yi shagalin suna sosai da aka haifi Al'amin, saboda yana tashen kuɗi a lokacin.
Tana kyautatawa 'yan uwanta na ƙauye ma, ciki har da sauran danginta da 'yan uwanta.
Rahila ta shiga ta fita, ta zama ƙawar Zahra sosai da sosai, Ibrahim ba ya ɓoye son da yake yi wa zahra, dan ko a gaban waye ko sun yi faɗa ba ya canza mata suna daga baby Zahra, ciki har da gaban 'yan uwansa.
Makaranta mai tsada sosai ya saka Abubakar, tun Al'amin bai cika shekaru uku ba, shi ma aka saka shi, saboda kukan da yake yi idan Sadik ya tafi makaranta.
Akwai soyayya mai ƙarfin gaske da shaƙuwa, a tsakanin Abubakar da Al'amin, cikin soyayya da kulawa suke rayuwarsu a tskanin Abbu da ummin su.
Ibrahim ya biya wa kansa umara, ya je da shi da Sadik, shekara ta zagayo, ya biya wa Zahra da Al'amin suka tafi, hakan ya ƙara hiafar da cecekuce a tsakanin dangin Ibrahim, wai saboda tsabar mugunta, ya biyawa yaran da zuwansu umara makaruhi ne, alhalin su ga su.
Sai dai a lokacin da suke maganganun, a lokacin yake ƙara nuna wa duniya irin son da yake yi wa Zahra da yaransa, a cewarsa ita ta juri tsantsar talaucinsa, yanzu kuwa dole ta huta fiye da kowa. Ta kammala karatun ta, ya ce sai ta juya degree, ta ce ta gaji, hutawa za ta yi, ya ce bai yadda ba.
A lokacin ba ta da wata aminiya da ta wuce rahila, rahila ta yi ta cewa kashe aurenta za ta yi, saboda ta gaji da zama da mijinta baban su Abba, Zahra tayi ta rarrashinta da nuna mata illar hakan, ta ƙara ƙaimi wurin taimakawa rahila, dan kuɗin makarantar su ma, ita take biya, tana bawa Rahila haƙuri a kan ta zauna ta kula da yaranta.
Dangin Ibrahim tsanar da suke yi wa zahra'u, suka haɗa har 'ya'yanta, suka din ga cewa asiri ta yi masa ta mallake shi.
Duk ƙoƙarin da Zahra ke yi a kan rahila, sai da ta kashe auren nan, ta ce ba zata iya ba ta gaji da rayuwar matsi, zahra ta sha bata labarin wahalar da suka sha, kan Ibrahim yayi arziki sun sha kwana fiye da uku, ba su ɗora tukunya ba, amma ta ƙi fahimta.
Ibrahim yana ta fafutukar, ta tafi bautar ƙasa, ta hau laulayin wani cikin, dan ma Allah ya taimake ta, ba ta ɗaukar ciki a kai a kai, dan lokacin, Al'amin ma ya kusa shiga Jss1 Abubakar yana da shekaru goma sha biyar.
Ta haɗu da ciki mai laulayi sosai da sosai, hajiya mamanta ta ce, ta koma gida ko wata ɗaya tayi, a kula da ita, Ibrahim ya ce tayi haƙuri, a bar masa matarsa yana kula da ita.
Rahila tayi ta zuwa tana yi mata aikace-aikace, da kula mata da su Abubakar.
Sadik da Al'amin su na da banbancin halaye, Sadik yana da haƙuri, da fara'a kamar ummin su, Al'amin kuwa sa ne, ba ka dariya sai hamma. Ba ya fara'a ko wasa a cikin yara baya yi. Idan kuwa yayi wasa cikin yara to tabbas sai wani yayi kuka, domin kuwa wasansa na kasada ne, kwaikwayon tsalle-tslle, da wrestling shi kawai yake yi.
Idan ka ga yana wasa wasu lokutan, ko yana dariya, tare da Abbu ne, ko Abubakar, Ummin ma faɗa suke yi, saboda tana yi masa faɗa a kan, rashin jin da yake yi na kasada.
