noƙe-noƙen da jin kunyar, ya raya darensa.
Sai dai ya shiga lissafi, duk da shi dai bai san dawan garin ba, amma kamar akwai banbanci tsakanin budurwa da kuma bazawara, amma bai mayar da hankali a kan tunanin hakan ba, saboda kukan da Shahida take yi, ya din ga bata haƙuri kamar wadda ya tafkawa laifi, har sai da ya bata tausayi.
Washegari da safe ma, ita tana jin nauyinsa, shi ma sai sinne kai yake yi, lokaci lokaci yana sakin murmushi.
Liti kuwa da kyar yayi bacci, saboda babu Walid babu Viper, yayi ta mita, wai suna can tare da bargo mai numfashi da sabuwar katifa, shi yana nan ya kasa bacci.
Da sassafe Liti ya kira Walid a waya, Walid bai watstsake daga bacci ba ya ɗaga ya ce "Lafiya?"
"Au haka ma zaka ce? Koma kira ni ka ji yaya nake?"
Walid ya ce "Haifarka na yi da zan kiraka da sassafe na ji yaya ka ke?"
"Allah sarki ni, wato kai yanzu ka yi 'yanci, yayi kyau, na ce ba, ka rage mini kazar ko kuma yaya?"
"Eh, ta na wurin mai zamani ka kira shi ka karɓa"
Liti ya ce "Ai da shi muka fara yin waya, Abuja fa zai tafi yau"
Da sauri Walid ya tashi zaune ya ce "Haba dai?"
"Wallahi haka ya ce mini, cikin dare aka tura masa saƙo, gashi har aka gama bikinsa ɗan mama baya nan"
"Amma shi aikin nasu babu hutu kenan? Mutum yayi aure amma ace ya fito washegari"
"Kai ma dai ka faɗa"
"Bari na kira shi" sun yi sallama da liti, amma ya kasa kiran Viper, saboda kunya, shi tunani ma yake idan ya koma kasuwa ko zai iya kallon Abbu.
Gidan Ango Al'amin kuwa, bayan sallar asuba Nabila ta koma bacci, ganin Viper bai dawo ba.
Ƙarfe tara ta tashi, still baya ɗakin, ta kulle bedroom ɗin, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta duba jakarta ta ɗauki brush ta wanke bakinta.
Ta canza kaya ta fita falo, tana kallon gidan.
Kitchen ta leƙa, ta tarar har ya dafa tea, tana tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falo, falon ta dawo a dai-dai lokacin da ya shigo.
Ta ɗan maze ta ce masa "Ina kwana?"
"Ban ganshi ba" ya amsa mata, tare da wucewa digning, ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo in da ya barta ya ce "Ga abin breakfast can, kazarki kuma da baki ci ba, tana kitchen.
Ni an turo mini saƙo tun cikin dare, ƙarfe sha biyu zan bi jirgi na koma Abuja.
Ba ta san lokacin da ta ce "Saboda me?" ba.
"Harkar aiki"
"A kawo ni juya yau kuma ka tafi, yaushe zaka dawo?"
"Ina ruwanki da lokacin da zan dawo? Dama ai ba ƙaunar ganina ki ke yi ba, tun da an aura miki annoba, idan na matsa sai ki sarara"
Cikin kuka Nabila ta ce "Ai dama na sani, a haka ka ke cewa na baka chance ɗin, ko na baka chance ɗin, na san babu wani da zai canza, ba na gabanka, ba ni da wani muhimmanci a tare da kai, am regretting this marriage"
Shareta ya yi ya wuce cikin ɗaki, ita da ta nuna ba ya gabanta, ko menene na ɗaga hankalinta kuma, dan kira shi wurin aiki oho mata.
Duk da a zahiri shi ma bai so hakan ba, amma dolensa ya tafi muddin yana son yin galaba a kan Indabo, ta wani fannin kuma, yadda Nabilan ke treating ɗin sa, gara ya tafi kawai ya rabu da ita.
