Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
119 / 121
yi magana ba, Nabila nata nuƙu-nuƙu da hijjabi, amma sai da Hafsa ta gano ta. "Abla, wai me ki ke ɓoyewa ne? Duk ɓoyonki ana gani ai" Kunya ta kama Nabila ta ce "Ake gane me?" "Ɗan baban mana" Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Ai na gaya mata ana gani, taƙi yadda, mai cewa sai ta yi good 2yrs a gidan miji, kafin ta ɗau ciki, amma farawa da bisimillah" Hafsa ta kwashe da dariya ta ce "Ai kura ta san gidan mai babban sanda, ai ita ta san in da za ta iya cewa, sai ta shekara biyun ba ta haihu ba, ba dai a gidan Viper ba" Nabila ta ce "Baku da aikin yi ne, ulcer ce ta kumbura mini ciki" "Viper dai yayi ajiya, shi ya kumbura miki cikin" Hafsa tayi maganar tana dariya. "Ku da Allah, kuna munafuncin mijina a gabana, wanda idan yana nan, ko tarin kirki ba zaku iya ba, a ƙyale mini shi kar a saka ya ƙware, yana can yana aiki, kuna nan ku na gulmarsa" Hafsa ta ce "Ke abin alkhairi ne ai, Ubangiji Allah ya inganta miki ƙanwata, ya rabaku lafiya" "Amin Anty hafsyna" Sumayya ta ce "Shahida ma na ga kamar an gamu" Hafsa ta ce "Nima ma gani, ai na je gidanta" Nabila tayi dariya ta ce "Mijinta ce mini yayi baya son saka ido mura take yi" suka yi ta hirarsu gwanin sha'awa, hafsa ta ce "Dan Allah ku tayani da addu'a, nima Ubangiji Allah ya sa ina da rabon ganin jinina a duniya, ni haryanzu shiru" suka yi ta kwantar mata da hankali da yi mata fatan alkhairi. Aka koma maganar bikin Sumayya, Hafsa na ta ƙara nanata mata, kar ta kuskura ta je ta sha wani abu da ba ta san menene ba, alhalin ga likitar mata. Nabila ta ce "In dai ki na son daga shiga kema ki ɗaukko magana, ki riƙe wa kayan likitar mata wuta, zaki gane baki da wayo, laulayi is not your mate " Hafsa ta ce "Rabu da ita, ta ji da assignment ɗin da Viper ya bata" Nabila na daga kwance a kan cinyar Sumayya ta ce "Wuta balbal idan aka ƙira sunan mijina" "An faɗa Aminu Viper, mai zamani" "Ku da Allah" Nabila ta dage ta din ga lallaɓa hafsa, sai da ta kira Alhaji mu'azzam, suka kwana a gidan. Ita dai kaf 'ya'yan babansu, da aka nuna mata, babu wanda take jin tana so, kamar hafsa, ita dai tana ƙaunarta sosai. Sai kuma suka koma hirar ƙalubalen rayuwar gidan auren, tare da ba wa junansu shawarwarin da za su fishshe su. Kwana biyun da suka yi mata ta ji daɗi sosai, bayan tafiyarsu zaman kaɗaicin ya ci gaba da damunta. Babu tsammani taga Viper ya dawo, aikuwa ta ji daɗin hakan. "Vi ya na ganka ka dawo yau?" "Shi ne lokacin da aka ce ki fara zuwa awo, ina lissafe ni ai" Tun daga Abuja ya taho mata da amala, saboda ya san tana sonta, aikuwa ta ji daɗin amalar nan. Ta ci kaɗan ta ga tayi awa biyu ba ta yi amanta ba, aikuwa ta rufar mata, ta cinye tas. Kwana tayi amai, ba ta yi baccin kirki ba. Da safe ya buga wa Abdul waya, ya ce masa zai kawo Nabila asibiti, ya ce masa to. Abdul ya yi mamki, ganin cikin Nabila wata huɗu, amma ya ɗago sosai. Suka gaggaisa, ya yi mata sannu. Viper ya ce "Ya ƙanwata?" "Tana gida sun yi hutu, ga saƙo ma ta bani, wai na kawowa