Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
96 / 121
da take so, a kan cin zarafin da aka yi musu, ya fi komai baƙanta mata rai, da ta tuno hakan sai ta ji ranta ya ƙara ɓaci. Alhaji mu'azzam ne ya je gidan, duba su ramma, su ka gaisa. Ya ce "Hajiya ku yi mini uzuri fa, ayyukan ne da yawa sosai sai godiyar Allah, kwana biyu ban samu na leƙo ku ba" Maman ramma ta ce "Wallahi babu komai Alhaji, ai muke da godiya Ubangiji Allah ya ƙara arziki ya sanya a fi haka" Ya ce "Amin, mun yi magana da Nabila ta ce babu wata matsala, amma ya na ga rahaman kamar a cikin damuwa ne?" "A'a babu komai, kawai dai ba ta jin daɗi ne" "An je asibiti ne?" "Eh lafiya lau". Ya ce "To Alhamdilillah ai Nabila ma ta ce mini ta na hanya, ina son jin ya ake ciki, zuwa yanzu yakamata ace ai an fara shari'ar, tuni a tura shi prison" gaban ramma ya faɗi, duk yadda ta so ta takura zuciyarta ta ji ta tsani Abdul a yanzu kasawa take yi, tausayinsa ya kanannaɗe mata zuciya baki ɗaya. Ba a jima ba sai ga Nabila ta iso, Ramma na ganin Nabila ta ji farinciki ya mamayeta, saboda itakaɗai ce take fahimtar ta, take lallaɓata ba tare da ta ƙosa ko ta hantareta ba. Duk su ka gaggaisa, Alhaji mu'azzam ya ce "Barrister ya ake ciki ne? An ce an ɗauki statement da komai, me ake jira ba a gurfanar da shi a gaban shari'a ba?" Nabila ta ce "Eh na je na tuntuɓa, ina ta bibiyar lamarin shi Abdul ɗin ba shi da lafiya sosai, haryanzu ya na fama, ya na kwance a asibiti ma, ya na karɓar treatment. Duk ina son na je na duba shi, dan na tabattar" "Yakamata, ki je da kanki, kar ayi wata cuwa-cuwar ko kuma ƙarya yake yi" "A'a ba ƙarya yake yi ba, ba shi da cikakkiyar lafiya dama" sai kuma ta yi saurin tsuke bakinta, ganin duk sun waiwayo su na kallonta, musamman mama da ta galla mata wata uwar harara. Kankarofi ya ce "Too, ikon Allah me yake damunsa haka?" Ta ɗan saci kallon mama, jiki a sanyaye ta ce "Ciwon ciki ne mai zafi" Ya ce "To Allah ya bashi lafiya, ayi Shari'ar nan, a ƙwatar miki hakkinki da ke da mahaifiyarki" Nabila ta juya harshe zuwa turanci, ta ce "Yallaɓai, ina tsoron yin shari'ar nan yarinyar nan ta bamu kunya, wallahi ta na son mijinta, daga ita har shi su na son junansu" Waro ido ya yi ya kalli Nabila ya ce "Haba dai?" "Ka ga abin da su ka yi a station kuwa? Ga mutuminka ya ɗauki zafi a kan lamarin nan, ka san fansa yake so ko ta halin ƙaƙa, a zuciye yake da su, nayi-nayi ya ƙi fahimta, ka san ba ta da wani tsayayye yanzu idan ba shi ba, ya kafe ya dage, dan kamar zai daketa, ga ciki kuma na rasa yadda zan ɓullowa lamarin nan" Kankarofi ya jinjina kai ya ce "Lallai akwai ƙura, to dama ni nawa support ne, na yi supporting ɗin ku, financially na baku security, decision kuma wannan naku ne, Ubangiji Allah ya bayar da sa'a duk abin da ku ka yanke, ni dai-dai ne a wurina" Nabila ta ce "Shikenan, hakan ma mu na matuƙar godiya, Allah ya saka da alkhairi ya sanya a fi haka" Ya amsa da "Amin Barrister, ai aikinki ya na kyau Ubangiji ya ƙaro mana irinku a cikin al'umma, kin sake komawa wurin mahaifinki kuwa, na je masa sau ɗaya, haryanzu ina jin nauyinsa ne abin da nayi". "Kar ka damu, ai ba mutum ne mai damuwa ba, iyaka idan ka na buƙatar ya dawo maka da matarka ne shikenan, sai na tayaka biko" ya ɗago ya kalli Nabila ya yi shiru, sai kuma ya miƙe ya tashi ya yi musu sallama. Nabila ta ce "Rahama, ki