mutumina, Allah ya baka duniya lahirar ma ka samu in sha Allah. Mahadi mai dogon zamani. Kai idan ba namijin gaske ba, kalli yadda ka mayar da mai hankali zararre cikin ƙanƙanin lokaci, kalli yadda yarinyar nan ta firgice ta koma zararriya lokaci ɗaya, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya tararka uban gidana, mahadinmu mai dogon zamani, Allah ya baka tsawon rai, ya kaimu ranar da zamu ba da jininmu domin ɗaukar maka fansa"
Geɓare baki Viper yayi kamar zai yi murmushi, dan kirarin ya tuna masa wasu abubuwa da dama da suka shuɗe.
Walid kuwa gaba ɗaya daga Viper har ɗan mama haushi suka bashi, kamar ya ɗura musu ashar, Nabila ko da cunen aka yi musu da iya, shi yaƙi ai ɗan zamba ne, kuma ko ba komai mace ce, bai kamata ya razanata har haka ba, tun da ya san mazan ma razana su yake yi.
Takalmansa ya saka, ya bi bayan Nabila, dan yadda ta fita a burkicen nan, komai zai iya faruwa, gashi ga dukkan alamu, ba ta da cikakkiyar lafiyar numfashi.
Viper kuwa, rigar jikinsa ya canza, Ɗan mama ya ce "Boss, wai ka taɓa karatun likita ne? Na san dai ka iya wankin ciwo, to kuma na ga yau kayi aikin likita".
Al'amin ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, na zauna da mai irin ciwon ta ne"
Ɗan mama ya ce "Na fahimta, amma dai ba fita zaka yi ba ko?"
"Zaka hana ni ne?"
Da sauri ya ce "A'a wane ni, ka san idan wannan jarababben ya dawo, ya tarar ka fita, masifa zai ta yi mini" bai saurari ɗin mama ba, ya bi ƙofa ya fita.
Nabila kuwa tun da ta fita da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba, sai da ta fita titi, shi ma babu ababen hawa, haka ta cigaba da tafiya tana waige-waige, sai a lokacin ta ji gefen cikinta, yana ta yi mata zugi, ta ɗaga rigarta ta ga plasta.
Ga jikin rigarta da jini, a hankali ta furta "Na shiga uku"
Addu'a ta din ga yi, tana cigaba da tafiya, cikin ikon Allah, Allah ya kawo mai a daidaita sahu, ta kama ta shiga, tana ta haki.
Sumayya tamkar yau ta shiga harkar aikin jarida, haka tattaunawar ta su da honorable Indabo take kasancewa, saboda yadda ya tsatstsareta da manya-manyan jajayen idanunsa, yana yi mata wani irin kallo, gashi daga shi sai ita a wurin.
Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Meyake damunki ne? Ki nutsu mana"
Ta jinjina masa ta kai, ta cigaba da yi masa tambayoyin da su aka yarje mata ta yi masa.
Sai dai ita kanta ta san amsoshin da yake bayarwa, na son zuciyarsa ne kawai, ba wani abu ba.
Jin ta yi shiru, ya sanya ya kalleta ya ce "Ya dai?"
Cikin girmamawa ta ce "Tambayoyin sun ƙare sir"
"Kamar bakinki akwai magana, akwai tambayoyin da ki ke son yi mini ko? Mu je zuwa ina saurarenki"
Ƙasan zuciyarta ta ce, ina ma da gaske ka ke, da ka ji ruwan tambayoyin da ko ka ƙi Allah, sai ka dangana da faɗar gaskiya, a zahiri kuwa ta girgiza kai ta ce "Babu sir"
Ya kalli kofunan gabansu, ɗauke da shayi, wanda shi yana yi yana shan nasa, ita kuwa ko taɓawa ba ta yi ba.