yayarta" yayi maganar yana nuna musu fulas ɗin abinci. "Ko menene a ciki, in dai yaji yayi yawa ba zaki ci ba, bar rawar jiki" yayi maganar yana harar Nabila. Tashi Nabila ta yi, ta buɗe flask ɗin, ƙamshin miyar jajjage ya daki hancint, tayi maza ta rufe dan da alama miyar mai yaji ce. Abdul ya ce "Ina ce mata zaku zo, ta zaunar da ni sai na taho miki da abinci" Viper ya ce "Duk in da muka je, har rawar jiki take ace mata ga abinci, kamar ba na ba ta abinci a gida" "Bana ƙoshi ne" tayi maganar tana dariya. Abdul ya ce "Maybe na gidanta ba ta iya ci, idan suna irin wannan halin sai haƙuri ai" Viper ya ce "Haka ne, amma ya na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?" Bai ɓoyewa Viper ba, ya gaya masa komai, Viper ya ce "Irin haka sai haƙuri, kuma ka ci gaba da addu'a, kuma kai ka kiyaye aikata makamantan laifukan da ya aikata" Kalaman Viper dai babu tausayawa ga Indabo, amma rarrashi ne ga Abdul. Ɗakin scanic suka tafi, bayan an yi wa Nabila gwaje-gwajen masu ciki. Viper yana tsaye a kan Nabila, yana riƙe da hannunta. Abdul yake gaya wa Viper, doctor Muktar ya tafi ƙaro karatu malesia. Abdul yana cikin maganar ya yi murmushi, ya kalli Viper ya ce "Congratulations bani goron Albishir" "Albishir ɗin me? Bayan dama can na san da akwai cikin?" Abdul ya ce "Ba zan faɗa ba ne, sai ka bani tukuici" Viper ya ce "Faɗi sai a baka" "Naƙi wayon, kawo kawai" Viper ya yi murmushi ya zaro dubu ɗaya ya ajiye masa ya ce "Faɗi idan yayi mini sai na ƙara maka" Abdul ya ce "Ai kai ne mayar da tukuicin, ai albishir ɗin namu ne gaba ɗaya. Twins ce dama ita ai ko?" Viper ya jinjina masa kai. "So congratulations, babynta biyu ne a cikinta, twins ne yaran" Waro ido Viper ya yi yana kallon screen ɗin injin scanic ɗin, tamkar zai gane menene a jiki. Jikinsa ya hau wata irin tsuma ya ce "Dan Allah da gaske ka ke ko da wasa?" "Yaya zan yi maka wasa da abu mai muhimmanci har haka? Wallahi da gaske nake, twins ne, kuma duk su na cikin ƙoshin lafiya" Viper ya miƙe ya yi sujudar godiya ga Allah, ya miƙe ya rasa me ma zai yi ko ya ce. Ya kwance agogon hannunsa, ya ajiyewa Abdul, ya zaro ɗaya daga zobensa na azurfa shi ma ya ajiye masa. Ya fara laluba aljihunsa, Abdul ya ce "Haba Viper, yanzu mun zama ɗaya sirikina ne fa kai, ina tayaka murna, Allah ya inganta ya raba lafiya, amma ku yi shiru kar wanda aka gaya wa biyu ne. Ga agogonka da zobenka ba zan karɓa ba" Viper ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar mu yi haka da kai, yarana biyu na rasa, ɗaya aka yi ɓarinsa, ɗaya kuma bai ma zo duniyar ba, yanzu Allah ya haɗa mini biyu. Na ma rasa wane irin farinciki zan yi ne, ba kai ka bani ba, saƙon kawai ka gaya mini, amma ba ka ji zuciyata ba, Alhamdilillah ala kulli halin. Na rasa jauhar, ga Nabila, na rasa yarana ya bani biyu Allah Alhamdilillah. Yayi maganar yana goge ƙwalla. Jikin Abdul ya yi sanyi, da ya tuna babansa ne silar ajalin matar Viper. Ya tuna lokacin da yake yi wa Viper kallon ɗan jagaliya, ɗan maula ƙasƙantaccen mutum da yake zuwa maula wurin mahaifinsa, yau gashi