Tun da suka ga Ummi da ciki suke murna, Abbu ya ce musu, baby girl za a haifar musu, Al'amin ya din ga murna, shi ma za ayi masa ƙanwa, yana son ya ga yana da ƙanwa mace, ya din ga hasaso irin kulawa da gatan da zai yi mata.
Yana jss1 sport master ɗin su, ɗan karate ne, Al'amin ya takurawa Abbu yayi masa register a makarantar karate, Ummi ta ce ba ta so, ya daina biye wa Al'amin, amma ya ce mata ba a dankwafe yaro.
Ta sha wahalar cikin nan sosai, da ya isa haihuwa, sai tiyata aka yi mata, aka ciro baby girl mai kama da ita, tun a asibiti ya ce sunan zahra zai saka mata. Nan ma 'yan uwansa suka hau surutun, bai saka sunan uwarsa da ta mutu ba, sai na mace, macen ma 'yar ƙauye.
Al'amin ya ƙallafa ransa a kan jaririyar nan, ko Sadik da yake yayansa, sai ya yi da gaske yake bari ya ɗauketa, 'yan barka ma rashin mutunci yake yi musu, ya ɗauketa ya ƙanƙame ya haɗa rai yana muzurai, ba za a ɗauketa ba.
Ana ta shirin suna, jikinta yaƙi daɗi daga ita har jaririyar, jaririyarma jaundice ya kamata, sai da aka sakata a kwalba, kwananta biyu 'yar ta koma ga Allah.
Al'amin ya shiga tashin hankali, ko abinci ya ƙi ci, saboda yadda Allah ya saka masa son yarinyar.
Zahra ta din ga wani irin zazzaɓi, haɗe da jijjiga, sai da aka kaita ɗakin duhu, an kaita da daddare da asuba ita ma ta koma ga mahaliccinta.
Tamkar ƙaramin yaro, haka Ibrahim ya din ga kuka, ya fita hayyacinsa, duk da ƙanƙantar shekarun Al'amin, ya san mutuwa, ya san idan aka yi ta ba a dawowa.
Sai dai ya kasa kuka, baya magana, baya cin abinci, saɓanin sadik da ya din ga kuka, da yawa sun ɗauka tsabar taurin rai ne, na Al'amin ya sanya ya ƙi yin kuka, sai dai a kwana na uku da rasuwar zahra'u, aka wayi gari aka tarar ya sassanƙare, jikinsa babu numfashi. Shima aka kwashe shi zuwa asibiti.
Ibrahim da sadik, suka ƙara shiga matsanancin tashin hankali da kiɗima, sai Alhaji sammani da dangin zahara'u da rahila, su ke ta damuwa.
Sai da Al'amin yayi sati biyu a asibiti, ƙarƙashin kulawa ta musamman, bai taɓa zaton haka yake ƙaunar ummi ba, haka yake sonta ba sai bayan ta mutu.
Aka watse daga zaman makoki, Hajiya ta ce "A bata su Sadik ta tafi da su, kan ya samu yayi wani auren". Nan ma ya ce shi dai tayi haƙuri ta bar masa yaransa. Ta ji haushin hakan, saboda a ganinta ita ma 'yarta ta rasa, yakamata ko yaya a ɗan bata yaran za ta ji daɗi.
Ya zamana daga shi sai su a gidan, wtaran haka yake saka su a gaba, yayi ta kuka, Sadik yana taya shi, Al'amin kuwa sai dai ya kom gefe yayi shiru idanunsa sun yi jawur, yayi ta ciwon kai.
Ibrahim ayi musu wanka, ya kai su makaranta, lokacin tashi, ya baro kasuwa ya zo ya kai su restaurant su ci abinci, su shirya zuwa islamiyya.
Sanin halin 'yan uwnasa ya sanya ya fito da duk wani abu, da abu da ya san mallakawa zahara'u, ya ce a raba wa su Al'amin, shi ya yafe gadon.
Nan ma ya sha caccaka da baƙaƙen maganganu, gaba ɗaya walwalar gidan ya zamana babu, rahila ta tsiri sintiri, da zuwa ganin su Sadik, ta yi musu hidima, Ibrahim ya nuna mata ba ya so, ita kuma ta ce saboda Allah take yi, da zumuncin da yake tsakanin su da Zahara.
