Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
108 / 121
muka yi ba babana, halayen da ka ke yi ne bama so, amm Alhamdilillah daga kai har uban ɗakin naka, naga nutsuwa a tattare da ku, Allah ya ƙara shirya mana ku" "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, na gode sosai da sosai Alhaji" Alhaji ya ce "Jeka Allah ya bayar da sa'a" ya amsa da Amin. Gwaggo ta fara masifa ta ce "Au barinsa zaka yi ya tafi? Kana kallonsa?" "Gwaggo ki yi haƙuri dan Allah, ba kowane lokaci ƙarfi da fushi yake amfani a wurin tarbiyya ba, wasu lokutan rarrashi da addu'a suke buƙata. Yanzu barin gidan da yayi, ba wai hakan ne ya saka ya ɗan nutsu ba, addu'a ce kawai, kina ji da tasirin wata yarinya a rayuwar abokinsu" "To shi ma ayi masa auren mana, tun da ya fara tsufa yana shashanci" Ficewa Liti yayi, dan idan ya biye mata, lokuta da dama a baya lokacin yana kan ganiyar shaye-shaye, ya sha yinƙurin ɗura mata ashariya, ko kuma ya sureta ya buga da ƙasa, saboda a cewarsa tana yi masa shishishigi da munafunci. ***** Saƙo ne ya riski Naja'atu Bunkure, a kan cewar ma'aikatar Shari'a ta soke lasisinta, har sai an kammala bincike a kanta. Hankalinta yayi mummunan tashi, ta kira Indabo a waya cikin tashin hankali, yana ɗagawa ya ce "Ya kuma aka yi?" "An soke lasisina daga ma'aikatar shari'a, wai sai an kammala bincike a kaina, dama ba ta janye ɗin ba?" "Kuma dai? Ta janye ƙarar fa, sai da na tabattar da hakan, kuma yanzu nima nake samun labarin wannan shegen yaron da na saka a kashe, dan ya ƙara zama jan kunne ga Vipern, bai mutu ba, wai yana raye a asibiti" "To ni ina ruwana, licensed ɗi na fa aka yi siezing, wane irin abu ne wannan, duk wahalar da na sha kafin na zo wannan gaɓar, sai da na kai ƙololuwa sannan zan yi faɗuwar baƙar tasa, wannan mummunan ƙarshen, wallahi ba zai yiwu ba" "Ki yi haƙuri ki daidaita nutsuwar ki, zan san abin yi, ki yi haƙuri ai hakan ba zai yiwu ba sam" kashe wayar tayi, tana jin yadda kanta yayi mata wani irin mugun nauyi, ta ma rasa me za ta yi ko ta ce gaba ɗaya. *** Walid jiki yayi kyau sosai, Viper yana gefensa yana yi masa magana, amma hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa da hannu ɗaya. "Ɗan marayan zakina, ya jiki, ina son na zo na ƙara dubaka, amma ina jin kunyar yaya, kuma ga mama babu lafiya ita ma" "Kar ki damu, ina samun saƙon gaisuwarki ai, jiki Alhamdilillah da sauƙi" "Allah ya ƙara tsare mini kai" "Amin ke ma haka" "Amma Yaya ya gaya maka na taɓa aure, har shekara uku?" Walid yayi mata reply da"Har ɗaurin aurenki mun je ni da Walid a madadinsa a lokacin yana tsare a gidan yari" "Lallai kun cika abokan amana, ina son abotarku. Amma kana ganin babu ƙwara a ciki, kaga kai ba ka taɓa aure ba, ni kuma na taɓa" Walid ya ce "Ko kaɗan, Viper ba zai haɗani da abin da ya san akwai cutuwa ba, kuma ni ba wannan nake dubawa ba, nima kin san irin rayuwar da muka yi a baya, kuma ni ba wani mai ƙarfi bane ba, buga-buga ce dai muke yin ta, amma kin ga ke kuma 'yar gayu ce, matar manya ce, ina fatan hakan ba zai zama da shiga