Allah ya canza komai, ya nutsu ya zama mai bayar da gudummawa ga al'umma. Ya ƙarasa ya ɗago Nabila, yana mata sannu. "Abincina" tayi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallonsa. "Ai dole ma a ɗaukko abincin nan Abla" "Kuma ka gaya musu su daina damuna, ko in ƙi haifarsu" Cikin murmushinsa da yake ƙara masa kyau ya ce "Za su daina in sha Allah" Abdul ya ci gaba da yi musu fatan alkhairi, da taya su murna. Tun da suka koma gida, duk in da Nabila ta yi sai ya bi ta da kallo, yana tunanin yara biyu ne a cikinta. Addu'a ya din ga yi, Allah ya sa yana rabon da ganin yaran, tare da yi musu fatan shiriya tun kafin su zo duniya, da fatan Allah ya sa kar laifukan da ya aikata su shafi yaransa. Nabila tunani ta din ga yi, na abin da za ta yi, da zai wayar wa da al'umma kai, a kan muhimmancin neman 'yancinsu, da ƙirƙiro abubuwan da za su taimaka wurin ƴaƙi da harkar daba da shaye-shaye da kuma bangar siyasa. Yanayin shirin bikin Sumayya da suke yi, ya hanata zama su tattauna yadda yakamata, ta na son ta yi magana da Viper ma, domin za ta so goyon bayansa ɗari bisa ɗari a kan abin da take ƙudurin yi ɗin. Aka yi taron bikin sumayya lafiya, aka gama lafiya, ita ma mijinta mutum ne mai rufin asiri, ya na da mace ɗaya da yara uku, cousin ɗin Alhaji mu'azzam ne, shi ne ya haɗa shi da ita ma. Major yana ta mitar Nabila kwana biyu ba ta zuwa gaishe shi, ya kirata ya ce mata shi zai zo ya ganta, amma ta ce masa ba ta nan, sai dare zata dawo. Bayan sallar isha'i kuwa sai gashi shi da Anty, tun da suka zo ta manne a wuri ɗaya ta ƙi tashi. Viper ya yi wa Major zancen rabon gadon Jauhar, za a sayar da kayanta, Nabila ta ce ba ta son kaya. Abba ya ce "Ni idan an yi wa kayan kuɗi a bani na saya, sai mu bayar sadaka Allah ya kai mata ladan". Viper ya ce "Ita ma ta ce kuɗin, ayi wani abu da su, Allah ya kai ladan kabarin Jauhar" Major ya ce "Hakan ma yayi kyau, amma a ajiye wani abu da za a din ga tunawa da ita dai" "Eh in sha Allah, ko ma muje gidan tare, sai na yi wa Baba magana muje a duba" Major ya ce "Duk yadda ka yi yayi, Allah ya saka maka da alkhairi kai ma, Allah kuma ya ƙara bamu haƙurin rashin Jauhar da mahaifiyarta" Har suka gama abin da za su yi, Nabila taƙi yi musu rakiya, sai Viper ne ya raka su, suna tafe a hanya Major yake mitar Nabila duk ta zama so silent, ko dai akwai wani ne da take ɓoyewa. Anty ta ce "Ciki ne fa da ita, take ta wannan nuƙu-nuƙun" "Kaii ciki, tun yanzu?" Anty ta ce "Ahh ikon Allah, wata nawa da yin auren?" "Lallai Major, wato Arfa ce 'ya, mu a shekara nawa muka haihu?" Ya ce "Ai ku tun zamanin baya ne, ita kuwa kamar yayi wuri, haryanzu ƙanƙantarta nake gani" "Shekara ashirin da shida?" "Eh mana, rainon ciki akwai wahala, kin ga ita ga ba uwa, ku ba tayi sakewar da za ta tunkaroku da wannan maganar ba, balle ma idan wani abin ne ku taimaka mata ba, bari na koma gida, zan kirata a waya, ko da wani abu da take buƙata" Waro ido ta yi ta ce "Sai ka tambayeta a kan cikin?" "To shi ne me? Ni uwar ni ne uban, ai cikin halak ne, mijinta ba mazauni ba ne