kai tayi da sigar magiya tana kallonsa.
"Hello. Hello, Arfa" muryar Nasir ta fito rangaɗau a wayar.
Viper ya ɗaga idonsa yana kallon ƙwayar idonta, ga mugun riƙon da ya yi wa hannunta da take jin tamkar zai ɓalle.
"Arfa kina ina ne? Hello kina ji na?"
Kallon da Viper yake yi mata, gaba ɗaya sai ta rikice, ga kusancin da suke da shi, ta ƙara rikicewa. Kasa daurewa tayi ta ce "Wayyo hannuna"
"Nabila, menene? Kina ina ne?"
Al'amin ya sakar mata hannunta, ya katse kiran, ta ja da baya tana murza hannunta tana ƙifta ido.
"Amm meye ma sunan naki?"
Ta kalleshi tana turɓuna fuska ta ce " 'yar madara"
Cikin sauri ya kalleta ya ce "Iyee?"
"To idan ban kai 'yar madara ba, ka din ga ce mini 'yar suga, ko mazarƙwaila" tayi maganar tana cigaba da murza hannunta.
"Baki shiryawa wannan ranar ba, ki ka yi gammon ɗaukar abun da baki san a ina zaki sauke ba?"
Ta gyara zamanta ta ce "Nayi mana, ai shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Amma yau da ka gaya wa DSP muna tare, da ka gama kashe ni da raina, ban gama da aikin gabana ba, ka sake ɓallo mini ruwa.
Zaman kotun nan na yau ya bani haushi, Alƙalin alamu sun nuna side zai ɗauka, gashi dattijon nan ya musa ya ce ba shi bane ba, sun kafa hujja da shi ne, wai lokacin da abun ya faru daga shi sai ita, kuma ita da shi da wata mai aiki ne, amma har gidan ɗayar naje ban same ta ba.
Su kawo ita rammar kotu, ba su kawota ba, ba su da wata tabbatacciyar shaida, recording ɗin da na gabatar, an soke an ce sai dai uwar taje da kanta, ni na rasa me ma zan yi wallahi" tayi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Ya nuna mata file ɗin hannunsa ya ce "Waye ya baki wannan?"
"Ban san waye ba, a kan teburina kawai na ganshi da safe" ya cigaba da daddana wayarta, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kin ɗauki hotona, dan ki nuna wa yayanki ya kama ni?"
Ta kalli wayar hannunsa, ta ce "Ai nayi hiding ɗin hoton, ya aka yi ka buɗe?"
Ya sake kallonta ya ce "Me kike da hotona?"
Nabila ta ce "Saboda in din ga kallonka, ina jin daɗi, askin nan da aka yi maka kayi mini kyau sosai da sosai ne" tayi maganar tana murmushi.
"Amm, amma dan Allah ina ka tafi, naji su Oga walid sun ce, ɓata kayi, wai ranar da muka rabu ina ka tafi? Can ka koma ko? A can aka ji maka ciwon nan. Na tsorata da naga an yanki cinyar wani, da sun ganni nima kasheni za su yi ko?"
Gyaɗa kai yayi, ya ce "Kina da system?"
"Eh tana gida amma" ya cigaba da danna wayarta.
"Wai dama kana magana haka? Baka taɓa yi mini doguwar magana ba sai yau. Hmmm da tabon wuƙarka da ka yi mini zan koma ga Allah, ka kusa fa kashe ni ranar farko da muka haɗu, ban san laifin da nayi maka ba ka kusa kashe ni. Amma dai yau ba ka sha komai ba ko? Naga yau ka yi mini kirki" jefa mata wayarta yayi ya tashi tsaye, ya ce "Ki kula da kanki, ana bibiyar ki, ana bibiyar wayar da ki ke yi da wata sumayya, akwai alamar tana bin diddigin abubuwan da ki ke yi, ko kuma ana bibiya bata sani ba". Ta tashi tana zare ido ta ce "Sumayyan?"