Sai dai a gefe, ta fara shiga malamai, dan ya auret, ta bi ta wurin sammani abokinsa, a kan ya lallaɓa shi ya aureta, ta kula da yaran Zahra'u, ita dai tana ƙaunar su fisabilillahi.
Sammani kuwa ya wuce mata gaba, duk da Abbu ya nuna ba ya so, shi hana cikin alhinin rashin matarsa, amma tasirin sihiri, da yadda sammani ya din ga lallaɓa shi, da nuna masa saboda yaran zai yi auren, ya haƙura ya auri Rahila, ta tare da nata yaran har su uku.
Hajiya ta ji haushin hakan, ta san alaƙar rahila da Zahra'u, amma ta so ko yaro ɗaya ya bata, saboda Zahra ce kawai ta rage mata, sai da ta binne 'ya'ya bakwai, ita ma da ta tsaya, ta koma ga Allah sai ƙanwarta guda ɗaya da suke uba ɗaya, baban su ya rasu babarta ma da ta kasance abokiyar zamanta ta mutu ta bari, ta riƙeta kamar 'ya.
Da fari kamar gaske, Rahila take kula da su, dan sadik ya fara sakewa da ita, tun da dama sun santa, ban da Al'amin da mutuwar umminnsu ya ƙara masa miskilanci.
Aka shafe shekaru uku, ko ɓatan wata ba ta yi ba, duk da tana kamantawa, amma ba ta iya ɓoye banbancin su da 'ya'yan da ta haifa. Ibrahim ya riƙe mata nata yaran, ganin nasan ma suna samun kulawa daga gare ta
Sannu a hankali, ƙawaye da dangin Ibrahim, suka nusar da ita, duk wannan wahalar da take yi, a banza, tun da ba ta haihu da shi ba, kuma yaransa maza ne, dan haka ta nema wa kanta mafita.
Nan ta ƙara riƙe wa bin bokaye wuta, ta fara ƙoƙarin cire wa Ibrahim son yaransa, saboda yadda yake tsara irin rayuwar da yake son ɗora su a kai, duk da yana kamanta yi mata kara a kan 'ya'yanta kamar nasa, amma yana nuna wa su Al'amin so, mussaman Al'amin da yake ƙarami, kusan kullum yana tare da shi, wataran ya ƙi cin abinci, sai ya zaunar da shi ya bashi, ko ya kwana da shi wuri ɗaya, saboda ya ɗebe masa kewa.
Wannan soyayar ba ƙaramin ƙular da rahila take yi ba, dan haka ta zage, da shiga da fita, a hankali soyyayar da yake yi musu, ta fara ja baya, ta fara wulaƙanta su, tana hantarar su, ba ta tsaya a nan ba, ta haɗa da hana su abinci.
Sadik take iya sarrafawa, yadda take so, ban da Al'amin, da kome za ta yi masa ba zai yi abun da take so ba.
Ibrahim ya zo ba ya iya cewa komai, azaba iri-iri, duk wani laifi da Al'amin zai yi, Sadik zai karɓi hukuncin, ba ya ƙaunar ya ga an taɓa masa Al'amin.
A haka ta samu ciki, tana murna tana fatan ta haifi namiji, ta haifo 'ya mace, wato shahida.
Ba haka ta so ba, amma ko ba komai dai hankalinta ya kwanta ta haihu da shi.
Ta frara yi wa su Al'amin horon yunwa, tunanin Sadik, yaya zai samo abun da zai bawa Al'amin, ƙiri-ƙiri da gatansu, amma Sadik har jari bola yake yi, saboda ƙaninsa, ya san Al'amin ba ya ga maciji da yunwa ko kaɗan.
Mutanen unguwa suka fara surutu, amma tayi burus da su, a lokacin ne suka sake komawa cikin gari ɗan agundi, saboda matsalar da Abbu ya samu a kasuwa, na damfara da aka yi masa amma gida suka koma mai kyau shi ma.
