zan taɓa yadda da hakan ba, labarin Viper da na ji, bai taɓa kisan kai ba, wa ka kashe?"
Tashi yayi, ya ɗauki wuƙarsa yayi gaba, kamar mayya ta tashi ta bishi cikin sauri, amma saurinsa ya ninka nata, dan haka ya rigata isa cikin gidan, kafin ta ƙarasa har ya shiga ɗaki ya rufe kansa.
Ta taga ta tsaya tana leƙawa "Dan Allah ka daina bani bayani guntu-guntu ka ƙarasa mini, hakan zai taimaka mini wurin sanin ina zan kama, wa ka kashe dan Allah?"
Ya tsaya ƙyam ya juya mata baya, ya dafa jikin bango, zuciyarsa tamkar ruwa na tafasa a ƙasan gagarumar wuta, haka wani Irin zafi ya din ga taso masa daga ƙirjinsa zuwa ƙwaƙwalwarsa.
Nabila ta din ga bubbuga ƙofar, tana yi masa magiya ya buɗe, amma yaƙi, ta koma ta window, ta ga tuni ya fara ɗurawa kansa allura.
"Dan girman Allah ka bari, lafiyarka da ta ƙwaƙwalwarka, wannan ba mafita ba ce ba, dan Allah kar ka illata kanka".
Liti ya ce "Zo ki fita, koma uban menene ba ke ce sila ba, uban waye ya ce ki zo, yau ya tashi da 'yar walwala kawai kin zo kin kuma tunzura shi".
Cike da tsananin damuwa, da tashin hankali ta baro gidan, tana tunanin to ita menene laifinta, da suke cewa ita ce sila idan ya ganta yake burkicewa.
***
Ramma ta zubawa Abdul ido, ya haɗa akwatin sa tsaf, ya kalleta ya ce "Ƙarfe huɗu jirgina zai tashi, dole na shirya da wuri, akwai in da nake son zuwa kafin na tafi"
Ta turɓune fuska, tayi masa shiru.
Ya zauna kusa da ita, ya ɗago haɓarta yana kallon fuskarta ya ce "Ya dai?"
"Ni dai kar ka tafi dan Allah, tsoro nake ji wallahi, nikaɗai zan zauna a nan dan Allah"
Ya kwantar da murya ya ce "You start missing me?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Your excellency, ba iya tsoro ne a idonki ba, missing ɗina zaki yi"
Ta ture hannunsa ta ce "Allah ya kiyaye, ni gaskiya tsoro nake ji"
Abdul ya ce "Tafiyar nan dole ce, sannan ina son na je garinku yau, zan ce wa mamanki kina gaisheta"
Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka mayar da ni mana"
Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba"
"Nan gaba zaka mayar da ni?"
"Eh to, sai ƙura ta lafa" tayi shiru tana wasa da yatsunta.
"Ki yi haƙuri, zan dinga kiranki kullum muna magana, idan da wani abun ma sai ki gaya mini, na ajiye miki komai na amfani a kitchen, ai kin iya girki ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
Ya ce "Yauwwa your excellency" ya tashi ya shiga wanka, yana ta shiri, ya zauna a gefen gado yana shafa mai, ta riƙe shirt ɗin sa tana kuka.
Nan ya lalace a wurin rarrashin ramma, "Wai wannan kukan duk dan kar na tafi ne?"
"Ni ina ruwana da tafiyarka, tsoro nake ji ne"
"Ƙarya ki ke yi rahama, faɗi gaskiya dai"
"Ni ba na ƙarya" tayi maganar tana murguɗa masa baki sannan ta ce "Kuma wallahi ka bi mata Allah ya isa" bai san lokacin da ya ƙyaƙyace da dariya ba, har sai da ya bata haushi.
Har ƙofar falon ta rako shi, tana kallonsa, ya kasa gane kallon me take yi masa har haka, yayi mata sallama, ya sanya mukulli ya kulleta, ya ja akwatinsa.
***
Kan Nabila tamkar zai yi bindiga, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, haka ta koma jiki babu daɗi, kanta fal tunani daban daban.
