kamar ya canza gaba ɗaya, ya dafo kafaɗarta kamar ƙawarsa ya ce "Bar wankin, zan yi ki haɗo da naki ma, idan na gama zan yi gyaran kwatar layin nan, duk an bari ta cushe da shara, me zaki dafa mana da rana?"
"Master ba ka da aiki sai zancen abinci ne?"
"To idan ban yi zancen abinci ba zancenki zan yi babyn roba"
"Saura ta katako, rana zata yi mini, ko wankin ka saɓa sai na yi mana ɗauraya"
Al'amin ya ce "A'a ki yi aikin ki zan wanke" yayi maganar yana yi mata wani irin kallo tare da murmushi.
Ita ma murmushin ta yi masa ta ce "Harshenka dogo ne, meyasa ka ke fito da harshe ne?"
Ya ce "Rantsuwa ce, kowane specie ɗinmu, akwai irin ta su".
Jauhar ta yi dariya ta ce "Wai specie kamar a biology?"
"To in ce kowane ɗan daba?"
Ta yi saurin girgiza kai ta ce "A'a ba na son wannan kalmar, babu daɗin ji"
Ba tare da ta gane ba, yayi mata wayo, ta daina fushin da take yi, dan babban burinta ya kula ta, ya sakar mata fuska.
Aka shiga satin bikin Hafsa, Anty Zakiyya ta kira Jauhar ta ce "Jauhar wai yaushe zaki zo ne? Ayyuka sun kacame, ko dai baƙin ciki ki ke yi da lamarin nan ne?"
Jauhar ta ce "Haba Anty, ba haka bane wallahi. Kin ga maigidan ne ba ya jin daɗi, idan na taho babu mai kula da shi".
"Kamar yaya? Au mijinki ya fi 'yar uwakki, kamar wani mijin kirki, da waye yake kula da shi idan ba shi da lafiyar?"
"A'a Anty, ai miji duk in da yake miji ne, yana buƙatar kulawa ne, ba dan....
"Dalla yi mini shiru, har wani tinƙaho ki ke yi da wannan abun? Makakken ɗan wiwi.
Ba tare da Anty ta sani ba, tuni ya karɓi wayar daga hannun jauhar, ya saka a kunnensa tana ta masifa "To ki zauna sai yadda yayi da ke, ai mutumin kirki mai kuɗi shi yake saka doka a bi, ba irin mijinki ba da har ki ke gaya mini wai ai miji miji ne ba".
"Makakken ɗan wiwi yana godiya, kuma kun san da makakken ne, ku ka aura mata ni. Ni na hanata zuwa matata ba baiwa ba ce, ta zo ta yi muku bauta, ba zata zo ba, idan kun ga dama ku bar bikin kar ku yi" Jauhar tana girgiza masa kai, amma sai da ya gama maganar ya jefar da wayar.
"Master, iyayena fa, ba a haka yakamata a gaya musu ba, da ka bi a hankali, na san yadda zan gaya musu".
Al'amin ya ce "Kin san bani da tarbiyya, ban iya magana da manya ba"
"A'a ba haka nake nufi ba"
"Idan ma dai hakan ki ke nufi, idan kuma ban isa ba, ki shirya ki tafi "
Jauhar ta ce "A'a ka ma isa, ai na fasa zuwan, amma ai ka yi mini alƙawarin zaka kai ni gidanta bayan bikin ko?" Tausayinta ne ya kama shi, ba dan haka ba da gidan hafsan ma ba zai bari ta je ba, amma ya tuna ɗan uwa duk in da yake daɗi ne da shi, kuma bai kamata ya hanata zuwa wurin 'yar uwatta ba, amma kamar ko a jikinsa ya ce "Zan yi shawara"
Anty Zakiyya kuwa, sai da kayan cikinta suka yanutsa, saboda tashin hankali da ta ji muryar Al'amin a waya.
Sai dai jauhar ta sha zagi a gidan, ana cewa baƙin ciki ne da hassada ya sanya ba zata zo ba.
