Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
105 / 121
ina dai tunatar da kai muddin ka gauraya halal ɗinka da haram, babu in da zaka je wallahi. Kuma ka ji tsoron Allah, kar masu ƙarfi su din ga amfani da kai, a kan marasa ƙarfi, saboda kana saka wannan kakin lokaci ne" Sosai kunya ta kama Nasir, saboda yadda asirinsa yake nema ya tonu, na ya karɓi cin hanci, ya din ga matsawa Nabila da ƙoƙarin daƙileta a kan nata aikin. *** Cikin dare hasken farin wata ya gauraye ko ina, Viper na tsaye a bakin window, yana shan sigari, hannunsa ɗaya yana kallon wayarsa, kwanaki shida kenan rabon da su yi waya ko ya sanyata a idonsa, babban mamakin da ta bashi, yadda ƙiri-ƙiri ya nuna mata yayi fushi, amma ko ta sake neman sa. Haka kurum ya ji ya ƙara fusata. Ya harɗe ƙafarsa, yana ci gaba da shan sigarin, kawai sai watarana ta faɗo masa, Jauhar ta tsare shi a gida, ta hana shi fita ko ina, kuma ta bashi kara uku na sigari kawai. Cikin dare ta yi bacci, ya tashi ya fita tsakar gida, ya shiga banɗakin tsakar gida, ya sha son ransa, ya daɗe hayaƙin ya ragu, sannan ya koma ɗakin ya kwanta. Ashe tun da ya tashi ya fita, tana kallonsa, yana kwanciya ta tashi ta matso kusa da shi, ta saka hannu ta matsa bakinsa, ta sinsuna, dan ta tabbatar masa ta san me yayi, ba ta ce masa komai ba, ta juya ta kwanta. Kamar wanda ta kama yana alfasha, yayi tsuru-tsuru, ya rasa me ma zai ce mata, kawai ya basar. Aka jima yana ƙoƙarin ya rungumeta, dan ya mantar da laifin da yayi, ta tashi ta bar masa gadon, ta yi alwala ta tayar da salla. Asubar fari ba ta tashe shi ba, yaje masallaci ya dawo, a gida yayi azkar, ya din ga 'yan kame-kame, amma taƙi kula shi, har gari ya waye, sai da ya gaji ya ce "Ni fa guda uku na sha kawai ba da yawa ba" Ta kalleshi ta ce "Me fa?" "Sigarin" ta ɓata fuska ta ce "Hakan ya tabattar mini da zaka iya cin amanata wataran, ka yi abu ban sani ba" Ya girgiza kai ya ce "Ai uku ce kawai ba wata mai yawa ba, ki ke wani haɗe rai " "To Allah ya baka haƙuri, na ga kamar na matsa maka" daga haka ta ci gaba da sabgarta. Ranar ba ta hana shi fita ba, ya zauna bai fita ba, ko zata huce, har da yi mata aikin gida, amma ya kasa cewa ta yi haƙuri, ta tabbatar da ya sha jinin jikinsa, duk ya damu, amma ya kasa ba ta haƙuri. Duk sallolin ranar a jam'i ya yi su. Kafin ya dawo daga sallar isha'i, ta sha kwalliya, yana dawowa ta rungunmi abin ta, kamar ba fushi tayi da shi ba, iya punishment ɗin nan da tayi masa, sai da ya ji kamar ya shekara a prison. Jauhar akwai iya dealing ta cikin ruwan sanyi, a lokacin babu wani abin da yake shakka irin yi mata laifi, saboda ta riga ta sanshi, ciki da bai ta san hanyoyin hukunta shi. Sakin guntuwar sigarin yayi, ya koma ɗaki ya kwanta ya cigaba da tunaninta. Da haka wani nannauyan bacci ya ɗauke shi, sai dai kasancewar da ita ya kwanta a ransa, sai ya din ga mafarki da ita, mafarki mai cike da shauƙi da nishaɗi irin na ma'aurata. "Master salla fa, zaka rasa sallar asuba." tayi maganar tana shafa sumar kansa. Ƙanƙameta ya ƙara yi, yana tura