gaya mini ina zaka je ba, gaba ɗaya tun da aka sha ruwa na kasa cin komai, ban san ina ka ke ba".
"To kukan zaki yi?"
"Baka gaya mini ina zaka je ba, hankalina gaba ɗaya ya ƙi kwanciya haba master dan Allah"
"Ohh murya kamar tsuntsuwa, yenyenyen, ki din ga buɗe baki ki yi magana sosai" kawai tayi shiru cike da takaici, idonta kawai ya kalla, ya san hankalinta a tashe yake.
Ƙeyata ya tura, zuwa ɗakinsa kawai ta tarar da jeren kwanuka, haɗaɗɗun fulasai, da uban kayan marmari.
Tayi saroro tana kallon kayan.
"Zo ki zuba mana mu ci, ba kayan wani bane, mun je campaign ne muka dawo aka shirya shan ruwa, na ce a gida zan ci na taho da shi".
A ɗan tsorace ta ce "Master duk wannan kuma?"
"Eh kwaso kwanuka"
Iya kajin sai da suka tsorata ta, dan sun kusa goma, fulasai ne na alfarmar gaske.
Ta ce "Ai ba zamu iya cinyewa ba".
"Gasu nan dai, ki yi abun da ya dace".
Duk son Jauhar da nama, sai da ya isheta, ta bawa maƙwabta, ta zuba wani ya kira guduma a waya, ya ce masa ya zo ya karɓa.
Hatta magenta, sai da ya ƙoshi da ciye-ciye.
Haka kurum ya din ga jin annashuwa a ransa, ganin ta ci ta ƙoshi, har abun ya gundureta.
Bayan jera masa godiya da ta gama yi, kamar yadda ta saba, tare da addu'oi, ta ce "Master Alfarma zan nema a wurinka dan Allah"
"Ina jinki"
Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ce "Dan Allah kar ka ce mini a'a, ko ba zaka yi ba".
"To kar ki tambayi abun da ba zan iya ba".
"Zaka iya mai babban suna, kaga naman nan yayi mana yawa, duk da an babbayar dan Allah sonake na ƙara gyara shi, ayi miya gobe in Allah ya kaimu, mu je yi wa su baba sannu da shan ruwa"
A take ya tsuke fuska, ya ƙi magana.
"Dan Allah Master, na neman albarka mu je mu gaishe su"
"Wai ke wace iri ce ne? Tun da muka yi aure, bayan su hajiya, kin ga wani ya zo gidan nan daga ɓangarena? Ko Abbun kin ga ya zo? Dama maraba suke nema da ni, har gara mahaifinki ma ya zo"
Jauhar ta ce "Kar ka ce haka, dama ba su yakamata su zo ba, mu yakamata mu je, ai su iyaye ba a fushi da su, kai fa ka yi wa wani faɗa a kan haka, bai kamata kai ace ka aikata haka ba, dan Allah ka yarda mu je" An kai ruwa rana sosai tsakaninta da shi, kafin ya amince.
Washegari suka shirya, bayan azahar suka fara zuwa gidan su Al'amin.
Suka fara zuwa gidan su Al'amin, suka yi sa'a Abbu yana nan, sai dai rahila tayi mamakin ganin Al'amin, yayi wani shar da shi, sai ƙamshin turare yake yi kayansa sun sha guga.
Ashe Abbu zuwansa gidan su biyu, ba ya samun kowa, a gidan, gashi Al'amin ya wanke ƙafarsa ya daina zuwa gidan.
Abbu baki ya kasa rufuwa, mamaki yake ganin Al'amin, a nutse da shi ya sako 'yar matarsa a gaba gwanin sha'awa, sai dai sai cika yake yi yana batsewa yana wani basarwa.
Dan tun da suka gaisa da Abbu, bai sake cewa komai ba, jauhar ce take bashi amsa idan yayi magana.
Rahila ma sai zuba take ta ce "Ikon Allah, anya ba a canzo wani Aminun ba, kun yi kyau abunku kun ƙara ƙiba, an ce kin yi rashin lafiya kwanaki, To na san dai ba zai wuce laulayi ba, Allah ya raba lafiya"
Al'amin ya ce "Amin, tashi mu tafi rana tana yi" kawai ta girgiza kai jin Al'amin ya amsa, idan ma haka ne ai kamata yayi, yayi shiru kawai.