Yaya saifu ya ce 'm"Jauhara ba ta da irin wannan zuciyar, hankalinta na kan mijinta, wannan aure dai, in dai dan cin amana aka yi shi, ba in da zai je zai watse".
A fusace Anty ta ce wa mama "Ki ja wa ɗanki kunne, kar ya sake aibata mini auren 'ya"
An kai kwanaki huɗu ana events kala-kala na auren Hafsa, jauhar sai kallo da ta din ga yi, tana murmushi tare da jin babu daɗi rashin halartar auren yayarta, ga 'yan uwa da abokan arziki duk an taru.
Ita ma ta ɗora hotunan, tana yi wa hafsan fatan alkhairi.
Aka gama biki, aka kai hafsa gidanta, wanda suke haɗe da uwar gidansa, kowacce part ɗin ta daban.
Aka yi sayen baki aka watse, ya tara su yayi musu nasiha, bayan Uwargidan ta fita, Alhaji mu'azzam ya ce "Bari na je na ɗan ƙara rarrashinta, na san tana cikin damuwa" haushi ya kama hafsa, dan a zatonta yana zumuɗinta, ba zai saurari uwar gidan ba.
Sai dai har ɗaya na dare bai dawo ba, ta kira wayarsa a kashe, tun tana saka ran ya dawo, har ta gaji, bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe ma, ga yunwa ga gajiya, amma ba ta ganshi ba, sai sha ɗaya na safe.
Ya ce "Jauhar am sorry please" ta kalle shi cikin takaici ta ce "Jauhar kuma?"
"Afuwan Hafsat, wallahi madam ce nayi ta faman rarrashinta, taƙi yin shiru kin san kishi babu daɗi, shiyasa na zauna da safen nan ma da ƙyar na fito, duk a cikin damuwa ta ke, yanzu haka kanta ciwo yake saboda kuka, ina ga da kaina zan fita nema mata magani"
Tamkar hafsa ta zabga masa mari haka ta kalleshi ta ce "Ni bana buƙatar kulawarka kenan sai ita?"
Ya ce "No ba haka bane ba? Ai ke sabuwa ce, sai ta fiki shiga damuwa, bari na je na sayo mata maganin na kai mata, na yi ordern abinci, idan ban dawo da wuri ba ki karya kawai.
Abu kamar wasa, har wurin kwanaki uku, bai saurari hafsa ba, wai uwargidansa ba ta da lafiya, har ma ya ɗauki fushi da ita, wai ba ta je ta yi mata sannu ba, ta ɗauki waya tana kuka ta sanar da Anty, Hankalin Anty ya tashi, ta ce ta je ta dubata ɗin, za su sake shiri su ma.
Baya nan hafsa ta shiga duba ta, ta ce "Na ji an ce baki da lafiya, na zo duba ki"
Ta ce "Ko ɗaya, lafiyata ras, kawai ina ƙoƙarin nuna miki ƙarfin ikon da nake da shi a cikin gidana da irin gangancin da ki ka aikata na shigo mini gida"
Hafsa ta ce "Shigowar ai ita ce mai wuyar, tun da an ce hanawa ki ke yi, ni kuma na yi nasara na shigo, mu zuba da ni dake".
"Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka, ga fili ga mai doki".
Har hafsa ta kwana bakwai a gidan nan, ba su haɗa shimfiɗa da Alhaji mu'zzam ba, duk ɗokin amarcin da take yi, komai ya fita daga kanta, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, ƙiri-ƙiri yake nuna mata shi ta matarsa yake yi ba ita ba, saɓanin abun da ya nuna mata a waje.
Jauhar kuwa ta cigaba da yi wa master magiyar, ya taimaka ya bari ta je gidan hafsa tun da an yi bikin, kuma ta na son ta je gida ta gaida baba, ta bashi gudunmawar biki.
"Ni fa nayi miki alƙawarin zuwa gidan yayrki, amma amarya ce, ya zaki je musu gida sati ɗaya da biki?"
Cikin rashin fahimta ta ce "To ba a zuwa?"
"Eh, idan sun shirya samun zuriya su, ai ba za so ki dame su ba, idan lokaci yayi zan kai ki".