"Ya ba ki sha shayin ba? Ki sha mana"
Sumayya ta sake risunar da kai ta ce "A ƙoshe nake ne"
Ya ce "I see, amma na yi mamaki da ki ka ce mini baki da tambaya a gare ni, duk da yadda ki ka ƙaryata hirar da na yi kwanaki, ki ka ce ban yi ayyukan da na ce na yi ba, na ƙyale ki ne kawai saboda managernku yayi ta bani haƙuri, kuma ke mace ce yarinya ƙara ƴar cikina.
Siyasa mu tamkar business take a wurinmu baby girl, we invest to make a profit, ita kanta gidan radiyon da ki ke aiki da su, nike hannun jari mafi tsoka a cikinta, dan haka abun da nake so shi ake yi, kuma domin yi mini campaign ya sanya na zuba kuɗina a harkar gidan radiyon"
Sumayya dai ta yi shiru, ba ta ce komai ba.
Ya miƙe tsam, ya zagaya ya zauna a kan kujerar da take kai, wanda hakan ya sanya ja da baya, tana maƙale jikinta.
"Mun gama abun da ya kawo ki, sai kuma abun da ya sa na ce a turo mini ke"
Da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi, tana mamakin abun da ya faɗa.
Ya ɗauki kofin shayinta ya sha, sannan ya ce "Yarinyar da na ganku tare, ranar da na yi zuwan ƙarshe, ita nake nema ba ke ba, amma ke ce tsanin da yakamata na taka na kai gare ta, wacece ita?"
A tsorace take kallonsa, ya ce "Ki amsa mini mana".
"Nabila ce, ƙawata ce, she's like a sister to me" ta faɗa a tsorace.
"Ba wannan nake son ji ba" yayi maganar yana sunkuyowa daf da fuskarta.
"Wacece ita?"
Sumayya ta ce "Ƴar wani tsohon soja ce, dan Allah idan wani laifin tayi maka ka yi haƙuri, ba zata ƙara ba, idan ma dan ba ta gaisheka bane ranar, dan Allah ka yi haƙuri ba zata sake ba, ba ta da lafiya ne ranar"
Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, tarko nake son na yi da ita, aiki za ta yi mini"
Jiki na tsuma Sumayya ta ce "Wane irin aiki kuma?"
Ya gyara zamansa ya ce "Kin san wani ɗan daba Aminu Viper?"
"A'a ban san shi ba wallahi"
Indabo ya ce "Kina ƴar jarida, ki ce mini ba ki san shi ba, jami'an tsaro na neman sa ruwa a jallo, na yi niyyar shafe tarihinsa, aka samu wani ya yi mini zagon ƙasa, ya rusa mini komai.
Har a yanzu ana ta ƙoƙarin kama shi, kwatsam na ganku, kuma na ga tana da wani abu da zan iya yi masa tarko da shi ya zo hannuna, dan haka ƙawarki za ta yi mini aiki"
Hankali tashe ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, mutumin da yake kashe mutane, tana mace ina ita ina ɗan daba, ba jami'an tsaro suna nemansa ba? Za su kama shi dan Allah ka ƙyale mu"
Yayi wata muguwar dariya ya ce "Kin san waye indabo kuwa? Kama Aminu ya zama gawa ne kaɗai zai samar mini da nutsuwa da kwanciyar hankali, dan haka dole ƙawarki za ta yi mini aiki"
Ta buɗe baki za ta yi magana, wayarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ta ga nabila ce take kiranta.
Ya ƙureta da idonsa ya ce "Ɗaga mana, ɗaga wayarki"
Jiki na rawa ta ɗaga, ta kara a kunnenta.
"Sumayya kina ina ne?" Muryar Nabila ta fito raɗau a wayar.
Sumayya ta ce "Ina nan ƙalau, lafiya kuwa? Na ji kamar kina numfashi da ƙyar, ciwon ne ya tashi"
"Sumayya na kusa mutuwa yau" tayi maganar tana sauke numfashi.