Har ta shirya, zata ci abinci, kawai ta tuna kwana biyu ba ta haɗu da Nasir ba, kuma ba ya shiga sabgarta, gashi tana son sanin a ina ya tsaya a binciken Viper, saboda duk yadda za ayi ba ta son ya gano Viper ba ta gama na ta binciken ba, idan ya so ko kotu za a shiga, ta shiga da ƙwarin gwiwar ta.
Gaba ɗaya mayar da hankali a kan aikinta ya sanya, ba ta shiga sabgar yan gidan, hakan ya rage yawan faɗace-faɗace da suke yi da 'yan gidan.
Ta fito falo, dan ta gaji da zaman ɗaki, abubuwa duk sun dameta, sai ga Nasir yayi sallama a falo, ta amsa sallamar tana kallon sa, amma ya basar da ita ya nemi wuri ya zauna.
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce "Sannu da zuwa"
"Yauwwa" ya amsa mata a ciki.
"Wai me na yi maka ne ka ke wani share ni?" Tayi maganar a shagwaɓe.
Rasa me zai ce mata yayi, yai shiru, ya kawar da kansa gefe.
Ta zagaya in da ya kawar da kan ta ce "Me na yi ne?"
"Bakomai". "To ka kula ni mana".
Nasir ya ce "Na gaji, kar ki dame ni dan Allah"
"Sai na gaya wa Abba kana hantarata"
Ya ce "Sai kin dawo" ta rausayar da kai ta ce "To ni dai ka yi haƙuri, dan Allah" ya kalleta ya ce "Ya wuce"
"Yauwwa DSP, to ya ake ciki ya aikin?" Ya gyara zamansa ya ce "Alhamdilillah, mu na ta fama ya naki?"
Ta kwaɓe baki ta ce "Babu daɗi, duk na gaji, da fa ajiye aikin zan yi, aka bani haƙuri" Nan ta bashi labarin abun da barrister Kabir yayi mata.
Nasir ya ce "Ke baki da haƙuri ne, shiyasa wasu lokutan ba kya cin ribar abubuwa, ki daina gaggawa"
"Ai abun ne ya bani mamaki, daga zuwana wurinta, har an kira barrister Kabir an gaya masa, baka ga abun da ya yi mini ba, da cewa na yi sai na gaya wa Abba ma".
Nasir ya ce "No, ba za ayi haka ba, duk abun alkhairin da yake yi miki, sai a kan laifi ɗaya ki yi fushi"
"To meyasa zai yi mini tijara a kan wata Naja".
Ya ce "Hakan yana alamta miki cewa, kin ɗaukko gagarumin abin da sai kin yi kyakywan shiri na gaske".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, ya ake ciki da naka aikin, yaya batun case ɗin Viper, akwai cigaba kuwa?"
"Wallahi ba wani cigaban kirki, ina da ta fafutuka, gashi sai hura mini wuta ake yi"
"Kai abun babu daɗi, but you can do it, na yarda da kai ai".
Mama ce ta fito fuska a haɗe ta ce "Nasir menene haka?"
Ya ce "Mama a ina?"
"Ban sani ba, uban me ka ke zaune a nan ka ke yi? Ka dawo gida tun ɗazu, amma ka gagara shiga inda nake?"
Nasir ya ce "Wallahi nayi tunanin bacci ki ke yi, shiyasa na yada zango a nan muke magana da Arfa, yi haƙuri"
Nabila ko a jikinta, ta sake gyara zamanta ta kwanta sosai a kan kujerar tana danna waya.
Mama tayi mata wani mugun kallo, ko a jikinta, sai ma wani irin murmushi da tayi.
Messages aka din ga turowa Viper, da private numbrn nan, da ake kiransa da ita.
"Muddin ka cigaba da biyewa yarinyar nan, asirinka zai tonu, kuma zata iya rasa rayuwarta a dalilinka, ba ka da sa'a wasu lokutan, kar ka bari ta zama raunin da maƙiyanka za su yi amfani da ita, wurin cimmaka har maɓoyarka" Ya din ga jujjuya wayar, yana sake tunanin waye wannan, kowaye ya sanshi, ya kuma san in da yake, kuma yana ankare da duk abun da yake yi, amma meyasa yaƙi bayyana kansa?.