Rahila ta sake cewa "To sai ayi ta kula da ita, ka san masu ciki sai ana lallaɓa su, ban da hantara da abun da zai ɓata mata rai, kuma ba zama zaka yi ba, ciki tun yana ƙarami ake fara sayayyar kayan jariri".
Jauhar ta ajiye food flask, da leda ta ce "Mama ga wannan, kwa yi buɗa baki, a saka mu a addu'a"
Abbu ya ce "Masha Allah, addu'a kullum cikin yin ta ake, Allah ya yi albarka"
Rahila ta ce "Iyee har da su suga da kayan marmari?" Ta buɗe fulas ta ce "Abbu kaza ce fa a ciki, ikon Allah sana'a ka samu ne haka? Ko kuma haryanzu miyagun ƙwayoyi ka ke sayarwa, gara mutum ya san halaccin abun da zai ci".
Al'amin ya kalli jauhar, irin kallon kin ga abun da nake gudu ko?.
Ya ce "Ubana na zo gani, kuma banda 'yar madara ta matsa, da sai dai na je ƙofar masallaci, idan ya fito na ganshi kamar yadda na saba, dan haka ba sai kin san sahihanci da halaccin cin sa ba, tun da bani da alaƙa da ke" ya tashi ya danƙi hannun jauhar a gaban su.
Abbu ya ce "Aminullahi tsaya mana"ya tsaya cak yana huci, jauhar sai ƙoƙarin zame hannunta take yi daga nasa, saboda kunya.
Abbu ya ce "Allah ya saka da alkhairi, ya yi albarka. 'ya ta Allah ya saka miki da alkhairi, yayi muku albarka gaba ɗaya"
Ta ce "Amin Abbu, a sha ruwa lafiya "
A zatonta, zai ta yi mata masifa, sai dai ta ji bai ce mata komai ba, ya wuce da ita unguwar su, ya kaita har ƙofar gida.
"Ki yi sauri ki fito mu tafi, mu koma gida"
Ta ce "To*
Ta sauka daga babur ɗin ta shiga gidan, suka gaggaisa, sai dai baba baya nan, ta ce "Dama ɗan abun sannu da shan ruwa na kawo masa, sauri nake yi na bar shi a waje, kar ya gaji da jirana"
Anty Zakiyya ta ce "Lallai jauhar, shi mijin naki ya fi ƙarfin ya shigo ya gaida mu kenan?"
"A'a ba haka bane Anty, kin san ba ya jituwa da 'yan unguwar nan, bana son wani abu ya faru ne"
Mama ta ce "Haryanzu bai shiryun ba kenan? Sai labari muka ji wai ya fito ai, Jauhar wannan naman kajin, shi ya saya ko ke?"
Ta ce "Shi ne"
Suryaya ta ce "To a dai yi a hankali, Allah ya sa ba na sata bane ba".
Jauhar ta ce "Allah ya tsare shi, Al'amin ba ya sata".
Anty Zakiyya ta ce "Wato Jauhar ba zaki yi mana Allah ya sanya alkhairi ba ko, ko kishi ki ke yi?"
Cikin rashin fahimta jauhar ta ce "Anty na me?"
"Alhaji mu'azzam ya dawo, tun da kin yi aure yanzu hafsa zai aura, ya bayar da miliyan biyu tayi lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin aure!"
Ayshercool
08081012143.
34
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
Abunka da zuciya, dumm haka ƙirjin Jauhar ya buga, da ƙarfin gaske, take wani abu da ba ta san menene ba ya taso mata.
A ranta ta ce "Saboda haka dama ku ka aura mini Al'amin, dan rusa aurena da Alhaji mu'zzam?"