ba, cikin fari ba ta san kan komai ba" "Amma ai ka bari mu mu tambayeta ko" "Tsakaninki da Allah yaushe rabonki da ita, ban da yau da na ce ki zo ki rako ni wurinta? Ni ba abin kunya ne a wurina ba, idan ta kama na dawo da ita gida, gani gata magajiya ta din ga kula mini da ita, ba ruwanku" Anty ta ja bakinta ta tsuke, dan ba ta ga tsari a hakan ba. Aikuwa kamar yadda ya faɗa, hakan aka yi, bayan ya koma gida ya kira Nabila yake tambayarta. Kasa ba shi amsa tayi, ta ji tamkar ta nutse a wurin, saboda kunya. "Idan kin san akwai matsala, ni sai na yi wa mijin naki magana, idan baya gari ki taho gida, ko na turo miki magajiya, ta din ga kula da ke" "Abba yana kula da ni, baba Magajiya kuma yakamata ace zuwa yanzu ta huta ita ma, ina iya yin komai ma" "Kin tabatta?" "Eh Abba" "Arfa ba na son kawaicin nan naki, Ni babu kunya a tsakanina da ke, baki da uwa a raye, kar ki bari wani abu ya shige miki duhu, idan ba zaki iya kirana a waya ba, ki yi mini message kin ji ko?" "To Abba" "Allah ne mai komai, amma ba zan so ki sha wahalar da mahaifiyarki ta sha ba" "In sha Allah" Ya ce "Yauwwa, sai da safe, ki gaida mijin naki, Allah ya yi muku albarka gaba ɗaya" "Amin mun gode, ayi wa Anty ya ta je gida" ta kashe wayar, Viper ya na kusa da ita, ya na saurarenta. "Abla" ta waiwayo ta ce "Na'am" "Kowane dangi, idan aka samu irin Abba ko guda ɗaya ne, mai jajircewa a kan zumunci, ba tare da kallon ɗora wa kansa ɗawainiya ne ba, da an rage wani abin. Mutum ne mai zafi, amma jajirtacce ya san abin da yake yi. Ke kaɗai sadaƙatul jariya ce a gare shi ko bayan ransa. Banda ladan zumunci hatta taimakon da ki ke yi wa al'umma yana da lada. Kin tsayawa dattijon nan babu ko sisi, kin tsaya wa rahama, kin tsaya mini duk babu ko sisi, kin siffantu da wasu daga cikin kyawawan ɗabi'unsa, da shi da Alhaji mu'zzam, da Walid da liti, mutane ne da al'umma ke buƙatar irin su." Nabila ta ɓata fuska ta ce "Ban da liti dai" "Haba masoyiyya, ya fa baki haƙuri. Wallahi Abdallah mutumin kirki ne fiye da yadda ki ke zato, kawai dai mutum ne da babu ruwansa da kara, zai yi abin da yake so ne, ko yayi maka daɗi ko ya kashe ka, bai damu ba" "Ai na ga alama, ni fa ban taɓa zaton ya na barkwanci ba, ranar da na fara ganinsa, a tal'udu wurin da yake sayar da katin waya, amma kayan maye yake sayarwa, sai da na tsorata. Babu alamar ɗigon imani a tattare da shi, sai fa da ya ce sai ya kashe ni, idan na sake zuwa" "Wallahi ba haka yake ba, sharrin ƙwaya ne kawai da kayan maye, Allah dai ya ƙara shirya mu, rayuwa duk ta fi yi mana daɗi a yanzu. Mutane kowa yana sonmu, yana son haɗa alaƙa da mu, har ana ɗora mana wasu nauye-nauye. Duk a baya, mu kanmu bamu jin cewa, a duniyar da mutane suke muke, hango duniyarmu muke yi daban, saboda kowa kallon mutane marasa amfani yake yi mana. Marigayiyya ce ta fara ƙoƙarin ankarar da mu, muhimmancinmu a cikin al'umma." Nabila ta jinjina kai ta ce"Jauhar ta yi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske, kuma in sha Allah, yana daga cikin abin da na ƙudurce a zuciyata, ci