Kiran Nabila ne ya shigo wayarsa,
tana zaune hannunta riƙe da waya a kunnenta tana kiran lambarsa, babu tsammani ta ji ya ɗaga.
Ta kalli agogon ɗakinta, ƙarfe goma daidai na dare.
"Barka da dare, duk da ba amsawa zaka yi wa ba. Amma ina fatan kana lafiya?
Na kasa jurewa ba zan ɓoye maka ba, ban ji daɗin yadda na baro ka ba, muna cikin magana ka tashi ka tafi, kuma ka je ka na yi wa kanka allura, gaba ɗaya ban ji daɗi ba, dan girman Allah ka rufa mini asiri kar ka yi wa kanka illa, ka bari mu yi nasara mu kamo bakin zaren. Na san maybe ka raina gogewa ta, kuma kamar ba zan iya ƙwato maka hakkinka ba, amma na san Allah yana tare da mu, dan Allah ka daina shan abun da zai yi maka illa, ba na jin daɗi, na san yayata ma 'yar madara ba zata ji daɗin hakan ba, dan gaskiya sai ta matsa mini na shigo, daga ni sai a rufe. Saboda son da nake yi mata make son mu kasance tare, idan na shiga gidanta, kaga gani ga ta, in ƙara koyon halayenta, in ƙara sonta, amma gaskiya ayi mana adalci, saboda kishi ne da ni sosai da sosai fa, kuma alamu sun nuna mini kana sonta da yawa"
Kamar mai sauraren karatu, haka ya nutsu yana jin ta, ɗan mama da yake kusa da shi, har kuma leƙa idonsa yake yi, ya ga reaction ɗin da zai yi, tare da jinjina rawar kan Nabila, a gaban Viper ko ƙwaƙwaran motsi ba ta iya yi, amma ta sameshi a waya, sai karairaya take yi tana shagwaɓa.
Ta sauke numfashi ta ce "Bari na ƙyaleka, amma yakamata na san ƙarshen labarin nan, saboda na san yanayin shirin da zan yi, kuma kar sai na gama zaƙewa 'yar madara duk kirkinta ta ce ba zan shigo mata gida ba, dan ni gaskiya idan ba gidanta ba sai rijiya. Sai da safe take care" tayi maganar tana ajiye wayar, cikinta na kaɗawa saboda ita kanta ta san ba ƙaramar kasada take yi ba, abun da take yi. Amma hanyar da matarsa ta bi ta iya samun kansa da farko, dole ita ma ta bi, domin cimma nasara, saboda gaba ɗayansa hukuma ne, sai da rarrashi.
***
Sanye yake da face mask, yana tuƙi a hankali, saboda yadda hanyar ta ƙara lalacewa, a ƙofar gidan su ramma yayi parking, ya fito ya tsaya a waje yayi sallama, amma shiru, ya shiga cikin gidan sai dai tsakar gidan babu kowa, ƙofofin ɗakin duk a buɗe.
Ya ɗan jira ko za a shigo, ko fita tayi, amma shiru, ba ta dawo ba.
Ya fita ya tambayi maƙwabta, suka sanar masa kwanaki huɗu kenan, su ma ba su san in da ta tafi ba, ba ta yi wa kowa sallama ba.
Yanayin gidan ya tabattar masa da ba fitar nutsuwa tayi ba, ya lissafa shi yanzu kwanaki uku kenan, da mahaifinsa ya kira shi yai masa magana a kan batun ramma balle ya ce ko mahaifinsa ne.
Yayi shiru yana tunanin to garin yaya haka, ya za ayi ta fita ta bar gida a buɗe haka babu kowa, tsawon kwanaki huɗu, ba ta yi wa kowa sallama ba, lallai akwai wani abu a ƙasa, yanzu me zai cewa ramma? Ya tambayi kansa.
Lallai akwai wani abu a ƙasa, gashi lokaci na nema ya ƙure masa, ƙarfe huɗu zai tafi.