Anty da Rahila suka cigaba da yawon bin bokaye, ƙauye-ƙauye, dan su sake kama Alhaji mu'azzam, kuma ya saurari hafsa.
Komai na buƙata gashi nan a zube, amma miji ya gagareta sai dai ta ganshi daga nesa.
Tayi iya ƙoƙarinta, duk wanda ya zo, ba ta bari ya fuskanci tana cikin damuwa, ta baka abinci ka ci ka sha, idan zaka tafi ta baka na mota mai yawa, tayi ta hura hanci, saboda tana cikin gida na alfarma ga motoci a parking lot.
Jauhar ta gaji da yi wa Al'amin magiya, ta ƙyale shi, dan kansa ya ce ta shirya, shi zai kaita gidan hafsan, su gaisa ya dawo da ita.
Ta din ga murna tana yi masa godiya, amma ta ce "Dan Allah master a sakawa baburin nan salansar sa, idan muka fita fa saboda ƙarar da yake yi, sai kowa ya waiwayo ya kallemu".
Ya ce "Ni fa na fi son abuna a haka"
Ta kwantar da murya ta ce "Na sani, amma a taimaka mini, ko so kake kowa sai ya ɗaga kai ya kalli babyn robar taka?"
"Zan duba"
"Yauwwa master na"
Yayi murmushi ya ce "Naki, waye ya baki?"
Ta ce "Allah ne ya bani, kuma na karɓa hannu bibbiyu ina yi masa godiya"
Ta kira hafsa a waya, hafsa ta ɗaga da ƙyar tana cika tana batsewa, Jauhar ta ce "Anty hafsa ina wuni, ina ta kiranki ba kya ɗagawa"
"Bana kusa ne, shiyasa"
"Adress ɗin gidan zaki bani, gobe in Allah ya kaimu zan zo in sha Allah"
Kamar hafsa ta ce mata ba ta so, b tare da la'akari da su ba su taɓa taka gidan jauhar ba, amma sai ta ga ya dace jauhar ta zo ta ga daular da take ciki, dan haka ta bata adress ɗin.
Bayan ta gama wayar, ta ce "Master ta bani adress ɗin, babu wuya ma gane gidan nata. Zo mu yi kallo a wayata" ta yi maganar tana zama a kusa da shi.
"Ni kallon nan gajiyar da ni yake yi"
Ta ce "Ahh haba dai, ko kaɗan nan, yana da kyau ka samu abubuwan da za su din ga ɗebe maka kewa"
Al'amin ya ce "To zaɓi ɗaya, ko dai ki sauke wannan abun, ko kuma a haƙura da kallon" yayi maganar yana nuna boti, da yayi ɗare-ɗare a kan cinyar jauhar.
Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "Boti master ya ce ka tashi daga cinyar matarsa" kwanciya magen ya ƙara yi, yana lafewa.
"Ban taɓa ganin abun da ya raina ni ba, kamar ke da magen nan ba"
Jauhar ta din ga dariya, ita yadda ba sa ga maciji da botin ma dariya yake bata.
Ta zauna a kusa da shi, tayi connecting da mp, ta saka musu film.
Ta kalleshi ta ce "Ka ji ko? Baby ake cewa mace, kai baka yi mini irin wannan kalar soyayyar, sai zare mini ido da sakani kuka"
Yayi murmushi bai ce mata komai ba, sai dai ta ji ya saka hannayensa ya riƙe nata. Mintuna goma da ta ɗaga kai ta ga yayi bacci. Ta zuba masa ido yana bacci, a ranta ta cigaba da yi masa addu'a.
Ta kashe wayar ta ce "Master ka tashi ka je ka kwanta tun da kallon ne ba ka so"
Yayi shiru bai motsa ba. "Master"
"Mmm" ya amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba.
"Mu je na yi maka addu'a ka kwanta"
Ya ce "Ɗauke ni, na gaji"
Ta ce "Na ɗauke ka, ai kuwa da sai dai wata ba ni ba, aikin me ka yi ka gaji har haka?"