hakkinki ba" Voice message ta yi masa, ya rage volume yana saurara ta ce "Babu wannan maganar, ni kawai sonake nima ka so ni kamar yadda ka ke son Yaya Al'amin, ka ji my, Allah ya sa kai nawa ne nikaɗai, kuma ka daina ce mini Shahida gaskiya, sunan soyayya zaka samo mini nima" ta ƙarasa maganar tana dariya, dan ta san ƙarshenta, sauka zai yi daga online ɗin. Aikuwa haka yi, ya rufe data yana murmushi, sai suka yi ido huɗu da Viper, da ya gaji da magana ya zuba masa ido, sai yayi sauri ya ajiye wayar yana ɓoyeta kamar yayi rashin gaskiya. Viper ya ce "Wai me ka ke yi a cikin wayar ne?" "Tilawa" yayi maganar yana mazewa. "A'a karatun kalaman da tayi maka kake yi wa tilawa kenan, ai fa Walid an fara soyayya babu sarki sai Allah, muna zaman zamanmu Viper ka saita masa hanya, yake ta zaƙewa" Viper ya ce "Ai naga alama, me take gaya maka ne har haka?" Liti yayi farat ya ce "Wai ɗan marayan zaki, wani gursumemen gardi, kwana yake yana murmushi" Viper ya yi murmushi ya ce "Na ji daɗin hakan sosai, ɗan uwana na cikin farinciki, Allah ya tabattar mana da alkhairi. Kai kuma goga wa zaka samo mana ne mu aura maka?" Liti ya ce "Mhmm, wani zance mara amfani tsohuwar nan ta gidanmu take yi, da na lalace cewa tayi a koreni, Alhajinmu yana sangarta ni, saboda ba ta son uwata. Amma akwai jikarta da take son uwatta, ta gama lalacewa yarinyar nan na girmeta, amma saboda tsabar yawo da gantalin bin maza, duk ta fara tsufa wai a haɗamu aure" Viper ya ce "A'uzubilalimatillahi" Walid ya ce "To meye a ciki, ku rufa wa juna asiri shikenan" "Wa za a rufa wa asirin? Wallahi da budurcina ba zan auri lalattaciya ba, ta gama bayar da free services a kwararo ba, Allah ya kiyaye" "Walid ya ce "A gidan uwar wa ka ke da wani budurci, mace ne kai? Kai ma fa a lalacen nan kake, shaida ɗaya zan yi maka bama kula 'yar kowa" Ya ce "Yauwwa to barka, a bar ni da ɓalla ƙarafa da caji, amma banda shashanci, dama aure ta taɓa yi da sauƙi, amma ta gama gantali wai a bani, kai tsohuwar nan ba ta ƙaunata" Viper sai da yayi dariya, jin yadda liti yake ta ɓaro zance. Tashi ya yi ya fita, yana son ganin Nabila sosai da sosai, amma ya fara tsorata da abubuwan da take yi masa, ya kasa gane da gaske take yi ba ta son shi, ko kuwa dai kawai rigima ce irin ta ta. Wayarta ya kira, sai dai sai da ya fara harzuƙa sannan ta ɗaga, murya ƙasa-ƙasa ta yi masa sallama. "Kina ina?" "Na je gidanmu ne" "Meyasa ki ka fita? Ban gaya miki kina cikin barazanar rashin tsaro ba?" A hankali ta ce "Joseph ne fa ya kai ni" tayi maganar kamar a shagwaɓe. "Meyafaru muryarki tayi ƙasa?" Nabila ta ce "Bana jin daɗi ne, bani da lafiya" "Meyafaru?" Ya faɗa kamar an yi masa dole. "Ka san an yi ƙura ne jiya, ina ta fama da tari, ban yi bacci ba sosai, sai kuma na tashi da ciwon kai" Ya ɗan lumshe idanunsa ya ce "Asibiti fa?" "Na sha magani a gida, zan kai rahama awo gobe in Allah ya kaimu zan ga likita daga nan" Ya ce "Ok take care, idan da wani abu let me know" Ta ce "Ok na gode sosai, a gaida Oga walid" Ta ajiye wayar tana jin wani iri a jikinta, tunani