Da fari kuka ta zauna tana yi, daga baya ta ga kamar ta faɗo ne, sai ma ya rainata, shi bai damu da ita ba, ita kuma ta damu da tafiyar sa.
Ta haɗa abin kari tana karyawa, kamar ta na cin magani, ya sake fitowa ya fita, aka jima sai gashi da kayan abinci niƙi-niƙi.
Ƙarfe sha ɗaya ya sameta a ɗaki, ta ɓuya tana matsar hawaye.
Kamar bai gani ba, ya ajiye mata kuɗi ya ce "Na san maybe zaki yi baƙi, ga kuɗi nan, idan kina buƙatar wani abu, na san kirana a waya abu ne mai wahala, zaki iya kiran wanda ki ka ga ya dace kin yarda da shi, ya kirani ya sanar mini" har ya bar ɗakin ba ta ce masa uffan ba.
Ya saɓa jakarsa ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi, yanzu yana ƙoƙarin gazgata Nabila ba ta ƙaunarsa.
Tafiyarsa babu jimawa kuwa baƙi suka din ga zuwa, dan haka sai damuwar ta ta ta ragu, sai dai ana watsewa komai ya dawo mata.
Walid kuwa hankali kwance ya ci gaba da shan sharafinsa da amarya Shahida.
Ranar da zai koma kasuwa, ta sha dariya har da riƙe ciki, wai kunya yake ji ya fita kasuwa ya haɗu da Abbu ma.
Da kyar ya samu ya fita, Allah ya sa ranar Abbu bai je kasuwa ba, sai dai duk bayan mintuna kaɗan, yana maƙale da waya yana kiran Shahida, sai da ya ji kamar ya janyo yanna ta yi ya koma gida.
Sai da liti ya gaji ya fara zage-zage da faɗar maganganu, Walid kuwa yayi masa banza, sai daga ƙarshe ya ce "Zafin gwaurantaka ke damunka, ba zan kula ka ba"
Sannu a hankali baƙi suka fara ɗauke ƙafarsu daga zuwa gidan Nabila, hakan ya fara damunta, ga Viper tun da ya tafi babu ko flashing, hakan ya ƙara ƙona mata rai, ita kuma ta kira shi, gani take ta faɗo.
Sumayya dai ta ci gaba da rarrashin Nabila, kusan duk kwana biyu sai ta zo wa Nabila, dan ta gaya mata Viper ya gari. Ita ma a hankali ta rage zuwa, an doshi sati uku, babu Viper babu labarin sa, ko baccin kirki ba ta yi sai aikin kuka, idan ta gaji kuma sai ta yi ta tasbihi, saboda yana daga abin da yake sauke mata fushi da wuri.
Babu tsammani ta ji ana buga mata gate, ta tashi ta fita tana tambayar waye?.
"Buɗe ki gani" tana buɗewa ta ga Walid da Shahida, murmushi tayi tana yi musu maraba.
Sun yi ƙalau da su, daga shi har ita, Walid ya kuma nutsuwa, kuma cikin manyan kaya yake, yanayin yadda suke magana akwai fahimtar juna a tsakaninsu.
Ita kuwa an zubar da ita a cikin gida, ya tafi aikinsa ko ta kanta baya waiwaya.
Walid ya ce "Bari na tafi kasuwa, da yamma na dawo mu tafi, dama Viper ne ya ce wai lallai in kawo miki ita, ta tayaki hira, kaɗaici ya dame ki, na ce masa to ya dawo mana"
Nan dai ya bar mata Shahida, shi kuma ya tafi.
Shahida ta ce "Anty Nabila, maman dr. Duniya ce, ai ni mun ƙulla alaƙa da ita, ai yanzu na san nayi aure, wannan auren mai kuɗin duk ba shi ne ba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Au da ba aure ki ka yi ba?"