A rikice sumayya ta ce "Mutuwa kuma, lafiya"
"Na haɗu da Viper, ya kusa kashe ni"
Ras gaban sumayya ya faɗi, indabo ya ƙura mata ido, yayi mata alama ta cigaba da wayar.
Jiki a sanyaye Sumayya ta ce "To maƙaryaciya, ni zaki jirga?"
"Wallahi ba ƙarya nake yi ba, ya na ji muryarki kamar wadda aka ritsa, kin je hirar ne? Ko wani abun ya faru ne?"
Sumayya ta ce "A'a, maƙaryaciya, mutumin da ake nema ruwa a jallo ki ka gani bai kashe ki ba?"
"Ban sani ba, tun da kin ƙaryata ni ki je ki ƙarata, ina fatan dai mutumin nan bai yi miki wani abun ba, dan mutumin nan yayi ruwan ƴan iska"
Kallonsa sumayya ta yi, sannan ta ce "Mu haɗu a gida"
Nabila ta ce "Ai dole mu haɗu yau, akwai magana, zan biya asibiti numfashin zai ɗauke, ki kula da kanki dan Allah, jikina yana bani kamar akwai matsala a in da ki ke, idan da wani abu, ki sanar da ni"
"Ke normal ne, sai mun haɗu" ta kashe wayar tare da kallon honorable Indabo ta ce "Wallahi ƙarya take yi, ba wani Viper da ta haɗu da shi, yayanta ne jami'in tsaron da yake bincikensa, amma wallahi ƙarya take yi"
Cikin ko in kula, indabo yayi dariya ya ce ce "Wato na yi zubin ƴan iska, wato a rayuwata ni mutum ne mai sa'a, na tsinci dami a kala, yanzu ke zaki yi mini aikin ba ita ba.
Dole ki tabattar idan da gaske take ko akasin haka ki sanar mini, duk wani aiki ko bayanai da nake son samu, ke zaki nemo shi a wurinta, idan ki ka saɓa umarnina kuma, zan saka a kawar mini da ke da ita baki ɗaya!"
Sumayya gabanta ya faɗi, ta rasa abun yi, kamar ta kurma ihu, wannan wace irin ƙaddara ce, ace babban mutum kamar wannan da ake ji da shi a kujerun iko, na ƙasa da jihar nan, ya rasa wanda zai saka a gaba sai su ƴaƴan cikin sa.
Ya ce "Buɗe wayarki ki bani" tamkar shashasha, haka ta cire password ta miƙa masa, yayi ƴan danne danne a jiki.
Wani mutum ne yayi sallama, ya shigo, ya ce "Gani sir"
"Wannan wayar zaka yi wa aiki"
Ya ce "Ok sir" ya karɓi wayar yana daddanawa, sannan ya miƙowa Indabo.
Ya ce masa "You can leave"
Ya miƙa wa Sumayya wayar ya ce
"Daga yanzu za ki din ga karɓar umarnin, abun da ake buƙatar ki yi, idan ki ka saɓa umarnin, zaki yi dana sani mara amfani, dan sai na fara da wulaƙanta rayuwarki, na tozarta ki, kodayeke dama wulaƙantacciyar ce. Dan ku ƴaƴan talakawa baku da wani amfani, kuma babu wani abu da zai faru idan na salwantar da rayuwarki, da kuma ta ta".
Sumayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, ƙirjinta na cigaba da bugawa.
"Tashi ki je sakatariyata zata sallame ki"
Sumayya ta tashi jiki babu ƙwari, ta bar ɗakin, tana tunanin wace masifar suke shirin shiga ita da Nabila. Allah wadaran bakin Nabila da bashi da saiti wasu lokutan.
Shi kuma yana babban mutum, menene alaƙarsa da wani Viper, wai shi waye ma wannan vipern, da ya fi kuɗi wahalar samu?
Tana fita sakatariyar ta miƙe tana murmushi ta ce "Har kun gama?"