"Wanda yake bibiyarki, shi ya turo miki wannan voice ɗin, ya baki tarihin bunkure, duk da bai baki complete ba. Yana bibiyar ki ko dan ya taimake ki, ko kuma yana da manufar da yake son cimma, dan haka ki kula"
Ta dafe ƙirji ta ce "Amma meyasa za a din ga bibiyata da sumayya? To wa ka ke tunanin yana bibiyata? Ka yi mini bayani sosai da sosai to me ma nayi za a bibiye ni?. Ya cigaba da tafiya bai bata amsa ba, tabi bayansa tana cigaba da magana.
Ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta, tsayawa tayi ita ma, tana kallonsa tana jiran taji mai zai ce?.
"Kin haɗu da Indabo?"
Shiru ta yi, sai kuma ta waro ido ta ja da baya, ta ce "Wai indabo ɗan siyasar nan, shi ne dai na cikin labarinka? Na ganshi a wurin aikin su sumayya, subhanallah shiyasa tun a ganin farko da nayi masa naji na tsane shi".
"Ya ganki?" "Eh, sai dai ban kula shi ba. Ai ni bai sanni ba, nima kuma ranar na fara ganinsa, sunansa kawai nake ji, amma menene?"
Ya girgiza kai ya ce "Shikenan" ya cigaba da tafiya.
Ta sake bin sa tana ɗan haɗawa da gudu, saboda saurinsa ya fi nata sosai, "To ka yi mini bayani, ni menene haɗina da shi to?"
"Babu, ki je ki mayar da hankali a kan wannan case ɗin, idan kin yi wining sai ki dawo, kar na sake ganinki a wurin nan"
Cikin rashin fahimta ta ce "To amma"
"Take your way, ki tafi na ce" yayi maganar yana nuna mata hanya, ƙyam ta tsaya tana kallonsa, mamaki ne ya cika shi, tsawar da yayi mata ko a jikinta, ta tsare shi da idanunta masu matuƙar haske, yanayin yadda take abubuwan ta, ya sake tabattar masa da akwai sangarta a tare da Nabila.
Ya juya ya tafi, ita kuma ta tsaya cak, tabi bayansa da kallo, tafiyarsa kawai gwanin burgewa, tafiya yake yi cike da ƙasaita, da bayyanar da ƙarfin da yake da shi, sai dai shi bai san yana hakan ba, har ya ƙulewa ganinta, sannan ta juya ta fara tafiya.
Sai yanzu take wasu lissafe-lissafe, tabbas sumayya ta canza, sun rage yin waya sosai yanzu, kuma ba ta kiranta da layinta sosai yanzu, kenan da gaske haɗa baki aka yi Sumayya a bibiyeta? To waye yake bibiyar ta ta? Farar motar nan ce ya faɗo mata a rai.
"To idan kuma an san ina zuwa nan fa, aka tona mini asiri, ina zuwa wurin mai laifi da ake nema ruwa a jallo. Wace amsar zan bayar na kare kaina?.
"Wai me ma ya aike ni tun farko? Ina zaman zamana" tana tafe a hanya, wani irin ciwon kai ya saukar mata, da kyar ta ƙarasa gida.
***
A kwance Abdul ya tarar da ramma, cikin damuwa ya ce "Rahama ya aka yi baki da lafiya, har na fita baki gaya mini ba?"
Ta yamutsa fuska ta ce "Na zata zan warke ne, ba sai na sha magani ba"
"Wannan ai ganganci ne, ko dai ciki ne?"
Da sauri ta ce "A'uzibillah, Allah ya yi mini tsari, ai kai ma ka san ba shi bane ba"
"Duk da haka, sai na gwada" first aid drower ɗin sa ya buɗe, yayi mata gwaje-gwaje, babu ciki sai malaria.
"Rahama, wurin nan babu sauro a ina ki ka samo malaria kuma?"
Ta kalleshi ta ce "A jikinka"
Yayi murmushi, ya haɗa allurai, zai saka mata cannula, ta hau kuka wai ba ta so.
"Rahama kina wahalar da ni, yanzu alluran baki zan yi ki shanye ko kuwa?"