"Taɓ, aka gama yi mini banke-banken magani, da shi da babu duk ɗaya, magani ya kusa illata ni, sai da na kwanta a asibiti, kuma na kasa faɗar abin da ya faru. Ga yan uwansa masifaffu, wai yana ta aure mata ba haihuwa, shi bai gaya musu shi ne mara amfani ba. Na sha wahalar auren nan, shekara uku sai da na ci na yi kallo, na zauna babu banbanci da ina gida, kuma kowa gani yake nayi aure a gidan hutu. Na cire kunya na gaya wa mama, wai sai cewa tayi, Allah ya rufa mini asiri zan tona wa kaina, nayi nayi ya sake ni yaƙi, ni kuwa na kaishi kotu, na ga zai saye su da kuɗi, na samu Abbu na gaya masa, aikuwa yayi ta faɗa"
Nabila ta waro ido ta ce "Abbun ki ka gaya wa wannan maganar?"
"Eh mana Anty Nabila, da ace masa gani can da aurena ina ɓarna fa? Idan cin abinci da kallo na je yi, in zauna a gidanmu mana"
Nabila ta ce "Gaskiya tun da na ji Hafsa ta yaba, kema kin yaba, na ƙara yadda da kayan maman dr"
"Sosai fa, zata baka abin da ya dace da kai, da aka yi mini auren fari, ai wata jahila aka samu ta din ga jibga mini kayan shashanci suka kusa kashe ni, ai maman dr tayi a rayuwa. Ni gidan Yaya muhsin duk da bashi da ƙarfi, ya fiye mini gidan tsohon mijina sau dubu, ga ci ga sha ga kwanciyar hankali, gashi lafiyayye, ban yi gyara a banza ba"
Waro ido Nabila ta yi ta ce "Kin fi ƙarfina Shahida"
"Hmm ba zaki gane ba, matan da suka tsinci kansu a irin halin da na taɓa tsintar kaina, sun san takaicin abin nan. Kana gidanku baka san komai ba dama, ya fi sauƙi hankalinka a kwance yake, amma an aurar da kai, mutum ya san ba shi da lafiya, saboda zunzurutun zalunci, ya aureka, kuma yan uwansa su addabeka, baka haihuwa, wallahi na kusa gaya wa babarsa ranar da aka ishe ni, kawai nayi shiru"
('yan uwa kar ku bari a baku labari, ko kuma a bar ku a baya, ku garzaya ku jarraba, kayanta, ga kyau ga kuma inganci 0706 971 1327)
Nabila ta ce "To Allah ya kyauta, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna, tun da kin samu abin da ki ke so"
Dariya tayi, ta ce "Amin, ina nan ina ta kwantar da kai ina lallaɓa abina, ko ƙuda bana son ya taɓa mini shi, ina matuƙar son sa da tausayinsa"
Nabila ta ce "Yakamata, ai Walid mutum ne na gari"
Sun sha hira sosai da sosai, dan sam Nabila ba ta bari, Shahida ta fuskanci damuwa a tattare da ita ba.
Bayan tafiyar su, da daddare ta rasa abin yi, ta buɗe wardrobe ɗin Viper, ta sauke kayan tana gyarawa.
Wani ƙaramin littafi ta gani, ta ɗauka ta fara dubawa.
"Wannan littafin na master ne, kar ka manta ka karanta shi safe da yamma"
Azkar ne aka rubuta shi, na safe da yamma da hausa, sai kuma Addo'in kwanciya bacci.
"Ka kula mini da kanka sosai master, duk lokacin da ka karanta, ka yi mini addu'a"
Ƙasa sai ta zana heart da sunansa, irin da na soyayyar ƙuruciyar nan.
Shafa littafin Nabila ta din ga yi tana kuka, ta ce "Allah ya sa auren mijinki, kar ya zame mini cin amanarki 'yar uwata, Allah ya sa ba ƙaddarar auren nan ne ya sanya ki ka bar duniyar nan ba, ina ƙaunarki duk da ban sanki ba"
Sosai Nabila ta yi kuka, mai ban tausayi, daga bisani ta tashi jiki a sanyaye.
Kamar wadda aka yi wa nasiha, washegari, ta tashi da matsananciyar kewar Viper, babu tunanin komai, ta ɗauki waya, ta din ga kiransa, amma wayarsa a kashe.
Kawai sai hankalinta yayi matuƙar tashi.