kansa cikin wuyanta, da yake fitar da daddaɗan ƙamshin turaren da yake matuƙar son jin tashinsa daga jikinta. "Viper wai ina zaka shiga a cikin pillown nan ne? Wai ko dai ka sha wani abu bamu lura ba, tun ɗazu fa muke tashinka, ka tashi mu yi salla dan Allah" A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa ya ga hasken fitilar solar, ya haske ɗakin, sai a lokacin ya lura da ya ƙanƙame pillow. Yayi miƙa tare da yin salati, ya kalli liti da yake tsaye a kan sa ya ce "Akwai gas ne?" "A'a ɗan kaɗan ne sosai, sai an yi refiiling ma zamu iya dafa karin kumallo". "Ɗora mini ruwa, ku yi sallarku zan yi wanka" "Wai Viper meyake faruwa ne kwana biyun nan, ko ka fara dawowa bil adama ne? Ni ina cewa ka yi wa addini hidima meyake faruwa" Ashar Viper ya yi masa, ba shiri liti ya ce "Allah ya baka haƙuri, ya ƙara lafiya" Walid kuwa dariya yayi, ya ce "Allah ya ƙara, uban son jin ƙwaƙwaf". Bayan sun karya Baba ya kira Viper a waya, ya ɗaga suka gaisa, ya ce "Aminullahi, dan Allah idan baka komai zuwa azahar ina son ganinka" "To Baba in sha Allah zan zo, nan gidan zan zo na same ka?" "Eh dan Allah" "Zan zo in sha Allah" "Yauwwa Allah ya yi maka albarka" Viper ya amsa da Amin. Ɓangaren Nabila ita ma kwanaki bakwan nan da suka yi, ba sa magana da Viper, abin ya dameta, ƙishirwar son ganinsa ta addabeta, ga ayyuka sun fara yi mata yawa, 'yat shaharar da tayi ta kwanan nan, ya sanya take ta samun cases ko ta ina. Ban da masu nuna suna sonta, manyan mutane da suke sonta da aure. Yau da mafarkin da tayi ta tashi a zuciyarta, mafarki tayi da mai kama da ita, wadda take da tabbacin jauhar ce. Tana nuna mata inuwar mutumin da yake ɗaure cikin sarƙa a baya, yanzu babu sarƙar, sai dai daga yanayin inuwar tasa, kamar a galabaice yake, duk da babu sarƙar sai tangaɗi yake yi. Tana murmushi ta cigaba da nuna mata shi, ta nufi in da take nuna mata, sai dai da ta waiwaya ba ta ganta ba, tana ƙoƙarin ƙarasawa in da mutumin yake, kawai ta farka daga baccin. A hankali ta furta Viper, a gurguje ta shirya, tayi ta trying lambarsa, amma yaƙi ɗagawa, ta din ga jin ko me zai yi mata, yakamata ta kira shi, ta ji ya yake. **** Ko da Viper ya je gidan su Jauhar, ya tarar da motoci a ƙofar gidan, bai damu da ko me ake yi ba, ya kira Baba ya ce masa gashi nan yana ƙofar gida. Baba ya ce ya shiga kawai, ya ƙarasa ya shiga, babu wanda ya kula a mutanen gidan, sai hafsa da suka gaisa ya shiga ɗakin Baba. Alhaji mu'azzam ya tarar, da Abbu, da kuma shi kansa Baban. Gefe ya samu ya zauna a ƙasa ya gaishe su, sai dai da ya zo kan Abbu kamar an yi masa dole, haka ya gaishe shi. "Ya gida ya ƙoƙarin Kuma?" Baba ya tambayi Viper. "Lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Ina yan uwan naka?" Viper ya ce "Su na gida, nikaɗai na zo". Baba ya ce "babu laifi, Al'amin" "Na'am Baba" "Na san zaka yi mamakin kiranka da muka yi, babu tsammani da wuri haka. To bakomai bane ya janyo, Nabila ta same ni, tayi mini wata magana ne, kuma nima naga hakan yakamata, duba da yadda abubuwa suka wakana. Al'amin su