take yi, ko ya daina sonta ne, ya ajiye maganarta a gefe kamar yadda ta nema?. Shi ma sauke wayar ya yi,  yana jin yayi kewar rigima da shagwaɓarta, kenan da gaske dai ba ta son sa kenan? Bai taɓa tunanin idan yayi mata maganar aurensu, za ta ce ba zata aure shi ba. **** Ramma ciki ya tsufa sosai, kullum cikin lissafi take, yaushe Abdul zai fito, gashi sati huɗu ake bata a wurin awo, wani abun tana ji tana gani, tana so, amma babu yadda ta iya, sai dai ta haƙura tayi shiru. Saboda tana tsoron tayi wani abun mama ta hantareta, dan sam ba ta ƙaunar cikin nan. Ramma ta san da Abdul ba a tsare yake ba, da zata ga gata da kulawa, amma tana matuƙar jin daɗin yadda Nabila take nuna mata kulawa da damuwa da ita da sumayya. Yau bayan ta kai ta awo, suka biya aka yi sayyayar kayan haihuwa. Daga nan ta kaita wurin Abdul, yau ma kamar kar su rabu, sauransa wata ɗaya ne ya fito daga prison, bakin ramma har kunne saboda murna. Washegari da yamma, Alhaji mu'azzam ya zo gidan, mama ta karɓe shi, kamar yadda ta saba har take tambayarsa yaushe za su koma ƙauye, sun zo sun zaune masa a gida. Ya ce "Haba Hajiya, ai kin girmi rayuwar ƙauye yanzu, ko dan asirin rahama, ba zaku koma ƙauye ba, kema kuma ina fatan Allah ya baki mijin aure, kema ki yi aurenki a nan birni ki huta". Maman ramma ta ce "Ashha, ga 'ya har da tsohon ciki nayi aure, ai aure kuma yanzu sai dai naga ana yi wanda nayi Allah ya sanya albarka" Alhaji mu'azzam ya ce "Saboda me, shekarunki nawa ne?" "Na kusa arba'in idan ma ban yi ba, tun ina shekara sha uku aka yi mini aure" "Kuma ki ce kin wuce aure, a'a ai aure garkuwa ne" Yayi waya aka shigo masa da wata shirgegiyar akwati, ya saka aka kirawo masa ramma. Ya ce "Sannu rahama, kin kusa shiga watan haihuwa ko?" Ta bashi amsa tana sunkuyar da kai ƙasa. "Babu wata matsala dai ko? Nabila na kai ki awo, naga an ware ni a gefe ni, ke da ita kuke abinku" ta sunkuyar da kai tana murmushi. "To Allah ya raba lafiya, ga kaya nan, naki da na jariri unisex ne kayan babyn, Allah ya raba lafiya" Maman ramma ta ce "Haba Alhaji, ɗawainiyar tayi yawa, jiya fa sun sayo kaya da Nabila" "Wannan mijinta ne ya bayar da kuɗin, wannan kuma ni a matsayinta na 'ya ta na saya mata. Kar ki manta a gidana fa koma menene ya sameta, dan haka ko me zan yi wa rahama, ba zan goge muku abin da aka yi muku ba, dan haka ba wani abu bane ba, Allah ya raba su lafiya" Mama tayi ta yi masa godiya, kamar ta shige cikin sa. ***** Nasir ya dawo daga aiki, ya ga manyan motici suna shiga street ɗin su, abin ya bashi mamaki, ya ƙarasa da motarsa, ya ga a ƙofar gidan su, suka yi parking. Abbu ne ya fara fitowa, mamaki ne ya cika Nasir, ya fara tunanin a ina ya san fuskar nan, Alhaji mu'azzam ma ya fito, hannunsa riƙe da waya. Sauran motoci biyun convoy ɗin Alhaji mu'azzam ne. Ya fito daga tasa motar, a dai-dai lokacin da Baban su Nabila ma ya fito. Ya ƙarasa suka gaisa da su, Alhaji mu'azzam ya ce "Yauwwa dama baban naka nake kira, na gaya masa zan zo masa da baƙi yau" Nasir ya ce "Masha Allah, tun da ya