'kul jauhar, Al'amin zaɓin Allah ne a gare ki, babu wanda yake da ikon canzawa wani ƙaddararsa, dama haka Allah ya tsara miki'
Cikin sauri ta ce "Ahh haba, amma ba a gaya mini ba, ga shi muna waya, ina yi muku magana ta what's app, Anty ke ma ina da lambarki, amma ba a gaya mini, ko dan kar in haɗa lefen na zo na ɗauki kayan kwalliya ne ya sa ba a gaya mini ba?"
Anty Zakiyya ta ce "A'a kar a gaya miki ki ji wani abu a ranki ne, dama Allah bai ƙaddara mijinki bane"
Jauhar ta ce "Haka ne, mijin wata baya auren matar wani, idan an gama haɗawa ni dai zan zo a bani kayan kwalliya".
Surayya ta ce "Au, ashe fa ba ayi miki lefe ba ke ko?"
Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a kin manta an yi mini sayayyar kaya?"
"Duk da haka wannan ai ba lefe bane ba"
Wayar jauhar ta fara ringing, ta cirota daga jakarta ta ce "Master"
"Fito mu tafi"
"To gani nan"
"Bari na tashi yana jirana, idan an saka lokaci sai a gaya mini"
Hafsa ta ce "An saka bayan salla da sati uku ne"
"To Allah ya sa zamu gani, a gaishe mini da baba, sai kuma Allah ya kaimu salla, Anty walida ku kuma na gaji da roƙonku ku zo gidana, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa yi mini kara ya zo".
Hafsa ta ce "Ke fa babu wanda zaki gani a gidanki, muna yayyenki zamu din ga zuwa gidanki, ko so ki ke mu zo mijinki yayi mana illa?"
"Haba dai, ba fa mahaukaci ba ne, da zai yi muku illa, da ban kawo yanzu tare da shi ba, sai anjimanku"
Zuba mata ido yayi, har ta ƙaraso, sai dai ya lura da jikinta a sanyaye yake, bai ce mata uffan ba, ya kunna babur ɗin, ya karkata mata ta riƙe shi ta hau suka tafi.
Sai yanzu ta ƙara gane dalilin yin amfani da yi mata sharri, wurin aura mata Al'amin, ba wai tana baƙin ciki da auren hafsa bane ba, ta san haka Allah ya ƙaddara kawai mamakin tsananin ƙin da suke yi mata take yi, ta san ko da kuɗi ba za su yadda su aurawa 'ya'yan su mutum irin Al'amin ba, saboda kar ta huta shiyasa suka yi mata wannan muguntar.
Kallon bayan Al'amin take yi, a ranta ta ce "Kai Allah ya zaɓa mini, kuma in sha Allah sai na yi kyakywar rayuwar aure da kai master'.
Da haka suka ƙaraso gida, sai dai yana ankare da yadda walwalarta ta gushe, take komai jiki a sanyaye babu kuzari.
Ɗan muzurunta na ta kewayata, yana yi mata ɗan kuka, amma ta kasa kula shi, wanda da tana cikin walwala da tuni ta ɗauke shi tana yi masa rawa, da ma shi ba shiri yake yi da muzurun ba, dan dana sanin kawo mata shi ma yake yi, saboda yadda take tsananin ba wa muzurun kulawa, kamar ya jefar da shi haka yake ji wasu lokutan.
Ya zuba mata ido, tana ta yi wa wani mayafi ado da beads, na kayan sallar mutane da take ta yi, sai dai a saɓule take aikin.
Muzurun ma ya gaji, ya koma gefe ya kwanta, saboda ta kasa kula shi.
Har aka sha ruwa, ko surutun yau ba ta iya yi, abincin ma cakalarsa kawai take yi, ta kasa ci ta ajiye ta tashi tayar da sallar taraweeh.
Ta cigaba da aikin beads.
"Ssss, Ji mana" ta ɗaga kai ta kalleshi.
"Zo mana"ta ce "To" ta yinƙura ta tashi, ta ƙaraso gaban sa, tana ƙoƙarin zama a ƙasa, ya nuna mata kusa da shi, ta zauna tare da sunkuyar da kanta.