Madam halima ce ta kira Nabila, suka gaisa ta ce "Nabila, gobe Joseph zai zo da safe, zaku tafi Abuja, Viper babu lafiya"
Ƙirjin Nabila ya buga da ƙarfin gaske, ta ce "Meya same shi?"
"Ban sani ba, Joseph ne ya zo yake gaya mini, dan haka ki zama cikin shiri" kuka ta saka wa madam, tana tambayar ta, idan wani abun ne ya same shi ta gaya mata, amma ta ce mata ba ta sani ba.
Ana idar da sallar asuba ta shirya, cikin matsanancin tashin hankali, addu'a kawai take yi Allah ya sa yana lafiya.
Ta waya suka din ga communicating da Joseph, ya zo gidan, ya ɗauki Nabila suka tafi, sai da ta tambaye shi ko ya san wani abu a kai, amma ya ce mata bai sani ba.
Sumayya ce ta kira Nabila, ta ce mata maza ta hau social media ta duba meke faruwa.
Hannunta na rawa ta buɗe tana duddubawa, wai tsohon riƙaƙƙen ɗan daba Aminu Viper, ya koma ɗan ta'adda, bayan da yayi attacking ɗin manyan mutane ciki har da honorable Indabo, da bindiga a wani guset house da yake Abuja.
"Impossible, this is not true, Vi ba zai yi haka ba, dole akwai wani abu a ƙasa"
Sai daf da azahar suka isa barrack ɗin da yake aiki a Abuja.
Nabila sama-sama take numfashi, a ganinta gawarsa kawai za su nuna mata.
Wani ɗaki aka shigar da ita, yana kwance a kan gado, ana ƙara masa jini, da gudu ta ƙarasa gaban gadon da yake, bakinta na rawa tana faɗin Innalillahi wa Innalillahi raji'un.
An nannaɗe kafaɗarsa da bandeji, ga cikinsa gefe a kumbure. Alamu ya nuna harbinsa aka yi a kafaɗarsa.
"Vi, ka tashi dan Allah ka tashi"
"Madam ki yi haƙuri, bai daɗe da samun bacci ba"
Ko ta kan mai maganar ba ta bi ba, ta ci gaba da kuka.
A hankali ya buɗe idonsa, ya ɗago ya kalleta.
"Vi, meyafaru haka, garin yaya aka harbeka, da gaske zuwa ka yi ka kashe indabo, meyasa zaka yi attacking ɗin sa haka?"
Lafiyayyen hannun ya ɗago, ya shafi fuskarta, ya ce "Aiki mu ka je, ban yi attacking ɗin kowa ba. Mun yi negociating da wasu hukumomin na tsaro ne, aka je gidan, amma an ce na yi laifi, zan iya fuskantar hukunci, na yi harbi ba a bani umarnin hakan ba, duk da yaransa sun yi yinƙurin kashe ni.
An kama Naja'atu Bunkure a gidan, da ƙanan yara mata da ake lalatawa da kuma maza, gidan da aka yi sanadiyar ran Nura ne, kuma mun kama makamai a gidan, da wasu manyan ƙusoshin gwamnati duk a gidan. Hukumar soja ba sa zargina sa ta'addanci, wannan sharrin media ne, da nake kyautata zaton mutanen Indabo ne suka saka ayi mini hakan, hukuncin da zan fuskanta na harbi ne ba ayi mini uzuri ba, ina da abubuwa da yawa da tun a baya na so mu tattauna, amma baki bani chance ba, baki bani da ma ba Abla, akwai abubuwan da nake buƙatar aiki da ƙwaƙwalwarki, saboda ta kan yi mini jagora a wasu abubuwan, amma ki ka ƙi saukko ki fahimce ni"
Ƙanƙame shi ta yi tana kuka ta ce "Am sorry Vi, ka yi haƙuri dan Allah, amma zan ɗauki kowane irin mataki, wallahi babu mai hukunta mini kai, wahalar da ka sha ma ta isa haka, wace irin ƙasa ce wannan? In dai ina raye babu wanda zai yi maka wani hukunci babu shu"
Ya saka hannu yana shafa kanta ya ce "Dan Allah ki zauna tare da ni abla, zamanki a kusa da ni, yana bani ƙwarin gwiwa ina jin am safe idan muna tare, tun ba yanzu ba Please" ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa.
