ayi masa sannu" guntun tsaki ya ja, ko arzikin gaisuwa ma bai samu daga gareta ba sai surutu.
Lokacin da ya koma, Shahida ta kawo abincin rana, suna zaune a ɗakin Abbu, ya samu har ya tashi zaune ya yi wanka, ya ci abinci.
"Ka dawo?"
"Eh ya jikin"
"Alhamdilillah"
Shahida ta gaishe shi ya amsa, liti kamar wanda aka matsa sai cewa yayi "Wai babarku ba ta san an kwantar da Abbu bane, naga tun jiya ba ta zo ba"
Shahida ta ce "Ai tun da aka kashe Yaya Abba, ita ma ba ta da lafiya, shiyasa ba ta zo ba"
Walid kamar ya zabga wa Liti mari, ko ina ruwansa oho.
Viper ya ce "Muhsin yakamata kuma ku je ku huta".
"Eh bari mu ci abinci tukuna, ko a gidan ka bar mana abin da zamu ci?"
Viper ya harare shi, ya ce "In dawo jiya, yau kuma na hau yi muku girki"
"Dama can ma ai mu muke yi, bayar da order kawai ka ke yi, sai ma idan an yi kai ta cewa bai yi daɗi ba"
Walid ya ce "Yaushe ma ya fara cin abincin, sai da Nabila ta shigo rayuwarsa, yanzu carryover wanda bai ci ba yake yi". Abbu kallonsu kawai yake yi yana murmushi, yana mamakin yadda suka iya zama da Al'amin, gashi dai ba dolensu ba, amma da shi da halinsa suke iya zaune da shi. Suka ci abincin suka tashi suka fita.
Viper ya ce "Shahida ta tashi ta tafi gida, tun da akwai wata mara lafiyar a gida, ba ta yi musu ba, ta tashi ta tafi.
Abbu ya kalli Al'amin ya ce "Aminu yaran nan suna matuƙar ƙaunarka, sai suka ƙara shiga raina, Allah ya ƙara muku haɗin kai"
"Amin, amma meye ya kashe wa Shahida aure? Ina fatan ba wani rashin kyautawar tayi ba"
Abbu ya girgiza kai ya ce "Nima ban san ainihin abin da yake faruwa ba sai yanzu, uwatta ce ta bawa mai kuɗi, da akwai wanda take so, ta ce ita ba shi take so ba, mai kuɗin zata aura".
"Abbu kuma ka bari?"
"Ya zan yi mata, ta dage tana nuna mini 'yar ta ce, sai kwanan nan Shahidan ta same ni, wai ita ta kai shi kotu, Khul'i za su yi, ya sauwwaƙe mata, na tambayeta dalili ta ƙi faɗa, na kira shi mijin nata ya ce shi ma bai san dalilin ta ba, sai da na ritsa uwarta, sannan take gaya mini wai ba shi da lafiya, tsawon shekaru ukun da suke zaune" guntun tsaki ya ja, ya ce "Da ina nan gaskiya ba zan bari ayi wannan abin ba, yanzu shikenan ta zama bazawara"
"To yaya zan yi, makaranta dai nake so ta zo ta koma, gaba ɗaya tausayinta nake ji, halinta ya sha bamban da na uwatta da yar uwatta, ba yadda muka iya da ƙaddara".
Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.
Abbu ya sake numfasawa ya ce "Yakamata na gaya maka abin da nake son na gaya maka, kar lokaci ya ƙure mini"
Al'amin ya tattara hankalinsa a kan Abbu.
"Zuwa yanzu Al'amin babu wani wanda ya san kan kasuwancina sosai, duk wanda na janyo sai yayi ƙoƙarin cutar da ni. Sannan akwai gadonka na mahaifiyarka da kuma ɗan uwanka, sun zama manyan kadarori, kar karɓi abinka ka tallafi rayuwarka, kuma ina son ko bayan babu raina, ka cigaba da jujjuya harkar kasuwancin nan, kar abun da zan bar maka ya ƙare ba tare da ka tsaya da ƙafarka ba"
Viper ya gyara zamansa ya ce "Babu in da zaka mutu ka je"
Abbu ya yi murmushi ya ce "Faɗa kawai ka ke kaima"
Ya rausayar da kai ya ce "Abbu already ina aiki, ni ba zan iya kasuwanci ba"
"Aikin me?"