Ta saka Abbu ya ɗaukar mata yaranta, Abba da Nazir yake tafiya da su kasuwa, amma ta hana ya din ga tafiya da su Sadik, lokacin Sadik yana da shekaru ashirin, Al'amin kuma sha biyar.
Ta saka ya cire su daga makarantar kuɗi zuwa ta gwamnati, ta nu na wa 'yan uwansa ta fi su iya barikanci, ɗan tallafi duk da yake ba su ta hana gaba ɗaya.
Hajiya sai dai ta zo ganin su Sadik, ba za a taɓa barin su, su je in da take ba, wani zuwa da tayi ta shiga tashin hankali, ganin Al'amin na yawo ko takalmin sawa babu. Ta ce "Rahila ki ji tsoron Allah, zumunci bai ce haka ba, wane irin riƙo ki ke yi wa yaran nan haka?"
Ta kada baki ta ce "Irin riƙon da ya dace da su mana, idan bai yi miki ba ki kwashi tsiyarki ku koma ƙauye"
Ibrahim ya dawo, ta kitsa masa ƙarya da gaskiya, ya ce wa Hajiya kar ta sake zuwa, idan yakamata ya sako su a gaba ya kawo mata su ta gansu.
Tana kuka Sadik na kuka, ta koma, ta ce da yardar Allah, ba zata sake taka gidan ba, da sunan zuwa ganin su Al'amin.
Al'amin duk ranar da yake jin yunwa, sai ya kwanta ya ce ba shi da lafiya, ba za shi makaranta ba, aikin ƙarfi babu wanda Sadik baya yi, saboda kar Al'amin ya zauna da yunwa saboda ya san baya jureta ko kaɗan.
Ta kai ta kawo, Rahila har sakawa take Abbu ya kama Sadik ya zane shi, dama Al'amin ba ya taɓuwa, tun ranar da ta saka aka dake shi, Abbu na fita, ya kama Nazir a waje, yayi masa dukan kawo wuƙa, duk wani skills da yake samu, a wurin karate ya sauke su a kan Nazir da ya ma ɗan girme shi.
Amira kuwa bala'in tsoronsa take ji, tun da ya taɓa ball da ita, ta targaɗe hannu.
Rayuwa ta cigaba a haka, har Al'amin ya yi candy, Sadik ya tsaya tsayin daka, ya shiga polytechnic.
Abbu ya bar su babu sana'a, ba abun yi, ya cire hannunsa daga kan karatunsu, amma ya ɗauki agololi ya kai kasuwa.
Ana haka 'yan daba ƙanana masu tasowa suka addabawa unguwar , su yi sare-sare, ko su je su tsokano 'yan wata unguwar. Ga Al'amin da yawon tsiya, idan yayi dare sai Sadik ya fita nemansa, idan ya gano shi da ƙyar suka dawo gida, sai su tarar Abbu ya rufe gida, wai sun tafi yawo, su koma in da suka tafi su kwana.
Rayuwa ta yi wa su Al'amin tsanani, ga rashin uwa, ga ƙiyayyar uba, da makircin matar uba, ga ƙiyayyar dangin mahaifi, dangin uwa kuma sun watsar da su.
Aka zaɓi Al'amin a cikin matasan da zasu je youth game, su wakilci Nigeria, Rahila ta ziga Abbu ya ce ba za shi ba.
Aikuwa ya zuciya, ya bar gidan, ya ce barin garin zai yi, Sadik ya dawo yana nemansa, Amira ta gaya masa abun da ya faru, ya bazama neman Al'amin, da ƙyar ya gano shi, ya lallaɓo shi suka dawo gida, Amma suka tarar Abbu ya rufe gida, ya ce shi ma Sadik ɗin ya bi Al'amin su bar duniyar ma gaba ɗaya ba garin ba, ba ɗan iska bane shi, da za su din ga dawo masa gida bayan goma na dare.