"Ƙasa muka kwashe tifa biyar, ban sha komai ba kuma na yi aikin, ni da su Walid"
Jikinta a sanyaye ta ce "Har tifa biyar master. Baka gaya mini ba sannu, amma dai sun biya ku ko?"
Ya tashi zaune ya ce "Eh, har na kai wa mai solar kuɗin, ya zo ya saka miki solar, ya kawo miki fankar solar zafi ya fara yawa kuma ba wuta".
"Solar kuma master? Da mun sai kayan abinci, zafi lokaci ne zai wuce, solar fa da tsada".
"An ce masu asma, ba sa son zafi" ya yi maganar yana tashi tsaye, tashi ta yi ita ma, sai ta rasa me za ta ce masa, ya nufi ɗakinsa, ta rasa ta ina yakamata ta fara ma. Akwai abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace yana yi da kuɗi, da solar da ya saya, kamata yayi ace ya sai musu kayan abinci, ya ɗinka sutura da ko ɗan takalmi ne mai kyau na kwalliya. Duk in da ya kwashi taklminsa soso haka yake ƙarawa gaba da su, kayansa ma ita ta ware masu kyan ta kai ɗakinta, sai idan za shi wani wuri na musamman ko juma'a ta bashi ya saka. Sai dai ta san bai kyautu, ta nuna ba ta ji daɗin abun da yayi ba, domin ko ba komai, yayi ne dan ya kyautata mata.
Ya nemi wuri ya kwanta, ta zauna a kan katifar, ta ɗora hannunta a kansa, tare da karanto masa addu'oin kwanciya bacci.
Abun da jauhar ba ta sani ba, bayan ciyar da shi da ta din ga yi farkon auren su, Addu'ar da ya ji tana yi masa cikin magagin ciwo, tayi matukar tasiri a zuciyarsa, Addu'a ce da idan ba uwa ba, ba kowa zai yi maka ba. Addu'oin da take yi masa idan yayi mata wani abu na kyautatawa ma, ba ƙaramin daɗi yake ji ba. Ga uwa uba kirarin da take yi masa wasu lokutan, da suke fasa masa kai. Duk wani abu da zai yi baya manta tarin alkhairin ta.
"Allah ya saka maka da alkhairi, ya buɗa arzikin ka, ya wadata mu da halal ya nesanta mu da haramun. Na gode sosai da sosai Allah ya biya ka da gidan aljanna, ya jiƙan iyayenmu"
Idonsa a lumshe ya ce "Amin 'yar aljanna, addu'ar ta yi daɗi" tayi murmushi ta tashi.
Washegari da wuri ta shirya, tana ta murna za ta je gidan hafsa, ta wanke laifinta na rashin zuwa biki.
Shi kuma ya ce zai kaita, amma ya din ga yanƙwanata.
Ba su fita ba sai sha ɗaya saura, tiryan-tiryan, har gidan hafsa.
Gida ne babba na gaske, Al'amin ya ce "Ba daɗewa zaki yi ba, da wuri zan dawo mu tafi"
"To Allah ya dawo da kai lafiya, take care".
Ya ce "To, ki shiga, sai na tafi"
"Saboda kar in gudu?"
"Idan kin gudu ma zaki dawo" yayi maganar yana tayar da babur ɗin sa.
Juahar ta shiga har falon Hafsat, ta din ga bata haƙuri na rashin zuwanta bikin nan ta ce "Kin san halik maza wasu lokutan sai a hankali, babu yadda ban yi ba, amma ya hana, ba shi da lafiya lokacin" Hafsa sai ɗan fizgar kai take yi, wai ita dole ga matar mai kuɗi.
Har la'asar tana gidan hafsa, bayan ta gama shan ƙamshin, ta saki jiki kuma suka hau hira, da yake ita ce sakuwar jauhar, daga ita sai jauhar.
Ta din ga koɗa mata irin son da Alhaji mu'zzam yake yi mata, dan ta tura mata haushi. Jauhar kuwa ko a jikinta, ta ce "Wallahi yaya hafsa idan Allah ya baka miji mai sonka tsakani da Allah, duk wani ƙalubale mai sauƙi ne"
Ta ce "Aikuwa shiyasa nake tausyinki, aure ba soyayya, ga miji sai a hankali"
Jauhar ta ce "Aikuwa ke da ki ka yi na soyayyar ma, ba ki fi ni samun kulawa ba, da farko a tsorace nake da shi, tun da muka saba Alhamdilillah"
"Taɓ, haryanzu yana safarar cocaine ɗin?"