"Sojoji nake yi wa aiki, ba zan iya haɗawa ba, ko zan haɗa ma, sai dai wani ya riƙe mini, wasu alfarma nake nema ka yi mini"
Cikin sauri Abbu ya ce "Na menene?"
"Na farko, ina so ka taimaka ka jagoranci Abdallah, liti ka mayar da shi wurin mahaifinsa, a nema masa afuwa, dan na san nine silar barinsa gida baki daya, ko ba ni bane, na taka muhimmiyar rawa a hakan.
Abu na gaba kuma, a yanzu Walid ba shi da kowa sai Allah sai ni, maraya ne, yan uwansa ba sa ta tashi, duk masu ƙaramin ƙarfi ne. Ina roƙonka ka sanya mini shi a harkar kasuwancinka, ka bashi babban gurbi, sannan ka aura masa Shahida" shiru Abbu yayi yana kallon Viper.
Ya cigaba da cewa "Na san zaka ga abin wani iri, amma bana zaɓen tumun dare, daga ni har su muna ta ƙoƙarin gyara kura-kuranmu, mu sake sabuwar rayuwa ne. Kuma Walid mutum ne mai amana, ba zai taɓa ci maka amana ba, duk rintsi duk wahala, Walid ba ya cin amana, ni na yarda idan ma ba zaka saka shi a kan naka kasuwancin ba, ka bashi gidana ɗaya, a sayar da sauran kayana, a koya masa harkar kasuwancin katakon, sannan ka aura masa Shahida. Ba kuma dan na cutar da ita ko rayuwarta ba, zan iya yi maka rantsuwa da Allah, ko Walid ba shi da komai, Shahida ba zata wahala ba, ina ƙara tabattar maka da mai amana ne. Shi liti shagon shayinmu yake so, ya ce ko na mutu shi zai gajeta tun da shi ne ya rayata ba ni ba, ya je ya ƙarata da ita, Walid ko duk wani abu da na gada za a ƙarar, dan Allah a bashi ba zan iya biyan bawan Allah nan ba".
Abba ya jinjina kai ya ce "Na ga alama, shikenan babu damuwa idan ma ya fi hakan za ayi masa, sai dai ita Shahidan ka yi magana da ita idan ta amince, ka san halin mata kar ayi abu, azo a ji kunya"
Viper ya ce "In sha Allah ba za a ji kunya ba, Walid mutum ne mai haƙuri da kawaici, kuma mai amana"
"To shikenan, ba zan taɓa maka kayan gadonka ba, amma zan ɗauke shi a kasuwa, zan bashi auren Shahida muddin ta amince, ni ma na shaida ɗawainiyar da yake yi da kai, Allah ya tabattar mana da alkhairi".
Likita ne ya shigo yayi musu bayanin jikin Abbu da sauƙi, jininsa ne ya hau sosai, kuma an samu ya sauka, zuwa washegari za a iya sallamarsa.
Maƙwabta da abokanan kasuwancin Abbu suna ta zuwa duba Abbu, suna ta so su magantu da ganinsa tare da Viper, ya ƙara girma, da kwarjini sannan akwai alamun ƙarin nutsuwa a tattare da shi.
*****
Bunkure ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin sanin abin yi, dan tun bayan da Nabila ta damƙa mata kundin ƙorafe-ƙorafen da zata kai ma'aikatar Shari'a a kanta, ta rasa yadda zata yi. Gashi ma'aikatar shari'ar duk waɗanda ta sani yanzu ba sa nan, an yi musu canjin wurin aiki, tana ta kasa kunne ta ji ta ina za a nemeta.
Tsananin damuwa ya sanya ko baccin kirki ba ta iya yi, sai ta sha tayi mankas tukuna.