"Kin ga muna zamanzamanmu, ki ka kwashe mu, muka je wurin mutanen nan, gashi kin je an yi miki wani abun kin kasa sukuni, shiyasa tun farko na ce kar mu je, ki ka dage, kin dawo kin kasa nutsuwa, me aka yi miki?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Bakomai"
Ya ce "Bana tambaya sau biyu"
"Ka yi haƙuri dan Allah, babu komai, zuwa da safe zan wartsake in sha Allah".
"Ba ki da juriya, kin fiye rauni, da wuri ake ganin gazawar ki, ki ƙara ƙoƙarin zama jaruma, ko dai ayi miki ki shanye ko shirya ramuwar gayya sama da abun da aka yi miki. Ki ajiye wannan abun da ki ke yi, ki tafi ki je ki kwanta"
Ta jinjina masa kai ta ce "To master, na gode sosai" ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ta kwanta.
Sai dai bacci ya gagari idonta, ta din ga tunanin, meke damunta kishi ne ko hassada. Sai dai ta tabattar wa da kanta ba kishi bane ba, saboda ta riga ta zama matar wani, ko ba komai a yadda yake ɗin nan, ta fara appreciating yanayin zaman na su yanz saɓanin da, dan haka tana matar wani ba zata yi kishi a kan wani ba.
Hakazalika ba hassada ba ce ba, ba ta ji ta damu dan hafsa zata shiga cikin daular da, da ita ce zata shiga, ta san wannan nufin Allah ne, kawai tana jinjina yadda suka shiga suka fita, suka aura mata Al'amin dan kawai kar ta auri Alhaji mu'azzam.
Wannan gillin ɗabi'a ce ga zuciya, da duk yadda ɗan adam ya kai ga dannewa sai yayi tasiri, ta din ga istigfari da roƙon Allah ya sanyaya mata ranta, ta manta ta fuskanci Rayuwarta.
Yanayin yadda Al'amin ya fara nuna damuwarsa a kanta, ya ke sanya wa ta ji tabbaci da ƙwarin gwiwar cewa wataran za ta ji daɗinsa, tun da dai babu duka ko zagi a tsakanin su, shaye-shayen sa da nema rigimarsa ne babbar matsalarta, gashi yanzu cefane ma yana yi ko ba kullum ba.
A cikin kwanakin da ta dage da addu'a, sai ta fara jin sassauci ta fara mantawa, ta cigaba da mayar da hankali a kan sana'arta, da yi musu Addu'a babu dare babu rana.
Al'amin ya fara rage yin shaye-shaye a gabanta, sai ta yi bacci, sai ya fita tsakar gida, ko ƙofar gida yayi, duk da wasu lokutan idan ta shiga ta tarar da shi yana yi, mazewa yake yi ya haɗe rai ya cigaba da shan abun sa, amma sosai yake rage abun da zai yi, wanda zai sanya ta shiga damuwa.
Ya mayar da ita asibiti, likita ya tabattar da jininta ya sauka, kuma ya dakatar da ita daga shan magani, na wani ɗan lokaci.
Saura sati guda salla, gidan jauhar mutane ne kawai ke shiga suna fita, masu mayafai, masu ɗinkuna da zata yi wa stone work, masu kitso da lalle, a haka kuma tana kasa kayanta, na shirin dutse, sarƙa abun hannu, jigida, ga kayan lemo, masu zuwa kitso suna yi mata ciniki. Ta zama very busy, idan yamma ta gabato, ga aikin abinci, sai dai garin Allah yana wayewa, ya fice ya bar gidan, saboda mutane.
Sai dai ana shan ruwa take sallamar kowa, ta ce sai gobe, za ta kula da mijinta.
Yana falo a zaune, ya gama shan ruwa ya kasa tashi, wata mata tayi sallama, tayi ta yi wa jauhar magiya, wai tana son ta turo yaran, ta wanke musu kai, tayi musu kitso, kowace yarinya ɗari da hamsin, su huɗu.
Jauhar ta ce "Haba Maman Nana, ki bani ɗari bibbiyu mana, ga wanke musu kai, ga kitso?"