"Ni hannunka da zafi gaskiya, ka samo wani yayi mini" ya harareta ya ce "Wani wa? Babu wani mahaluki da zai ganar mini jikinki a doron duniyar nan, ina kallon shi"
"Eh amma ai kai ka iya kallon na wasu"
"Duk cikin aiki ne, kuma ki yi mini shiru nayi aikina, ko na caccaka miki allurar har a baki"
Ya saka mata cannula, yayi mata allurai, ya saka mata ruwa, da duk ya ajiye su a gidan, saboda ramma.
Ya rungumeta a jikinsa, yana shafa saman cannulan, ɗaya hannun kuma yana matsa jikinta a hankali.
Ya zubawa hannunta ido, daga lokacin da ya ɗaukkota zuwa yanzu, ta canza sosai da sosai, fatarta tayi kyau, tayi haske. Ramma ba wani shahararren kyau ne da ita ba, amma yana jinta a kusa da zuciyar sa, duk da ba wani shiri suke yi ba, duk in da ya tafi tana ransa.
Bai taɓa raping ɗin mace ba, sai a kan ramma, hakazalika bai taɓa tarayya da virgin ba sai ita. Bai taɓa jin kunya da dana sanin wani rashin mutunci da ya yi ba, sai a kan abun da yayi musu, yanzu kuma uwa uba, ɓatan mahaifiyarta, bai san me zai ce mata ba, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya gano in da take.
Yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Sannu, kan ya daina ciwo?"
"A'a, amma Alhamdilillah ya rage"
"Masha Allah, ki bani labarin ƙauyenku mana, zan cika alƙawari, na yi magana da ɗan majalisar ku, lokacin da naje Abuja, zai shigar da ƙudurin hanyar ku, burtsatse ma da ki ka ce, ina jiran injiniyoyi su gama lissafi su turo mini, za ayi muku guda uku" ta tashi zaune ta kalleshi ta ce "Da gaske dan Allah?"
Ya jinjina mata kai yana murmushi, itama murmushin ta yi, ta ce "Yan garinmu za su ji daɗi, mun gode Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai, yan garinmu mun daɗe muna koken rashin hanyar nan, amma ba ayi mana ba, mun gode"
"Yau ba Allah ya isan?"
"Ai wancan abun da ka yi mini daban, wannan ma daban, amma Allah ya isa tana nan"
Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki yafe mini mana sweetheart "
Ramma ta ce "Ka mayar da ni wurin mahaifiyata, ka nemi afuwarta, amma haryanzu a zuciyata ban ji zan iya yafe maka ba, daga kai har anty maijidda, da wannan bayahudiyar matar"
Yayi shiru ya sunkuyar da kai, zuciyarsa babu daɗi, ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ce "Oho, ba zaka bani tausayi ba, ka tuba ga Allah ka gyara halayenka, dan ka samu kyakkyawar makoma. Ka cigaba hannun ya fara zafi" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da shafa mata hannun.
Ta saka ɗaya hannun ta juyo da fuskarsa, taga idanunsa sun yi ja, sun bayyanar da tsantsar damuwa.
"To meye kuma?" Ya girgiza kai alamar babu komai.
"Ka tabattar?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"Shikenan, to kayi haƙuri dai, ni gaskiyata na gaya maka, baka san zafin abun da ka yi mini bane, amma naga kamar ka ji haushi"
"Meyasa zan ji haushi, carbi zan sayo ki zauna ki yi ta jan Allah ya isan son ranki" ta murguɗa masa baki, ta kawar da kanta gefe.
***
Madaki ya zuba wa cinyarsa ido, yadda ciwon da Viper ya ji masa yayi wani irin mugun rami, maimakon ya yi ja ma, sai ya koma yayi kore, wasu irin jijiyoyi duk suka ɗaɗɗaga a gefen ciwon, ƙafar ta ƙara riƙewa, ba ya iya takata sai dai ya dinga jirgata.
Ya kalli babban amintaccen yaronsa ya ce "Lakwari, ciwon nan fa cigaba yake yi, kenan ta tabatta alkadarina ya karye?"