Duk da abokan aikinta, na ta ƙarfafa mata gwiwa, da nuna mata cewa za ta iya fuskantar ƙalubalen da yake gabanta. Ga mutane duk sun dawo daga rakiyar Foundation ɗin ta, kuɗaɗen da suke tallafawa ƙungiyar domin taimakon mutane, duk sun daina saboda sun gano cewa cuta ce.
A dalilin Nabila, mutane da yawa suka samu 'yancin yin magana, tare da sanarwa duniya tallafin da aka nema da sunansu, ko aka basu, ana dawowa a karɓa, wasu kuma ma ba a basu.
Sosai social media da gidajen rediyo, maganar bunkure ta yamutsa hazo, ko ina zancen ake yi.
****
Washegari aka sallami Abbu daga asibiti, suka koma gida.
Shahida na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alqur'ani, Viper ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ta yi masa iznin shiga, ya shiga ya zauna, ya dube ta ya ce "Kin gama idda ko?"
Ta jinjina masa kai, ba tare da ta ɗago ba.
"Magana nake son mu yi, shawara ce, ba dole zan yi miki ba, zaki iya cewa a'a idan abin bai yi miki ba"
Ta jinjina masa kai.
"Na san zaki ji abin wani banbarakwai, amma ba zan yi miki zaɓen tumun dare ba, kuma ba dole zan yi miki ba, ina son Abbu ya haɗa aurenki da Muhsin ne, abokina Walid. Na san zaki yi mamaki, ko ki ji babu daɗi, saboda duba da yanayin mummunar rayuwar da muka yi a baya. Dama kowane mutum tara yake bai cika goma ba, duk wani halin kirki na mutum, sai an tarar da shi da wani hali da ba a so, kuma yanzu muna ta ƙoƙarin gyara ɓarnar da muka yi ne a baya. Ina baki tabbacin Muhsin mutumin kirki ne, kuma zaki ji daɗin zama da shi, ya fi ni nagarta da halacci, da zunzurutun haƙuri. Kema kuma na san mutuniyar kirki ce, a dalilinki ina fatan ya ƙara shiryuwa, amma ina baki tabbacin zaki iya dukan ƙirji a gaba, ki ce kin yi dacen mijin aure. Amma ba dole nake yi miki ba, na tuntuɓe ki ne dai da maganar, kafin nayi masa, idan kuma ba kya son sa babu wani abu shikenan shawara ce".
Sai da Shahida ta ji dummm, tabbas Walid ma tsohon ɗan sara suka ne, kuma bata san shi da wata sana'a ba, amma kwana biyun nan da take zuwa asibiti, suka ɗan zauna tare, akwai nutsuwa da dattaku a tattare da shi, kuma karo na farko kenan, da Al'amin ya yi ƙoƙarin yin wani abu a kan rayuwarta, ta san ba zai cutar da ita ba, dan haka ta numfasa ta ce "To yaya duk yadda ka yi dai-dai ne, in dai ka amince, nima na yarda".
"A'a kar ki yi mini haka, ki gaya mini abin da yake zuciyarki, ko kuma dai na fara turo shi ya nemi yardar ki da kansa, amma magana ta domin Allah bamu iya soyayya irin wadda ku ke so ba, sai dai ki koya masa, kin san mazaje we are always serious" yayi maganar yana ɗan murmushi.
Ita ma murmushin ta yi tana sunkuyar da kai.
Nan ya cigaba da koɗa mata nagartar Walid, da ƙoƙarin da ya din ga yi wa rayuwarsa.
Za ta iya cewa, ba ta taɓa zama sun yi hirar kirki mai tsawo da yayan nata ba sai yau.
Da daddare ya bar gidan, ya tafi can gidan da suke zama, Walid suna ta faɗa da liti, a kan liti yayi musu wanki, ya ce ba zai yi ba, ya saka Viper ya dawo da ɗan mama yayi, tun da ya fi jin maganar sa, dama ɗan mama ne yake yi musu.