*GA MASU JIRAN DOCUMENT, ZA SU IYA PAYMENT YANZU, FEW PAGES YA RAGE, ONGOING PAGES NE 500 COMPLETE DOCUMENT KUMA 1K. VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143
Ayshercool
08081012143
"I promise that, ina tare da kai ɗari bisa ɗari, komai tsanani da wahala, is enough yakamata ka huta haka, masifun nan sun yi yawa"
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ina ga haryanzu sakamakon laifuffukana ne suke ci gaba da bibiyata".
Ta ce "A'a, Allah ba azzalumin sarki bane ba, kuma yana son bayinsa masu neman gafararsa. Wannan wata jarrabawa ce ta daban, kuma zamu cinyeta ita ma in sha Allah, sannu Vi" ya jinjina mata kai kawai bai sake cewa komai ba.
Wayarta ta ciro, ta lalubo lambar Alhaji mu'azzam, ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa masa ta ɗora da cewa "yallaɓai ka ga abin da ya faru da Viper?"
"Wallahi ɗazu na gani Nabila, raina yayi mummunan ɓaci, na je Kano ne, amma anjima kaɗan zan shigo Abuja in sha Allah, kuma already na yi magana da ministan tsaro ma, za ayi bincike a kan lamarin"
"Wane bincike kuma, ana cewa wai sai an hukunta shi yayi harbi ba bisa ƙa'ida ba, ga harbi da aka yi masa, ni idan har haka aikin yake, kawai zai ajiye musu aikinsu, wannan wahalar ta isa haka"
"Ki yi haƙuri Nabila, na san halin da ku ke ciki, na kuma san wahalhalun da ya sha, duk kitumurmurar indabo ce, ina kyautata zaton an ce an sake shi ma, sai dai na zo kawai" tana cikin maganar wasu sojoji su uku suka shigo, da alama manya ne sosai a cikin rundunar tsaro, ta katse wayar.
Joseph ne ya ƙame ya sara musu, sannan ya kalli Nabila ya ce "Ko zamu ba su wuri?" Ko kallonsa ba ta yi ba ta ce "Ba in da zani".
Ɗaya ya ce "Sannu Viper"
Viper ya jinjina kai sannan ya ce "Thank you Sir"
Nabila ta ce "Da gaske ne wai sai an hukunta shi saboda yayi harbi?"
Suka kalleta gaba ɗaya, ɗayan ya ce "Muna tattaunawa a kan lamarin ne, an ce ba shi yayi harbin ba, Dss ne, kuma mun duba bindigarsa, yayi harbi da bullet biyar"
Ta ce "Yanzu idan na ɗauki bindiga zan harbeka, ga bindiga a hannunka tsayawa zaka yi sai wani ya baka order zaka kare kanka?" Ba ta damu da mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu ba ta ci gaba "A matsayina na lauya nake yi muku magana, wadda ta san 'yancinta, ni ba soja ba ce ba, kar ku yi expecting wata special girmamawa daga gare ni, na san ƙarshenta dai ace a kashe ni. Yanzu da an kashe mini shi, gawarsa kawai zaku kawo mini kuna yi wa gawar faretin banza da na wofi, babu lallai a samu hukumar ta sake bi ta kaina a matsayina na matarsa.
Masu laifin da ya taimaka aka kama, ba ƙasa ya yi wa aiki ba? Harbin da aka yi masa bai isa ba, kuma sai an yi masa wani hukunci, ga suna an ɓata masa an kira shi da ɗan ta'adda amma ba ku ce komai ba"
Viper ya ce "Nabila"
"Ka ƙyaleni Vi, sai dai a kashe ni, kun san abin da ya yi going through in his life, washegarin tarewata da aurenmu, ku ka ce lallai ya zo bakin aiki, yazo kuma yayi abin da ku ke so, kuma this is what he deserves, da haka za a saka koya wa matasanmu ƙauna da kishin ƙasa? Masu laifi na sharholiya masu kare ƙasa ana gana musu azaba, a kan laifi ƙanƙani, i will fight for his right" numfashinta sama yake yi sosai cike da ƙunar zuciya da takaici. Viper kuma ba shi da ƙarfin da zai hanata, saboda jirin da yake ji, da kuma jinin da ake ƙara masa.