na cin abinci kuwa duk kin rame" Maman tayi caraf ta ce "Ina fa za ta ci, ta ɗauki soyayyar ɗa namiji ta saka a zuciyarta, ba ta tausayina ba ta kallon a masifar da ya saka mu a ciki wata da watanni ina yawon yadda za ayi na ganta, hankalina a tashe" A marairaice ramma ta ce "Mama ya ce nemanki yayi ya rasa, shiyasa bai dawo da ni ba, saboda za a iya kashe ni, dan a kare shi kuma wallahi ni ba soyayyarsa na saka a raina ba, a kan me zan so wanda ya keta mini haddi" "Rufe mini baki, ko na zaune ki, soyayyata ki ka saka a ranki ai ko? Tun safe yanzu sha ɗaya na safe, ba ki fito kin nemi abin karya ba, ki na kwance ki na tunani" Nabila ta katse hirar da"ba zai yiwu ba, tashi mu je ki dafa abinci da hannunki, mu fita shan iska, kya samu ki huta ke ma" Ta saka ramma a gaba, su ka shiga kitchen, ta ce mata ita ba ta son ko ƙamshin abinci, ita ba za ta iya cin komai ba". Nabila ta ce "Dubiya za mu je, mijinki ya ce lallai ya na son ganinki, idan kuma ba kya so shikenan" ai babu shiri ramma ta zage, ba tare da ta san tayi hakan ba, ta yi girki, zuwa azahar su ka yi salla, Nabila ta ɗauke ta su ka fice. Har asibitin da Abdul yake su ka je, jami'an tsaro na ƙofar wurin a tsaye. Nabila su ka shiga tare da ramma, ƙirjinta sai dukan uku-uku yake yi. Shi da wani su ka tarar da shi, su ka gaisa da mai jinyar wato Salim wanda abokinsa ne kuma ɗan uwa dan su na da alaƙa, Nabila ta ce "Lauya ce ni, ko za ka iya bamu wuri for some moment" ya ƙarewa Nabila kallo, ya ce "Na gane ki ai" daga haka ya tashi ya fice. Abdul ya na kwance, ya na bacci, ya na sanye da wando 3quater da vest, fuskar nan ta yi fayau saboda ciwo. Ramma har tsuma take yi, ta na bin sa da ido. Nabila ta ce "Bari na je waje na jira ku" ta fice daga ɗakin ita ma. Kamar jira take Nabila ta fita, ta ƙarasa da hanzari ta saka hannu ta riƙe hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ta ɗan jijjiga shi ta ce "Doctor, Abdul tashi ni ce" a hankali ya juyo, ya buɗe ido, da sauri ya kalli ɗakin ya kalleta ya ce "Rahama, ke ce ya aka yi ki ka zo nan?" "Anty Nabila ce ta kawo ni" "Wannan lauyar ta ki?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Abdul ya ce "Ai na ga kamar ta na da tausayi, ba kamar wannan mai zamanin ba mara imani" Ramma ta ce "Yayana ne fa, shi kuma yar uwar matarsa ce, yan biyunta ce" "Ke ma kin san ba shi da kirki, ko tausayinmu ba ya ji, am missing you sweetheart" yayi maganar yana janyota jikinsa. Luf ta kwanta a ƙirjinsa, ta ce "Ya jikin naka?" "Wallahi ba zan ɓoye miki ba, babu sauƙi, ni kawai a kaini kotun, idan a can prison ɗin zan mutu shikenan, idan ina da rabon na rayu, gara ayi a kai ni na fara lissafin shekarun da zan yi" Cikin rauni ta ɗago ta kalleshi ta ce "Dan Allah ka daina cewa zaka mutun nan, idan ka tafi binka zan yi, ko bacci ba na iya yi, na rasa abin da yake yi mini daɗi" "Dan Allah da gaske rahama? Ki na so na kenan? Wallahi ciwon nan nawa har da damuwa, hepatic tuberculosis  ke damuna, TB ta kama mini hanta, ikon Allah ne kawai zai saka na rayu, saboda shaye-shayen da na yi ne na san ya haddasa mini hakan" Ramma ta ce "Zaka rayu in sha Allah, ka daina irin wannan maganar, ka na karya mini zuciya" tayi maganar tana hawaye. Ya tallafi fuskarta, ya ce "Rahama dan Allah kan na mutu ki ce ki na so na, ko sau ɗaya ne" "Wai ba zaka daina zancen mutuwar nan