Viper ya ce "Rabu da shi mai laya, kai ka kusa shiga daga ciki, a din ga haɗa kayan ka masu datti a bayar wanki, ka bar Liti"
"Wace zata aure shi, bai iya komai ba sai saka aiki, daga kai har shi?"
Viper ya ce "Seriously, Walid Abbu zai baka auren Shahida, abin da ya rage maka kawai ka nemi yardarta" waro ido Walid yayi ya ce "Wane Walid ɗin?"
Liti ya yi shewa ya ce "Sai dai kai maigida, Allah ya ja zamaninka ka daɗe ka yi ƙarko irin na dabino, Allah dai ya saka da alkhairi"
Walid ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, uban waye zai bamu aure a haka? Mai zamani ka daina wannan wasan"
Viper ya kwanta ya ce "Ba wasa nake yi ba, da gaske nake, ka nemi soyayyarta kawai, aure zan yi muku, Abbu ma ya san zancen. Kai kuma liti sai dai ka nemo da kanka, tun da na san kai ba gwaninta ake yi maka ba"
Walid ya ce "Dan Allah a daina wannan wasan, wai waye ma zai bani wani aure? Dan Allah ka bari ta samu mutumin kirki ta aura"
Viper ya tashi zaune, ya dafa kafaɗar Walid ya ce "Kai ma mutumin kirki ne, shiyasa ba zan so wata ta samu ba, alhalin ga ƙanwata, ku daidaita kawai sai da safe" yana gama maganar ya kwanta.
Walid ya zauna kamar soko yana rarraba ido, Liti kuwa dariya ya din ga tuntsirawa, saboda har gara Viper ma da Walid, dan shi kamar ma tsoron mata yake ji, shi ko da wasa bai taɓa tare budurwa ba.
Liti ya din ga tsokanarsa, yayi masa banza ya kwanta, hango Shahida yake yi, yarinya nutsatsiya yar gayu, wai kuma ta aure shi shi dai abin bai yi masa tsari ba.
Washegari za su je duba Abbu da yamma, kamar ya fasa zuwa, saboda gaba ɗaya kunya ce ta kama shi.
Kasancewar Viper ya riga su tafiya, ya sanar wa Shahida, su Walid za su zo duba Abbu, dan haka ta shirya, za su yi magana ita da Walid ɗin.
Duk abin nan, rahila ba ta san me ake shiryawa ba.
Sai bayan la'asar, su Walid suka zo, duk yadda yake ɗan sakin jiki da Abbu su yi hira kasa yayi, ya din ga mutsu-mutsu, kamar ya nutse a ƙasa, liti yana ankare da shi, kamar ya yi dariya.
Liti ya ce zai je ya dawo, ya fita ya yi nasa wuri, bayan sun yi wa Abbu sallama, a ƙofar gida Viper ya ce "Na yi mata magana, za ta fito ku yi magana, mu haɗe a jungle"
"Dan Allah Viper ka ce da wasa ka ke yi, ni wallahi ban san me zan ce mata ba, wallahi kunya nake ji"
"Malam yakamata ka girma, ka yi mata tatsuniya if you like" zai sake magana, suka yi ido huɗu da Shahida, ta fito cikin doguwar rigar abaya maroon.
Viper ya yi gaba yana murmushi, Walid ya ɗan diririce.
Ta ƙaraso tayi masa sallama ya amsa, ta saci kallonsa, dogo ne shi ma, sai dai bai kai Viper jiki da tsawo ba, kuma yana da haske sosai, sai dai laɓɓansa baƙi ƙirin, idanunsa kuma jajaye, yana da dogon hanci da gemu kaɗan ba mai yawa ba.
"Sannu ya jikin Abbu?"