Sumayya ta ce "Eh"
Ta miƙa mata envelope ta ce "Ga wannan ya ce "A baki"
Sumayya ta karɓa ta duba, kuɗi ne maƙudai a ciki, gabanta ya faɗi, tabbas idan ta karɓi kuɗin nan, ta tabatta sai ta din ga bin umarninsa, gashi ba ta san wane irin umarni za a bata ba.
Ajiye envelope ɗin ta yi ta ce "Ba na so"
Ta nufi hanyar fita, tana tuna yadda ya kirata da wulaƙantacciya.
Tana gaggawa ta kai ga ƙofar da zata fitar da ita waje, mutumin da ya karɓi wayarta ɗazu, ya sha gabanta, wanda hakan ya tilasta mata tsayawa.
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kamar yadda honorable ya gaya miki, ke zaki yi mana aiki a zahiri, bama buƙatar ta san kina yi mana aiki, dan haka ko kin karɓi kuɗi, ko baki karɓa ba, baki da zaɓi dole sai kin yi komai kasadarsa, ko da kuwa yana nufin sanya rayuwar ƙawarki a siraɗin rasa ranta, zamu yi amfani da ita, idan kuma kin zaɓeta zaki iya rasa taki rayuwar"
Cikin matsananciyar damuwa Sumayya ta ce "Muna mata, menene alaƙarmu da ƴan daba, wannan ba aikin hukuma bane ba?"
Yayi murmushi ya ce "Shi zaki gayawa hakan ai tun a ciki, idan kuma zaki kai wa hukumar ne, ga fili ga mai doki"
Wani abu mai ɗaci, ya tokarewa sumayya a ƙirji.
Cikin ɓacin rai ta ce "Amma dai ba ku yi mana adalci ba, wannan tamkar rusa mana rayuwa ne, tayaya muna ƴaƴa mata zaku yi tarkon kama mutum mai irin wannan hatsarin da mu"
"Ai ba ke aka ce ba, ƙawarki aka ce, dan haka ina kina son lafiyarki, da mutuncinki, kiyi abun da aka umarce ki, ita ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba. Ki yi ta kanki kawai, idan har ki ka yi abun da aka buƙata, babu wata alfarma da zaki nema a ƙasar nan ki kasa samu, zaki zama ɗaya daga cikin yaran honorable, za ki yi kuɗi, zaki ɗaukaka za kuma ki shahara, ki nutsu ki yi tunani da kyau, kar ki yi wawanci, ki je aikinki ya fara daga yanzu"
Shiru ta yi tana kallonsa, har ya gama maganganun da zai yi, sai dai gaba ɗaya ta rasa wani tunani ma yakamata ta yi.
Ba ga ce uffan ba, ta raɓa shi ta buɗe ƙofar ta fice.
A cikin mota, direban gidan radiyon, da wanda suka rakota suke tambayarta, yaya program ɗin ya kasance?.
Cike da basarwa ta ce musu lafiya ƙalau.
Kafin su ƙarasa gidan radiyon, ta ce su sauketa, tana da uzuri, dan haka ta sauka, ta kira Nabila a waya.
Tana kira Nabila ta ɗaga, "Yaya kina ina ne? Kina asibitin ko kin tafi gida?"
Nabila ta ce "Ina can, wai sai bayan 2-5hrs za su sallame ni, idan na zama stable, haryanzu numfashi yana bani wahala"
"Ok to gani nan zuwa"
"To masoyiyya Allah ya kawo ki lafiya"
Sumayya ta sauke wayar, kamar ta fashe da kuka, duk yadda take da Nabila, ace ta ha'inceta, ta saka rayuwarta a hatsari, anya amana ta ce haka kuwa?.
A haka ta ƙarasa Asibitin, ta tambayi ɗakin da Nabilan take, aka nuna mata.
Nabila na ganinta ta ce "Oyoyo sumyna"
Sumayya tayi murmushin yaƙe ta ce "Ya jikin?"