san da zuwanku, bisimillah mu shiga" Suna ƙoƙarin shiga, sannan Viper ya fito daga mota, ɗaya daga cikin sauran motocin. Nasir yana jinjina tsabar taƙama da jin kan Viper, shi ba kowan kowa ba, sai a yanzu ya gane in da yake tunanin sanin Abbu, kamarsa ɗaya da Viper, sai ya lura irin tafiya ɗaya yake yi da mahaifinsa, sai dai shi harkar daba ce ta ƙarawa tasa tafiyar taƙama. Major na jin sallamar baƙi a falonsa, ya miƙe cikin farinciki yana yi musu maraba, sai dai yayi tururs da ya gansu tare da Bashir. Fuska babu walwala ya ƙarasa karɓar su. Alhaji mu'azzam ya yi gyaran murya ya ce "Duk da baƙin naka, wasu sanannu ne, wasu kuma baka sansu ba, wannan shi ne mahaifin Al'amin Viper, wanda ya auri 'yar uwar Nabila, wannan kuma Al'amin, wannan kuma baban su Nabila, kamar yadda ka sani. Mun zo ne a tare da shi, mu sake baka haƙuri a kan abin da ya faru, dan Allah kayi haƙuri ya wuce, ko dan samun nutsuwar ita yarinyar". Major ya kalli Alhaji mu'azzam ya ce "Ka kuwa san abin da yayi mini? Har duniya ta naɗe ba zan manta ba. Babu ƙoƙarin da ban yi ba na yafe masa na manta, amma na kasa, mussaman idan ina tuna yadda yarinyar nan ta mutu da sunansa a bakinta, duk tsananin kunyar bafulatana, amma ba ta son laifinsa, sosai take nuna son mijinta, amma ta wulaƙanta mini yar uwa ya tozarta ta, ya barota a dajin Allah ba ta san kowa ba sai shi. Na bashi yarinya amma ya aurawa ɗan daba ya kasheta" Alhaji mu'azzam ya ce "Ashsha! A bar tuna baya major, shi fa yaron nan da ka ke magana a kai, ga shi a zaune a gabanka, ga mahaifinsa ba zai ji daɗin ka din ga jifansa da irin wannan maganganun ba. Ni nan ni na fara neman auren Jauhar, Allah bai yi ba ta auri Aminu, amma zan iya ce maka, a duniya jauhar ma da ƙaunar mijinta ta bar duniya, saboda yar uwatta da na aura, kan yi zancenta da rayuwar gidanta. Kawai sharrin yan siyasa ne da rashin ji da yayi tsautsayi ya faru, idan zan gaya maka gwagwarmaya da wahalar da ya shiga bayan mutuwarta, to a matsayinka na uba, sai ka zubar da hawaye. Nabila dai ita ce da ta shiga rayuwarsa ta taimake shi, Al'amin ba ƙashin yarwa bane ba, amma ka yi binciken ka kaima, kar laifin mahaifinsu ya shafe shi dan Allah" Abbu yayi gyaran murya ya ce "Ranka ya daɗe, ita duniyar guda nawa take, duk da Alhaji Bashir yayi mini bayanin komai, bai ishe mu darasi da mamaki, ace duk da ka nesanta yaran biyu, da juna Nabila ta afka rayuwar Al'amin ba tare da ta san waye shi ba? A duniya ina gaya maka idan mutum bai yi dacen mace ba, sai addu'a kawai. Ka ganni nan, da sanya hannayena bibbiyu, a lalacewar ɗa na, bayan mutuwar mahaifiyarsa na auri ƙawarta, ina saka ran ta kula mini da 'ya'ya, amma a ƙarshe saboda makirci irin na ɗiya mace, sai da ya zama tsakanina da Al'amin babu jituwa, kamar maƙiyina, dan Allah a bar tuna abin da ya wuce" Bashir ya ce "Maitama na san duk abin da zan gaya maka, ba yadda zaka yi da ni ba, amma a irin yadda na auri Chubaɗo na fara rayuwa da ita, ka san ban aureta dan na cutar da ita ba, ƙaddara da makircin mata, ya sanya abin da ya faru