iyaye, ba a fushi da su, kuma duk lalacewarsu iyaye ne, balle babu lalacewa a cikin iyaye, yakamata ka sasanta da mahaifinka, yanzu ina jauhar, ina mahaifiyarka, ina ɗan uwanka, ko da kuɗi ba zaka sake ganinsu a gidan duniya ba. Dan haka ka yi haƙuri, mun san mu masu laifi ne a wurinku, amma ku yi haƙuri a yafe ya wuce dan Allah ba dan halinmu ba". Viper ya yi shiru, kamar mai nazari amma bai ce komai ba. Abbu ya ce "Al'amin, nauyinka da nake ji, ya sanya na kasa nemanka gaba da gaba na nemi afuwarka, na san in dai dan halina ne, da abin da na aikata maka, ba zaka sake kallona a matsayin mahaifi ba, amma ba dan halina ba domin Allah. A ƙaddarar rayuwarmu, na ɗauki darasi da dama, daga illar da mutum zai yi wa rayuwarsa, shi ne auren mace domin buƙatarsa kawai, ba tare da tunanin abin da gobe ka iya haifarwa ba. Duk da ni a zatona dan gobenku na auri Rahila, amma ta ci amanata, kuma nima na san da laifina na rashin bibiya da tantance abin da take ɗora ni a kai, amma dan Allah ka yi haƙuri Al'amin, ka yafe mini ka dawo gida mu yi rayuwa a ɗan abin da yayi mini saura na rayuwata" Alhaji mu'azzam ya ce "Viper, ka yi haƙuri dan Allah, duk wani abu da ya faru, ya wuce tun da bawan Allah nan shi yayi silar zuwanka duniya, kuma wani abin idan bai yi maka ba, wani yayi maka, yana cikin tashin hankali da damuwa sosai" Viper ya numfasa ya ce "Ko a baya ni ban ƙi Abbu ba, ina matuƙar ƙawazucinsa da son kasancewa tare da shi, Abbu shi ne ya ƙi ni ya kore ni, amma tun da yanzu ya nemi na dawo shikenan, ya riga ya wuce. Amma ni a yanzu na girmi zaman gida, ba zan iya rabuwa da su Walid ba, sai na tabattar da rayuwarsu ta inganta suma, kamar yadda suka rayu da ni lokacin da kowa yake mini kallon mara amfani. Kuma idan na koma gidan nan, zai iya cigaba da haddasa husuma, wanda ni kuma bana fatan hakan". Abbu ya ce "Hakan ma na gode Al'amin, Allah ya ƙara shirya mini kai, dan Allah idan ka samu dama, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ka zo gida, ina son mu yi wata muhimmiyar magana da kai" Viper ya jinjina kai, Baba ya ce "Bari a kawo abinci mu ci baki ɗaya" Al'amin ya ce "Baba ayi mini uzuri dan Allah, ana jirana ne, ayi mini afuwa" ya fita ya sanya takalmansa ya tafi. Rarrashin Abbu suka din ga yi, saboda yadda jikinsa yayi sanyi, dan gani yake yi, kamar da wani abun a ran Al'amin haryanzu, duk da ya san halinsa farin sani, ba kowane lokaci ake iya gane yanayin sa ba. *** Washegari Nabila ta kira Abbu a waya, domin ta ji ya ake ciki, ko Al'amin ɗin ya saukko?. Abbu ya ce "Kin san ɗan nawa hukuma ne sai da rarrashi, ya ce dai ya wuce, amma bai tsaya mun ci abinci tare ba, yau dai ina jiransa, ina son ya zo zamu yi magana da shi, idan ya zo kin ga sai na ɗan ƙara saka ran ya saukko ko?" Sai ya ba wa Nabila tausayi, ta ce "Abbu ka kwantar da hankalinka, Viper yana sonka haryanzu, shi ba abubuwan da ka yi masa ne suka dame shi ba, korar da ka yi masa ce kawai ta tsaya masa, amma tun da ya ce maka ya yafe, ya yafe ɗin ne, dan Allah ka kwantar da hankalinka Abbu, idan