Ɗaya daga cikin sojojin, da Nabila ke kyautata zaton shi ne babbansu, sai ya yi murmushi, cikin harshen hausa ya ce wa Viper "Kai ka auro zakanya kamar kai, she's lioness and fearless, i like her confidence.
Madam, we are working on your husband issue, muna supporting ɗin sa, a kan ayyukan da yake yi, kin san mu bamu da hurumin kama mai laifi, sai dai muna hana yi wa ƙasa ɓarna.
Mun yi haɗin gwiwa da wasu hukumomin, Viper shi ya gano gidan, kuma tare da shi aka je, a ƙoƙarin kama masu laifin, aka fara harbe-harbe.
Kuma mu bamu fitar da report na ga abin da ya faru ba, and abin da viper ya yi bamu gama yanke hukunci a kai ba, kin ɗauki zafi da yawa ki yi haƙuri, Viper aikin sa ba zai iya ajiye shi yadda ya ga dama ba, ya san dokar aikin ai. Kuma zamu bincika duk wanda yake da saka hannu, wurin wallafa wannan labarin zamu baki dama, ki kai ƙararsa ki yi haƙuri"
Joseph kansa da ya fara tsuma, bai san hukuncin da za a iya yi wa Nabila ba, wannan kwarmaton da tayi ba, amma abin mamaki, sai ya ga an ɓuge da rarrashinta.
Hawayenta take gogewa, amma sun kasa tsayawa, saboda wani irin matsanancin tausayin Viper, da ya takura zuciyarta, ya wahala da yawa.
Ɗaya sojan ma, rarrashinta ya din ga yi, yana kiranta da 'yar sa. "Da kin san matsayin da mutane masu muƙamin Viper suke da shi a rundunarmu, da baki ce ya ajiye aiki ba, amma muna baki tabbacin, zamu san abin yi a kan sa"
Suka gama maganganun da za su yi, da rarrashinta suka fita.
Matsawa ta yi sosai jikinsa, sai bin sa take da ido.
"Abla"
"Na'am vi" ya juyo a hankali ya riƙeta ya ce "Ki zauna a kusa da ni, kar ki je ko ina dan Allah"
"Ina tare da kai in sha Allah vi"
"'yar madara ta tafi ta bar rayuwata da duhu, kin fara hasakata amma kina ta so kema sai kin bar ni, Please"
Ta katse shi ta hanyar cewa "Vi dan Allah ka yi shiru, Allah ya baka lafiya na ɗaukeka mu tafi, Allah ya baka lafiya"
Ya sake cewa "Amin, indabo azzalumi ne abla, an kama shi, amma na san sakinsa za su yi, na yi iya yi na, na bar wa Allah sauran"
Nabila ta ce "In sha Allah kuma zai isar maka"
Ta lallaɓa ta tashi, ta yi alwala ta yi salla, ta zo ta yi masa alwala, ya gabatar da salla yana kwance.
Wasu sojojin ne suka sake shigowa su biyu, ba su ce mata uffan ba, aka cire masa jinin da yake shiga jikinsa, kasancewar ya ƙare, suka ɗaga shi zaune, ya jingina da jikin gadon.
Suka sara masa, sannan suka juya za su tafi.
Viper ne yayi gyaran murya, suka tsaya suka waiwayo.
Yayi wa ɗaya alama ya zo, ya tako ya ƙaraso, Viper ya nuna masa abincin da suka shigo da shi.
Babu musu sojan ya buɗe kowanne ya ci, ya rufe. Da hannu ya yi musu umarni suka tafi.