ya faru, tun da ko da na aureta ka san ba mutumin banza ne ni ba. Na haɗu da sharrin mata ne da suka yi mini sihiri a kan mairamu, a gaban Nabila suka din ga faɗar abin da ya faru, amma dan Allah ka yi haƙuri, ka yafe mini" "Ba wani sihiri, dama mutum ya tara mata ya zauna ba addu'a, ba neman tsari, ba dole kowane abu ma mata su yi wa mutum ya kama shi ba" Abbu ya ce "A dai yi haƙuri, ya wuce dan Allah" "To yanzu me ku ke so?" Baba ya ce "Ina son ka bani Nabila ne, haryanzu ina kewar Jauhar, dan Allah ka bani 'ya ta" Wani mugun kallo ya yi wa Bashir, ya ce amma dai ba ka san me ka ke cewa ba ko? Nima da na rasa 'yar uwata haƙuri nayi na faullawa Allah. Kai Alhaji mu'azzam yaya muka yi da kai, ba cewa ka yi da ta kammala shari'a zaka dawo mini da 'ya ta ba? Kawai sai ku zo mini da wani zancen daban, Nabila tun da Allah ya haɗaku, duk lokacin da take so, ta je ka ganta, amma wallahi ba zan bayar ba". "Maitama kar mu yi haka da kai, ka bani 'ya ta ka tausaya mini mana" "Ita ma ka kaita su yi mata asirin kenan? Ba zai yiwu ba wallahi, kuma kai Alhaji mu'azzam, kai mun yi da kai zaku dawo mini da 'ya ta ai". Alhaji mu'azzam ya ce "Haryanzu da sauran issue ne, amma za ta dawo, tun da ai haryanzu tana zuwa nan ɗin" Abbu ya ce "Amma dai muna fatan ka yafe masa, a manta da abin da ya faru a baya?" "Ya wuce, mantawa kuma wannan ba lallai ba, 'ya kuma a ƙyale mini 'ya ta, Allah ya sa mu dace" Alhaji mu'azzam ya ce "Hakan ma Allah ya saka da alkhairi, kuma tun da ka ce duk lokacin da take so taje taga mahaifinta, Allah ya saka da alkhairi ya huci zuciyarka" Major ya numfasa ya ce "Amin" Baba ya tashi ya ƙarasa ya miƙa wa Major hannu, ya ce "Ina ƙara neman afuwarku da ahalinku, a kan abin da nayi muku, ku yi haƙuri ku yafe mini" Major kamar ya maze, ya haƙura ya miƙa masa hannu suka gaisa, Abbu ya din ga Alhamdilillah, Allah ya ƙara muku fahimta. Viper kuwa dama tun da suka fara hayaniya, ya fice ya koma ƙofar gida. Major ya ce "Bari na kira muku mutanen gidan ku gaisa, da mariƙiyar Nabilan" Ya tashi ya sauka falo, ya ce "Magajiya, ki zo ga mahaifin Nabila ne ya zo, kai Nasir ina babarku, ku zo ga mahaifin Nabila da mijin 'yar uwatta ku gaggaisa" Jikin Nasir yayi mugun sanyi, wani irin kishi da fargabar dalilin zuwan Viper da mahaifinsa ya tsaye masa. Aka gabatarwa da Baba kowa, ya din ga yi musu godiya da fatan alkhairi. Bayan tafiyar su, sannan Nabila ta dawo, ake gaya mata su Baba sun zo, ta ji babu daɗi rashin tarar da su, sai dai ta yi wa Abba godiya, jin cewar ya yafe wa mahaifinta, kuma ta san duk jajircewar Viper ce. Ta samu Abba, ta din ga yi masa godiya, da nuna masa farincikinta, a kan yafewa mahaifinta da yayi. Abba ya ce "Eh na yafe masa, amma ban yadda da maganar ki koma gidansa ki zauna ba, ban yadda da wannan ba". Nabila ta ce "Nima dama ba zan koma can ba, amma na gode sosai da sosai da ka yafe masa". Da daddare bayan ta yi sallar isha'i, ta kira Viper, yana ganin kiranta ya ɗaga, ta ce "Hello Vi" "Mmm" "Ashe kun zo gidanmu bana nan, baka gaya mini zaku zo