Saif ya kira a waya, ya sanar masa halin da ake ciki, saif ya ce "Kuma baka tunanin ko guduwa tayi, ko kuma daddy ne yayi mata wani abun?"
Abdul ya ce "Bana tunanin haka, shekaranjiya yayi mini zancenta, da shi ya saka aka ɗauke ta zai gaya mini, na rasa wani lissafin ma yakamata na yi"
Saifu ya ce "Ka tafi kawai, zan tsaya na sake bincikawa, in Allah ya yadda ba wani abu".
Ya ce "To shikenan, ina saurarenka dan Allah" ya ajiye wayar yana cigaba da tunanin lamarin.
***
Abdul yana sauka a Abuja, sai da ya kira Ramma, ya ce mata ya sauka, sai dai ba ta amsa masa ba sai cewa tayi "Yaya ka baro mini mama? Tana nan lafiya? Ta tambaye ka yaya nake?"
"Ni ba zaki tambayi ya na sauka ba, sai mama kawai?"
"Dan Allah ka gaya mini, ko na ji daɗi"
Abdul ya ce "Zan gaya miki da daddare idan na huta" ya katse wayar yana fargabar ranar da ramma ta san halin da ake ciki, bai san ya zai yi ba. Ya san duk laifin shi zata ɗorawa.
***
Katafaren falo ne, ya sha ado da kayan alatu na zamani, manyan mutane ne su uku, zaune a falon wanda kaf ɗin su sanannun fuskoki ne da su a ƙasa.
Kayan shaye-shaye ne a gaban su, suna sha suna hira, gefe ga kayan marmari.
"Distinguish ma'aruf Indabo, ya ake ciki ne gaba ɗaya baka walwala?"
"Komai ma ya dame ni ne, Abdul sai so yake yi sai ya watsa mini lissafi, da ƙyar na yaƙo shi, ya tafi Abuja, zaman taron nan, nima gobe in Allah ya kaimu zan tafi birnin tarayyar"
"Ya salam, wai meyasa Abdul yake haka ne? Ya san wahalar da muka yi kuwa kafin mu zo nan, shi me yake damunsa ne?"
Indabo ya kora ruwan lemon da yake cikin kofin hannunsa, ya ce "Oho masa, gaba ɗaya na kasa gane kansa, ina tsoron Allah ina tsoron ya aikata wani abun da zai yi dalilin takarar nan, amma ina nan na kafa na tsre ina monitoring activities ɗin sa".
"Ohh Allah ya kyauta, ya batun wannan yaron ne da ake nema?"
Indabo ya girgiza kai ya ce "Hmm honorable kenan, wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, kamar wani iblishi, ya gagara kamuwa, na rasa uban da yake tsaya masa, sai dai na samo wata yarinya da nake son ayi masa tarko da ita, to ita kanta yarinyar ba ta da cikakken saiti, wata barrister ce, 'yar wani tsohon soja, idan na matsa zata iya tona mana asiri, na saka ana yi mini monitoring ɗin ta, ta hanyar ƙawarta. Saboda wani furuci da tayi. Duk dai na ga hanyoyin ba sa yi mini sauri, na san dole yaron nan bakam yayi mini, at any cost sai na canza dabara, wadda za ta ɓulle mini da wuri, na kashe Aminu na huta"
Haka suka cigaba da jimantawa, tare da tattaunawa da neman mafita, suna yi suna shaye-shaye.
Ramma tana duƙunƙune a cikin bargo, karnukan estate ɗin, da na gidan sai haushi suke yi.
Video call suke yi da Abdul, ta ce "Ba ka ce mini komai a kan mama ba"
"Mama tana lafiya, ta ce a gaishe ki"
Ta ce "Hmm, to ya take, tana cikin damuwa ko? Tayi kuka?"