"Alhamdilillah da sauƙi"
"Baki kira kowa a gida ba, na ganki ke kaɗai?"
Nabila ta ce "Rabu da ni, ba wanda na kira, ƙarshe dai walida ko baba magajiya ne za su zo, dama da DSP yana gari ne, to shi ma wai ya tafi workshop ko me oho dai, Abuja ya tafi, dama da zai zo, to sai anty, ni kuma bana son takura musu, sai dai ba yadda na iya, na gaya wa Abba, kar su ji ni shiru. Amma ya na ga kamar kin yi kuka? yaya program ɗin?"
Sumayya ta ce "Wani irin kuka ana zaune ƙalau, program lafiya ƙalau, ga recording ɗin ma ban kai ba, na ce bari na zo na fara ganinki tukuna".
Nabila ta haɗe fuska ta ce "Ki gaya mini idan wani abun yayi miki, mu san abun yi, na gaya miki ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, dai-dai nake da shi idan wani abun yayi miki, in yi fito na fito da shi, sai in da ƙarfina ya ƙare."
Sumayya ta haɗe rai ta ce "Ke da ya yi mini wani abu kya gannin a haka, ba wannan ba, maganar da ki ka gaya mini a waya, da gaske ki ke ko kuwa?"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Baki yadda ba ko?"
"Yaya za ayi na yadda, mutumin da ake ta fafatukar yaya za a kama shi, ki ce mini kin haɗu da shi, kawai in yadda ta yaya?"
Nabila ta kaɗa kai ta ce "Kusan watana guda zuwa na biyu ma, kawai ina fafutukar yaya zan ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa. Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da ya ganni"
Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce "Kamar yaya?"
Nabila ta ɗaga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a wurin.
Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce "Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama da gaske ki ke?"
Ta saki rigar ta ce "Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi, wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi"
"Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?"
"Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni, kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya".
"Ta me kuma?!
"Wayarsa na sato, kan na taho!".
Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages, domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*.
₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan account ɗin.
0009450228
Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012143
14
🔞
*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*
*Ina masu buƙatar sayen nagartattun kayan magungunan mata, wanda babu cuta ko algus a ciki, ku yi joining link ɗin nan, domin samun nagartattun magungunan mata*
https://chat.whatsapp.com/BLqFsnlyNf0B483RhoWq8v
Tsoro Nabila ta fara ba wa Sumayya, "Are you serious? Nabila da ya kashe ki fa, ko kuma idan ya biyo ki fa? Meyasa ba kya tausayawa rayuwarki ne?"
"Wallahi nima na yi tunanin hakan, amma ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, ai bai san in da nake ba, yadda zan ba wa DSP wayar nake tunani, ba tare da ya yi mini faɗa a kan dalilin da ya sa na yi ba, ko tuhumata"
Ta ciro ƙaramar waya mai madannai, ta miƙawa sumayya, sumayya ta karɓa tana salallami, da sarawa sheɗancin Nabila.
Nabila ta ce "Wayar babu caji, sai na je gida zan sakata a caji" tayi maganar tana karɓar wayar, ta sakata a aljihun ƙaramin wandonta na ciki.
Ta sauka daga kan gadon, ta ce "Bari na shiga banɗaki na fito, na baki labari" ta sauka ta shiga banɗakin da yake cikin ɗakin.
Sumayya tayi ƙuri da ido tana kallon ƙofar da Nabila ta shiga, tana tunanin yadda abubuwa masu karo da juna suka sakata a tsakiya.
Wayarta ce ta fara ringing a cikin jakarta, ta ɗaukko taga baƙuwar lamba, ta ɗaga tayi sallama.
Muryar namiji ce ya ce "Ya ku ka yi da ita?"
Sumayya ta ce "Ita wa?"
"Wurin wa ki ka je?" Aka tambayeta.
Ta basar ta ce "Wa ke magana?"