gaba da yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ta hanyar nuna wa wanda suka tsinci kansu a harkar, su ma 'ya'ya ne, kuma akwai amfanin da za su yi wa al'umma. Ina son da ni da kai, sa sumayya, barrister Habib, da wanda suka kamata, mu ga abin yi, idan ta kama ko ƙungiya ce mu kafa, ko mutane goma ne suka shiryu a sanadinmu, mun yi nasara" "Duk a bar wannan maganar, sai Allah ya saka kin sauka lafiya, sai ayi ta, tunani mai kyau sosai da sosai. Sumayyan nan taki ma 'yar aljanna ce da yardar Allah, na ga tana yinki saboda Allah" "Ko ba Sumayya ba, ba ka ga Abba ne yayi waliccin aurenta ba ma, ƙawar amana kenan, ina alfahari da ita" Haka Viper suka ci gaba da tattaunawa da shi da abar ƙaunarsa. Kwanci tashi asarar mai rai, cikin Nabila ya yi watanni shida, amma kamar zata haihu a lokacin, saboda girma, hakan ya saka ta daina fita gaba ɗaya, saboda nauyin cikin. Shahida kuwa matar Walid, ta fita nauyi, dan ita nata ya kusa shiga watan haihuwa. Ramma na gida ta dawo daga makaranta, tana ta sauri ta gama abin da take yi, ta san Abdul ko ya dawo, ko ya aiko a ɗaukar masa abinci. Kiran waya ta gani, da baƙuwar lamba, ta ɗaga tare da yin sallama. "Matar doctor Abdul ce?" "Eh nice" "Ok, dan Allah maza ki taho Asibiti, Doctor ne ya yanke jiki ya faɗi" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ta furta jikinta yayi wani irin sanyi. Ayshercool 08081012143 Jikin ramma tsuma ya din ga yi cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, fargabarta Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya faru da shi ba, dan kuwa yanzu a duniya tana matuƙar buƙatar Abdul a cikin rayuwarta. Ko rasa shi tayi, ta san abu ne mai wahala samun mijin da zai tsaya a kan lamuranta kamarsa. Hijjabi kawai ta zura ta fice daga gidan ta tafi asibitin da ya ce mata zai je ganin marasa lafiya. Har an bashi ɗaki, yana kwance ana ƙara masa ruwa. Cikin tashin hankali da damuwa, take tambayar meyasame shi. Wani likita yake yi mata bayani "Bamu sani ba, ya gama ganin marasa lafiya, aka kira shi a waya, ba mu san me aka ce masa bai fi mintuna sha biyar ba ya faɗi, amma ya farfaɗo ɗazu har yake ta kiran sunanta, aka yi masa allurar bacci. Ta ɗauki wayarsa, ta saka thumb print ɗin ta, ta buɗe wayar. Call log ɗin sa ta duba, ta ga wanda suka yi waya ta ƙarshe da shi Honorable speaker ta gani. Ta kalle shi, ta san ba zai wuce a kan maganar mahaifinsa ba ne ba. Tausayin sa ya kamata, ta matsa kusa da shi tana shafa kansa, yanzu da ya nutsun nan, har wani kyau ya yi na musamman. Rashin ji da gagara ba su da wani amfani. Aka kira sallar la'asar, ta shiga banɗaki ta yi alwala, tana fitowa taga Mummy da Anty Jidda a ɗakin. Mummy ta ce "Ga shaiɗaniyar yarinyar nan" Jidda ta kalli ramma, yarinyar da take mata aiki,  wahalalliyar 'yar ƙauye tayi ƙiba, fatar nan tayi kyau. "Ramma, ke nake gani haka?" Ramma ta dake ta ce "Eh, nice anty Jidda, kin yi zaton tozarcin da ki ka yi mini Allah zai wulaƙanta ni ne? Ai shi Allah yana kishin bawansa" "Ramma ni ki ke gaya wa haka?" "Ai ba tun yau ba, na