"Da sauƙi Alhamdilillah"
"Amm na san wataƙila mai zamani ne ya takura miki, idan ba kya so na, ki rabu da shi kawai, Allah ya zaɓa miki miji nagari, rigimarsa ce kawai ta saka ya ce wai zai aura mini ke" yadda duk yake a rikice ne ya sanyata murmushi ta ce "Yaya Muhsin, mu yi addu'a mana, bamu san me Allah ya ɓoye ba, mu nemi zaɓin Allah, in dai nima zaka kula da ni, ka din ga lallaɓa ni kamar yadda ka ke yi masa ai ba wani abu" sunkuyar da kai ya yi yana murmushi, sai dai kamar ya zuba da gudu dan kunya. Bai fi mintuna goma ba, yayi mata sallama.
Da ya koma can gidan da suke, kamar wanda ya aikata zunubi, liti ya saka shi a gaba, ko murmushi yayi, sai ya ce tunanin Shahida yake yi, ya hana shi sakat.
Da daddare Shahida ta kira Viper, ta tambaye shi ya suka je gida. Maimakon ya bata amsa, sai ya miƙa wa Walid wayar.
Tayi masa ya yaje gida, sannan ya ce zai ɗauki lambarta a wurin Viper.
Washegari da sassafe, Viper ya shirya ya fice ya bar su, dan yai zai koma wurin likitan ƙwaƙwalwa, kuma yana son ya ga Nabila.
***
Ƙarfe tara na safe, Nabila ta fito falon madam Halima, hannunta riƙe da jakarta, da court ɗin ta, kawai ta ga Viper a falo, suna magana da Madam.
"Mummy good morning"
"Morning sweetheart, kin fito?"
"Eh, Good morning" tayi maganar tana kallon in da Viper yake, bai amsa ba, ya ci gaba da magana da Madam.
Kitchen ta nufa, kusan mintuna biyar, madam ta tashi ta shiga ɗakinta, Viper ya bi bayan Nabila.
Sai da ta tsorata da ganinsa unexpected.
Wuri-wuri ta yi da ido tana kallonsa.
Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce "Abin da ki ka yi mana kina ganin kin kyauta ko? Nayi tafiya mai hatsari, ya na je ya na dawo, bai dame ki ba? Kin yi mini laifi amma ba ki iya bani haƙuri ba, yau zamu koma asibiti you don't even care to call me. And a gabana ki ka bi kankarofi, duk dan ki tura mini takaici".
Tayi shiru ta ɗan kalle shi ta ce "Ba faɗa ka ke yi mini ba, komai ka yi ta hantarata"
Ya ce "Ke ki ke yin abin da zan hantarekin ai. Akwai muhimman batutuwa da yakamata muyi discussing, kawai kina wani fushi mara dalili.
Ana ta matsa mini lamba, za ayi posting ɗina wurin aiki, da zarar na kammala aikin da nake yi a kan Indabo, ina son ayi aurenmu dai-dai lokacin da zan tafi aiki"
"Kai da wa?"
"Ni da waye a nan wurin?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa.
"Allah ya baka madadin matarka da ka rasa, ba zan iya aurenka ba Vi, i fulfill my work on you, amma mu bar wannan maganar Please"
Sai da ya nazarceta sannan ya ce "Ƙarya ki ke yi mini da ki ka ce ki na so na kenan?"
Ta ɗan ja da baya, saboda tsoron yadda idanunsa suka fara sauyawa ta ce "Ko ma ya ne, kai ka fara discouraging ɗina, a lokacin da ka yi fatali da tayina, ka ce mini ba wannan maganar, bayan jauhar baka kallon kowace mace. Nima kuma na gamsu da hakan ba zan iya auren mijin 'yar uwata ba. Amma Alhamdilillah na cimma burina a kanka, tun da ka dawo yadda take fata kafin ta mutu".
"Ba kya so na kenan? Ba zaki aure ni ba?" Ta jinjina masa kai, tana kawar da kanta gefe alamar eh.
Juyawa ya yi, ya fara takawa, wayarsa ta fara ringing, ya cirota ya saka a kunnensa ya ce "Na'am"
A razane ya ce "What Walid ɗin? How?"
Ayshercool
08081012143
100
Cike da gigicewa ya ce "Gani nan, kar ka sanar da kowa"
Saboda rikicewa, sai ma ya rasa ina ne hanyar fita, sai daga baya.
