kin gama?"
Nabila ta ce "Eh mu tafi"
Suna tafe ta kira Viper a waya, ta ce "Hello V snake"
"Barrister"
"Naje wurin gayen nan, amma yaƙi magana, nayi nayi, yaƙi magana"
Viper ya ce "Rabu da shi, zai yi ta ƙarfin tsiya, ki tafi kawai"
"Ok, na ma taho, amma yakamata yayi magana gaskiya, bari na ƙarasa gida sai anjima" ta kashe wayar.
Sumayya ta ce "Nabila wai wurin wa ki ka zo ne?"
"Zan yi miki bayani, amma ba yanzu ba"
Ta ce "Ok shikenan"
***
"Rahama kina ji na?"
"Ina jinka"
"Zamu sake barin gidan nan" "Zuwa ka mayar da ni gida?"
"Wai na mayar da ke gida ki yi me? Ai kin san iya wuya muna tare, nan zamu bari temporarily, daga can kuma zan kai ki gida, sai kuma makaranta, a abuja zaki koma da karatu ai"
"Yar ƙauye a Abuja, to ai ban iya turanci ba, ni gaskiya na fi son makarantar garinmu"
Abdul ya yi dariya ya ce "Ai Shiyasa zaki je Abujan, zaki iya turanci, kan ki gama ki ƙara gogewa ki zama her excellency rahama"
"Taɓ abun ma ba tsari"
"Kamar ya babu tsari?"
"Wata zaka aura ai, kuma ni a lokacin mutane zasu ji daɗin nuna ni suna aibata ni"
Abdul ya girgiza kai ya ce "Muna tare, babu wanda zai aibata mini ke"
Ramma ta yi murmushi ta ce "Ba zaka iya canza komai ba, ɗabi'ace ta al'ummar hausawa"
Ya ce "Shikenan, mu bar maganar"
Ta ce "Ya dai fi"
Wayarsa ya ɗaga, ya ɗan gyara zamansa ya ce "Na'am Mummy"
"Wato Abdul kafi son ka yi ta sakani a tashin hankali da damuwa ko?"
"Mummy me nayi kuma?"
"Ban sani ba, ka saka babanka yana yi mini kallon ni nake goya maka baya ka ke yi masa rashin ɗa'a, ka fito da yarinyar nan ka huta su huta ka ƙi, rashin mutuncinka har ya kai ka ajiye mace kana lalata da ita, bayan na keta mata haddi,, ga ɗan uwanka can an mayar da shi america, sai abun da Allah ya yi, shiyasa ake ta fafutukar ka zama gwamnan nan ko a samu ya fito, amma ka ƙi, ya ka ke so na yi Abdul, in bar muku duniyar ka huta ko?"
Cikin damuwa ya ce "Mummy ki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 76 Chapter of 121