ba, wallahi zan daina zuwa idan za ka din ga wannan maganar" Ya ce "To na daina" Ta goge hawayenta ta ce "Ga abinci na kawo maka, ai za ka ci ko?" "Ba na iya cin abinci, amma tun da ke ki ka kawo, dolena na ci ai, your excellency rahama Abdul yasar" Murmushi ta yi, ta ɗaukko flask, ta zauna a kusa da shi, ta fara ɗebowa ta na kai wa bakinsa. Ci yake yi ya na kallonta, ba zai iya misalta abin da yake ji a kanta ba, na soyayya. Hannu ya saka ita ma ya na bata, sai su ka so manta halin da suke ciki. Ta gama, ta raka shi banɗaki, ya yi alwala, ya dawo ya zauna ya tayar da salla. Duk abin nan Nabila na zaune ta na danna waya, ta yi shiru ta na kallon ƙofar ɗakin, da alama ma sun manta da ita ne a wajen, ta jinjina kai lallai mata da miji sai Allah. Ban da Abdul ya na da gata, ya za ayi ma a kawo shi wannan asibitin jinya, kamar ma ba wanda ake tsare da shi ba. Nabila na ɗaga kai ta hango babar Abdul na tahowa, tare da security ɗin ta, hannunsu da fulasai. Abdul kuwa bayan ta gama ba shi abinci, sai ya marairaice wai dan Allah ta yi masa wanka, wai da kansa yake yi, baya bari kowa yayi masa, kuma idan yayi baya fita. Ya lallaɓata da daɗin baki, ta saɓa hijjabinta, su ka tafi toilet. Maman Abdul na zuwa Nabila ta tashi, ta ce "Sannu da zuwa, bari ayi musu knocking tukuna, ya na da baƙuwa ne" kallon banza ta yi wa Nabila, kawai ta buɗe ƙofar ɗakin. Abdul ya na kwance ruf da ciki, ta yi masa wanka, ta na shafa masa man zafi a bayansa. Tashi ta yi cikin tashin hankali, ramma ta ja da baya, ta na zazzaro ido, tare da ƙoƙarin sanya hijjabinta. "Me zan gani haka, wannan matsiyaciyar yarinyar har asibiti me ki ke yi a nan, ke wace irin 'yar isaka ce ne?" Abdul ya ce "Mummy ba 'yar iska ba ce, mata ta ce fa" "Rufe mini baki ko na ɗauke ka da mari" Nabila ta ce "Hajiya, ba ramma ce ta kawo kanta ba, shi ya nemi ya ganta ta hanyar lauyansa, su ka roƙi alfarma na kawota, amma ba 'yar iska ba ce" "Rufe mini baki, banda munafunci, kun haɗa baki a kan lallai sun kun kassara mini iyali, kun dage sai kun kulle mini ɗa, kuma saboda iskanci kin kawota ta na yi masa karuwanci, ƴar ƙanƙanuwa da ke kin iya bariki" "Mummy dan Allah ki daina aibata mini mata, wane irin karuwanci fisabilillahi. Ni fa ina buƙatar matata a kusa da ni" Ta ƙarewa ramma kallo, ciki ne a jikinta ya fara tasawa. "Me nake gani a jikinta kamar ciki ma? Amma dai ba na ka bane ko?" Abdul cikin damuwa ya ce "Dan Allah Mummy ki daina aibata mini mata, ba dan ni ba, ina son matata, idan laifi ne na yi musu laifi, dan Allah ki daina aibata mini ita, ina jin zafi sosai" galala ta buɗe baki ta na kallon Abdul. Nabila ta ƙarasa ta danƙo hannun Rahama, ta ce "Zo mu tafi" Riƙeta Abdul ya yi, ya na yi mata magana ƙasa-ƙasa. "Na gode sosai da sosai your excellency tun da aka kama ni, ina cikin baƙin ciki da damuwa, amma na yi farinciki sosai da sosai, na gode rahama. Allah ya saka da mafificin alkhairi, ki cigaba da yi mana addu'a" Jan shi mahaifiyarsa take yi, amma ya yi ƙam da rahama, ya na yi mata magana a kunne. Jinjina masa kai kawai take yi, idanunta na cika da hawaye. Hankaɗe ramma ta yi ta na ce mata munafuka, Nabila ta riƙe ta, ta kalli maman Abdul ta ce "Ki bi a hankali, wannan zafafa ƙiyayyar ba naki ba ne ba, rayuwar ɗanki na hannun Allah ta na da alaƙa kuma da Rahama, duk wannan fusatat da ki ke yi akwai rabo a