Nabila ta ce "Vi menene? Meyafaru?" Bai kulata ba, yana ƙoƙarin fita, Madam Halima ta ce "Au nan ka biyota, na zata tafiya ka yi ai" sai dai yanayin fuskarsa ya nuna mata akwai damuwa.
"Viper menene? Meyake faruwa ne?"
"Walid, gayen nan da muke zuwa da shi, na baro su a gida, ya fita yin refiiling, shi ne bai koma ba, Abdallah ya bi hanya ya tarar da cylinder gas ɗin a gefen hanya, da takalmansa da agogonsa, that means ɗauke shi aka yi" tuni kamanin Viper suka canza, saboda tashin hankali.
Yana ƙoƙarin fita, madam ya ce "Wait Viper, tattara hankalinka ka nutsu, tunani al'amarin nan yake buƙata da nutsuwa, ba gaggawa ba.
Yanzu na san Joseph ya ƙaraso, zai fita da Nabila, ya kai ka ku je a tabattar da abin da yake faruwa, sannan ka kira Oga ka sanar masa da halin da ake ciki" ya jinjina kai ya wuce cikin hanzari ƙirjinsa na bugawa da sauri.
Da sauri Nabila ta ce "Bari na bi shi Mummy, kar ya je yayi wani abun, kin san shi da zuciya da wutar ciki"
"Kya ma gama gulmarki ne daughter, Allah ya bayyana shi cikin aminci" ta amsa da Amin.
Kafin ta ƙarasa har ya riga ya shiga mota, sai da ta haɗa da sauri, sannan ta ƙarasa ta shiga baya, kasancewar gaban motar ya shiga.
Tana shiga ta ji Viper yana waya "Liti kar ka matsa daga wurin, gani nan zuwa, kuma kar ka gaya wa kowa, ka kira wayarsa ne?"
"A gida fa ya manta ta a kan window ya fita"
"Shikenan gani nan zuwa"
"Nabila na ta son tayi masa magana, amma ta san a ƙule yake da ita, dan haka ta ja bakinta ta tsuke"
A haka suka isa dai-dai wurin da liti yake, yana ta buge-bugen waya.
Yana zuwa ya tarar da Liti a hanyar shiga rukunin kamfanunnukan da a bayan su gidan nasu yake, bai taɓa komai ba, yadda ya tarar da takalman walid, da cylinder gas da agogonsa a yashe.
Viper ya yi shiru, yana nazartar wurin, Joseph ma fitowa ya yi, suna dudduba wurin, ya kalli Viper cikin broken English ya ce "Oga, da alama sai da aka yi kokowa da shi kafin a tafi da shi"
Su na nan tsaye Viper yana duba wayarsa, sai ga motar Civil defense sun zo wurin, su ka yi wa Liti tambayoyin da yakamata, suka yi investigation a wurin. Su ka yi ta bawa Viper haƙuri, da ƙoƙarin kwantar masa da hankali.
Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Ka yi haƙuri, in sha Allah yana cikin ƙoshin lafiya, bari na tafi"
"Ki shiga mota, mu ajiye ki, zan bi bayan civil defense ɗin nan, na ji me ake ciki"
Ta jinjina masa kai, ta shiga mota suka tafi suka ajiyeta a wurin aiki.
"Idan kin kammala, ko za ki je wani wurin, ki kira ni kar ki fita, i don't think you are safe".
Nabila ta ce "Ok shikenan na gode"
Abu kamar wasa, aka shafe kwana biyu, babu Walid babu ɗuriyarsa, hakan ya ƙara ɗaga hankalin Viper fiye da tunani, tun yana ɓoye-ɓoye, har maganar ta fita, sai da ya sanar da Abbu. Duk da ba wata shaƙuwa tsakanin ta da Walid, amma ta san shi da yayanta, kuma yana nuna damuwa da abin da ya shafe su. Sosai hankalinta ya tashi, Abbu kansa da shi ake ta zarya.