"Ya zama dole fa ki yi aikin da aka saka ki, ko kina so ko ba kya so, a in da taken nan idan aka so za a iya kasheta, ko a saceta ayi abun da ake so ta yi, yin abun da aka saka ki ne kawai zai tseratar da rayuwar ta. Ta haɗu da shi ko kuwa?"
ta sunkuyar da kai ta ce "Wai dan Allah a tunaninka, tayaya mutumin da ƴan sanda ba su kama ba, ita ta haɗu da shi? Ƙarya kawai take yi dan ta raina mini hankali, Nabila tana da yawan wasa wasu lokutan, amma ƙarya take yi"
Nabila ce ta fito daga banɗaki, ta ce "Da wani garan ake waya? Ko kin yi sabon kamu ne?"
Sumayya ta katse wayar ta ce "Ba wani sabon kamu"
"Sumy, ciwon nan na cikina ne yake yi mini zafi fa"
Sumayya ta ce "Ai Allah ya ƙara, ni dama shegen duka ya yi miki, ya kakarya ki "
"Ta Allah ba taki ba muguwa, wallahi sumayya da dukana yayi, zai iya kashe ni, kin ga ƙirarsa kuwa, kin ga tsawonsa?. Kin ga a yadda ya din ga kallona, na kasa gane wane irin kallo yake yi mini"
Ta kashingiɗe kanta tana gwadawa Sumayya irin kallon da yake yi mata.
"Wallahi sumayya ban taɓa ganin ido mai ban tsoron nasa ba, kin ji muryarsa, daga cikin ƙirjinsa yake fitar da ita, abun tsoro, ya ci sunansa viper".
Wayar sumayya ta fara vibrating, ta tashi tsaye ta ce "Ina zuwa"
Ta fita waje ta ɗaga wayar ta ce "Ya aka yi kuma?"
"Idan har ba ta haɗu da shi ba, meye dalilinta na gaya miki ta haɗu da shi?"
Kamar sumayya za ta yi kuka ta ce "Yayanta ɗan sanda ne, na gaya muku, a bakinsa da kafafen watsa labarai kawai take jin sunansa" katse wayar aka yi, ba tare da an sake ce mata komai ba.
Ta koma ɗakin da Nabila take, sai dai abun mamaki taga Nabilan kamar matacciya.
Da sauri ta ƙarasa ta taɓa ta, ta ga bacci kawai take yi, daga fitarta zuwa yanzu bai ci ace har ta yi wannan baccin ba.
Message aka turo mata "Idan ki ka bamu bayanin da yake saɓanin gaskiya, abun zai wuce haka, ya zama dole ki bi duk wani umarni da zamu baki, muna bibiyarku daga ke har ita"
Sumayya ta ajiye wayar, ta dafe kanta tana salati.
Tsaye yake ƙyam a kan ƙololuwar dutsen, yana kallon yadda rana ta doshi faɗuwa, gari ya fara duhu sosai, a hankali ya ɗago hannunsa, ya kalli inhaler da take hannunsa, seretide inhaler ya din ga jujjuyata, yana sauke ajiyar zuciya.
"Boss" ya ji muryar Walid a bayansa.
Ya zagaya gabansa ya ce "Ka saukko haka dan Allah, magana nake son mu yi"
"Bana buƙata kowace iri ce"
"Na san na yi maka laifi, amma ka yi haƙuri, zan nemota duk in da take, kuma zan dawo maka da wayarka ina mai baka haƙuri"
Ko motsawa bai yi ba, balle walid ya saka ran zai yi magana, daga bisani ya goya hannayensa a bayansa, ya cigaba da kallon rana.
"Amma me ka ke tunani game da yarinyar nan? Anya babu wani abu a ƙasa da yakamata mu sani?"
A hankali ya juyo, ya dafa kafaɗar Walid, ya matsa da ƙarfi ya ce "Hakan bai dame ni ba, koma wacece, Ma'aruf , madaki, da kuma wannan yarinyar da ka kawo, sai na tabattar da na kashe su gaba ɗaya, ko ta halin ƙaƙa".