"Nima na gani maigida, kaga ana ta saka maganin, amma sai cigaba yake yi. Ba zamu yi saurin yanke hukunci ba, mu bi dare kawai, muyi makabeli mu ɓace mu yanka gabas, mu koma in da aka fara, ya duba mana, idan da wani abu da za a yi a kai, idan ba haka ba, mai zamani ya yi maka muguwar illa, kuma yana sane yayi hakan".
Madaki ya jinjina kai ya ce "Haka ne, babban abun da ya bani mamaki, bai wuce wanda suka zo suka ɗauke shi ba, ban san suwaye ba. Ta tabbata yana da waɗanda suke goge laifukan da yake aikatawa, yakamata na sanar da indabo"
Lakwari ya ce "Haka ne, amma mu fara neman mafita, a karya dafin nan da ya saka maka, kafin duk wata magana ta biyo baya".
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan".
***
Sumayya da murtala ne a zaune a gaban MD sun yi fiƙi-fiƙi da idanu, gefe ga lawisa a zaune.
"Abun da ku ke yi, da kai da sumayya ya fara yawa a wurin nan, ko dai ku bi tsarikanmu, da abun da muka ce dan cigaban tashar nan, ko kuma ku ajiye mana aikinmu. Duk jajircewarku akwai waɗanda suka fiku. Gashi kun saka hankalin mutane gaba ɗaya ya yo kanmu, saboda recording ɗin da ku ka saki a duniya da yake bayyanar da zargi ga Naja'atu Bunkure, wands duniya kowa ya shida mutuniyar kirki ce, mai yi wa mutane hidima".
Murtala ya ce "Tuba muke, muna neman afuwa in sha Allah ba zamu sake ba"
"Daga kai har ita, wannan ne karo na biyu da kuka aikata mana laifuka, muna ƙyaleku, na uku kora ce. Yanzu dole mu san yadda zamu yi mu gyara wannan shirmen da kuka yi" Murtala yayi ta bayar da haƙuri, sumayya kuwa fafur ta yi shiru, taƙi cewa komai.
Sun fito daga ofishin MD, tana hura hanci, ta tarar da Nabila.
Sumayya ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita, ta ce "Ke kuma daga ina? Kin je kin haɗa kai da Uncle murtala, mun saka recording ɗin da yayi miki, a kan shari'ar nan, yanzu aka gama sauke mana kwandon jaraba a ka.
Nabila ta ƙurawa sumayya ido, ta ce "Sumy why?"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Don't mind me, mota fa ta iso, na zo na sanar miki"
Ihun farinciki sumayya tayi ta ce "Are you serious, ko kuma jirgani ki ke yi?"
"Da gaske nake, amma Abba ya ce ba zan hau ba, sai driving licence ɗina ya zama ready, kin san shi da ƙa'ida"
Cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah, summa Alhamdilillah yawo ba kama ƙafar yaro, Allah ya saka wa Abba da alkhairi, uban marayu mai uban ma goyawa yake yi. Amma dan Allah arfat ki kula, ki san in da zaki din ga zuwa, banda rigima da faɗa da mutane a titi" ta din ga kallon sumayya, da son tabattar da abun da Viper ya gaya mata, yanzu sai ayi amfani da ita, a cutar da ita, sam ta kasa yarda gaba ɗaya.
Wada M karofi ne ya kira Nabila a waya, ta ɗaga ta ce "Hello sir"
"My beautiful angel, ya kike yau bamu gaisa ba gaba ɗaya, kin ƙi bari mu haɗu, gashi na koma wurin aiki"
Ta ɗan kashe murya ta ce "Ba haka bane ranka ya daɗe, ka san aikin namu ne babu zama, amma very soon zaka zo har gida mu gaisa" yayi murmushi ya ce "To shikenan, na san maybe kina wurin aiki, da daddare zamu yi waya in sha Allah"
"Ok Allah ya kaimu, ka kula da kanka sosai, kar ka yi aiki ka gaji da yawa"
Yayi dariya ya ce "Thank you my dear"
Sumayya ta ce "Ohh wa kuma ake yaudara, wa aka kwaso mana?" Nabila ta bata labarin wada M karofi.