Ya ce "A'a, na bata tabbacin kina nan lafiya, har hotonki na nuna mata"
Ramma ta ce "A'a hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba, ka manta rashin ɗa'ar da ka yi mata, ranar da ka je ka tabattar mata da kai ka keta mini haddi, kuma ka tafi da ni, ai a yanzu idan akwai wanda ta tsana bai wuce ka ba, kodayeke akwai wanda suka yi mata wasu laifuffukan"
Yayi shiru jiki a sanyaye ya ce "Laifin da suka yi mata irin nawa ne? Ai na nemi afuwarta"
"Ta ina ka nemi afuwarta? Hmm ta ce ta yafe maka ne? Kai baka ganin girman laifin da ka aikata fa saboda mu talakawa ne kana da kuɗi.
Mama ta sha wahala sosai, gashi duk mun ɗaiɗaice, kaga ƙanina sani daka je?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Ina ga yana makaranta"
"Shikenan, sai da safe, bari na rintse idona ko zan yi bacci, haushin karnukan nan ya isheni"
Ya ce "Ni kuma sanyi ne nan ya dame ni, da muna tare da kin bani ɗumin jikinki"
Cikin tsiwa ta ce "Saboda gani heater ko?"
Ya ce "No, jikinki akwai ɗumi sosai, da duk ba zan ji wannan sanyin ba"
"Sai da safe"
"Dan Allah ki tsaya ban gama ganinki ba"
ta ce "Sai kuma ka yi ai"
"Miƙo bakinki na yi miki kiss"
"Ba na so" tayi maganar bacci yana kwasarta, tana lumshe ido.
Ya ce "Rahama"
"Na'am" ta amsa tana buɗe ido da kyar. Sai kuma yayi shiru yana cigaba da kallon fuskarta, har bacci ya kwasheta, yana kallonta, tausayinta ya din ga ratsa zuciyarsa.
***
Yau weekends, Nabila tana gida, tana kai komonta, ta bayar da wankinta ayi mata, ta fito harabar gidan tana zagawa, Nasir ya fito da shirin fita.
"DSP sai ina? Ko zance za a tafi rana tsaka"
"Wurinki zan zo zancen" tayi dariya ta ƙarasa gabansa ta ce "Ina zuwa yanzu?, La'asar ta kusa?"
Ya kalli agogon hannunsa ya ce "A kan Viper ne"
Cikinta yayi ƙuuu, amma ta maze ta ce "Ya ake ciki?"
Ya ce "Eh to, na canza dabara ne, a yanayin neman nasa, mun riga duk mun yi connecting da mutanen unguwar su, an ce yana zuwa gidansa da ya zauna, to kwana biyu bai je ba. Abokin faɗansa da na kama kwanaki madaki, an ce ya dawo yana cikin gari, akwai ƙishin-ƙishin na zai iya zuwa unguwar, neman rigima da shi madakin, duk mun baza komar mu, akwai wurin shayin yaransa, an ce ma wurin nasa ne, zuwana biyu wurin cikin fararen kaya, an kwatanta mini wani yaronsa Walid, na haɗu da shi a wurin, amma ko kaɗan ba sa zancensa a wurin. Da na so na zunguro zancen daba ma, na kama sunansa, cewa suka yi na tashi na fita. Ina kyautata zaton wannan Walid ɗin ya san in da yake, motsinsa zan sakawa ido sosai, ana ta yi mini binciken ina yake da zama, da a unguwar suke zaune, amma tun da Viper ya bar prison, sun daina kwana a unguwar sai idan za su yi aikin rabawa ƙanan dealolinsu wiwi. Ba zan motsa da wuri na kama shi Walid ɗin ba ba, kar shi ma ya zille mini, kuma an tabattar mini da ɗan amanrsa ne, ina dai ta bibiyar su ta hanyar mai unguwa, da wasu daga mutanen unguwa. Wanda nake baki labarin nan ma ɗan mama, ya daina zuwa arear da aka gaya mini kai kayan shaye-shayen na su, abun ne dai duk sai a hankali".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani aiki sai mai shi, Allah dai ya ba da sa'a, sannu da ƙoƙari DSP"
"Yauwwa arfan Abba, bari na tafi"
"To yanzu can ɗin zaka tafi?"