"Taimakawa zaki yi jauhar, idan ki na son gobe mu kawo miki coustomers, kin san yadda garin yake, ubansu bai bani ko sisi ba, ni nake wahalata dan yaran su fito fes, ko hankici bai yi mana ba"
Jauhar ta ce "To shikenan, bari na sallami master, gobe in Allah ya kaimu akwai mutane sosai, turo su yanzu a wanke musu kan, in dafa ruwa a heater tun da da wuta, gobe in Allah ya kaimu da sassafe sai ayi kitson"
"Ke, na hana kitson, kwashi yaranki ki tafi wani wurin ayi miki" ta ji muryarsa a ƙofar falo.
Jauhar ta ce "Master meyasa?".
"Na hana kitson, duk wannan wahalar da ki ke wuni kina yi a ɗari da hamsin? Dama wuni ki ke wahalar banza, saboda aikin yi yayi miki ƙaranci? Get out malama kwashe yaranki ki fita, iyayen son banza".
Kamar jauhar ta yi kuka ta ce "Master dan Allah...
"Shhh" yayi maganar yana ɗora yatsansa a kan laɓɓansa.
Matar ta fita ta kalleshi kamar za ta yi kuka ya ce "Na ga aiki ne yayi miki ƙaranci, mu je ina da aikin da zan baki ni, ki zauna ki wuni kina wahala, a ɗari da hamsin, ina zaki kai kuɗi ne wai? Duk kin rame saboda kin saka azabar son kuɗi a ranki" Yayi maganar yana kallon ta, tana tsaye tana tura baki.
Ya fizgota gabansa ya ce ya kai hannunsa wuyanta ya ce "Wannan ƙashin na wuya da ki na shi? Duk kin yi wuri-wuri ga azumi ga wahala" da sauri ta ɗan kama jikinta, saboda unexpected ya saka hannunsa a wuyanta.
Maimakon ya sauke hannunsa, sai ya miƙar da hannunsa zuwa kan maƙogwaronta, ya fito da dogon harshen sa har wurin haɓarsa, ya lanƙwasa shi, sannan ya mayar cikin bakinsa ya ce "Na ga kina motsa baki, me zaki ce?"
Jauhar ta ce "Ai shikenan ka korar mini coustomer, kuma ka shaƙeni zaka kasheni ka huta. Kuma sai ka biyani kuɗin wanda ka korar mini, ɗari shida"
"Bana son ganin wannan ƙashin, kwana uku kawai na baki ya koma" yayi maganar yana sake shafa wuyanta. Riƙe hannunsa tayi, tana kallon idonsa, da abun da yake yi matan ko a jikinsa.
Ɗan muzurunta ne, ya yo tsalle yana yakushin ƙafar Al'amin, saboda riƙe wuyan jauhar da ya yi, yana kuka.
Al'amin ya kalli muzurun, yayi cilli da shi, ya ce "Na kusa mayar da abun nan in da na ɗauko shi, ya fiye zaƙewa, zo ki yi mini aikina"
Ta biyo shi tana mitar ya korar mata coustomer's , ya nuna mata kujera 3seater ya ce ta zauna.
Ta nemi wuri ta zauna, ya kwanta ya miƙe ƙafafuwan sa a kan cinyarta ya kaɗa mata yatsunsa, alamar tayi masa tausa.
Ta ji haushin yi mata asarar ɗari shidan da yayi, shi kuwa ko a jikinsa, sai dai ƙasan zuciyarta mamaki take yi, ashe yana kallonta har haka da ya gane ta rame.
Iya ƙarfinta ta saka tana jan yatsun ƙafarsa, tana son yayi magana, amma ko a jikinsa.
Tun tana yi da marmari, har ta fara gajiya, dama gashi wuni tayi aiki, tun tsakiyar azumi rabonta da baccin kirki.
A take ta fara gyangyaɗi, bacci mai ɗan nauyi ya yi gaba da ita, kamar a mafarki ta ji abu yana taɓa cikinta, ta buɗe idonta ta ga menene, babban yatsansa ya saka yana taɓa cikinta.
Da sauri ta ɗame cikinta, ta kalle shi, ya rufe idonsa kamar mai bacci. Ta riƙe ƙafarsa, ta sake kallonsa, amma ya saka ɗayar ya cigaba.