daɗe ina fatan Allah ya haɗa ni da ke, na gaya miki abin da yake raina. Duk bauta da wahalar da nake yi miki da yaranki, iftila'i ya same ni a gidanki, ki nuna baki sanni ba, in haɗu da ke ma, ki ka toshe kowacce irin kafa, ki ka wulaƙanta ni, aka hana mu shiga gidan ma, babu wata magana mai daɗi ko rarrashi, saboda ni baitil mali ce mara galihu. To da yake shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa ai yanzu ku na gani, ko iftila'in zawarci ma ya ishe ki" Buɗe baki suka yi su na kallon ramma. Ko a jikinta ta sake cewa "Wallahi darajar mijina ki ka ci anty Jidda, amma niyya na yi na roƙi Allah ya sa yi wa 'yar ki abin da aka yi mini, a kan idonki ki ji abin da ni da uwata muka ji, sai dai kash ƙaddara ta riga fata, yaranki ba su suka yi mini laifin ba, kuma wanda ya yi laifin ya yi tuba na haƙiƙa, kuma na yafe masa har gaban abada, amma ba dan haka ba ba zan gushe ba ina yi miki fatan Allah ya jarrabeki ke ma, ko alhakin mai gadinki da aka kashe, ya isheku nauyi". Mummy ce ta fara zage-zage, ramma kuwa ta tayar da salla, tare da jin sassauci a zuciyarta ko ba komai yau ta amayar da wani abu da yake ci mata zuciya. Wani likita ne ya zo yayi musu magana, a kan ko su yi shiru ko su fita, Abdul yana buƙatar hutu. Anty Jidda dai azabar mamaki ya hanata magana, kallon ramma kawai take yi, yarinyar da magana ma wahala take yi mata, amma ita ce ta zama haka take gaya mata magana. Ramma ce ta hango Abdul yana motsi, ta tashi ta nufe shi da sauri, su Mummy ma suka yi kansa. "Doctor, meyafaru ne? An kira ni aka ce mini ka faɗi" Babban abin da ya ƙular da Mummy bai wuce yadda yake kallon ramma ba, ko ya nuna ya gansu. "Rahama, embassy na Nigeria sun yi iya yin su an shiga an fita, ba za a iya fitar da Daddy ba, za a gurfanar da shi a gaban kotu" yayi maganar muryarsa na rawa. Salati suka saka gaba ɗaya, dan su ba su ma sani ba sai yanzu. Ramma ta riƙe hannunsa ta ce "Ka yi haƙuri Abdul, kowace rai akwai kalar jarrabawar da Allah subhanahu wata'ala yake yi mata, ka yi haƙuri. Mummy ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka, ta ciro wayarta tana dannawa, Jidda na ta ba ta haƙuri, ramma a ranta ta ce "Allah ya ƙara, kaɗan ma ku ka gani, ni kam Allah ya ƙara shirya mini kai ya kare mini kai da ci gaba da aikata duk wani mugun aiki. A zahiri kuma ta ci gaba da rarrashinsa, tana kwantar masa da hankali. ***** Rahila Allah ya taimaketa, aka sallamota daga asibitin masu rangwamen hankali, sai dai duk tayi wani iri, tsufanta ya fito sosai da sosai. Shahida ta zauna ta yi ta mata nasiha a kan tayi haƙuri, ta kwantar da hankalinta, kar ta ɗorawa kanta kishi, idan ba haka ba ta bari Abbu ya saketa ba ta da wurin zuwa ta zauna. Shi kuwa Abbu, hankalinsa ya kwanta, Al'amin ɗin sa ya zama mutum, ya nutsu ya shiryu, ga maman ramma sam ba ta da damuwa da hayaniya, su na zamansu lafiya. Abdul ya takura a asibiti shi a sallame shi, da aka sallame shi su ka koma gida, ko fita baya iya yi, abinci ma sai ramma tayi da gaske yake iya ci. Ta kira mama ta gaya mata, mama ba