"Eh, zan je in sake zaɓar yarana su shiga unguwar su madakin a farin kaya"
Ta ce "Shikenan, a sauka lafiya, Allah ya tsare" ya amsa da Amin, ya nufi motarsa.
Cikin sassarfa, ta nufi ɗakinta, Wayar Viper taƙi shiga, ta din ga kira amma a kashe.
Hankalinta ya ƙara mummunan tashi, har la'asar wayar viper ba ta shiga.
Shiryawa tayi ta saka niƙab, ta lallaɓa ta fice, ba tare da yi wa kowa sallama ba.
Sauri take yi tamkar za ta tashi sama haka take fafaka sauri.
A hanya aka fara kiraye-kirayen sallar la'asar, har ta ƙarasa kiran lambarsa take yi, amma shiru bai ɗaga ba.
Ɗan mama ta tarar a tsakar gida, shikaɗai, yana ta shafawa wuƙaƙe wani abu, da ba ta san ko mene ne b. Ya miƙe yana kallonta ya ce "Dan Allah suna ina?"
"Su wa?"
"Su viper, da sauran".
Ɗan mama ya ce "Oga Viper ya fita, ya tafi cikin gari wurin madaki, da shi da Oga liti, Oga walid sun yi faɗa ya fita"
Jikinta na rawa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi Walid ɗin ina ya tafi? Wai ma meyasa Vipern ne yake da taurin kan tsiya, akwai hatsari a hakan fa "
"Ke, Oga Vipern ki ke faɗar baƙar magana a kan shi?"
Ta juya zata fita ya ce "Ina zaki?"
"Bin sa zan yi"
Ya waro ido ya ce "Ina?"
Ta tsaya ta kalleshi ta ce "Dabar madakin, ai na san wurin" zai yi magana, ta fita da sauri sosai.
Shida saura na yamma, ta isa unguwar su madaki, saboda azalzalar da ta din ga yi wa mai adaidaita sahun da ta hau.
Ta cikin niƙabinta, take kallon unguwar, ba zata taɓa manta, yadda aka sakar mata karnuka ba, suka kusa cinyeta.
Ta nufi cikin unguwar, sai dai kamar babu mutane, sai ɗaiɗaikun mutane da suke guje-guje.
Ta tsaya tana neman wand zata tambaya meyake faruwa, amma kusan kowa ta kansa yake yi.
"Kai ku tafi gida, wannan ɗan tijarar ne ya shigo neman masifa, mai zamani ne da yaransa, suke faɗa da yaran madaki" taji muryar wani matashi, yana yi wa wasu yara magana" maimakon ta tsorata sai ta kutsa kai ta cigaba da tafiya tana fatan Ubangiji Allah ya sa kar wani abu ya same shi, Allah ya sa ta ganshi.
Tana saka kai wani layi, ta ga an yanki wani a cinyarsa, jini ya yi tsartuwa, ta gigice cikin tashin hankali ta fara ihu, ji tayi an ja hannunta da ƙarfi, an shiga da ita wani layi daban.
Ayshercool
0808012143
54
Cikin matsanancin tsoro, ta rintse idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri sosai.
Da kyar ta iya buɗe ido ta ga wanda ya ja ta, kallo ɗaya ta yi wa idanunsa ta cire nata, saboda mugun kallon da yake yi mata.
"Uban me ya kawo ki nan?" Mamaki take yi, yaya aka yi ya ganeta da niƙab.
"Ba magana nake yi miki ba?"
Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai? Meyasa zaka fito, kana da tabbacin idan suka kamaka a wannan karon zasu barka da rai ne, ba fa za su yadda su sake wannan kuskuren ba, dan Allah kar ka ɓata mini aiki, dan Allah ka daina fitowa" mayafin da ya rufe fuskarsa da shi, ya sake gyarawa, ya sake damƙar hannunta, ya din ga ratsa hanya da ita, kowa ya gudu gida ya ɓuya.
A haka suka ƙaraso titi ya ɗaga wa wani mai baburin adaidaita sahu hannu, ya yi mata nuni ta shiga, shi ma ya shiga.
Ta kalli yadda duhun magariba yayi, sai a lokacin hankalinta ya kai kan me za ta ce a gida.
Ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya saka a kunnensa, a hankali yake magana ba ta iya jin me yake cewa a wayar, ya zirawa mai napep ɗin dubu ɗaya ya kama ƙarfen adaidaita sahun, ya dire ba tare da mai napep ɗin ya tsaya ba.
Cikin sauri ta leƙa, ta ga wani ya tsaya a babur sanye da face mask, Viper ya hau suka yi wani wurin.
Tana jin yadda wayarta take ta ringing, amma taƙi ko ɗaukkota, balle ta ga waye.
Ta gaya wa mai napep in da zai kaita, tuni aka fara kiraye-kirayen sallar isha'ai, motar Abba ta tarar da ta Nasir, alamar duk suna gida, gabanta ya faɗi.
Sannu a hankali ta ƙarasa falon, ta tarar da Abba a tsaye, hannunsa riƙe da waya, take wayarta ta hau vibrating alamar ita yake kira a waya.
Yayi mta wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa.
"Daga ina ki ke?"
Tayi tsuru-tsuru da ido, tana kallonsa.
Nasir ya ce "Magana fa ake yi miki"
"Amm, Abba dama wallahi wata shaida nake so na haɗu da ita, wani case ne a hannuna shiyasa na fita".
Abba ya ce "Wa ki ka gaya wa zaki fita?"
Mama ta ce "Yaushe za ta gaya mana, tun da bamu isa ba"
"Wato arfa kullum rashin jinki ƙara gaba yake yi ko? Idan baki yi wasa ba, hatta aikin sai na hana ki zuwa, an ce tun safe ba kya gidan nan, wace irin shaida ce haka?"
Nasir ya ce "A'a har azahar tana nan ina ga da la'asar ta fita"
"Koma menene yanzu yakamata ta shigo gida, ƙarfe takwas da wani abu tun la'asar?"
Ta sunkuyar da kai ta ce "Dan Allah Abba ka yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake ba"
"Daga yau, ki ka sake fita babu wanda ya sani, zamu gauraya da ke" ta jinjina masa kai, ta wuce tana yi wa Allah godiya, da bai yi mata faɗa sosai ba.
Addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar Viper ya aikata wani abu da za a kama shi, ko kuma ya yi wa kansa illa.
Gashi ba ta samu sun yi magana a kan abun da ya kaita ba, na shirin da Nasir yake yi na son kama shi ta hanyar Walid ba.
Madaki ne a tsaye yana kallon Al'amin da yake tsaye a gabansa, duk da duhun dare ne, amma manyan fitilun solar sun haske ko ina da ina.
Idon Al'amin kamar ana hura wuta, Madaki yayi dariya ya ce "Mahadi mai dogon zamani, ka ci na wasu gaka kana cin naka. Viper ka ke maciji mai hatsarin gaske, dodon cinnaku masu ƙaryar kaki.
Barka da sake haɗuwa da kai a dai-dai wannan lokaci, bayan dogon lokaci bamu yi ido da ido.
Tabbas labarin Mai zamani ba zai taɓa cika ba, sai an ambaci madaki.
Maza gumbar dutse ya ake ciki ne?"
Yana rufe bakinsa, Al'amin ya soka masa russia a cinyarsa, a take jini ya fara kwarara a jikin madaki. Madaki ya kalli cinyarsa, ya kalli Al'amin.
Al'amin ya kalli madaki ya ce "Na san zaka yi mamakin, yaushe na samu makarin tsafinka, amma na ƙyaleka a raye kana cin karenka babu babbaka.
Yadda daba ta bar mini mugun tabo a zuciyata, ka rubuta ka ajiye, kamar yadda ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaci sunanka. Ina mai tabbatar maka Viper zai yi maka saran da bai taɓa yi wa wani irinsa ba.
Kamar yadda ka canje ni, ka ke yi wa Indabo aiki, a madadina, ina da saƙon da zan baka ka bashi. Ka gaya masa ya toshe dukkanin ramukan da ke gidansa, ofishin sa da duk wani wuri da yake
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 56 Chapter of 121