ma bai zo ba na yi maka alƙawarin kawo maka shi har gida in sha Allah" Abbu ya ce "To shikenan, na kwantar da hankalina, Allah ya saka miki da alkhairi" "Amin bakomai Abbu, sai anjima" Shahida ita tayi girke-girken zuwan Al'amin, Rahila na gefe tana kallonsu, sai yan surutai take da ƙanan maganganu saboda ƙwaƙwalwarta ta riga ta taɓu, amma har aka yi sallar magariba Viper bai zo ba. Hakan ya ƙara sanya Abbu karaya nesa ba kusa ba, domin kuwa yana da muhimmiyar magana da yake so su yi. Shahida tayi ta ci gaba da bashi haƙuri, amma a washegari ma still babu Viper, babu dalilinsa, tun Abbu yana sanya ran ganinsa har ya sare. **** Viper yana ganin kiran Nabila, amma ya shareta. Message ta turo masa "Ka ɗaga wayata, is an emergency" Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yana hura hanci. "Vi wai dan Allah meyake damunka ne, kai mutum nawa ka yi wa laifi kai ko neman yafiyar ma baka yi, kai shikenan komai naka babu sauƙi, Abbu ya nemi afuwarka, amma ka yi burus, ya ka ke so yayi ne?. Idan shi ma ya mutu sai ka huta, ni dai nayi iya yi na, sauran na bar wa Allah, ban san ya zan yi maka ba kuma, Abbu yana Asibiti ya yanke jiki ya faɗi, ana addu'a Allah ya sa ba ɓarin jikinsa ne ya taɓu ba, yana ta kirana a waya, yana gaya mini kamar baka yafe masa ba, ya nemi ka je ka ƙi zuwa, to yanzun ma Viper idan ka yi ra'ayi ka je, idan ba ka yi ra'ayi ba shikenan, ni fara gajiya da halinka" Ba tare da ta kashe wayar ba, ya ajiye wayar, yana duba agogon hannunsa, sauran awa ɗaya ya shigo garin Kano, ranar da ya baro wurinsu, aka tura shi Jos, kuma yana sane da kiran da Abbun yayi masa, dajin da yaje ko network babu. Sai dai ƙirjinsa ya din ga bugawa, hankalinsa yayi mummunan tashi, ya shiga fargaba da zullumin rasa abu mai muhimmanci a rayuwarsa karo na babu adadi. Ayshercool 08081012143 99 Har zai sake bin Nabila a waya, kawai ya tuna yadda ta ɗaga masa murya, ya ɓata masa rai ƙwarai da gaske, kawai ya fasa kiranta ya kira Walid a waya. Walid ya ɗaga ya ce "Mazaa ka ƙaraso ne?" "Ina hanya, yarinyar nan ta kira ni ta ce Abbu yana Asibiti, ka je ka bincika mini" Cikin tashin hankali Walid ya ce "Asibiti kuma? Wane Asibitin? Nabila ce ta gaya maka?" Viper ya ce "Ban san wane asibitin ba ne, ka tambaya mini kawai ka bincika mini, idan ma mutuwa yayi kawai ka gaya mini ba wani abu" "Ahh no, in sha Allah yana raye, tambeyata yana wani Asibitin?" "Manta da ita, ka duba mini kawai" "Ok yanzu kuwa in sha Allah" Allah ya sa yana wurin shayinsu, dan haka ya tashi ya tafi gidansu Viper, ya rasa wa zai aika gidan, Shahida ta fito hannunta riƙe da leda. Gaida Walid tayi, ya amsa. Ya ce "Ya ake ciki, mai zamani ya kirani, ya ce an kwantar da Abbu a asibiti na zo na bincika masa" Ta kalle shi ta ce "Dan Allah da gaske shi ne ya ce ka zo ka bincika masa?" "Eh mana, yanzu muka gama waya da shi ma" Ta ce "Damuwar yaƙi zuwa, ya sanya Abbu ya faɗi, Abbu yana ta roƙon ya yafe masa amma yaƙi damuwa da hakan" tayi maganar tana share hawaye. "Kin ga ki daina kuka, ya gaya mini ya zo sun