Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
24 / 121
nan ma ya zo yana yi musu shaye-shaye kar ya ɓata musu yaran unguwa. Suka yi suka gama, yayi shiru kamar mai zancen zuci, suka yi suka gama, D.P.O ya ce "Malam Aminu, ka ji abun da mutanen unguwar da ka tare suka ce, me za ka ce?" Sai da ya ja wasu seconds, sannan ya ɗaga kai, ya kalle su da jajayen idanunsa masu matuƙar kwarjini, duk suka yi shiru, suna sauraren sa, ya ce "Haryanzu ban ji an ce ga abun da na yi ba ai. Ba zan ce komai yanzu ba, gobe in Allah ya kaimu, mu haɗu a nan ƙarfe huɗu na yamma, zan faɗi abun da na yanke". D.P.O ya ce "Ina fatan ba wata ɓarnar zaka yi ba?" "Ba na sara sai an zo ramina" daga haka bai kuma cewa komai ba, ya tashi ya fice, ba tare da ya jira iznin hakan ba. D.P.O ya ce "Abun da nake so da ku shi ne, ku bi yaron nan a sannu a samu maslaha, kar ku yi wani abu da zai tunzura shi, ya fara yi muku fitina a unguwa, ku bari mu bi a hankali mu sasanta, ɗan ƙasa ne yana da damar zama a in da yake so, ku bi a hankali ayi musu sulhu". Shi kuwa yana fita, ya kira wayar liti, bugu biyu ya ɗaga. "Liti, nan da mintuna arba'in zuwa awa ɗaya, ina son ka tattara mini, duk wasu yara marasa ji a arear unguwar nan da nake da kewayenta, duk wanda ya yi gardama, ayi masa ɗaurin igiya da swizaland gaba da baya, a layin gidana nake son su taru". Liti ya amsa da "An gama shugaba" Sahura kuwa, sai da ta je har gidan maman halimatu ta ƙare mata cin mutunci, a kan yadda Al'amin ya je har gida, ya ƙare mata tanadi, a kan ta sai kayan matarsa, maman halimatu ta din ga ba ta haƙuri, ta ce su shiga gidansa su yi magana da jauhar ɗin, amma ta ce ai ba mahaukaciya ba ce ita, da zata shigar masa gida ya ritsata ya kashe. Jauhar tana ta aikin stone, ta ji ana wata irin busa a unguwar, kamar da ƙaho ake yin busar, irin bushe-bushen da aka din ga yi, ranar ɗaurin aurenta, dan haka gabanta ya faɗi ta shiga cikin tsoro. Sannu a hankali, hayaniya ta fara cika layin nasu, da surutan matasa, ɗaki ta gudu ta rufe ƙofar falo, dan tunani ta fara yi, ko yaran madaki ne, gashi ba waya ce da ita ba, balle ta kira Al'amin Kafin ya ƙarasa layin gidan, liti ya kira shi a waya, ya sanar masa sun fara taruwa matasan, dan haka bai bi ta cikin ba ya bi ta baya. Jifff! Ta ji dirar abu a tsakar gida, ta katanga ya diro gidan, ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon, amma a rufe ya jijjiga ya jijjiga amma ya ji a rufe. Ya shiga bugun ƙofar kamar yaƙi, ƙulewa tayi a ɗaki, ta hau addu'a, tare da tunanin ta ta ta ƙare, yaran madaki sun zo neman Al'amin, ko sun zo sassarata. "Ke malama ki zo ki buɗe mini ƙofa" sai da ta ji muryarsa, sannan ta fito ta buɗe, ta kalle shi, ta leƙa tsakar gida ta ce "Ai ban san kai ba ne, biyoka aka yi ne?" Wani irin kallo ya yi mata, ya ce "Matsa ki bani wuri" ta matsa ta bi bayansa tana surutu "Master ka daina dirowa ta katanga dan Allah, gaba ɗaya na tsorata wallahi, na zata madaki ne, suka zo nemanka na ji sai busa ake yi ga