Alhaji mu'azzam ma sai kwantarwa da Viper hankali yake yi, liti ya fi kowa shiga damuwa, dan kuwa har wata irin muguwar rama yayi, a ƙa'ida shi ne yakamata yaje yayi refiiling ɗin, ya tsaya jan jiki, Walid ya zuciya ya tafi ya yo, tsautsayin ya faɗa masa. Duk in da ake tunanin samun Walid, an duba ba a same shi ba, Liti har wata irin rama yayi.
Duk ƙaunar Viper da Abinci, baya gabansa, ba ya iya ci, saboda damuwa da tashin hankali.
Gashi yana ta gargaɗin Nabila a kan yawo anyhow, dan ya san tun da aka farmaki Walid, a kowane lokaci za a iya sake kai ma wani na kusa da shi hari.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, yana zaune ya kasa bacci, yana ta tasbihi, yana fatan Allah ya kuɓutar masa da Walid, wayarsa ta fara ringing.
Cikin azama ya ɗaga, ya saka a kunnensa ya yi shiru.
"Ban yi mamakin jin idonka biyu ba, saboda sai da na duba, na duba na tabattar da wanda na kama, shi ne na kusa da zuciyarka, da taɓa shi zai tabattar maka da ina sane da kai, ban manta da kai ba".
"Ina ka kai Walid, kar ka bari sabgar nan ta juye zuwa wani abu daban, ka fito da shi, duk in da ka kai shi"
"Ta daɗe ba ta juye ba, ka manta tare ku ka din ga yi mini aiki a baya, ai ina ganin kamar shi haryanzu ba shi da wani muhimmin tabo, da bangar siyasa tayi masa kamar kai.
Ai talaka ba shi da wani amfani, ban da ku yi mana hidima, amma kun dage zaku kai ni ƙasa, zan saki Walid ne, a lokacin da wa'adin zaman Abdul yasar ya ƙare a gidan yari. Sannan zan sake duba abu mai muhimmanci a gareka, na yi masa ɗaurin talala, yana raye amma kamar matacce, kamar yadda ka saka aka ɗaure mini ɗa a ƙasashen waje. Na samu labarin kana aiki a kaina, sai ka ga bayana, gani gaka, ɗan halak ka fasa".
Viper ya ce "Wannan shi ne kuskure na biyu mafi muni da ka aikata Indabo. Ni da kai muke harƙalar nan, kuma batun ɗanka, hukunci aka yi masa dai-dai da abin da yayi. Ina mai gargaɗinka da kakkausar murya ka saki Walid, idan ba haka ba zan razana duniyarka da abin da baka taɓa zata ba, awanni arba'in da takwas kawai ka ke da su, kuma ka fara ƙirgawa daga yanzu" yana gama maganar ya kashe wayar, ya dafe kansa, cike da wata irin nadama da danasanin biye wa Indabo ya din ga aikata ɓarna.
Wato a duniya idan amfaninka ya ƙare kai ba a bakin komai ka ke ba, meyasa zai ɗauki Walid maimakon ya ɗauke shi, tun da da shi yake yi, ba Walid ba.
Da sassafe Viper ya tafi barrack, saboda Nabila, yana tsoron ita ce next target na indabo, tun da tare suke yin komai da ita, sai dai tayi noticing rama da kuma damuwa a tattare da shi.
Tana ta shiri, yana falon madam yana jiranta, gani yane da ya kawar da kai, komai na iya samunta.
"Vi" ya ji ta kira sunansa.
"Ka karya sai mu fita" ya girgiza mata kai bai ce komai ba.
Ta fuskanci damuwa na ƙara saka shi miskilanci da rashin magana.
Nabila ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ka ci ko kaɗan ne, duk ka yi wani iri"
"In ci Abinci ban san halin da ɗan uwana yake ciki ba? Shi ya ci? Duk a dalilina, shikenan duk wanda ya raɓe ni a haka rayuwarsa za ta ƙare a wahala da tashin hankali, menene laifin Walid ne?"
Cikin rauni ta ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 106 Chapter of 121