Ta saka duka hannunta biyu, ta rirriƙe ƙafafunsa, tana ajiyar zuciya kamar mara gaskiya.
A hankali ya buɗe idonsa, yana kallonta, ta sake ɗaga kai ta kalleshi, suka haɗa ido, tayi saurin kawar da kanta.
"Dambe zamu yi ne ki ka rirriƙe mini ƙafa? Tausa fa na ce ki yi mini".
Kamar ta yi kuka ta ce "Na gaji bacci nake ji"
"Eh da aikin banzanki ne, ba zaki gaji ba ai, kin ga yanzu kya samu lada sama da ɗari shidan da ki ke yi mini ƙunƙuni a kanta"
A shagwaɓe ta ce "Ni ba ƙunƙuni nake yi ba fa, ka yi haƙuri to" ya janye ƙafafuwan sa daga kan cinyarta, ta tashi da sauri, muzurunta ya bi bayanta, ta saka hannu ta ɗauke shi ta nufi ɗaki.
Baba ya ji daɗin abun da ya tarar jauhar ta kai masa, ya din ga murna da sanya mata albarka, tare da yi mata addu'a iri-iri.
Ganin hankalin Jauhar yana kan 'yan kuɗaɗen da take samu, na sana'ointa, ya sanya ya ƙyaleta, baya son yawan takura mata.
A goman ƙarshen nan, haka ta din ga damunsa, a kan yawaita ibada, dan azumin kawai yake yi, ba sauran ibadu. Da ƙyar take saka shi yayi salla cikin dare ko raka'a biyu ce.
Dama idan aka sha ruwa, ya ƙoshi sai ya je dabar su, sun yi shaye-shaye tukuna ya dawo gida.
Ana jibi salla, ta saka shi a gaba da naci, da magiya, su je ayi masa aski saboda gabatowar bikin salla ƙarama.
Ya ce na za shi ba, ƙarshe ita ta zauna, ta wanke masa kan, ta rage masa sumar da almakashi, tayi masa gyaran fuska da shaver, tamkar ɗa da uwa.
Ana gobe salla, ta yi masa list dai-dai na talaka, ta ce ya sayo, za ta yi abincin salla, dan abubuwa da dama idan ba ta ce masa yayi ba, ba zai yi ba, idan kuwa ta ce ya sayo zai sayo, idan ba shi da hali kuma zai gaya mata ba yanzu ba.
Da sassafe ƙarfe bakwai, ta shigo ɗakinsa da mp ɗin ta, an sako kabarbari da ake yi yayin tafiya idi, tana maimaitawa.
*Allahu Akbar, Allahu Akbar la'ilahaillala*
*Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd*
*Allahu Akbar kabiran*
*Walhamdilillahi kathiran*
*Wa subhanallah bukratan wa asila*
"Master, kar mu makara sallar idi fa, ka tashi" ya motsa a hankali yana yamutsa fuska.
Ta miƙa masa hannu ta ce "Barka da salla? Ina fatan ka yi sallar idi lafiya"
Yayi miƙa tare da hamma, ta ce "A'uzibillah, Alhamdilillahilazi ahyana, ba'ada ma amanatana wa ilaihil nushur. Ga ruwa mai zafi can, ka zo ka karya mu shirya"
"Sai na karya tukuna"
"To taso ka yi brush, ko sai na ɗauke ka ne, sai ƙara maƙalewa ka ke yi a katifa"
Kukan ɗan muzurun nan ne ya sanya Al'amin shi tashi zaune ba shiri, ya biyo jauhar yana yi mata ɗan kuka.
Ta kalli muzurun ta ce "Sweetheart, mu je na baka abinci" Al'amin ya tashi ya bar ta da muzurunta, saboda zaƙewar muzurun ta fara yawa a kan matarsa.
Ya fito daga wanka, ta shigo ɗakin da wata leda, ta saka dogon hijjabi light blue, sai zuba ƙamshi take.
"Master yi sauri zamu makara"
Ya shafa mai, ta buɗe ledar ta fito da ɗinkakkiyar shadda light blue, da hula, ga agogo sai takalmi soso na ta da nasa, iri ɗaya na ta na mata na sa kuma na maza.