ta taɓa zuwa gidan ramma ba sai lokacin, suka je tare da Abbu. Duk da da sauran pain ɗin abun da Abdul ya yi musu a zuciyarta, amma sai da ya bata tausayi. Ta din ga jinjina girman ikon Allah, ganin katafaren gidan da rammar ke ciki, komai na jin daɗin rayuwa dai-dai gwargwado akwai shi. Su ka jajanta musu, Abbu ya yi ta yi masa nasiha, tare da nusar da shi muhimmancin addu'a da kuma juriya. **** Nabila kuwa na ta rainon cikinta, da aka raba kayan jauhar, kayan jariran da suka saya, ya faɗo a rabon Nabila, ya tambayeta ta na so ko a sayar a bata kuɗin, ta ce kayan take so. Major buni-buni, sai ya zo gidan Nabila ya dubata, cikin nan yayi girma sosai da sosai. Gaba ɗaya ta zauna a gida ta daina fita, saboda duk wanda ya ga cikin sai ya yi magana. Liti ya saka babansa a gaba, tun da ya ga ya san Major, yake ta yi masa nacin, yaje ya tambayar masa auren Walida, amma babansa yaƙi ya ce sai ya ga kamun ludayinsa sai ya ƙara hankali. Abbu ya samu mahaifin liti ya ce masa shi ne yake tare da su a kasuwa, liti ya yi hankali sosai da sosai, kuma shekarunsa ja suke yi. Da kyar ya amince ya yi wa Major maganar, amma ya yi masa bayanin komai. Major ya ce "Ai ɗanka nawa ne prof, kuma tun da shi ma ya shiryu haka muke so, in dai yarinyar ta na son sa, Ubangiji Allah ya tabattar mana da alkhairi, dama tuntuni  yayarta Nabila ta fara yi mini zancen, idan kun shirya ku zo ayi magana kawai" Liti har gida ya je ya gaya wa Nabila Major ya amince ya bashi auren Walida, tare da ƙara yi mata godiya, bisa ƙoƙarin da ta yi masa. Cikin Nabila na ganin gata, domin kuwa tuni a wannan karon ma Viper ya fara sayayyar kayan jariri, idan ya tambaye ta zaɓi, sai ta ce ita duk abin da ya saya shikenan, ita dai damuwarta ta rabu da cikin nan lafiya. Shahida ce ta fara haihuwa, matar Walid, daga kai ta asibiti cikin dare tana ciwon baya, aka ce ai ta kusa haihuwa, abin har mamaki ya bashi. Viper ba ya gari, Nabila kuma ta yi nauyin da ba za ta iya fita ba, Walid baki yaƙi rufuwa, wai shi ne ya zama uba, Allah ya bashi ɗa namiji. Liti har ya fishi murna, kamar ɗansa, ya din ga bin sa yana cewa "Saura ka saka masa sunan Viper, alhalin gani, sunana zaka saka masa" "Kai a wa?" "Ni a baban yaron mana, dan Allah Walidi ka saka masa sunana Abdallah, na san rashin m ɗinka, tsaf zaka saka masa sunan Viper, dan muraran ka ke nuna fifikon ka fi son sa a kaina" Kafin suna Viper ya zo gari, Nabila ta so ta bishi ta je ta ga yaron, amma ya ce ba zata fita a din ga tanka ta ba. Viper kamar ya tafi da yaron, ya din ga addu'a Allah ya nuna masa na sa haka shi ma. Yayi masa addu'a sosai da sosai yaron. Walid ya sanya sunan mahaifinsa Umar. Dubu ɗari Viper ya bawa Walid, ya ce masa yayi haƙuri, abubuwa ne sun yi masa yawa. Yanayin jikin Nabila, ya sanya Major ya tura Baba magajiya ta zauna da ita. Sai dai idan Viper yana nan 'yar kallo take zama, sai dai ta yi ɗan aikace-aikacen gida. Hatta wanka sakata yake a toilet ɗin ƙurya ya wanketa, undeas ɗin ta, idan ta cire duk shi yake wanke mata. Shi kansa ba

Chapter 119 of 121