haɗu a gidansu jauhar, har Abbu ya buƙaci ya zo su yi magana, wai wani wuri aka tura shi a Jos, wurin ko network babu, shiyasa bai zo ba, amma wani Asibitin ne?" "Can zan je yanzu, in da muke ganin likita ne" suka rankaya suka tafi, yana ta bata haƙuri. Ga mamakinsa a can suka tarar da Nabila da Sumayya, har da Murtala abokin aikin Sumayya. Suka gaisa da Nabila, cikin damuwa Nabila ta ce "Oga walid, Vi ba ya kyautawa ko kaɗan, wane irin abu yayi haka fisabilillahi?" "Allah ya baku haƙuri, mun gode sosai da kulawarku a kan babanmu" Nabila ta ce "Ai ba dan shi muka yi ba, dan Allah muke yi, dan kuma ƴar uwata, ayi mutum sai zafin rai, komai ba zai yi a hankali normal kamar kowa ba" Walid ya ce "A'a fa, muna fa kawar miki da kai duk da haka, kar ki ƙure mu Barrister, ba fa haka Jauhar take yi mana ba" Nabila ta ce "Taɓ ai ita wannan, idan ana ganin ɗan aljanna a duniya sai a nunata, ina zan iya, wataran sai baƙin ciki ya kasheni. Kayi ta yi wa mutum magana, amma ya gagara responding ma, ya ƙame yana harararka" Yayi murmushi ya ce "Yanzu yaya mai jikin?" "An yi masa alluran bacci ne, an ce mu jira kar wanda ya shiga sai bayan 2hours tukuna, amma jikinsa Alhamdilillah. Nima sumayya ce ta gaya mini ba shi da lafiya, sun yi waya da wannan sistern ta shi" tayi maganar tana nuna Shahida. Tun da Nabila ta fara magana Shahida take kallonta, a nan take ƙara gano bambancin Jauhar da Nabila, Jauhar ba zata taɓa reacting a hasale haka ba, komai girman laifin da ya yi mata kuwa. Wannan kuma a tsaye take, ba ta ɗaukar komai a hankali. Har mamakin yadda take faɗar maganganu a kan yayanta take yi. Viper ya sake kiran Walid a waya, "Ya mutu ne ko kuwa?" "A'a lafiyarsa ƙalau, yana samun kulawa ta musamman" "Walid, dan Allah kar ka ɓoye mini, ba wani abu ka gaya mini kawai, ba yau na saba ji ba" yayi maganar haɗe da wani irin wahalallen numfashi na razani. "A'a wallahi da gaske nake yi maka, muna tare da Nabila ma, ko na baka ta tabattar maka" "A'a, tura mini adress ɗin, yanzu zan ƙaraso in sha Allah" Shahida dai gefe ta koma ta zauna, tana ta kallon Nabila, babu yadda za ayi ka ce ba Jauhar ba ce ba. "Haryan ƙoƙarin tantancewa ki ke yi ne?" Ta ji maganar Walid unexpected. Ta ce "Eh wallahi, haryanzu na kasa yadda, abin mamaki yake bani" Yayi murmushi ya ce "Haka ne" Sai da aka yi kusan awanni uku, sai ga Viper, tamkar an hankaɗo shi, ya yi duhu sosai da sosai, idanunsa jawur, yana zuwa Walid ya miƙe ya nufe shi. "Walin yana ina?" "Yana cikin ɗaki, likitoci sun ce kar a shiga" ai take ya ture Walid, ya nufi ɗakin, ana kar ya shiga, amma ko waiwayowa bai yi ba ya shiga. Wata nurse ya taho ta ce "Ya za ku bari ya shiga, isasshen bacci ake so yayi" Walid ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, yanzu a kan ku hana shi shiga, duk sai ya tayar mana da hankali, ku ƙyale shi dan Allah". Viper kuwa gaban gadon Abbu yaje ya durƙusa, ya ɗora hannunsa a kan cikinsa, ya tabattar da yana numfashi, sai dai still ya kasa yarda, gani yake kamar Abbun ya mutu ne. Ya cigaba da ta tattaɓa