Sadik ya din ga rarrashin Al'amin, da ya riga ya zuciya, ya samo musu aron tabarma, suka shimfiɗa suka kwanta a waje, Cikin dare aka tashi faɗan daba, suna cikin bacci Al'amin ya ji an buga masa abu a ka, ya tashi a gigice, bai gama wartsakewa ba, aka danƙo shi, za'a soka masa almakashi, Sadik ya tashi a rikice, ya riƙe almakashin ya ce "Bawan Allah me muka yi muku? Mu ba 'yan daba bane"
"Amma ai 'yan unguwar nan ne ko? Fansa muka shigo ɗauka, dan haka duk kan wanda azal ta faɗa shikenan" ya fizge Almakashin ya soka wa Sadik a cikin sa! Maimakon Al'amin.
Ayshercool
08081012143
36
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
Ya saki Sadik a ƙasa bayan ya caka masa almakashin, cikin tsananin tashin hankali, Al'amin ya yi kukan kura ya danƙi ɗan daban, amma wani daga cikin yaransa, ya lallaɓa ya sake maka masa gora a baya, ya gantsare yana wani irin ihu, suka yi gaba suka bar su.
Ya din ga dukan gate ɗin gidan, yana ƙwalawa Abbu kira, ya koma kan Sadik, ya rungumo shi, yana jijjiga shi.
Sai da garin yayi shiru, sai kururuwar Al'amin yana kiran Yaya.
Maƙwabcinsu ya fito, na kusa da shi ma ya fito, aka din ga buga gidan su Al'amin, har aka tafi nemo mota, sannan Abbu ya buɗe. Sai dai ya shiga tashin hankali, ganin Sadik a kwance kamar mara rai.
Cikin tashin hankali Abbu ya tafi kici-kicin fito da mota, Al'amin ya zuciya ya ɗauki Sadik a kafaɗarsa, kawai yayi gaba.
Da ƙyar aka riƙe shi, aka saka Sadik a mota.
Al'amin sai zubar da hawaye yake yi, ya na kiran "Yaya ka buɗe idonka ka kalleni, ka tsaya yanzu zamu je asibiti"
"A galabaice, Sadik ya motsa ya riƙa hannun Al'amin, sai kuma hannunsa ya saki. ko da suka je Asibiti, aka tabattar musu da Sadik ya koma ga Allah.
Al'amin ya durƙusa a kan gawar, ya din ga rusa kuka, kukan da ko lokacin da umminsu ta mutu bai yi shi ba, maƙwabta na ta rarrashin Al'amin.
Cikin kuka Abbu ya ce "Al'amin komai ya samu ɗa na kai ne sila, ka sa nayi rashin ɗa mai biyayya"
"A'a Alhaji Ibrahim, kar ka sake ka ɗorawa Al'amin laifi, kai ne babban mai laifi, kana sane sarai unguwar nan babu kwanciyar hankali, ka bar su a waje, da ka buɗe musu sun shiga gida, koman dare ai da haka ba ta faru ba".
A daren aka yi wa Sadik sutura, Al'amin gani yake yi kamar a mafarki, awannin da suka gabata suna tare amma a yanzu wai babu Sadik. Kodayeke Abbu yana da gaskiya shi ne sila, da bai ce zai bar gidan yayi tafiyarsa ba, da haka baya faru ba, dan kuwa Sadik ba ya yawon dare.
Har jami'an tsaro sai da suka zo suka ɗauki bayanan abun da suka faru, sai dai Al'amin ya kasa magana.
Sadik ya tara ɗimbin mutane, yara da manya matasa da dattawa wurin sallatar gawarsa, kasancewar sa mutumin kirki.
Al'amin ya ji ina ma shi aka kashe, Sadik ya rayu, yayan nasa guda ɗaya tal da yake saukewa duk wata damuwarsa ya ɗauka babu ƙosawa ko gazawa, an kashe masa shi.
Alhaji sammani, ya yi wa Ibrahim tatas, a kan yadda ya koma soko a kan gidansa, tare da ci wa Rahila mutunci tsaf, a kan abubuwan da take aikatawa.
Ƙarshe ta shiga ta fita, ta raba abotar da aka yi shekaru ana ginata, suka rabu dutse a hannun riga, suka yi uwar watsi.