Nabila tana jejjera masa sannu, ya kalleta ya ce "Ga abinci nan ki ci"
Ta ce "A'a sai dai kai na zuba maka ka ci"
Ya girgiza kai ya ce "Na ƙoshi"
Cikin damuwa ta ce "Ka ƙoshi kuma, vi kamar dai akwai wani abu kuma da yake damunka" ya ɗago ya kalleta.
"Menene ka gaya mini mana"
"Ba komai" ya faɗa a taƙaice.
Ta marairaice ta ce "Please, Vi menene ka gaya mini"
"Jikina ne kawai babu daɗi"
"Sannu, bari na zuba maka, ko kaɗan ka ci"
Baya son ta ci gaba da takura shi da tambayoyi, dan haka ya daure ya din ga haɗiyar abincin, tamkar yana haɗiyar magani.
Ya gama ta bashi ruwa, ta dubi hannunsa ta ce "An cire bullet ɗin ne?" Ya jinjina kai ya ce "Tun ranar aka cire".
"Amma yaya aka yi ka je gidan da kanka, har tsautsayin nan ya faru?"
Ya ɗan numfasa ya ce "Tun bayan rasuwar Nura, da ya gaya mini in dw zan samu Simon, na je na same shi. Shi ne ya gaya mini in da gidan yake, da abubuwan da suke wakana a gidan.
So ban yi wani abu a kai ba, har tsautsayin nan ya faru, so bayan nan na daɗe ina fakon gidan, ina da informers ɗina a kan gidan. Sai dai yadda ake gudanar da laifuka a gidan, akwai tsari da taka tsantsan ɗin da babu lallai a gane, tun da da haɗin kan wasu daga cikin jami'an tsaro ake abin da ake yi.
Nayi magana da shugabannina, muka yi haɗin gwiwa police da DSS, sai da na tabattar da Indabo yana gidan, muka je operation, sai dai bayan mun shiga, wasu daga ma'aikatan gidan suka far mana da harbi.
An kama Indabo Naja'atu ma tana gidan, da wasu manya a ƙasar nan, police sun tafi da su, amma bana tunanin za ayi wani dogon bincike, rahotannin da na samu, kamar an ce an sake shi ma, amma bani da tabbas.
Ina takaicin mutum kamar Indabo ace ya ci bulus a kan abubuwan da ya aikata, amma babu komai"
"Wallahi ba zai ci bulus ba, dole ya girbi abin da ya shuka ko da me yake yawo"
"No, kar ki kuskura ki ce zaki yi wani abu, yanzu ma abin da ki ka yi, ikon Allah ne ya tsallakar da ke, kin san suwa ki ka tsaya a gabansu ki na faɗar maganganu kuwa? Bani da ƙarfin hana ki a lokacin, amma da sun yi yinƙurin yi miki wani abu, to da zan nemo ƙarfin duk in da yake na baki kariya, ko da kuwa hakan na nufin na rasa raina ne.
Gidan soja ne nan, ba a misbehaving, idan ki ka yi dole na karɓi hukuncin da za ayi miki. I don't know why you are so much lucky"
"I am lawyer, 'yanci na sani, dan haka ba ruwana da dokar koma gidan waye, mijina nake son ya samu 'yanci"
Murmushin gefen baki yayi ya ce "Kamar gaske"
"Da gaske nake Vi"
"Na ji amma ban yarda ba"
Alhaji mu'azzam ne yayi sallama ya shigo, suka amsa gaba ɗaya, ya ƙarasa suka gaisa da Viper.
Cikin damuwa ya ce "Sannu Viper, ya jikin?"
"Alhamdilillah"
"Ashe abin da ya faru kenan, nayi magana da shugabannin naku ai, kuma ministan tsaro ya bayar da umarnin lallai su yi magana su wanke ka"
Nabila ta ce "Alhamdilillah, har shi ma ya ji?"
"Eh tun kafin na zo muka yi waya ai, kuma zamu gurfanar da gidan jaridar da suka sanar da wannan labarin ƙaryar, dan na san biyansu aka yi suka yi hakan".
Viper ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 113 Chapter of 121