Sumayya ta ce "Allah ya sa shi ne mijin, kakarmu ta yanke saƙa, kin san waye mutumin nan kuwa Arfa? Allah ya tsaga miki farinjinin manyan mutane, kar ki yi mana buƙulu dan Allah".
Nabila ta tashi ta ce "Taɓ gaskiya ba na son shi, ki zo gida kiga motarmu"
Sumayya ta ce "Dolena" Nabila tayi mata sallama ta fito, zuciyarta na cigaba da wasi-wasi a kan Sumayya, har ga Allah tana ƙaunar sumayya har cikin zuciyarta, ta kasa yadda da abun da Viper ya gaya mata.
Nabila na tafiya aka kira Sumayya a waya, ta ɗaga tayi shiru.
"Sumayya meyasa ki ke wasa da rayuwar ki, da ta ƙawar taki ne? Bayan ɗan waken zagaye da ki ke yi, Ki ke kiranta da wasu layukan daban, shi ne ki ka yi disconnecting ɗin bibiyar kiranki da ita da muke yi ko?"
"Ni kuma, ban gane nayi disconnecting ba? Wallahi ban yi disconnecting ba"
"Ƙarya ki ke yi, some hours back, aka yi disconnecting, zaki ga matakin da zamu ɗauka a kanki da ita, sannan zuwan da tayi me kuka tattauna?"
Sumayya ta dafe kanta ta zauna, sannan ta ce "Mota aka saya mata, sai labarin sabon saurayinta da tayi, Alhaji Wada M karofi, sai ƙorafin rashin nasara da take hangowa a kan shari'ar da suke yi".
P.A ya maimaita "Ki ka ce Alhaji wada M karofi?"
"Eh, shi"
"Ki cigaba da sanya ido a kanta, kina kawo mana rahoto, akasin haka zaki ga abun da ba kya so " ta kashe wayar ta dafe kanta.
***
"Indabo ya ga yarinyar nan"
Gaba ɗaya suka kalli Al'amin, liti ya ce "Shikenan, ai na san a rina"
Walid ya ce "Ya aka yi ka gane haka?"
"Mun yi magana da ita sosai yau, ana bibiyar ta, ana bibiyar kiranta da wata ƙawarta, na yi disconnecting duk wata hanya da za a cigaba da bibiyar kiranta. Amma rayuwarta na cikin hatsari, kuma idan ta cigaba da zuwa za a gane inda muke".
Liti ya ce "Shiyasa tuntuni na ce, a sallameta ta daina zuwar mana nan, amma walid ya nace".
"I think i will sealed a deal with her"
Suka haɗa baki suka ce "Kamar yaya?" Yayi shiru yana lissafa yatsun hannunsa.
Liti ya ce "Ka yarda da ita ne? Ni haryanzu tantama nake yi a kanta ne"
Walid ya jinjina kai ya ce "Lallai a tafawa mata" Viper bai sake ce musu komai ba daga haka, ya tashi ya fita.
***
M karofi yana zaune yana shan shayi, wani jami'in tsaro, ya shigo da Indabo cikin falon.
Karofi ya kalli Jami'in tsaron ya ce "Zaka iya tafiya" ya mayar da idonsa kan Indabo ya ce "Barka da zuwa sirikina, kwana da yawa, muna haɗuwa a Abuja, amma da ni da kai, babu wanda yake ziyarar wani. Duk ni yakamata ace ina kawo gaisuwa. Bisimillah zauna mana.
Indabo ya zauna, ya kalli M karofi ya ce "M karofi"
"Ma'aruf Indabo"
"Sabo da kaza fa, baya taɓa hana a yanka ta"
Karofi ya ce "Wannan haka yake, ko a siyasance, ko ma a normal life"
"Auren 'yar uwata maijidda da kake yi, ba zai hana idan kayi mini kan kara nayi maka na itace ba, hawainiyarka ta kiyayi ramata"
Yayi murmushi ya ce "Yakamata kayi mini fashin baƙi, akan wannan kurman baƙin da kake ta karanta mini"
Indabo ya yi wata ƙwafa ya ce "Soyayya da ka je ka fara da 'yar cikinka, saboda abun kunya, kuma yarinyar da take ta gwagwarmayar sai ta tona mana asiri, wadda ka tsayawa, wallahi muddin asirin Abdul ya tonu kaine ba wani ba, kuma sai nayi maganinka a siyasance da duniyance"
M karofi ya ce "Iko sai Allah, kana nufin Nabila wai? Taɓ ai ni ban taɓa sani ba, banda yanzu da kake gaya mini. Ina da lawyer a law firm ɗin su, shi naje gani, na ganta naji ina sonta, kai idan nayi niyyar tonawa ɗanka asiri, da wani zancen ake yi ba wannan ba.