Depression ya nemi ya kama Al'amin, babu wand yake ta tasa, gashi yanayin halayarsa idan ba wanda ya sanshi ya saba zama da shi ba, ba kowa zai iya masa ba, saboda miskili ne, ga nuƙufurci, ba zai taɓa cewa wani ga damuwarsa ba, shi ba abokai ba, haka ya din ga ragaita a layi, raɗaɗin mutuwar Sadik taƙi barinsa.
Ya tafi wurin 'yan sanda ya tambayi, ko sun kama wanda ya kashe yayansa, suka ce masa bincike suke yi a kai, dan har a lokacin ba su tabattar da wanda yayi kisan kan ba, kuma a ranar ba Sadik kawai aka kashe ba.
Al'amin ya koma gida, yayi ta addu'a Allah ya sa a kama wanda ya kashe masa Sadik, duk da dare ne, amma a ko ina ya ga wanda ya kashe shi zai gane, dan kuwa ƙofar gidan su akwai security light.
Duk bayan kwana biyu sai Al'amin yaje, tun suna sauararsa har suka fara korarsa.
Ga matsi ya ƙaru daga gidansu, babu in da zai samu abinci, ya yanke shawarar fara zuwa kasuwa ya duba ko dako ya fara, sai da ya je ya tarar ashe dakon ma sai ka san wani, sai an san da kai, duk sana'ar da yayi tunanin farawa sai ya ga dole sai da jari, gashi Rahila ta cigaba da ziga Abbu, ya ƙara tsanar Al'amin wai shi ne silar mutuwar Sadik.
Al'amin ya fara gajiya da yunwa da take neman tagayyara shi, ya fara zuwa gida ya ɗauki duk abincin wanda ya tarar ya cinye, idan ya tafka wannan tsiyar, sai ya gudu ya kwana a kangwaye, gashi ya koma HND tun Sadik na raye, dama shi ne yake ta fafutukar tara school fees ɗin sa kan ya rasu, yanzu kuma ga yunwa da rashin kuɗin transfort dan haka ya daina zuwa makaranta gaba ɗaya.
Gashi ko a maƙwabta aka rasa wanda zai yi wa Abbu nasiha, ko su din ga taimakonsa, saboda ana ganin babansa yana da rufin asiri.
Yana can garin yawonsa, kawai ya hango wanda ya kashe Sadik, a tsallaken titi, da tawagar matasa 'yan daba, da gudun gaske Al'amin ya tsallaka titin, sai dai kan ya ƙarasa sun ɓace masa, cikin tashin hankali ya ƙarasa wurin wani mai ice ya ce "Malam dan Allah wanda ya wuce ɗin nan ina yayi?"
Ya kalli Al'amin ya ce "Meye haɗinka da shi?"
"Yayana ya kashe da almakashi, bai yi masa komai ba, 'yan sands suna ta nemansa"
"Taɓ, ka raba kanka da wannan. Madaki kenan gawurtaccen ɗan daba ne, hukuncin kisa ma aka yanke masa a gidan yari, amma muka ga an sake shi, duk ya gallabe mu, ya hanamu sukuni mu ma, sai dai ka bar wa Allah kawai" Ai Al'amin bai tsya jin ƙarshen zancen ba, ya shiga cikin unguwar ya din ga yawo, amma bai ga madaki ba.
Washegari da sassafe, ya koma wurin 'yan sanda ya gaya musu ya ga wanda ya kashe yayansa, su tafi tare da shi a nemo shi, an gaya masa sunansa madaki.
Wani ɗan sanda ya kada baki ya ce "Ka san mutum nawa madaki ya kashe aka ƙyale shi?" al'amin ya ce "Ni ina ruwana da mutum nawa ya kashe, ku kama shi a kai shi kotu ni dai".
"Ko an kai shi ma, za a sake shi, ka je ka yi haƙuri haryanzu bamu tabattar da shi ya kashe shi ba".
Kasancewar Al'amin yana kan tashen balaga, ya sanya ya tsaya yana yi musu rashin kunya, aka saka wani sageant, ya zane shi aka kore shi. Hakan yayi matuƙar tunzura zuciyar Al'amin, ya din ga jin jinin ɗan uwansa ba zai tafi a banza ba.