warin kayan shaye-shaye...... Haɗiye maganar tayi, da ya waiwayo yana yi mata kallon warning. Ta ce "Yi haƙuri, ka ga abokanka sun dawo da carfet ɗin, wai wanke shi suka yi, amma dai yakamata na je na bawa dillaliyar nan haƙuri, ai ka ga an shiga hakkinta, har gida ta zo tayi wa maman halimatu masifar abun da ka yi" ɗakinsa ya shiga, ya kulle ƙofar ya saka sakata ya bar ta a bakin ƙofa. Sai abun ya bata dariya, kafin awa ɗaya matasan nan sun kusa cika layin nan, sai hayaniya suke yi. Malam lawan kuwa, a waya matarsa ta kira shi, ta ce kar ya kuskura ya dawo yanzu, 'yan daba sun cika layin nan. Jauhar na ɗakinta, tana aikinta, ta ji yana buɗe gate, a razane ta fito saboda yanayin bushe-bushen da ake yi, ya tabattar mata da akwai matsala. Yana fita wurin yayi tsit, kamar ba su ne suke hayaniya ba da. "Sai da kai sarki, ƙaramin dodo magajin babban, ko ma in ce ka ɗara shi. Mu na yi maka maraba da zuwa wannan unguwar, mun fito ƙwanmu da kwarkwata domin yi maka mubayi'a". Cewar guduma yana geɓare baki, yanayin yadda yake maganar kawai a buge yake. Viper ya goya hannunsa a bayansa, ya ce "Manyanku sun kai ƙarata a kan yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ni da ku zan yi wannan yarjejeniya. Abu goma a cire bakwai a tara da ɗaya zan gaya muku, a bi iyaye, ayi caji kaɗan saboda lafiyar jiki da ƙwaƙwalwa, a kiyayi taɓa kayan wani. Babu zubar jini a tsakanin ku, ko duk wani wanda yake unguwar nan, abu na ƙarshe mafi muhimmanci da fari salin alin na so zama a unguwar nan, wataƙila na ɗan lokaci na baku wuri, amma tun da abun ya zo da haka, sarki biyu ba zai yi sarauta a zamani ɗaya ba. Ko dai mutum ya yi mubayi'a ko ya bar unguwar nan. Kar kuma a kuskura a matsi ramina idan ba haka ba, zan yi ɓarna. Mu haɗu da shugabannin dabar Unguwar nan da kewayenta gobe a station ɗin unguwar nan, domin yarjejeniyar zaman lafiya. Kuna iya samfewa" Su ka din ga yi masa kirari, yana jin kansa yana sake fashewa. Bayan sun watse, maman halimatu ta shigo, tana ba ta labarin abun da sahura ta zo ta yi mata. Jauhar ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri maman halimatu, dan Allah ki bata haƙuri, ba yadda zan yi, na so mayar mata ma da kayan, ya ce idan na sake sayar da wani abu, zai ɓata mini rai. Wallahi yana ankare da komai, ko cokali na sayar zai gane, ni har tsoro yake bani, bari na baki dubu goma a kuɗin, ki kai mata ta ƙara ki bata haƙuri dan Allah" Maman halimatu ta ce "To shikenan, Allah ya kyauta" ta bata dubu goma ta kaiwa dillaliya, ita kuma ta bata kyautar dubu biyu, sauran kuɗin kuma ta ɗan yi musu cefane dan kuwa shi babu ruwansa. Washegari tun ƙarfe biyu, su mai unguwa suka koma police station, suna jaddada dole a kori Al'amin, dan jiya kafin su je gida ya rigasu zuwa, ya tara musu dandazon 'yan daba a unguwa. Al'amin bai je ba, sai ƙarfe huɗu tare da rakiyar su walid, da kuma matasan yara 'yan shaye-shaye da sun kai ashirin da wani abu. D.P.O ya ce "Lafiya, waɗanan fa?" Al'amin ya kalli mai unguwa, ya nuna masa guduma ya ce "Ka san wannan? Ko ba ka bani amsa ba ɗanka ne, meyasa ba ka kore shi daga unguwarka ba? Ko dan shi ɗanka ne?.  