Kuma ni ban yi abun kunya ba, sonta nake yi da aure. Tun da ƙanwarka ba yar gwal bace, da zata hanani zama da mata ba.
Naji daɗin wannan gargaɗi da kayi mini sosai da sosai, amma ka kwantar da hankalinka, babu ruwana da shari'arku, nima aikina nake yi. Zaka iya tafiya idan baka da abun cewa".
Indabo ya tashi, ya kalli idon kankarofi ya ce "Kifi yana ganinka mai jar koma"
Karofi ya ce "A juri zuwa rafi dai " Indabo ya fice yana baza babbar riga.
***
Nabila ta sake komawa gidan abokiyar aikin ramma, amma still bata same ta ba, aka sake gaya mata ta koma garinsu, sai dai samun sunan garin ma ya gagareta, ta kasa samu.
Tana kwance a kan gadonta, ta buɗe videos da hotunan da ta yi wa Viper, ta zuba masa ido, tana jin daɗin tsokanarsa da take yi, na cewa tana son shi, tana son zama kishiyar 'yar madara, mugun kallon da yake yi mata, ba ƙaramin dariya yake bata ba.
Mussaman da ta samu ya kulata, a haɗuwar su ta ƙarshe, duk da a ƙarshe, korarta yayi.
Tana kallon hotunan tana murmushi, ta ɗauki ƙaramar wayarta, ta saka lambarsa ta kira.
Sai da ta kira da ainihin lambarta, sannan ya ɗaga.
"Ohh Allah, kayi saving lambata ne?, Ina ta kiranka da ɗaya layin amma baka ɗaga ba. Ina ta kallon hotunanka, ina son in yi bacci .
Ka san ranar da nayi maka hotunan nan, har murmushi fa kayi, ka din ga fara'a murmushi yana yi maka kyau sosai dear. Yaushe zaka ƙarasa bani labarinka ne? Yakamata ka gabatarwa jauhar ni, a matsayin amarya, zan yi mata biyayya sosai da sosai, in tayata sonka. Ba zan yi kishi da ita ba, ina sonta sosai da sosai, dan Allah ko sau ɗaya ka haɗani da ita mana" kamar da iska take, haka yayi shiru ya ƙi magana.
Ba ta gaji ba, ta sake cewa "Ina ƙaunar yar madara saboda Allah, dan Allah ka ƙarasa mini labarin ta".
"Meyasa ki ka shigo rayuwata?"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin dogo ne, ba zan ɓoye maka ba, da dai ina taya Yayana nemanka ne, saboda nayi suna, na rama abun da Bunkure ta yi mini, na wulaƙanta ni a gaban jama'a. Shi ne na din ga up and down, har na haɗu da wannan litin, mara kirki".
"Saboda ki yi suna ki ke son taimakona?"
Nabila ta ce "Eh, a da ba, amma jin labarinka gaba ɗaya ya canza mini tunani, nake jin zan iya yin komai, dan na ga na ƙwato maka hakkinka, da kai da yar madara, duk da ban san ƙarashen labarin ba. Amma gwiwata ta fara sanyi, na fuskanci Naja'atu Bunkure nan, tana da goyon baya daga sama, kuma indabo babban mutum ne shahararre sosai, ina buƙatar support sosai, kai kuma sai korata kake yi kana hantarata".
"Idan na ƙarasa miki labarin, that means duk tsanani babu gudu babu ja da baya, zaki tsaya a shari'ata komai wahala da sarƙaƙiyarta?"