duk wasu sassa a jikin Abbun, domin tabattar da yana raye. Caraf ya ji Abbun ya riƙe hannunsa, ya ce "Al'amin" "Na'am, sannu ya jikin naka?" "Na ce ka zo, amma kaƙi zuwa, ko dai haryanzu baka yafe minin bane ba, k yi haƙuri, idan baka yafe mini ba na mutu a haka, na san sai Allah ya tambayeni, tun da kana da hakki a kaina" "Dan Allah ka daina maganar nan, kaima sai ka tafi ka barni? Ba ƙin zuwa nayi ba, aiki aka tura ni wani daji can jos, shiyasa ba wai ƙi nayi ba" Ya kalli Viper ya ce "Aikin menene haka?" "Zan gaya maka amma sai ka warke tukuna in sha Allah" yayi maganar yana shafa saman hannun Abbun. "Matso na rungumeka nima, nayi kewarka sosai" Viper ya gyara zamansa, ya ɗora kansa a ƙirjin Abbu. Ya ɗora hannunsa a kan sumar Viper ya ce "Lallai kana cikin maraici, da jauhar na nan ba zan ganka da wannan sumar ba, Allah ya yi mata rahama" Viper ya yi shiru ya kasa magana. "Al'amin" "Na'am" "Kana ganin idan muka nemi auren yar uwar jauhar za su bamu? Ina son yarinyar ita ma" Viper ya ɗago ya ce "Ka samu ka koma baccinka, zan je na yi salla" Abbu ya ce "To, ka ci abinci ma, ina ga Shahida ta kawo abinci, sauran yaran nawa duk su ci abinci, na ji daɗi yadda duk suka zo suka tsaya tare da ni, Alhaji Bashir ma bai daɗe da tafiya ba, na ji daɗi sosai da sosai." "Tom, amma ka yi shiru" ya fita. Ya tarar daga Nabila sai Walid, da Shahida, liti ma ya zo duk suna zazzaune. Yana fitowa suka fara tambayar sa, ya jikin Abbun. Fuskarsa babu walwala ya ce "Da sauƙi har ma mun yi magana, bari na je na samu wuri na yi sallar la'asar" Nabila na nan zaune, jira take yi, Alhaji mu'azzam take yi wa kwatance, zai zo ya duba Abbu. Bayan mintuna talatin, liti ya amsa waya, ya kalli Nabila ya ce "Viper ya ce ki je" "Ina?" "Wallahi ban sani ba, sai dai ki kira shi" Sai da ta ja lokaci kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta tashi, tana tunanin ta ina ma za ta ganshi da zai ce ta je, me ma za ta yi masa. Tana tafe tana waige-waige, kawai ta ganshi a can wani wuri yana amsa waya, ƙarasawa tayi, ta tsaya ya gama wayar, da alama wayar ta shafi aiki ne, yayi ya kammala sannan ya waiwayo ya kalleta. Yanayin kallon da yake yi mata, sai da ta tsorata kamar zai kai mata duka, ya tsuke fuska sosai ya fuskanceta, sannan ya ce "Daga rana mai kamar irin ta yau, ko a waya, ko a zahiri idan ki ka kuma yi mini shouting, ko gaya mini duk maganar da ta zo bakinki, i will mercilessly deal with you, i am not your mate" motsa baki tayi za ta yi magana, amma ta kasa, ya juye mata ya koma mata Vipernsa sak, fuskar nan sam babu annuri. Amma ta sake tattaro jarumtarta ta ce "Ba shouting na yi maka ba, gani nayi idan ba haka nayi maka ba ba zaka zo ba, kuma... "Keep quiet malama, idan ma na zo idan ban zo ba ina ruwanki?" Ta ɗago ta kalleshi, ya sake tsareta da idonsa, dolenta tayi ƙasa da kanta. Ya nuna ta da yatsansa ya ce "This is my last warnin, idan ki ka sake zaki sha mamaki, wuce mu je" zungui-zungui tayi gaba, ya biyo bayanta, zuciyarta kamar ta fashe dan haushi, deep down kuwa a