A wannan ba wannan matasan wakilai ne da suke jagorantar wasu yaran a ƙarƙashin su, wanda duk a cikin unguwarka suke, kana nufin a sati biyu da zuwana duk ni na lalata su? Har na tare a unguwar nan, ba su san waye ni ba, sai jiya da na saka a tara mini su. Dama can kuna da lallatun yara, harƙallata nake, ba na lalata ɗan kowa, duk ɗan wanda ya lalace, dama lalataccen ne. Ina sake maimaitawa ba na harbi sai an matsi ramina ko in da nake. Ga mafita zan bayar, wadda ba zan ƙara ko rage wani abu daga abun da zan faɗa ba. Mafita biyar ce ba uku, ko dai a haɗa a kore ni, da ni da yaran nan, ko kuma ku yi wa gidana kuɗi ninki uku, yadda zai isheni na sai wanda ya fishi, na bar muku unguwa, idan ba haka ba....... Ba na ƙarasa magana sai dai na aikata. Duk sai suka yi ɗif D.P.O ya ce "Mai unguwa mai ku ka yanke?" Shiru suka yi ba su ce komai ba, D.P.O ya ce "Tashi ka ja zugarka ka tafi, babu wani abu in sha Allah". Ya miƙe ya ce "Galibi yaran nan secondary school drop out ne, wasunsu idan son zuciya ne ya kai su wannan halin, wasun su laifinku ne, ko dai ku nutsu ku gyara rayuwar matasan yaran nan, ko kuma su cigaba da lalacewa kuna rusa al'ummarku da hannunku" yana gama maganar suka fice da shi da su. D.P.O. ya ce "Yaron nan fa ya san abun da yake yi, jiya kuna barin wurin nan, daga can unguwar su, Aka kira ni aka ce a gargaɗe ku, babu ruwanku da shi, yaron 'yan siyasa ne, dan Allah ku lallaɓa ku zauna lafiya da shi. Bayan sun bar station ɗin, wani irin ɓacin rai ya din ga cizon zuciyarsa, a duk lokacin da aka samu matasa ire-iren sa, al'umma ba su da wani burin da ya wuce, yin watsi da shi, da nesanta kansu da ire-iren su, bayan su ne ƙashin bayar lalacewar ta su. Yau abun na sa ya fi na kullum, domin kuwa a buge ya dawowa jauhar, wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, ya wuce ɗakinsa, ba ta kula shi ba ta koma gefe ta zuba masa ido. Washegari da safe shiru bai fito ba, ta leƙa ɗakinsa, ta tarar da shi a kwance yana bacci, gefensa ga kwalin ashana da na taba, ga kwalabe. Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, a hankali ta fara magana "Sun san da haka suka aura mini kai, Allah na roƙi ka bani mafita ka zaɓa mini shi, Allah ka kawo mini mafita, Allah ka shirya mini shi, Allah shiriya taka ce, Ni da shi duk bayinka ne, Allah bai gagari ikonka ba, Allah ka shirya min mijina. Allah ka sa ya daina abun da yake yi, Allah kar ka sa ya mutu yana saɓa maka" ta yi maganar tana kuka. A hankali ya yi juyi, satchets ɗin ƙwayoyi, suka zubo daga aljihun gaban rigarsa, ta saka hannu ta kwashe su, da kwalaben, ta hau caje ɗakinsa, duk wani nau'i na abun da ba ta yarda da shi ba, sai da kwashe daga ɗakin. A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa, ita kuma ta fice daga ɗakin. Da ƙyar ya iya tashi, dama bayan sallar asuba, ya sake yin shaye-shayen. A