"In sha Allah, i promise it"
Ya sake cewa "Kin tabattar zuciyarki zata iya ɗauka komai muni, komai daɗin abun da zaki ji?"
Cikin ƙwarin gwiwa ta sake cewa "Eh zan iya"
Viper ya ce "Take your time to think, ki yi comparing da ƙalubalen da ka iya biyo bayan hakan"
Ta lumshe idonta, hatta muryarsa, mai daɗi ce, duk a buɗe take saboda bayan naturally yadda take, wiwi da shaye-shaye sun ƙara making ɗin ta deep.
Ba ta bashi amsa ba, ya kashe wayar.
Walid ya ce "Mai zamani, ka yadda da maganarta kenan? Zaka ɗauki fansa ta hanyar shari'a"
Mai zamani ya girgiza kai ya ce "Ta riga ta shiga tarkonsu, kuma na fuskanci ba ta ji ko kaɗan, zata iya salwantar da rayuwarta". Walid ya yi murmushi mai cike da jin daɗi ya ce "To ɗaya maganar fa? Zaka gaya mata?"
Al'amin ya kalli walid, yayi shiru bai ce komai ba.
***
Jikin ramma da sauƙi sosai, tana zaune a gefen gado, Abdul yana bata abinci, gefe ga magungunan ta. Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya saka a hansfree ya ajiye ya ce " 'yar mutanen bunkure, ya ake ciki ne?"
"Abdul"
"Na'am"
"Ya ka yi da yarinyar nan ne da ka yi wa fyaɗe? Wata yarinya ta tsaya kai da fata, sai ta wanke dattijon nan, mun yi duk abun da yakamata, ta koma tana amfani da social media against me, hankali na ƙoƙarin dawowa kaina, sai sintiri take yi wai lallai sai an kai yarinyar gaban shari'a, ga wani voice message da yake yawo na uwar yarinyar...... Abdul ya cire wayar daga hansfree, ya saka a kunnensa, yana kallon ramma.
"Ka gaya mini yaya ka yi da ita? Tana raye ko ta mutu? Mu san abun da zamu shirya a kan shari'ar, an je gidansu babarta bata nan an nemeta an rasa"
"Kina ji? Zan zo in anjima yanzu ina wani uzurin ne" ya kashe wayar, ya kalli Ramma zai yi magana, amma ya kasa saboda mugun kallon da tayi masa.
"Rahama ki tsaya ki saurare ni ki ji"
"Kayi mini shiru tun ba shaƙeka ka mutu na huta ba, azzalumin banza da na wofi, in sha Allah sai Allah ya tarwatsa ka da kak kai da duk masu goya maka baya kuna cutar mutane"
Fafur ta ƙi saurarsa, tayi watsi da kayan karin kumallon, ta tashi ta bar masa ɗakin.
***
Nabila ta daina shiga harkar Nasir, dan sosai ya sakata a gaba, da masifar lallai sai ta daina case ɗin bunkure, saboda lafiyar ta da rayuwarta, ita kuma ta ce babu wanda ya isa.
Sumayya ce ta kirata da wata lamba, ta ɗaga ta ce "Waye?".
"Ke ni ce"
Nabila ta ce "Yar 419, yau kuma da lambar wa ki ka kirani, ko aiki ki ke yi a kaina ne?"
"Nabila, bar wannan maganar kin san menene?"
"No"
"Maganarki da muka saka a radio, a kan bunkure, wata mata ta zo mini, ta ce lallai ke take son gani, akwai information da zata baki a kan bunkure, ta ce macuciya ce, abun babu daɗin ji, bama itakaɗai ba, akwai gwarama, mutane sun fara magantuwa fa"
Nabila ta ce "Abubuwa sun fara yi wa kaina yawa, zan zo har gida na same ki"
Ta ajiye wayar ta dafe kai tana tura baki. Duk da tayi farinciki da haka, dan kuwa gagarumin cigaba ne, amma gaba ɗaya ba ta yadda da sumayya ba yanzu, dole tana buƙatar ganin Viper kafin tayi wani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 59 Chapter of 121