tsakanin su, gara ki kwantar da murya ki lallaɓata da iyayenta, dan wannan abun da yake yi a kanta, ba soyayya ce kawai ba jarrabawa ce". "Wallahi ƙarya na bi matsiyata yan ƙauye ina roƙonsu, shi ma asiri su ka yi masa" Nabila ta ce "Idan ke ba ki bi su ba, shi gashi ya lalace ai a kan yar ƙauyen" "Ke ki iya bakinki ko na kifa miki mari, na saka ayi dukan tsiya" "Barrister ce ni, tsaf hakan zai saka ke ma a yanka miki tikitin tafiya in da mijinki da ɗanki ke shirin tafiya". Ramma kuka kawai take yi, Abdul kuwa ya kasa magana, sam bai ji haushin abin da aka yi wa mummyn ba, shi matarsa ce kawai damuwarsa. Nabila su na tafe a hanya, ta ce "Rahama za ki iya yafe wa Abdul yasar?" Ramma ta kalli Nabila amma ta yi shiru. "Ki na son mijinki ko?" Still shirun ta yi ta na wasa da yatsunta. "Ki gaya mini masalaha nake son a nemo" "Ba na son shi, kawai tausayi yake bani" Nabila ta yi murmushi ta ce "Rahama kenan, menene son menene tausayin, ki na tsoron abin da zai biyo bayan amsar da zaki bani ne kawai. Abin da ki ke so dole shi za ayi, idan ki na son mijinki, ki gaya mini a nema masa sassauci ko ma ki yafe masa, ku yi rayuwar aurenku, na san yadda zan ji da Mama da Vi" Ramma dai ta yi shiru, ba ta iya cewa uffan ba. Tunani ta tsunduma, yadda suka kasance tare yau tare da Abdul, "Dan Allah rahama kar ki bawa kowa zuciyarki har na fito, zuciyarki tawa ce nikaɗai" "Ba zaka yi shiru ba, sai na saka maka sabulun nan a baki, da kyar ka ke magana sai haki ka ke yi" Ya marairaice ya ce "Dan Allah ki bar mini zuciyarki" "Nawa zaka saya?" Yayi murmushi ya ce "Ai darajar zuciya, ba a iya musayarta da komai, sai zuciya 'yar uwatta" "Ji yadda ka ke magana, kamar a film juya ko na zuba maka dundu ni" Ya lumshe ido ya ce "Dundun ƙauna ne" murmushi ne ya suɓucewa ramma, ba tare da ta shirya ba, Nabila kawai ta kalle ta, ta girgiza kanta. A falo su ka tarar da Viper, fuskarsa babu rahama babu annuri, tuni Ramma ta tsure, Nabila kuwa ta sha jinin jikinta. Cikin dakewa ta ce "Vi sannu da zuwa, dama zaka biyo nan ne? Na zata tafiya kawai ka yi" Miƙewa ya yi tsaye ya ce "Daga ina ku ke?" "Amm...mm" ganin ta na neman ƙaryar da za ta yi masa ta kare kanta, ya sanya shi ɗago mata wayarsa. "Duk in da ki ka je ina gani, kuma na jira Emanuel, ya gaya mini in da ya kai ku, Me ki ke shirin yi ne, me ki ke shirin aikatawa? Are you human being, kamar ba mace ba? Idan ita ba ta da hankali ke fa? Dan me za ki ɗauke ta ki kaita wurin wannan ɗan iskan yaron? Me ki ke shirin aikatawa ne? Yadda da na yi da ke ya sanya nake jin za ki iya ragamar komai yadda ya dace, amma na rasa in da ki ka dosa. Ko ke ma kin sauya layi daga in da na sanki, ta kanki su ka biyo kenan saboda case ɗin ya sha ruwa? Rahama ba za ta taɓa zama da wannan yaron ba, kuma dole a hukunta shi" Maman rahama ta ce "A'a Aminu, a bi komai a hankali, ta na ƙoƙari ai" Nabila ta kalli ramma ta ce "Jeki abinki rahama, Allah ya huta gajiya" Ta kalli Viper ta ce "I so much respect humanity, yardar da ka bani, yanzu babu ita ka na doubting a kaina, saboda kawai na kai rahama wurin mijinta. Idonka ya rufe fansa ka ke so ko ta halin ƙaƙa shiyasa ka ke son sai an hukunta Abdul da laifin da ya yi da wanda ba na sa ba. Hukuntaka da aka yi da laifin da ba naka ba ya sanya na tsaya kai da fata, tun ban san ina da alaƙa da kai ba, a kan ƙwato maka