yunwace, ba tare da ko wanke baki yayi ba, ya hau cin abinci, saboda kayan shaye-shayen sun rarake masa ciki, ji yaya ko tsayuwa ba zai iya yi a kan ƙafafuwansa ba, sai da ya gama ci ya dawo dai-dai. Ya shiga banɗaki, ya wanke bakinsa ya fito falo, ko ɗaga jauhar ba ta yi ba, balle ta kalleshi. Ya je gabanta ya miƙa mata hannu. Ta ɗago ta kalleshi. "Bani abun da ki ka caje mini ɗaki ki ka ɗauka" gabanta ne ya faɗi, mutumin da yake bacci ya aka yi ya san ta ɗauka?. "Bani mana" "Na zuba a shara an zubar!" (Yau juma'a mu yawaita salati, ga shugaba Sallallahu alaihi Wasallam) Ayshercool 08081012143 24 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa Arewabooks ayshercool7724 Duk da cikin matsanancin tsoro da tashin hankali ta bashi amsar, amma ta tattaro jarumtarta ta dake, ta ƙi kallonsa. "Ai ɗago kai zaki yi ki kalle ni, ki bani amsar da ki ka faɗa yanzu" Ta yi shiru, tana jiran yayi mata duk abun da zai yi mata. Ya ce "Dama ba ni na kawo ki gidan nan ba, kuma ba ni na ce a kawo ki ba, idan kin gaji ki tafi dama kin isheni, kuma idan ki ka kuma zuwa kaina ki ka tsaya ki na kuka, sai na ɓarar da ke". Gabanta ya faɗi, a buge ta tarar da shi yana bacci, ya aka yi ya san duk abun da ya faru, sai dai kalmarsa ta ƙarshe da ya ce a kawota ba, ta yi mata ciwo. Ta zata zai yi mata tijara, da ta ce ta zubar, sai kuma ta ga ya tashi ya nufi hanyar fita, kawai ta fara kukan da ba ta san na menene ba ma. Waiwayowa ya yi yana kallon ikon Allah, da ta samu bai casata ba, da ta ɗebe masa kaya,ta ce ta watsar kuma ya san ƙarya take yi ba ta zubar ba, shi ne saboda samun wuri har da ɓare baki tana kuka. Sosai yarintarta ta fito, yadda ta tura baki tana kuka, tamkar irin 'ya'yan madarar nan shagwaɓaɓɓu. Kawai ya girgiza kai ya fice, kafin ta fusata shi. Rahila da Zakiyya kuwa sai shewa suke yi, tare da farincikin yadda shawarar da suka yanke ta yi amfani. Zakiyya ta ce "Ni fa na zata yadda yake ɗin nan, ana kaita ya korota tun da ba son auren yake yi ba, amma dama na san ko zai daketa ya cinye abu ne mai wahala ta faɗa ko tayi yaji, juriya ce da ita kamar dutse shegiya". Rahila ta ce "Shi ɗin me? A duniya akwai namijin da zai ce ba ya son mace ne, ke ban da abun makirci wannan yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa, wa zai ce ba ya so, dan ma ƙarama ce, gashi ai sati biyu kenan sun yi luf daga shi har ita". "Wallahi na zata ba zai saurareta ba, ƙila ma ya korota, a yadda ki ke bani labarin yadda ya zama, da kuma rashin jin da yake yi". "Ba fa mahaukaci ba ne, idan ta iya zama da yaron nan, ba lallai ki ji kansu, ai duk wannan bala'in da nake yi da tashin hankali a kansa, wasu lokutan shi da 'yar uwassa yana yi mata abu, ke har magana shahida take gaya mini a kansa" Cikin mamaki zakiyya ta ce "Kai haba dai?" "Wallafa Allah, ba suna school aka yi auren ba, sai da na kusa dukan yarinyar nan, ƙiri-ƙiri wasu lokutan take nuna in daina takurawa ɗan uwanta, aikuwa ubanta nake ci". "Gaskiya kar ki zauna a kanta, ita ana