Duk da jauhar ta ji haushin maganar ta ce "Da safarar cocaine yake, ai mun girmi zaman Kano sai Abuja"
Al'amin ya kira jauhar, ya ce ya zo ta fito su tafi.
Ta leƙa ta window falo ta hango shi, a cikin harabar gidan.
Ta ce "Ɗago kanka sama ka ga" ya ɗaga kai, ya hangota.
"To ka tafi, ba yau zan dawo gida ba, sai gobe"
"Wallahi idan ba ki fito ba, zan shigo har ciki"
"Kaikaikai, gidan mutanen za ka shigo?"
"Sai na shigo ɗin tukuna kenan?"
Tayi dariya ta ce "A'a, rufa mini asiri, kar ka saka da ni da kai a zanemu, gani nan"
Hafsa ta yi ƙuri da ido, tana kallon jauhar, tana leƙen Al'amin kuma suna waya, tana ta dariya.
"Yaya hafsa, bari na tafi"
Hafsa ta tashi ta ce "Mu je na raka ki".
Suka fito harabar gidan tare, yanayin Al'amin a yanzu, akwai nutsuwa a tare da shi, ba kamar lokacin da ya je gidan su ya ɗauki jauhar ba.
Hafsa ta ce masa "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau" ya amsa idonsa a kan jauhar.
"Ya ka ke hararata ne, ba gani na fito ba"
Ya ce "Zaki yi bayani" motar Alhaji mu'azzam ce ta shigo gidan, yana hangen jauhar, ya ci wani irin wawan burki ya buɗe motar ya fito.
Ya ƙaraso ya kalli Jauhar ya ce "Jauhar, dama kina nan?"
Tayi murmushi ta ce masa "Eh, ina wuni?"
"Lafiya ƙalau jauhar, sai dawowa na yi aka ce mini kin yi aure, na ce ko wani laifin na yi miki? Hafsa ta ce mini dama akwai wanda ki ke so, shi ki ka aura, ni kuma baki gaya mini ba lokacin da nake neman aurenki"
Kallo ɗaya jauhar ta yi wa Al'amin, ta ga ya murtuke fuska, idonsa ya fara kaɗawa zuwa ja.
Ta ce "Eh, gashi nan a gabanka mijin nawa, Allah dama ya ƙaddara yayata zaka aura. Yaya hafsa sai anjima".
Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode"
Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke.
Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.
Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.
Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raɗaɗin abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.
Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin ɗin sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ɗakinsa.
Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.
"Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?"
"Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma".
Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je".
"Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?"
"Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ɗauke da igiyar aurenka a kaina"
"Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba"
Cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.
Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa.
Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.
Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ɗaki, idan yana falo tana ɗakinta, idan yana ɗaki sannan zata fito.
Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.
Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ɗan yi nauyi da yawa.
Ya tashi ya tafi ɗakinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.
Tana banɗaki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ɗin.
Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar.
"Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.
"Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba.
Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ɗakin yayi duhu, ba ta ganin komai.
"Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya.
Direction ɗin da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne"
Ayshercool
08081012143
39
🔞 LITTAFIN KUƊI NE ₦500 VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143
YOUR RECEIPT VALIDATE YOUR PAYMENT.
Cikin cunkusa baki ta ce "To kuma shi ne zaka tsorata ni? Ko gama wankan ban yi ba na fito"
Ya ce "To mu je na ƙarasa miki"
Tsuke bakinta ta yi ta kasa magana, jin abun da yake yi, da ba ta yi zato ba.
Kasancewar bayanta, yana jikin ƙirjinsa, yana jin bugun zuciyarta yana fita da sauri-sauri.
"Meyasa ki ke shareni? Kwana uku kin yi mini laifi, kuma kina gaba da ni ko?"