Turus yayi yana kallonta, cikin tsananin mamaki.
"Ungo saka, bari na je na rufe ɗakina kan ka gama"
Kamar soko ya kasa karɓar kayan.
"Ko ba ka so ne?" Tayi maganar a sanyaye.
"A ina ki ka samo wannan kayan?"
Ta ce "Dama ana samo kaya ne? Neman kuɗin da ka ke cewa na saka a gaba ne, ka san wata nayi ina yi mana tarin nan? Hmm saka kayanka ina zuwa bari na ɗaukko wayata da darduma" ta ajiye masa ta fice.
Kallon kayan ya din ga yi yana jujjuya su, har da aiki a jikin kayan, shi bai yi mata kayan salla ba tayi masa?.
Ya saka wandon, ya tsaya yayi shiru yana kallon rigar, har ta dawo ɗakin.
"Master saka mana" ta karɓi rigar tana ɓalle botiran jiki, ya karɓa yana sakawa ta ce "Alhamdilillahilazi kasani haza saub, waraƙatani min gairi haulin minni wala ƙuwwa"
Ta saka masa hula, ta saka masa lence ɗin hannun rigar, ta ɗaura masa agogo, tare da saka masa farin glass na maza.
Tayi wani irin murmushi ta ce "Tubli wa yuklifllahu ta'ala. Wallahi kana da kyau master, ka ga yadda ka yi kyau kuwa? Subhanallah saka takalmin mu ke falo na yi maka hotuna" gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, ashe matan ma sunan suka tara? Wace irin mace ce jauhar.
"Master ka yi dariya mana, sai hoton ya fi kyau"
Ta gama yi masa hotunan, ta riƙo hannunsa, ita ma ta saka nata gilashin fari, suka fita sallar idi.
Musulunci mai daɗi, al'ummar musulmi na ta ɓarkowa ta kowane angle zuwa masallacin idi.
Shi rabonsa da zuwa sallar idi ma, har ya manta lokacin, amma yau albarkacin auren mace ta gari, ta saka shi a gaba har zuwa masallaci.
Aka idar da sallar idi, suka haɗu a wani gate ɗin daban, bisa koyi ga sunna, jauhar ta bawa wata wayarta, ta ce dan Allah tayi mata hoton first eid with habinbi.
Ta ɗauka zai ce baya so, bisa ga mamakinta, sai ta ga ya saka hannu, ya dafo kafaɗarta jikinsa, yana kallonta, ta saka hannu ta zagaya a ƙugunsa kasancewar da kaɗan ta wuce ƙugunsa, ta kalleshi ita ma tana murmushi. Hotunan sun yi kyau sosai, banda wanda ya yi wa Al'amin kyakkyawan sani, ba zai gane shi ba, sai ya zama very decent and calm.
Har suka dawo gida, hannunta na cikin nasa, cike da shauƙi da nishaɗi.
Ya karɓi mukulli ya buɗe musu gida suka shiga, jauhar baba ta fara kira, ta yi masa barka da salla, ya ce mata idan mijinta na da account, ta tura masa ya saka mata barka da salla.
Ta kira yaya saifu ma, haka ta din ga bin family tana yi musu barka da salla.
Ta kalli Al'amin ta miƙa masa wayarta ta ce "Saka mini lambar baba, mu yi masa barka da salla"
"Bani da ita" ya bata amsa.
Ta marairaice ta ce "Dan Allah master"
Ya ce "Sai kuma ki yi"
Haka ta haƙura ta tashi ta ƙyale shi, ta tafi ɗakinta, ya din ga kallon kayan jikinsa, yana sake jinjina ƙoƙari da ƙarfin hali irin na jauhar, wai shi ta yi wa kayan salla.
A status ɗin ta, ta yi posting "Alhamdilillah first eid with my amazing Habibi, Allah ya ƙara wa zamaninka tsayi, ya maimaita mana"
Surayya ce ta fara ganin status ɗin, ta din dariya tana nuna wa 'yan gidan, suka din ga cewa pretending
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 121