neman mafita tana shirme? Ni kam yanzu menene abun yi ne? Ƴan uwan Alhajin nan fa sun zo, wai ayi aure ayi visa ta bi shi china" Rahila ta ce "Aikuwa sai dai a lahira idan ana zuwa". "Aikuwa, wai yanzu ya fasa dawowa nan da watan ɗayan ba, ina nan dai ina ta lallaɓa uban, a kan ya haɗa shi da hafsa". "Ai ba iya lallaɓa shi ba, malamai zamu cigaba da yi, in sha Allah sai abub nan ya tabatta, ita waccan ai an gama da babinta". Zakiyya ta ce "Haka ne kam, to Ubangiji Allah ya amince, ni dai ko nawa ne zan kashe, idan ta aure shi na san zan mayar da kuɗina". "Kar ki damu ai ba zama, za ayi duk mai yiwuwa, hafsa zata auri mutumin nan". *** "Ku yanzu a ganinku ya dace mu na ji mu na gani, baƙo ya zo unguwarmu ya saka mu yi masa mubayi'a? Baƙo ne fa, mu kuma a nan aka haife mu muka girma, muka kafa sabgar nan, kuma ace sai dai mu bi shi, ba dai ya bi mu ba?" "Wallahi nima dai haka na gani, abun yayi mini ciwo, guduma ya fi kowa bani haushi shege, ai wallahi sai dai a rabu biyu, ayi ta zubar da jini, har sai ya yarda ya bi mu, ba wani shege da zai shigo arearmu ya buɗe mana ido, mu zagaya mu ji ta bakin sauran, mu ji su waye suka bi, kuma suwaye za su yi tawaye". Ɗaya matashin, ya hurar da hayaƙin wiwi ya ce "Mu tabattar da suwaye a tare da mu tukuna, zamu yi masa sara na warning, idan ma ta kama, mu kawar da shi da ga sararin nan, ba wani ɗa da zamu yi wa biyayya, tun da muka yi wa iyayenmu ma tawaye". Suka cigaba da tattaunawa a kan yadda za su ɓullowa lamarin, su yi maganin Al'amin. ***** Kamar masu kasa gyaɗa, haka suka kewaye farantin wiwi, suna naɗawa a takarda. Suka mayar da wata ƙwaya garri, suka haɗata a cikin wiwin, ita ma suka ɗaura ta daban. Matasa ne suka din ga shigowa da ɗai ɗai, suna karɓa, suna zube balance, suna karɓar kaya. Liti ya shigo cikin ɗakin da Al'amin yake, da robar abinci, ya zauna ya ce "Taso ga abinci" Ya tashi zaune ya kalli miyar kan abincin, sai ya ji ƙyanƙyamin abincin, miyar sam ba ta ji mai ba, ga ta ba ta soyu ba, ba irin wadda waccan taɓararriyar yarinyar take bashi ba. Guntun tsaki ya ja, Walid ya ce "Lafiya?". "Na ƙoshi" "Meyasa?" Ya girgiza kai ya ce "Bakomai". "Ka ce mini kawai, abincin amarya zaka je ka ci, wai mu ko sau ɗaya ba zaka kawo mana abincin na ta mu ci ba? Sai dai ka yi ta ci kai kaɗai?". Kai tsaye ya ce "Ba zan kawo ba" "To ka ƙarata, ku ci ku kaɗai, dama ni naga kamar haushina ma take ji, ban san me nayi mata ba". Ya tashi yana fatan Allah ya sa ya je ya tarar ta yi abinci. Sai kuma ya tuna kukan da tayi kan ya fito, ƙila ma ba ta yi girkin ba. Sai dai kafin ya ƙarasa gidan, aka tsuge da ruwan sama, dan haka ruwa yayi masa duka, yayi ta sauri ya ƙarasa gida, ya san ƙarshenta ruwa yau ma ya shigar mata falo. Sai dai yau aka yi sa'a, ruwan bai shiga da yawa ba, sai dai tsakar gidan ya cika da ruwa. Tana ɗakinta tana salla, ya fara cire kayan da suka jiƙe, ta shigo da sallama, sai dai cikin matsanancin hanzari, tayi wani irin burki, ta juya. Shi mamakin ta yake yi, sam ba ta da zuciya ba ta fushi. Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Ina da ruwan zafi a flask, na kawo maka ka yi wanka, sai ka ci abinci kar ka yi mura saboda ruwan da ya dake ka?". "Kawo" sumi-sumi kamar mara gaskiya. Ihunta ya jiyo a tsakar gida, bai san ya aka yi ba, sai ganinsa yayi a tsakar gida, cikin hanzari yana zaton wani abun ne ya sameta, tayi jifa da flask ɗin a gefe, Allah ya sa na silver ne tana ihu, ta maƙale a jikin bango. "Ke menene? Meyafaru?" "Kwaɗo ne, zai riƙe mini ƙafa" Ji yayi kamar ya ƙarasa, ya kwaɗeta, wai kwaɗo take yi wa wannan ihun. "Zaki rufe mini baki ki zo ki wuce, ko sai na zo na tumurmusa ki?" Jauhar ta ce "Tsoro nake ji wallahi" tayi maganar tana ɗagowa, idanunta har sun yi ja. Sai dai mayar da kanta ƙasa tayi, da sauri, tana tsuma saboda babu riga a jikinsa, wani irin gashi ne a jikinsa, tun daga ƙirjinsa har saman cibiyarsa. "Ke ba na son gulma, miƙo mini flsk ɗin, idan ya so ki dauwwama a wurin" Cikin shagwaɓa ta ce "Wallahi da kwaɗo a cikin ruwan nan, tsoronsa nake ji" tayi maganar idanunta na bayyanar da tsantsar tsoro da tashin hankali. Cikin ruwan ya biyo, ya zo ya ɗauki flask ɗin, zai bar kitchen ɗin ya bar ta, ta saka hannu ta riƙe masa wando, tana ihu. Sai yanzu ya leƙa ya ga kwaɗon ne da gaske, amma girmansa ba wani ƙato bane take wannan ihun, shi bai taɓa jin wai ana tsoron kwaɗo ba, sai yau. A ransa ya ce 'Laifin iyayeki ne da suka zaɓa miki wannan rayuwar' Kwaɗo ya tsalla yayi waje, ita kuma jikinta sai rawa yake yi, cike da tsoro. "To ai sai ki cikani, tun da ya tafi ko?" Cikin tsananin jin kunya, ta sake shi, ta koma gefe. "A nan wurin zaki dauwwama kenan?" Ta ce "A'a idan ruwan ya bushe, na wuce, ka duba ɗakina akwai man zafi a kan mudubi, idan ka yi wankan ka ɗan shafa kar ka yi mura, abincinka yana ɗakinka" kallonta yake yi, yana son gane nature ta ce a haka, ko kuma iya shege ne, amma yadda take ƙifta ido a tsorace ya tabattar masa da gaske take. Ba ta yi tsammani ba, ya saka hannu ɗaya ya ɗago ƙugunta, hannunsa ɗaya kuma da flask taku kaɗan yayi, ya direta a tsakiyar falo. Kallonsa take yi da mamaki, shi kuma ya nufi ɗakinsa. Har ɗan tsalle ta yi, dan ta tabattar ta na da nauyi ne, ko ba ta da shi, da ya ɗauke ta kamar wata 'yar teddy. Ta fi mintuna sha biyar tana cigaba da mamakin yadda ya ɗagata kamar a bar banza. Tuwon shinkafa ta yi da miyar taushe, kamar ya cire kunne dan daɗi, ga katifarsa ta saka sabon bedsheet, ɗakin yana ta ƙamshi, amma hakan bai hana shi goge mata hannu a jiki ba, ya gama ya miƙe yana bacci, kayan na sa ma sai ƙamshi suke yi. Leƙawa ta yi ɗakin nasa, ya mimmiƙe a kan katifa, bai saka rigar ba yana bacci ta lallaɓa ta shiga da sanɗa zata kwashe kwanukan. Yanayin garin da sanyi saboda ruwan da aka yi, amma ya takure yana bacci. Ta fitar da kwanukan, ta ɗaukko bargo daga ɗakinta, ta zo zata rufe shi, ɗan ƙura masa ido ta yi. Al'amin ba shi da wata makusa, da yake baccin nan ma he looks very innocent and calm. Kasa