"A'a master, mace ce, wataƙila sakata aka yi, dan Allah ka yi haƙuri, zan yi maka bincike a kanta "
"Idan ka kuma gaya mini wannan sunan, zan hankaɗaka daga kan dutsen nan"
Walid ya yi murmushi ya ce "Baka girmama sunan ne viper, idan har ka damu har haka, yakamata ka bawa kanka da lafiyarka kulawa, ta haka ne zaka yi abun da ka ke so, yanzu ka taimaka ka sakar mini kafaɗata, wallahi kamar na karye"
Ƙurawa walid ido yayi, Walid ya sunkuyar da kansa, ya san ya tunzuro zuciyar Viper, sakar masa kafaɗarsa ya wuce shi, ya fara sauka daga kan dutsen.
Har bayan azahar Nabila ba ta farka ba, su kansu ma'aikatan asibitin, sun yi mamakin irin baccin da Nabila take yi.
Hankalin sumayya kuwa yayi mummunan tashi, ganin Nabila ba ta farka ba.
Bayan la'asar sai ga Abba, tare da Salim, wanda ƙani ne ga Nasir.
A ɗakin da Nabila take suka tarar da Sumayya.
Sumayya ta gaishe su, Abba ya amsa ya ce "Sumayya ke ce a wurinta?"
Ta jinjina kai ta ce "Eh Abba"
"Ai ni ce mini tayi, ba wani abun damuwa bane, ana gama yi mata abun da za ayi mata, za ta koma gida, sai da na koma na tarar ba ta dawo ba"
Sumayya ta ce "Eh, ai ta samu bacci ma".
Idonsa ya sauka a kan gefen rigarta, da take a huje ga jini, cikin mamaki ya ce "Ya nake ganin jini a jikinta?"
Da sauri Sumayya ta ce "amm, dama wai faɗuwa suka a adaidaita sahu, shi ne ta ji rauni"
"Amma ni bata gaya mini haka ba ai" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Wata irin miƙa Nabila ta yi, tare da yin salati, duk suka yi kanta suna yi mata sannu.
Suka din ga jera mata sannu, suna yi mata ya jiki.
Sumayya ta kirawo likkta, ya zo ya ƙara duba Nabila, yayi rubuce-rubuce a file ɗin ta, ya sallame ta.
Abba ya din ga yi mata faɗan meyasa ba ta gaya masa ta faɗi a adaidaita sahu ba, ta nunawa likitoci ciwon da ta ji.
Sumayya ta kalleta, suka haɗa ido, sai ta fahimta, dan haka ta ce "Ai ba wani ciwo bane Abba, mu tafi gida na gaji".
"Kin tabattar babu wani abu da yake yi miki ciwo?"
Ta jinjina kai alamar eh, suka fito zuwa motar Abba, suka tafi tare da sumayya, su ajiyeta a gida.
Sumayya ta kalli Nabila ta ce "Wai ya aka yi ɗazu daga fita ta, ki ka fara bacci, kusan awa huɗu ki na bacci?"
Nabila ta ɗan yi shiru tana tunani, ta ce "Wani likita ne ya shigo yayi mini allura"
"Ba Nurse ba, likita da kansa?"
Nabila ta jinjina kai alamar eh, Sumayya ta yi shiru ba ta ce komai ba, a zuciyarta, take jinjina tsagwaron rashin imanin honorable Indabo, kenan idan ba ta yi abun da suke so ba, za su kashe Nabila kenan.
Gabanta ya faɗi, ta kalli Nabila da ta kashingiɗa, tana ta lumshe ido, alamar baccin bai isheta ba.
Tunani take da wa zata tattauna wannan maganar ne? ko wurin hukuma ta kai, ba ta da shaida ta zahiri, kuma ta san babu wani mataki da za a iya ɗauka a kai.
***
Yana kwance a kan gadonsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 121