Ba ta yi mamakin ƙarfin hali, da ƙwarewa a iya rainin hankali, irin na Al'amin ba, wato ma zaman jiran ta bashi haƙuri yake yi.
"Kin san zaki yi gaba da ni, meyasa ki ka bari muka saba? Ba ni da saurin sabo, ki ka yaudare ni ki ka sa na fara sabawa da ke, shi ne zaki wani din ga mazewa. A din ga manta abu a kwana ɗaya ya wuce kawai a cigaba da life. Ni kaina ban san dalilin da ya sanya nake matuƙar jin baƙin ciki idan na ga wani abu ya raɓe ki ba"
Da ƙarfi ta ce "Master" tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa.
Hankali kwance ya ce "Yes" ba tare da daina abun da yake yi ba.
Cikin rauni ta ce "Wai meye haka?"
"Aure" ya bata amsa kai tsaye.
Shiru yayi, jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugawa da sauri, tana nema ta fara haki, saboda tsoro.
A hankali ya ce "Common, relax mana"
"Babyn roba" tayi masa shiru, "Kodayeke yanzu babyn ƙarfe ce, ki amsa mana" still ta yi masa shiru, yana jin yadda ta saka ƙarfinta ta riƙe hannunsa.
Fito yake yi mata a kunne, hakan ya sanya ba shiri, ta saki hannunsa, ta toshe kunnenta.
"Ki amsa mana, tambaya zan yi miki mai muhimmanci. Kin san bana mantuwa, kamar na'aura mai ƙwaƙwalwa nake, in dai ka ajiye zaka zo ka ɗauka. Idan ban manta ba kin ce kina so mu rayu tare. Ina ta tsoron taɓa abun da nake ganin ban dace da shi ba. Ba na son cutar da rayuwarki, in yi silar gurɓacewarta kamar yadda tawa ta gurɓata, duk da kin daɗe ki na nuna mini ina rintse ido, Al'amin ba ya abu bisa zalunci"
"Na nuna maka me?"
"In faɗa kenan, ko shekaranjiya meya kawo zancen zuriya? Ke 'yar yarinya kallonki kawai nake yi, amma kar ki damu da hakan ai lafiya ce" wato da wani ne yake ba wa jauhar labarin maganganun nan daga bakin Al'amin suke fitowa, sai ta ƙaryata, amma ƙiri-ƙiri, ya shige duhu yana sakin maganganu yadda yake so, alhalin ya ce ba ya jin komai.
Tana cikin tunanin ta ji ya ce "Kin amince mu rayu tare, a matsayin abu guda? Ba na son cutar da ke, ke ma kin shiga ƙalubale da dama, bana son ki sake shiga matsalar rayuwa, rayuwarki ta tafi a haka kawai. Idan kin amince, zan yi iya ƙoƙarina wurin zama da ke da zuciya ɗaya, amma sai kin yi wa yanayin rayuwata uzuri, duk da a yanzu ma kin taka muhimmiyar rawa a rayuwata. Be mine"
Haka kurum ta fara kuka, kukan da ba ta san na menene ba ma.
"Talk babyn roba".
"To ka ƙyale ni, gobe da asuba sai na gaya maka"
Cikin buɗɗiyar muryarsa, da take fitowa daga ƙirjinsa, ya ce "Na ƙi wayon, yanzu zamu gama maganar"
"Master"
"Mmmm"
"To zaka daina saka ni kuka?"
Ya ce "In sha Allah"
Ta ce "Zaka daina shaye-shaye?"
"In sha Allah, ina iya ƙoƙarina, ba abu ne da zan daina lokaci ɗaya ba. Mu bar wannan maganar, baki bani amsa ta ba, zaki cigaba da zama da ni, a yadda nake, ina talaka marayan da ya rasa kulawa, sai bayan shigowar ki rayuwata?"
Tana kuka ta ce "Dama ai kai ka ke cewa zaka sake ni, ka ke sakani kuka, ina son in zauna da kai"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Duk wani abu da ki ka yi mini na alkhairi, yana rubuce a ƙirjina, ba zai taɓa gogewa ba, ban taɓa mantawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 121