rufe shi ta yi, ta tafi tunanin ya aka yi ya fara shaye-shaye, ya aka yi su mama suka samo shi ma, suka aura mata? A ina yake ina ne gidansu? Duk take tambayar kanta. Tashi ya yi zaune kamar aljani ya ce "Meye ne kin zo kin sakani a gaba kina kallona" Zabura ta yi ta ce "Yi haƙuri, na zata bacci ka ke yi, ba kallonka nake yi ba, na ga kamar kana jin sanyi ne, bargo na kawo maka" tayi maganar tana tsuma. Ya miƙa mata hannu, ta bashi bargon, ya ware shi ya lulluɓa, ta fita tana mamakin al'amin idan yayi wani abun mamaki yake bata, har da ajiyar zuciya ta ji yana yi alamun baccinsa yayi nisa, amma kawai ta ganshi a zaune. *** "Allah ya taimaki maigida" "An gaisheka, ya ake ciki?" "Komai normal, ba wani abu" "Yaya za ayi? An kama Ja'afar da kaya, hukumar nan sun ƙi sakinsa, ba zan matsa ba, amma ina buƙatar a musanya shi da wani" "Oga ba zan iya sakinsa kai tsaye ba, amma dole za'a samu wani a kama shi da kayan, sai a saki jafar a kama shi, ka san wannan karon shugaban namu, yana da sanya ido sosai" "Shikenan, ayi abun da yakamata kawai" "Ok sir". Cikin ikon Allah, matar nan tela, tana biyan jauhar, duk da ba wani kuɗin kirki take bata ba, amma tana jin daɗi sosai da sosai, ta sayi katin tara kuɗi, ɗan abun da tayi cefane, sauran sai ta saka a kati, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki. Yaran maƙwabta idan sun shigo, tayi musu tsifa da kitso, babu ko sisin iyayensu. Ta duƙufa tana aikinta, ba ta ji motsinsa ba, sai jefo mata bargo yayi a ka. A razane ta tashi, bargon kuma ya cukuikuyeta. Ya ce "Zaki taka kwaɗo" Ihu ta saka ta samu ta cire bargon da ƙyar, tana dube-dube, yana tsaye yana kallonta, kamar ba shi yayi maganar ba. Ta ce "Ina kwaɗon?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Ta kalli yadda stone ɗin ya zube kamar ta yi kuka ta ce "Kalli yadda ka saka na zubar da kayan sana'ata." Ta durƙusa za ta kwashe, sai kuma ta yi sauri ta hau kan kujera, ta maƙale ƙafafuwanta ta ce "Ina kwaɗon ya shiga ne?" Haryanzu shi dai bai daina mamakin yadda kwaɗo ya zama abun tsoro ba. Hanyar fita ya nufa, ta gane tsokanarta yake yi, nan ta ƙara jinjinawa ƙi faɗinsa, har ya iya ya tsokaneta, amma ya sha kunu ba fara'a. "Master" ta kira shi. Ya tsaya bai waiwayo ba. "Dan Allah idan Allah ya yassare, ka taho da omo, zan yi mana wanki". Yanzu ma bai yi magana ba ya fita, ta naɗe bargonta, ta cigaba da aikinta. Zakiyya kuwa, kamar zata zare, Rahila na ta janta wuraren malamai kala-kala, yadda za su samu, Hafsa ta auri Alhaji mu'azzam da zarar ya dawo. Har sha ɗaya na dare, jauhar na aikin jera stone ɗin ta a kan gadonta, dan tun tana jin tsoron zaman gidan, har ta saba, sai da ta ji bacci yana kama idonta sosai, sannan ta tashi ta ajiye kayan, tayi wanka ta fito tana shirin kwanciya. Ji ta yi ana buɗe ƙofa, dan haka ba ta damu ba, ta san mai gidan ne, sai dai bayan wasu mintuna ta ji kamar yayi jifa da wani abu a falo, yana ta haki mai kama da kakari, gabanta ya faɗi ta fito da sauri, ta

Chapter 24 of 121