hakkinka. Ko hukunci za ayi, iya laifin da Abdul ya yi kawai za a hukunta shi da shi. Ina rashin karɓarka da al'umma su ka ƙi yi a lokacin da ka ke buƙatar su, shi ne musababbin sake shigarka mawuyacin hali? Da na ƙyamace ka, ko na gujeka da a wani stage ka ke yanzu? Kar ka manta har yinƙurin kashe ni ka yi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, an nemi rayuwata wuri daban daban saboda kai, amma hakan bai sanya na haƙura na ƙyaleka ba. Kar ka manta a yadda ka ke, aka ɗauki auren 'ya aka baka, shikenan mutum ba zai yi kuskure ya tuba a karɓe shi ba, sai a ɗauki laifin nasa kawai a saka a gaba. Zunzurutun kuɗi miliyan nawa ya kashe a garinku, kuɗin da a sanadinsu, ubansa ya na can ya na fuskantar tuhuma, ya biya kuɗin makarantar ramma har jami'a, kuɗin rainon cikinta da abin da za ta haifa, hatta kuɗin kula da al'amuransu na yau da kullum ya bayar, duk dan ya wanke laifin sa,ni da ku mun san banda ƙaddara rahama ba ta isa zuwa in da Abdul yake ba, son da yake yi mata jarrabwa ce kawai. Ban da an tsaya mana mu ma, Abdul  ya na da gatan da za a iya sakinsa, kawai dan mun samu manya sun shiga abin ne, amma ya zaɓi a hukunta shi, muddin rahama za ta yafe masa. Mama ke ma fa uwa ce, kuma Allah ya taɓa Jarabtar ɗanki da kauce hanya, ke ki ka zaɓa masa zama hakan? Duk da yanayin abin da ya faru, da Abdul sakaci da tarbiyyarsa ne, amma za a iya kamanta rahama da jauhar, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce ka yi sanadin shiriyar mutum ɗaya, ya fi a baka jajayen raƙuma guda ɗari. Ba mu san me Allah ya ɓoye a lamarin nan ba, ga juna biyu a tare da ita, ku na nan ta yi masa alƙawarin ya je ya gama prison ya dawo ta na jiransa. Duk wannan abun fa zai iya yiwuwa wata jarrabawar ce daga Allah muma yake yi mana, Abdul fa bawansa ne shi ma, kuma ya na kishin abin sa, ci gaba da jansa dan Allah ya ara mana dama ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Amma ina mai neman afuwar ku, ba ina nufin shari'ar Abdul ta sha ruwa ba ne, sam sonake ayi tunanin mafita. Yallaɓai Al'amin, Allah ya baka haƙuri ni babu wanda ya bani wani cin hanci, ba kuma ƙoƙarin cin amanarka nake yi ba. Zan yi iya yi na Abdul zai je prison in sha Allah, muddin hakan zai samar muku da nutsuwa" ta ƙarasa maganar a nutse, ta ja da baya ta fice. Ramma ta na tsaye ta na ji, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta fashe da kuka, ganin yadda ta ja aka ɓatawa Nabila rai. Sojan da yake ba wa Nabila kariya, ya bi ta ya na yi mata magana, amma ta share shi, a ranta ta ce "Tsohon munafiki kawai" Napep ta tara, ta nufi gidan Abba. Maman ramma na shirin yin magana, Viper ya rigata, ya ce bari ya tafi. A ɗaki ta iske ramma, ta yi mata ta tas, ta ce "Ramma ba kya tausayina, ɗa na ya rasa ransa a banza, a gabanki yaron nan saboda rashin tarbiyya, ni kaina so yayi da ya haike mini, amma yanzu kin fifita shi a kaina, na gode rahama" Tabbas da zuciya za ta yi mata adalci, to da ba ta fara ƙaunar Abdul ba, amma ita haryanzu ta fi yarda tausayin sa take ji, ya ake so ta yi da rayuwarta ne. Viper na fita, sojan ya fara gaya masa tafiya ta yi, ya ce ya rabu da ita, su tafi kawai. Da daddare Viper ya din ga kiran wayar Nabila, amma ta ƙi ɗagawa, hakan ya tabattar masa da ta yi fushi ne. Gidan major babu wanda ya kulata, babu wanda ta kula sai baba uwani, ta shirya ta tafi gidansu sumayya, sun daɗe su na tattaunawa, ta na yi mata nasiha da ba ta ƙwarin gwiwa. **** Monday morning 9:30a.m Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun kallo. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau. Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate ɗin shigowa harabar kotun. Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun. A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat. Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa. "Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kai ne abun dogarona, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari. A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta. Ayshercool 08081012143 91 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne. 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Sannu a hankali ta ke ƙoƙarin shiga cikin kotun, "Nabila" ta jiyo muryar sumayya a bayanta. Ta waiwaya, sumayya ta ƙaraso ta ce "Ya aka yi ki ka riga ni zuwa?" "Oho miki dai" Sumayya ta yi murmushi ta ce "Best of luck my dear, Allah ya ba da sa'a" Nabila ta ce "Amin sumayya, amma a tsorace nake, wannan shi ne trial mafi haɗari da nake tunanin zan fuskanta a rayuwata" Sumayya ta ce "Haba mutuniyar, tsoro ba naki ba ne ba, ke jaruma ce i trust you dear, mu je kawai" Su ka ƙarasa su ka shiga cikin kotun. Su na nan zaune, Alhaji mu'azzam ya shigo, barrister Habib ma ya ƙaraso, sai ga murtala, su liti da Walid, cikin mamaki sai ga Nasir ma duk a cikin kotun daga baya sai ga mai gayya mai aikin shi ma ya iso kotun. Ƙirjin Nabila na ta bugawa, amma ta tsananta maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, la haula wala ƙuwwata illa billah" Ana ta gabatar da shari'oi, aka kira ƙarar su Nabila. Tashi ta yi cikin nutsuwa, ta fita gaban shari'a. Ta tsaya ta gabatar da kanta a da cikakken sunanta, da kuma wanda take karewa. Lauyan da yake kare lakwari, ya fito ya gabatar da kansa, da wanda yake karewa. Nabila ta nemi a karantowa masu laifi, laifin da ake tuhumar su da shi, a nan ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya karantowa lakwari laifin da ake tuhumar sa da shi, da Madaki, duk da madaki ya na gadon asibiti ya na jinya. Aka karanto tuhumar da turanci, cewar ana zarginsu da shiga cikin gidan Aminu Viper, su ka kashe mata da ɗan da kuma ɗan yake cikinta. Kotu ta waiwayi lakwari domin jin ta bakinsa, bayan an fassara masa ƙusnhin tuhumar da ake yi masa, cikin harshen hausa. A nan take lakwari ya musanta zargin, kamar yadda ya musanta a wurin 'yan sanda, da kuma yadda lauyansa ya jaddada masa kafin zuwan su kotu, domin kuwa ba ƙaramin kuɗi aka ba wa lauyoyi ba, a kan su yi duk mai yiwuwa ayi ta jan Shari'ar har ta lalace. Daga haka kotu ta ɗaga cigaba da shari'ar, zuwa sati biyu domin bayyanar shaidun kowanne bangare. Viper daga in da yake zaune, lakwari kawai yake kallo, ko ƙiftawa ba ya yi, zuciyarsa na raya masa kawai ya kashe shi ya huta, yanzu da haka za ayi ta jan ƙafa a shari'ar nan a ɗauki dogon lokaci ba a kammalata ba? Zuciyar sa azalzalarsa kawai take yi, ya na jin tamkar ba zai iya jira ba. Ya na kallon lakwari, taswirar abin da ya faru a daren da jauhar ta mutu, na ƙara dawo masa a cikin ƙwaƙwalwarsa, yadda ya kasa kataɓus, ya na ji ya na kallonta ta na miƙo masa hannu. Knasa ne ya yi wata irin sarawa, ya tashi

Chapter 96 of 121