ba, da na dawo da wuri, naga shiryawar Baba da Abbana" yayi shiru bai ce koma ba. "Na san wannan duk ƙoƙarin ka ne, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, Allah ya jiƙan 'yar madara da jaririnta, ya baka abin da ka ke nema duniya da lahira na gode, na gode" "Godiyar ta isa haka, nima na gode" "Ba ta isa ba Vi, ban san me ma zance maka, da zai tabattar da irin godiyar da nake son yi maka ba, na gode sosai da sosai" "Nima na gode sosai " "Tom sai da safe" "Nabila" "Na'am" "Haryanzu kina nan a kan bakanki ha zaki aure ni ba?" "Dan Allah mu daina wannan maganar Vi, a wuce ta dan Allah, ni na riga na gaya maka matsayata, mu yi haƙuri da wannan maganar" Ya ce "Ok, babu laifi" ya katse kiran wayar. ***** Walid ya warke sarai, hannu ya miƙe, sai dai da Viper ya yi masa zancen Abbu zai ɗauke shi, a kasuwa a nuna masa harkar kasuwanci, sannan ya bashi jari, a fara maganar aurensa da Shahida. Walid ya kasa magana yayi shiru yana kallon Viper. Viper ya ce "Menene kuma? Ko ba wannan sana'ar ka ke so ba? Idan da wani abun da ka ke so ka faɗa, sai a san abin yi" Walid ya ce "Anya gatan nan bai yi mini yawa ba Mai zamani? A bani jari kuma a bani auren 'ya?" "Ware, ka cancanci fiye da haka mai laya, yanzu yakamata mu je ko wurin ƙannen mahaifinka ne, saboda su nema maka auren Shahida, ni kuma zan je Lagos ne aiki" "Lagos kuma mai zamani, babu kai babu ɗan mama" Al'amin ya numfasa ya ce "Tafiyata can na cigaba da aiki, ya fi alkhairin zamana a nan. Dama na yi zaton ko Nabila zata aure ni ne, amma ta ce ba ta so na, dan haka zan yi tafiyata kawai, na yi aikina na fi samun kwanciyar hankali da manta wasu abubuwan" "Viper, daga kai har Nabila kuna son junanku, kawai dai rashin fahimta ne. Kaga Jauhar a sadaka ka auret, baka san duk wata wahala da ake sha, wurin neman aure ba. Yanzu ne zaka yi fafutuka da gasken gaske, idan ba haka ba ka bari ta auri wani babu lallai ka iya jurewa" "In biye mata tayi ta wulaƙanta ni?" "Ba wulaƙantaka take yi ba, kai ka fara watsar da tayinta a farko, ka din ga nuna mata da farko, an ce mata ba sa mantuwa, amma ka yi haƙuri ka nemi aurenta, Abbu ya nema maka Aurenta" Viper dai yayi shiru bai ce komai ba. ***** Major ne ya kira Nabila, ta same shi a ɗakinsa, ya ce "Yauwwa babanki ya turo mini baban yaron nan da ya auri 'yar uwakki, wai yana son ya aure ki, zasu kawo kuɗin aure, na ce sai na yi magana da ke, kina ganin kin yarda da nutsuwarsa a yanzu zaki iya aurensa?" Nabila ta yi shiru. "Magana fa nake yi miki Arfa" "Gaskiya Abba ni ba zan iya aurensa ba" "Saboda me?" Ta girgiza kai ta ce "Ni dai kawai a bar maganar nan, ka ba su haƙuri" "To uban meyasa ki ka gayyato shi rayuwarki, so ki ke ace ni na zigaki ko?