Ya din ga sintiri a unguwar da madaki yake, kasancewar ba su da nisa sosai, ya samu duk bayanin da yake son samu a kan madaki, da in da yake zama da shi da yaransa.
Ya je gida ya shiga kitchen ya samo, wuƙa sabuwa gal, ya je ya ɓoye, ya saka a ransa shi ma sai ya kashe madaki, ko da kuwa za a kama shi a kashe.
Sai dai aka yi rashin sa'a, Madaki bai fiye zama a unguwar ba, sai idan zai shigo yayi rashin mutunci, Al'amin ya din ga fakonsa, har ya yi wataran sa'a ya tarar yana nan.
Gadan-gadan ya ratsa tarin matasan da suke ɗauke da makamai suna shaye-shaye, ya nufi madaki da wuƙa.
Matasan suka mimmiƙe, amma madaki ya ɗaga musu hannu, a kallo ɗaya madaki ya gane Al'amin.
Kafin ya ƙarasa gaban madaki, sani ya sanya ƙafa ya taɗiye Al'amin dan haka ya faɗi a gaban madaki, suka kwashe da wata irin dariya.
Al'amin ya yinƙura zai tashi, madaki ya saka aka take masa kafaɗun Al'amin da ƙafa, yana ƙoƙarin tashi, amma cikin ƙarfin Al'amin ya tashi, madaki ya tako gaban Al'amin ya shaƙe wuyansa.
Take Al'amin ya ji kamar an shaƙe shi da wata muguwar sarƙa mai nauyin gaske, a take ya ji numfashin sa na neman ƙwace masa. Al'amin ya saki wuƙar ya koma kokowar raba hannun madaki da wuyansa, madaki ya tsare shi da jajayen idanunsa da ya rambaɗa musu farin kwallin tsafi, yana ƙyaƙyata wata uwar dariya, daga bisani kuma ya tsuke rai tamau, ya ƙara tsananta shaƙe Al'amin, sai da ya ga ya daina motsi, sannan ya watsar da shi a wurin, ya kalli wani ya ce "Ku kai shi arear su ku watsar"
"Ba za a saita ma hanya daga duniyar ba ya ci bulus kenan?"
Madaki ya girgiza kai ya ce "Yana cikin tsananin ɗacin rashin ɗan uwansa, idan aka yage shi daga sararin nan, hutawa zai yi, sai ya gane kuskuren da ya aikata na yinƙurin da yayi"
Suka ɗauki Al'amin suka kai shi unguwar su, suka jefar da shi a sume a gaban wani mai kayan miya, suka ce wa mutanen wurin "Gashi nan, ajiyarmu ne, zamu din ga bibiyar sa ku kira tsohonsa ya ɗauke shi idan yan buƙatarsa".
'yan unguwa suka ɗauke shu, suka kai shi gida, Abbu yana nan, aka kwantar da shi a tsakar gida, ana shafa masa ruwa, mai kayan miya ya gaya wa Abbu abun da yaran madaki suka ce, aka shawarce shi a kan ya kai maganar wurin jami'an tsaro, amma Abbu ya ce babu ruwansa, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, shi bai aike shi wurin 'yan daba ba.
Tun daga nan madaki ya mayar da Al'amin kamar karen farautarsa, ya saka rayuwarsa a gaba, wataran har cikin unguwar su yake aikawa, a nemo masa Al'amin, a kai masa shi har dabarsa, su casa shi da zalunci kala-kala, wai sa ya saduda ya nemi afuwar abun da ya yi wa madaki, dan ba a taɓa samun wanda ya yi abun da Al'amin yayi ba, ya rasto har dabarsa ya nemi ya kashe shi, yana ƙanin ƙanin bayansa.
Al'amin ya kalli madaki ya ce "Ka yi kaɗan na nemi afuwarka, baƙin kare kuma in sha Allah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Chapter 112
Chapter 113
Chapter 114
Chapter 115
Chapter 116
Chapter 117
Chapter 118
Chapter 119
Chapter 120
Chapter 121
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 121