zuciyarsa kewarta yake yi, yanayin yadda tayi masa magana, da yadda ta daina kiransa ne ya ƙara tunzura shi, amma ya ji daɗin ganinta a wurin mahaifinsa da yadda ta nuna damuwarta. Tun daga nesa liti ya hango su, ya san babu arziki faɗa suka yi, ya zo ya zauna Shahida ta zuba masa abinci ta bashi. Liti sai tambayar ƙwaƙwa yakw yi wa Viper, a kan aikin me yaje yi. Suna zazzaune sai ga Alhaji mu'azzam ya zo ya duba baban Al'amin, aka yi sa'a ya ɗan sakar masa fuska, suka yi magana a kan rashin lafiyar Abbu. Har suka keɓe suka yi magana, a kan aikin da yaje yi, tare da shi Viper aka kai ɗan mama can kudancin Najeriya, in da zai karɓi nasa horon na musamman, sai dai bai kai na Al'amin tsauri da takura da kuma daɗewa ba, shi shekara guda kawai zai yi. Suka gama maganar, Kankarofi yayi musu sallama zai tafi, Nabila ta ce "Honorable dan Allah ku ajiyeni a hanya, na samu abin hawa" Kankarofi ya ce "Babu damuwa, ina motarki ne?" "Ta lalace ta zama gwangwani" Ya ce "To Allah ya mayar da sabon alkhairi, amma babu risk a a hawanki public vehicles, ina masu fita da ke?" "Ai na gama aikina, ba wani abu da zai same ni in sha Allah" sai ya lura kamar tana sane, basarwa yayi ya ce "Shikenan muje" yayi musu sallama amma Viper bai sake cewa komai ba. Wami abu mai zafi ya tsayawa Viper, ganin sun jera ita da Alhaji mu'zzam sun yi gaba, amma ya dake ya shanye, yayi shiru ya maze, dan idan ya ce zai tanka ɓatacciya za ayi. Yana Asibiti har dare, Liti ya ce "Boss ka koma gida, mu sai mu kwana da Abbun, ka je ka samu ka huta" Viper ya ce "Ba zan iya tafiya ba, gani nake idan na tafi komai zai iya faruwa, gara na kwana da shi kawai". Walid ya ce "Ba gamu ba, babu abin da zai faru in sha Allah" "I am sorry, ka bar ni kawai" Walid ya ce "To shikenan, na ga dare ya fara yi, bari na raka Shahida gida, sai na dawo" Viper ya ce "To a sauka lafiya" A hanya Shahida take ƙara bawa Walid labarin yadda aka kashe Abba, ya jajanta masa sosai da sosai, saboda abin gwanin ban tausayi, sa'ar da aka yi shi ne an kama yaran da suka kashe shi ɗin. Bayan ya dawo tare suka kwana su uku tare da Abba, yana kan gado, suka yi shimfiɗa a ƙasa, suna hirarrakin su ƙasa-ƙasa dan kar su takura masa, har aka jima kuma su ka yi bacci. Viper kuwa idonsa biyu, ransa a matuƙar ɓace da abin da Nabila ta yi masa, ga kuma kewarta da take ta addabar ruhinsa. Abbu kuwa kallonsu yayi, yadda suka jere su uku a ƙasa a kwance, ya sake jinjina girman ikon Allah. Dukkannin su, kowanne gidansu daban, ba su haɗa wata alaƙa ta jini ba, sai ta rashin jin su, amma sun riƙe juna da tsantsar amana, da ƙauna. Da ya motsa dukkaninsu ƙoƙarin su, su ji meye damuwarsa me za su yi masa, sai ya ji ina ma ace duka nasa ne. Da haka gari ya waye, suka takura Viper ya je gida ya yi wanka sai ya dawo su ma su tafi. Haka aka yi, ya tafi ya je yayi wanka, ya ɗan huta, ya ga message ɗin Nabila "Assalamu alaikum, ya mai jiki? Ba zan samu zuwa yau ba, daga wurin aiki zan je ganin likita, idan kuma na kammala da wuri zan zo in sha Allah,

Chapter 105 of 121