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Tashi ki je, Allah ya shiryeki" ta tashi sumi-sumi, ta tafi sai dai kuma haka kurum ta din ga jin tausayin Viper. Sumayya ta kira take labarta mata abin da ya faru, Sumayya tayi shiru, ta ma rasa me za ta ce mata. "Sumy ya ki ka yi shiru?" "Nabila me zan ce miki, abin da ki ka yi zalunci ne, ya za ayi ya sakankance, yana sonki zai aureki, amma ki ce ba kya son sa?" "Point of correction, nake son sa dai, amma ba yake so na ba" Ƙarshe sai da suka kusa yin faɗa, suka rabu tsiya-tsiya a wayar. Sumayya da kanta ta kira Abbu, suka gaisa ta fara bashi haƙuri, a kan abin da Nabila tayi. "Bakomai kar ki damu Sumayya, ai macece idan ma tayi haka ba tayi laifi ba, na san halin kayana sarai" "Abbu Nabila na ganin Ba ya sonta ne, kawai dai zai aureta saboda tana kama da jauhar ne" Abbu ya ce "Na fahimceki, ita ma kuma haka, yanzu dai zan ba su lokaci, shi kansa ya zuciya yanzu haka yana hanyar Abuja, can aka kai shi ba Lagos ba kuma, ya ce auren ma ya haƙura, amma ta nan ɓangarenki, dan Allah ki ɗan lallaɓata, ni idan ta kama ma sai na zo da kaina, ba zan so ya tafi yaje ya zauna haka babu auren ba" Jiki a sanyaye Sumayya ta ce "To shikenan Abbu, in sha Allah" Ta sake kiran Nabila, tana gaya mata yadda suka yi da Abbu. Nabila ta kada baki ta ce "Dan Allah Sumayya ki ba wa Abbu haƙuri, ba wai ina ƙyamar ɗan sa bane ba, amma ina yi masa fatan alkhairi a duk in da yake, Allah ya bashi mace madadin Jauhar". Ayshercool 08081012143 102 A ƙule Sumayya ta ce "Kina ganin hakan da ki ka yi shi ne dai-dai? A gidan uban wa ki ke tunanin zai samo madadin matarsa? Ke kin san baki isa ki ƙi aurensa ya bari ki zauna lafiya ba" Nabila ta ce "Lafiya ƙalau zan zauna in sha Allah, kar ki damu da ni Sumy, Allah ya nuna mini aurenki" "Nabila kar ki mayar da abin nan wasa, ya ki ke tunanin mahaifinsa zai ji, kin yi rejecting ɗin ɗan sa?" Sumayya, wai kina ina lokacin da na din ga gwagwarmaya, ina nuna wa mutumin nan so yana wahalar da ni?" "Ramawa ki ke kenan?" "Da zan rama abin da Vi yayi mini, ko kallonsa ba zan iya yi ba, kawai dai ba zan aure shi bane" "Munafuka, kina wani kiransa Vi, kina wulaƙanta musu ɗa, nan ki ka roƙi Allah ya baki kowane irin miji ne, mutum ya nuna yana sonki, amma kina wahalar da shi, zaman gidanku da wannan cin mutuncin ne da ake yi miki bai ishe ki ba, ki ƙarata" Nabila ta ce "Bakomai, na ji na yadda" **** Alhaji mu'azzam ne a ƙofar gidan su Hafsa, ya fi mintuna ashirin yana surutu, amma Hafsa ta yi masa banza ta ƙi kula shi. "Hafsa" ta ɗago ta kalleshi. Ya ce "Meyasa ba zaki yafe mini ki koma ɗakinki ba?" "Meyasa zan koma in da ba a buƙatata? Gara na barka waɗanda kake ƙauna". Ya ce "Na san ban kyauta ba, amma ki yi haƙuri, zan gyara kuskurena" murguɗa baki tayi, ta sake juya masa baya. Murmushi ya yi a ransa ya ce "Komawar ki gidana ita kaɗaice mafita a garemu baki ɗaya" a zahiri kuma ya ce "Shikenan sai da safe" Ba ta kula shi ba, kawai ta shige cikin gida ta bar shi a wurin. Yayi murmushi ya furta mace kenan, duk yadda ake ganin girmansa da mutuncinsa a ƙasa, yana ta bin yarinya ƙarama tana wana shi. **** Viper ne a tsaye a banɗaki, ya sakarwa kansa ruwa, a hankali ya kammala wankan ya fito, jikinsa duk babu ƙwari. Ya shafa mai, yayi shirin kwanciya bacci, gaba ɗaya abin da Nabila tayi sai cin zuciyarsa yake yi. Yana jera

Chapter 108 of 121